Kenza eBookz

Diddigar kaya complete - Chapter 18

Diddigar kaya complete - Chapter 18

Diddigar kaya complete Chapter 18: Diddigar kaya complete Chapter 18. Sam wlh babu wadda yake kallo a parlorn bayan ita be san Fatima na parlorn ba har…

3,349 words

Sam wlh babu wadda yake kallo a parlorn bayan ita be san Fatima na parlorn ba har lokacin seda yaji ta ja wani wawan tsaki ta wuce ɗakinta tare da doko kofa.

Duk kallon kofan suka yi kan suka kalli juna yace "yauwa ƙanwata! Pls zamu samu abinci? Akwai baƙo a parlor yayi tafiya me nisa"

Tace "kwarai kuwa baza'a rasa abinci ba, bari na duba mishi"

Kallonta yake ya ga ko zata fita a haka saide ga mamakin shi ta shiga ɗaki ta dau hijab ta saka kan ta fito ta nufi ƙasa, fuskanshi kaman gonar auduga ya bita da kallo har ta ɓace mishi.

Hira suke yi da husna tana mai rigimar ina tsarabarta har ta dawo ɗauke da jug da cup ɗinshi me kyau bisa tray, a gefenshi ta tsuguna ta tsiyaya mishi tare da miƙa mai.

Hannu ya sa yana karɓa sanyin abun na aika mishi da zakuwar son ɗanɗanawa Dukda be san me bane, kurbi daya yayi ya lumshe idanu yace "wannan kuma me sunanshi ƙanwata?"

Husna tace "laaa uncle kunun aya ne baka sani ba?"

Yace "Husna uncle be saba shan me daaɗi da kaurin wannan bane but it's so so giving wlh"

Dariya suka saka mishi, Fauza tace "Yaaya ya su mammi da Jaddah? Baba prof da Baba Alhj da kowa da kowa dake gidan kowa na nan ƙalau?" Ta faɗa a marairaice.

Yace "kowa na lafiya, duk sun gaida ke" Sossai tayi kewan su.

Bayan ya gama sha ya mike yana ce mata bari ya kai bakon nan masauki, ze yi magrib kan ya shigo. Seda ya gama faɗa kuma se yaji wani iri sbd ba sabawa yayi ba.

Tace "Allah ya tsare a dawo lafiya"

Seda ya leƙa ya gayawa Fatima da ta amsa da kyar kan ya juya ya fice.

Fitowa Fatima tayi tana kallon Fauza dake kwashe abubuwan da ya sha kunun ayan tace "mtseww ba girin girin ba dae tayi mai..."

Fauza bata yi niyyar tanka ta ba ta sake cewa "cushe ba farin jini"

Dariya Fauza ta saki sossai kan tace "Eyyaaa ai Alhamdulillah tunda ni umarnin iyaye nake bi kuma seda aka ɗaura na zama tashi kan nake cushen wata fa da ta gina komai a ƙarya?"

Matsowa tayi tace "karki ga kaman kin ci galaba a kaina last week sbd cikina da kika ɓarar wlh yanzu se in nuna miki na riga ki shan iskar duniya"

Fauza ta mata kallon sama da ƙasa kan tace "ko? Allah sarki abunda kuma aka koyar dake kenan? Iya shi kenan ko har da barbaɗe? Kin San Allah in da nayi niyyar shayar dake bakin ciki marar misaltuwa da nayi tuntuni ki kiyaye ni... Kaman yadda nake faɗa ki tsaya matsayarki sannan Haɗa jiki dake ai zubda aji ne, Allah sarki yayana bana so kayi tsiya, don kin san Haɗa ƙashi da kishiya miji yake janyowa tsiya.. Kuma komai lalacewar masa Fatima ai ta fi karfin kashin shanu"

Tana kai nan ta wuce ɗakinta don husna tuni ta shige, a daskare Fatima take tana bin bayanta da kallo, lallai yarinyar nan ta gama raina ta, ya tana mata kallon biri ita kuma tana mata na Ayaba? Ashe dama Fauzan kura ce lulluɓe da fatar akuya? Waye yake hure mata kunne ta mamaye min gida? Ihu ta kurma kan ta nufi ɗaki tana ji kaman ta sa wa gidan wuta kowa ya huta.

Bayan ya dawo ta gabatar mai da abinci Dukda bata yi niyya ba amma ganin yau suka dawo yasa ta bashi, amma gobe kam matarshi da ta iya girki ita zata cigaba da sama mai abunda ze ci dama taimako tayi.

Tuwon alkama ne da miyar kuka ya ji ma shanu naman kazan nan yayi raga raga a ciki, ya ci sossai kuwa kan ya kira su duka parlor, nan yayi musu faɗa sossai akan rikici tsakaninsu ya kuma gargadesu da kar ya kara ji bare gani, daga karshe ya ɗaura da "Fatima tunda kina da mota Zaku dinga tafiya school da fauza har muga yadda za'a yi"

Tace "Toh Yaya in shaa Allah"

Fauza da bata so ba kuma har a fuskanta ya nuna ya kalla se tace "in shaa Allah, mun gode"

Daga haka ta mike tayi ɗakinta da kallo ya bita har ta shige, sadda Fatima bata nan kusan a parlorn suke kashe lokacinsu amma yanzu tana so ta komawa halin farko da ta fara zama a gidan.

Mikewa yayi ya bi bayanta, husna na kallo ya nufi wurinta don tana tsaye ne gaban wardrobe kuma in ba husna ta taso ta zo wurin ba ba ganinsu zata yi ba.

Dab da ita ya tsaya har tana jin kamshin shi na cika mata ciki, yace "Bakya so ne?"

Ta ɗago tace "me fa?"

Bakinta yake kallo kan yace "seems like baki ji daaɗin zancen tafiya school da Zaku ke yi da Fatima ba, for now it's my only option don in aiki ya min yawa ba zan dinga iya kaiki ina ɗauko ki ba and I hate it so much in ga matata tana hawa motar haya ko bolt ne kuwa"

Juyawa tayi tana kokarin buɗe wardrobe ɗin tace "ba komai, na fahimta"

Har yanzu ranshi be bashi ta gamsu da hakan ba, ya rasa me yasa ya matsu kuma yake so ta fahimce shi ba don cin fuska bane yayi hakan, amma dae haka ya hakura ya fita kar ya janyowa kanshi raini a faɗar shi fa kenan.

Washegari da safe ya fito tsab a shirye saide ganin Fatima tsaye a dining yasa ya san yau kam ze yi missing girkin Fauza, zama yayi tayi serving ɗinshi kaɗan ya ci ya miƙe yana duba agogo yace "zan ɗan fita wani meeting ba zan dawo yanzu ba ku kula pls"

Daidai ya nufi cikin parlorn Fauza ta fito rike da hannun husna shirye cikin hijab dogo tayi kyau sossai, tace "Ina kwana yaya?"

Yace "lafiya ƙalau ƙanwata"

Shiru duk suka yi ya ɗan tsaya kan yace "Na fita"

Tace "Allah ya tsare ya kiyaye" Dama abunda yake son ji kenan se yayi murmushi ya nufi gangarawa.

Dama sun sha cereals yau a ɗaki don bata yi wani girki ba, zaman jiran Fatima tayi seda ta ga dama kan ta fito suka sauka zuwa motanta, gaba ta tura husna ta buɗe baya ta zauna.

Tak be Haɗa su ba har suka isa makarantar, Fauza tayi dept ɗinta suka haɗu da Afnan suka yi lecture hall, Afnan ƙanwar matar Faisal ce Dukda basu haɗu da matar ta Faisal ba amma Afnan na yabon halinta hakan ya kwadaitar mata da son zama dasu ko zata rage kaɗaici barin ma in husna ta koma.

Ko da aka tashi saida ta jira Fatima har ranta ya soma ɓaci kan ta zo suka yi gida, abinci marar nauyi ta Haɗa musu suka zauna suka ci da husna kan suka haura sama abin su.

Ko da ya dawo ma abincin Fatima ya samu haka dae ya ci yana Tunanin kwaɓar da yayi da yadda ze gyarota.

Washegari ma hakan ce ta kasance.. Suna zaune a ƙasan bishiya ita da Afnan da husna wurin akwai students haka dake kai kawo duba wani handout take yayinda Afnan ke kara mata bayani don an yi farkon lectures ɗin bata nan.

Wani shirgegen ƙadangare taga yana saukowa daga bishiyar ita ba wai tana tsoron su chan chan bane amma bata so su zo kusa da ita ganin ya tsaya yana ta gyaɗa kai gashi marar kyaun gani yasa ta ɗan ɗaga hannu tayi shhh, ai kaman ta ce mishi ya zo yayi wani irin tahowa da gudu ta kafafunta kan ta miƙe tsaye ya shige mata hijab ƙara ta saki tana ambaton Hasbunallahu wani'imal wakeel....!

***

Tsaye yake gefen Faisal yace "kwaɓa nayi faisal kuma duk tunanina na rasa yadda zan warware shi wlh"

Faisal yace "Toh kai ɗin ma kenan bare mu? Wani irin kwaɓa ne haka da ya dameka?"

Shafa kanshi yayi yana jan iska tare da fesarwa yace "ka gane ko? Yarinyar nan ne a sadda ta zo na ɗauka tayi kankanta da ɗawainiyar gida kuma bazata iya wani aikin a zo a gani ba bare har ta iya girkin da zan iya ci, to my biggest surprise abubuwan da ta iya ko chef da yayi ten years in profession be iya ba, ta kula da cikina tsawon lokacin da Fatima bata nan yanzu kuma Fatima ta dawo se ta sakar mata"

Faisal ya kwashe da dariya yana cewa "kana raina yaran yanzu my guy... Dama baka raba musu kwana bane?"

Girgiza kai yayi yace "she's too young" Shi karan kanshi da ya faɗa ɗin he's not so sure of his self bare Faisal me sauraro.

"Maganan gaskiya shine ka fito ka raba musu kwana ko da bazaku kwana tare ba ya zamana ran kwanan ta bakwa tare da Fatima ta hakan ne zaka iya kwasar girkin tunda kana so" Shi ba fa hakan ne baze iya ba yanzu yadda ze fuskanci Fauza ne yace ta cigaba da girki bayan a fuskanta ya jefe ta da mugun kalamai yana cewa ba ze iya cin jagwagwalonta b.....

Gigitaccen Ƙara da yaji da Hasbunallahu wani'imal wakeel shi ya saka shi saurin miƙewa daga jinginen da yake..

Muryarshi na rawa yace "Fauziyya..!" Da gudu shi da Faisal suka yi inda suka ji ƙaran tana kokarin cire hijab ɗinta yayinda wani dake daga gefe yake kokarin kai hannu da taimaka mata, cikin zafin nama Faizan ya damki hannun nashi ya cillar kan ya fusgota kaman yadda take a rude haka shima ta ruɗa shi.

Fahimtar ƙadangare ne ya sa ya sure ta gabaɗaya yayi wurin motan shi yana sanyata ya zare hijab ɗin gabaɗaya ta haukace da kuka da kiran sunan Allah daidai ƙadangaren ya zo kan bayan wuyanta se ya tsaya Chak a wurin ko motsi baya yi.

"Yaaaya.. Don Allah ka cire min wayyo kafafunshi na shiga min fata, da zafi sossai ka cire min don Allah" Yadda take kuka take abu kaman shafan aljanu yasa ya matse ta bisa kirjinshi yasa hannu da nufin fusge ƙadangaren sede duk iya gwada karfinshi ƙadangaren nan ya ƙi ko motsi, hankali tashe yake kallon ƙadangaren wani irin tashi tsikar jikinshi yayi da sauri ya fiddo waya ya fara kiran Baba prof.

Cikin hanzari ya mishi bayanin abunda ke faruwa gashi Fauza ta dena motsi, Baba prof yayi salati ya sallamar kan yace "ku yi sauri ku je wurin prof ghali na tabbatar ze yi duk abunda ya dace yanzu yanzu Faizan karka ɓata lokaci bari na kirashi"

Kofan motar ya tura ya kira Faisal tare da cila mai key don yanzu ba ze iya tuki ba gabaɗayanshi ya sauya idanunshi har sun sanja kala, Afnan da husna da har sun fara hawaye ne suka shiga gaba. A take ya ja mutane suna ta mamakin wannan abu da Allah ya kiyaye haka students suka watse.

A hannu ya ɗauke ta zuwa wurin malam ɗin, already Baba Prof ya kirashi ya mishi bayani, a jikinshi ya sanya ta Tare da kwashe gashinta da ya baje Malam ghali na kallon kadangaren yace "la haula wala quwwata illa billah..." Da sauri ya janyo ruwan zamzam da wasu Adu'o'i ke ciki ya tashi ya shiga dakinshi mintuna biyu ya fito da wani Allon karfe ruwan ya zuba a Allon kan ya saka ya buge ƙadangaren yana ambaton sunan Allah.

A take ƙadangaren ya fice fit daga jikinta ya faɗi ƙasa ya fara kokarin guduwa wannan ruwa malam ya diba ya fara zuba mai nan ya fara wani kalar birgima da mutsu mustu ba'a ɗauki lokaci ba ya zama baƙi kirin ya tamushe kaman wadda wuta ya babbake.

Faizan na ta patting kumatunta yana cewa "Ke Fauza buɗe idanunki kiga an cire... Fauza! Fauziyya..!!"

Malam yace "bazata tashi ba Faizan kwantar da ita"

"malam me yasa bazata tashi ba? Don Allah kayi wani abu" Yadda yake maganan kaɗai zaka san ba karamin ruɗe wa yayi ba, me hakan ke nufi? Yau da baya school ɗinsu fa? Haka zata shiga wannan hali ita kaɗai?

Malam ghali yace "wato wannan ƙadangaren ɗan aike ne, a yadda ka ganshin kila ta ambaci Allah a sadda ya nufi hawa jikinta da bata ambata ba ƙara kawai ta tsaya yi da yanzu ganinshi ma wahala ze mana don jikinta ze shiga, ko ya lahanta mata abubuwan ciki ta mutu ko kuma yayi mata illar da warakarshi se rabba"

"waye ze mata hakan? Waye yake neman illatar da lafiyar ta haka? Me ta musu?" Kaman ze yi kuka yayi maganan.

Malam yace "wannan mu barwa Allah, yanzu mu tsaya kan lafiyanta"

Ruwan Adu'a malam ɗin ya bashi yace ya shafe ta dashi, bayan yayi ya saka shi saka mata a baki, nan ya bashi za'afaran da habba da suke dauke da Adu'a yace ya shafa mata, fuska, hannaye, gashin kanta da kafafunta nan take yayi.

Ya zauna yayi shiru yana kallonta cikin jiran malam ya gama Adu'ar da yake yi, yana gamawa kuwa ya watsa mata se ta ja numfashi a kuma ruɗe tayi hanzarin mikewa tana mutsu mustu..

"Yayaaa ka ciremin... Wayyo zafi, Hasbunallahu wani'imal wakeel... Wayyo Jaddah..." Duk bata san tana wannan sambatu ba kamata yayi ya rungume a hankali ya sauke hannunshi bisa bayanta ya zagaye kan ya da matse ta a jikin shi cikin rarrashi yace

"shhhh ƙanwata, yi shiru an cire baya jikinki... Shhh" Lub tayi.

Malam yace "ku je a duba jikin nata in ya so ko maganin asibiti se a sake bata watakila yana da dafi, amma ga wannan ta dinga anfani dasu zamu yi magana da Mahaifin naka"

Prof ghali babban malami ne don tsohon professor ne na musulunci abokin Baba prof ne, kuma dama chan Faizan kan leƙa ya gaida shi idan ya samu time.

Zamewa tayi daga jikinshi kanta a ƙasa, haka suka miƙe suka fito, hijab ɗinta ya sanya mata yana kallon bayan wuyan nata da shape ɗin ƙadangaren har yanzu yake kwance yayi baƙi sidik...

"Me ke shirin faruwa ne?" Yayi maganan yana sake kallon hannunta da ta gimtse a cikin nashi har yanzu yana iya jin yadda jikinta ke rawa ta ciki....

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.

🖤Gureenjoh🖤

25

Ko da suka isa asibitin Jafar ne ya duba raunin aka yi mata allura, ganin ko tsorata bata yi ba kaman yadda ta saba ba ya san har lokacin bata dawo daidai gabaɗaya ba, haka dae Jafar ya dawo dasu gida yana kallon yadda gabaɗaya Faizan ɗin Damuwa me yawa ya nuna a fuskanshi.

"Ka tafi da motar na ga kaman hadari ko gobe se ka ba driver ɗinka ya dawo dashi" Cewar Faizan bayan sun sauƙa yana rike da hannunta, Afnan tayi mata Allah ya kiyaye kan suka fice daga gidan.

Haurawa suka yi zuwa ɗakinta, cikin kulawa yace "bari na Haɗa miki ruwa ki watsa se ki sha magani ko?"

Girgiza kai tayi idanunta tab da hawaye ta sake riƙe hannunshi da yake Shirin zarewa cikin nata. Fuskanshi cike da tausayinta yace "babu abunda ze sake faruwa yanzu kin ji? Sake ni kiga"

Nan ma girgiza kai tayi se hawayen ya gangaro, babu yadda ya iya illa ya sa hannunshi ɗayan ya share mata kan ya ce ta tashi su tafi, a tare suka shiga bayin ya Haɗa mata ruwan ya zare mata hijab ɗin se ta ɗan ja baya amma bata sake shi ba, yace chan ƙasa "Toh yanzu kiyi wankan bari na fita"

Cikin wani irin murya a shagwaɓe cike da sangarta tace "uhm uhm ni de don Allah karka fita ka barni ka Juya bayanka kawai"

Babu yadda ya iya ya matsa daga bakin kofa ya juya mata baya, sharp sharp ta watsa ruwan tana ta kalle kalle, tana gamawa ta janyo towel ta ɗaura tana kokarin jan hijab ɗinta ta saka Bon ɗin da ta kama gashinta dashi sakwa sakwa ya kunce zuban gashin ya haɗu da ruwan dake jikinta yayi mugun firgitata ta kwalla ƙara, a hanzarce ya waigo kan yayi wani yunkuri ta faɗa jikinshi yayi saurin taro ta, yana cewa

"menene kuma?" Siririn kuka ta saki tana cewa ya taimaka ya duba mata bayanta motsi taji kaman ƙadangaren ne ya dawo.

Daga ita har shi jikinsu rawa ya ɗauka, zuciyarshi na bugawa da karfi karfi jin yadda take kara mannewa jikinshi hannunshi na cikin wet gashinta yana shafa bayan wuyanta zuwa bayanta, ya salaaaam ya ambata cikin ranshi jin yadda take kokarin kunce mai notikan kai gabaɗaya.

Janyeta yayi suka fito daidai nan Fatima ta buɗe kofan ta shigo tare da nufo ciki gabaɗaya ai se idanunta suka mata mugun gani, baƙin kishi ne ya taso ya Rufeta idanunta har rawa suke yi.. "Me...me me zan gani haka? Me wannan?"

Be tankata ba yana rike da fauza har zuwa dressing mirror saide bata zauna ba ta kara mannewa a jikinshi fuskanta cikin kirjinshi tana sauke numfashin dake gigitashi ba tare da ta san me take aikata mishi ba.

"Zauna" Ya faɗa calmly. Zama tayi ya juya ga Fatima dake tsaye yace

"Next time pls ki nemi izinin me wuri kan ki shigar mata, and bata da lafiya find something da zata ci don bazata bari na fita nema mata abinci ba" Har kaman zata lailayo Ashar ta maka se kuma ta fasa ta ficeee fuuu

Sama sama ya shafa mata mai, kan suka tafi tare ya buɗe wardrobe ɗinta ya duba mata riga marar nauyi ta sanya, bayi suka koma suka yo alwala a tare daidai lokacin da ruwa ya tsuge sossai kaman da bakin ƙwarya Dukda daminar bata wani shiga sossai ba especially a ta north ɗin nan amma Abuja ba laifi suna samu akai akai tun last week.

Shi ya ja su sallar magrib bayan sun idar ya bata Alqur'ani ta karanta, cikin tattausan muryarta ta fara karantawa wadda ya taimaka sossai wurin ƙara natsar da ita, se a sannan ya mike yaje ya duba Fatima ta kusa gama girkin ya sakata tayiwa husna wanka duka ranta a cunkushe, tunani kawai take me ya faru tsakanin fauza da Faizan da har yake riritata haka?

Shi kuwa wanka yayi ya sake alwalan isha ya fito sanye da dogon wando da jallabiya, hannunshi waya ne yana magana da Baba prof da yake ta jimamin wannan abu, nema yayi da ya bata wayan shima kuma dama daidai lokacin yake isa wurinta se ya zauna daga gabanta ya miƙa mata wayan.

Tana sawa a kunnenta ta fara hawaye cikin rawar murya suka gaisa da baban yake rarrashinta karta damu babu wani abu ta rike adu'o'in da ya bata sossai kuma ze kara mata wani, rikici ta sanya mishi akan ita kam zata dawo wurin jaddar ta tana jin tsoro.

Da kyar ya shawo kanta zata zauna Abuja ɗin kan ya ba wa babanta wayan shima dae ya mata sannu da Allah ya kiyaye gaba haka jadda da mammi ma, bayan ta sauke wayan se ta miƙa mai ƙin ƙarba yayi.

Idanunta da suka yi laushi yau ɗin gabaɗaya ta ɗaga se suka faɗa cikin nashi da ya kara lumshesu yana kallonta, a hankali tace "Yaaaya ga wayan"

Ya rasa yadda take kiran nata yaayan da yake jinshi har cikin ɓargonshi ba ƙarya, a hankali yace "ba zan karɓa ba" chan ƙasa

Kara marairaicewa tayi tace "Meyasa to?"

"Me yasa kike son barin ɗakinki ki koma gida sbd wannan abu da be taka kara ya karya ba? Baki san kowacce mace da akwai abunda take fuskanta a nata gidan aure tana zama jaruma ne tayi over coming komai ba? Na Gaza wurin kula dake ne?" Ya karashe tambayar da wata murya da ta sakata maida kanta ƙasa kan ta girgiza tace

"A'a ka yi hakuri" Yace "na hakura, tashi muyi sallah"

Isha suka gabatar da kanshi ya fita ya karbo abincin don Fatima dangwalarwa tayi a dining ta wuce ɗakinta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull