Kenza eBookz

Diddigar kaya complete - Chapter 20

Diddigar kaya complete - Chapter 20

Diddigar kaya complete Chapter 20: Diddigar kaya complete Chapter 20. Itama Fauza Abaya ta saka milk and brown tayi kyau sossai barin ma ɗan face ɗinta da…

3,344 words

Itama Fauza Abaya ta saka milk and brown tayi kyau sossai barin ma ɗan face ɗinta da ya fita a Tarhan da tayi, ta gaishe shi kan ta gaida Fatima a dakile ta amsa, baki Fauza ta taɓe tare da serving husna tayi serving kanta tunda Fatima tayi serving mijinta ne kaɗai.

Quitly suka ci abincin Dukda ita kam Fauza kaɗan taci ta miƙe ta koma parlor tana jiran shi.

Kallon Fatima yayi yace "Am kin kuwa san yau da yamma husna zata bi iyayenta?"

Kai ta girgiza tace "ban sani ba tunda babu wadda ya faɗa min"

Kallonta yayi kaman ze yi magana se kuma kawai ya fasa, ya lura harshen Fatima ba a kame yake ba Sam bata san yadda zata ke mai magana ba.

Mikewa yayi yana goge bakinshi da tissue hannunshi rike da husna suka fito parlorn yace "mu je ko?"

Mikewa Fauza tayi Fatima tayi saurin cewa "Ina zaku? Ko ka manta kana cikin girki na ne?"

Yace "don ina cikin girkin ki se aka ce ba zan fita da fauza ba? Ko ke kika ajiyeni da dole se kin san duk inda zani?"

Fauza dae bata ce musu komai ba ta kama hannun husna suka nufi ƙasa.

Yace "yarinyar nan husna kaman yadda take ƴa a wurin mu haka kema amma ko kallon arziki da mutunci ba zan ce ya taɓa hada ki da ita ba, ina faɗa miki zata tafi yau amma me? Kina wani bada amsa cikin gatse to in miki yaya kike so?"

Yana kai nan ya nufi gangarawa abunshi.

A gaba ya samu husna ita tana zaune baya ya ja motar suka fice, shopping sossai suka yi mata tana ta basu dariya da hirarrakinta, they all enjoyed the moment Har azahar don Fauza bata da lectures kan suka biya suka ci abincin rana a yadda Fatima ta gayamai bazata dawo ba se huɗu tun jiyan yasa be ma tuna wani jira ta koma ta mai girki ya ci ba.

Daga nan suka yi gida Fauza ta haɗe mata kayan tsab. Sam Faizan be so ta koma ita ɗaya ba amma baze iya kaita ba don akwai tafiyar da ze yi Tuesday da safe kuma ze yi 2-3 days.

Da farko ya tuna ko su je da fauza sede bata da visa, ko international passport be yi tunanin tana da shi ba, Seda suka yi la'asar kan suka fito suka tafi Airport... Suna tsaye wata cabin crew ta iso a shirye cikin irin shigar sun nan bakinta ya ji hot red lipstick se yanga take yi..

"Sir good evening" Ya amsa fuskanshi ba yabo ba fallasa yana nuna mata husna yace "she's my niece nd she will be flying with you guys pls take good care of her"

Ita ce shugabar crew ɗin na yau hakan ya sa yake bata amana kuma sun san shi bashi da wasa, baya shiga harkarsu idan har ba maganan aiki bane, gasu Allah ya ɗaura musu maitarshi da kwaɗayinshi, a yangance tace "Worry not sir, we will make sure we give her all the care and attention from the boarding to departing"

Yace "Good"

Fauza ya kalla se yaga duk fuskanta ba fara'a kaman ɗazu, ya san duk kewar Husna zata yi, dukawa tayi tana rike da hannun husna take ce mata ta gaida kowa da kowa in ta isa.

Kaman kar su Rabu haka tayi ta ɗaga musu hanu seda suka bace kan Fauza ta fara sauke hawayen da take rikewa dama bata son yin kukan ne sbd husnan.

Kawai ji tayi lallausar hannunshi ya shiga cikin nata yana matsewa a hankali alamar rarrashi.

Zare hannunta tayi suka nufi mota, har suka isa gida bata ce mishi komai ba kewan husna duk ya dameta, hakan ya sa suna isa ya je ya duba wayan nan ya bata akan ta kira su jadda.

Ɗakinta ta shiga ta kira su kuwa sun jima suna ta waya har Amminta ta kira suka gaisa saide bayan nan bata ce komai ba ta kashe wayan, tsintar kanta tayi da gwada saka layin sakina ta kira, ringing na karshe ta dauka "Ke! Fauza ce"

Ihu sakina ta saki tana cewa tana ina ne a Abujan? Sun yi ta neman layinta shiru wannan ne sabon layinta? Tace na mijinta ne.

Rahama ce ta karɓa take ce mata Zubair ya kusa haukace musu akan ta kuma har yanzu be hakura da neman location ɗinta ba har fa cewa yake ze kai su baba court sbd an mata auren dole.

Dariya tayi tace "Zubair kenan"

Sam bata san ya shigo ba se ji tayi ya zare Wayanshi daga hannunta yana yi mata wani irin kallo kan ya juya a fusace ya fice yana buga kofan da karfi...

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.

🖤Gureenjoh🖤

27

Ba karamin tashi hankalinta yayi ba ganin yadda ya fita a mugun fusace.. "Innalillahi wainna ilahi rajiun na shiga uku! Yanzu me ze yi tunani?"

Ta furta tana mikewa tsaye, bata taɓa jin buƙatuwar wani ya fahimce ta ba kab rayuwarta se yau, ta san yanzu Fatima ta riga ta shiga ɗakinshi da kyar ta iya barin wa gobe ta ga abunda hali ze yi, wlh Allah ya gani ba da wani niyya mummuna ta kira sakina ba kuma ita yanzu Zubair baya cikin rayuwar ta don har ta mance dashi ma.

Haka dae tayi wanka ta zo ta kwanta ko abinci bata nema ba zuciyar ta fal tunani, washegari da safe bayan ta idar da sallah tana zaune tana azkar taji alamun tashin mota, da sauri ta miƙe taje jikin window se ta hangi motar shi na fita, ajiyar zuciya ta sauke ta dawo ta zauna da gaske fushi yayi? Ta tambayi kanta don ba zata Iya tuna sadda ya fita be gayamata ba tunda suka ɗan fara shiri.

Gari yayi haske taje tayi wanka ta zo ta shirya cikin jalbab ɗinta dogo har ƙasa don tana da lectures, fitowa tayi bayan ta sha cereal ta zuba chocolates masu yawa a jakan bayanta, Fatima ta gani zaune tana karyawa.

Kaman ba zata mata magana ba se kuma tace "mun tashi lafiya?" Ko kallonta Fatima bata yi ba, zama tayi tana jiran ta ko don ta san tana jiran ta ne ita kuwa ta fara jan lokaci, ganin zata ɓata mata lokaci har a shiga lectures yasa ta miƙe ta fice.

Mai gadi ya gaida ta yana buɗe mata gate ta taka da kafa har ta samu taxi ta ɗauki shata ta wuce school.

Se karfe huɗu ta dawo gidan nan ma da taxi don bata ga Fatima ba, Seda tayi sallah ta zo ta shiga kitchen ta fara girki sanin itace yau da girkin, tuwo tayi mishi na doya da miyar ɗanyen kifi bayan ta gama taje tayi wanka tare da sallar magrib ta shirya cikin kananun kaya, ba karamin kyau tayi ba tayi isha kan ta fito ta zauna a parlorn saman Dukda bata ji motsin shi ba.

Se a lokacin Fatima ta shigo basu tankawa juna ba, ita dae Fatima ganinta yasa ta san bata san mijin da ake yiwa kwainanen baya ma ƙasar ba, dariya ta sheke dashi tana cewa "lallai kuwa za'a yi jiran gawon shanu"

Tana kai nan tayi wucewarta ciki, ganin har karfe tara be shigo ba yasa tayi Tunanin ko baya ƙasar, ranta dae ba daaɗi kaman yadda tun safe yake har Afnan take tambayarta tace babu komai, yau gabaɗaya abu mai nauyi be shiga cikinta ba, tuwon ta dibi ɗan kaɗan ta ci kan ta tattara taje ta adana a frigde daga nan ta haura tayi shirin kwanciya ta kwanta.

Washegari bata yi breakfast ba miyan kifin ta yi microwaving ta ci da bread, yau ma bata jira Fatima ba tayi ficewarta yau ma dae haka ta kashe ranar da tunani, lectures ɗin ma bata wani fahimta..

A kwana na ukun har kuka tayi, ta rasa gabaɗaya me ke damunta da fushin shi, da a gidansu ne da yanzu in duka ne an daketa an wuce wurin amma shi ba duka ba zagi kawai ya ɓace mata ba tare da ta san inda yayi ba alhali yana fushi da ita.

Hadari ne sossai ya haɗe garin har ana iska, Afnan ta riga ta wuce ita kuma tana tsaye tana neman taxi da sauri ta sanya hannu ganin motar Fatima amma ko bata tsaya ba tayi wucewarta kuma ta tabbatar ta ganta ba bata ganta ba, da kyar ta samu wani taxi Dukda ya tsula mata kuɗi bata damu ba ta shige da sauri sbd ita bata son ruwa ya taɓa ta, ko yaya ya jiƙata se tayi mugun zazzaɓi.

***

Karfe shidda ya iso gidan yayi parking motan shi da dama Airport ya kan bari yayi tafiyar shi, Gaisawa suka yi da gate man kan ya wuce ciki yana kallon motar Fatima dake nuna alamun bata jima da shigowa ba.

Gidan ya shiga yana jin wani kewa chan ƙasan ranshi da duk yadda yayi kokarin dannewa ya ƙi dannuwa, lumshe idanu yayi ya buɗe a sadda ya shaki sassanyar turaren wutan da ta kan yi anfani dashi wa gidan, a natse ya haura yana jin yadda aka tsuge da ruwan kaman da bakin ƙwarya.

Ɗakin Fatima ya fara shiga tana ganinshi cikin farin ciki ta tare shi tana mishi sannu da dawowa, ya amsa fuskanshi a sake kan yace bari ya duba Fauza se yaje yayi wanka.

Tace "Ai ina ga bata dawo ba fa..."

"Bata dawo ba?" Ya watsa mata tambayar cikin mamaki.

Kanta ta mayar ƙasa tace "eh bata dawo ba don ban ji shigowarta ba"

Yace "ban gane ba, ina ce tare kuke tafiya ku dawo? Ya aka yi ke kike gida ita bata nan? Me ze ajiye ta a waje har an yi magrib?"

Tace "ni dae wlh ban sani ba, abunda na sani dae tunda ka tafi bata sake tsayawa mun tafi tare ba taxi take fita ta hau haka dashi take dawowa Dukda nayi kokarin jan hankalinta akan baka son ɗabi'ar shine ma musababbin da yasa ka saya min mota amma taki saurare"

Be tanka ba sbd yadda ya sake jin sabon ɓacin rai na rufe shi a kanta, duk yadda yake kokari akan yarinyar nan me yasa take so ta fara bashi matsala? Sau nawa ya gayamata baya so matarshi ta hau taxi? Ɗakinta ya wuce kamshin ta na tashi a ɗakin wadda ya dawo mishi da sabon kewanta kaman yadda ya kashe kwanaki biyun cikin kewar nata ko abincin kirki bai iya ci.

A balcony ɗinta ya tsaya dake shine ke facing gate, ya rasa hukuncin da ya kamata ya ɗauka a kanta, sheɗan ke ta wassafa mishi kila tana chan da Zubair tunda har ta fara ambatarshi, hangar taxi yayi ya sauke ta, ba lema hannunta hakan yasa cikin hanzari ta iso gate ɗin ta fara bugawa saide gate man ɗin kaman baya kusa don baya jinta, ta kai mintuna biyu tsaye cikin ruwan tana knocking da ƙarfi sede ƙaran ruwa ya hana gate man ɗin ji, ya so ya kyale ta ruwan yayi ta jiƙata se kuma ya ga baze iya ba.

Da sauri ya juya ya nufi fita ganin ta juya itama ta bar gate ɗin da sauri sauri, da hanzari ya buɗe gate ɗin ya fara duba ta, chan ya hangota tana tafiya tana dube dube ko zata samu inda zata fake kan ruwan ya tsagaita..

Sam bata san da isowar mutum ba se ji tayi an ɗaura mata wani suede me kauri wadda a take ta dena jin Sauƙar ruwan jikinta, a hankali ta ɗaga kai se suka Haɗa idanu ruwan na zuba a jikinshi sossai.

"Yaa..." Be bata daman magana ba ya riƙo hannunta suka juya suka yi gida, a kofan ɗakinta ya saketa ba tare da ya bi ta kan suede ɗinshi ba ya shige dakinshi.

Ta ɗan jima tsaye a wurin kan ta shige ta cire suede din ta ajiye ta wuce toilet ta cire kayanta da ya jike gabaɗaya ta hada ruwa me zafi sossai tayi wanka, a ɗakin ta Haɗa tea me kauri da zafi ta sha jin jikinta ya fara rawa alamar zazzaɓi.

Da kyar ta iya gabatar da sallah kan ta hau gado ta ja bargo ta shige tana rawar dari.

Yayi wanka shima ya sauya kaya ya fito ya duba Fatima yace ta sama mai wani abu marar nauyi don yana jin yunwa, ranta fal farin ciki sanin yayi fushi da fauza ne tunda girkin ta ne amma ya saka ita tayi mishi.

Kitchen ta shiga ta sama mai abinci yana zaune a parlor yana kallon Tvc news ta shigo ta ajiye mai, kallon kofan Fauza yayi kan ya maida kan abincinshi ya fara ci yana Tunanin me ya hanata fitowa ta nemi wani abu ta ci?

Har ya gama ci suna tare da Fatima, tana ta kokarin jan hankalinshi sede idanunshi ne kawai gareta, tana tattare kwanukan ya miƙe ya nufi ɗakin Fauza ɗin.

Kwance ya tarar da ita tana rawar ɗari sossai, yaye bargo yayi ya taɓa gefen wuyanta wani irin zafi jikinta yayi da har yayi saurin zare hannunshi, da kyar ta buɗe idanu ta kalleshi..

Harara ya zabga mata, kan yayi tsaki ya wuce toilet ɗinta towel ya samo da ruwa ya zo ya karasa yaye bargon yana ɗauke idanunshi daga kan santala santalan cinyoyinta da suka bayyana, ɗagota yayi ya fara saka Towel nan a ruwa yana shafa mata, wani irin numfashi take saukewa wadda ke rikirkitashi ganin ruwan baze Sauƙar mata da zazzaɓin ba gashi ta fara mishi kananun kukan fita hayyaci ya sa ya rufe ta da faɗa don abubuwa dayawa ne suka haɗu mai.

Sossai yake mata faɗan abubuwan da ta aika ta ɗin, harda taurin kanta take shirin dawo mai dashi to baze ɗauka ba, shi ba lusarin namiji bane da ze ke gindaya mata sharudda tana tsallakewa he could remember vividly yadda ya gayamata baya so matarshi ta hau taxi amma me ta aikata? Har tana tuna wani katon gardi ɗan shaye shaye cikin gidanshi.

A hankali ta sabule daga hannunshi da yake rike da kafadunta ta faɗa jikinshi tare da kankameshi tana kuka kawai don bazata iya magana ba.

Tsit haka maganan ya yanke mai, ya sanya hannu ya tarbeta, fuskanta take ta gogawa bisa kirjinshi alamar tana kara fita hayyacinta ne, da sauri ya kwantar da ita ya kashe wutan ɗakin tare da zare jallabiyar jikinshi, ya saura daga shi se boxer, Rigan jikinta ya cire mata don bata taimakon body contact kan da safe su tafi asibiti.

In a romantic way ya sanya lallausar hannunshi ya ɗagota a hankali ya kwanta kan yayi mata masauki a faffaɗar kirjinshi, a tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya, mannewa ta sake yi ta shige jikinshi kaman zata tsaga shi ta shiga ciki sbd sanyi da taji jikin nashi na dashi wadda hakan ya bashi daman sake kanainayeta ya cusa fuskanci tsakanin wuyanta yana sauke numfashi me nauyi, cikin wani irin salo yake shafa mata sajen nashi a hankali hankali cikin wuyanta, siririn ƙara ta sake tana kara kankameshi jin ya saka babban ɗan yatsan kafan shi yana wasa da tafin kafafunta, duk su biyun sun haukace da wannan masifaffen body contact da suke samu, shi da yayi da niyar taimako ma ya fi azabtuwa.

Hmmm wani irin moment ne suka yi spending wadda baze Mantu ba, gabaɗaya seda ta gigitashi da albarkatun jikinta wadda duk ba cikin hayyacinta take hakan ba, ba jikinsu kaɗai ba a lokacin ze iya rantsuwa cewa numfashi ma guda ɗaya suke yi ba biyu ba, Seda suka shafe mintuna sama da talatin suna rabawa juna temperature ɗinsu kan ya mirginata, hancinshi yake gogawa da nata yana jin yadda su biyun duka numfashi ta hanci yayi musu kaɗan suna Haɗawa da baki, a hankali ya fara brushing lip ɗinshi kan nata, yana kokarin haɗe lip ɗinsu tayi wani miƙa da ya tabbatar da zazzaɓin ya sauka, yaraf ta dawo kan pillow a take wani wahalallen bacci ya sure ta, zamewa yayi ya kwanta daga gefenta yana jin yadda zazzaɓin tan ke shirin dawowa jikinshi.

Bacci me nauyi ne ya kwasheta yayinda shi kuwa yace be san zance ba, janyo ta ya sake yi jikinshi ya rufa musu bargo sbd jikinshi wani irin rawa yake yi... Ya fi awa kwance cikin wannan yanayi Ganin in yana cigaba da barin ta haka a jikinshi komai ze iya faruwa ya sa ya miƙe dafe da marar shi ya fice a ɗakin.

Kitchen ya shiga ya matsa lemon tsami a lipton ya kwankwade tunda yau ba kwanan Fatima bane bare ya rage wani abun, tunda yake be taɓa jin irin wannan sha'awa ba se yau, ɗakinshi ya shige ya zube rub da ciki bisa gadon shi yana juye juye.

Ita kuwa bacci tayi sossai, chan wuraren karfe uku na dare taji kaman ana kiran sunanta, cikin gigin bacci ta buɗe idanunta se taga ɗakin gabaɗaya ya sauya mata ya koma wani irin Ƙango me cike da abubuwan razanarwa, a firgice ta miƙe sede bata iya ambaton komai ba kaman ɗaure mata baki aka yi ko numfashi da kyar take iya ja amma bakinta ya ƙi furta komai.

Wasu irin abubuwa taga suna motsi daga jikin ginin ɗakin, sanyi taji me yawa a jikinta waigawar da zata yi taga wani irin hallita da bata taɓa sanin akwai irin shi ba baƙi sidik, me munin gani da razanarwa, ƙara ta saki wadda taji muryar yayi amsa kuwwa iya ɗakin, da sauri ta sauƙa jikinta na rawa ta nemi riga ta saka ta suri hijab ɗin sallarta ta saka, jakan da ta dawo dashi jiya ta zara ta fice da sauri daga ɗakin.

Parlorn kasa taje chan lungun dining ta makale ta takure Kaman wacce ta rasa gata, jikinta wani irin karkarwa yake gabaɗaya bazata ce ta san me take yi ba, banda tsanar gidan da tsananin tsoronshi babu abunda take ji.

Tana nan har aka kira sallar asuba fuskanta har ya kumbura da kuka, kaman wuta ake rura mata a gidan haka take ji, tana ji ya sauko da nufin tafiya masallaci, da sauri ta miƙe ta bi bayanshi yana fita itama ta fice daga gidan ko waiwaye babu....

**Ayi comment in takarkare in baku na dare😎**

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Se ki tura shedar biya ta wannan layin 09039206763. Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.

🖤Gureenjoh🖤 DƘ

28

Saboda rashin baccin da be samu ba jiya ya sa ko azkar da kyar ya iya yi ya mike ya dawo gidan, ɗakinshi yayi direct ya kwanta ba shi ya tashi ba se wuraren karfe goma sha ɗaya, wasai haka ya ji shi Adu'a yayi kan ya sauƙa ya wuce toilet ya watsa ruwa har a lokacin ze iya cewa yana jin tsadaddiyar jikinta cikin nashi, yana jin duk wani moment da suka yi spending a jiyan cikin ƙashi da ɓargonshi.

Haka ya gama wankan ya fito ya shirya cikin kananun kaya, fitowa yayi yana baza kamshinshi me natsuwa da kwantar da hankali, ɗakin Fatima ya fara dubawa bata nan da alama ta tafi school, ɗakin Fauza ya nufa haka kawai ya tsinci kanshi da sakin murmushi.

A hankali ya tura kofan saide turus ya tsaya ganin kaman an yi wasan kura a ɗakin, komai kaca kaca a wargaje abinda ba ɗabi'arta ba.

Sunanta ya fara kira yana shiga ciki ciki sede bata kan gadon, bayin tura ya shiga nan ma bata nan. Saukowa yayi kasa ya je wurin Peter yake tambayar shi ya ga fitan Fauza ko tare suka fita da Fatima?

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull