Kenza eBookz

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 23

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 23

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 23: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 23. *Lame.Ng Skin Beauty and wellness* *Duk masu son sanin…

4,372 words

*Lame.Ng Skin Beauty and wellness* *Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.* *07036662633*

*Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253*

Ya yi shiru ya ce "To Baba zan dan shiga cikin gari gobe zan dawo in sha Allah". Ran Baba ya yi k'ololuwar b'aci ba zato ya suri robar ruwan Eva da ba'a bude ba, rab'a ta lullube robar saboda sanyin ruwan. Da dukkan k'arfinsa ya kantaraqa Sulaiman a gadon bayansa. Babu zaton Sulaiman ya ji saukar dukan ya karade jikinsa a gigice ya mik'e yana waiwaiye tare da tunanin oga Asad bai tafi ba ne, don bai taba tunanin Baba ne ya kwada masa abu haka ba. Don kuwa suna k'ananu ma bai tana dukansu ba. Murya ba amo Baba ya ce "Ni ne na kwada maka ba kowa ba, matso nan". Sulaiman ya tsugunna nesa da shi don gabadaya ya rikice. Muryar Baba na rawa ya ce "Matso nan Wallahi Sai na Ƙara maka." Da sauri Sulaiman ya rarrafa gaban Baban kansa a kasa don ya kubutar da shi daga yin kaffara. Baba kuwa ya cire tausayi da rauni ya shiga kantara masa jarkar nan har a kansa ya dinga maka masa. Momi ta fito ganin Baba na dukan Sulaiman da iyakacin k'arfinsa l, shi kuma yana durk'ushe yana dan karewa da hannuwansa idan za'a kwada masa a kansa. Da hanzari ta iso ta janye shi tana fad'in "Yi hakuri, ayi masa nasiha dai ai ya wuce duka Alhaji". Hawaye na zuba a idon Baba ya ce "Da yake idan mutum ba shi da mahaifa sai gata ya yi masa yawa, sannan babu mai iko da shi ko?" Momi ta fashe da kuka tana fad'in "A a ba haka bane Alhaji". Yayin da Sulaiman yake durk'ushe hawaye na tsere akan fuskarsa wanda na tausayin Baba ne, ba na dukan da ake yi masa mai shiga kansa ba. Da rawar murya baba ya ce "Duk wulakancin da wannan yaron ya yi mini na jure na karbe shi, shine ya samu kuzarin fad'a mini zai tafi ya samu masauki saboda nan ba gidan ubansa bane! Da ace ubanka na da rai da ka ga yadda zan saka a zane mini kai, amma tunda babu shi, sai na yi maka iya yadda zan iya don wataƙila idan na saka guda cikin yayunka su lallasa mini kai, za ka yi zaton na saka ya'yana sun ci zarafinka tunda ni na haifesu.! Hankalin Momi ya yi tashin gauron zabi a dalilin yadda ta ga Baba ya shiga matsanancin b'acin rai. Ta dinga ba shi hak'uri tare da kokarin kwantar masa da hankali. Yayin da Sulaiman yake kuka marar sauti. Daidai lokacin Abida da junior suka dawo. A guje ya shigo sai dai ya yi turis ganin Momi da Baba suna kuka. A sanyaye ya ce "Menene?" Kafin su ba shi amsa Abida ta shigo. Ganin suna kuka bai bata mamaki ba. Sai kawai ta durk'use kusa da Sulaiman da kansa ke k'asa. Ta tausasa harshe ta ce "Ka yi hak'uri Baba! Dan Allah dan Annabi ka yafe mana ka cire mu a cikin sahun waɗanda suke tayar maka da hankali. Ni dai na bi Allah na bika, na yi kuskuren bijirewa umarnin da ka ba ni, akan na koma d'akina, yanzu kuwa tunda Allah ya sa ya dawo to zan tabbatar na gyara kuskuren da na yi, zan bi umarninka, zan bi shi duk inda za shi zan kuma zauna lafiya da shi". Baba ya ce "Ke ma ban isa da ke ba, bare shi da yanzu ya tabbatar mini ni ba ubansa ba ne, alhalin ubansa ma ni ubansa ne". Sulaiman ya dago da fuskarsa da ta yi face face da hawaye ya ce "Wallahi Baba ba hakan nake nufi ba". Dak'uwa Baba ya yi masa tare da fad'in ka ci ubanka! Me ka ke nufi to? Matso nan".

Momi ta ce "A a Alhaji ai ya daku bar shi haka dan Allah! Yayin da Sulaiman ya yi k'asa da kansa yana fad'in "Ka yi hakuri Baba dan Allah". Junior ya yi tsuru tsuru. Abida ta yafito shi tare da fad'in "come to Dady junior". Ba kuzari ya isa kusa da ita ya tsaya a dalilin ya ga kan Sulaiman a k'asa yana kuka yana goge fuska da hankici. Abida ta zaunar da shi a jinyarta. A ladabce ta ce "Baba ina sake baka hak'uri, sannan Allah shine shaidar na yafewa Dr yaya Sule tafiya da ya yi ya rataye ni. Don haka ka daure ka yafe mana ka saka mana albarka komai ya wuce. Kawai ya d'auke mu yi tafiyarmu". Kansa na k'asa ya ce "Baba ka fad'a mata ba da ita kake magana ba, ta daina saka baki idan kana mini fad'a ". Momi ta ce "ina zata yi shiru kuwa". Abida ta yi maza ta kame bakinta. Baba ya ce "Kada ki sake bude baki ki yi magana, tashi ki shiga ciki ma".

*Contact Bojuwa herbs@ 08032773332 what'sapp only* *For all your kayan mata gangariya* *Bridal package* *Maijego package* *Uwargida package* *Bazawara package* *Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego* *Ciccibin garari* *Tsumin saiwowi* *Hakkkn daka emergency* *Gumbar ridi* *Gumbar saiwowi*. Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:02] *Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855* *Surayya Ibrahim Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wadannan lambobin* # 08032773332# # 09069067488#

*DINGISHIN KWADO 4*

*BY* *SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR* *HALIN YAU* *SABO DA KAZA* *BAK'AR TA'ADA*

Ta tashi a sanyaye. Baba ya kalli Sulaiman ya ce "Kana sane ai ban huce da kai ba, amma tunda mukaa sauka kake ta bata mini rai. Ga ka, ga yayanku ka kasa bude baki ka yi masa magana? Wanne irin al'amarine haka Sulaiman? Kullum addu'ata Allah ya bayyana mini kai, ta dalilinka zumunci zai daidaita sai kuma ka dawo da dabi'un jahilai?" "Ka yi hakuri Baba". Sulaiman ya fad'a a hankali. Baban ya nisa ya ce "Ya kamata kasan ka girma kuma dole ka yi hak'uri da sha'anin rayuwar nan mussaman a al'amarin zumunta. Yanzu ka kalli yaro an haifa maka har ya girma baka san shi ba, bai sanka ba, wanne irin Bakar Ta'ada haka ka yi?" Ya kasa magana wato cikin Abida bai zube ba kenan?" Baba ya zarce da fad'in zan "hak'ura na huce ne idan ka je ka tattaro mini y'anuwanka ka kawo mini su gabana don tunda ka tafi idan ka d'auke Bilkisu. Ansari da Saddiqa kad'ai na sanya a idanuwana suma zan iya lissafa maka.". Murya ba amo Sulaiman ya ce "Da ikon Allah zan kawo su Baba amma ka dubi Allah duk uzziri da alfarmar da zamu nema ka yi mana". Baba ya ce "Zan muku Sulaiman indai kun yarda ni din ubanku ne to menene ba zan yi muku ba?" Sai kuma kuka ya k'wace masa. Sosai hankalin Sulaiman ya yi tashin gauron zabi. Ya dinga bawa Baba hak'uri cikin rauni. Yanzu ka je d'aki ka yi wanka, Idan muka yi sallah sai mu dan kwnaata kafin laasar mu dan huta."

Kafin Sulaiman ya yi magana Abida ta fito daga dakin mami hannunta d'auke da mukullin guest room, da confidence ta zo ta d'auki jakar Sulaiman ta rataya, ta ja trolley yayin da junior yake rik'e da tsintsiya da parker da detergents. Sulaiman ya ce "Ajiye mini ina da hannu". Abida ta d'auki salati mai tsananin gaske ta ce "Yaya Sule yanzu duk nasiha da Baba ya yi maka baka risina ba, ina jiye maka ya sake tunzura to ni dai kam darajar Baba na yafe komai. ba kuma zan sake yarda da fishinsa mai yawa ba a kaina ba." Ta kalli Baba ta ce "ka shaida na huce na yafe masa, ina kuma neman shiri saboda na riga na gaji da wannan danbarwar". Sulaiman ya yi shiru a ransa kuma mamakinta yake ba zata taɓa canjawa gabad'aya ba. Wato ta nan zata bullo masa? Kwatsam ya ji Baba yana saka mata albarka har da fadin tabbatuwar aurensu na cikin abubuwan da suke da muhimmanci a zuciyarsa, dan haka ta cigaba da juriya in sha Allah zata yi albarka, don yiwa miji biyayya da hak'uri da shi, alamun mace na kan turba madaidaiciyane. Gabad'aya Sulaiman ya ji duk wani azancinsa ya k'wace Abida ta binne shi da ransa. Baba kuma ya tula masa k'asa cikin girma. Yana ga ni ta fice da jakunkunansa wanda ya yi amannar sai ta bude masa kafin ya je d'akin tunda haka dabiarta take. Ya bi yaron da bai bar komai na halittarsa ba da ido da ya bita a baya da kaya a hannunsa yana ja. Cikin lokaci k'alilan ta karkade Dakin da kanta ta share, ta shi ga bandakin ta wanke toilet din da k'ura ce kawai a cikinsa. Sannan ta koma ta dauko bedsheet dinta wankakke goggage da blanket ta hado kuma ruwan moping. Baba yana ganin yadda take ta safa da marwa cikin rawar jiki da falli. A ransa dariya ne fal akan lamarin Abida sai dai ba ya so ya yi a gaban Sulaiman don ya lura gabad'aya Sulaiman din ya zama wani iri ya kasa katabus. Baba fad'i yake yi a ransa ja'irar yarinya ta ji jiki iya jiki, ta yi laushi tub'us ya kuma gane sulhu take so ko na dolen doliya ne. Mintina biyar suka ga ta shigo da sauri sosai ta yi d'akinta. Zuciyar Sulaiman ta harba ya ce "Baba k'irata na tabbatar ta ɗauko mini wani abu" . Baba ya ce "Haba Sulaiman ai yanzu ta yi hankali ba zata dauki wani abunka dan ta boye ba. " Sulaiman ya yi shiru ba don ya gamsu ba, sai dan ba zai yiwa Baba gardama ba. Amma tabbas ta d'auke masa wani abu.

Ta fito fuska ba walwala hannunta d'auke da burner da kwalbar turaren wuta mai kyau. Ta wuce tana fad'in to na gama gyara maka da kaina Dr yaya Sule ". Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:04] *Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*. *Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*. *Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Sanyi flusher kuwa best seller ne* *Just DM for your order @08033773332*.

Bai amsa ba bare ya motsa. Ganin haka ya sanya Baba mikewa da ƙyar. Sulaiman ya yi maza ya mike ya rik'e shi har zuwa bak'in k'ofar d'akinsa. Sannan ya bar shi Abida ta yi maza ta fice kan dole ya bi bayanta. A harabar hate don ya hango junior na buga ball. Ba dan sadda ya bar k'asar Farukun Bilki ya fi shi shekaru Banda ya ce shine don tsananin kamarsu. Ba tantama dansa ne don ga shi nan sak shi tamkar kakinsa ya yi. Ba ya inkarin jininsa ne amma sai ya yamutsa Abida. Kuma tunda Baba ya yi masa fahimtar tafi ne don bai d'auke shi ubansa ba, to kuwa sai sun gurfana shi da ita a gaban Baba an baje komai a faifai da ya huce duk da dabararta kuwa. Sai tula masa k'asa take cikin dabara. Momi kad'ai ba Baba ba, kunyarta yake ji akan Abida. Dole ya hak'ura amma sai sun sake yinta da wajewa. Ba zai sake d'aukar wulakanci irin wadda ta yi masa ba. Don haka ba zai bata fuska da wuri ba. Suna shiga ta wuce bayi, tuni ta kai masa brush da makilin d'insa da ta ga ni cikin jakarsa Hadi da soso da sabulu. Sai da ta had'a ruwan wanka ta fito tare da fad'in "Dr , Yayana, mijin Abida, kuma Baban junior with dew respect nake sanar maka na had'a maka ruwan wanka, mu je na taimaka na dunduma maka kanka na ga gefen can ya dan kunbura kad'an. Gaskiya na tausaya maka Yaya Sulena ka bugu a hannun Baba". Sai hawaye shar shar a idanuwanta. Ya zuba mata ido yana ganin yadda hawaye ke tsere, hannunta rike da tawul dan k'arami da ya gamsu da gaske take yi dundumen zata yi masa. Ya rasa ma ajin da zai ajiye ta. Ya matse bai ce komai ba, jakarsa ya bude ya fito da tawul da jallabiyar sannan ya ce"kauce Malama! Don ya gama gasgata bai gama karantar halayyarta ba . Ta kuwa yi maza ta kauce din sai dai bata yi shiru ba. "Ba damuwa sai na yi maka dundumen da daddare." Yayin da ya wuce yana ayyana ai yasan duk juyin da zai yi ba zata yarda ta yi fishi ba a yanzu. Ya fito daga wanka sanye da jallabiyar. Sai da ya fesa body spray mai dad'in k'amshi sannan ya kwanta. Ta tausasa harsehe tare da fad'in "Yaya Sule na yi maka irin tausarrr nan da ka ke yi mini idan mun dawo daga asibiti?" Ya yi mata shiru. Ta sake maimaitawa Ya kaurara murya ya ce "A a ". "To yaya Sule bari na cire maka dattin kunne ka ga ma cotton buds din na d'auko, nasan zuwa yanzu datti ya cika maka kunne tunda baka iya cirewa da kanka". Kaitsaye ya ce "To idan kuma a can din ina da matar da take cire mini fa?" Zuciyarta ta buga don tasan wataƙila hakan zai iya kasancewa. Amma ta aro jarumta ta cije ta ce "Tunda yanzu ni ce tare da kai, ka bari na cire maka mana. " "To ba zan bari ba". Ya fad'a a takaice. Ta cuna baki tana kunkuni. Shi kuma ya yi kamar bai ji ba. Can ta nisa ta ce Yaya Sule na yi kewar chest dinka, na zo na kwanta zaka yi hugging ɗina da tausayawa?" Ya kasa ce mata komai don ya ga so take ta shashantar da shi ta rubta shi ya fad'a tarkonta. Daidai lokacin junior ya turo k'ofa ya shigo. Abida ta yi maza ta ce "koma ka yi sallama, ka jira a amsa maka". Ya koma din. Ya dinga knocking tare da fad'in assalamu alaikum cikin muryar yara. Ta amsa masa da fad'in walaika salam shigo Habibina". Sulaiman ya zuba mata ido shi gabad'aya mamakinta yake yi. Jiniyo yhigo ya isa kusa da ita. Ya ce "Ammi dadin nawa bai yi mini irin yadda Dady oga yake yiini ba". Ta murmusa ta ce "Ba shi da lafiya ne. Idan ya warke fiye da Dady zai dinga yi maka." Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:05] Sulaiman daga kwancen ya mik'a masa hannu ya ce "zo mu gaisa." Junior ya isa gare shi ya hau Gadon ya zauna Yana kallonsa. Yayin da Abida take mamakin tsananin kamar da suke yi da juna. Farha da junior da kuma Farukun Bilki ba inda suka bar Bilki da Sulaiman kwabo da kwabo kuwa. A hankali Sulaiman ya ce "ya sunanka?" Da hanzari junior ya ce "Sulaiman Sulaiman. Junior ake ce mini". Ina ne school dinku?" Ya ce "Ba'a sa ni ba, amma ammi ta ce mini zaka saka ni a makarantarsu Yaya Noor da Yaya Farha ". Zuciyarsa ta harba a dalilin suanar Farha da ya ji. Idan kuma har ba mancewa ya yi ba to Noor itace last born din oga Asad. Yasan Bilki na Abuja tunda an fad'a masa ta bar Katsina. Don haka idan makantarsu Noor aka saka Farha ba zai yi mamaki ba. Ya ce "Amminka ce zata saka ka ka ji". Junior ya ce "Amma fa Yaya Noor ta fad'a mini kowa dadynsa ne yake saka shi a school ". Ya nisa ya ce "Hakane ". "To ka ta shi mu je ka saka ni a makarantarsu pls". Sulaiman ya ce "Zamu je amma ba yau ba". Junior ya yi shiru ba dan ya ji dad'i ba. Ya sauka daga gadon ya nufi Abida fuska a kwakkwabe yana son yin kuka. Ta yi maza ta ja shi jikinta ta ce "Shhhh shima baya son kuka irin Baba. Zai saka ka fa, amma kana bude bakinka ka yi kuka to ba zai saka ba." Nan da nan kuwa ya had'iye kukan. Sulaiman ya bisu da ido yana mamakin yadda Abida ta k'ware a tarairayar yaron har cikin idonta yake ganin soyayyar yaron. Ya tuna yadda ta bar shi da rainon Farha. Matuƙar yana gida to fa shine mai raino duk juyin da zai yi kuwa. Tsakaninta da yarinyar ta bata nono amma canja diaper ma sai ta so matuk'ar ta k'yalla ido ta ga yana gida. Abida ta yi sharafinta iya sharafi don tana rayuwa ne akan uwa da uba duka sun yi tarayya akan raino da tarbiya ba wai uwace kawia mai lura da wannan b'angaren ba. Ga mamakinsa sai ya ji tausayin yadda ta yi fama da goyon ciki da haihuwa hadi da rainon yaron da babu wata kamarta da ya d'auka ko kad'an. Take kuma ya fahimci ita da yaron a takure suke rayuwa don tana cewa baya son kuka irin Baba nan da nan yaron ya kama bakinsa da hannuwansa. Wani sashe na zuciyarsa ya kore tausayin da ya taso masa tare da hujjar ita ta so hakan ta faru da ita. Tunda idan ya zo da bukatarsu bata yi masa k'wange ko raki. Haka nan idan suka fita asibiti har su dawo girmamawa mai yawa take yi masa a idon jama'a. Amma suna dawowa gida zata nade a gado da sunan ta gaji sai ya yi mata tausa. Kafin a samo Mata yar aiki raba musu aiki take yi shi da ita. Ba k'aramin jarumta ya gwada ba kafin ta daina cewa idan ta yi wanke wanke yau, gobe shi zai yi. Sai da ya yi da gaske ya yi rantsuwar ba zai yi wanke wanke ba sannan ta hak'ura akan dole take yi kullum. Amma sauran ayyuka tare suke yi. Rainon Farha kuwa ba k'aramin wahala ya sha ba, don idan ranar dutinsa ce komin kukan yarinyar ba zata karbe ta ba. Matuk'ar ta bata nono to fa sai sai dai ya yi ta fama da ita. Ganin ta bar masa kaso mai yawa na hidimar yarinya sanya ya tubure akana a raba. Don haka rana rana suke yi wato kowa da ranar da zai kula da yarinyar a tsakaninsu. Bai samu kansa ba sai da aka kaiwa Bilkisu ita wanda sau uku suna saka ranar da zasu kaita suna d'agawa don tsananin alhini. Abidar ce ta fishi jarumta a ranar da suka yi shahadar kaita don ita ce ta kafe a ranar kuwa zata tafi, alk'awarin da ta d'auka na bawa Bilki ita sai ta cika don ko mutuwa ta yi sai an bawa Bilki ita.

Ga shi dai sadda ta yi alak'awarin bawa Bilkisu d'iyarta shi baya k'asar bai kuma k'ulla soyayya da ita ba. Amma q hakan da ta yiwa Bilki ya k'ara masa sonta tare da kaita matsayin a zuciyarsa. Duk da shi din ba k'aramin takura ya yi da rasnin Farha ba a lokacin .Ya Dade yana kokawa da zuciyarsa kafin ya hak'ura. Da kansa ya yi amannar kaf duniya Bilki zai iya yiwa hakan. A yanzu kuma ya rage Jim zafin da ta ce don ta bawa Bilki Farha ya sanya ya aure shi, don Idan ba shine uban Farha ba ai kyautar zai zama ba irin yadda take a yanzu ba. Don uban yarinyar da danginsa ma sun dinga yin abin da kowa zai gane ba ita ta haife ta ba. Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:07] Ya kuma gasgata dukkan zuciyarta take son Bilki tamkar yadda yake sonta. Don ya dan rage jin zafinta kad'an ne a lokacin da Usman ya ce Wai ko zata tafi da d'iyarta? Wannan kalmar tana yawan fad'ar masa da gaba. Wai Usman nasa da suka taso tare ne ya yi masa irin haka akan laifin da ba shi ya yi ba? Bai taimake shi akan ya daidaita aurensa da kanwarsa ba.Sai ma yake bata kariya akan izgilin da take yi na na zata zauna da shi ba, tare da son ya nukurkusa Bilki da bak'incikin rabata da d'iyar da ta k'wallafa rai a kanta. Duk sadda Sulaiman ya tuna wannan batun yana yawan tambayar kansa ko dai Usman ya manta shine uban Farha ba wani ba? Shi kuwa a duniya ba zai taba yiwa Bilki gayya da abin da ya haifa ko ya mallaka ba. Wallahi ya so a ce Abida ta ce zata karbi y'arta da kuwa ya nuna musu lallai MAMI ce ta haife shi kuma nononta da ya sha bai furzar ba, yana kuma alfaharin kasancewarta uwarsa. Don sai ya yi wulakancin da zai sake girgiza gidan gabad'aya. Sai kawai suka yi sa'a daga ita har Usman din ta ce 'wai munafuki ne yake magana biyu.' Hakan da ta fad'a sai jikinsa ya mutu fishinsa ya sauka, sannan bak'inta ya ragu da kad'an a zuciyarsa. A fili ya furta "Dole sai an zauna". Abida ta ce "Me ka ce ?" Ya yi shiru tare da rufe idonsa alamun barci zai yi. Kan dole ta sunkuci junior da yake ta gyangyadi a jikinta. Ya bi bayanta da ido har ta bude k'ofar ta fita. Kukan Baba ya karya masa lagonsa kwarai da gaske har yake jin Idan ya ce ya saki Abida Baba zai tabbatar lallai baya ganin mutuncinsa ne. Amma ya ya zai yi da bak'incikin maganganun da ta yi akan uwarsa. Ko lokacin da ta yi eannan BAK'AR TA'ADA din ta zube jini ya tsinke mata ne. Ya kaita asibita da zummar jdan ta warke ta dawo sai ya yanke Ma3ta hukunci. Sai kuma bata dawo ba ta tafi. Ana cikin haka mamin ta rasu amma zuciyarta bata risina ba a cikin gayya ta yi masa gaisuwar, ta sake saka k'afafuwanta ta bi iyayenta duk kuma ana kallonta alhalin sun sa ni ba sakinta ya yi ba. Hawaye ya k'wace masa yana jin lallai ya hak'ura da ita shine ya zama d'an kirki, nakudar da mami ta yi kafin ya iso duniya bata yi a banza ba. To amma ya zai yi ne da Baba? Lallai tsugunne bata k'are musu ba. Don kuwa la shakka duk matsanancin son da yake yiwa Abida. Ya fi son MAMI. Sannan mami tana da alfarmomin da duk wanda yake k'arkashinsa sai ya girmamasu bare kuma ace wai matarsa ce zata keta mata alfarma cikin isgili a gabansa to ba yi wannan lalacewar ba kuwa. Mami ba zata yi wannan arahar ba ila yaumil qiyama ko me ta yi na kuskure kuwa.

*Duk girman rikicin da zai gitta da mijinki kada ki yi gangancin zagin iyayensa matuk'ar ba shi da dabi'ar zagin iyayenki, basa manta zagin da macen da aurensu ta yi musu cikin sauk'i*. *Shawara ce kyauta*.

* A zaune ta tarar da Baba bai shiga ciki ba. Ta isa kusa da shi ta kwantar da junior. Ta koma gefe tana dan haki. Ya kalle ta ya ce "Ina fatan baki fesa masa Bilkisu na tare da yayanku ba?" Murya a sanyaye ta ce "Tun a Saudi da ka ce kada na fad'a ban fada din ba Baba." "Madallah! Baba ya furta hakan a takaice. Ya ce "To anjima zaki kai Shi ya gaida yayanku daga nan sai ya ga twins kalarsu Baban Munira". Abida ta murmusa. Ta ce "Zai yarda na kai shi ne?" Ya ce "umarni zan ba shi ai, ke dai ki shirya kawai " Dad'i ya kamata. Da walwala ta ce "To Baba ". Daga haka Baba Babba ya mike ya nufi d'akinsa. Abida ta ciccibi yaron zuwa nata d'akin. * Bilki na zaune a d'akinta. K'ofar d'akin a bude kuka take yi k'asa k'asa yayin da Alti take fad'in "Abin da na yi ta guje miki kika ji. To wai menene ba za ki bude baki ki fad'a masa ba kya son hotunan ba?" Cikin kukan ta ce "Bai ba ni dama ba Alti. Tunda na zo gidan nan fa bai taɓa ba ni damar da zamu tattauna ba. Komai za'a yi mini kalmar d'aya ce 'ki yi hak'uri yara ne." Daidai lokacin oga Asad ya sauko basunji Shi ba. Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:09] Kunnensa ya jiyo Bilki na fad'in "An zage ni, an zagi uwata ya ga ni bai ce komai ba illah k'uruciya da ya jingina musu. Amma ni da na zagi maimurabus da uwarta ai laifi na yi, laifin da ya zama sanadin da ya yi mini hukuncin da sai da na shafe sattitika a gadon asibiti. Duk ana ga ni an kasa tsawatar masa. Ke ma yanzu da nake ganinki ina jin dad'i ya k'wace mini ke kin koma bin bayansa to Allah dai yasa ni ce ta ki, ba shi ba. Yanzu ban da ya riga ya kud'iri aniyar sai ya kunsa mini bak'inciki ace Yaya Sulaiman din da ake nema ruwa a jallo ya dawo ace an shata mini layi da zuwa wajensa?" Kuka mai cin rai ya k'wace mata. Alti hankalinta ya tashi ta ce "To ki ba shi hakuri mana. Indai kina son zuwa ki gyara barakar da ke tsakaninku. Yanzu ki saka direba ya kai ni, na gaishe shi a madadakinki. Anjima ki je masa kwana ki ba shi hak'uri ku shirya gari na wayewa da kansa zai kai wajensa". Bilki bata ce komai ba. Illah gunjin kuka. Yayin da Oga Asad ya dinga istigifari tare da wanke Alti daga zargin da yake yi mata na bata faɗawa Bilki gaskiya. Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:04] *Surayya Dahiru* 08032773332. *Littafin kud'i akan manhajar telegram*. *1k* *Via* 2384876855 *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank*

*Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*. *Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*. *Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Sanyi flusher kuwa best seller ne* *Just DM for your order @08033773332*.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull