Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 22
Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 22: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 22. Bilki na zaune a d'akinta k'arfe shabiyun dare tana bawa…
4,540 words
Bilki na zaune a d'akinta k'arfe shabiyun dare tana bawa Baba K'arami nono. Alti na zaune tana jiran ta gama ba shi ta mik'a mata Shi tunda ita take barci da su. Kira Sai shigowa wayarta yake yi ba kakkautawa. Ta Kuma san oga ne. Kan dole ta amsa k'iran.urya ba amo ya ce "Ki kawo mini shayi yanzu." Daga haka ya katse wayar. Har d'aya saura kwata bata tashi ba, ita kuma Alti bata san komai ba. Amma ita da kanta tana ganin tunda Bilki ta fara sallah tuntuni ya kamata ta koma turaka mussaman da ta ga sati biyu da suka suka wuce an kawo mata kayan mata na mussaman daga Kano na Bojuwa herbals 08032773332. Ita ce ma ta dumama mata kazar da ta iso da sanyinta tunda idan wani garin za'a tura sai an yi freezing dinta ta zama kankara sosai gudun kada ta lalace ko ta yi tsami. Haka na matsi duk ta kammala amfani da su da taimakon Alti da take tafasa mata., Sanyi flusher kuwa tun dadewa aka kawo ta sh na sati biyu. Amma duk wannan gyaran da take yi bata ga tana zuwa wajen miji ba. Shiyasa yake yini da kwana yana zarya tsakanin samansa da na Bilki wanda Alti take jin kunyar hakan k'warai da gaske. Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 16:00] Cikin rarrashi da girmamawa ta yiwa Bilki magana da ta ga wayar da ta amsa don tasan ba mai k'iranta a daren sai shi. "Mahmah gaskiya fishin ya isa indai ba so kike na bar miki gidan ba. Yini yake yi yana son ya faranta miki, magana d'aya tak idan kika yi masa kamar an masa bushara da gidan aljanna don zumudi amma sai tumbatsa kike sake yi kullum. Idan fa kika koya masa jurewa fishinki ke ce a ciki. Haka nan irinsu Alhaji fa da kud'i da ilimi ya zauna musu har ofis dinsu ake kai musu mata da suka kai mata. So kike sai ya fad'a tarkon shaidan ne. Haba abin ya yi yawa fa gaskiyar magana. Ki tashi ki sake wanka ki tafi dakin mijinki." Da rawar murya ta ce "Allah Alti nima ina son na huce amma gaskiya ba zan je d'akinsa irin zuwan da kike nufi ba, kowacce kusurwa fa hotonsa da na matarsa ce. Ya je na barwa hoton shi. Kuma fa abu kad'an sau ya ce ita ba haka take yi masa ba, ita mai biyyaya ce" . Ta fara kuka sosai. Alti ta yi sakare tana mamakin Kishin da take ganinsa har a idanuwanta. Wanda ita kam bata ga ta yi kishin Hawwah irin haka ba. A fili ta ce "Tirk'ashi. To ban da abinki Mahma ba sai ki fad'a masa a hankali cewar ba kya so ya daina ba, sannan da kin iya AI da tuni an cire hotunan daga dakin ya dawo da su dakin y'ay'anta". Ta girgiza kai ta ce "Da Dai yana sona ne zai yi hakan, nima ai mun yi hotunan da suka fi nata kyau ma amma bai girke su ba , saboda baya sona". Hawaye ya sake k'wace mata. Alti ta numfasa tare da fad'in "ko makaho ya zauna da ku yasan yana sonki mana, ki yi hak'uri, ki kwantar da hankalinki da sannu za ki mayar da shi irin yadda kike son ya zama. Amma wannan fishin da kauracewar da kike yi masa nisanta kanki kike yi a zuciyarsa fa".
Daidai lokacin k'iran ya sake shigowa bata amsa ba suka ji an yi knocking k'ofar sau d'aya. Kan dole ta bawa Alti yaron ta d'auki hijab ta saka sannan ta fita. A bakin k'ofar ta gan shi. Ya saka hannu ya ruko nata hannun. Bai ce komai ba, itama bata ce komai ba, tiryan tiryan har samansa. A falo ta turje ta ce "Bari na hado maka shayin". Ya girgiza kai tare da fad'in "Ke nake bukata ba shayi ba, tunda ke ba kya gane al'amura sai an bayyana miki". Ta bata fuska ta ce " To zo mu je wajena". Da hanzari ya ce "Alti ta nan ga yara nan kin dawo da su kwana wajen ki, shine nima zan je cikinsu na kwanta?" "D'akina guda nawa ne?" Ta tambaye shi idonta a cikin nasa. Ya juyar da kai ya ce "Ina ce d'aya d'akin su Amal ke kwana a ciki?" Ta ce "To d'ayan fa na kusa da shi?" Kaitsaye ya ce "Amma dai kinsan zasu iya jina tunda bana iya kama bakina idan ina tare da ke ko?" Ta ce "Sai ka fara rikewa ko na samo salatif na manne maka shi". Ya zuba mata ido baya son ya tunzura tunda a matse yake. Kan dole ya kwantar da kansa cikin rarrashi ya ce "Tunda fa kika zo gidan nan sau uku tak kika kwana mini kullum ni nake bin ki. Tunda yanzu gun na ki da mutane ya kamata ki mutunta ni ki dinga zuwa mini, ta ya ya zan yi ta jele a gaban yara da masu aiki fisabidillahi fa Maigado?" Ta cuna baki tare da juyar da fuska gefe. Ta kasa bude baki ta ce masa hotunan matarsa ne ba zasu bari ta iya kwna ba. Ganin tana tsaye ba alamun zata yi masa yadda yake so ya sanyaa shi fad'in"Shikenan je ki abinki, tunda ba son yi kike yi ba. Idan na matsa ma b'acin rai zan tarar, je ki kawai Allah ya bani ladan hakuri. ". A sanyaye ta juya ta bar shi. Amma ta kasa shiga dakinta. Tunda ta sauko tana zaune a falo har aka aka fara kirayekirayen sallar asuba. Tana zaune ya zo ya wuce ta ya yi k'asa dan zuwa masallaci. Jikinta ya sake sanyi don ta ga ya koma Yaya Asad ba Baban Bilkisu ba. Da ƙyar ta ja jikinta ta shiga dakin. Alti ta dinga yi mata sannu. Wanda kunya ta dabaibaye ta. Bayi ta fad'a ta doro alwallah. Bayan sun gaisa Alti ta kalle ta ta ce "Basu su sha sai ki kwanta ki yi barci ki huta". Ita dai ba baki don gabad'aya wani iri take jinta. Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 16:02] * Karfe shida na asuba jirgin da Baba da ahalinsa suke ciki ya sauka a filin saukar jirage na Nmadi Azikiwe na birinin tarayyar Abuja. Tare da Dr Sulaiman. Bai sha wahalar sahalewar hukumar asibitin ba tunda dama tun watan jiya ya mik'a takardar neman izinin zai ke gida. An ba shi watanni biyu.
Yaya Asad da tawagarsa suka zo ɗaukansu, don suna idar da sallar asuba suka nufi airport din. Motocin da suke biye da motar da yake ciki guda uku. Mamaki ya kashe oga Asad da ya ga Sulaiman rike da Baba suna tafiya a hankali yayin da Faruku yake binsu a baya da k'aramar jakar Baba a hannunsa. A kan dole Sulaiman ya shiga tsaleliyar motar oga Asad da ya zo a ciki don d'aukar Baba da da Momi. Yayin da Abida da Faruku suka shiga d'ayar. Mutanen da suke airport suna kallon y'an gatan tsofaffin da aka zo d'aukarsu in comboy. Bayan haka yadda yan snada suke sarasu musu abin sha'awa ne k'warai da gaske. Oga Asad da shi yake tuka motar da kansa. Ya kasa hak'uri ya ce "Baba a ina kuka ga wnanan yaron?" Baba da yake fama da mura ya ce "A Saudi ikon ai ikon ALLAH yafi ga hakan. Addu'armu ta karbu sai ga shi kamar jifa Abida ta gan shi, da yake nemansa take yi, sai ta yi jarumtar rike mini shi da ai so ya yi ya tsere". Momi ta ce "Ba tserewa fa zai yi ba Alhaji! Kaucewa rik'on da Abida ta yi masa yake yi". Daga Baba har oga Asad suka kece da dariya yayin da Sulaiman ya matse. Bai bude baki ya gaida yayan nasu ba. Shi ma kuma oga Asad bai ce masa kanzil ba. Har suka isa gida Sulaiman kala kanzil bai ce ba. Daman Baba Babba bai faɗa ma kowa sun ga Sulaiman ba, ya kuma ce Faruku da Abida kada su faɗawa kowa, su bari kawai sai dai a ga Sulaiman ɗin kawai. Karfe takwas da rabi daidai a falon gidan ta yi musu. Oga Asad ya tunzura iya tunzura ganin ga shi ga Sulaiman amma uffan bai ce masa ba yana jira ne shi ya gaishe shi kenan? Alhalin har magana ya yi masa yana tambayar a ina aka gan shi. Bayan duk wulakancin nan da ya gwada musu shine zai sake dawowa da mugun kulli a ransa? Cabdi jam aikuwa sai dai Baba ya yi hak'uri ba zai dauki wannan rainin da iyashegen da yake ga ni a idanuwan Sulaiman ba. Ya rasa me ya yiwa y'ay'an mami gabad'ayansu sun washe shi tamkar shi ya kashe ta ko kuma rashin zuwa yi musu ta'aziya an fad'a musu ba za'a yi mata Rahma a dalilin bai je ba. Haba ya gaji, ko Bilki ma ya yi imanin ba iya abin da ya yi mata ya sanya ta bijire masa haka ba. Gabad'aya ta taurare babu wata alama na tana sonsa ya yi imanin maganganu take ji iri iri akansa a bakin makusantanta. Shi yanzu ma ga ni yake gidan mijinta take son komawa. Ya gama gasgata k'arfin k'addara da rabon haihuwar twins ya sanaya ya kafe ya matsa sai da ya aure ta, ban da haka mai ma zai saka ya kafe akan ta irin haka ne? Tunda ya san ba sonsa take yi ba, alfarmar Faruku ya shiga. Cikin mintina k'alilan ma'aikatan gidan suka baibaiyeshi da cima iri iri tare da yi musu barka da zuwa cikin farinciki da girmamawa. Abida ta shige daki tana son ta faɗawa Bilki kiranyensu ya karɓu sai kuma ta cije ta hak'ura tunda Baba ya ce kada a faɗawa kowa. Sai da ta yi wanka ta fece da kwalliyar da aka jima ba'a ga ta yi irinta ba, ban da sunan twins da ta taya Bilki yin kwalliya. Amma ko sunan junior haka ta yi shi babu kwalliya babu kuzari. Sai da ta daure fuska iya daurewa sannan ta fita falon inda ake karyawa. Zuciyar Sulaiman ta buga da ganinta k'amshinta ya kai masa caffa. Ya yi iya kokarinsa wajen kin dagowa amma daga k'asa idanuwansa na kanta. Ta zauna kusa da Baba ta fara serving kanta. Baba ya ce "Abida har kin yi wanka? Irin wannan gayu haka Sulaiman aka yiwa ko kuwa har za'a tafi dauko junior ne?" Nan da nan ta samu mafita don kuwa ba wacce take son ga ni irin Bilki. "Baba zan je na ga Bilki tunda mun barta babu lafiya daga nan sai na d'auko shi". Baba ya murmusa ya ce "To ki yi mata albishir wataƙila ma nasan ta biyo ki". Save Restricted Content Bot, [Oct 15, 2025 at 16:03] Nan da nan oga Asad ya mik'e ya yiwa Baba sallama akan zai je gida sai yamma zai dawo. A zuciyar Baba bai ji dad'in rashin gaisarwa da basu yi ba. Yasan dai oga Asad ba zai taba yarda ya gaisar da Sulaiman ba. Ai ko Usman da ya girmi Sulaiman da watanni uku suka taso tare ba zai yarda ya fara gaishe Shi ba bare Asad. Har Ila yau Baban sai ya tsinci kansa da jin tsoron ya ce da Sulaiman ya bai gaisa da yayansa ba? A ran Baba ya dinga jinjina wannan zamanin da ya riske Shi mai wuyar sha'ani yadda kirikiri ake kin tsoron y'ay'a. Da ace zai iya canja zuciyar Asad ta zama irin tasa da ya yi, to ikon sarrafa zuciya ba'a hannunsa take ba. Halin Baba K'arami ne da shi, Duk juyin da aka yi kuwa ba zai risinawa na k'asansa ba mussaman idan shima yana ganin akan gaskiya yake. Gabad'aya Baba ya ji ya takura don kuwa rashin jituwar Asad da Sulaiman tana nufin al'amura masu yawa marasa dad'i. Dukkansu kowa zai samu k'anne magoya baya, gyaruwar zumnta a tsakaninsu zai yi wahalar gaske matuk'ar wadannan biyun da kowa yake babba basu jitu ba. . *Surayya Gwaram* *Wannan littafin na kudine* *Pay 1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank*. 08032773332. *Don samun damar karantawa cikin aminci a telegram*.
*Teemah data service mtn monthly* *1gb @550* *2gb @950* *3gb @1450* *5gb @1700* *Dm 08112392177* *Call 8037026306 Fatima Musa Ibrahim opay*
*For your beautiful kids wears:tees,shorts,trousers,dresses,kids towels, perfumes,body mist contact 08067239846*
Makullin motarsa ya bawa Michel akan ya ja shi don gabadaya ya rasa nutsuwarsa ai kuwa la shakka sai ya lallasa Sulaiman kafin ya kiyaye Shi. Shi zai ga ni ya kalle shi ya watsar? A fili ya ce "Wai me na yi musu ne?". Ba sukuni Bilki ta ga ya dawo ya wuce wajensa ko ganin twins da ya zame masa k'aida kafin ya k'arasa wajensa bai yi ba. Haka ya wuce ta tana falo bai ce mata kanzil ba. Ta sake jin babu dad'i don a yanzu shima shariyar ya d'auka. Ya daina kula ta ko kad'an. Zai dai je ya ga y'ay'ansa, ya tambayi Alti lafiyarsu. Ko so yake a kai masa su sai dai ya saka Hafcy ko Bilkisu su kai masa. Idan kuwa suna school Aysha yake sawa ta dauko su. Amma tsakaninsa da Bilki ido ne. Ko ta gaishe shi a fizge ko a ciki ciki yake amsawa. Alti kuma ta saka ta a gaba da fad'in ai hakan ya yi mata kyau. Ita kam bata taɓa zaton zata yi haka ba. Dazu ma Alti har cewa ta yi idan ta yi sanadin da aurenta ya mutu Wallahi ba zata bita gidan baba Babba ta zauna ba. Ita tana da kunya sai dai ta tafi gidan gajiyyayu. Daga haka kuma ta dinga yi mata kuka tamkar dai mutuwa aka rafka. Bilki dai ta rasa inda zata tsoma ranta ta ji sanyi. Tsakaninta da Allah oga Asad ne ka cin zalinta ta hanyar son kansa da yawa. Amma yanzu ya fitittike ya dauki gaba mai tsananin gaske don kawai ta k'i zuwa d'akinsa kwana. To yanzu ya zata yi masa kenan? Ta bi shi da ido tana ganin yadda yake tafiya gaf gaf tamkar zai kifa. K'afar bene ma bibbiyu ya dinga hadawa. Sai da ya b'acewa ganinta sannan ta numfasa tabbas ta takura da fishinsa sai dai tana nan a kan ra'ayinta ba zata je d'akinsa da nufin wata mu'amala ba matuƙar da waɗannan hotunan. Sai dai Alti ta yi hak'uri kawai.
Ba jimawa soaai da dawowarsa Abida ta iso. Kusan a guje ta hawo saman tamkar yadda Farha take yi. Bilki ta zabura tana fad'in "Lafiyarki kuwa?" Suka rungume juna, kafin Abida ta ce "Allah yasa Dady bai shigo ya riga ni fad'a miki ba". Bilki ta ce "Ya shigo a gaggauce ya hau sama ko ta kaina bai bi ba. Gaba ya k'ulla da ni haka siddan". Abida ta rausayar da kai ta ce "Kina masa taurin kai ne, shi kuma haka yake da tauri tamkar goruba, amma zan samo mana mafita don na lura ba abin da yake tasiri akan rijalu irin a yi ta buga musu addu'a a sujjuda idan ba haka ba, a tsaye zamu mutu da bak'incikinsu! Bilki ta jinjina kai tare da fad'in "To Abida". Daga haka Abida ta ce "Jarida ce zan siyar miki da farashin da ban taba siyar da ita ba". Bilki ta fad'ada murmushi tare da fad'in "Idan jaridar d'auke take da kiranyenmu ya ci Malam Sule to tabbas zan siye ta da k'ololuwar tsada k'anwar Bilki". Abida ta ce "Kin riga kin sa ni Idan na fesa miki labari sai kin biya kudin dan haka Ki shirya". Bilki ta ce "fad'a mini kawai, Ni kuwa ba zan yi k'wangen Baki farashi Mai daraja ba tunda har yanzu baki gaji da tara dukiya a dalilin jaridarki ba." "Da murmushi sosai ta ce "To Dai kiranyenmu ya kama jikan Malam Uzairu sai muka yi kicibis a Saudi". Bilki ta gigice ta kasa magana. Da kyae6ta daidaita tunaninta ya ce "Kina nufin wai kun gan shi ra'ayil ayni?" Da k'arfin guiwa Abida ta ce "Sosai fa, na fad'a miki ya dinga guje guje Sai da Allah ya Bani sa'a na yi ram da shi. Ba yadda bai yi ya kubucewa rik'on da na yi masa ba ya kasa k'wacewa hae sai da na damka shi a hannun Yaya Faruku. Yaya Faruku kuwa ya tisa shi har gaban Baba. Baba kuwa ya taho da shi yanzu haka na barsu a falo suna cin abinci." Bilki ta sake kidimewa ta ce "Alhamdulillahi lallai kuwa na siya wannan jaridar don shine labari Mafi dad'i a cikin dukkan labaran jaridarki Abida!. Amma Baban Bilkisu bai san ya dawo ba ko?" "Ya sani mana ba da shi aka je d'auko mu ba, Yaya Sulaiman din ma tare da bada momi motar Dady din suka shiga". Jikin Bilki ya yi sanyi wato fishinsa har ya yi tsananin da ba zai fad'a mata wnanan daddan labarin ba? Lallai oga Asad ya fita iya gaba. A sanyaye ta ce "Bai fad'a mini ba ba fa Abida ". Abida ta ce "Hmm haka yake yiwa wacccar matar fa, ranar da na ji tana faɗawa shegiyar Surayya nan wai ya fi k'arfinta a shimfida, a ranar na ji tana kukan idan ta nemi bijire masa kuma ko ta nuna ta gaji sai ya yi fiye da sati biyu yana yi mata fishi mai tsananin gaske. Yanzu mu hadu mu sake had'a kanmu Bilki. Dama ni da ke bata b'aci kada ki kalle ni a k'anwar miji, nima ba zan miki kallon haka ba. Kawai mu taimaki kanmu, mu hadu mu wasko kan wadannan tsayayyun mazajen da Allah ya had'a mu da su. Idan ba haka ba zamu sha wuya a hannunsu. Yanzu mu je ki gaishe shi, sai ki faɗawa Baba ni na yafe masa rataye nin da ya yi babu waiwaiye, kawai ya ba shi Umarni ya d'auke ni salin alin mu tafi gidanmu. Idan kika yi haka to ni duk sababinsa indai ina gidansa zan jure, ina da wuridi iri iri da zamu dinga yi har mu raunana zukatansu." Dariya ta k'wacewa Bilki mai tsananin gaske. Yayin da Abida ta tunzura ta ce "To Bari na tafi kowa ya yi ta kansa tunda na ga alamun halin da kike ciki bai yi tsananin da zai hana ki dariya irin haka ba. Ni kuwa idan ba gani na, na yi a d'akin jikan Malam Uzairu ba, ban ga ta dariya ba. Kuma Wallahi idan ba ki taimake ni ba, ki tabbatar nan gaba ganina sai ya yi miki wahalar gaske bare ki nemi shawarar yadda zaki yi da wannan murdadden ba". Na da nan Bilki ta gintse dariyarta "To Abida, zan iya k'ok'arina! Ta fadi hakan da dukkan zuciyarta. Don a yadda take ganin oga Asad a kwanakin nan yana iya zabga mata mari don gabad'aya ya murd'e fiye da azancinta. Ta ciro zoben hannunta guda daya wanda na gold ne ta mikawa Abida tare da fad'in da wannan na sayi jaridarki". Abida ta karɓa ta ce "Lallai kin ji dad'in labarin nan na gode". Ta mak'ala shi a hannunta. Ya mike ta ce "Zamu tafi tare ne ko sai anjima za ki zo?" Bilki ta ce "Bari Alti su dawo na aikesu kasuwa tare direba ta tafi da junior. Kada su dawo bai ganni ba". Abida ta kalli agogo ta ga shabiyun rana ta gota ta ce "Sun jima da tafiya ne?" Bilki ta daga kai tabbacin sun jima din". Daidai lokacin kuma suka ji ana bude musu gate. Junior ya fara haurowa yana fad'in Mahmah Alti ta siya mini ball". Hannunsa d'auke da madaidaiciyar ball mai kyau. Ya yi turus ganin Abida sai kuma ya kwasa a guje yana fad'in "oyoyo Ammi". Ta dago shi tana fad'in "oyoyo my boy, ina su Yaya Noor da Yaya Farha?" "Suna school. Ammi nima a saka ni a school dinsu". Ta ce "To mu je ka faɗawa dadynka ya dawo". Ya zabura ya ce "Na pics din wayarki da kike fad'a mini zai dawo anytime?" Ta gyada kai ta ce "Shi fa kuma ya dawo junior ". Ya falfala d'akin Bilki ya dauko jakar kayansa ya kalli Bilki ya ce Mahmah sai wata rana". Haka kawai zuciyarta ta karye don kuwa irin haka Faruk ya ce mata a ranar da zata bar Katsina a harabar makarantarsu. Ga shi yaron kama yake yi da Farukun. Daidai lokacin Alti ta shigo falin hannunta d'auke da leda. Da murmushi take fad'in "Lale da mutanen Saudiiya, yasu Baba, ya kuma ibada?" Fuska a sake Abida ta amsa mata tare da tambayar lafiyar tagwaye. Daidai lokacin ta mik'e ta nufi d'akin Bilki don ta ga yaran da bata tambaye su ba sai yanzu. Bilki ta bita yayin da Alti ta had'a ruwa da lemo ta soya samosa ta kaiwa Abida. Bilki ta kalli junior "Zo mu je ka yiwa Dady sallama". Ya bita suka je. A zaune suka same shi ya rik'e kansa da hannuwansa. A sanyaye ta yi sallama ya amsa a ciki. Junior ya ísa kusa da shi ya yi saluting d'insa don sosia junior yake son ya yi masa haka. Oga Asad ya ya sauke hannunsa ya ce "Magajin Dady ya kake?" A nutse junior ya ce "Dady Zan tafi ammi ta ce "Dadyna ya zo". Oga Asad ya ce "To ka gaida Momi ya mik'a hannu ya janyo office bag d'insa ya fito da bandit din Yan 500 ya ce "Ga shi ka kaiwa a5mmi ka ce ta kaika ka yi shopping tunda har zaka tafi baku je shopping din ba." Ya karɓa da hannu biyu, ya mikawa Bilki shi Kuma ya kame ya yi gaisuwa gidan tsaro Wanda oga Asad dariyar da bai shirya ba ta subuce masa don yaron tamkar Wanda ake training d'insa. Kan dole ya mike Shima ya yi saluting d'insa tare da fad'in God bless you future police." "Thank you oga." Ya furta tamkar ba dan shekaru uku ba. Ya juya ga Bilki ya karbi kudinsa ya fice a guje. Bilki ta tsinci kanta da fargabar yi mass magana don ya tsare gida iya tserewa. Jikinta ya sake mutuwa wato Duk faricincikin da ake ciki na ganin Yaya Sulaiman ba zai saka ya huce Har ya nemi yi Mata albishir ba daga nan su shirya kansu ba. Kan dole ta ce "Zan bi Abida na Ga yaya Sulaiman ta ce ya dawo ". Ya yi bakam tamkar dai ba da Shi take ba. Ta sake maimatawa. Cikin nutsuwa ya zuba mata idanuwansa ya ce "Ba za ki je ba, daga nan har kwanakin wata kada ki sake ki ce mini za ki fita". Daga haka ya mik'e ya shige cikin d'akinsa. Idanuwanta ya cika da k'walla. Ita tunda ta yi aure ba'a taba hanata fita unguwa ba. Ko wani Gari zata je idan ya ce ba yanzu Idan ta nuna lallai tana son zuwa baya zafafawa, bare kuma Idan a cikin gari ne d'aukar mota take yi kawai ta je ta yi uzzirinya baya tambayar ba'asi. Babbr damuwar Bilki yadda ya fitittike ya koma mata wanccan azabben Asad din mai dealing din kannensa with iron hand. Yayin da shi kuma haushinta da na y'anuwanta da suka tsangwame Shi haka siddan ne ya tayar masa da hankali. Wai Shi Sulaiman zai ga ni a gaban Baba amma ya kasa bude baki ya yi masa magana. To Idan Baba na jin tsoron kada ace ya yi son kai tabbas shi baya tsoron maganar mutane sai ya ci masa mutunci ya tuna masa lokutan baya da yake saka su kneel down a rana ko frog jamb shi da Usman. Sannan idan Hamida bata kiyaye Shi ba Sai ya taka har gidanta ya ci Mata mutunci tunda ya gama nazarinsa ita da Sulaiman sune kan gaba wajen gaba da shi to duk zai ci kazar ubansu ya danna ashariya a fili. Wato rashin zuwa su ha twins ba fa k'aramin soya k'irjinsa yake masa ba, wanda hakan ne ya sanya ya sake tsananta fishinsa da Bilki tunda ya tafi a fahimtar zugata suke yi ta dinga wulakanta shi wanda ta yi kad'an. Ya kuma gasgata da a wani gidan ta haifi yaran ba a gidansa ba zasu so. Abin da Sulaiman ya yi masa a yanzu kuma ya sake gigita Shi don Ki yake tamkar ya yi ta zunduma ihu da iyakacin k'arfinsa. A kasalance ta koma wajen Abida. Murya na rawa ta ce "Ya hana ni fita Abida. Ko za ki masa magana?" A zabure ta ce "Ban isa na yiwa Dady magana a yanzu ba, ai tunda na ga ya fito a gigice nasan a birkice yake haka nan tunda Bai fad'a miki dawowar Dr Sule ba nasan to kin yi saken da zai fara yi miki fitinannen fishinsa mai cunkushe mak'oshi." Hawaye ke zarya a fuskarta wai duka aure haka yake zuwa da k'alubale. Shi ya yi mata laifi, sannan ya girke hotunan matacciya a d'akinsa da falonsa bayan haka motsi kad'an ya ce ta fita Kaza, Shai ba haka aka Saba masa, Duk bai yi tunanin yadda take jin ciwo a ranta ba,sl Sai Kuma ya gindaya gaba Mai tsauri irin haka a tsakaninsu? Ace Sulaiman ya dawo amma ya kasa fad'a mata? Ta ce zata je ta gan shi ya ce ba zata ba don gadara da son ya musguna Mata. Yayin da Abida ta sake tsotaya da lamarin maza wato dama har yanzu ana hana mace zuwa wajen da aka san mai muhimmanci ne a wajenta. Nan Duniya Sulaiman na cikin abubuwan da suke da daraja hadi da muhimmanci a duniyar Bilki. Ya yi shekaru kusan hud'u ba'a san inda yake ba, ya dawo kuma a hanata zuwa ta gan shi? Ita da kanta Abida al'amarin ya girgizata tana auna tamkar itace ta ce zata je ganin oga Asad bayan an shafe shekaru ba'a san inda yake ba ace kuma miji ya ce ba zata ba. "Tirk'ashi! Ta fad'a a bayyane. Ganin Bilki na kuka sai ta yi maza ta had'iye kaduwar da ta shiga ta ce "Share hawayenki, idan ya yarda zan rakito shi mu zo ya ga twins." Cikin kuka Bilki ta ce idan bai yarda ba fa?" Abida ta ce "Zan saka Baba ya yiwa Dady magana ya bari ki zo." Ta goge hawaye ta ce "To". Amma k'asan zuciyarta ya yi mata nauyi tare da jin k'ololuwar gajiya da zaman gidan oga Asad kisan mummuke kawai yake yi mata. Haka Abida ta tafi da junior. Sai da Bilki ta shanye kukanta sannan ta fad'awa Alti Yaya Sulaiman ya dawo. Alti murna sosia ta dinga tare da adduar Allah yasa ya dawo kenan. Bilki ko jikinta ya sake sanyaya don kuwa Idan ba sa'a ba Yaya Sulaiman ya yiwa oga Asad wulakanci shiyasa ya dawo a firgice bai kuma fad'a mata ya dawo ba, sannan ya hanata zuwa wajensa. A ranta kuwa ta san rikice ne zai sake tashi sai dai Allah ya shiga al'amarin kawai. .. Sulaiman ganin Abida ta fita ya sanya ya tausasa murya ya ce "Baba ina son na wuce yau. Amma zan dawo na ji sharadina da zaka gindaya mini satin sama". Mamaki ya tuke Baba a zaune Ya nisa ya ce "Ina zaka ke Sulaiman" Kansa a k'asa ya ce "Zan je Katsina Baba." Baba ya girgiza kai ya ce "Za ka je amma ba yanzu ba".