Kenza eBookz

Diddigar kaya complete - Chapter 16

Diddigar kaya complete - Chapter 16

Diddigar kaya complete Chapter 16: Diddigar kaya complete Chapter 16. Tun daga wannan rana kullum da safe da dare kaman ka'ida se tayi mishi tea ɗin nan,…

3,340 words

Tun daga wannan rana kullum da safe da dare kaman ka'ida se tayi mishi tea ɗin nan, yawanci tana samun shi ko a dining ko a parlor ta ajiye mai, sadda Fatima tayi noticing kusan hauka ta saka mishi ai ba bata iya bane be ce yana so bane, shi kuwa namijin duniya kai tsaye ya ce mata na hannun Fauza yake so ba nata ba shiyasa be tambayeta ba, tayi kukan maganan nan, kudirinta da haushinta kan Fauziyya kuma ya ƙaru, dukda Auntyn ta tayi fushi me girma da ita sbd abunda tayi kwanaki tace ya so lalata musu aiki don in ta bari Faizan ya fara tausayawa Fauza so ze iya shiga idan kuma so ya shiga tabbas ze saka alamar tambaya akan son da yake yi mata ita.

Ta dawo daga lectures tana haurowa suka kusa cin karo da fauza dake shirin sauƙa da kayan tea ɗinshi da yanzu kenan ya gama sha take shirin sauka dashi, tare ta Fatima tayi.

Matsawa tayi zata bi ta gefe ta sake tare gefen, tana kallonta tace "Fauza me kike nufi da mijina?"

Har kaman bazata amsa ba se kuma tace "me kuwa nake nufi? Last time da na bincika duniya sun sheda Cewar matan Faizan biyu ne, ko kunnuwanki sun toshe ne a sadda amsa kuwwa ke bayyana cewa an shafa Fatiha fauza ta zama ta Faizan?"

Wani irin takaici ne ya zowa Fatima wuya "ke har kin kai macen da zaki yi ikirari namiji kamille irin Faizan ze so ki? Sauran wasu ce fa da sauran shaye sha...."

"Shhhhhhhhh" Fauza ta faɗi tana sa mata hannu a lips ɗinta tace "wannan kuma tsakaninmu ne kin gane ko? So kiyi ta kanki gwara ni ban bi hanyoyi masu yawa da haramci wurin mallakarshi ba, ban kuma zauna na ɓata hawayena wurin kukan in ban same shi ba zan mut....."

Ɗaga hannu Fatima tayi zata mareta tayi saurin tarewa wadda ya saka tray ɗin hannunta faɗuwa ya fashe tartsatsa, hannun Fatima ta cillar wadda ya sakata loosing balance ta tafi suuuu tana kwala ƙara.

Razanar da tayi yasa Dukda bata faɗi kan cikinta ba cikin ya ƙulle har jini ya balle mata, Da sauri ya karaso yana ambaton innalillahi wainna ilahi rajiun, Fauza ta buɗe baki zata mishi magana ya ɗauke ta da wani irin mari wadda ya sakata yin baya kafanta na dama ya sauƙa a kan glass da ya fashe a wurin, runtse idanuta tayi da karfi tana jin zafafan maganganun da yake jefanta dasu.

Bata buɗe ba har ya sauka ya kama Fatima dake kuka haikan sbd baƙin ciki don ta san wannan ciki kam se wani ikon Allah suka fice daga gidan da hanzari.

Ilai kuwa Fatima ta rasa cikin tayi kuka har kaman ba gobe, likitan ya tabbatar musu da cewa mahaifanta is weak already shiyasa abu kaɗan ya iya ɓarar da cikin, haka ta saka shi a gaba tayi ta kuka wadda ya saka tausayinta kama zuciyarshi, Baba prof ya kira ya sanar mai da ɓarin.

Ko da ya tambaya ta yaya hakan ya faru cewa yayi haka Allah ya tsara wadda kai tsaye Fatima ta dakatar da kukan tana kallon shi tace "Haka Allah ya tsara fa kace yaya? Ko kuma Fauza ce ta zubar min da shi?"

Be so baba prof ya ji ba sede a yadda tayi maganan dole ya ji, tambayar shi yayi ya hakan ya faru? Taya Fauza zata zubar mata da ciki? A gaban jadda da Baba Alhj yake amsa wayan wadda duk hankalinsu ya koma kanshi jin wani sabon zance.

Yace "Baba ban san me ya hada su ba na fito daidai lokacin da Fauziyyar ta hankaɗa hannunta wadda ya saka kafafunta gaucewa kasancewar tsaye take a kan stairs hakan ya saka ta faɗi amma bata faɗi kan cikin ba tsoratar da tayi ne ya saka cikin ɓarewa"

Kuka me karfi ta saka tana cewa yana shirin baiwa Fauza kariya bayan ya gani kiri kiri ita ta turo ta ta faɗi, yadda take ta maganganu har take nema ta wuce layi yasa baba prof yace ya bata wayan amma shima bata wani saurare shi ba sbd kuka da take tayi.

Allura kawai Faizan ya sa aka mata a take bacci ya ɗauke ta, Baba prof ya tambayi ina Fauza?

Se a lokacin Marin da yayi mata ya dawo mai, lumshe idanunshi yayi yana ɗan sauke numfashi yace "tana gida baba"

Baba yace "To ka tabbatar baka yanke hukunci cikin fushi ba, ka zauna kaji both side da yadda komai ya faru, abunda ya faru ya riga ya faru fushi ko hatsaniya ba ze dawo dashi ba, in har ka gama sulhunta gidan ka se ka Haɗani da Fauziyya ɗin"

Ya amsa a ladabce.

Baba Alhj yace "tayi wani abu kuma ko?"

Baba prof yace "tayi, amma wannan tsakaninsu ne, ba zamu saka baki ba sbd idan muka zama masu saka idanu da yawan magana akan rayuwar gidanshi to lallai zuciyarshi zata mace, mu zuba idanu kawai ya gyara gidanshi da kanshi idan ba ya nemi mu shigan bane babu anfanin shigan"

Duk sun gamsu da hakan prof mutum ne me hange sossai, sun fahimci dalilin shi na yin hakan don duk sauran yaran nashi ba idanu yake saka musu a Gidajensu ba Idan har ba sun zo gabanshi bane da matsala so na me ze saka akan su Faizan?

A ta ɓangaren shi kuma ya jima zaune zuciyarshi babu daaɗi, dukda be kwallafa rai a kan cikin ba amma akwai zafi ace ka rasa gudan jininka da kake fatan gani a duniya, abunda kuma ya fi bashi haushi yadda sautin Marin da yayi mata ya kasa barin kwalwanshi a kuma ranshi yake jin zafin hakan.

Mikewa yayi ya nemi izinin tafiya zuwa anjima ze dawo su kula da ita sossai pls, Dr yace ba damuwa ba ma lallai ta tashi yanzu ba don allurar ze jima yana aiki sbd bata samun cikakken hutawar ruhi dama chan.

A hankali yake murza sitiyarin motar yana amsa wayan Jafar a kasalance, yana faɗa mishi matarshi na asibitinsu tayi miscarriage, tausayinshi yasa Jafar yayi ta bashi baki murmushi kawai yake ɗan yi yana furta ba komai haka Allah ya tsara.

Bayan ya kashe be fi mintuna biyar ba se ga kiran Faisal wadda shi kuma lecturer ne a makarantar su Fatima, shima cikin tausayawa don a cikin abokanansu Faizan ne kaɗai be da yaro ko yarinya wacce zata kai shekaru bakwai sbd be yi aure da wuri ba, bayan yayi auren ma ga wani matsala nan na ɓarewar ciki.

Shima dai nuna mishi yayi haka Allah ya tsara.

A harabar gidan yayi parking ya sauka yana karewa gidan kallo kaman sabo ne a idanunshi, kofan motan kawai ya tura ya nufi ciki, a stairs na karshe ya tsaya yana kallon broken glasses dake zube a wurin, gabanshi ne ya faɗi ganin jini me yawa da har ya soma bushewa a wurin.

Da idanu yabi ɗigon ɗigon da jinin ya bi se ya kare kan kofar ta, yana haurawa husna dake zaune jugum ta tashi ta zo wurinshi da gudu kaman zata yi kuka tace "uncle na tashi bacci na samu Aunty tana ta kuka daga karshe ma ta koreni tace in zo in kalli MBC waye ya daketa?"

Shafa kan yarinyar yayi yace "Babu, na san ma ta daina husna je ki kalli cartoon ɗin bari na duba ta"

A hankali ya buɗe kofan ɗakin nata ya sanya kai ciki, jinin ya diga har gaban gadonta, tana kwance rub da ciki kafan na daga ƙasa ɗauke da kwalba me girma jini se diga yake har lokacin amma ita kam kuka kawai take yi, ita kanta ta rasa wannan kuka da take yi don tana da taurin zuciya ta rasa yadda aka yi abunda Faizan ya mata yayi mata zafi sossai da sossai.

"Subhanallah! Fauziyya?" Ya ambaci sunanta yana riƙe kafan, zare kafan tayi daga hannunshi ta maida gefe tana me cigaba da kukanta, sake riƙe kafan yayi ta sake zamewa, guwiwanshi ɗaya ya saka kan gadon ya mirginota tare da ɗaga ta zaune se ta kara sautin kukanta cewa yake

"baki da hankali ne zaki zauna jininki na ta diga haka a ƙasa in ya kare fa?"

Ba tare da ta kalleshi ba tace "se in mutu kowa ya huta tunda dama an tsane ni....." Cakkk magananta ya tsaya jin ya sungumeta gabaɗayanta tayi hanzarin saka hannayenta ta zagaye wuyanshi gudun kar ta faɗi....

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.

🖤Gureenjoh🖤

22

Yana kallon tsakiyar idanunta da suka kumbura don kuka yace "kika sake cewa tak zan sake ki ki faɗi se ki san ba'a sonki an tsaneki da kyau.."

Haushi maganan ya bata kawai ta sake sakar mishi kuka, idanunshi ya runtse kawai ya juya da ita a hannunshi suka nufi kofa.

"Baby taso ki zo" Ya kira husna, da gudu ta bisu ita ce ta buɗe mishi kofa ya sanya Fauziyyan, ta shiga baya ita kuma, ya zagaye ya shiga ya ja tare da ficewa daga gidan, minti minti yake kallonta har suka isa asibiti bata bar kukan da take yi ɗin ba.

Nan ɗin ma saɓarta yayi zuwa office na Jafar husna na binshi a baya, a kan gadon office ɗin ya dire ta yana cewa "washhh Allah, mutum kaman buhu"

Ɗago rinannun idanunta tayi ta zabga mishi harara ya ware mata nashi gabaɗaya alamar ni kike harara? Se tayi saurin maida kanta ƙasa, idanunshi na kan kumatunta da hannunshi ya kwanta har Jafar ya shigo daga ward.

"Subhanallah kai kam yau gidanka da alama ba sa'a kuka tashi, garin yaya ta taka kwalba haka kuma kuka barshi har kafan ya kumbura ba'a zo asibiti ba Faizan?"

Yana ɗauke idanu daga kanta yace "bayan mun zo da Fatima ne ta taka so saida kuma na koma na sameta hakan"

Yace "sannu Amaryarmu" Kai kawai ta ɗaga mishi. Cikin sanyin muryarta tace "Ina yini"

Ya amsa yana isowa da kayan aikinshi wurin gadon, se da ya gama kallon kafan kan yace za'a mata allura kan ya fara taɓa kafar, nan fa idanunta suka raina fata, duk bala'inta in aka zo fagen allura tsoron shi take.

Daga yadda reaction ɗin ta ya nuna ya gane tana tsoron Allurar, har aka gama Haɗawa ya matso yana cewa ta gyara idanunta na kan allurar yayinda gogan kuma nashi ke kanta, idanunta na da kyau a kowani yanayi...

Girgiza kai tayi muryarta har yana rawa tace a cire haka ba se an yi allura ba, a hankali taji shigar tattausan hannunshi cikin nata, Ɗayan kuma ya saka ya rungumo ta jikinshi, fuskanta ta binne bisa kirjinshi har yana jin hucin numfashin ta wadda a take gabaɗaya tsikar jikinshi suka tashi, har aka yi Allurar dukansu basu farga ba saida Jafar yace

"Romeo and Juliet an gama Zaku iya ɗagowa" Da sauri ya saketa yana ɗan matsawa ya zabgawa Jafar harara, ita kuma ta dukar da kanta.

An sha gumurzu kan aka cire kwalban tayi kuka sossai wadda har saida yaji a ƙasan ranshi be kyauta ba, bayan an gama ya ɗan Harare ta yace "taɓararriya kawai" Bakinta ta tura mishi ya kai hannu kaman ze ɗalle mata bakin tayi saurin saka duka hannunta biyu ta tare tana zare idanu wadda ya saka shi sakin murmushi yana girgiza kai, shi duk labarinta da ake bashi be ga ko ɗaya ba banda sanyin hali da tsoro kaman farar kura.

Fita suka yi da Jafar zuwa masallaci suka yi sallar magrib, bayan sun dawo suka shiga wurin Fatima sun samu ta farka, dukkansu biyu da kyar ta amsa musu gaisuwar su, babu wadda ya sake magana sbd ganin yanayinta se Faizan ne ya bata umarnin tashi su wuce, haka ta mike yace taje mota ta jira shi gashinan zuwa.

Ita kuwa tana zuwa motan ta buɗe baya ta shiga a dole tana fushi da shi na goyon bayan Fauza da yayi, yana isa office na Jafar ya samu ma har baccin wahala ya ɗauke ta.

Haka ya sa hannu ya ɗauke ta, ta gyara kanta kan kafadanshi ta cigaba da baccin ta, husna ta biyo bayansu Jafar da ya rakosu ganin Fatima a baya ya sa hannu ya buɗe mai gaba ya sanyata.

Ashar Fatima ta lailayo ta buga, da sauri ta sauko tace "Ya Faizan wai me kake nufi dani ne?"

Yana gyara Fauza yace "kaman ya kuma Fatima? Duk maganan da zamu yi yanzu ki bari mu je gida pls"

Tace "in bari mu je gida? Na rasa cikina sbd wannan karuwar...."

"Shutt uppp Fatima!!" Ya daka mata tsawar da har saida Fauza ta tsorata tare da watsakewa daga baccin da ya cika mata idanu.

Itama cikin kukan baƙin ciki tace "ba zan yi shiru ba yaya, ba zan yi shiru kayi ta zaluntata ba... Ta ɓarar min da ciki baka ce mata komai ba, asibitin ma ka zo ka ajiyeni kayi tafiyarka wurinta, ni da ya kamata ka ɗauko ka kawo mota baka ɗauko ni ba ka je ka dauko ta a hannu sbd tayi bacci, ni gani ƴar iska marar gata... To Alhamdulillah na gode Allah da baka sameni a watse kaman kofar taxi b......"

Mari yake shirin sauke mata sbd yadda ranshi ya ke tafarfasa Jafar yayi saurin riƙe shi.

Ita dae Fauza bata ko motsa ba banda idanu da take binsu dashi, sbd yadda idanun Fatiman ya rufe bata yi shiru ba tace "ka barshi ya mareni Jafar, ya mareni tunda ni ce karamar dangarshi me daaɗin hawa, ba se ka mareni zaka nunawa duniya cewa ni ɗin ba jininka bace, ba se ka mareni zan san cewa kana fifita wanchan karuwar ƴar shaye sha...."

Marin da bata sha ɗazun ɗin ba shi ta sha yanzu saida ta kusa kaiwa ƙasa, hannun da ya nuna ta da shi har yana rawa yace "Ki kiyaye ni Fatima, ki kiyayi ganin ɓacin raina kuma ki rufe min baki ki shiga motar nan mu tafi...!"

Jafar yace "Haba Faizan in ita ta rasa hankalinta tana faɗar abubuwan da basu dace ba kai be kamata ka biye mata ba, ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi har ita ta sauko kan ka nuna mata rashin kyautawar abunda tayi ɗin, zafin kishi ne kawai ke dawainiya da ita da kuma na rashi da tayi ka san dae se ta fi ka jin zafin hakan"

Kallonshi Faizan yayi yace "zafin kishi? In zafin kishin ne se aka ce a rashin hankali yake zuwa?" Juyawa yayi kanta yace "I can tolerate anything but don't u dare cross ur boundaries... Ki wuce ki shiga mota mu tafi I won't repeat myself"

Yana kai nan ya buɗe motar ya saka husna da har ta fara kuka, kan ya juya ga Jafar yace "zamu yi magana"

Daga haka ya zagaye ya shiga motar, ya tayar idanunshi na zube kan hanya, saida yayi kaman mintuna uku da tayarwa har yana shirin jan motan yayi gaba kan Fatima dake kuka ta shiga, ita dae Fauza sannu bata ce musu ba ya tsaya restaurant ya musu takeaway kan suka kofanufi gida.

Yanzu ɗin ma zagayawa yayi ya buɗe ya ɗauke ta, ko Fatiman be kalla ba ya nufi ciki, a kan gadonta ya ajiye ta har ya juya ze fice tayi saurin riƙe hannunshi wadda dukkansu saida suka ji har cikin ƙashinsu.

Fuskanshi ya juyo ya kalleta cikin sanyin murya tace "I'm sorry...! Ban san hakan ze faru ba da ban biye mata ba, pls kayi hak'uri" Ta karashe tana duƙar da kanta ƙasa.

Zama yayi yana ɗan murza hannunta dake cikin nashi Ɗayan kuma ya ɗaura a kan kumatunta da har yanzu yake kumbure ya ɗan shafa dukkansu suka lumshe idanu, wani sanyi ya ji a ranshi wadda be san na menene ba, ɗago idanunta tayi ta kalleshi dasu daidai shima ya buɗe nashi dake lumshe.

Chan ƙasan maƙoshi yace "it's not ur fault, haka Allah ya tsara cikin ba me zama bane... Amma me ya Haɗa ku?"

Tiryan Tiryan ta bashi labarin abunda ya faru bata ɓoye komai ba, yadda suke kallon juna a cikin idanu kuma ta bashi labarin ba rawar murya ko wani kame kame ya san cewa babu ƙarya a cikin labarin nata, murmushi ya saki kawai da nufin tsokanarta yace

"Eyye ashe ƴar gurguwa kunnuwanta na ji da kyau tunda har ta ji sadda loudspeaker ke sanar da cewa ita ɗin ta zama matar Faizan" Da sauri ta zare hannunta tare da kare fuskanta tana murmushi shima yana murmushi yace

"Haba ƴar gurguwa kunya kuma?" Baki ta turo tana cewa "ni Allah ni ba gurguwa bace"

Yana miƙewa tsaye yace "Toh Ladi chogal" Ihu ta sake tana kukan shagwaɓa ya fice abunshi yana dariyar shagwaɓar tata.

Se bayan ya fita ta saki murmushi ashe ya Faizan haka yake?.

Abincin da ya sayo ya koma ya ɗauko, a plate ya juye takeaway biyu da ruwa ya sa kan tray ya ɗauka ya kaiwa Fauza ɗin, yanzu kam be ce mata komai ba ya ajiye mata ya baiwa husna nata kan ya juya ya fita.

Na Fatima ya ɗauka ya nufi ɗakinta dashi Dukda yadda yake jin ɓacin rai na abunda ta mishi ɗin amma be fasa zuwa ba.

Tana zaune tana kuka ya shiga ɗakin, abincin ya ajiye mata kan ya juya shima yaje ya ci nashi, an riga an yi isha so ɗakinshi kawai ya shiga ya watsa ruwa yayi sallah, bayan ya idar ya mike yaje ya duba maganin Fauza ya nufi ɗakinta dashi.

Samu yayi tana sallah daga zaune, toilet ɗinta ya shiga yana yabawa tsaftarta don bayin ta ba zaka ce ana anfani dashi ba ya samu roba ya tare ruwan zafi ya samu Towel ya fito.

Husna tayi bacci ya ɗauke ta ya ɗaura ta kan gado ya sauya mata kaya daidai lokacin ita kuma ta idar.

Da taimakon shi ta koma bakin gado, ya janyo stool ya zauna tare da ɗaukan kafan ya ɗaura kan cinyar shi.

Ruwan da zafi sossai haka yayi ta danna mata tana raki tana yarfa Hannu, da muzurai da komai aka gama dannar ya bata magani ta sha, yace "dube ta..!"

Baki ta turo kayan bacci yaje ya ɗauko mata ya ajiye mata gefenta kan ya dube ta yace "akwai wani abu kuma?"

Kai ta girgiza yace "tohm se da safe Allah ya qara sauƙi"

Tace "thank you"

Ya juya ya fice ta bishi da kallo har ya maido mata da kofan ya rufe.

Maganin Fatima ya ɗauka ya nufi ɗakinta.

Har yanzu tana kuka, zama yayi bakin gadon yace "Fatima!" Yadda ya kirata ɗin dole ya sa ta ɗaga idanu, yace tashi zaune.

Mikewa tayi ta zauna, yace "menene matsalarki? Me yasa kike ganin an miki rashin adalci?"

Kallon tambaya ta ma kake ta mishi, kan ta ɗauke idanunta bata ce komai ba, shima ɗauke nashi yayi yace "Ki tashi ki ci abinci ki sha magani" Yana kai nan ya ajiye mata maganin ya tashi ya fice abunshi don ta ƙi magana.

Ya gaji ainun so yana kwanciya bacci ya sureshi, da asuba yana dawowa daga sallah kenan ya hangi ɓacewar mota kaman kuma ta Fatima, me gadinshi ya tambaya ya tabbatar mishi da yanzun nan Fatima ta fice.

Be ce komai ba ya haura yaje yayi kwanciyar shi don yau bai da wani aiki, be tashi ba se karfe goma da rabi.

Wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya ya fito, zaune ya same su suna kallon wani animation, zama shima yayi ta dube shi tace "Ina kwana?"

Ya amsa da lafiya yana kallon kafafunta yace "ya jikin?"

Ta amsa da "Alhamdulillah"

Duk shiru suka yi, ta san Fatima bata nan don itama ta hangi fitanta ta window kuma bata ji alamun dawowarta ba, ta barshi da yunwa kuma be dace ba tunda sun yi girki kuma ya saura.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull