Kenza eBookz

Diddigar kaya complete - Chapter 19

Diddigar kaya complete - Chapter 19

Diddigar kaya complete Chapter 19: Diddigar kaya complete Chapter 19. Kasa hakuri tayi ta kira Auntyn ta take tambayarta meyasa bata fara ganin abunda tace…

3,350 words

Kasa hakuri tayi ta kira Auntyn ta take tambayarta meyasa bata fara ganin abunda tace ba, Auntyn tace mata an samu akasi amma ba shi ze sa su karaya ba, ta cigaba da zubawa sarautar Allah ido, rayuwar Fauza a gidan kaman a tafin hannunta yake.

Husna ya ɗauka da tayi bacci a parlorn yayi ɗakin Fatima da ita, tana sauke wayan yana buɗe kofan da sauri ta gyara zamanta, a kan gado ya kwantar da ita yace

"zata kwana wurinki yau" Juyawa yayi ya fita yana mamakin yadda Fatiman ta kasa zuwa tayiwa Fauza ko ya jiki ne, har ya taɓa handle ya dakata ya juyo fuskanshi ba yabo ba fallasa yace

"kaman na ce miki Fauza bata da lafiya ko?" Tace "eh ka faɗa, me zan mata bayan girkin?" Ta faɗa cikin gatse.

Yace cikin mamaki "wai dama haka zuciyarki yake ne ko yanzu ne ya koyi sabbin ɗabi'un nan? Fatima sannu bazaki iya zuwa ki mata ba? Wai me kika ɗau kishi ne?"

"Me kuwa na ɗauke shi? Ni yaya meyasa kake min haka ne? Meyasa a ko yaushe abu ya Haɗa mu ni ce da laifi? Ni da nayi ɓari ko sannu ta min bare Allah ya kawo na mora? Gwara ni na mata girki ita ko ruwa ta kawo min? Duk baka ce komai ba se ni yanzu da ban san hawa ko Sauƙar ciwon munafurcinta ba zaka wani ce in je in gaisheta? Kayi hakuri ba zan iya ba"

Dawowa yayi ya zauna ganganta yace "Fatima ki fahimce ni, babu wacce nake fifitawa tsakaninku illa ma ita da nake tauye ta, kina sane tunda ta zo gidan nan sati na shidda kenan nake ga ban taɓa ware kwana ɗaya tal da sunan nata ba, ban cika mata duk wani hakki na matsayin matata ba kina kallo baki taɓa ce min hakan ba daidai bane, annabi fa cewa yayi mafi darajar mace itace wacce zata taimakawa mijinta wurin bautar Allah in taga zai kauce ta dawo dashi daidai, duk na rasa wannan daga gareki..."

Hawaye ta share tace "zaka ce haka ai tunda ta baka ka kwasa" Ya rasa me ke damun Tunanin Fatima, mikewa yayi ya fice tunda ta ƙi fahimta tana kan rashin daidai.

Tsaye ya samu Fauza tsakiyar parlor tana ganinshi ta nufo shi yayi saurin saka hannu ya riƙe nata ganin kai tsaye jikinshi take shirin shigewa wadda illar da take mishi a yadda ya san kanshi idan be yi da gaske ba baze yi bacci ba yace "menene?"

Tace "Motsi nake ji a ɗakina" Yace "Ina kin yi azkar kuma kin karanta Alqur'ani?" Kai ta gyaɗa yace "to ki yi yaƙini da hakan ki saka a ranki babu wani abu da ze iya cutar dake kinji?"

Kai ta gyaɗa ya Janyeta suka yi ɗakin nata inda yace ta kwanta, zama yayi ta kwanta a kan pillow yana shafa kanta idanunta a lumshe yayinda shi kuma nashi ke kan fuskan nata yana kare mata kallo har bacci ya ɗauke ta.

Fita yayi ya tabbatar da komai daidai a gidan kan ya dawo ya rage musu wuta ya cire jallabiyar tare da kwanciya da dogon wando kawai be damu da saka kayan bacci ba, har ya lumshe idanu ya tuna magungunan ta bata shafa ba.

Sauka yayi ya ɗauko ya zo ya zauna tare da zuba mata idanu na mintuna kan a hankali ya fara sakawa a hannunshi ya shafa mata a kafafu, ya sake sakawa ya shafe hannayenta dashi, daga nan se gashin kanta ya shafa mata. Sauran na hannun nashi ne yake shafa mata a fuska a hankali wadda ya saka ta ɗan buɗe idanunta dake cike da bacci tana Kallonshi.

'Tsarki ya tabbata ga Allah da ya halicci wannan idanu' baze taɓa cewa ya taɓa ganin abunda har ranshi yake mishi kyau irin idanunta ba, a hankali yake shafa kumatunta idanunsu sarke da na juna se chan ta turo baki tace

"bacci" cikin muryar da bacci ya ci karfi.

"Yi baccinki an gama" Ya faɗa a natse kan ya miƙe ya adana magungunan ya dawo ya kwanta daga gefenta yana lumshe idanu, baya son kawo Tunanin komai a ranshi in yace ze yi tunanin wadda ya aika mata da wannan ƙadangare tabbas ze fara zato kuma ya san zunubi ne, in yace ze yi Tunaninta kuma tabbas ze iya Jawa kanshi damuwa wadda baya fata ya kasance yanzu don baze iya ɗaukar abu guda biyu ba idan abunda yake gudu ya kasance.

Haka dae yayi bacci da blank thought, asubar fari ita ta fara buɗe idanu se ta ganta kwance dab dashi kansu a kan pillow ɗaya yayinda hannunta ke kwance bisa faffaɗar kirjinshi, a hankali ta kai idanunta fuskanshi da dim haske ya bayyana haske da kwarjininshi, dukda bacci yake yi but ba karamin kyau yayi ba sajenshi dake kwance lublub gwanin sha'awa.

A hankali ta ɗago hannunta ta ɗan shafa sajen nashi tana mamakin yadda aka yi tun da chan bata taɓa ganin kyaun nashi ba se yanzu, karab taji ya riƙe hannun da take shafa mai fuskan, a hankali ya waigo yana kallon ta, kunya ne ya rufeta se tace "Ina kwana?"

Daga haka ta zame ta sauƙa tayi toilet, murmushi ya saki kan shima ya sauƙa, zuwa yayi ya kunna Alqur'ani don da asuba sunna TV karatun Alƙur'ani mai girma suke sakawa, daga haka ya ɗauki jallabiyarshi ya fice dakinshi a chan yayi alwala ya zo ya fice masallaci.

Ko da ta idar da sallah azkar tayi tare da karatun Alƙur'ani, bayan ta gama ta miƙe ta shafa magungunanta da kanta daga kai har kafa kan ta saka riga dogo marar nauyi, tana zama a cikin kujerun ɗakin yana shigowa.

Ganinta haka ya sa ya sakar mata murmushi itama ta mayar mai tana sake cewa "Ina kwana?"

Yace "kin tashi lafiya? Ya jikin?"

Tace "Alhamdulillah"

Matsowa yayi kusa da ita tare da rankwafowa yana duba bayan wuyanta inda ƙadangaren ya bar tambari sede wayam babu, ajiyar zuciya ya sauke wadda numfashin a wuyanta se da ya sakata saurin kame jikinta tana ɗauke numfashi.

Mikewa yayi yace bari ya ɗan kwanta, dakinshi ya wuce ita kuma ta mike ta fara gyaran ɗakinta daga nan ta sauka ta musu abin kari ita da husna, tana haurowa ta gamu da Fatima, abunda ya faru jiya ne ya dawo mata se tayi saurin kauda Tunanin Dukda gabaɗaya gidan babu wadda ya san ainihin su Fatima se ita amma bazata ce sune suka mata hakan ba tunda bata da shaida..

Har zata wuce se ta tsaya tare da waigo wa ta dube ta tace "Faɗan bayan fage na lusari ne, harara a duhu kuma baze sa in chanza rawa ba kirrr nake kallonku, wai baki yi mamakin yadda nake yawan faɗin cusa kanki kika yi wurin samun ya Faizan ba? Ko kwakwalwarki a toshe yake baya tunani? Toh duk wani sirrin ku yana tafin hannuna the next time kuka sake yi min abu makamancin haka ina me tabbatar miki za'a yi walƙiya... Karku yi gangancin tarar aradu da ka don tabbas kuka tara se kun samu, ni ɗin kafin Allah ce!"

Tana kai nan ta nufi ɗakin Fatiman ta tado husna suka yi ɗakinta har lokacin Fatiman na tsaye tana juya maganan, kenan Fauza ta san suna da mission akan ahalin prof? Ta yaya? Kuma a ina ta sani? Da sauri ta nufi ɗakinta don kiran Aunty hankalinta a tashe.

Fauza kam bayan tayiwa husna wanka ta zuba musu abincin da already ta hauro dashi suka fara ci, har sun yi nisa don har husna tana cewa ta koshi ya tura kofan ya shigo.

A tsakiyar center rug ya samesu suna ta cin abinci, har a ranshi yaji sanyi ganin har ta iya yin girki kenan ta ji sauƙi, zama yayi husna na gaidashi.. Daidai lokacin ta gama itama ta fara tattare wurin ganin bata mishi tayi ba kuma ranshi ya riga ya biya yace

"Ni baza'a bani breakfast ɗin bane?" Ɗago kai tayi ta kalleshi kan ta kauda don bazata iya faɗar abunda take son faɗa ba matukar tana kallon cikin idanunshi tace

"Ni? Wani jagwalgwalon zan baka?" Kallon mamaki yake aika mata magana take shirin gaya mai ko me?

Yace "Eh jagwalgwalon dae zan ci"

Tace "ai wannan ba zaka iya ci ba, na tabbatar matarka da ta kware a girki ta tanadar maka hadadde ma kuwa"

Kallon husna yayi yace "je parlor ki kalli cartoon" Da gudu ta tashi ta fice.

Yace "Me kike nufi ne kam?" Ganin ta mike tana shirin tattare kwanukanta tace "Yaaya pls me yasa kake so se na fito na faɗa kai tsaye? Toh ina nufin ba zan iya baka ba gaskiya don jagwalgwale ne kaje wurin matarka ta baka me daaɗi.. Ko ba haka kace ba?"

Tayi maganan tana kallon gefe... Mikewa yayi ganin da gaske take yayi saurin riƙe hannunta yana cewa "Toh yanzu zan cigaba da cin jagwalgwalon don raba muku girki zan yi kwana bibbiyu yadda addini ya tsara"

Kai tsaye tace "ni kam ba zan yi ba" Ta karashe da murguda baƙi idanunshi gabaɗaya ya waro yace "ni kike yiwa rashin kunya da murgude murgude?" Me makon yaji haushi ma dariya take bashi ala dole fushi take yi.

Tana kunkuni tace "ni dae ba zan yi ba bana so ai tun farko ba'a nuna ana so ba se yanzu! Ni de babu wani girkin da zan karɓa" Hannu ya kai ya dalli bakinta

"ni kike yiwa kunkuni?" Haba ai se ta sakar mai kukan shagwaɓa har da bubbuga kafafu wai zafi...

"Yaa ilahil alameeen" Ya furta akan lip ɗinshi kawai yana kallonta, yarinyar nan bazata kashe shi ba.

Ganin kaman yayi fushi yasa ta dangwalar da abincin tana tura baki ta zuba mai, ba tare da ya kalleta ba yace "ɗauke kayan ki ba zan ci ba"

Da sauri ta fara kokarin ɗaukewa yayi hanzarin rike hannunta suka zubawa juna idanu....

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.

🖤Gureenjoh🖤

26

"Wai da gaske ɗaukewar zaki yi?" Ya faɗa a marairaice, se ta saki ta tsuguna ta zuba mai tare da miƙa mai.

Karɓa yayi yana cewa "thank you" Tana shirin magana Wayanshi ya ɗauki ringing, dubawa yayi se yaga Faisal suka gaisa yake tambayar shi me jiki, Seda ya kalleta kan ya amsa da da sauki, faɗa mishi yayi matansu zasu zo su duba ta.

"Zaki iya tarban baƙi kuwa?" Ya faɗa bayan ya sauke wayan.

Kai ta gyaɗa tace "Sossai ma, ni da nake so in ga mutane mutane su ganni.."

Yace "families ɗin Faisal da Jafar ne wai zasu zo"

Tace "Tohm Allah ya kawo su lafiya"

Ya amsa da 'Ameen'

Bayan ya gama ci yaje ya shirya ya zo ya tambayeta ko akwai abunda zata buƙata ta amsa da babu kan ya duba Fatima ya faɗa mata tare da umarnin ta fito suyi aikin bibbiyu sbd sauƙaƙawa, ta dae amsa yana fita ta kwanta abin ta ta fara bacci.

Girki me rai da motsi Fauza tayi musu, dukda bata yi yayi yawa ba saide tayi varieties ta tsara shi kuwa yayi kyau sossai, ita da husna suka dinga jigilar kaiwa sama, bayan ta gama ta je tayi wanka.

Bata shafa mai ba se ta shafa magungunan nan da prof ghali ya bata ta shirya cikin lace riga da skirt ne da dinkin yayi matukar amsarta, ga colourn lace ɗin blue da onions se ya haske fatarta, ɗan kwalin irin hular nan ne so gyara parking ɗinta kawai tayi ta sanya ta nemi jewelries da suka yi matching ta saka.

Tana cikin shirya husna ya turo kofanta da sallama, ta amsa tare da ɗagowa.

Gabaɗaya idanunshi ya sake a kanta yana karewa halittar Allah kallo, tambayar kanshi ya fara wai me yake ji a kan yarinyar nan ne takamamme? Ko ta ina ta cike mishi zuciya da Tunaninta, idan ya fita yana marmarin ya dawo ya ga shigarta da kwalliyarta, hancinshi ya shaki sassanyar turarukanta masu saukar da natsuwa, bakinshi a ko yaushe yana marmarin tasting abincin ta...

"Yaaaya sannu da dawowa" Abunda kenan ya dawo dashi daga duniyar da ya tafi.

Kasa riƙe compliment ɗin yayi yace "Masha Allah kin yi kyau"

Tana murmushi tace "thank you"

Yana kallon husna yace "Na gama shirye shiryen tafiyar husna fa jibi ne da misalin karfe 5 na yamma jirgin su ze tashi"

Da sauri ta kalleshi kaman zata yi kuka tace "Wai dama da wuri ne?"

Kai ya gyaɗa yanayinta gabaɗaya se ya sauya, yace "Ki bar musu nasu ke ki haifi naki tunda dae kayan aro baya rufa asiri"

Yi tayi kaman bata ji ba, se ma tace "kaman sallama ko?"

Fita yayi ta bi bayanshi aiko iyalan abokanshin ne da su kansu kasancewar Saturday ne, Fauza kaman ta san su kuwa tayi musu tarba na mutunci bata bar matan anan ba ta ja su ɗakin ta bayan sun gaisa da mazan suka mata sannu da jiki.

Yaran Faisal biyu mace da namiji matarshi hafsat da ciki, se na Jafar uku matarshi firdausi tana goyon na huɗu.

Ruwa ta gabatar musu da fruits suka sake Gaisawa sossai hafsa ke gayamata yadda Afnan ke kai mata labarinta nan suka ɓarke da hira kaman sun jima da haɗuwa, mikewa tayi ta fita musamman ta je ɗakin Fatima ta shaida mata da zuwan baƙin amma bata ko tanka ta ba.

Su ɗin sun riga sun jima suna son zuwa gidan Faizan ɗin saide Allah be yi ba ko da suka ji ya ƙara aure ma su suna team uwargidaye ne abun mamaki se suka ga Amarya ke ta ina za'a saka ina za'a aje dasu.

Abincin ta gabatar musu bayan sun yi sallah suka ci suka yi nak suna cewa ita da bata da lafiya ta iya yin girki haka, tana ta murmushi kawai.

Yini sur suka yi amma Fatima bata leko ba se gab zasu tafi ta fito suka gaisa kawai ta koma, Hafsat da Firdausi wayayyun mata ne kuma sun fahimci kishi irin na Fatima a take suka dau yi mata lecture da yadda zata karkatar da hankalin miji kanta ita kaɗai, kaman yadda Burin kowacce macece ace ta zama tauraruwa a gidan mijinta kuma sarauniyar birnin zuciyarsa.

Ta Haɗa su da turarukan wuta kuwa ta zubawa yaran snacks masu yawa da Faizan ya saya musu suka yi ta murna, har mota suka raka su suka tafi.

Juyowa Faizan yayi yana kallonta fuskanshi cike da murmushi na burgewa da jinjina yace "Allah ya miki albarka"

Murmushi tayi tace "Ameen"

A tare suka koma be zauna ba shi ya taya ta suka tattare gidan tsab, tana tsaye kitchen tana shirin wanke wanke kenan taji kamshinsa ya bule kitchen ɗin waigawa tayi se ta ganshi tsaye sanye da red riga marar hannu ta shan iska da ya bayyana damatsanshi da suke a murɗe se three quarter milk, hannayenshi zube a aljihun yana kallonta.

Maida kanta kawai tayi ga dauraye kwanukan kan ta zuba ruwan sabulu se ta nufi drawer don ɗauko lemon fresh da ta ɗaura shi chan sama sbd husna dake yawan son wasa dashi.

Hannunta ta miƙar har tana ɗagel don ɗauko wa kawai taji hannun mutum bisa nata, da sauri ta waigo se fuskanta ya kusan dukan kirjinshi sbd kusantota da yayi sossai, idanu suka zubawa juna na seconds kan yayi gyaran murya yana cewa "Amm jikinki ba wani matsala ba?"

Fuskanshi na kusan kan nata sbd tsawo sossai da ya fita hakan ya sa ta kasa magana se da ya ɗan matsa baya kan ta saukar da kanta ƙasa tace "Ai na warke"

Wani dogon tsaki da suka ji yasa duk suka kalli kofa, Fatima ce tsaye tana Kallonsu hawaye ne ke zuba a idanunta ta fara cewa "Wallahi Allah se ya saka min, Allah baze taɓa barinki ba Fauziyya kaman yadda kika yi min kema Allah ya miki, kin zo kin sameni gidana ina zaune lafiya da mijina kika shiga tsakaninmu kika juye hankalinshi gabaɗaya to Wallahi ban yafe miki ba"

"Kai kuma" ta nuna shi.

"Allah kaima se ya bi min hakki na, watana biyar a gidanka ka kara aure, a wata biyar da nayi ban taɓa yin sati ɗaya cikakke da kai ba kana chan gobe kana nan amma tun zuwan Fauziyya gidan nan baka taɓa fita daga Kasar nan ba, kai ka ce min baka iya komai a harkar kitchen ba, zan iya rantsuwa baka taɓa shiga kitchen da sunan aiki ba amma yau gashi nan kana taya ta... A haka kake cewa kana min adalci Toh wlh ban yafe ba idan ina da hakki Allah ya bi min..."

Yadda take kuka duk suka tsaya suna kallo, kan Fauza ta taɓe baki ta nufi gaban kayan wanke wankenta ta fara wankewa, shi kuwa a natse ya isa gabanta ya sa hannu ya riƙe nata ya fusge ta suka fice be tsaya ko ina ba se Ɗakinta ya daka mata tsawa

"wai me yake damunki ne Fatima?? Me yasa bakya so kiga an zauna lafiya? Meyasa kika kasa sakawa zuciyarki salama? Kullum ƙorafi an yi miki kaza an yi miki kaza? Yanzu da zan yi baƙi ban taka har ɗakinki na faɗa miki ba amma me kika musu? Babu. da babu Fauziyya haka zan kunyata? Ke baki san zuru ba? To karki yarda ki kai ni bango ba zan lamunci wannan ba, ki sani na raba muku kwana jiya da yau kwanan ta ne gobe ke zaki ci gaba, kaman yadda bata sa miki ido a naki ba karki saka mata a nata bana son fitina... Kin gane ko?"

Kallonshi kawai take kaman bakonta tunda ta shiga gidan yau ne rana na farko da ya zage ya rufe ido yake ta mata faɗa Dukda ita har lokacin bata ga laifinta ba, son shi da take kawai yayi yawa shine laifinta, irin attention da yake ba Fauza da take so kawai shine laifinta? Kuka take yi sossai tana jin kaman tayi hauka.

Lallai Mahaifiyarta bata kyauta mata ba da ta kwadaitar da ita Faizan tun bata gama sanin menene so ba, son shi yayi mata zurfi wadda bazata iya Daena ƙorafi ba in har akan wata macece.

Fita kawai yayi ya kyale ta.

Be koma kitchen ɗin ba se yayi ɗakinshi kawai, Fatima na da matsala abubuwa dayawa da tayi tayi a farkon aurensu se yanzu yake ganin rashin dacewarshi ko dama sbd ita kadai ce kuma he was new in the system yasa be gani ba amma yanzu duk asalin halayyar ta kishi ke hankaɗosu.

Har dare ma be sake haduwa da kowaccensu ba, se da ya dawo isha ne ya shiga ɗakin Fauza itama ganin ranshi har lokacin ba'a sake ba yasa bata ce komai ba ta gabatar mai da abinci da tea ɗinshi.

Yana Ci ya dube ta yace "gobe zan koma wurin Fatima pls idan tayi kwana biyu ki cigaba da naki and ki dinga ajiye mana a dining zamu ke haɗuwa muna ci mu duka that should be the policy"

Tace "Toh"

Yace "jibi da safe zamu tafi yiwa Husna shopping"

Ta amsa "Allah ubangiji ya kaimu"

Ya so ya kawo maganar waya don Jafar ya kirashi wai matarshi na son layin Fauza don sun manta basu yi exchanging ba se kuma ya fasa don har yanzu be jin ze iya saya mata waya tukuna.

Ranar dae kam kowa ɗakinshi ya kwana, tayi kwanciyarta da husna.

Sunday ma ya ɗan yi short tafiya kwata kwata basu haɗu ba se dare shima abinci ya ci wadda Fatima ne ta karɓa tunda yamma ya riga ya shiga, saida ya tabbatar basu da wani matsala kan ya wuce room ɗinshi Fatima ta bi bayanshi Fauza kam ko a jikinta ta kama husna suka yi ɗakinta.

Washegari Fatiman ce tayi breakfast itama tayi wanka ta shirya cikin Atampha dinkin bubu, sanye da kaftan dinkin zamani ruwan ƙasa ya fito, ya haɗu har ya gaji.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull