Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 24
Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 24: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 24. Haka ya wuce su zuwa masallacin don yin sallar laasar.…
3,361 words
Haka ya wuce su zuwa masallacin don yin sallar laasar. Kukan Bilki ya taba shi sosai. Amma shi so yake yasan me ya yi mata ne a yanzu? Me yasa zata kafe ba zata je d'akinsa ba? Kansa ya kulle ainun amma ya fi gamsuwa y'anuwanta da suka d'ora masa k'ahon zuk'a ne behind everything. Ko kuma ya ce Hamida kaitsaye. Kuma yanzu ya sake gasgata Sulaiman ma zai d'ora nasa famfon tunda daga dirarsa k'asar ya tabbatar masa shima gabar yake yi da shi. Ban da darajar idon Baba, da ba sai ya wulakanta Sulaiman ba. Idan juninsa zafin kai ne, da ya nuna masa bai iya komai ba, ya saka kafa ya bar mace da aurensa a kanta har da ciki shekaru hud'u ba kad'an. Sannan akan dole ya dawo, sai da aka yi masa tilas kuma duk wannan wulakancin da ya yi musu da ubansu har yana da kuzarin da zai sake yin wani sabon wulakancin da raini daga dirarsa? Ya hurar da iskar b'acin rai. Yana jin Baba babba ne cikas d'insa akan kudirinsa na cin mutuncin Hamida da Sulaiman. Sai dai kuma matuƙar Hamida bata kiyayi shiga tsakaninsa da iyalinsa tare da yi mata famfo a kansa ba, tabbas sai ya wulakanta ta idan ya so su sake shata layi da shi tunda shi kad'ai suka wasa, ko kad'an basu tisa Faruku a gaba da bala'i kamarsa ba. Tun lokacin aurensa da Bilki da ta zugata tare da ankarar da ita bai je gaisuwar mami ba yasan ta washe shi. Yanzu kuma rashin zuwa ta ga twins ya sanya har zuciyarsa ya washe ta don ya tabbatar shine bata so ba Bilki ba. Yana tafe yana sake saken yadda zai bullowa lamarin har ya iso gidan. Ya tarar Alti na falon k'asa. Ta yi masa barka da dawowa ya amsa ya wuce. Ita kuma ta shige d'akinta da a cikin falon yake. Kaitsaye d'akin Bilki ya yi burki. Ya tarar ta idar da sallah. Ya kalle ta zuciyarsa ta tsinke a dalilin yadda ya ga ta rame Ga fuskarta ta yi kuyes idanuwanta sun jan sun fito gwara gwara. Ya ji ba dad'i. Ya had'iye fishinsa ya ce "Me yake damunki. Ta girgiza kai ta ce "Ba komai". Ya ce "To kukan na menene?" Ta suake ajiyar zuciya bata ce uffan ba. Ya jijjiga kai ya isa gadon da yaran suke shimfide. Idonsu biyu dukkansu sai shure shure suke yi tabbacin a kwashe Duke. Sun yi bul bul da su tamkar sun kai watanni hud'u alhali kwanakin baya kad'an suka cika watanni biyu. Ya zauna ya dauki kowanne ya yi masa wasa sannan ya kwantar da su a hankali. Ita mamaki yake bata yadda yake yi musu tamkar k'wai. Idan aka ga yadda yake b'arin jiki a kansu sai a zaci gabad'aya bai samu haihuwar ba ne sai a yanzu da shekaru suka fara tura masa. Wani zubin ita da ta haifesu ganin gazawarta yake yi akan kula da yaran. Komin dare idan ya jiyo kukansu sai ya zo ya tambayi ba'asin kukan ko ya ce a daren zai kaisu asibiti a duba lafiyarsu. Da Alti ta gane shi sai take ce masa ai kukan ne alamun suna lafiya, sannan alamun zasu yi kwakwalwa ne. Tunda ya ji hakan kuma sai ya koma tambayar yau kuwa sun yi kuka da ba nan? Alti yau basu yi kukan dare ba fa? Ko dai basu da lafiya ne?" Aysha da kullum ita take gida tana kallon ikon Allah. Tasan dadynsu na sonsu k'warai da gaske. Amma da wayonta da hankalinta aka yi goyon Amal da Noor tabbas bai yi irin haka ba. Sannan ba ya taya Momi rainon yara, abin da ta san baya damuwa akan abinci ne, ta bude ido ta ga da daddare idan ya dawo zai bada order chep ta yi masa abin da yake so. Amma tun zuwan anti Maigado ta ga ya canja, matuƙar ta ajiye masa abinci sai ya ci. A yanzu baya iya saka chep ta yi masa sai ya dinga raragefe kafin ya sanya a yi masa abin da yake so. Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:07] Duk abin da ta girka haka yake ci, babu musu wanda lokacin mominsu shine yake da lasisin zabar abin da zai ci bayan ya dawo har da tsirfar baya cin abincin da ya shiga warmers. Gara ma a kwanakin nan ta ga chep angela ke yi masa. Takaici ke cinta me yasa yake rianon wadannan, ko ita kanta jele take yi tsakanin samansu da saman anti Maigado da Kuma saman Dady ba don komai ba sai don ta kaisa masa yaran, ko ya ce ta je ta karbosu a wajensa suna jin yunwa. Kuma yaran da zata iya hadesu ta d'auke su sai ya ce da d'aid'ai zata kai su ko ta sauko da su. Idan kuwa ta d'auke guda a cikinsu ya dinga fad'in "Aysha handle them with care. Ki sauka a hankali ban da garaje! Me yasa yake wannan barin jikin akanasu, shin dan sun kasance maza ne ko kuwa don sun kasance y'ay'an Maigadon da yake so kuma Abida da mominsa suke sonta? Kullum sai ta yi kuka a d'akinta wanda na kishin yadda yake son wata macen alhalin uwarsu na kushewa. Gata da riritawa ba wanda ba ya yi musu amma gabad'aya zaman gidan ya yi mata tsauri so take ta barwa Maigado da Abida guri su cinye gidan ma gabad'aya. Tunda ta gama gamsuwa ya fi son Maigado akan mominsu. Ya dinga ganawa momi azaba da fishinsa akan ya'yan da ta haifa. Amma wata katuwa ta zo ta zanesu ya yi muk'us bai yi mata azababben fishinsa da yake sanya mominsu yini tana goge k'wallar bak'inciki. Amma wannan ko kwakkwaran motsi kasawa ya yi sai ma kwasarta shopping da ya yi suka raba dare a waje. Idan ta ga hips din Maigado har kan harshenta take jin ciwo tunda a dalilin momi na son ta zama irin yadda yake so ta salwantar da rayuwarta. Ga shi ya samo wacce take da su natural ba artificial ba yana sharafinsa yadda yake so. Sune kad'ai suka yi asarar rashinta sai ko danginta. Wadannan dalilan ya sanya Aysha ta kasa sakewa da Maigado amma kuma ko kallon banza ba ta yi mata. Ya mike ya fice ba tare da ya ce mata kanzil ba. Yayin da ita kuma kuttunsa ya zo mata har wuya. Idan har yana da imani ya tambayi ba'asin kukanta? Ya kumshe a gida yana faman Hana Mata azaba. Ace Sulaiman Yana Abuja a hana ta zuwa wajensa? Da ace maimurabus ce yama isa ya fara yi irin wnanan kama karyar? Oh namiji dai baya fita a wajen mace, baya gwaninta ko wacce ga ni take yi yafi son wata a kanta. Yan shiga d'akinsa wayarsa da layin da iya family ne suke da Shi ya hau kara. Ya duba ganin Baba ne ya sanya ya zauna sannan ya amsa cikin girmamawa. "Baba dafatan ka kwanta ka yi barcin gajiya?" Baba ya amsa da fad'in "Na dan yi. Sai dai ban wani jima ba a dalilin zuciyar babu dad'i". Ran oga Asad ya baci a ransa ya ce "Ina zuciyarka zata yi dad'i ka k'wallafa waɗanccan ja'iran a ranka."
A fili kuma ya ce "Ayyah sannu Baba ka Ƙara hak'uri ka kuma dinga yawan istigifari.". "Ina yi, amma zan dage da yi. Ina son ka bude kunnuwanka da zuciyarka ka saurare ni da kyau". Zuciyarsa ta buga don kuwa la shakka al'amarin da za'a bijiro masa mai nauyi ne! "Asad Asad Asad! Baba ya k'ira shi har sau uku cikin dakakkiyar murya. A sanyaye ya ce " Na'am Baba". Anjima ka shirya tarbar Sulaiman a gidanka. Zai zo ya gaisheka daga nan ya gaisa da Maigado ". Tamkar an kwada masa guduma haka ya ji wannan batun na Baba Babba. Murya ba amo ya ce "Wallahi k'arya yake yi ba dan ni zai zo ba Baba wajen kanwarsa zai zo". "Wallahi bai san Maigado iyalinka ba ce bai san komai ba". Nan da nan Asad ya gamsu don kuwa baba ba ya rantsuwa.sai ta k'ure. Ya numfasa ya ce "To Baba ko direba ya kawo Maigadon kawai Su gaisa don yanzu fita da Zan yi". Baba ya ce "Sulaiman zai zo gidanka ya gaishe ka daga nan ya ga tagwaye duk da bai sna wacece ta haifa maka su ba". "Amma baba.. Baba ya yi maza ya katse shi da fad'in "Shi da yake na isa da shi, ina yi masa fadan bai gaishe ka ba, ya ba ni hak'uri, a take na zartar masa da hukuncin ya biyo ka har gida ya gaishe ka, to kawai ya ce mini saboda giyar kud'i da mulki basu fara bude masa idanuwansa ba". Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:09] Hankalin oga Asad ya tashi ainun ya shiga ba shi hak'uri tare da fad'in "Ka yi hak'uri Baba zan zauna na jira shi. Ina maraba da mijin Abida". Nan da nan dad'i ya kama Baban ya yi murmushi da ya isa har kunnen Asad din. Ya ce "Yauwa oga Asad Allah ya tsare ka da tsarewarsa." "A sanyaye ya ce "Ameen Baba". Don tausayi ya ba shi na yadda ya shiga tsakaninsa da Sulaiman da son ya yi musu sulhu. A fili ya ce "Allah ka karbi kyakkwar niyyar Baba akan zumunci. Allah ka shirya tsakaninmu gabad'aya." Baban ne ya katse wayarsa yana jin tunda ya danne Asad to ya samu sauk'in matsalar. Don ba k'aramin aikinsa ba ne idan Sulaiman ya je gidansa ya saka a hana shi shiga duk da Bilki na cikin gidan kuwa. Da kansa Baba mamaki yake yi yadda y'ay'ansa uku halayyar kaninsa suka kwashe tsaf ta kar ta san kar. Asad Usman da Abida wadannan ukun idan aka taɓa su basu da d'adi ko kad'an. Yayin da Faruku, Salaha da Munira idan ta sune kiyama ba zata tsyaa ba. Haka nan yana mamakin yadda Bilki ta kwashe kammaninsu da halayyarsa, haka Sulaiman shi dazu da ya rike shi yana dukansa sai ya ga ma duk yafi su Faruku kama da shi sak sai dai halayyarsu tazarace mai yawa don kuwa yana rukunin su Asad da suka samo halin Baba K'arami. Baba k'arami kuma ance halin mahaifinsu ya yi har kama, yayin da shi Baba Babba ya yi kamar gyatumarsu shiyasa ba wani kama suke yi da baba K'arami ba. Amma ya'yansu an garwaya musu saboda tsananin tasirin jini. Shi ya haifi masu kama da Kaninsa, haka shima baba Karami ya haifi masu kama da shi. Tunda suka dawo daga sallar laasar ya ce wa "Sulaiman zai aike su tare da Abida ya shirya zo. Ya ajiye wayar ba jimawa Sulaiman din ya shigo cikin tsadaddiyar Farar jallabiya. K'amshin ya cika falon. Sosai ya yi kyau ya Dora farar hula irin Dai yadda suka.ga Baba Babba Yana sanya Farin tufafi. Da walwala Baba ya ce "Sulaiman ka ga yadda ka juye ka koma tamkar sadda nake cikin shekarun k'arfi irin naka?" Sulaiman ya durkusa akan kafet din ya ce "Ai tunda na yi sa'a na yi kama da kai komai koyi nake yi da kai Baba ". Farincikin Baba ya dada fad'ada ya ce "Amma fa ni bana gaba, da kullaci sosia kuka nake son zumunta da dabbaka shi ". Zuciyar Sulaiman d'aya ya ce "Baba kullum Ina addu'ar na Zama irin Hakan, ina ji a jikina Kuma addu'ar ta karɓu jira nake yi Kawai na ji na gama sauyawa gabad'aya. Dariya Baba ya yi ya ce "To bari mu ga ko kai a karan kanka kana son ka canja din. So nake.ka me gidan yayanku ka gaishe shi sannan ka yi masa murnar haihuwar tagwaye da aka yi.a gidansa kuma karon farko da aka haifa masa yara maza." Zuciya Sulaiman ta harba baki mai yanka wuya. Zuwa gidan Yaya Asad ba k'aramin takura ba ne. Ya yi shiru. Nan da nan Baba ya gane baya son zuwa. Ya numfasa ya ce "Ka ga shi da yake na isa da shi, ina fad'a masa zaka je gidansa da murnarsa ya ce da fita zai yi amma ya fasa fitar zai zauna ya yi dakon ka". Kan dole Sulaiman ya ce "Ni ma ka isa da ni mana Baba. Zan je din" "To Allah ya yi maka albarka sai ku tafi tare da iyalinka ta raka ka." A kan tilas ya ce "To" Don kada Baba ya ji da ya'yan cikinsa kad'ai ya isa ba dan haka ba, ba abin da zai saka ya fita unguwa tare da Abida a yanzu.
Daidai lokacin Abida ta fito cikin kwalliya ta burgewa. Ta tsugunna a kusa da Baba. Ta tausasa harshe ta ce "Baba ba Zan Ga ji da fad'a maka na yi kuskuren kin ji Umarnin da ka ba ni a baya ba. Ka ce na Koma dakin mijina na bijire, Sai Dai bijire maka da na yi ka zuba mini ido ka mayar da ni y'ancin yin Duk da abin da na so daidai ko ba daidai ba na matuƙar saka Ni tashin hankali. Ka yi hak'uri Baba nima ka dinga bani Umarni kan Duk abin da ya dace Konda ba na so dan Allah Baba ". Idonta ya ciko da hawaye. Tausayinta ya kama baba, sannan yadda take wanke shina idon Sulaiman da iyakacin gaskiyarta ya sanya kin ya huce da ita. Ya tausasa harshe ya ce "Zan fara yi miki hakan idan Allah ya sake ara mini na ga kin koma dakinki kin nutsu kina zaune lafiya da mijinki ". Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:13] Sulaiman ya ji wani iri Baba Sai tula masa k'asa take yi cikin hikima. Yayin da salama ta shigi Abida don har cikin zuciyarta take jin matsananciuar damuwa idan ta ga Baba na yin iko da y'an gidansu kaf dinsu amma ban da ita. Tun sadda ya yiwa Bilki kacakaca ya ce ta koma gidan mijinta ta gano tana cikin had'arin rayuwa don kuwa duk abin da zata yi a rayuwarta ido da to ne tsakaninta da Baba da Momi. Babu Mai ce mata a a , ko meyasa konba yanzu ba. Ashe ka samu mai saka da mai habaka ma ba k'aramin rahma ba ne? Sannan yadda suke nan nan da ya'yansu Yaya Faruku da na Yaya Asad basa yi da junior. Farha kad'ai suke nunawa soyayya mai yawa ita kuwa tasan don tana hannun Bilki ne. Junior kam saffa saffa. Idan bata nan suna kula mata da shi amma akan idonta kam basa wani jansa a jiki illah kyara akan yana da fitina tare da fad'a mata ta samgarta shi. Wanda hakan na cikin dalilan da ya sanya kullum sai ta yi kuka, sannan zaman gidan ya yi matuƙar gundurarta. Shiyasa Idan ta yi sadaka sai ta ce a yi mata addu'a Allah ya bayyana mijinta. Baba ya ce "Ku je ki raka shi gidan yayanku." Da azama ta ce "To Baba bari je yamma na yi." Ta mike tana fad'in "sai mun dawo tunda sai da ta shiga ta yiwa Momi sallama kafin ta fito falon. Haka Sulaiman din ya mik'e tare da fad'in "mun tafi". "A dawo lafiya ka gaida mini takwarorinmu". "To". Sulaiman ya amsa a nutse. Daga haka ya fita don tuni Abida ta fice. Abida ta kalle shi ta ce "Za ka jamu ne?" "Ba walwala ya ce "Nasan gidan ne?". Bata ce komai ba, ta bude mass gaban motar. Ya shiga babu musu a ransa ya dinga tuna da shi yake yi mata irin haka. Ya rufe, sannan ta zagaya ta shiga ta ja motar aka bude musu gate ya fice. Suna tafe Sulaiman na kallon yadda Abuja ta sake cigaba. Cikin wata irin murya ta ce "Yaya Sule wai baka kewata ne?" Cikin gatse ya ce "Ina yi mana dumudumu". Ta murmusa Yaya Sule gatse ko wasa?" Ya yi mata shiru. Ta nisa ta ce "Ba Zan iya zuwa guest room na kwana maka ba alhalin momi.da baba na nan, yanzu ya za'a yii taimaki kanmu". Ya yi shiru tare da mamakinta. Bata da kumbiya kumbiya ko kad'an. "Still cikin gatse ya ce "Ki kawo mana solution ". Kaitsaye ta ce "To idan mun dawo daga gidan Dady kawai.mu samu lodge." Ya ce "Mu kwana kenan?" Ta ce "a a, zuwa magharib idan muka gama da gidan Yaya Asad. Ko 10 muka koma gida ya yi ai". Ya ce bai yi ba. Idan zamu kwana na yarda mu je ki mana lodge Haj Abida. Idan kuwa Yan awowine to a bari kawai". "Ya Sule akwai batun da nake so mu tattauna tsakanina da Allah! Haka kawai ya ji ya ba shi tausayi don bata maganarsa zummar wake. Amma ya cije ya ce "Zamu tattauna ai gaggawr me kike yi?". Nan da nan ta ce "To gaskiya Yaya Sule zaka biya ni kudin kunyatar da na yi. Ta ya ya zan cire kunya na yi inviting ɗinka amma ka yi rejecting. Don haka Wallahi sai ka biya diyya". Da mamaki ya juya yana kallonta, gabad'aya ta yi kicinkicin da fuskarta. Ya kaurara murya ya ce "You are trying me ko Abida?" Ta tura baki ta ce "Gaskiya ne fa, don haka zan saka shi cikin lissafin basukan da nake bin ka". Da mamaki ya ce "Ni kike bi basuka ba ma bashi ba?" Kaitsaye ta ce "Kai kuwa". Ya yi shiru yana ayyana wai yaushe zata daina son kud'i ne" Kaf y'ay'an gidansu mata babu mai kudin Abida. Amma kudinta nata ne ita kad'ai. Bata yarda ko bashi ya had'asu, amma yanzu ta kaikaice tana fad'a masa basuka take binsa. A yadda kuma ya ga yanayinta da gaske take yi, kuma duk yadda yake jin zafinta idan har ya mayar da ita d'akinta sai ya biya basukan nan. Ya rasa me zata yi da kudade haka. Kud'insa nasu ne tare amma nata kam nata ne ita kad'ai. Basu sake magana ba har suka isa inda suka nufa. Oga Asad da kansa ya tarbe su a katafaren falon da yake ganawa da manyan mutane. Gabansa ya fadi da ya ga Sulaiman da shigar da ya yi. Take ya tuno Baba Babba a shekarun baya da ya ke kai su makaranta shi da Faruku mussaman sadda suke sakandire a Rumfa college Kano. Sak haka yake tamkar Sulaiman a yanzu. Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:16] Bai san sadda ya daidaita ya yi saluting din Sulaiman tamkar yana saluting ogansu na koli I.G. Dad'i ya kashe Abida don a tsorace take tundaa ta gane Dady yana jin haushin Sulaiman na jingine musu ita da ya yi. Haka a dazu ta fahimci shima Sulaiman din haushinsa yake ji da gasken gaske. Don haka ta shiga rud'anin zuciya tamkar yadda baba ya shiga idan basu jitu ba, tana cikin tashin hankali don kuwa Baba da Momi ne kad'ai suka zartasu a zuciyarta.
*Sabon littafin marubuciya Binta Abbale na Shirin riskarku*. *Littafin da ya samu nazari da azanci yayin rubuta shi*.
*Gudun Aure*
*Sunan labarin, dafatan za'a bibiye Shi da zarar ya Fara sauka*.
*Na gode*. Save Restricted Content Bot, [Oct 22, 2025 at 11:40] *Surayya Dee* 08032773332. *Littafin kud'i akan manhajar telegram*. *1k* *Via* 2384876855 *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank*
*Contact Bojuwa herbs* 08032773332 what'sapp only* *For all your kayan mata gangariya* *Bridal package* *Maijego package* *Uwargida package* *Bazawara package* *Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego* *Ciccibin garari* *Tsumin saiwowi* *Hakkkn daka emergency* *Gumbar ridi* *Gumbar saiwowi*
Sulaiman ganin irin gaisuwar da Yaya Asad ya yi masa ta k'arshen koli a gidan tsaro sai kawai ya tsugunna a gabansa dan shima ya gaishe shi da k'ololuwar girmamawa. Hakan da ya yi ya burge Abida da take ta faman yi musu hotuna da vedios don tana ganin oga Asad ya k'ame ta fara yiwa Baba recording. Asad ya dago shi ya rungume Shi. Daga haka suka zauna a kujera. Gabad'aya Sulaiman ya ji yayansu ya kashe shi da kunya don baisan sadda ya zube masa tamkar mai neman gafara ba. Yayin da oga Asad kuma har cikin zuciyarsa ya ji tsanar Sulaiman da ta darsu a dazu ta gushe daga zuciyarsa. Cikin mintina k'alilan angela ta kewaye gabansu da cima kala kala.