Kenza eBookz

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 18

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 18

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 18: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 18. *Contact* *Deenah cakes and more -Kano* *09038055790* *IG…

4,232 words

*Contact* *Deenah cakes and more -Kano* *09038055790* *IG @Deenah cakes and more * *For all your* Snacks such as : *Birthday cakes* *Cupcakes* *Samosa* *Springrolls* *Meatpie* *Frozen snacks* *Event snacks* *Pls Patronize my daughter*. Ya ce "Ai tunda rashin kunya ne makamanki sannu sannu zan bi na karairayesu." Still bata ce komai ba illah ido da ta zuba masa babu kiftawa. Ya tsargu da kallon da take binsa da shi. Don ya ga ta zama wata iri. Don haka ya had'iye maganarsa ya hau samansa. Ba jimawa ya fito sanye da kakinsa hakan ya tabbatar mata office zai wuce. Kwanaki suna ta shud'ewa Bilkisu ta dank'ware ranta. Tsawon sati kenan da ta shata layi da mijinta. Tsakaninta da shi gaisuwar safe bayan haka bata sake bude baki ta yi masa magana. Ta koma yanayin shirun da tun filazal yake fad'in ya yi masa yawa. Ta k'i bari ya kebe da ita, Idan ya matsa sai ta fara kukan ciwon ciki, kuka kuwa mai tsananin gaske. Haka ya hak'ura ya zuba mata ido. Bilkisu Amal da Noor suna tare da ita ko da yaushe, sai dai ita din bata da walwala. Haka Aysha da Hafcy sun ajiye shakiyancinsu da kaso tamanin cikin dari. Kawai hawa samanta su zauna ne basa yi. Amma suna gaishe ta cikin mutunci.. Yanayin da ta koma ya damu oga Asad k'warai da gaske. Haka suke tafiya har aka shafe kwanakin wata. Ranar da ta cika kwanaki talatim da dawowarta gidan tura ta kai bango ya kusance ta a dole wanda babu armashi a had'uwar ko kad'an k'arshe sai da kuka aka kammala. Daga bisani kuma ciwon cikin da take karya da shi kullu yaumin ya taso mata haikan. A gigice ya shirya ta sannan Shima ya kinsta ya sunkuceta zuwa mota ya saka ta sannan ya shiga ya ja motar da kansa ya fice. Y'ansanda da suke tsaronsa suka bisi a mota d'aya. Kaitsaye asibiti kai zaman kansa() da take awo ya nufa da ita. Nan da nan kwararrun likitoci suka rufa a kanta. Shud'ewar awa guda, sannan likitar da ta jagoranci dub Baki ta fito zuwa ofishinta. Asad ya bita. Da girmamawa take yi masa bayanin halin da Bilki ke ciki. "Oga jininta ya hau fiye da kima sannan yaran a zaune suke Wanda ba'a son Hakan". Da yake a rude yake sai bai fahimci kalmar jimillar yaran da aka yi ba. Murya ba amo ya ce "Yanzu ya za'a yi ne, bana son ta samu matsala Dr. Last year na rasa first wife d'ina bana son na sake rasa wannan! Dr ta numfasa ta ce "Dole zamu rik'e ta on bed rest don gaskiya tana buk'atar hutu da nutsuwar zuciya. Bayan haka kuma zamu dinga duba yanayin zaman cikinta har zuwa komai ya daidaita don idan ba a bata kulawa ta mussaman zata iya haihuwa a yanzu wanda da sauran lokaci a k'aida. Ka yi hak'uri zamu rik'e ta har zuwa ta fita daga had'arin da suke ciki ita da abin da yake cikinta. Hankalinsa ya dungunzuma ya tashi tare da k'alubalantar kansa me yasa ya yi mata batun da shine sanadin da janye dukkan walwalarta? Me yasa yau ya matsa mata alhalin da gaske bata son ya kusance ta? Gabad'aya ya ji so yake ya fita da ita zuwa UK don lafiyarta da ta babynsu ta tsira. Haka ya kwana da ita tana kwance ana kara mata ruwa bata san inda kanta yake ba. Sai washegari sassafe ya buga ya faɗawa Momi sannan ya k'ira Faruku ya sanar masa a asibiti suka kwana. Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:05] *Surayya Dee* 08032773332

Daidai lokacin Jamilan Faruku ta iso tare da Alti d'auke kwandon da abinci. Sai kusan azahar Abida ta mayar da Baba da Momi gida. Yayin da aka yanke shawarar Abida da Alti su kwana da ita. Da yammaci direba ya kawo su Aysha dukkansu suka dubata. Daidai lokacin Abida ta dawo tare da Farha da junior akan Yaya Faruku zai juya da su tare da matarsa. Farha ta kalli Bilki da take kwance tana barci . A fili ta ce "Allah na gode maka da Mahmah ba guduwa mini ta yi ba kamar yadda muka guduwo su Yaya ba." Asad da yake gefe ya ji wani irin abu ya soke shi. Gabad'aya k'alubalantar kansa yake yi. Akan me zai mata wannan batun a halin da take ciki? Me yasa bai bari ta haihu lafiya ba? Ga shi yanzu ya janyo ta shiga tashin hankalin da bai san yadda zai dire ba. Ba abin da yake tayar masa da hankali irin yadda aka tabbatar ita d abin da ke cikinta suna cikin garari. So yake ya ganta cikin nutsuwarta ya bata tabbacin zai dawo mata da d'iyarta har ma da Alti. Sai dai da alamun komai ya k'wace masa don tun jiya take kwance tana barci bata san wanda yake kanta ba. Gabad'aya hankalinsa ya yi mugun tashi. Daga Faruku har Baba ba wanda ya tuhume shi. An zuba masa ido. Komai ya tsaya masa cak. Idan ya koma gida ya ga yara ne su kad'ai suke rayuwa sai ya ji damuwarsa ta sake rub'anya ga su Noor da suke tambayarsa yause Mahmah da Farha zasu dawo ne a kullum? Sa'a daya ma bai sallami y'ansanda mata da ya dauko lokacin da zai tafi Calabar ba. Wasa wasa sai da Maigado ta shafe sati biyu a asibiti. Zuwa lokacin ma an hana yin zarya da sunan dubata. Alti da Abida ne a wajenta sai shi da kullum sai ya je sau uku. Ta shiga watan haihuwarta ta kuma dawo cikin hayyacinta. Sai dai kuma ta koma yanayi na shiru sosia. Yana wahalar gaske ta yi magana mussaman ace da Asad ne. Gara gara tana yiwa Abida da Alti suma ba haka siddan ba. Amma ko Farha da Alti take cewa a kawo mata ita idan ta zo hannu kawia take mik'a mata. Hankalin Amrah da Faruk ya tashi da basa jin muryarta, kullum Alti da Abida cikin kwantar musu da hankali suke yi tare da basu tabbacin jikinta da sauki. Ranar juma'a Abida ta zauna kusa da ita ta ce ",Yanzu Bilki ba za ki dinga yiwa yaran nan magana ko hankalinsu ya kwanta ba? Ba hutun school ake yi ba bare su taho su gan ki. Idan ba za ki yiwa kowa magana ba, ki taimakemu su da basa kusa ki yi musu mana. Haba da tausayi fa! Ta dinga yi mata nasiha da rarrashi har ta samu ta bude baki ta ce "Ni maganar ce bana son yi Wallahi! Da kulawa Abida ta ce "Kada ki yiwa kowa amma su ki daure ki dinga amsa wayarsu. Yanzu tunda suna gida bari na kirasu ku gaisa dan hankalinsu ya Kwanta". Bugu d'aya Amrah ta d'auki wayar tare da fad'in "Ammi ya jikin Mahmah dai?" Da walwala ta ce "jiki da sauk'i gata ma". Ta mik'a mata wayar. Ta masa suka gaisa. A sanyaye ta ce "Amrah na ji sauki sosai idan na yi magana da yawa gajiya nake yi ne, ba wai ciwon ne ya tsananta ba. Ai kinsan ko da ina nan wani lokacin maganata na daukewa ko?" "Eh Mahmah ".. Amrah ta masa babu kuzari. To idan baku jini ba ku daina damuwa, da sauki sosai jikina. Ina Yaya Faruk?" Ya karbi wayar ya ce "Mahmah idan bamu jiki ba, gaskiya munsan ba ki da lafiya, maganar kada mu damu kuwa babu ita". Ta murmusa kad'an ta ce "To yanzu da kuka jini hankali ya kwanta?". "Eh amma ba sosai ba, sai mun zo mun ganki da idonmu. Ina Farha?"

*Wannan littafin kudine* *Duk wacce ta karanta bata biya hakkkn wahalar rubutu ba, ina bin ta bashi*.

Ta ce "Yau bata zo ba." Daidai lokacin oga Asad ya turo kofar d'akin ya shigo. Alti ta gaishe shi ta fice, don shi kam bata saba da shi ba, babu sakin jiki a tsakaninsu. Ya tsaya a kusa da Abida yana sauraren Bilki na magana cike da mamaki.

Daidai lokacin ya jiyo Faruku na fad'in "Dady ma ya ce "Idan mun yi waya na fad'a miki yana yi miki sannu". Ya kurawa Bilki ido mussaman da ya ji ta ce "Na amsa ka ce masa "Na gode, ina k'anwarku?" "Lubaba tana nan an yayeta jiya." Faruku ya fadi hakan. Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:08] "To ka siya mata biskit da sweet idan Daddy ya baka kudin break ranar Monday ". "To Mahmah guda nawa zan siya mata?". "Guda shida shida". "To zan siya mata , dazu ma Yaya Amrah ta soya mata samosa ta kai mata". "Ta kyauta, to sai anjima" Daga haka ta mikawa Abida wayarta. Ta gyara ta kwanta. Abida ta mike ta ce "bari na je asibiti sai dare Zan dawo in sha Allah." Ta dauki jakarta ta fice. "A dawo lafiya". Asad ya amsa mata babu wani karsashi don sosia ya ji wani iri da ya ji Bilki na magana da yaranta amma shi tunda ta zo asibitin nan bata taɓa bude baki don ta amsa masa ko da sannun da yake yi mata ba. Kuma ta ga ya shigo amma ta bude baki ta ce ta amsa gaisuwar tsohon mijinta. Sai da Abida ta fita sannan ya zauna a kujerar gaban gadon. Ya ja kujerar daf da ita, ya zauna ya kama hannunta na dama ya rik'e Yana dannawa a hankali. Murya ba amo ya ce "Sannu Maigado" Bata amsa ba, ya sake maimatawa a karo na biyu, maimakon ta amsa da baki sai ta daga masa hannu tabbacin ta ji ta amsa. Takaici ya mak'ure shi tunda ya fahimci tafi tsananta rashin yin magana a kansa.

Ya numfasa ya ce "Na so mun tafi London kin haihu a can. Momi kuma ta ce 'ba zai yiwu ki yi tafiya a yanzu ba'. "Ba zan iya ba, kuma bana son tafiyar ma". Ta fad'a a hankali. Daga haka bata sake magana ba, Duk yadda yake ta yin maganganu na rarrashi da kwantar da zuciya. K'arshe ma sai ya ga barci ya yi awon gaba da ita. Ya tsura mata ido abubuwa masu yawa na taso masa a kanta. Ya fahimci gabad'aya ta hak'ura da shine. Damuwa ta yi masa ya yawa. Ya rasa inda zai tsoma ransa. Suna cikinn haka k'iran Yaya Hamida ya faɗo wayarta. Ta dauka suka gaisa ta yi mata sannu, daga suka yi sallama tunda tasan bata iya doguwar magana. Mintina biyu a tsakani k'iran Ansari ya shigo, Shima ta amsa, bata ajiye wayar ba na Saddiqa ya shigo, haka ma na Anisa. Oga Asad yana zaune yana jinsu kowa jikinta yake tambaya tare da fad'a mata ta yi hak'uri ta cire damuwa bawa ba ya wuce k'addararsa. Ya yi shiru yana nazarin wato Hamida ce Duk ta fad'a musu yau ta samu Bilki shine duk suka k'irata d'aya bayan d'aya amma su basa k'iran kowa a cikinsu hatta Baba kuwa in aka cire Saddiqa da Ansari da su din ma sai an d'auki lokaci mai yawa. Auren da yake kan Hamida kad'ai ne ya shatawa Oga Asad layin cin mutuncinta amma tabbas ya washeta tamkar yadda ta washe shi. Bata da mutunci ko kad'an. Tunda ya auri Bilkisu ya ga bata zo ba, har yau kuma bata tako ta zo gidansa ba, ya tabbatar da gaske take gaba da shi. Rashin zuwa yi mass ta'aziyar Rukayya bata bige shi ba kamar rashin zuwanta aurensu. Anan ya tabbatar hatta ubansu ma bata ganin kimarsa ko kad'an tunda gidan da yake nr ba zata zo. Shiyasa bai cika zafafawa akan kiyayyar da suka girka masa ba haka siddan, tunda wan ubansu ma bai tsira ba. Ya kuma yi ammanar ita ta cusa wa k'annenta k'insa don ya yi imani da Allah ita ta zuga Bilki ta so fasa aurensa bisa hujjar baya son uwarsu bai zo musu ta'aziyar rasuwarta ba9baya son yayansu Sulaiman. A yanzu ba zai ce musu komai ba amma idan Sulaiman din ya bayyana ya ci ubansa a gabansu sa yi a hankali da shi.

A hakan dai ake tafiya ta fara samun sauk'i sosia amma fa babu magana. Baba da Momi da Yaya Faruku kawia take bude baki ta gaishar, suma daga gaisuwar bata sake ce musu uffan sai ido. Su duk suka damu yayin da Abida ta fahimci ba matsalar da sauki tunda tana gaida wadanda ta san ya kamata ta gaishe da su. Oga Asad ne kawai bata gaisarwa, sai kuwa su members. A ranta ta ce yanzu zaka gane Bilki ta fini daru da gaske, ni hayaniya na fita sannan kalata a bayyane take. Amma irinsu Bilki kafin a gane azaabr da suke ganawa mutum ai sai ya kusa shekawa lahira. Tana kallon yadda idan ya zo yake bare baren yiwa Bilkin magana tare da rarrashi da tambayar me take so ita kuma tana yin biris tamkar wacce ta hadu da lalurar rashin ji. Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:11] Har zuciyarta take dan jin babu dad'i na yadda take yi masa, amma ta yi maza ta cire abin a ranta tana fad'in kun fi kusa, matsalata kad'ai ta ishe ni. Amma ita da kanta Abida mamakin zaman Farha a wajen Momi take yi. Tunda Bilki ta koma ta ga Farha da Alti na gidan ta tambayi momi akan yaushe zasu tafi ne, gara Farha ta tafi tunda makarantarsu d'aya da Noor. Kuma makarantar tafi kusa da gidan Bilkin. Haka kawai ta fad'aomi ta balbale ta da fad'a ina ruwanta da maganar Farha. Bilki take rikewa ita kafin ta haihu. Ta daina tisa ta a gaba tana yi mata tambayar da ba huruminta ba ne. Guiwa a sake ta bar d'akin Momi tana ayyana tunda zamanta ya yi nisa dole a gundura da ita. Abu kad'an zata yi momi ta yi ta mata sababi. Yanzu Hatta junior idan yana wasan tsaleltsalle momi zata hau fadan ya fitine su, baba baya son hayaniya amma ta bar d'anta ya cika musu gida da k'iriniya. Har ta kai ta kawo matuk'ar suna gida rufe su take yi a d'aki shi da ita tana ayyana Sulaiman ne ya janyo mata ta zama mujiya a gidansu. Ita mamaki take yi wai kuwa ba a canja zuciyar iyayenta a kanta ba? A yadda take ganin take take momi ba dan kullum tana fita asibiti ba, da sallamar y'an aikinta zata yi. Tunda indai tana gidan bata saka y'an aiki hidima kowacce irice. Komai Abida zo ki yi kaza, Abida je ki wanke mini band'aki, Abida zo ki yi mana girki ni da Babanku. Abida na fi son ki wnake mini kayana da kanki. Abubuwan dai tamkar da gayya, ta tabbatar momi ta gaji da ganinta a gidanta. Bata da wanda take iya faɗawa laifin momi sai Yaya Salaha da take Ibadan a yanzu. Itama hak'uri take bata tare da fad'a mata ta bita a hankali komai zai wuce. Tun yammaci Bilki ke ta fama da ciwon cikin da ta tabbatar yau kam haihuwa za'a yi ta da ikon Allah. Da yake tare da Abida zasu kwana sai bata faɗawa kowa ba. Sai dai wajen asuba ciwo ya tsananta hankalin Abida ya tashi ta fara tunanin ta amince a yi amince a yi mata c.s. Ta shige cikin likitoci asibitin aka fara shirin yi mata aiki. Ana idar da sallar asuba ta kira baba ta fad'a masa halin da suke ciki. Tana kashewa ta k'ira oga Asad ya sanar masa. A kidime ya ce "Sai da na ce zan tafi London da ita aka ki". A sanyaye ta ce "Just pray Daddy in sha Allah aikin will be successful." Daga haka ta katse wayar a dalilin yadda haihuwar ta taso gadan gadan. Nan da nan suka kewaye ta. Ta haifo yaro kukansa ya cika dakin. Aka yi kokarin rabasu. Jikin Abida ya mutu a dalilin yadda ta ga Bilki ta galabaita Anya zata iya sake haihuwar na biyun da kanta? Tunda ita tasan twins zata haifa tuntuni ta fad'a mata, yanzu kuma da take duba file dinta ta ga ni. Itama kuma bata faɗawa kowa ba, zata taya Bilki bawa family suprise. Haka dai aka yi ta fama da gurmuzu suka sake tayar mata da nakuda. Cikin taimakon Ubangiji na biyun ya iso duniya. Shima da kukan ya iso tamkar gyare. Sai da suka kwashe mata jini bayan mabiya ta fito sannan aka yi mata dinki dan kuwa ta samu tear sosai. Tunda Bilki take haihuwa bata taɓa cin ko da kwata din azabar da sha a wannan haihuwar ba. Sai Dai kuma ana gama mata dinkin da aka gyara mata jiki ta sha tea sai ta ji babu wanccan azabar da ta kwana a cikinta. Ana kammala shirya yaran Abida da rawar jiki ta d'auki guda d'aya ta fita da shi. Kaitsaye Baba ta mikawa da suke zaune a reception tare da Momi da oga Asad da kuma Yaya Faruku. Ya karbe shi da Bismillahi ya yi masa addu'a ya duba kunnenta ya ga da duhu ya ce "To wannan bamu bane su baba K'arami aka kwaso" . Asad bai ce komai ba don kuwa ya fahimci duhun fatarsa ya d'ebo. Wani irin tsuma yake yi so yake ya karbi yaron ya gan shi da idanuwansa ashe dai zai samu boy a duniyarsa? Sai dai nauyin idon iyayensa ya saka ya had'iye zakuwarsa. Baba ya yi mass addu'a Abida tana Shirin cewa zata basu suprise Kawai baba ya ce "Je ki dauko mini d'ayan Abida". Da mamaki ta ce "Ai d'aya ne Baba! Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:15] Ya girgiza kai ya ce "Na kai wata a jere kullum sai na yi mafarkin Bilki ta haifi tagwaye. Tun abin bai shiga raina ba har na gamsu tunda tsohonmu tagwaye ne ya biyo. Haka a dangin gyatumarmu sun gaji haihuwar tagwaye." Abida ta yi murmushi ta ce "A a Baba to Dai dan d'aya ta haifa ". Ya jijjiga kai ya ce Idan na yi mafarki na rik'e ban manta ba, sannan na sake yin irinsa to Sai na Ga abin nan a zahiri bare wannan na yi jar na kagu na ga yanbiyu cikin ahalinmu". Ta murmusa ta ce "To menene tukuicin wannan jaridar Baba?" Daga shi har ita jikinsu ya yi sanyi a dalilin sun tuna da, don da a shekarun baya ne da saniya ko tunkiya zai bata. Ganin hakan ya sanya ta juya da sauri. Yayin da oga Asad ya mik'e tsaye ya kasa zama, gabad'aya sai kai komo yake yi, tare da tunanin dama Bilkisu da Babanta har ma da Abida sun sani shine ba wanda ya taba fad'a masa. Ikon Allah yake ta fad'a a fili a k'asan zuciyarsa kuwa hailala yake yi tare da istigifari. Haka ya hango Abida sabe da sabon jariri lullube cikin shawul irin na d'anuwansa. Tabbas Bilki ta san twins zata haifa tunda ga kaya nan iri daya a jikinsu tabbacin an yi musu shiri. Kai wannan shine mafi girman ba zata da aka yi masa da bai taba jin dad'i irinsa ba. Baban ta sake mikawa ya ce wanne ne babban kenan?" Ta nuna wanda ta kawo yanzu. Ya ce "To Abdallah ne ga kuma Abdulrahman". Abida ta ce "Baba gaskiya ba haka za'a yi ba, ka yi mini alfarma nima na yi iko irin wanda Bilki ta gwada mini akan sunan junior ". Murmushi na sosai Baba ya yi tare da fad'in "Ho Abida". Dad'i ya ratsa ta don kuwa rabin da ta ga wnanan murmushin na gaskiya a tsakaninta da shi tun komai bai taɓarbare musu ba. Ya yiwa wanda ta kawo addu'a ya duba kunnensa shima ya ce "A a wannan ma baya bangarenmu duk kune Abida. " Ta ce gara da ya biyo mu ai Baba, don kun fimu yawa." Daga haka aka bawa Momi ta gansu sannan aka mikawa Yaya Faruku. Abida ta ce "ABBA duba ka ga wadannan layinmu ne ba naku ba." Ya karɓa da Bismillahi tare da kurawa yaron ido yana mamakin fuskar oga Asad akan ta yaron. Haka da ya duba d'ayan ma sai ya ga dukkansu kama suke da junansu irin sosia din nan, tamkar babansu ya yi kakinsu. Ya yi musu addu'a. Ya kalli Abida ya ce "Wanne sunan za ki saka musu rigimatu?" Ta ce "Sunan Baba Babba da Baba K'arami zasu amsa. Dukkansu har baba da Momi na wanda ya tanka tabbacin sun aminta da ra'ayinta. Faruk da kansa ya kaiwa Momi yaran. Ita kuma ta rik'e Su a jikinta. Baban Bilkisu tamkar ya je ya karbe su ya gansu Amma ya daure ya cije ya yi jarumtar kawar da kai. Amma k'asan ransa ba k'aramin takura ya yi ba. Har aka dawo da Bilki ainihin d'akin da take kwance suna asibitin Basu tafi ba. Gabad'aya suka dunguma zuwa d'akin don yi mata sannu. Tana zaune ta shirya tsaf tamkar ba itace ta tsallake siradi ba Sannu suke ta yi mata, tana amsawa a hankali. Abida ta ce "Yanzu me yake yi mini ciwo?" A hankali ta ce "Ciki amma ba sosai" . *Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*. *Dan Allah ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*. *Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Sanyi flusher kuwa best seller ne* *Just DM for your order @08033773332*.

"Sannu zai daina tunda an yi miki allura. Yanzu bari Ki ci abinci ki sha magani sai ki kwanta ki huta". Abida ta fadi hakan da kulawa.

Momi ta mik'a mata yaranta cikin tufafi iri d'aya farare kal. Ta noke ta k'i karɓa ta ce "A a zan gansu ne momi". Asad ya ji wani iri Ashe da gayya Shi ta ki ba shi yaran. Momi zata sake da kowa amma ban da shi har yanzu bata ware da Shi ba. Zata yi hira da Faruku tamkar ta goya shi amma shi indai ta ja doguwar magana a tsakaninsu laifi ya yi. To nan kam ta dinga yi masa fad'a tare da yi masa jirwayen Faruku ne dattijo mai halin manya. Kai Hausawa da kuttu suke Wallahi. Save Restricted Content Bot, [Oct 9, 2025 at 17:18] Idan ka zo a dan fari a shekarun baya kana cikin talajaurar duniya. Daidai da sunanka uwarka mahaifiya ya haramta ta fad'a kaitsaye. Har ya yi aure wannan yaron take ce masa. Sai da y'ay'ansa suka fara girma ne ta koma cewa yayanku. Amma da kunnensa bai taba jin ta ce Asad ba, kai ko Abubakar ma bata fad'a. A ransa ya fara jin takaicin zamowarsa dan fari dama Faruku ne babba ba shi ba. Ya numfasa tare da auna banbancin iyayen da na yanzu. Y'ay'an yanzu don sun zo a farko iyaye mata basa yin alkunya a gaban kowa suke nan da nan da su ko da kuwa a gaban iyayensu ne ba ruwansu. Muryar Abida ta katse masa tunaninsa da ta ce "Ya kamata su sha nono, dazu basu sha sosia ba." Ta kalli inda Asad yake zaune a takure ta san kuma ganinsu Baba ya hana shi sukuni. Ta karbi yaran a hankali tare da fad'in "Bari Dady ya Gansu momy ". Cikin nutsuwa ta bashi Su sannan ta ce "Ga Baban Abida da Baban Munira nan Allah ya raya su." Bilki bata ce komai ba, jikinta ya gama bata matuk'ar ya tabbata maza ta haifa to kuwa Sunan da zasu amsa kenan. Amma a yadda Abida ta ce Babanta da na Munira ta fahimci so take ta gane itace ta zaba musu suna. Don a da da suke yara idan ta so bakanta mata sai ta ce "Baba Babba babanta ne Baba k'arami kuma na Yaya Munira ne ita yar rik'o ce daga danginsu baba shiyasa take kama da shi". A lokacin Bilki ba wayo sai ta yi ta kuka. Baba K'arami kuma ya gasgata batun Abida na cewar rik'o aka kawo ta gidan. Bilki ta girgiza kai tare da murmushi kadan Abida ta yi tsiyataku mata kala kala. K'asan zuciyarta kuma zargi take yi itama iko ta nuna mata kamar yadda itama ta nuna mata akan junior. Zata yi magana Kawai hankalinta ya kai Kan talabijin din da take makale a jikin bango inda tashar T.V.C News ta rubuta breaking news. Hankalin Bilki ya raja'a ta mayar da hankalinta kan talabijin din. Tabbas ba gizo idonta yake yi ba. Sunan dai shine babu kuskure. Ta kalli y'an d'akin duk hankalinsu ba ya kai, mussaman oga Asad da yake rungume da yara yana ta faman kallonsu. A ranta ta ce "Ya tisa yara a gaba da kallo a gabansu Momi. Bakinta ya yi nauyi ta kasa fad'in komai kawai ta fara nuni da hannunta izuwa talabijin din. Hankalinsu ya kai kan fuskar talabijin din don ganin abin da take yi musu nuni. Save Restricted Content Bot, [Oct 10, 2025 at 10:49] *Surayya Dee* *08032773332*. *Wannan littafin na kudine* *Ga mai son biyan hak'kin wahalata 1k ne* *2384876855* *Zenith Bank* *Surayya Ibrahim*

*Lame.Ng Skin Beauty and wellness* *Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.* *07036662633*

*Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull