Kenza eBookz

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 15

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 15

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 15: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 15. Ita dai bata iya bude baki ta ce masa uffan ba. Ba kuma ta…

4,497 words

Ita dai bata iya bude baki ta ce masa uffan ba. Ba kuma ta ji a jikinta zata motsa bare ta ba shi amsa ba. Don kuwa ita dai ta riga ta gaji da yadda take rayuwa cikin gidansa. Ya yi rarrashi, iya rarrashi amma bata tanka ba. Ya gaji ya zauna yana fad'in "Innalilahi wa inna ilaihir rajiun! Ya dafa kansa da alamu suka nuna juya masa yake yi ko kuma ciwo mai tsananin gaske. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "Murya babu amo, kuma cikin bacin rai ya ce "Da kina sona Bilki na tabbatar za ki yi hakuri da dukkan laifukana, za ki jure, bare na ce ki yi hakuri zan gyara. Amma kin kafe na tabbatar da ace Faruk kika aura za ki yi hakuri da matsalar da tafi wannan tsanani a tare shi, na kuma yi imani kin ci karo da matsalolin da suka fi wannan nauyi da tozarci a cikin aurenki da yaron can, amma ba wanda ya taba ji ko ganin kin yi yaji kin bar gidan duk da k'arancin shekarun da kike da shi a lokacin.! Duk da a cikin kuka take sai da maganganunsa suka yi mata dabaibayi, suka nemi d'arsa mata tausayinsa tare da haifar mata da sanyi jiki magashiyan. Bai jira jin ta bakinta ba, ya sake tsananta rukon hannunta ya ce "ki ji tausayina Maigado. Kin sani tun kina budurwa nake son ki, dan haka zancen ki ce ba dan ina sonki na aure ki ba ai tatsuniya ce kawai irin ta shifcin gizo. Don a lokacin haihuwar Bilkisu da kin ba ni dama da tuni na aure ki. Amma kika bijire mini, kika yi tamkar ba ki gane inda na dosa ba. Na tabbatar zuwa yanzu an kwashe shekaru kusan sha takwas, idan kuwa hakane ai bai kamata ki ce bana sonki ba, ko da wasa ba kuwa, domin Wallahi tunda ga lokacin har zuwa yanzu ban huta da bugawar zuciya a dalilin soyayyarki ba. Na tabbatar Ubangiji ne ya musanya mini da ke a daidai lokacin da ya yi mini jarrabawar mutuwar uwar ya'yana, tunda ya sani ya jefa mini soyayyarki mai yawa a zuciyata, idona da gangar jikina gabadaya." Na sassauta kukan da nake yi domin yadda yake magana kasan yana yi ne cikin tsantsar k'arfin zuciya. Domin tamkar ya rushe da kuka. Tsawon lokaci ina shesshekar kuka yayin da ya yi bakam yana saurarona. Can ya numfasa ya ce "Tashi mu tafi". Ko kwakkaran motsi ban yi ba a karo na biyu. Ya saki hannuna daya ya dago hab'arta ya zuba mata ido sosai, itama ta zuba masa nata idanuwan da suka yi luhu luhu, suka yi jawur tsabagen kuka. Ya yi kasa da murya ya ce "ki yi hakuri, daure mana, ki ji tausayina, idan har ke da kike jinina kin gaza akan lamarina da yarana wa kike tunanin zata rungumemu? Ba ni dama guda daya tak idan har ban sauya ba na amince da duk hukuncin da zaki dauka. Ina son ki, ina son rayuwa da ke, dan Allah ki daina tayar da hankalinki, me yasa kike son mayar mini da abin da yake cikinki sabon maraya, zuciyata zata iya bugawa idan ke ma na rasa ki tamkar yadda na rasa Rukayya. Hawaye ya sake balle mata domin tabbas ya bata tausayi ta yadda ya raunana kwarai da gaske. Ta kuma gasgata shi mutum ne mai k'arfin zuciya na gaske. Ya zaro tissue a aljihunsa ya hau goge mata hawaye yana ce wa "sorry Maigadona, very sorry! Murya babu amo ta ce"Zan kwanta sai da safe" Ya ce "Na dauka fa zamu tafine Sarauniyar shaiba! Ta girgiza kai ta ce "ka yi hakuri kaina ciwo yake yi, kasan kuma likita ya ce na dinga yin barci a wadace." Nan da nan ya hau gyara mata gadon da shimfidarsa take a hargitse. Ta bishi da ido tana kallon yadda yake gyara mata gado mutumin da zai iya ajiye zaratan yan sanda dubu su yi masa. Amma da kansa yake yi cikin rawar jiki da son ta ga gwanintarsa. Ya dawo kusa da ita ya ce "za ki shiga bayi ne?" Kai ta girgiza tunda fitowarta daga bayin ke nan ya shigo. Ta mik'e ta d'ingisa ta hau gadon domin ji ta yi ƙafar ta yi mata tsami. Ya tofe ta da addu'o'i tare da shafe mata jikinta. Tana jinsa yana ta faman laluben k'irjinta dan ya gane sune weak points ɗinta. Ilai kuwa nan da nan jikinta ya amsa ta nemi birkicewa. Sai kuma ta yi jarumtar saka hannu ta make masa tare da ce wa "Bana so, da iyayenmu a tare da mu kake yi mini haka?" Ya mike daga durk'ushen da ya yi, murya babu amo ya ce "Na tafi Maigadona ki yi hakuri ki huce so nake gobe na zo mu tafi gidanmu. Kin san ba ni da juriya akan ki Balqees ki taimaki yayanki kin ji". Ta gyara bargon sannan ta ce "Ni fa ba zan koma ina kallon yadda ka zuba ido yara na mini yadda suke so ba, ba zan koma kana daukan alamuran da suke hakkinane kana basu ba. Wannan shine gaskiyar magana ". [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ya fesar da iskar damuwa ya ce "Amma na ce "Zan gyara ko? Akan me ba za ki ba ni dama ba? Na gamsu na yi kurakurai, na kuma yarda zan canja menene kuma ya yi saura indai ba tada zaune tsaye kike so ba! Ya fada cikin fishin da yake ta danne shi kar ya k'wace masa. "Hmm" kawai ta furta dan kuwa ba yarda zata yi ta koma ba, sai an baje maganar nan a gaban manya. Ta riga da ta fahimci kawaicinta ba zai yi tasiri akan lamarin yaran nan ba. Ba wacce take mamakinta irin Hafcy. Yarinyar da shekarar da aka yi aurenta yar yayace, tare da tuna irin soyayya da take a tsakaninta da Hafcyn har su Aysha amma wai yau sun yi girman da suke ganin bata kai ta zame musu uwa ba. Sun washi su bude ido su ga babansu ya shiga al'amarinta ko dakinta. Tunda dangin uwarsu sun zugesu, tare dafad'a musu rabon aurenta ya kashe musu uwarsu. Ya juya ya tafi bai sake cewa komai ba. Ta idar da azahar ke nan ta koma gado k'arfe shida na asuba. Wayarta ta dinga gumza(vibration). Ta saka hannu ta duba ganin Baban Bilkisu ne ya sanya ta ajiye wayar ba tare da ta amsa ba. Amma tana katsewa k'iran ya sake shigowa. Ta dauka ta yi masa sallama murya babu amo. Cikin taushin harshe tamkar ba shine ya tafi da fishi ba jiya. Ya ce "Maigadona tafiya ce ta kama ni kwatsam zuwa Calabar dan Allah, dan Allah na roke ki, ki raka ni domin kowa da matarsa za shi. Ki mini wannan rufin asirin sarauniyar shaiba. Na gamsu na amince idan mun dawo nan zan dawo da ke ba gidana ba" . Ta yi shiru tana tunani tare da nazarin yadda zata ce wa su Baba zata yi masa rakiya alhali ta ce musu ta gaji da zama da shi. Ya tausasa harshe ya ce "Pls sarauniyar shaiba ki kubutar da ni kunyata a idon magauta. Taron karramaq manyan jaruman tsaro za'a yi ki taimake ni, alk'awari na yi zan dawo da ke inda na d'auke ki." Ta numfasa ta ce "To me zan ce wa su Baba?". Da sauri ya ce "Kawai ki fad'a musu na roke ki za ki raka ni Calabar za'a yi bikin karrama mu". To yaushe za'a dawo? Yini ne kawai, ya yi tsananin gaske ne a tsallaka gobe". Ta saki ajiyar zuciya ta ce "To". Dad'i ya ratsa shi yana ganin nasara a k'udurinsa. Ya ce "Ki shirya jirgin k'arfe goma na safiyar nan zamu shiga. Zan sanarwa da su Baba. Me da me zan dauko miki?" A sanyaye ta ce "To". Dan gaskiya ta yi missing d'insa da kalolin jagwalgwalonsa masu tsuma zuciyarta da gangar jikinta gabad'aya. Ta zarce da fadin "Sabbin abayas din nan da ka siya mini a wajen Umm Aslan mai Egyptian abayas har da rigar barcin nan da ka ce ta yi maka kyau". "Na gane su, rigunan barcin ma ai kamar a wajenta ne ko?" Ya tanbaye ta a hankali. "Eh duka a wajenta ne lokacin da muka je Eggypt, ka tuna har da su jewelleries da su jakunan mata na k'asaita". Ya amsa da fadin"Ai zan sake siya miki wasu don ina matuƙar son products din da take siyarwa dukkan kayanta da wahalar gaske ka ga irinsu a wani waje." +2349162662750 +201121544627 A hankali ta furta na gode. Tare da fad'in zan yi barci ko na 1 hour ne ". Ya ce "Amma ki tashi kafin takwas don ki shirya, zan zo kafin tara kin ga kafin mu isa iyafot ma tafiya ce mikakkiya." Murya babu amo ta ce"To" Alarm ta saita ya tashe ta k'arfe 7:45, ta ajiye wayar a gefe sannan ta gyara ta yi kwanciyarta. Bata fita ba sai da ta yi wanka ta shirya tsab , cikin jikinta ya bayyana alamun ta fara nauyi ke nan. Sosai ta yo kyau, filazal bata rabuwa da materials din Umm Nihla. Don sosai take jin dad'insu bare yanzu da ta yi nauyi ba abin da take sanyawa sama da su, shafal suke babu zafi babu takura. Gasu farashinsu daidai da aljihun kowa ne. Yanzu haka ma tattaunawa take yi da ita akan ta dinga turo mata daga Malaysia ta dinga siyarwa a Abuja tunda duk wacce ta ganta da shi sai ta tambaye ta a ina zata same su?" Gara kawai ta dinga sarowa tana siyarwa. Malaysianfabrics raina kama ne. 7020695644. Tana rike da jaka da ledar kayan da ta zuba, sai kuma ta fara tunanin yadda zata fadawa musu zata yi masa rakiya zuwa wani gari. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Kan dole ta fita ta tarar da su a falo. Ta zauna a kan kafet yayin da su suke kan kujera. Cikin nutsuwa ta gaishesu. Sai kuma ta kasa cewa komai. Cike da kulawa Momi ta ce "Ki je ki zuba abin karyawa a kicin ya ce zai zo ya kai ki, ki ga likita daga can zaku je Calabar amma yau zaku dawo". Ta yi shiru tana tunanin ni ya ce mata zasu kwana d'aya zuwa biyu. Su kuma ya ce musu tafiyar yini ce. To ko dai basu fahimta ba ne?. Ta furta hakan a fili. Na tarar da Alti na dama kunu mai aikin Momi na soya dankali turawa dan Jos wanda kaitsaye dukkan ahalin suke siya duk abin da ya shafi dankali d doya da kuma kalolin vegies daban daban ta hannun Haj Rumanatu shugabar Raudatul Jannah foods Jos. 08065530483. Kai dankalin Jos duniyane don shine asalin dankali mai dad'i. Da girmamawa ta ce Mamah ina kwana?" Ta amsa cikin mutuntawa don kuwa dattijuwa ce sosai fiye da Alti. Da azama ta dauko plate ta zuba mata wanda ta kwashe. Ta sake dauko bowl ta zuba mata ferfesun kaji. A dining din da yake kicin din ta zauna dan haka da ta bata sai ta ta cika katon kofin tangaran da kunun gyada. Tana fadin "na sanki da son kunun gyada". Bilki ta murmusa ta ce "Na gode kuwa". Cikin nutsuwa take karyawa. Sai da ta kammala ya iso. A gurguje ya gaisa da su Baba a dalilin lokacin tashinsu ya kusa. A sanyaye ta yi musu sallama ta wuce sukuku, tamkar marar gaskiya. Haka kawai take jin wani irin yanayi na takura a tare da ita. Ba dan tana kewar jagwalgwalonsa ba da ba inda zata bishi. Sallar azahar a hotel d'in da suka sauka suka yi. K'afafuwanta suka d'an kumbura kad'an saboda dogon zaman da ta yi. Da suka idar ya zauna ya dinga matsa mata k'afafuwanta sannu a hankali. Yana yi fad'in "Sannu Maigado." Yayin da take jin dad'i na ratsa ta tunda ga tafin k'afar har kwanyarta saboda dalilai biyu. Na farko ta yi kewarsa ba dan kad'an ba, na biyu kuma ta yi amannar shi baya cikin masu biye biyen mata. Sosai ya tsiyayarata da ruwan kanta ya mantar da ita wai fishi take yi masa. Kwanansu biyu suna holewarsu tamkar kwanakin farkon amarcinsu. Kwanansu biyu bata ga ya je ko ina da sunan taro ko meeting ba. Tunda suka dira d'akin hotel din bai fita ba, tunda babu masallaci a wajen sai sune idan sun ga lokacin sallah ya yi yake janta su yi tare. Wannan zaman da suka yi sun shaku da juna ainun, zuciyoyi sun huta, sannan kuma sun kashe wa juna k'ishin kewar junansu. Kwana na uku tana kwance a k'asan kafet ta yi filo da cinyoyinsa ta ce "Baban Bilki yaushe zamu koma ne tunda na lura ba wani aikin da ya kawo ka?". Ya yi murmushi mai sauti ya ce "Marmarin jihar Cross River ne ya fitine ni kinsan birinin mai dad'i da kyau, shekarar da aka yi aurenki aka dawo da ni jihar nan, a lokacin ina cikin tsananin gaske a dalilin rashinki sai gabad'aya garin ya yi mini kunci a dalilin zuciyar a kuntace take. Ban wani ji dad'in zaman ba, shekaru biyu na fara warwarewa sai kuma aka tura ni jihar Ebonyi. Shine yanzu na dauke ki don na rayu da ke na wasu kwanaki a garin da na yi ta kukan rashinki a boye babu kakkautawa ". Ta murmusa ta ce "Hmm ai cuta ta ka yi, da baka bayyana da k'arfinka ba, ka tsaya yin raragefe, ni sai na dauka tsoron matarka kake ji, nima kuma ga ni na yi a lokacin ta fini ilimi da shekaru, ga yara ta haifa maka ai wahalar gaske zan sha idan na shiga cikinku". Ya ce "Ke dai kada ki fake da wannan kawai Baban Su Amrah ya yiwa zuciyarki kamun kazar kuku idonki ya rufe, sannan da yawa mata ai ba kwa son mai mata! Da kin amince da kin gane ba abin da zai hana ni sonki, Idan an kere ki da wasu abubuwan ai ke kuma kina da k'uruciya, kinsan alfarmar k'uruciya kuwa?" Ya girgiza kai tabbacin al'amarin babba ne. A ranta kuma ta gasgata shi don itama ta ga tasirin kuruciyar yadda Sahal ya dinga rawar jiki akan Hawwah. Sai dai shi Yaya Asad ya yiwa matarsa adalci tunda mutuwa ce ta rabasu duk yadda ake ganin Sahal da kad'an ya girmeta to tazararta da Sahal tafi tazarar Asad da Rukayya don kuwa shekara d'aya tak ya bata shiyasa Abida take ce mata Anty Gyatum. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Da wayo da hila da gwada soyayya mai zama a zuciya sai da suka yi kwanakin sati. Ko maganar su tafi ma bata yi. Sai dai Akai akai ta kan ce Farha na can na kukan nemana. A duk sadda ta fadi hakan kuma baya tankawa, asalima sauya fuska yake yi. Idan su Amrah sun k'irata a waya yana karba su gaisa ya yi ta yi musu tambayoyi akan karatunsu da kuma menene matsalarsu. Amma maganar Farha baya um bare um um. Jiya ma da Alti ta k'ira ta had'a su da ta ce a bawa Dady bai amsa ba, ya ce dai yana gaishe ta. Har zuciyar Bilki bata kawo komai ba. Ranar da zasu koma Abuja daidai da satinsu guda. Ya kalle ta ya ce "yanzu sarauniyar shaiba duk yadda kika dinga makale mini ba zai saka mu wuce gidanmu kaitsaye ba, duk kirkin da na yi miki, kalli fa yadda kika zama tamkar yanzu za ki haihu? Kawai mu wuce gidanmu washegari sai muje mu gaida su Baba mu ce musu mun shirya! Ta girgiza kai ta ce "Daga rakiya sai na ce musu na koma gidana alhalin na ce musu na gaji ba zan koma ba, gaskiyar magana kunya ma zan ji, kawai ka bari sai na haihu din". Ya jijjiga kai yana gasgata bata da wayo. Ban da rashin wayo akwai kunyar da ta wuce ta koma musu gidan bayan ta biyo shi ta yi sati guda tare da shi, sannan ta koma da sunan cigaba da zama a gabansu. Amma bari ya zuba ido ya ga yadda zata kwashe tsakaninta da Baban nata da ya zuba mata ido take yin yadda ta ga dama, kafin ta dawo ya mata hukuncin da zata dinga sanin me zata dinga furtawa a gabansa. Ya rausayar da kai ya ce "Shikenan Maigado amma kada ki dinga kashe wayarki, sannan duk ranar da zaki je awo zan zo da kaina na kai ki, idan an kammala sai mu je mu na gaisa da unborn, tunda kin nesanta ni da jinsa duk sadda na so". Ta sinne kai tana murmushin kunya da jin dad'i. K'arfe goma na safe suka dira a airport din Nmadi Azikiwe da yake birinin tarayya. Motocin y'ansanda sun kai shida da suke takewa tsaleliyar motar da suke ciki baya. Shadaya daidai a kofar gidansu ta yi musu. Har cikin gate din motar da suke ciki aka shigar dasu, yayin da motocin yan rakiya ya ce su tsaya a wajen. Daga bakin falon ya ce "Ki gaishe su da kyau. Sai dare ko gobe zan zo na gaishe su, offiice zan wuce ana jirana da gaggawa". Ya mik'a mata jakar kayanta. Ta karba a sanyaye don so take ya rakata cikin, saboda tana sauka daga motar ta ji kuma wani abu mai kama da kunya na bibiyarta. Daga tafiyar yini ko kwana d'aya ne ta kwashe kwanaki bakwai? "Dankari". Ta furta a bayyane.

*Lame.Ng Skin Beauty and wellness* *Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.* *07036662633*

*Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253*

*Surayya Dee*[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Save Restricted Contents Bot, [Sep 25, 2025 at 20:10] Kuka ya k'wace mata don bayan kunyar da ta yi mata dabaibayi kalaman Baban sun yi mata tsauri matuƙa da gaske , haka nan idon da su momi suka zuba musu ya sake muzanta ta ainun. Baban kuwa bai kula da kukanta ba don sosai ya ji haushin sakarcinta ya kuma lura idan ba tausayinta ya cire a ransa ba to ba zai ga yadda yake so akan aurenta ba, tunda har Asad ya gwada masa irin wannan rashin kunyar cikin dabara, to nan gaba ba abin da ba zai yi ba, na nuna iyaka. Da b'acin rai ainun ya ce "Ashe sadda kika zo nan kika ce mini na zubawa Abida ido ban mayar da ita d'akin mijinta ba rashin kunya kika yi mini, ba wai fad'a mini damuwarku kika yi a matsayina na ubanku ba! Yana rufe baki ta bude baki ta rushe da kuka sosai don gabad'aya bak'in cikin Asad da kunyar duniya ne suka rufar mata. Baba ya yi waiwaiye bai ga wani abu da zai dauka marar illa da zai makata ba. Don haka ya zakudo ya dawo bakin kujerar sosai ya saka dukkan hannuwansa biyun ya rik'o dukkan kunnuwanta ya murd'e da k'arfi tar da fad'in "Rufe mini wannan ja'irin bakin na ki, dukanki na yi ko me?" Ta sassauta kukan ya ce "Borin kunya kike yi tunda kika yarda kika bi miji hotel akan idona, amma kika k'i binsa gidansa. Yanzu kenan duk sadda yake da bukatarki zai zo ya dauke ki, idan ya gama sai ya dawo mini da ke tunda haka kika zabar mana ni da ke ko?" Tashin hankali ya sanya jikinta b'ari ga kunnuwanta na hannunsa , kamar zai cire mata su, azaba ta sanya kukan ya tsaya cak, illa zufa da take yanko mata. Tunda take a duniya bata taɓa tozarta irin yau ba. Bai saki kunnen nata ba ya ce "Ba za ki zauna mini a gida ba, yanzun nan ki k'ira babban ja'irin ya dauke ki, don na tabbatar bai yi nisa ba, ba wani office da zai je. Sannan bana son na kuma ganin k'afarki a gidan nan har sai na bukaci ganinki da kaina. Idan kin so ki ce na yi son kai. Idan kin so ki zauna lafiya da mijinki da iyalinsa, idan kin so kuma ki gudun, ki je, ki yi zaman kanki tunda na fuskanaci taketakenki na raini a kaina. Zan zuba miki ido irin yadda nake zubawa duk wacce na bawa umarni ta kafe akan ni zan bi ra'ayinta saboda tana ganin ta yi ilimi mai zurfi". Nan da nan Abida ta muzanta tare da shiga wani irin tashin hankali farat d'aya. Don kuwa lah shakka wannan karatun nata ne.

*Contact me* 08032773332 *For all your kayan mata gangariya* *Bridal package* *Maijego package* *Uwargida package* *Bazawara package* *Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego* *Ciccibin garari* *Tsumin saiwowi* *Hakkkn daka emergency* *Gumbar ridi* *Gumbar saiwowi* *Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.

Cikin kuka na sosai Bilki ta ce "Dan Allah Baba ka yi hakuri". Murya ba amo ya ce " Zan huce da ke ne idan na ga mijinki gurfane a gabana yana yi mini godiyar ba shi aurenki da muka yi. Zan huce da ke idan kin kwantar da hankalinki tare da bada gudunmawar daidaituwar zumuntarmu. Kina tunanin idan su Ansari suka ji kina jele tsakanin gidanki da nawa gidan da sunan bacin rai zasu sassauto gabad'aya ne su sake mayar da ni ubansu?" Cikin kuka ta ce "Baba kai ubanmu ne babu abin da zai sauya hakan ". Ya ce "Kayya Maigado ke din dai da kuma Saddiqa haka ma Ansari yakan gaishe ni idan ya bushi iska amma Sulaiman Hamida Abida Anisa da Ansari kullum da bak'incikinsu nake kwana nake tashi. Indai na mutu a yanzu tabbas suna da alhakin mutuwata, ki yi a hankali kada ki shiga sahunsu a idona da zuciyata". Hawaye ya dinga tsere a fuskarsa a sanyaye ya saki kunnawanta ya koma cikin kujerar sosai ya jingina.

Jikin kowa ya mutu ba abin da ake ji sai gunshekin kukan Maigado da na Abida. Abida a ran take jin zahirin wanda Baba yake so duk cikinsu daga su har su Sulaiman gabad'aya Bilki ce. Ita ya tsaya mata kada aurenta ya taɓarbare, yayin da ita ya barta ta yi yanda take so, da komai ya k'wace mata kuma ya koma tsakaninsa da ita ido ne, komai ta ce zata yi to kawai yake cewa, haka momi wannan zurun da suke yi mata tare da bata cikakken dama da y'ancin ta zaɓarwa kanta yadda zata yi da rayuwarta ke saka ta kuka kullu yaumin, tunda ta yi gardamar ba zata zauna da Sulaiman ba, aka kyaleta har yau babu wani da Save Restricted Contents Bot, [Sep 25, 2025 at 20:14] ya taba yi mata batunsa ko nuna tausayawa ga HALIN YAU din da take ciki. Yaya Asad ne kawai shima sai da ya fara zawarcin Bilki yana son ta shawo masa kanta, ya sanya yi mata alak'awarin za'a fara binciken inda yake, ga shi har matarsa zata haihu bata ji komai game da batun ba. Ita kam tana ganin tasku da ainihin kuttun namiji. Kuka ta yi shi irin wanda bata taɓa zaton wata mace ta yi irinsa ba. Ba abin da ta nema ta rasa, amma bata samun walwalar iyayenta irin na da duk da basu taba ce mata komai ba. Amma yanzu ta fahimci tana cikin garari tunda duk yadda take a wajen Baba ya saka ta cikin wadanda suke tayar masa da hankali, suke k'ulla masa bak'in ciki. Don haka zata fara neman Sulaiman duk inda yake a duniya, idan ta gan shi kuwa sai ta shekara bata zo gidan ba sai dai waya, ko zai dinga dukanta kullum kuwa, zata yi hak'uri ta zauna a d'akinta duk runtsi. Har sai BABA ya je nemanta da kansa in sha Allah Baba ba zai mutu da bakin cikinta ba. Tsawon lokaci suna kuka ba wanda ya ce musu kanzil. Bilki na ayyana wannan rayuwa da wahalar gaske take. Babu wani cikakken jin dad'i. Gabad'aya k'alubalen da yake cikin rayuwar yafi jin dad'insa yawa. Ba macen da zata ganta ta zaci tana da matsala a gidan aurenta. Ga tsalelen gida, ga tsaleliyar mota, ga ingarman miji mai rike da madafan iko, ga lafiya Allah ya bata ga kuma satisfaction, ga niimar haihuwa. Amma kuma sai aka jingina mata k'alubalen fuskantar kiyayyar y'ay'an mijin da ubansu yake tsananin sonsu. A da ta d'auka idan ta rabu da Sahal ta samu wanda zata dinga samun satisfaction to duk wata matsalar da zata zo ba zata d'auke ta a a matsayin damuwa ba. Ashe ba hakan ba ne, mutum na girma matsalolinsa na sake bunkasa, matsalar y'ay'an mijin da babu uwarsu babbar jarabawace da ba mai gane girmanta sai wadanda suke cikin matsalar, gara yaran masu uwa, idan har sunada tarbiya Kuma suna mutunta uwarsu AI dole su mutuntunta Matar ubansu, Idan kuwa basu da tarbiya basa mutuntata uwarsu ai shafawa Kanka ruwa zaka yi ka Koma gefe ka yi kallon yadda sakayyar rayuwa zata hau kan kowa. Da ace Rukayya na da rai suke mata irin haka, to da ita kuma a kanta zata rama iyashegensu tunda itace abokiyar burminta, idan y'an arziki ne sai su kiyaye ta. Amma yanzu ba yadda zata yi sai fatan Allah ya kawo musu miji su je suma su fara fuskantar yadda rayuwar take, tunda haka rayuwar take kowa hak'uri yake yi da yadda k'addara ta zaba masa. Allah dai yasa mu wanye lafiya kawai. Cikin muryar umarni ya ce "Ki tashi ki koma d'akinki, Alti na gidan Faruku sai jibi zata dawo matarsa ce ta je biki shine ta je ta taya yar aikinta kula da yara. Jibin ko gata direba zai kawo ta tare da d'iyarki".

Ta kasa tashi tsabar kunya da nauyin da jikinta ya yi mata na tausayin Baba. Gabad'aya k'arfin hali yake gwadawa akan su Yaya Hamida da suka share shi. Cikin kuka ta ce "Dan Allah Baba Yaya Faruku ya raka ni". Murya babu amo ya ce "Ba zai raka ki ba, shi ja'irin mijin naki ya zo ya dauke ki, ko ki shiga ki dauko mukullin motarki ki tafi ai kinsan hanya". Sai lokacin Momi ta ce "Alhaji da dai ka yi hak'uri ya kaita din, ba zata iya tuki cikin nutsuwa ba, kuma ta inda aka hau, ai ta nan ake sauka. Shi ya kawo ta ranar da ta yi yajin, yanzu don ya mayar da ita ai babu komai, daure dai Alhaji kada ta tafi ita kad'ai." Baban ya ce "Yadda ta fito haka zata koma, ina ce a gabanmu ta wuce ta bi miji uwa duniya, don zata koma gidansa ita kad'ai sai ya zama abin jin nauyi? Kin san Allah Asad na k'ofar gida yana jiranmu ni da ita. Ai wannan abin da ya yi sakone mai harshen damo ya yi mini, kin ga ai ya fahimtar da ni da yaren da na ji shi har cikin k'wanyata. Momi ta kasa magana don gabad'aya kunya Baba yake bata a gabansu. Yayin da shi kuma ko a jikinsa yake ta nanata rashin kunyar Bilki da rashin mutuncin Asad.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull