Kenza eBookz

Diddigar kaya complete - Chapter 15

Diddigar kaya complete - Chapter 15

Diddigar kaya complete Chapter 15: Diddigar kaya complete Chapter 15. Wani haushi ne ya sake turnike Fatima, yau Faizan ke kare Fauza? A kufule tayi…

3,300 words

Wani haushi ne ya sake turnike Fatima, yau Faizan ke kare Fauza? A kufule tayi serving ɗinshi ta mike yana tambayarta bazaki ci bane? Ko bata juya ba tayi ficewarta, girgiza kai yayi yana mamakin halayyar da take nuna mishi tun daga shigowanta gidan, tabbas ba don shi jajirceccen namiji bane da se abunda Fatima tace a gidan za'a yi, ita in har ba'a yi ra'ayinta ba tayi ta fushi kenan tana kumbure kumbure?

Abincin shi ya ci ya koshi ya wuce toilet yayi brush da wanka ya zo ya sauya zuwa kayan bacci, kwanukan ya fitar da sauran abubuwan makulashen da ya sayon ya kai fridge ɗin kitchen, daga nan ya wuce ɗakinta ya samu wai har ta kwanta be tanka mata ba ya fito ya nufi ɗakin Fauza.

Suma ya sa mu sun kwanta kuma har ma sun yi bacci, fitowa yayi kawai ya koma dakinshi ya kwanta shima don yana da flight 8 zashi Lagos amma around 9 na dare ze dawo..

Washegari yana idar da sallah yayi sauri ya watsa ruwa ya shirya kan ya fice bayan ya leƙa Fatima da bata tashi Bama, don ita wai don ze yi tafiyar sassafe ta samar mai abinci bata san wannan ba sede in yaje airport ya karya a chan kan ya wuce, be damu ba sbd dama chan haka yake yi.

Tana jin fitan motan shi ta mike zaune, tare da sauka daga gadon dama tayi wanka kawai ta saka kaya ta yafa gyalen ta ta fito, tun wata biyun farkon aurensu ya koya mata mota kuma ya saya mata wata karamar Hyundai, direct kitchen na sama taje ta rufe da key, ta sauƙa kasa ma ta rufe ta haɗe keyn ta watsa jaka kan tayi ficewarta daga gidan.

Bayan su Fauza sun tashi tayiwa husna wanka itama tayi suka gyara gidan tare duk bata lura kitchen a rufe ba se bayan ta gama taje ta murɗa kofan ta ji shi a rufe, kitchen na sama ta dawo taji a rufe, da mamaki take kallon kofan kan ta wuce kofan Fatima ta murɗa shima a rufe, ajiyar zuciya ta sauke kan ta kama hannun Husna suka koma ɗakinta da Tunanin Fatima ba nisa tayi ba Dukda dae ita bata taɓa gani an rufe kitchen ɗin ba duk zamanta a gidan.

Sauran kazan jiya ta turawa husna da Admiral 'A Dukda yayi sanyi sossai haka dae ta lallaɓa husnan ta ci, bata san lokacin da zasu dawo ba hakan yasa bata ci ba ita gudun kar kuma basu shigo da wuri ba husna ta sake jin yunwa.

Wasa wasa har azahar babu wadda ya dawo a cikinsu gashi lokacin yunwa ya fara kama Fauza da babu abunda ta saka a cikinta, sauran kazan ta sake baiwa husna ta cinye.

Tun suna kallo har taji bazata iya cigaba da kallon ba sbd yunwa da yake shirin yi mata illa, bayan sun yi la'asar ta duba jakanta ta fiddo kuɗin da Jaddah ta sanya mata ciki tun randa za'a kawo ta tare da sanya hijab ta kama hannun husna suka fito, saide me gadin wadda yoruba ne yace mata oganshi ya mishi umurni kar ya barta ta fita daga gidan ba tare da izininshi ba.

Rokon shi ta fara saide tsoron rasa aikinshi yasa be kula ta ba, don Sam be san ita ɗin matar Faizan bace ba ma, haka suka hakura ganin tsayuwar baze yi musu ba suka koma ciki amma fa ganin magrib yayi ga dukkansu biyu yanzu sun jikkata don husna har ta fara kuka yasa ta sake fitowa ta roke shi ko ze kira mata ogan nashi da Wayanshi don ta san dae duk muguntar Fauzan in har ita ze iya mata to baze iya yiwa ɗiyar kaninshi ba, unfortunately layinshi baya wucewa.

Haka suka sake dawowa parlorn kasan tana jin yadda ƙasan cikinta ya riƙe kam kam kaman zata mutu, daurewa take tana rarrashin husna da yanzu ta fara kiran iyayenta se tausayin yarinyar ya kama ta, fita tayi ta fara duba gidan, ba irin gidansu bane bare ta iya zamewa ta fita, ba kuma zata iya faɗawa me gadi abinci babu zata je su saya ba sbd ta san hakan kaman wani tonon asiri ne ga Faizan wadda be kamata gida kaman nashi ace babu abinci ba me gadin ma ba yarda ze yi ba.

Hawaye ne ya gangaro mata ta sa hannu ta share, bata da waya bare tayi order a kawo mata har gida.

Komawa sama tayi zuwa dakinshi banda sassanyar kamshi shi babu abunda yake tashi, duk irin dubawar da zata yi bata samu wayan da ya ara mata jiyan ba. Kuma Sam bata kula da lockers ɗin gefen fridge ba waenda snacks ne a ciki da su dangin cereals tunda ta san ita nata babu komai ciki.

A ƙasa ta saka gwiwowinta ta ɗaura kanta a kan gadon hannunta dafe da mararta dake wani irin kugi, husna ce ta biyo ta tana kuka sossai ita tana jin yunwa, miƙewa tayi ta kama ta tace "mu je mu yi isha se mu koma ko mai gadin ze yarda mu fita"

Komawa ɗakinta suka yi ta bar ɗankwalinta anan a ɗakinta suka yi sallah shima ba natsuwa, ko da suka sake fitowa neman yiwa mai gadin bayani take saide be kula ta ba, masifa zata fara mishi saide bata da karfin hakan kasancewar bata bar ko ruwa ne ya shiga cikinta ba.

Rarrashin husna kawai take suna tsaye kaman marayu se suka ji horn, da sauri me gadin ya karasa ya duba ganin oganshi ne yasa yayi hanzarin wangale gate ɗin.

Wutar motar shi ne ya haske mishi su yadda suke tsayen yasa gabanshi faɗuwa. "Peter, me ya kawosu bakin gate?"

Peter yace "Sir tun da afternoon suke ta so su fita kuma ka ce kar in yarda in bar kowa fita bayan madame, ta sakani nayi ta kiran phone naka saide baya shiga sir"

Ganin hawaye a fuskokinsu duk su biyu ya sa ya san ba lafiya ba, da hanzari ya karasa da motan tare da buɗewa ya fito yana kallon su yace "Fauziyya lafiya? Me kuke yi a nan? Ina Zaku je?"

Kasa magana tayi se hawaye, da gudu husna taje ta rungume shi tana cewa

"uncle yunwa muke ji, tun safe Aunty bata ci komai ba nima sauran kazan da ka sayo mana jiya tayi ta bani kuma ya kare nima na fara jin yunwa, gateman kuma ya hana mu fita mu sayi abinci... Ina ta kuka amma Aunty tana ta rarrashina dukda itama tana kukan bata so na gani"

Wani irin yanayi marar misaltuwa ya shiga, yana rike da yarinyar yace

"yunwa? Fauziyya?? Me ya samu kayan abincin gidan?"

Kanta ƙasa tace a hankali "tun da muka tashi suke rufe"

Kokarin controlling bacin ran da ya shiga yake yace "Fatima fa?"

"Itama mun tashi bamu sameta ba"

Ze yi magana se ga knocking na Fatima, me gadi yaje ya buɗe ta shigo tana ganin Fauzan tace ."Oh baby ashe ka dawo? Ina ta kiranka tun six bana samunka, ka ga ban dawo da wuri ba ko? Wlh na fito lectures 6 mota na ya lalace masu gyara suka ta ɓata min lokaci yanzu haka ma na bar musu ne na biyo bo....."

"Fatimaaaa!" Ya daka mata tsawa muryarshi with so much anger yace "me ya rufe kitchens ɗin gidana tun safe?"

Zata yi magana ya sake daka mata tsawa "don't you dare lie to me, me yasa kika rufe kitchen kika tafi da keys alhali kin san akwai mutane a gidan? Kisa kike son yi? Fatima a gidana har a yini da yunwa??"

Kuka ta fashe dashi tana rasa abun faɗa don kwakwalwanta rasa irin karyar da zata yi tayi, in ina ta fara daga yadda fuskanshi yayi turning red ka san ranshi ya kai makurar ɓaci.

Kallon Fauza da bata sake Kallonsu ba yayi yace "Fauziyya shiga mota muje"

Wucewa Fauza tayi ta buɗe back seat ɗin motan shi ta zauna yayinda yake rike da hannun husna yana nuna Fatima da hannu wacce ta fara cewa

"A'a ina zakuje? Ga fa keys ɗin na dawo dasu..."

"Ki tabbatar kin tanadi furucin kare kanki a gareni kan in dawo don wallahi wallahi ranki se yayi mummunan ɓaci akan wannan abunda kika aikata, ko babu aure Fauziyya da husna sun fi karfin yunwa a gidana Fatima..."

Yana kai nan ya zagaye da husna ya buɗe mata gaba ta shiga, ya dawo side ɗin driver ya ja motar ya fice da gudu.

Hannu Fatima ta ɗaura a kai tace "na shiga uku!" Da gudu tayi cikin gidan don kiran Auntyn ta ta nemi mafita kan ya dawo, garin neman gira tana shirin rasa idanu, ita da ya kamata ta nisanta su gashi tana shirin kawo kusanci tsakaninsu, ina zasu je? Me zasu je suyi? Shine kawai tambayar dake ta mata kai kawo.

Driving yake yana sauraron sheshekar kukan da fauza ke yi, husna ganin Fauza bazata yi shiru ba yasa itama ta fara kuka tana waigawa ta kalli Fauza da ta ɗaura fuskanta a tafin hannunta ta kuma kwantar bisa cinyar ta tace "Aunty yunwa kike ji ko? Kiyi haƙuri yanzu zamu je mu ci abinci ko uncle?"

Shima Fauzan yake kallo a kai a kai ya gyaɗa kai yace "in shaa Allah Husna"

Restaurant mafi kusa ya kaisu, husna na fita ya zagaye ya buɗe mata kofan.

A hankali ta sanya kafa ta fito yace "kukan nan shi ze kosar dake ne?"

Bata tanka shi ba suka nufi ciki tana tafiya a hankali sbd cikinta da ya kama, tea me zafi ya fara ordering Allah ya sa VIP ɗinsu room ne so in ka shiga babu me ganinka, suna shiga ta nufi zubewa yayi saurin tarota suka karasa kan lallausan shimfidun dake wurin ya ajiyeta ta zame ta kwanta, sake kiransu yayi a landline dake wurin cikin mintuna se gasu da shayi kan ya basu ordern abincin da zasu kawo musu.

Da kanshi ya ɗagota ya miƙa mata shayin, kurbi biyu zuwa uku tayi se amai.. Da gudu ta karasa washing hand base dake wurin ta fara kwala amai, yana riƙe da kafadanta hannunshi ɗaya na shafa bayanta cikin tsantsar tausayi yake furta "sorry! Sannu am so sorry"

Daga ka ga aman ka san na wahala da yunwa ne, bayan ta gama suka sake dawowa ya bata tea ɗin ta sha, bayan ta shanye ya matsar mata da abincin da aka kawo ɗin tuwo ne da miyar vegetable, yatsina fuska tayi tana kallon tuwon, husna har tayi nisa a cin nata.

"Bakya so?" Kai ta gyaɗa don ita bata son tuwo, janyewa yayi ya sake kiransu tana ta Kallonshi da idanunta da suka kara girma, yadda duk tausayinsu ya kasa boyuwa a fuskanshi kaman ze yi kuka, tambayarta yayi tace rice and stew with plantain. Nan take ya faɗa musu suka kawo.

Zama yayi yana kallon yadda take cin abincin Dukda yunwa da take ji amma cin ba wani sauri ko hargagi a natse take kaiwa bakinta, ganin zata ɗago yasa ya ɗauke kai ya fara cin tuwon da taki ci ɗin.

Ba su suka dawo gidan ba don ya biya dasu sahad sun sayi abubuwa snacks masu yawa dangin su biscuit da su drinks da kayan tea su custard da oat, golden morn, coco pops ba abunda be saya ba.

Don anan ma yaga laifinshi da be ajiye musu abubuwa haka a ɗaki ba, tunda daga dakinshi har na Fatima akwai snacks da drinks kuma a fridge.

Pizza da shawarma spot suka je ya sake saya musu kan suka nufi dawowa gida, duk abubuwan da yake yi ɗin sede suyi hira da husna amma ita kam tak bata ce ba, tana jingine da jikin motar daga karshe ma bacci ne ya kwashe ta.

Ko da suka dawo gidan a gate ya tsaya ya cewa gate man ɗin ya janye maganan da ya faɗa duk sadda Fauza ta nemi fita ya barta ta fita.

Daga haka suka karasa ciki, zata ɗauki kayan yace ta bari.

Haka ta wuce ta Barsu da husna, bata ko kalli Fatima dake zaune a parlorn kasan ba ta haura abunta, kayanta kawai ta sauya ta kwanta akan gado sbd wani irin bacci da take ji.

Shi kam dashi da Husna suka kwashi kayan zuwa sama saida ma yayi sawu biyu, da kanshi ya shirya abubuwan inda suka kamata, kan ya kama hannun husna suka yi ɗakinshi tana cin shawarma.

"Yaya..!" Fatima ta kirashi ko kallonta be yi ba, tayi saurin binshi ɗaki ya juya ya daka mata wani hargitsatsen tsawa "get out of my sight tun baki sanya ni yin abunda zamu zo duka muna dana sani ba.."

Zata sake magana yace "outt!" Ya sake daka mata tsawa, da sauri ta fice tana kuka.

Duk abubuwan da ya kamata yayi yayi har wanka yayi ya sauya kaya kan lokacin husna tayi bacci, ɗaukanta yayi ya fito zuwa dakin Fauza.

Saida ya sauya mata kaya kan ya nufi gadon da ita ya kwantar idanunshi kan Fauza dake bacci peacefully, Adu'a yayi musu kan ya fito.

A hankali ta buɗe idanunta ta bi bayanshi da kallo har ya maida kofa ya rufe, ajiyar zuciya ta sauke kan ta gyara kwanciyarta cikin nazarin yadda zata ci uban Fatima na abunda tayi mata...

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.

🖤Gureenjoh🖤

21

Kimanin sati biyu kenan da faruwar abunda ya faru amma ta lura har yanzu ba wani shiri suke yi da Fatima ba, ya bata key ɗin kitchen na ƙasan gabaɗaya sbd rashin zamanshi don sun koma aiki ka'in da na'in, bata shiga harkar Fatima da take ji kaman ta hadiye zuciya ta mutu sbd yadda Faizan ya ɗauki fushi da ita akan abunda take ganin be taka kara ya karya ba, ita da ya kamata yanzu ya tarairayeta ya bata kulawa.

Ita dae Fauza tunda tana da husna bata da matsala don yarinyar na debe mata duk wani kewa, tare suke koman su cikin hira da dariya lokuta dayawa gani take kaman husnan sa'ar ta ce in gujel gujel ne ma duk haka suke zagewa su yi kayansu.

Kaman yau a parlorn ƙasa suka yi la'asar sbd cookies da suke yi kar ya ƙone, bayan sun idar suka zuba shi a tray me kyau, da Homemade pineapple juice tayi musu har zasu haura dashi se husna tace "Aunty mu je garden pls you promised fa cewa weekend nan zamu je ni kam I want to play with swing"

Fauza ta kalleta tace "ke kam kina da aiki mutum baya mantuwa? To mu je"

Juyawa suka yi suka fito, daga hannun hagunsu akwai wani ƙofa suka shige sun ɗan yi tafiya kaɗan se ga garden ɗin masha Allah kore sharrr, akwai lilo sbd hutawa, gefen shi akwai table da chairs, nan ta ajiye snacks ɗin, suka je suka hau Lilon suna lilawa Fauza na tsoron juwa bata so da karfi amma da gangan husna ke wullawa da karfi wadda ke saka Fauza ihun kiran sunanta ita kuma ta watse da dariya.

Zaune yake a balcony ɗinshi bayan ya dawo daga sallar la'asar sanye da farar jallabiya wacce bata kai kasa ba don kana iya hangen black trouser da ya sa daga ciki, fuskanshi yayi wasai yayi wani irin kyau, dariyar su da kuma ƙarar Fauza shi ya saka shi miƙewa tsaye, chan ya hange su suna ta lilo, lumshe idanunshi yayi ya buɗe kan tray ɗin dake gefensu, ba karya his tongue have been craving for the tatse of her food again barin ma tea ɗin nan da sati biyu kenan da yake so yace ta mishi yana fuskewa.

Jaridar ya ɗauka ya koma ɗakinshi ya buɗe kofa ya sauƙa ƙasa, a natse yake tafiya cikin ƙasaitacciyar tafiyar shi da already ya zamar mishi jiki ya isa garden ɗin.

"Husna bari! Bar lilawa hakanan jiri ze yarda ni" Ta faɗa tana runtse da idanu, husna kam ina ruwanta ta maida kafafunta baya ta cilla da karfi daidai ta buɗe idanunta ita kuma ta hantsila tana shirin faɗuwa yayi azamar tare ta duk idanu suka zubawa juna..

Da sauri kuma ta miƙe tsaye tana gyara ɗan kwalinta da ya zame ya bayyana baƙi sidik ɗin gashinta da ta tsefe kitson bukin ta ta tufke saboda ihun da husna tayi na "Uncle zo ka hau lilo tunda Aunty na tsoro.."

Ta faɗa tana wangale mishi wawulonta, murmushi yayi yace "zan zo babyn uncle amma yanzu cigaba da abun ki ke kam"

Ya karashe yana zama akan chairs ɗin wurin tare da crossing kafanshi, duburcewan da tayi yake kallo ƙasa ƙasa duk in yana wuri sakewarta ba sossai ba don tun sati biyu da in har yana gari ya kan shiga sau biyu ya duba su ya lura da hakan musamman idan husna ta rike shi da surutu ya ɗan jima se ta rasa natsuwa.

Juyawa kawai tayi tana cewa husna "in kin gama se ki dawo ɗaki"

Har ta juya ta ji sassanyar muryarshi me cike da natsuwa ya ce "Ji mana..!"

Baki ta tura tace a ranta se kace wata budurwa da ake shirin tarewa a titi.

Juyowa tayi bayan ta gyara bakin da ta turon tace "Na'am"

Yace yana kallonta kai tsaye wadda har tsikar jikinta take jin kallon "Ni dodo ne da in na zo wuri kike guduwa?"

Bakin ta sake turowa tana cewa a ranta "ai ka fi dodon ma razanarwa, in ka so kayi kirki in ka so ka tabka tsiya ko a gyalenka"

A fili kuma tace "A'a kawai ina da abunda zan yi ne a cikin"

Yace "ok, before then zan samu shayi?"

Kai ta gyaɗa mishi kan ta juya ta fice, cookies ɗin ya ɗau ɗaya ya sa a baki yana mamakin yadda ta iya abubuwa haka masu daaɗi.

Cikin mintuna da basu fi ashirin ba ta dawo da tray me ɗauke da karamin glass tea flask da cups ɗinshi a jere a gefe, a gabanshi ta ajiye tana kallon yadda yayi nisa a cin cookies ɗin nata.

A ranta tace "ko tayi ba'a yiwa mutum ba ya zage ya cinye mana abunmu"

Kaman kuwa ya san me take cewa yace "daina min kallon ba'a gayyaceni ba na ci, ladan kati na da kika ƙarar ranan ne"

Wara idanu tayi a kanshi yana tsiyaya tea ɗin a cup bayan ya gama ya ɗago yace "yes"

Ta langwabe kai tace "to Ayya in sake maka cookies ɗin ka bani in sake waya dasu? Bana jin daaɗi yadda na kwana biyu ban ji su ba"

Yace "no bana son wannan, wani abu daban nake so"

Ta Yi saurin cewa "menene?"

"Zaki dinga dafa min wannan tea ɗin kullum"

Da saurinta tace "eh na yarda"

Murmushi ya saki wadda ya sakata kusan shagala da Kallonshi yace "wayan na sama in mun haura zan baki"

Tsallen murna tayi tana cewa ta gode, kallon da yake mata yasa ta natsu ta juya ta wuce cikin don bazata iya zama a inuwa ɗaya dashi ba Sam bata iya sakewa.

Kaman yadda yayi alkawari bayan sun hauro da Husna ya bata ta kai mata, taji daaɗi sossai amma ta ji haushi da ta duba taga ya goge hotunan da tayi a wayan kuma da gayya ne tunda ga na matarshi da nashi na ciki nata ne ya goge, a daren suka sha hira da jadda har da su fa'iza da faaazila sun gaisa sbd tayi kewarsu.

Mammi ma sun jima suna waya kan ta ba husna ma ta ishe ta da surutu, bayan sun gama ta bata wayan ta maida mishi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull