Kenza eBookz

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 14

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 14

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 14: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 14. Abida ta ce "Sosai fa Allah dai ya sanya muna da zafin yawu…

3,876 words

Abida ta ce "Sosai fa Allah dai ya sanya muna da zafin yawu Bilki". Abida ta fice zuwa ɗakinta da hanzari yayin da Bilki ta sake tsorata idan har Abida yadda take cikakkiyar yar boko, mai kuma baudadden hali, sannan a bayyane yake Abida bata son maza, kusan ma feminist ce amma ta shiga tarkon namiji take karban kebra masu radadin gaske ai dole ita da take sonsu ta lallaba ta iya takunta tun kafin abin ya dawo kanta. Sai dai kuma tabbas ba zata bari ya dinga daukar hakkinta yana bawa yara ba, haka nan ba zata lamunci su dinga cin zarafinta yana kallo ba zai dauki matakin da ya dace ba. Daidai lokacin Abida ta dawo d'auke da jotter da biro a hannunta. Ta zauna gefen gadon ta mikawa Bilki ta ce "duba ki ga ni." Bilki ta karɓa tana karantawa. Ta kammala ta ce "Zamu iya yinsu ai babu wahalar yi. Kin ga kiranye yaya Asad ba zai yi wuya ba tunda kiran sunan nasa daga kansa ne zuwa kan kakanmu na biyu. Amma na Yaya Sulaiman fa zai bamu wahalar gaske ina muka san kakanmu na shida?" Abida ta ce "Na rantse idan har na ga wannan ta ci zan gurfana gaban Baba ne ya fad'a mini sunan kakansa na biyar ". Bilki ta gimtse dariyarta akan dole don idan ta tsananta yin dariya yanzun nan gayyar zata waste. Sun yi alwallah zasu fara yin sallar daga nan su zarce da yin wuridin kafin junior ya tashi. Bilki ta ce "Idan na yi Ladifu d'ari ba d'aya cikon na d'arin ne zan ce "Asad ibn Musa ibn Garba ibn Bello ko?" Cikin gasgatawa da yin imani Abida ta ce "Yauwa kin fahimta haka ma za ki yi idan kin yi iyaka na abudu 99 cikon na 100 din ki kamo sunansa har zuwa kan babansa na uku. Damu suke zancen". Suka yi sallar la'asar suka dukufa wuridin Iyaka na abudu wa iyaka nasta'in da kuma ya Ladifu. Fiye da shud'ewar awa guda suna yi, tun Bilki na yi da cikin iyashege da dariya har ta gimtse take yi da gaske, tabbas tana son ya zo amma idan ya so din ba binsa zata yi ba, tare da an baje magana a faifai ba. Suna daf da kammalawa wayar Bilki ta hau kuwwa alamun k'ira ne. Abida ta yi maza ta ce uhum uhum tare da girgiza kanta da k'arfi alamun kada ta katse wuridin. Bilki ta fahimci manufarta dan haka bata katse ba ta bar wayar ta katse dan kanta. Sai dai k'iran cigaba ya yi da shigowa har sau uku sannan aka tsagaita. Sai biyar da kwata suka kammala. Abida ta ce "Bari na dauko wayar mu ga ko shine aka fara tsikarin zuciyarsa, ai ba dan so nake ya ji jiki ba, da na tab'o shi na ji halin da yake ciki". Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:29] Jikin Bilki ya yi sanyi da yadda ta ga Abida ta dage tana taya ta jin ciwon abin da ya yi mata duk kuwa da a bayyane yake Baba da Momi ne kawai suka sha gaban Yaya Asad a wajenta. Akwai kauna ta mussaman a tsakaninsu kamar dai ita da yaya Sulaiman. A zuciyarta take ayyana ko zata iya taya Abida dankwafe Yaya Sulaiman kamar yadda take yi mata akan Yaya Asad a yanzu? Ta kasa bawa kanta amsa don ita kanta bata sani ba a yanzu sai zuwa gaba tukun. Abida ta yi shewar murna tare da fad'in "Wallahi shine! Ta jijjiga kai cikin gamsuwa ta ce "Yanzu muka fara har sai ka kawo kanka gaban Baba." Daidai lokacin k'iransa ya sake faɗowa wayar. Abida ta dauka ta gaishe shi ta ce masa barci take yi. Ya numfasa ya ce "Autar Momi wai mun bata ne?" A sanyaye ta ce "Me ka ga ni Dady?" Ya ce "Tun shekaranjiya yarinyar nan ta baro gida ban sa ni ba, amma ko ki k'ira ni Abida?" Ta numfasa ta ce "Ai da yake ni mace ce, kasan duk haka muke bama son a taka mu". Jikinsa ya yi sanyi don Abida bata fadan rashin gaskiya, duk anincin da kusancinta da mutum bata bin bayan k'arya. Hakan ya sanya suka yi ta samun sabani na gaske shi da Rukayya don zai iya ce wa duk rikicin da zasu da ita mai tsanani akan Abida ne. Bisa hujjar Rukayya na yana fifita Abida fiye da ita, sannan ba dama Abida ta ganta da zani ko gold sai ta ce tana so, shi kuma sai ya siya mata fiye ma da nata. Bayan haka ta ce Abidan ce take b'ata ta a wajen Momi, shiyasa Momi tafi son matar Faruku da ta Usman a kanta. Shi kuma ya gane Abidan gaskiya ta fita, itace take k'yashin hidimar da yake yiwa kanwarsa, ta kuma yi kuskuren da ta bari Abida ta gane tana kishi da ita shiyasa ita kuma take baje mata kalolin shegantaka kalakala tare da yin shagulatin bangaro da ita, tana kanbabama sauran surukan gidan fiye da ita. Jikinsa ya yi sanyi don ya lura itama fishi take taya Bilki. Ya numfasa ya ce "Siyar mini jarida Abida! Me ta fad'a miki na yi mata da ya sanya ta yi mini yaji?" Ta murmusa a dalilin ya ce ta siyar masa da jarida tabbacin tuna mata da k'uruciyarta ya yi. Ta ce "Yara na zaginta har kuma da yar sakabu tsabar samun wuri, kai kuma ba zaka tsawatar ba, ba gara ta gusa ba". Ya yi turus don kamar camfi Idan Abida bata baka support ba, baka yin tasiri. A sanyaye ya ce "Yanzu tsakaninki da Allah ya kamata ta banbanta y'a'yana da nata?" Kaitsaye ta ce Bai kamata ba". Yauwa autar momi ita Maigado wata irice, kullum tana mak'ale da Farha Amal da Noor a ware da k'yar na banbare wariyar da take nunawa, yanzu da zata yi yaji sai ta dauke Farha ta watsar da sauran indai don Allah ne mai zai saka ta bar su tunda sun saba da ita sun Kuma Saba da Farha. Na fita Sai kawai na dawo na tarar Babu ita babu Alti da Farha, zan ji dad'i? " Jikin Abida ya yi sanyi ta ce "Ta yi kuskure amma fa bai kai naka ba gaskiyar magana. Ko rashin zuwanka nasan daga Yaya Faruku da ya baka ita har baba sai sun diga maka ayar tambaya". Ya nisa ya ce "Gobe zan zo in sha Allah bana jin dad'i ne yanzu. Bata wayar". Nan da nan Abida ta ce "A a barci take yi, zuwa bayan magariba ka sake k'ira, sannan ta tashi." "To" Ya fad'a a sanyaye. Yayin da Abida ta jijjiga kai ta ce "Duk taurin kanka Sai mun lausasashi da wuridin nan ". Ta kalli bilki6da take zaune ta ce "Maigado this very powerful du'a. Zamu fara yiwa yayanki". Bilki ta murmusa ta ce "Bayan kin k'wace mini shi Abida! Murmushi Kawai Abidan ta yi.

Washegari sassafe zai fita a motarsa ya d'auki Bilkisu da Laura, suka kai ta har makaranta shi da tawagarsa ya k'i daukan Hafcy ya ce direba ya kai ta wanda hakan ba k'aramin damuwa ya jefa ta ba, karon farko da ya fita a harkarta don kuwa kowa ga ni yake yafi sonta. Har cikin gate din makarantar suka shiga da ita. Sosai Bilkisu ta ji dad'in wannan k'aramcin da Dady ya yi mata don ba zata iya tuna rabon da ya kawo su makaranta da kansa ba. Dan haka zata sake kamewa daga shiga rikicin da ba zai amfane ta da komai ba, tunda ta yi ba dawo da Momi zai yi duniya ba, ba kuma shine dalilin da zai saka ya auri anty Laura ba. Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:32] Kaitsaye Kaduna suka nufa suka kai Laura har gidan gaban Hajiya, kaitsaye ya mata bayanin rikici suke yi da matar gidan tunda itama yarinyace zaman nasu ba zai yiwu tare ba. Dan haka a yi hak'uri amma har gobe shi ne ubanta dan haka ba abin da ba zai yi mata na hidima ba, komai ya shafe ta yana kansa zai yi, kada kuma a ji nauyin fad'a masa dukkan al'amarinta. Sannan idan maneminta da gaske yake yi to ya turo a yi maganar aure. Ya ajiye mata bandir din y'an dubu dubu sabbi k'al guda uku. Bayan kayan abinci da aka ta shigowa da su masu yawan gaske. Ba kuzari Hajiyar ta yi masa godiya. Ya yi sallama ya tafi. Hajiya ta ja dogon tsaki ta ce "Namijin hotiho sallamamme na namamajo ko yaushe Bilkin ta zama yarinya? Abu da tana da budurwar yarinya. Kawai ita ta saka ya koro ki tunda tana ganin da aure a tsakaninku, don babu yadda zata yi da su Aysha. Zaman lafiya kuwa babu shi a gidansa".

Laura cikin kuka ta ce "Wallahi Hajiya "A kanta ne, dama ta fad'a mini "Sai ta saka ya yi mini korar kare ga shi kuwa don da asubar yau din nan da ya dawo daga masallaci ya ce mini na shirya zai zo Kaduna ta'aziya zai sauke ni a gida, su Ayshan ma gabad'aya ya fita a harkarsu cikin kuka na barta ita da Hafcy. Bilkisu da su Amal kawai yake kulawa." Hajiya ta sake jan dogon tsaki ta ce "Dama Bilkisu ba tamu ba ce tunda ya saka mata sunan shegiyar ai dole ta zama munafuka don kuwa suna na tasiri! Ta fad'a cikin k'unan rai. Ta sake zabura ta ce "Irin kuttun da Rukayya ta sha akan yaran nan ba dama ta doke su ko ta hana su cin abin da suke so ita da ta haife su ma, amma wannan ja'irar harbta samu lasisin karya Hafcynsa amma ta kwashe kalau, sannan har tana da kuzarin hana a yi musu girkin da suke so Duk yana kallo? Tabbas ita ta biyo sawun uwarta na dibar albarka, ban da ta fita ta shiga ta ga gidan daula ta karkato da hankalinsa da na ubansa har ya kalle ta mabare aure ya gitta a tsakaninsu? Ai ko Alhaji Musa ba haka ta bar shi ba, tunda kotu suka maka shi Allah ne yasa bai kanannade ba saboda tsananin bak'incikinsu da na shedaniyar uwarsu, ta ta baza mugun iri." Da kuka Laura ta ce "To Hajiya kawai ke ma ki shiga, ki fita ki wasko mini kansa dan Wallahi sonsa nake yi! Ta fad'a cikin kuka na tashin hankali. Jikin uwar ya yi sanyi tub'us. A sanyaye ta ce "A a Laura ba ni da halin da zan yi shiga da fita irin nasu, kinsan an ce kudi ne da ita, sannan gadonsu da aka raba ai ba k'aramin kuɗade da kadara suka samu ba. Irin wnanan don su kashe milyoyin kudi akan buk'atarsu ba komai ba ne. Ki dai yi hak'uri tunda Har ya kawo ki gabana da kansa ai kinsan tafi k'arfinsa Idan ma kin shiga ke ce a ciki. Ni kuwa da ki yi zmaan boranci a gun miji gara ki hakura, ki auri Wanda kike so ba Wanda ke kike so ba. Mu duk zuri'armu Bama boranci ba kuwa zan yarda ke ki fara ba, shi din ma AI kwallon shege ne wacce wuyar ce Rukayya bata sha a hannunsa ba? Kawai idan mace tana auren mai wadata sai a yi ta mata kallon jin dad'i. Amma yadda ya fifita ahalinsa akanta da yadda yana ganin ibilishiyar Abida take mata isgili kala kala, take wareta tana son sauran matan y'anuwanta amma ita tana kallonta kamar kashi kinsan dama ya bayar a taka Rukayya ai. Tunda ya ce kallon diya yake yi miki, to ki yi hak'uri ki yi kwance kwance ki ta tatsar ja'iri.

Wurin azahar ya isa Abuja sai dai ba samu zarafin isa gida ba sai wajen azahar saboda a dalilin matsanancin goslow. Kaitsaye gidansu ya zarce. Cikin sa'a ya tarar da baba da Faruku suna zaune a babban falon dawowarsu daga masallaci kenan, ruwa ya goce. Jira suke yi jiran ruwan ya dauke Faruku ya raga Baban tattakin da yake yi da yammaci don sosia tlyake jin dad'in jikinsa idan ya yi atisaye din. A cikin motar ya bar yaransa a dalilin ruwa zai jikasu. Kaitsaye ya shiga cikin falon ya yi sallama suka amsa masa babu wani walwala. Jikinsa ya yi sanyi ya isa gaban Baba ya cire hularsa ya yi saluting d'insa sannan ya tsugunna yana gaishe shi. Baban ya amsa ciki ciki fuska a daure. Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:35] Faruku ya mik'a masa hannu ba wani karsashi.a Nan da nan ya fahimci fishi suke yi da shi. Bai zauna ba yana durk'ushe Kan k'afafuwansa tamkar mai zaman tahiyya. Murya ba amo ya ce "Baba ya jiki dafatan baka cikin damuwa?" Baba ya harzuk'a matuƙa da gaske. "Cikin kunar rai ya ce "Kusunuwarka Asad! Ba Asad din da aka zaga ba, hatta Farouku zabura ya yi don kuwa basu taɓa jin ya yi zagi irin haka ba, duk kuwa da yadda ransa zai baci dama Baba k'arami ne ainihin Bakatsine shine yake danna musu ashariya kala kala. Hankalin Asad ya yi mugun tashi wannee irin abu ya yi mai muni haka da ya saka mahaifinsu fusata ya yi masa zagin da bai taba yiwa wani sun ji ba. A gigice ya ce "Dan Allah Baba ka yi hak'uri, a gafarce ni! Baba ya ce "Ni zaka yiwa wulakanci irin haka? Me kake da shi, waye kai?" Murya na rawa ya ce "Dan Allah a yafe mini Wallahi ban san me na yi ba". Ran Baba ya ce "Oh baka san me ka yi ba kake fad'a mini? Na d'auki yarinyar nan na baka bayan an sha dogon fama da ita kafin ta amince da kai shine da ka cimma manufarka sai ka mayar da ita banza da wofi a cikin gidan, ka k'ure hak'urinta ta taho wajena, shine ka yi zamanka idan na matsu zan neme ka da kaina saboda kana ganin kai wanine ko?" Murya ba amo "Ya ce "Ko kad'an ba haka bane Baba, amma na gamsu na yi laifi a duba Allah a yi mini afuwa, fishinka irin haka a kaina guba ce dan Allah Baba! Ya fad'a a rikice ainun. Nan da nan kuwa baba ya sassauta ya dinga yi masa nasiha tare da nuna masa illar gooyin gatan da yake yiwa ya'yansa da sunan tausayi. "Ka bari sun sangarce su an kai su d'akinsu su kasa zama lafiya da mazajensu saboda ba'a masu tarbiyar da ta dace da su ba". Kan Asad na k'asa ya ce "Duk na d'auki matakin gyarawa, in sha Allah Baba za'a ga sauyi, a mini hakuri". "To batun yarinyar nan k'anwar matarka lallai ta koma gaban gyatumarka duk abin da zaka yi mata na alheri ka aika mata zaman ya isa haka". Cikin nutsuwa ya ce "Yanzu ma daga Kaduna na ke da kaina na mayar da ita gida. Dan Allah Baba ka yi hak'uri". Baban ya numfasa ya ce "Ai yanzu tunda Bilki ta kwnaa biyu baka nemeta ba na gasgata Lallai Sulaiman ba ni kad'ai zai iya yiwa wulakanci ba Har Baba k'arami don kullum sai na yi kukan da mahaifinsa na da rai AI ba zai yi mini abin da ya yj ba, amma kai ma da gwada mini Sai na gane ashe fahimta ne ban yi daidai zai yi mini ko baban naku na da rai". Faruk6ya kamu da tausayin Babansu don kuwa babu yadda za'a yi rana ta fito ta fadi Baba Bai yi maganar Sulaiman ba, kullum bakinsa da zuciyarsa na ambatonsa amma Shi dan tsabar iskanci ya yi tafiyarsa ya bar kowa da kowa babu waiwaiye. Ya k'udire a ransa duk ranar da ya dawo gida tabbas sai ya saka saka dorina ya zane shi ciki da Bai yasan ba zai cukume Shi da fad'a ba, amma bak'incikn da ya kunsa musu ya kunsawa baba Babba ba zai tafi a banza ba. Sai ya tabbatar masa dan babu baba Karami ba shine zai yiwa Baba Babba wannan dibar albarkar kuma ya share kalau ba. Hankalin Asad ya kai k'ololuwar tashi ta ya ya baba zai kwatanta laifinsa da na Sulaiman din da ya shafe shekaru uku yana cikin ta hud'u da fantsama duniya? Kwanaki biyu kacal da bai zo ba, alhalin shima ta ci mutuncinsa, bayan haka ba cewa ya yi ta taho ba ai, inda wanine mijinta ya tabbatar a take za'a mayar da ita tunda zaman Abida a gabansu ba k'aramin dukansu yake yi ba gabad'ayansu. Murya babu amo saboda tashin hankali ya ce "Ka yafe ni Baba, na ci darajar manzon Allah! Gabad'aya suka ce "S.A.W.. Baba ya nisa ya ce "Na hak'ura amma lallai ka yi gyara a gidanka, ka san me kake ci, sannan lallai ba Aysha kad'ai za'a aurar ba har da Hafsatu , itama Khadijah da take London tunda bana zata gama duk a had'asu a kawar da su. Idan babu maneman sai a nemo musu". "To" Baba ya amsa a ladabce. Sannan ba zan ce Bilki ta koma ba, Faruku ma ba zai saka baki ba, ka yi mata magana da kanka idan ta yarda zata bika ku koma haka nake so, idan ba ta yarda ba to lallai zata cigaba da zama har zuwa sanda zata sami nutsuwa. Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:39] Asad a zuciyarsa ya ce "Ai kuwa Wallahi ba zan yarda da wannan hukuncin ba tunda tauye ni aka yi da nuna son kai". A fili muma ya ce "Na gode Baba Allah ya k'ara lafiya." Daga haka ya mike ya nufi d'akin Momi . Jikinsa ya sake mutuwa a dalilin a shake ta amsa gaisuwarsa har da yi masa shaguben ba zai hucewa Baba Babba takaici ba, tunda tun yanzu murnarsa ta fara komawa ciki na kyakkwan zaton al'amura zasu daidaita a dalilin aurensa da Maigado. Ya dinga bata hak'uri. Ta ce ita ba ruwanta amma tabbas ba zata saka baki Maigado ta koma gidansa ba tunda ba tsarin musulunci yake bi wajen yiwa yara tarbiya ba. Idan ya shawo kanta ta huce ta ce zata koma shikenan. A sanyaye ya bar dakin ya nufi na Abida. Ya ga bata nan. Ya tuna Ashe bata dawo daga asibiti ba. Ya fito ya shiga na Maigado ya tarar tana kwance. Ya Kira sunanta yafi sau biyar ta yi bakam ita ala dole barci take yi. Murya a dakushe ya ce "Duk wulakancin da kika yi mini na zargina da yarinyar da nake yi mata kallon d'iya hakan bai isa ba sai kika saka k'afafuwanki kika bar gidana babu iznina, kika dauko diyarki, kika watsar mini da yara. Sannan kika mini sanadin fishin Baba da Momi ko?" Ta yi shiru tana sauararensa zuciyarta ta fara karyewa don yadda yake magana babu kuzari tasan a rikice yake ainun.

*Dan Allah ku dinga dannawa labarin nan likes a YouTube.* *Episode 1_10 Kawai ake buk'atar likes din.* *Na gode muku gabad'aya Allah ya saka da alheri*.

*Surayya Dee* ✍ [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ta cuno baki cikin fishi na sosai ta kawar da fuskarta daga kallon gabas ta mayar zuwa arewa. Ya sassauta ya sake matsowa kusa da ita sosai ya ce "Zo mu tafi gidanmu kin ji Maigadona. So nake yau mu jijjiga gadon zinaren nan na ki da kyau. Ta so mana ai na ce ba zan sake ba, ki huce dan Allah kin sa duk ahalin gidan sun dau fishi da ni ba kuma wanda ya yi nufin taimakona a cikinsu." Ko uffan bata ce ba. Ya gurfana a gabanta ya ce "Zo ki d'are na goyo ki, mu tafi gidanmu". Dariya ta subuce mata, dattijo da shi zai wani ce ta ta zo ta d'are alhalin Baba babba ko momi zasu iya ganinsu. Wato dai shi namiji babu ruwansa da kunya. Ta kawar da fuskarta tare da ce wa "Ba fa zan koma ba, ka yi tafiyarka, na riga da na gane ba zan iya wannan zaman ba. Ban iya yaudara ba, idan ma na iya ai ba zan yaudare ka ba Baban Bilkisu! Ka yi hakuri kada maganar nan ta sake cakalcakala mana al'amarinmu". Ya mike tsaye cak. Ya zuba mini idonsa na saci kallonsa na ga har wani tsumuwa yake yi watakila da wani k'aramin d'an sanda ne ya bata masa rai da ya d'and'ana kudarsa domin ya fusata ainun. Da kakkausan harshe ya ce "Kawai dama dai ki ce auren manufa kika shirya yi da ni?" Ya yi mata kwarjini k'warai da gaske, tsoronsa da ta rayu da tashi ya taso mata. Ta kasa ce wa komai. Jin bata ce komai ba ya sanya ya sake maimaita tambayar da ya yi tabbacin amsatra yake dako. Murya na rawa ta ce "Ba Hakan bane ko kadan. Ban same ka a yadda na zace ka bane. Na dauka ka aure ni dan kana sona kana kuma burin ka rayu da ni cikin adalci da jink'ai tare da wanke mini dukkan bak'inciki da na kwankwada. Sai dai tun tafiya bata yi nisa ba na gane manufar aurena bata wuce ace kana da iyali a idon jama'a ba, sai kuma dan ka sauke buk'atarka a duk sadda ka so. In ka cire hakan babu wani dalilin so, ko tausayina a tare da kai da na ga ni a aikace idan kuma akwai to tuna mini dan ni ban gansu ba." Ya numfasa ya ce "Amma ai na ba ki hakuri, na ce zan gyara dukkan laifukuna, indai ba wani abu bane a ranki ai sai ki bani wata damar, idan ba ki ga sauyi ba, na amince da kaina zan dawo da ke gaban Baba babba cikin mutunci za'a yi komai tamkar yadda ya ba ni ke cikin mutunci. Da hankalinki Maigado ba za ki taimake ni ba, gabadaya fa daga Momi har Baban fishi suke yi mini. Ba akan komai sai a kan ki" Hawaye ya b'alle mata ta ce "Saboda hakan ai na ce zan tafi na kama haya, ba zai yiwu na ce ba zan zauna da kai ba, sannan na zauna a gabansu indai ina da kunya da mutunci " Kuka sosai ya k'wace mata, yinsa take yi tunda ga k'asan zuciyarta. Tare da ayyana dama dai ta yi hakuri ta rayu da y'ay'anta, da ta yi hakuri bata tirsasa mijinta ya sake ta ba, da yi zamanta a gidanta ta rayu da ƴay'nta. Idan mijin ya zo fine Idan bai zo bama fine. Don ta riga da ta saba da rik'e gida, dan haka ba zata gaza ba. To ko bai kawo komai ba. Tana da rufin asirin da zata rik'esu ba tare da ta ji komai ba. Amma yanzu ta bar yaranta suna ragaita a hannun yarinya k'ank'anuwa, ta zo tana hidima da yaran da suke ganinsu daidai da ita sannan babu godiya ko yabo a wajen mahaifinsu. Kukan da take yi, ya yi matukar tayar masa da hankali domin dai ba yaro bane ya fahimci kukane na tsantsanin damuwa. Kukane mai nuna kololuwar gajiya da kunsar bak'inciki. Jikinsa ya yi sanyi sosai ya ce "Dan Allah ki yi hak'uri! Gaggawa fa kika yi, dama zan d'auki mataki kuma yanzu haka fa na mayar da Laura gida tunda kin ce ba zata zauna miki a gida ba. Ki yi hak'uri ki yi mini uzziri."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull