Diddigar kaya complete - Chapter 17
Diddigar kaya complete Chapter 17: Diddigar kaya complete Chapter 17. Miƙewa tayi tana ɗan ɗingisa kafafunta ta nufi ƙasa da kallo ya bita har ta ɓace mai,…
3,354 words
Miƙewa tayi tana ɗan ɗingisa kafafunta ta nufi ƙasa da kallo ya bita har ta ɓace mai, sanye take da blue Indian gown da ya zauna mata sossai a jiki, be kai ƙasa ba se wandon shi da ake hangar adonshi daga gwiwar kafanta, yana da tsagu me tsayi daga gefe da gefe, ta ɗaura gyalen ɗaurin turban a kanta, ba karamin kyau tayi ba barin ma da ta gyara fuskanta ta saka lip gloss, bata jima ba ta dawo.
A gabanshi ta ajiye tray ɗin da ta hauro dashi ɗin.
Wani fancy bowl ta zuba kifi da yafi yanayi da soup don yayi kauri ta ɗaura kan plate ɗinshi, a idanu kaɗai abun sha'awa ne gwanin kyau bare a baki, akwai kuma warmer a gefen plates ɗin ta buɗe ta ɗaga miyan ta ajiye gefe doya da ta soya da kwai ne ya ji kwai ta zuba a plate ɗin kan ta matsar mai, ta sake miƙewa ta fice chan se gata da wani karamin tray wadda shayin shi da ta saba dafa mai ne ciki, ta zo ta ajiye mai ganin ya fara cin abincin ta tsiyaya mai da kanta.
Idanunshi na kanta yana kiyasta abubuwa masu yawa a ranshi yace "thank you"
Ta miƙe tana ɗan murmushi bata zauna a parlorn ba se ta nufi ɗaki.
"Fauza!" Ya kirata yadda kowa ke kiranta, da sauri ta juyo yace "kin sha magani?"
Kai ta gyaɗa mai yace "to dawo ki zauna" Dawowa tayi ba musu ta zauna a parlorn.
Bayan ya gama cin abincin da kanshi ya tattare kwananukan amma kitchen ɗin sama ya ajiye, a tare suka yi spending time me yawa Dukda babu me magana cikinsu banda husna da ta ishe Fauza da surutu sede ta amsa da eh ko a'a, azahar da aka kira ya saka su duk mikewa.
Ya fita be dawo gidan ba se yamma lis. Yanzu ma abincin ta kawo mai tuwon semo ne da miyan busashiyar kubewa sbd shi tayi tuwon don ta san yana so, ita kam indomie ta dafa ta ci, husna ma tuwon ta ci, se bayan magrib ya zauna cin tuwon gefen shi papers ne, bayan ya gama ya wanke hannu ya dube ta kan yace
"Dukda ban so ki fara karatu nan kusa ba saide Baba prof ya ƙi aminta da kudiri na hakan ya sa dole na shiga nemar miki admission kuma Alhamdulillah yau gashi kin samu, ina so ki san rayuwarki na da da na yanzu ba ɗaya ba, idan da kin yi abubuwa masu yawa ganin u r free yanzu kina da aure, matsayin aure kuma ya wuce duk wani matsayi da kike tunani, duk laifin da zaki aikata yanzu ki sani ba iya ke da zuri'arki ba har mijinki da ƴaƴanki wannan image ɗin baze mantu a idanunsu ba, sannan zunubinki se ya fi na da sbd kin wulakanta sunnah, in Allah ya kaimu gobe zaki je ki ƙarasa sauran abubuwan da ban karasa ba ki fara shiga aji"
Karɓan admission da ya miko mata tayi tace "na gode Allah ya saka da alkhairi in shaa Allahu zan kiyaye"
Wayanshi ne ya ɗauki ringing ganin baba prof yasa ya ɗaga tare da sallama bayan sun gaisa baban yace "Faizan me ya faru? Meyasa zaka bar matarka tayi yaji kuma ta kamo hanya daga Abuja zuwa yola a mota bayan ka san ba lafiya ne da ita ba?"
Yace "Yola ta tafi kenan? Hmm baba maganan nan ba na waya bane ta zauna a gidan in Allah ya sa Fauziyya ta warke zan zo"
Baba yace "Assha Fauziyyan ma ba lafiya?"
Yace "Eh amma da sauƙi"
Baban yace ya bata, miƙa mata yayi a ladabce ta gaishe shi ya tambayi jiki take ce mishi ai ta warke ma bayan sun gama ya ba jadda da suke tare itama ta mata sannu tana tambayar me ke damunta, tace kwalba ta taka amma da sauƙi.
Miƙa mishi wayan tayi tana Kallonshi, kallon lafiya kike kallo na yayi mata se tayi saurin kau da kai ta miƙe. "Gulma" Ya faɗa yana maida kanshi ga TV🤣
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤 DƘ
23
"Aunty fa wai kinga kuwa yadda ya ɗauke tan ne? Be fa hukunta ta na abunda ta aikata ba, wallahi zuciyata zata bu...." Zazzafar mari Auntyn ta sauke mata tace
"zuciyar ta buga Fatima, nace ta buga ɗin.." Dawowa tayi ta zauna ganganta tace "Fatima kin san irin asarar da kike shirin ja min? Kin fa san shekaru sama da goma sha wani abu nayi ina wannan tanadi meyasa se lokaci ɗaya zaki nemi watsar min da buri? Ni da nake zaune lafiya da kowa a gidan nan alhali zuciyata dankare take da haushi da tsanarsu duka ni me ya sameni? Toh wallahi ba zan ɗauka ba, bazaki zama wawuya shashasha, lusara a gidan Faizan har ki barwa Fauza shi ba..."
Cikin kuka Fatima tace "Aunty fa kin san makircin Fauza, da gangan yarinyar nan ta sauya gabaɗaya ni bata min rashin kunya bare shi ballantana in ce zasu samu sabani har ya sauya mata kamanni don baya daukar rashin kunya.."
Dakuwa Aunty tayi mata tace "baya ɗauka kin sani kuma kika mishi? Fatima wallahi wallahi zan iya sauya ki idan baki yi hankali ba bazan taɓa zama ki wargaje min mafarki na ba, sarai kin san tun kan na shigo gidan nan nake da buri a cikinshi, target na ba Sulaiman bane amma saboda in yi anfani dake yasa na auri Sulaiman yanzu bayan kin girma kuma ki kasa yi min komai ba, kin san wahalan da muka sha kan Faizan ya aureki"
Fatima tana kuka tace "Amma Aunty ai laifin ki ne, kin sanya min soyayyar faizan tun ban san target ɗinki ba, kuma mun yi yarjejeniya a aikinki ba za ki taɓa cutar da shi ba, wlh rasa shi daidai yake da na rasa rayuwata, bala'in son da ban san adadinshi ba nake mishi shiyasa kusancinsu da fauza ke kasheni... Aunty ke kika ce aure kawai za'a ɗaura ba ze shiga lamarin ta ba sbd tsanar da yake mata amma gashi nan reshe na shirin Juyawa da mujiya... Ko ki san yadda zaki yi dani ko kuma wallahi kowa ya rasa nashi Burin..."
Wara idanu Auntyn tayi tana kallon Fatima tace "Fatima? Are u threatening me?"
Mikewa tayi tana share fuskan ta tace "ba threatening ɗinki nake yi ba, ina gayamiki ne ki ɗaukar min mataki akan Fauza in ba haka ba daga ni har ke dab muke da rasa burikanmu" Tana kai nan ta fice daga ɗakin.
***
Kaman yadda ya faɗa washegari bayan ta gama Haɗa musu abin kari ta shirya a dining taje tayi wanka, doguwar riga marar nauyi ta saka tare da sanya hijab coffee color wadda yaje mata har ƙasa, ta shirya husna ma cikin doguwar riga da baby hijab, daidai sun fito shima ya fito murmushi ya sakarwa husna wadda ya saka Fauza daskarewa a wurin tana ganin cikakken haiba da kyaun bawan Allahn nan, daga baba prof har mammi ba wadda ya bari duk seda ya bi ya zaftare musu kyau da kwarjininsu.
"Madam chogal" Ta faɗa yana kallonta da neman tsokana, ai kuwa baki ta turo tana cewa "Allah yaya ni ba chogal bace gashi ina tafiya da kyau" Ta fara tafiya tana nuna mai dariya yayi yace "ni dae idanuna chogal suka gani"
Dining suka nufa tana ta tura baki, idanunshi kafe kan lips ɗin da take ta turowan ta saka pink lipstick da yayi mata kyau sossai.
Bayan ta gama sa abincin ta tura mishi ta zubawa husna ta kuma zuba nata Dukda yadda take a takure a kuma sarge sbd yadda yake aika mata kallon ƙasa ƙasa haka ba yadda ta iya ta zauna a wurin ta fara ci, Seda suka gama suka yi hamdala kan ya saka hannu ya zari tissue ya miƙe.
Taku biyu ya iso dab da ita har suna shaƙar numfashin juna, ƙashim jikinsu na gaurayuwa, duƙowa yayi yana rarraba idanunshi tsakanin kirjinta dake bugu da sauri har yana iya kallo da kuma idanunta da suke kashe shi, da kyar ya samu ya tsayar akan lips ɗinta da yanzu suka zama abu na biyu da baya iya gajiya da kallo a jikinta, saukar hannunshi taji da tissue ɗin ya ɗan kwashe lipstick ɗin cikin wani salo da ya saka su jin yarrrrrr gabaɗayansu.
"Haka is ok" Ya faɗa chan ƙasan maƙoshi kan ya miƙe tsaye ya juya tare da cusa hannayenshi cikin aljihu ya fara takawa don fita daga wurin.
Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kirjinta, 'oh ni fauza me ke faruwa ne kam?' Ta tambayi kanta sede ba amsa.
Mikewa suka yi duk suka bi bayanshi, husna ta tura gaban motan ita ta shiga baya, har suka isa da shi da husna suke hiran su ita bata saka musu baki ba.
Microbiology ne course da aka bata yayinda Fatima take yin biochem kusan dept ɗinsu wuri daya ne, sauka suka yi suka nufi ciki inda office ɗin Faisal yake nan biology dept, kan su isa ta Haɗa idanu da en mata sama da biyar waenda idanunsu kan Faizan kaman zasu cinye shi danye, ɗan Kallonshi tayi taga abunda suke kallo.
Ash trouser ne a jikinshi me taushi se farar shirt wadda ya zauna mishi sossai ya fitar da siffanshi ta kakkarfan namiji, sajenshi ya kwanta lublub a kyakyawar farar fuskanshi ga fuskan cike da haiba Dukda ba murmushi yake ba amma be kama ba, taɓe baki tayi ta maida bisa hanya har suka karasa office ɗin.
Faisal ya fi Jafar wasa haka yayi ta jan ta yana tsokanarta ita kam kanta ƙasa murmushi kawai take tana kuma jin idanun gogan nata jikinta alamu ita yake kallo, wata yarinya Faisal ya kira a waya ba'a yi mintuna biyar ba se gata a ladabce ta gaishesu yana kallonta yace
"yauwa Afnan ga ƙawa nayi miki Dukda dae da hafsa ne kawancen asalin amma a nan kawar ki ce, ku je ki nuna mata wurare sannan Naga kuna da lectures 9-10 duk ku shiga tare kin ji?"
Tana murmushi tace "Toh Yaya, Aunty mu je"
Murmushi Fauza tayi kan ta miƙe tsaye se ta kalli Faizan da nufin neman izinin tafiya, murmushi me kyau da ya tafi da imaninta ya sakar mata kan yace "a kula, ina jiranki anan"
Kai ta gyaɗa itama ta ɗan yi mishi murmushi kan ta bi bayan Afnan dake Kallonsu da burgewa tana amsa bye bye ɗin husna.
"Kan uba! Kai fa ɗan iska ne Faizan so kake ka hana yarinya karatu da wannan narke narken?"
Harara ya zabga mishi yace "ka manta ɗan guguwa ne.." Dariya suka yi a tare, Faisal yace "Masha Allah amma Amaryar ka na da hankali gata sweet sixteen shiyasa mana ka makale a gida ka kasa fita outside countries tunda aka kawo maka ita, Haba ai biri yayi kama da mutum"
Duka Faizan ya kai mai yana cewa "ba da aljani ba?" Dariya sossai faisal yake mai, daga karshe suka saki hiran Fauza suka kama wani, don sun san Faizan mutum ne da baya so ko a junansu ne suke kawo maganganun iyalansu in har ya zamana sirrinsu ne, ya sha gayamusu girman sirri dake tsakanin miji da mata da kuma tanadin Allah ga me fallasawa walau miji walau matar, lokutta dayawa in sun zauna daga sun fara in ya dakatar dasu zasu fara mishi tsiyar social ustaz ko young sheikh ya hana dole a hanu.
A ɓangaren Fauza kuwa taji daaɗin makarantar fiye da yadda ta zata, Afnan na da hankali ga saurin sabo nan da nan suka saba, a tare suka ɗan yiyyi signings da bata yi a course form ba suka kuma shiga lectures, basu dayawa don haka ba wani surutu kuma for the first time Fauza ta natsu a class har ta saurari malami ba zagi, faɗa ko neman tsokana.
Bayan sun tashi ta same shi a office ɗin kaman yadda ya faɗa suka nufi gida. "Amm Faahim ya ƙira Visa ɗin husna ya fito zata bisu"
Da sauri ta kalleshi idanunta na cika da hawaye sede bata ce komai ba, ya fahimci kewan husna zata yi to amma ba yadda suka iya dole ne zata koma wurin iyayenta, har suka dawo gida jikin ta a mace, juicy pasta bolognaise tayi musu sharp sharp suka ci yayi daaɗi kuwa sossai, har ya kasa shiru yace
"Ni kam Fauza duk wa ya koya miki abubuwa masu daaɗi haka?" Murmushi tayi zata yi magana husna ta ɗauki pillown kujera taje bayanshi tana kare mishi tace "haka fa mommy ke yiwa Daddy idan yana cin abinci yana santi, wai kunnenshi na motsi..."
Duk dariya suka saka Fauza ta kasa tsayar da nata har ya shagala da kallonta for the first time he admits it she's so cute and beautiful, da kyar ta tsagaita dariyar ganin irin kallon da yake mata tayi gyaran murya tare da cewa "Na koya wasu wurin friends ɗina though idan na biya wurin koyan kullum se na sha duka amma haka nake zuwa bcs shine abinda ke sani farin ciki time ɗin, se kuma da nayi waya nayi classes masu yawa online"
Kallon tausayi ya mata yace "then me yake hana ki faɗin ga inda kika je a time ɗin? Me yasa ba zaki ce a saka ki a catering school ba?"
Idanunta ta kaɗa wadda yaji har tsakiyar kwanyarshi tana ɗaga kafada tace "Taurin kai irin na Fauza"
Kallonta kawai yake yana mamakin ita kuma wannan haka Allah ya yi ta ko kuwa? Tattare wurin da ta fara ne yasa ya ɗauke idanunshi kanta.
A haka suka kwashe kwana bakwai curr kullum ita zata yi musu breakfast ya sauke ta makaranta ya wuce inda zashi wani lokacin kuma ya tsaya wurin Faisal in an tashi ya maida ta ko karfe nawa zata kai baze ci abinci ba ze jira har ta gama su koma ta sama musu abunda zasu ci.
Be taɓa zaton rayuwa da ita in a shade ze zama haka ba, yarinyar tana da tsafta, kunya ga iya girki har ba'a magana, sau dayawa yana mamakin ina wannan kunyar nata yaje har take yawon hotels da shaye shaye, lokuta dayawa idan ya tuna hakan halin da rayuwarshi ke shiga baya mishi daaɗi hakan yasa yake ta kokarin rufe baabin ganinta da yayi a hotels da kuma irin shaye shaye da tayi.
Ranar Sunday bayan ya karya yake sanar mata ze je yola amma gobe da yamma ze dawo, kaman zata yi kuka haka tayi mishi Dukda tana tsoron kwana haka baya nan amma da sauƙi tunda ga husna, Seda ya tabbatar babu abunda suke bukata kan ya wuce bayan ya bata Wayanshi da take yawan anfani dashi ɗin nan.
***
"Na fahimce ki yanzu Fatima, an samu matsala ne girma da daraja irin na aure ya kunce ɗauri masu yawa akan Fauziyya ɗin hakan ne yasa kika ga halinta gabaɗaya kaman sake mata shi aka yi, sannan gidanta akwai kariya sossai amma jikinta da sauƙin kariyar, mijinki ze zo ku koma kawai ki zuba idanu kiyi kallo kaman yadda kika bar gidan haka itama zata bari ba na kwana bakwai ba ita kam na har Abada" Aunty ta sauke Ayar cikin cin alwashi.
Murmushi Fatima ta saki tace "yauwa Auntyna maganin kuka na"
Ko da ya iso se dare suka zauna da Baba Prof ya gayamusu duk abunda ya faru, kai tsaye Fatima ta Musa wadda ya saka baba prof kallonta cikin mamaki don tabbas ze iya cewa fauza bata yi karya ba kan yayi magana ma baba Alhj yace.. "Ko ni da ban shaku da fauza ba na san wannan ɗabi'ar tata na rashin ƙarya, ta kan faɗi gaskiya ko hakan ze ja mata dukan mutawa ne". Da sauri Fatima ta kalleshi har zata ce kenan ita ɗin an mata shedar karya kenan Aunty tayi saurin cewa
"ai duk maida magana bata taso ba, na yiwa Fatima faɗa sossai akan shiga harkar Fauza tunda an samu tana zaune lafiya karta dinga shiga harkar ta idan har ba mutunci ne ze Haɗa su ba, kuma in shaa Allahu ta ɗauka"
Baba prof yace "masha Allah, to yayi" Faɗa ya ɗan mata akan yadda Faizan ya mayar mai yadda take maida mishi magani ya nuna mata girman miji da matsayinshi kan ya sallame su akan gobe zasu wuce.
Faizan wurin mammi ya kusa cinye daren suna hira tsakanin uwa da ɗa, amma fa kusan duk hiran na Fauza ne ita ke mishi yana ji, ta bashi labarin yadda Fauza ke kula da ita da cimarta in bata da lafiya har ta faɗa mai Adu'ar da Fauzan ke mata in kafanta ya tashi yanzu bata nan ne sede tayi da kanta Dukda bata tausan kafan yadda ya kamata.
Tana bashi labarin tana kula dashi da a da ne da yanzu duk wani fara'arshi ya kau kilan ma da ya bar mata wurin amma yanzu har murmushi ya kan yi, se dare sossai ya miƙe yayi mata se da safe, har ranta ta ji daaɗin fahimtar da tayi akwai haske a lamarinsu.
Yana isa ɗaki a kan three seater ya kwanta ya fiddo ainihin Wayanshi ya fara neman layin shi dake wurin Fauza ɗin.
Har Seda ya kusa katsewa kan ta ɗaga "Assalamu Alaikum warahmatullah" Ta faɗa ƙasa ƙasa wadda a take muryar ya saukar mishi da kasala yaji gaɓoɓinshi a gajiye.
Shima chan kasa ya amsa ta kan ya ɗora da "kin yi bacci ne?"
Tace "uhm na soma kenan, ka isa lafiya? Ya ka same su?"
Ya ɗan yi shiru kan yace "lafiya ƙalau duk suna lafiya, mammi na ta missing ɗinki"
Tana murmushi tace "Allah sarki mammina nima nayi kewarta sossai"
Yace a ƙasan maƙoshi "ɗan mammi fa?"
Dariya me sauti tayi tace "Husna na ta tambayar ka, gidan shiru mu kaɗai shiyasa ma muka kwanta da wuri"
Shima basarwa yayi kaman yadda ya fahimci ta basar da tambayar shi yace "in Shaa Allah gobe warhaka muna nan Kice mata kar ta damu sannan ki ce mata nayi missing ɗinku" Yana kai nan ya yanke wayan....
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤
DƘ
24
kaman kuwa yadda ya ce ɗin karfe biyar daidai a bakin kofan gate ɗin gidan ya musu kaman kuwa sun Haɗa baki da wadda ya tuƙo motar Fatima ɗin tun asuba don suna parking shima yayi horn aka buɗe mai ya shigar, hana shi tafiya Faizan yayi yace ya shiga ya ci abinci in ya so ya sama mai wuri ya kwana se gobe ya wuce da sassafe ta tasha.
Godiya sossai mutumin yayi kan suka shiga ciki a tare, parlorn ƙasan ya sha gyara se kamshin turarukan wuta masu sanyi yake zubawa, murmushi ya saki sanin aikinta ne don kamshin a wurinta ya saba ji irin wannan kam, ji yake kaman yana ɗakin mammi ko jadda sbd natsuwa da ya saukar mai.
Kujera yayiwa drivern izinin zama shi kuma ya nufi sama don tuni Fatima ta jima da wucewa..
"Yaaa salaam!" Ya furta a ranshi a sadda idanunshi suka faɗa kanta, itama dakatawa tayi tana sakin murmushi da ya Karasa saukar mai da gajiya, da gudu husna taje tayi hugging nashi hakan ya dawo dashi daga wata duniyar da ya tafi, ɗauke kai yayi saide idanunshi basu koshi da kallonta ba.
Tayi kyau sossai cikin wani material silk da aka yi mata doguwar riga fitted ya fitar da duk wani siffanta ta saka jewelries fashion gyale baƙi a ɗaure bisa kanta, tana murmushi tace "sannu da dawowa yaya"