Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 21
Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 21: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 21. Ya ce "Sake ni tun ban miki sanadin da za ki tozarta ba."…
4,279 words
Ya ce "Sake ni tun ban miki sanadin da za ki tozarta ba." Ta d'auke kai ta ce "Ba wani tozarcin da zaka yi da zai fi wanda ka yi mini. Ka tafi ka bar ni da aurenka a kaina shekaru hudu babu waiwaiye, kuma ba wanda yasan inda ka ke, sannan yanzu ka ce zaka tozarta ni, wanne irin tozarcin kuma?" Ba fargaba ya ce "Jira nake yi na ji kin yi aure na dawo mu sake shiga kotu, kinsan na tsotsi kafiya da rashin mutuncinta". Ta rikice gabadaya take ta ji ta rasa kuzarinta don har rikon da ta yi masa sai da ya yi sakwasakwa. Idanuwanta sun ciko da k'wallar nadama ta ce "Na janye kalamaina, ban tab'a jin nadama a dukkan tsayin rayuwarta irin wacce na yi akan kalaman da na jefeka da su ba, ka yi hak'uri. Na yarda ban kyauta ba. Allah ya baka hak'uri! Ya murmusa ya ce "To sake ni." Ni fa ba zan sake ba har sai Baba Babba ya gan ka.". Abida ta fad'a idanuwanta cikin nasa. Ya zabura ya shammace ta ya fizge ya fara k'ok'arin tafiya wajen adana motoci. Ta kuwa sake kai masa wawura. Takaici ya k'ume shi ya ji tamkar ya gaggaura mata maruka masu zafi ko ta shiga taitayinta amma ba zai iya ba. Juyin duniya ya b'anb'are hannunwanta tuburan ta k'i ba shi damar hakan tabbacin da gaske take yi sai ya gurfana gaban Baban nasu. Suna cikin haka securities suka zo wajensu. Suka yi magana da Sulaiman da larabci ita dai ba ta ji me suka ce ba ta ga sun tafi ne kawai. A hassale ya ce "ba za ki sake ni ba ko?" Ko uffan ba ta ce masa ba illa iyaka tsananta rikon da ta sake yi. Ita da kanta mamakin cakuikuiye shin da ta yi take yi, bata gane matsanancin son da take yi masa ba sai a ranar. Don kuwa ji ta yi matuk'ar zai sake kubuce mata bayan ta gan shi gara ta mutu ko ta huta da azabar da ke dandana ta rashinsa. A haka ta hango ya Farouk ya shigo. Nan da nan ta bude murya ta ce "Yaya Farouk ga shi na rik'e maka shi". Da hanzari ya iso kusa da su ya kallesu kowa fuskarsa babu walwala sai suka tuna masa shekarun baya da suke y'ar tsama da junansu. Ya kaurara harshe ya ce "Sake shi Abida ya za ki cakume shi irin haka?" Nan da nan Sulaiman ya ce "Ba ta riga ta raina ni ba. Saboda tana da gatan da zata yi komai yadda take so, ba tare da an kwabe ta ba. Ya fad'a cikin fishi sosai. Ta sake shi a sanyaye don ta lura fishi mai tsananin gaske ya yi da su.
Deenah cakes and more -Kano 09038055790 IG @Deenah cakes and more Snacks such as : Birthday cakes Cupcakes Samosa Springrolls Meatpie Frozen snacks Event snacks Patronage my daughter.
Yayin da Faruku ya hassala da kalaman Sulaiman. Amma ya yi jarumtar had'iyewa ya ce masa "Wuce mu je ciki". Cikin sigar umarni. Bai musa ba ya yarda suka tafi ba don komai ba sai saboda Yaya Farouk mutum ne da kowa a gidan nasu yake jin kunyar yi masa rashin kunya saboda tsananin kirkinsa da haba haba da yake da su ba tare da tunanin su din k'annensa ba ne. Tiryan tiryan har d'akin da su baba suke ciki. Kaitsaye gadon da Baba Babba yake zaune Sulaiman din ya nufa ya durkusa tare da fad'in "sannu Baba ya jikin, ya kuma iyali?" Duk d'akin aka zuba musu ido domin dai Baba Babba bai amsa masa gaisuwar da ya yi masa ba, asalima d'auke kai ya yi tare da juyar da fuskarsa d'aya gefen. Hankalin Sulaiman ya tashi ya yi k'asa da kansa cikin girmamawa ya ce "Ka yi mini hakuri Baba a gafarce ni dan Allah". Baba bai ce komai ba, bai kuma juyo ba. A sanyaye yaya Farouk ya ce " A yi hakuri Baba.". Amma ko motsi Baban ya k'i bare ya tanka musu. Karon farko da suka ga an gaishe shi ya tankwabar da gaisuwar a dukkan tsayin rayuwarsu gabad'aya.
Ganin haka ya sanya Momi ta ce "daure Alhaji, sake yin hak'uri." Hankalin Sulaiman ya yi tashin gauron zabi duk da shima cike yake da gillin ba'a yi masa abin da ya kamata ba, amma ya gamsu ya yi laifin da Baba zai yi masa fishi. Fishinsa a kansa kuwa tamkar fishin mahaifinsa ne don haka zai yi iya k'ok'arinsa don ganin Baban ya huce ya karbi gaisuwarsa har ya saka masa albarka. Ya mik'a hannunsa ya rik'e hannunsa cikin girmamawa da taushin harshe ya ce "Dan Allah Baba ka yi hak'uri, na yi kuskure ban kyauta ba. Dan Allah a gafarce ni! Sai lokacin Baban ya juyo da fuskarsa ya d'ora akan ta Sulaiman sai ya ga ya sake girma da kuma alamun yana cikin nutsuwarsa. Ya ce "Anya kuwa Sulaiman zan hak'ura da abin da ka yi mini? "
Kansa a k'asa ya ce "Da kaina ina k'alubalantar kaina Baba. Amma dai ka daure ka yi hak'uri ka karbi tubana da gaisuwata dan Allah!
Baba ya nisa ya ce " Zan karbi gaisuwarka ne kad'ai idan ka yarda ka zo mun tafi gida, don sai mun je gida zan fad'a maka sharadina akanka idan ka amince da sharadina to sannan zan hak'ura na kuma huce. Idan ba haka ba kuwa to lah shakka ba zan karbi gaisuwarka ba, bare na huce da kai, kuma yanzu na gane kai ne Dr Isa din da zai yi mini aikin ido to kuwa ba zan amince a mini aikin ba gabad'aya ". Nan da nan Sulaiman ya ce "Zamu tafi tare Baba. Zan nemi izinin tafiya da hukumar asibitin, idan da rabon zan dawo na cigaba da aikin da su sai na dawo, idan kuma iya adadin da k'addara ta rubuta zan yi aikin da su shike nan sai na yi zamana a asibitin k'asata." Dad'i ya kama Baba Babba ya ce"Madallah da Sulaiman ya bayan rabuwa?" Kunya ta kama shi ya yi k'asa da kansa ya kasa amsawa. Daga haka ya juya ya gaida momi daga durk'ushen da yake. Ta amsa da sakakkiyar fuska tare da tambayarsa aikinsa. Bai tashi ba sai da ya gaida Yaya Farouk duk da shi Farouk din hannu ya ba shi tare da mik'ar da shi yana fad'in Dr Sule sai kuma Dr Abida ta yi mana ram da kai! Gabadaya d'akin aka hau dariya ban da Sulaiman da ya maze. Ita kuwa Abidan murmusawa ta yi wanda tun daga k'asar zuciyarta yake kutsowa. Dadai lokacin nurse din da zata yiwa Baba allura ta iso d'akin. Ta yi aikinta ta fice. K'arfe goma na dare aka shiga da Baba dakin tiyata k'arkashin jagorancin d'ansa Dr Sulaiman Isa Funtua! An yi aiki cikin nasara kwana d'aya ya sallame su. Sulaiman da kansa ya kai su masaukinsu tare da bawa Baba tabbacin zai sayi ticket din da zai bisu Nigeria in sha Allah. Baba dai duk hidimar da Sulaiman yake yi masa kallonsa kawai yake yi don kuwa da ace yana cikin shekarun k'arfinsa, kuma ba Abida ce matarsa ba da zane Sulaiman zai yi tabbas. Washegari momi da Abida suka fara shiga kasuwa yiwa yara tsaraba. Tun ranar da aka ga Sulaiman Baba ya gargade Slsu gabad'aya akan kada a sake a bayyana an gan shi, a bari sai Allah yasa sun isa lafiya kowa ya gan shi. Duk zumudin Abida akan ta sanarwa Bilki wuridin kiranyensu ya ci haka ta had'iye ta kama bakinta bata fad'a mata ba. A hanya Momi ta kalle ta ta ce "Abida ban ga kina gaida Sulaiman ba, ba sai na fad'a miki komai akan halayyarsa ba. Ki bi shi a hankali ki ajiye girman kanki ki lallaba ku sasanta ki koma dakinki tunda dai bai sake ki ba. Kin ga dai yadda ya jingine ki tsawon shekaru babu waiwaiye, idan kuma kin ki jin shawarata ki tabbatar kwabarki ce zata sake cabewa. Ya bar ki da k'aramin cikin da wataƙila ma bai san da shi ba. Ga yaro nan yana gudu har yana gwalantun surutu. Duk sababinki Sulaiman ya dame ki ya shanye kin sani sarai, dan haka ki kwantar da kai har Allah yasa ki koma dakinki". "To momi shine fa baya ko kallon inda nake, sau biyu ina gaishe shi yana yin kamar bai ji ba tsabar dan sababi ne, shiyasa na daina, ni dai ki taimake ni, ki fad'awa Baba a cikin sharadin da zai gindaya masa har da ya dauki iyalinsa ya zauna da su lafiya". Dariya momi ta yi ta ce "Sannu Abidan Baba! Amma ai kinsan ba zai yi hakan ba. Da dai ace ba ke ce iyalin nasa ba zai yi hakan. Yanzu ke za ki gyara laifinki, tunda ke ce a k'asansa." Abida ta ce "Ni Wallahi Momi wulak'ancisa ne bana so. " Da sauri momi ta ce "Ai tunda ya fara sonki ya daina yi miki, sannan kin sani da kuka yi auren ai rarrashin zuciyarki yake yi. Daga baya kuma ke kika bijire akan ba za ki zauna da shi ba, akan laifin da ba shi ya yi mana ba. Ni dai na fad'a miki gaskiya ki yi maza ki gyara tazarar da kuka haifar a tsakaninku. Don kuwa ke kanki kin san na gaji da ganinki a gidana". 101
**** 102 A sanyaye ta ce "To." A zuciyarta kuwa itama ta gajin kawai bata son dan tijarar ya gane ne, bare ya sake samun kuzarin cin kasuwa akanta yadda ya so". Don gabad'aya tunanin ta inda zata bullo masa take yi. Ta tabbatar ba k'aramin artabu zasu yi ba, mussaman da ya ce ya yi jirwayen an zuba mata ido tana yin yadda ta ga dama babu mai kwabarta. Murmushi ya k'wace mata a dalilin ta tuna fad'ansu na k'uruciya a duk sadda aka tare shi idan ya yi nufin kai mata duka sai ya tunzura ya ce 'Ana bata lasisin ta cigaba da raina shi, a yiwa Allah a taimake shi a bar shi ya yi mata dukan da ko mai irin sunansa ta ga ni sai ta shiga taitayinta. Ana marawa Abida baya ta cigaba da yin isgili yadda take so". Ta tuna mafi yawa baba Karami yake hana shi dukanta. Ya kan ce masa "Sulaiman ai ba'a kanta zaka gwada kwanjinka ba, daure ka daina kula ta ai kanwarka ce. Ni dai zan so na ga k'arshen wannan fadan naku da baya k'arewa. Ba dama ku zauna a inuwa d'aya. Shiyasa da ya ji suna soyayya har sun amince a yi musu aure ya dinga jinjina k'arfin k'addara dan dai shi ba mai barkwanci bane irin baba Babba ba. Amma tabbas ya yi mamaki, ya yi murna ya dinga ce wa 'Sulaiman ashe da na sani na bari ka yi mata dukan da zaka targad'a ta da shikenan sai ka zama mijin gurguwa.' Gabadaya wata irin nutsuwa da walwala ne ya dabaibaye zuciyar Abida. Ta dinga jin wata irin soyayyar Sulaiman na sake bin dukkan ilahirin jikinta. Amma a yadda ya karbe ta ta tabbatar ba k'aramin gumurzu zasu yi ba kafin su daidaita. A zuciyarta ta kud'ire duk inda k'arfin zuciyarta ya buya sai ta lalubo shi, duk yadda ta matsu ya bayyana, duk yadda take jin soyayyarsa ba zata bari ta bayyana masa muraran ba tunda shima k'wallon kansa ne, to ba zata bari ya jata a k'asa don tana son ya zauna da ita ba. Barinta da ya yi tsawon shekaru hud'u ya isa hukuncin zaginsa da ta yi ba zata bari ya sake wani hukunci mai yawa ba.
** Abuja
Oga Asad da Bilki dai zama ya yi tsami kowa harkarsa yake yi a tsakaninsu. Abinci ma sai ya dawo yake saka Angela sabuwar chep din gidan ta yi masa abin da yake son ci. Hakan ba karamin sake tunzurata ya yi ba. Yana gama uzzirinsa kuwa zai saka Bilkisu ta karbo masa twins ya dinga fama da su har sai dare ya fara nisa sannan zai mayarwa Alti su. Ya tattara ya fita a harkarta. Sai dai daga shi har ita kowa ya shiga damuwa. Bilki ta fara gasgata lallai ta fara sonsa. Fishin da ya dauka ya dameta ainun. Ranar alhamis tura ta kai masa bango. Har sha d'ayan safiya yana gida tamkar ba ranar aiki ba. Tun goma kuma twins suke wajensa. Wayar Bilki ya dinga k'ira tunda ta ga shine take biris har sai da hankalin Alti ya kai kan kiran da yake shigowa. Ta ce "Mahmah duba ana ta miki waya ko Alhaji ne ga kukan Baba Babba Ina dan jiyowa." Bilki ta ce kunnenki ne Alti, ni ban ji ba". "To amsa k'iran dai". Dole ta amsa. Tana dauka cikin sigar umarni ya ce "Ki zo yanzun nan". Takaici tamkar ta yi ta zunduma ihu. Kan dole ta tashi ta nufi samansa tana jin idanuwan Alti na takura mata ba don kada ta dinga jin babu dad'i a ranta tare da jin bata isa da ita ba da ba zata je k'iran nasa ba. Tana isa ta tarar kuwa baba Babba ke kuka sai dai kukan ya ragu ba kamar dazu ba. Ya sassauta ya ce "Zo ki zauna. Bata musa ba ta zauna din. Ya dad'e yana kallonta. Ta gama sacewa duk wani kumburi ya sace ta yi kyau sosai hannuwanta d'auke da kalle mai ban sha'awa ga kuma zobunan gold suka sake kawata yatsun nata. Ya nisa ya ce "Maigadona da alamu dai kin kwashe kayan rankatakaf a gaban ma'aikin Allah!. Ta kawar da fuskarta gefe yaune zai ce Maigado. Kwanakin baya ai Bilki ya dinga cewa gatsal wanda Har zuciyarta ta ji wani iri tunda tun filazal baya ce mata Bilki. Amma saboda ya so k'ank'anci ya dinga fad'in gayan sunan nata". Ya sassauta ya ce "Amsa mana sarauniyar shaiba ke dad'ina da ke rashin wayo". Ta sake matsewa ta ce "Na'am ". Ya nisa ya ce "D'akina ne ya yi kura sosai, da kanki nake son ki gyara mini mussaman shimfida gadon nan". Nan da nan ta gane jirwayen nasa ya gaji da fishin don yana da bukatarta. Ta jijjiga kai lallai kuwa zasu sake hawa sama don kuwa ba zata taba yarda ta kwanta akan gadon da aka girke hoton wata mace a gefensa ba ". Ta mike ta ce "Bari na gyara maka ". Ya yi maza ya ce "To zauna ki ba shi ya sha ban son idan kin fara gyara shimfidar ya katse ki da kuka". Kaitsaye ta ce "Ai tuni bana Basu nono Sai Madara tunda ka ce baka san alherina ba, na daina basu Sai Idan Alti ta matsa, tunda shari'a ma ta ce idan ba zan iya ba, ka nemo wata ta shayar da su ka dinga biya ". Ya yi sakare yana kallonta. Tabbas akwai matsala babu tantama Hamida and co sun yi tasiri a cikin gidansa. Ya had'iye fishinsa ya ce "Na janye kalamaina. Dan Allah ki yi hak'uri, kada ki yi mini haka mana". Ta yi shiru. "Pls Maigado kin ga dai fiye da watanni biyu rabonmu da juna. Tsakanina da Allah na gaji hakanan, sannan bana son mu sake samun matsala da ke. Dan Allah kada ki gwada ni ta nan, akansu zan iya haduwa da hawan jini tsakanina da Allah. To ban da ma abinki, alherinki ai na daban ne, twins fa kika haifo mini sannan ke ce kika haifa mini boys din da ba ni da su, don kuma raina ya b'aci na yi subutul kalam sai ya zama kin manta komai". Ta numfasa ta ce "To shikenan amma ka zaba ko dai na shayar maka da su ko na gyara maka shimfidar." Ya yi shiru ya ce "Duka biyun nake so Maigado". Ta kwakkwabe fuska har k'walla sun cika idon ta ce "Wallahi d'aya zaka zaba". Ya yi kalar tausayi can ya nisa ya ce "Na hak'ura ki shayar da su sarauniyar shaiba". Ta mik'a masa hannu akan ya bata yaron. Bai ce komai ba ya mik'a mata. Ta gyara ta fara shayar da shi, yayin da ya tsura mata ido yana ganin yadda ta zarta yaron hasken fata. Sosia suka yi masa kyau. Ya shiga tashin Baba K'arami don shima ya sha. Har zata yi magana sai kuma ta k'yale shi. Sai da yaron ya k'oshi dan kansa. Sannan ta saka shi a kafaɗa ya yi gyatsa. Ta kwantar da shi a gefenta. Shi kuma ya yi maza ya mik'a mata Baba k'arami ta karɓa babu musu ta shiga shayar da shi. Shima sai da ta saka ya yi gyatsa sannan ta kwantar da shi kusa da d'anuwansa ta mike ta ce "Sai anjima". Ya kasa cewa uffan, illa ido da ya bita da shi har ta bacewa ganinsa. A zuciyarta kuma ta kud'ire Wallahi indai a d'akinsa zata kwanta to kuwa sai idan babu hotunan maimurabus duk sababinsa kuwa. Ya numfasa a fili ya ce "Yadda na shaida musulunci gaskiya ne, haka na shaida mata ja'iran halittu ne masu tsiyatakun da suke gigita mazaje. Mata da manta alheri suke. Ka ciyar da su safe, rana, dare cimuka kuma gwargwadon k'arfin arzikinka, haka suturar ma, mazaje su sha wahalar gina gida su saka mataye a ciki har a koma fad'in gidansu, su kula da lafiyarsu amma idan ka kuskure musu sai su manta komai na alherin namiji har su iya bude baki su ce me ake yi musu? Ai ciyarwa da tufatarwa ba alfarma ba ne wajibine hak'kinsu da ya rataya aka sauke. Mata da butulci suke shiyasa Annabi ya ce butulcin mace ne ya sanya suka fi yawa a wuta. Ya nisa ya ce "Allah ka shirya mana wadannan karkattatun halittum tunda ka jarrabe mu da sonsu. Duk wahalarmu akansu ce amma gabad'aya sun rantse idanuwansu sun mayar da maza abokan hamayyarsu".🤣 Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 15:52] *Surayya Gwaram* *Wannan littafin na kudine* *Pay 1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank*. 08032773332. *Don samun damar karantawa cikin aminci a telegram*.
*Teemah data service mtn monthly* *1gb @550* *2gb @950* *3gb @1450* *5gb @1700* *Dm 08112392177* *Call 8037026306 Fatima Musa Ibrahim opay*
*For your beautiful kids wears:tees,shorts,trousers,dresses,kids towels, perfumes,body mist contact 08067239846*
*Saudiyya.* Tunda Abida ta ga Sule ya yi d'iban karan mahaukaciya da ita sai ta yi maza ta kame kanta. Tsakaninta da shi ina kwana, ko ina yini idan ya zo duba Baba. Gabad'aya sai ta canja salon addu'ar ta. Tunda ta yi imani addu'ar kiranyen da ta dinga buga masa ne ta karbu sai ta koma buga masa ta a jarrabe shi a kanta fiye da yadda aka jarrabe ta a bayan ya bace mata. Ta yi dawafi akan kada ta wulakanta a hannunsa ba adadi. Tana kammala dawafin kuwa zata yi ta buga nafila tana kama sunansa a sujjuda akan a cika zuciyarsa da tausayinta da zai hana shi matsa mata. A kuma cika k'irjinsa soyayyarta da zata hana shi jarumtar damfara ta da k'asa. Sai ta yi addu'a ta jero sunansa har kan ubansa na biyar. Duk sadda ta gan shi ta ga ya dauke kai itama sai ta kwafse a ranta kuwa tana fad'in "Da ni kake zancen Malam Sule dan Uzairu. Babzai yiwu ka tafi ka bar ni shekaru uku da watanni sannan yanzu na yarda da wani nau'in wulakanci ba. Duk sababinka da zarar na koma d'akina Sai mu fafata don kuwa ba yarda zan yi na bayyana maka soyayyarka da take k'irjina ba bare ka samu Dama a kaina ".
Sulaiman. Yana kwance shi kad'ai a d'akinsa ya yi shiru yana tunanin yadda zai bi su Baba Nigeria a jibi. Zuciyarsa sai harbawa take yi a dalilin yadda al'amura masu nauyi suka dabaibaye shi. Ya rasa me yasa yake yawan jin fad'uwar gaba matuƙar ya d'ora idanuwansa akan Abida. Bai zaci sonta na da k'arfi a zuciyarsa ba har yanzu. Ba sonta ya daina ba dama, amma dai ya yi raunin da yake jin zai rabu da ita, rabuwa ta har abada kuwa. Don bai yi lalacewar da zata zagi uwarsa ya kuma tsaya rarrashinta ba. Bayan haka ta cire ciki nisa hujjar ba zata sake had'a jini da shi ba. Duk kuma aka zuba mata ido saboda sahaffafiya ce y'ar Madara. Ya juya yana tuno siradin da ya tsallake wanda bai samu kansa ba sai shekara d'aya da ta shud'e. Tunda ya bar Nigeria ya isa Germany kwanansa biyu kacal gwamnatin k'asar ta kama shi tare da wasu bakaken fata su uku bisa zargin suna kai yara mata k'ananu karuwanci k'asar ba bisa k'aida ba. Birinin Barlin ya sauka. Ya yi niyyar ya dan yi kwanaki biyu kafin ya wuce birin Hermburg. Da aka tsananta bincike sai aka sake jingina masa laifin ya shiga k'asar ne ta haramtacciyar hanya. Ya yi kokarin nuna shaidarsa amma ya nemi passport d'insa sama ko k'asa ya rasa. Wanda ba shi da laifi ko kad'an illa mugayen mutanen da suke aikata laifin sun had'a wurin zama a jirgi da shi. Da aka kamasu ne don tsananin k'eta da mugunta suka ce tafiyarsu d'aya da shi. Haka aka tattrata aka kai su prison. Ba'a waiwaiye su ba sai da suka shafe watanni goma sha uku. Bisa hujjar da embassy ta gabatar basu shiga k'asar legally ba don haka ba zasu bibiye su ba. Sa'a daya ma kurkukun ba irin namu ba ne. Amma dai kam nadama da kaicon barin gida Sulaiman ya yi shi yafi cikin kwando. Kan dole ya hak'ura ya koma ga Allah ya dinga Ibada tukuru. Amma gabad'aya ya gigice da tunanin makomarsa. Idan ya mutu a wajen nan shikenan ba wanda zai san ya mutu. Idan ya tuna Bilki, Baba da Farha sai ya sake rikicewa k'warai da gaske su kad'ai ne idan ya tuna su ya kan ji rauni na kama shi. Yana cikin haka kwatsam tawagar likitoci da hadakar kungiyoyin jin k'ai daban daban suka kai ziyara gidan yari. Nan ya ci karo da babban malaminsa kuma ogan asibitin da ya yi aiki da su shekarun baya. Da madaukakin mamaki yake tambayar Sulaiman ba'asin zamansa. Tiryan tiryan Sulaiman ya yi masa bayanin azal din da ya fad'a ya nuna wanda yake sanye da irin kayansa ya ce "Ga masu laifin nan daga k'asar Alge suke. Sune da alhakin komai." Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 15:59] Gabad'aya aka kamu da tausayinsa don kuwa hatta b'acewar passport d'insa sune suka cire masa a ƙaramar jakarsa bayan sun isa masaukinsu a ranar da suka sauka a birinin Berlin. Sai da suka ga sun dade a gidan suke neman afuwarsa tare da ba shi hak'uri wanda ya zama na banza. Gabad'aya wajen duk jikinsu ya yi sanyi tare da tausayin Sulaiman k'warai da gaske. Haka wannan Malamin da sauran kungiyoyin suka shiga al'amarin Sulaiman bayan an kai komo mai yawa sannan ya shaki iskar y'anci bayan watanni biyu. Idan an fahimta Sulaiman ya shafe watanni sha biyar a gidan yari a babban birinin k'asar Jamus. Da ya fito yana k'arkashin kulawar hukumar jami'iar da ya yi karatu da taimakon kungiyoyin sa kai. A haka dai har kes d'insa ya kai gaban mahukuntar k'asar da taimakon ofishin jakadancin Nigeria a k'asar. Watanni biyu da fitowarsa ya samu aka yi masa passport din da zai iya barin k'asar sannan gwamnatin k'asar ta ba shi makudan mahaukanta kudade don ya rage radadin bata masa lokaci da aka yi ba bisa hakkinsa ba. A lokacin ya so barin k'asar amma malaminsa ya hana shi, ya saka ya koma makaranta don ya sake kwarewa a b'angaren ido wanda zai yi kwas na watanni goma sha biyar. Gabad'aya nadama da danasani sun masa k'awanya. Ya tabbatar hakkkin barin Baba Babba a halin jinya ba tare da ya yi masa sallama ba, bare ya saka masa albarka ne ya sanya ya hadu da taskun duniya. A dole ya zauna yake karatun nan. Ya kammala karatun cikin nasara, da ya ce zai tafi gida shine aka tura shi aiki asibitin k'asar Jamus da ke Birnin Riyadh, da nufin Idan ya fara aikin a hankali Sai ya je ya Ga iyalinsa. Watansa shida aka dawo da asibitin da yake birinin Makka. A yanzu watansa biyu a birinin Makka. Zuwa lokacin hankalinsa ya karkata matuk'a da son komawa gida don ya murmure ba wanda zai gan shi a tagayyare, kud'i kuwa ya yi shi ba na wasa ba. Yana yawan tuna Baba dasu Hamida. Bilki kuwa yana da labarinta Hatta ajiye aikin da ta yi ya ji, da barinta Katsina ta bakin abokinsa Salim Buba wanda sanadinsa ya samar mata aiki a UmYU. Wanda ya samu lambarsa a Facebook ne bayan ya fito da gidan yari. Sai dai bai ji labarin auren da ta yi ba. K'arshen wata dama ya yi booking din tafiya Nigeria sai kuma suka yi kicibis da shi a tsakiyar wata. Ya juya ya numfasa wato ba k'aramin nauyi da kunyar Baba ne suke yi masa rubdugu ba. Zai bi shi Nigeria zai kuma karbi dukkan sharuddan da zai gindaya masa, amma kam bai huce da Asad da Abida ba. Yana kwance yana hakaito ta, tabbas har yanzu bai ji ya tsane ta ba, amma kuma a shirye yake da ya rabu da ita don kuwa uwarsa tafi komai a wajensa. Matar da yake aure kuwa ta yi kad'an ta rainata ko ta fadi maganganun banza akanta ta kuma kwashe k'alau. Har a bayan ranta tana da alfarma matuƙar yana shakar numfashi. A yadda kuma yake ganin take takenta tanan nan da sauran zafin kanta, bai gama goge mata hadda ba. Ya nisa a fili ya ce "Da sauran ki kuwa, da sannu za ki gane na kerewa duk wasu tsiyatakunki."
*Abuja*