Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 17
Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 17: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 17. Ta yi masa godiya ta tashi ta koma d'akinta.Tana jin…
3,963 words
Ta yi masa godiya ta tashi ta koma d'akinta.Tana jin nutsuwar zuciya, tana da tabbacin tunda ABBA ya ce Dady ya huce to babu haufin ya huce din. Faruku ya mike yana fad'in"Bari na wuce "Allah yasa ba zan sake zuwa gidan nan da sunan bacin rai ba Oga Asad". Murmushi Asad din ya yi tare da ce wa "Idan ta ji faɗanku ta kwantar da hankalinta ta ajiye tsiyatakun da ta aro ba zaka sake zuwa ba mana Baba Faruku". Suka fita waje tare. Har jikin motarsa ya raka shi suka yi musabaha. Yana tsaye yana jallon Faruku har ya fita daga gate din aka rufe sannan ya yi ciki. A ransa yana ayyana Duk cikin family lmsu ba wanda ya more irin Faruk. Shine bai taba aikin gwamnati ba a rayuwarsa, amma kuma attajirine na sosai. Sannan yafi kowa yiwa iyayensu hidima da jikinsa don shine yake da lokacin kansa, kullum yana tare da Baba yana yi masa hidima. Haka duk jinyar da zai yi Faruku na gefensa yana kula da shi. Shi kad'ai ne ya yi wannan sa'ar, su kam sai dai su yi da aljihunsu. Hak'uri da sadaukarwarsa ya sanya hatta Momi da Baba kunyarsa suke ji bare kuma su. Yadda suke yi masa kacakaca ko su share shi basa taba yiwa Faruku haka. Ya nisa ya ce "Allah ka sake son Faruku." Ya shiga cikin gidan har ya zauna a falon sai ya tuna ya tashi da hanzari zuwa saman. A d'akinta ya tarar da ita tana zaune a k'asan kafet ta mikar da ƙafafuwanta da suke a kumbure. Murya ba amo ta amsa sallamarsa. Ya zauna a k'asan yana fuskantar ta. "Maigado ya aka yi kuma kika dawo alhalin kin ce Sai kin haihu, Babanki ma ya jaddada mini hakan?" Takaici ya shak'e ta. Ta yi masa shiru amma idanuwanta sun cika da k'wallar takaicinsa. Ya yi murmushi kad'an ya ce "To ya aka yi ne? Fasawa kuka yi ne ko ya ya ne?" Murya na rawa ta ce "Na gode da muzancin da ka janyo mini Baban Bilkisu ". Ya cije ya ce "Wacce magana kike yi ne haka. Me na yi miki?" Hawaye ya k'wace ta ce "Akan me zaka ce mini yini kawai za'a yi ko kwana d'aya alhalin ba hakan bane a ranka." Ya tattaro dukkan alhini ya yaba a fuskarsa tare da ce wa "Hakan ne a raina mana. To yadda kika dinga mak'ale mini ne ya sanya na fahimci kina buk'atar mu k'ara kwanakin, da na ce zamu k'ara kuma ba ki yi inkari akan haka ba. To menene laifina dan Allah, dole na yi mike ko kuwa kin tayar mini da hankali akan sai mun dawo?" Ta kasa ce masa uffan tunda bata da bakin magana. Ta girgiza kai ta ce ka koya mini darasi zan kiyaye a gaba". Ya dauke kai ya ce " Allah ya nuna mana gaban lafiya." Ya gyara zama ya ce "Ki saurare ni da kyau ki fahimci jawabin da zan yi miki da kunnen basira." Ta goge fuskarta da tissue sannan ta nutsu sosia alamun shi take saurare. Ya ce "Na mayar da Laura gida kamar yadda kike so, na sallami Jummai haka Charity goba zata koma inda na samar mata wani aikin, abin da yasa ma bata tafi ba kenan tuntuni, ba zai yiwu na rabata da wajen aikinta na farko ba, sannan yanzu na sallame ta ba tare da na samo mata wani aikin ba." Bilki dai ido ta cigaba da zuba masa. Ya zarce da fad'in "Yanzu za'a samo sabbin masu aiki, kin ga wanda za suzo basu saba da yara ba, bare su dinga girmama umarninsu sama da na ki."
Ta dan ji dis amma ta maze ta ce "Tom amma da ba'a kawo wasun ba, tunda dai akwai ma'aikata da yawa. Ga masu shara da wankewanke da goge goge, ina ganin hidimar girki a bar mini tare da taimakon Alti zamu yi komai" . Ya ce "Kina iya shiga kicin duk sadda kike so, amma gaskiya ina son na ga ina da chef a gidana." Zuciyarta d'aya ta ce "Ka manta nima girke girken na karanta? Sannan Alti ta iya girke-girke kala kala na ban mamaki". Ya daure fuska ya ce "Alti ai ba zata dawo mini ba, tunda ta biki kuka tafi bata hana ki yi mini yaji ba, to na dakatar da ita. Wani irin al'amari ya daki zuciyarta. Nan da nan idonta ya ciko da hawaye ta ce "Baban Bilkisu ya haka kuma? Alti fa bata da kowa a duniyar nan sai ni, tun haihuwar Faruku muke tare da ita, yanzu idan an sallame ta ina zata je dan Allah?" Save Restricted Contents Bot, [Sep 26, 2025 at 11:51] Ta je koma ina ne". Ya fad'a a dake. Bilki ta zuba masa ido tana ayyana abubuwa masu yawa, ba k'aramin artabu zata sha da wannan mutumin ba lallai. Ta tausasa harshe ta ce "Amma tun kafin mu yi aure sai da na ce Baba ya fad'a maka da ita zam zo gudun irin haka fa". Kaitsaye ya ce "Na amince a farko ne ba tare da na yi tunanin komai a kanki ba. A yanzu da na gane inda kika dosa a kaina ba zai yiwu kuma na bi yadda kike so ba. Wallahi ba dan Baba ba, da kinsan kin zage ni a gabana. Amma tunda dole wani ya ci albarkacin wani na hak'ura na k'yale ki, amma Alti da Farha su zauna a gidan Baba wajen Momi." Wannan karon bayan bugawa zuciya har y'ay'an cikinta sai da suka motsa da k'arfin gaske. Ta fashe da kuka mai tsananin gaske. Takaici har makoshi. Cikin fitar hayyaci ta ce "Na rantse da Allah ba zan yarda ba, kawai ka sallame ni, dama ba sona kake yi ba tun filazal, ka samu abin da kake so shiyasa kake fito mini da halayya iri iri. Ko tafiyar nan da ka yaudare ni muka dade da kana sona ai ba zaka mini sanadin da zan muzanta irin haka ba, ka cigaba da cin zalina yadda ka saba tuntuni ".
Ya yi murmushin da babu nishadi ya ce "Ai da muka je din ba dole na yi miki ba, yanzu ma kuma ai ban daure ki ba, sai dai ki sani idan kika yi kuskuren sake saka k'afarki kika bar gidan nan, sai kin yi kuka na gaskiya don kuwa za ki dawo ne ki tarar da wata a cikinsa". Kuka ya tsaya mata cak, ta zuba masa ido a maimakon ta ji tsanarsa yadda take ji a da, sai bata ji ba, ta kasa gane me take ji a ranta game da shi tunda babu so, kuna babu kiyayyar. Ta tuna yadda suka rabu da Baba Babba da yadda ya tabbatar mata tashin hankalinsa ace bata zaune lafiya da mijinta, farincikinsa da burinsa bai wuce ace ta bada gudunmawar da zai daidaita zumuntarsu ba, bugu da ƙari Baba ya ce" Ba zai huce da ita ba sai ya ga Asad tsugunne a gabansa yana yi masa godiyar auren Bilkisu da aka ba shi. Wanne irin nauyi Baba ya dora mata, wacce irin biyyaya yake son ta yi, wanne irin dabaibayi Baba ya yi mata? Zata yi komai, zata jure komai amma ban da rabata da Farha. Haka nan ba zata rabu da Alti ba har sai Faruku ya girma ta damka masa amanarta, shi take rikewa ita, yadda ta ci wahalarsa da rainonsa da ikon Ubangiji zai rik'e ta akan tsufanta a lokcin da zata fi koka rashin y'aya' da dangi. Hawaye face face a idonta ta ce "Ayyah Baban Bilkisu amma alk'awari bai ce hakan ba. Magana biyu ba taka ba ce. Ni fa zan iya rabuwa da komai da kowa amma rabuwa da Farha mutuwa ce kad'ai zata gitta a tsakaninmu". Ya sake harzuk'a ya ce "Asad ya rabaku alhalin ba mutuwa kika yi ba. Ai tunda kika gwada mini wulakanci kala kala akanta to ba zan zauna da ita ba. D'iyar Sulaiman ta fi ta kowa saboda rashin kara da wulakancinki ya kai k'urewa." Ta yi sakare tana jin wani irin abu na mamayarta ashe shi a haka ya fassarata? Murya ba amo ta ce "A haka ka dauka kenan? Ni fa Wallahi mantawa nake yi ba ni na haife ta ba. Gaskiya ni ba haka a raina, ban yi zaton zaka mini irin wannan fassarar ba, haka zalika ba zan iya rayuwa babu ita ba, na tsallake na bar y'anuwanta a Katsina amma ita kam tabbas ba zan iya ba. " Ya sake girgiza kai ya ce "To zan ga yadda za'a yi na zauna da waɗanda bana son zama da su a gidana kuwa".
*Na gode sosia da soyayyarku ga rubutuna*. *Na gode da uzzirinku*
*Surayya Gwaram* ✍️ Save Restricted Content Bot, [Oct 8, 2025 at 13:20] *Assalamu alaikum barkanmu da lokaci!* *Na gode da hak'urinku Allah ya saka da alheri ya bar zumunci*. *Na gode da waɗanda suka mini addu'ar samun lafiya. Allah ya bamu lafiya gabad'aya* *Zamu d'ora daga yau in sha Allah* *Allah ya taimakemu gabadaya*. *Godiya ta mussaman ha dukkan waɗanda suka siya labarin nan, Surayya ta gode Allah ya saka albarka da dukiyarki da ya'yanku*. *Fatan alheri ga dukkan yan comments section na labarin Dingishin kwado Allah ya saka muku da alheri Allah yasa mu dade muna yi har a aljanna*.
*Wannan littafin na kudine biya 1k 238487685* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank* *08032773332*.
Bak'in ciki ya yi mata k'awanya ta rasa yadda zata yi sai kawai ta dage ta dinga zabga ihu da iyakacin k'arfinta. A farkon ya dauka wasa ne amma da ya ga tana neman shidewa ya sanya ya bude baki ya ce "Wanne irin abu kike ne haka? Sai ka ce jahila?" Bata saurare shi ba, ta cigaba da kukanta bilhakki. Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi ya matsa kusa da ita da niyyar rik'e ta, ta goce ta ce "Kada ka taba ni, da ikon Allah na barka Yaya Asad dama dan a kirga mini aure ne ya sanya ka matsa ka kafe sai da ka aure ni". Cikinta ya cure ya dunkule ta rasa yadda zata yi kawai ta kwanta rigingine tana murdaddawa tare da kuka mai gunji. Ya kalli yadda cikin ya yi k'asa tamkar zai fito duniya a lokacin. Murya ba amo ya ce "Ba za ki kwantar da hankalinki ba? Sai kin janyo mana sanadin wahala? Cikin kuka ta ce "Da ikon Allah mutuwa zan yi na bar maka duniyar nan, in sha Allah sai na mutu na barka da sabbin jariran da zaka rasa mai basu nono, da ka raba ni da Farha gara na mutu na huta, in sha Allah sai ka sake samun sabbin marayu a gidanka" Ta sake kecewa da matsanancin kuka. Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi mussaman yadda ya ga ta jik'e da zufa duk sanyin AC da na iskar da standing fan take bayarwa a d'akin. A firgice ya dagota, ta fisge ta sake komawa tana cigaba da ihu da murkukusu. A sanyaye ya ce "Ta shi mu yi magana na janye batuna to". Ta sassauta kukan amma ta k'i tashin. "Tashi mana! Ya fad'a da sigar umarni. Still ta k'i ko da motsi. Ransa ya b'aci ya ce "Kin ga taurin kan nan na ki ne bana so, ba yadda za'a yi na ce da Rukayya ga yadda zata yi mini, ta kalle ni ta watsar da batuna. Amma ke ban isa da ke ba kwata kwata." Hawaye na zuba a idanuwanta ta ce "Allah sarki ai sai ka bita makabartar ka cigaba da bata umarnin da ba zata sab'a maka ba." Ya yi shiru yama rasa mai zai ce mata. Kan dole ya ce "Ki cigaba da yin fito na fito da ni". Babu fargaba ta ce "ka cigaba da kwatanta ni da mai murabus". Duk yadda ransa ya b'aci Sai da dariya mai sauti ta subuce masa. Sai ya gintse fuska sai dariyae ta sake k'wacewa. Da ƙyar ya yi jarumtar danne dariyar ya ce "Yanzu Bilkisu duk yadda baiwar Allan nan take haba haba da ke ba zai saka ki dinga raga mata ba? Ya za ki ce mata maimurabus don ta mutu, ai bata mutu a zuciyata ba, saboda Allah fa?" Ta d'auke kai tare da zumbura baki, a yadda take jin takaicinsa cikin jikinta ne cikas din da ya hana ta nada masa duka da sunan jinnu ne suka tashi. Don idan ta shammace shi ta dinga kai masa bugu da cizo kafin ya ankara ya ji jiki. Sai dai ba zata iya ba, tunda ita kanta fama take yi da kanta. Amma matuk'ar suna tare ya cigaba da yi mata batun mai murabus tare da nuna mata tafi ta yi masa biyayya zata dauki mataki. Murya ba amo ta ce "Ya za'a yi ta mutu a zuciyarka tunda nima victim ce na shaida ba'a daina son first luv duk tsawon lokacin da za'a dauka ba'a tare kuwa". Zuciyarsa ta harba. Gatse ta yi masa ko kuwa. To waye first luv din da take so Faruku ko wanccan sahalallen? Ya ce "Da na janye batun rashin dawowar y'arki da Alti. Amma yanzu na jaddada dokar tunda babu nadama a lafuzanki". Kuka ya sake k'wace mata duk da hakan sai da ta ce "Ba zan yi nadama ba, baka biyo ta hanyar da zan risina maka ba. Kuma in sha Allah sai ka fini nadamar wannan hukuncin da ka d'auka. Na yiwa Baba alk'awarin ba zan sake fita da sunan yaji ba, Sai Idan kai ka sake ni. Save Restricted Content Bot, [Oct 8, 2025 at 13:22] Amma Wallahi yadda ka kuntata mini ka shirya fuskantar naka kuntatar zuciyar, babu kai babu farinciki a gidan da kake ƙirarin naka ne. Kuma Wallahi ba dan ina tsoron kada ka kawo wata bane zai hana na fice na bar maka gidan ba. Kunyar Baba ta sanya zan cigaba da zama a cikinsa har zuwa lokacin da zaka gama bayyana dukkan manufarka a kaina". Ta yunk'ura ta mike. , kai tsaye bayi ta shiga don gabad'aya zufa ke yanko mata ta tashin hankali. So take ta ba shi hak'uri amma tunda ya kawo maganar Rukayya a muhallin da bai shafe ta ba to ba zata ba shi hak'urin ba. Zata yi hak'uri har zuwa ta haihu lafiya ya ga kalar tata tsiyar.. Shower ta sakarwa kanta. Mintina biyar sannan ta tsane jikinta ta fito. Yana zaune inda ta bar shi. Yayin da isa gaban wadirof ta bude ta jima tana nazarin kayan da zata sanya wanda bai da nauyi. Can ta hango riga da wando irin na Pakistan din nan masu taushi da tsada. Ta dauko ta saka bayan ta fesa spray din oriflame na lame skin care. For your order contact Aisha 07036662633. Ta sake fesa turarenta na weekend. Kaitsaye ta fice zuwa kicin dinta na da yake falon nata na samanta. Kulikulin Ummiel foods ta dauko ta juye shi a plate din ralzapalace08109544470. Tana mamakin sabuwar ledar da aka canja masa ga kuma tambarin Nafdac a jiki. Yadda yake da d'adi ya kuma karbu a cikin kasar nan da wajenta dole Nafdac tasan da shi mussaman da ake samunsa a store daban daban a cikin Kano da Abuja. Kulikulin Ummiel foods yafi kilishi dad'i ku siyawa kanku da iyayenku da aka hana su cin nama tabbas zai kashe musu kwadayi. 08036355535 For your order. Ta bude firij ta dauko fresh milk ta zuba a glass cup sannan ta fito ta dawo falo ta zauna tana ci tana duba wayarta. Amma gabad'aya bata gane komai. Duk d'adin kulikulin nan a yau taunawa take yi kawai. Haka fresh milk din ma bata jin dad'insa a baki. Sakin da Sahal ya yi Mata ya yi mugun bugunta a dalilin ya zo Mata a bazata sannan yadd6ua ce don iyayenki masu son zuciya ya yi mata tsauri k'warai da gaske. Amma a yau hukuncin rabata da Farha ya buge ta fiye da sakin. Hawaye ya dinga silalo mata. Ta kasa jurewa ta lalubo lambar Baba.
Bugu d'aya ya dauka bai yi mamaki ba don kuwa yasan za'a sha artabu da ita. "Ya ya ne Bilkisu?" Ya tambaye ta cikin kulawa. "Baba ka fad'a masa sakon da na faɗa maka na cewa da Farha da Alti zan je gidansa?" Ta fad'a cikin shesshekar kuka. A sanyaye ya ce "Na fad'a masa, ya ce kuma ya amince. Amma ranar da na yi masa ba dadi akan lamarinki da yadda ya zuba ido tarbiyar y'ay'ansa ta lalace ya bani hakuri tare da alk'awarin zai gyara, zai kuma yi garanbawul a gidan. Ya roke ni arzikin na rik'e miki Farha har zuwa lokacin da zai kammala gyare gyaren da zai yi a gidan ". Ta yi shiru. Ta nisa ta ce "Ka amsa masa ka amince da wannan batun nasa Baba? D'iyar da aka bani ita tun bata zo duniya da shekeru sama da goma ne zai yanke ta a jikina? Sahal da ba ni da alakar jini da shi ya zauna da ita cikin adalci sai shine zai ce ba zai rik'e ni da ita ba, alhalin sai da na ce a faɗa masa da ita zan zo masa, ya amince da hakan. Baba ni kam gaskiya wannan hukuncin ya yi mini tsananin gaske tsakanina da Allah ba dan kai ba, da na yi rikicin da kowa zai san an taɓa ni.". Baba ya nisa ya ce "Na gode da kika hango ni, yanzu ki saurare ni da kyau. Ai ya ce mini ya baki Bilkisu, Amal da Noor to yanzu ki jasu a jikinki irin yadda kike yi da Farha suma y'ay'an ki ne kin ji Maigado.". Ta kasa cewa komai don kuwa bata taba ganin mutum irin Asad mai son kansa ba. Shi dai a yi masa yadda yake so ba ruwansa da damuwar wani, tun tana k'arama ya dasa mata k'insa saboda azabarsa shine har yanzu ba zai shafa mata lafiya da takurarsa ba? Cikin kuka ta ce "Baba yanzu shikenan an raba ni da ita? Ni kad'ai nasan yadda nake ji a zuciyata da tunanin y'anuwanta na Katsina. Ban gama warkewa da rashinsu ba sai a sake raba ni da ita kuma duk a zuba ido ana kallo?" Save Restricted Content Bot, [Oct 8, 2025 at 13:25] Ta fad'a cikin kuka na tashin hankali. A sukwane ya ce "Zata dawo fa, ya ce yana gyare gyare ne. Ki yi hak'uri mu ba shi nan da ki haihu, idan bai yi magana ba, zan shiga maganar a lokacin. Kin ga mu maza bama son a zo a yi mana hukunci a gidanmu. Ki yi hak'uri, ki zuba ido ki ga iyakacin gudun ruwansa. Tunda ya ce ba dama ya baki umarni ki ce to kaitsaye sai ya yi fama da ke". Ta kasa cewa komai wato dai Asad mugune lamba d'aya. Sai da ya gama fadan laifukanta sannan ya yaudareta ta bishi a gabansu. K'arshen tozarci da muzanci ya yi mata. Ba kuma komai bane ya sanya ya yi Hakan ba saboda Yana ganin ita nympho ce. To kuwa zata ba shi mamaki. Matuk'ar ita mace ce yadda ya gurfana gurfana gaban Baba ya ce a bawa Momi rik'on Farha, da kansa zai sake gurfana akan ya je d'auko ta. Shine da kansa zai dauko ta ya kawo mata ita ba waninsa ba. Ta had'iye kukan ta ce "To Baba." Ya dinga sanya mata albarka da fatan Allah ya sauke ta lafiya. Ta ajiye wayar tana mai tsurawa cikinta da ya yi tsiri ido. Lah shakka wannan ciki ya yi mata shigar sauri, k'addararsa ne ya sanya ta auren Asad. Gabad'aya ta ji duniyar ta yi mata zafi tunaninta ya kulle. Ba wacce take so ta faɗawa wannan matsalar Sai Abida. Amma kuma Duk yadda Abida bata jingina Farha gare ta hakan ba zai kore itace ta haife ta ba. Bayan haka ta sani bayan baba da Momi Abida bata so wani kamar Asad a gidansu ba. Ta tuna a ranar da suka kammala Fgc Bakori. A ranar da ta yi alkawarin bata abin da zata fara haifa ta ce ina sonki Bilki fiye da Yaya Faruku da yaya Munnira. Ita kuma ta ce so nake ki soni fiye da Yaya Asad. Amsar da ta bata shine ba zan miki karya ba Maigado don kuwa ban so wani a cikinmu kamar Yaya Asad ba. Ta zukar da fuskar b'acin rai tana hakaito yadda shima baya iya karar daidaita su a lokacin da suke yara, sai da suka zama y'anmata ne da ya fara sonta shine yake nuna equal suke har ma ya fara dank'a mata abu idan zai basu tare a maimakon ya bawa Abida yadda ya saba. Yaya Faruku ne da Munira basu taba nuna mata Abida ta fisu asalima Munira bata shiri da Abida ne a dalilin yadda take takura mata. Haka ma Yaya Faruku. Amma Asad kam dama tun can mai son kai ne na gaske yanzune take sake fahimtar haka tunda da ya daina banbantasu ma ai jarrabarsa aka yi da sonta ba dan haka ba, ba zai daina ba.
Yanzu kuma lah shakka ta sani laifin Sulaiman ya jingine Abida har tana kukan nemansa ne ya sanya shi hucewa akan y'ar da bata san shi ba. Ya manta ba Sulaiman ne ya bata Farha ba Abida ce. Kuma ko da ba Sulaiman ne ubanta ba, zata so ta, zata yi mata riko na amana sannan a bakinta dai wani ba zai ji ta furta ba ita ta haife ta ba. Sai kuma aka yi sa'a irin na gam da katar Sulaiman ne ubanta. Yadda yake jin yana son Abida haka take sonsa, haka nan yadda yake jin yana son ya'yansa fiye da haka take sonta don idan ta ce tafi jin yarinya a ranta fiye da su Amra ba k'arya ta fad'a ba. Duk tijararsa matuƙar zata amsa sunan matarsa to sai ya zauna da Farha, ko baya so kuwa. Ta janye tunanin faɗawa Abida wannan badakalar don kuwa tasan ko ya ya sai ta ji babu dad'i. A dalilinta kuwa ba zata so su sami sabani ba. Kaitsaye ta kira Faruku. Ta daure ta had'iye kukanta. Ta yi masa bayanin halin da ake ciki. Yana bude baki ya ce "Ki yi hakuri Momi zata rik'e miki ita, kuma ma ba kwaanan za ki haifi wata ko wani ba?" Ta ce "A a Yaya Faruku kafin na haifi wannan din da kake maganar zan haifa, ai ina da wasu. Amma kuma dukkansu ba zasu maye mini gurbin Farha ba". "Bilkisu ki yi hakuri mu zuba masa ido kin ji". Ta kasa cewa komai. Ya dinga rarrashinta akan ta kwantar da hankalinta, tare da bata labarin yadda yau Aysha ta dinga kukan a ba shi hak'uri. Ki bi shi a hankali ya gamsu ya isa da ke, da kaina zan kawo miki ita. Don hankalinki ya kwanta ya sanya na d'aukar miki Alti. Idan komai ya daidaita zasu dawo kin ji Maigado ". Save Restricted Content Bot, [Oct 8, 2025 at 13:27] A sanyaye ta ce "To Yaya Faruku na gode. Amma fa gaskiyar magana raina ya b'aci da wannan abin da ya yi mini, kuma Wallahi darajar baba da k'imar ka ya sanya zan yi shiru na zuba idon na ga ni din. Amma ba dan haka ba da mun yi tawarwatse a yau din nan". Ya ce "Na gode miki Maigado ai tunda kika yi sa'a kina jin maganar manyanki ko bata yi miki dad'i ba komai zai daidaita miki sannu a hankali." Daga haka suka yi sallama. Daidai lokacin ya fito daga dakin nata. Ya kalle ta ya ce "Kin gama buge bugen waya kina kai k'arar a tursasani na zauna da waɗanda bana son zama da su ne?" Uffan bata ce masa ba. Ya gama tsayuwar jiran ta tanka. Amma tsawon lokaci bai ji ta ce uffan ba.