Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 28
Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 28: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 28. Da sauri Bilki ta karbi na hannunta tana fad'in "Sannu…
4,397 words
Da sauri Bilki ta karbi na hannunta tana fad'in "Sannu Alti. " Sai da ta gama basu. Ta kalli Alti ta ce "Bari na kaisu wajensa. Ki yi sallah sai na zo mu d'ora abinci". Alti ta ce "To". Ta fita zuwa d'akinta da kuzari don tunda ta ga Bilki na b'are b'are tasan an shirya sannan walwalarta ta dawo babu k'unci da share k'walla akai akai. Ja'ira itama ta ji jiki". Alti ta fad'a a ranta. Ta hadesu a babban shawul ta ciccibesu ta yi samansa. Yana ganinta ya zabura ya mike daga kwanciyar da ya yi. Ya tare ta jikinsa har rawa take yi. Ya ce "A a wannan ganganci ne Maigado. One by one za'a dinga kawo su, ko ki dinga cewa na zo na d'auke su da kaina. Yayarsu bata nan ne da ba ki ce ta ɗauko daya ba?' Baban Bilki tunda ta fara service fa sai yamma take gida ai". Kuma su Hafcy kowa na makaranta." Ya kwantar da su yana duba jikinsu ko an matse su. Har ta juya ya ce "Wai me zan ci ne Maigado?" Ta dawo ta bude k'aramin firij din da yake cikin dakin. Ta d'auko fresh milk ta bude ta dauko tumbler ta cika masa ya karɓa ya kwankwade. Ta rufe ta mayar. Ta d'auko inibi ta fita zuwa k'aramin kicin d'insa ta wanke ta zubo a bowl ta kawo masa gabansa. "Na gode sarauniyar shaiba". Ya fad'a yana kallonta. Ta ce "Zan je na yi girki". "To a yi lafiya a gama lafiya". Ta duka ya sumbace shi kad'an. Ta juya ta tafi ba tare da kalle shi ba. Ya sake binta da ido. Shi kam ana masa k'arfin hali. Angela ba zata yi girki ba indai zai dawo gida ya yi lunch. Breakfast din yara da wanda suke tafiya da shi school kawai ne aikin angela na dole. Idan ba haka ba, sai ta ga dama take yarda ta yi girki a gidan. Sai idan za'a yi bak'i da yawa ko idan za'a kai masa office da yawa. Shine zata yarda ta yi wasu daga cikin abincin da za'a kai tunda kala kaala ake yi musu. A fili ya ce "Ban da dai na yi laushi ya za'a dinga mulkata irin haka? Kuma an hutar da ke amma don fitina ba zaki huta ba? Allah sarki Rukayya, Allah ya yi miki rahama ". Ya fad'a a sanyaye don ita a haka ta rayu. Komai yake so bata da y'ancin yi masa musu matuƙar abin kaitsaye shi ya shafa. Ya sa ni a bayan idonsa tana yin abubuwan da ta ga dama. Amma ko kad'an bata samu damar da Bilki ta samu a wajensa ba. Faricincikinsa d'aya ma yadda bai yi mata iyaka da kuɗinsa ba. Ta yi facaka da kud'i son ranta. Ya dawo sallar la'asar sannan ta gabatar masa da abinci. Ya sauko tare da ita suke ci. Yana ci yana yaba dad'in abincin. Save Restricted Content Bot, [Oct 27, 2025 at 16:39] Tabbas ya gamsu ta iya sarrafa girki daga ita har altin tata. Ranar haka bai fita ba. A gida Aysha ta dawo ta same shi. Haka ma sauran yaran. Ya zauna cikinsu suka dinga hira kowacce na fad'a masa abin da take so ya siya mata. Shi kuma ya amince zai siyawa kowa abin take so. Gida ya kacame da murna tunda cewa ya yi ma su shirya after Isha za'a fita shopping da kansa kuma zai tukasu. Idan ya fita da su da kansa suna jin dad'i don komai suka dauka baya iya hanasu sabanin idan su kad'ai ne account mai takaitaccen kudi yake basu damar tabawa. Ya kalli Bilki da ta bishi sama ya ce "Da ke zamu je ne ko sai daga baya zan kai ki?" Dan ya ji dad'i sai ta ce "A a zan biku na tayasu zabe kada yaran su debo abubuwan da ba wani amfanarsu zasu yi ba". Dad'i ya kama shi ya ce "yauwa Sarauniyar sheba dama nafi son na tafi da iyalina gabad'aya". Aysha da Hafcy suka hawo saman Bilki suka d'auki jariran suka fara ficewa. Farha ta kalli Alti ta ce "To me kike so na siyo miki?" Dad'i ya kama Alti don Farha na nunawa irin ita ce tata tunda tare suka zo gidan. Ta ce "Ki siyo mini Rufaida da kulikulin Ummiel ". Farha ta ce"To nasan Dady ma zai siyowa su Momi da Baba". Bilki na d'akin oga tana tsaye ya gama shiryawa. Tuni ta shirya cikin tsadaddiyar Yasmin abaya. Ya kalle ta ya ce "Dr Sulaiman fa ya ce ya kamata ki ga likita". Ta ce "Baban Bilkisu k'alauna fa Wallahi. Tsabagen kuttun da kake nausa mini ne ya nemi zautar da ni. Yau kad'ai duk wanda ya ganni ya ga real Bilki ba wacce aka share ake kuma nuna mata wata mace ta fita ba! Mamaki ya kama shi. Ya yi maza ya isa kusa da ita ya ce "Ba a fiki ba, ba kuma za'a fiki ba sarauniyar sheba. "
Surayya Dee 08032773332. Save Restricted Content Bot, [Oct 28, 2025 at 10:59] *Surayya Dee* *08032773332*
A yammacin wannan ranar Abida a falon baba na ciki. Kusa da Baban tske zaune tana nuna masa videon yadda ya wakana tsakanin.oga Asad da Dr Sulaiman. Dad'i ya kama shi k'warai da gaske. Da kuzari ya ce "Amma shine ba ki nuna mini wannan abin farincikin ba sai yanzu?" "Baba da muka dawo ka shiga ciki. Yau kuma sassafe na fita zuwa asibiti. D'azun nan na shigo ". Murna kan murna yake yi tamkar an zauna an yi sulhu komai ya wuce a tsakaninsu. Addu'ar fatan alheri ga oga Asad da Dr Sulaiman ya yi musu ba adadi. Motsi kad'an zai ce "Sake kunna mini na ga gaisuwar mai d'amara da civilian ". Abida aka dinga kunna amsa ba gajiya. Suna cikin haka ta ce "Baba dai har yanzu baka huce da ni ba. Kana ta yiwa Dady da Yaya Sule addu'ar tsari daga abin k'i da kuma albarkar rayuwa amma ni da na yi maka wannan vedion da ya sanyaka farincikin da kake ciki baka yi mini addu'ar ba." Ya shafa kanta ya ce "Allah ya yi miki albarka Abidan Baba, Allah ya shirya miki zuri'a." Dad'i ya kamata don rabon da ya ce Abidansa ta mance. A sanyaye ta ce "Ameen Baba. Ya nisa ya ce "Dazu Sulaiman ya ce mini jibi ko gata zai tafi Kano. Zai yi aikin ido a asibitin Makka na cikin Kano . Wanda wata gidauniyar tallafawa k'asashe masu tasowa ta Saudiiya take d'aukar nauyi. Ya ce sati biyu zai yi ya dawo." Jikin Abida ya yi sanyi. Ta fara kukan da ya tayar da hankalin tsohonta. A sanyaye ya ce " menene na kukan kuma?" Tsawon lokaci ta kasa magana. Sai kuka take yi k'asa k'asa amma mai nauyi ainun. Jikin Baba ya yi sanyi. A sanyaye ya ce "Ki yi hak'uri Abida. Ki yi addu'a komai zai wuce tamkar ba'a yi ba". Da kuka sosai ta ce "Baba na yi hak'uri, na yi addu'a. Da kanka ka fad'a mini Yaya Sule yafi k'arfina. Yanzu da ya dawo ai sai ka taya ni. Nauyinka zai saka ya hak'ura. Kuma Wallahi Baba da ace Bilki ce a gida, Dady ya ce zai yi tafiya cewa zaka yi ya tafi da matarsa, ni nasan hakan zaka yi masa ko ba ya so, sai ya tafi da ita duk laifinta zai zama ka roka mata afuwa. Amma ni dukkanku ana kallo zai tafi ya bar ni, ana kallon bai yi wani motsin sama mini inda zan zauna ba. Duk tsawon lokacin da ya rataye ni amma ya dawo da niyyar cigaba da rataye ni. Kuma ba wanda ya yi ko da tari ne a cikinku" Ta rushe da kuka wiwi har Momi da take kicin ta fito a sukwane. Cikin kuka sosai Abida take fad'in "Baba ka shiga tsakanina da shi. Ka ba shi umarnin ya dauki iyalinsa ka gaji da rik'e masa. Ka yiwa Allah ka tursasa shi yadda ka ke tirsasa Dady da Yaya Usman. Wallahi na gaji. Ba wani aikin ido da zai je yi. Gidan iyayen yarinyar da yake nema zai je. Daliba ce a Saudiyya suka hadu. Yanzu da na dawo, wajensa na fara shiga, na tarar yana band'aki. Na ga wayarsa na dauka akan na k'ira lambata don na samu layinsa sai kawai na ga hirarsu. Wallahi Baba ce wa ta yi ya je ya gaida iyayenta daga nan sai ya tura manyansa". Murya a dakushe Baba ya ce "Nutsu ki saurare ni." Tsawon mintina biyu yana kallonta tana kuka mai dauke da nauyayyen gunji. Tausayinta ya daskarar da su hatta Momi idanuwanta sun cika da k'walla. Yadda ba ya nan nan da junior kad'ai ya sanya sun gane Sulaiman ya yi nisa bai zo da niyyar sulhu tsakaninsa da ita ba. Yaron kansa jikinsa ya yi sanyi baya wani d'okin ya je wajensa. Baba ya numfasa ya ce "Ki kwantar da hankalinki Abida. Kada ki mayar da duba wayar namiji dabi'arki. Yanzu ga shi kin ganowa kanki abin da zai hanaki sukuni. Abu d'aya ne ya sanya na Zan iya tursasa Sulaiman akan Ki ba saboda Ni na haife ki. Anan falon a inda kike Bilki ta fad'a mini na zuba miki ido ban mayar da ke d'akinki ba saboda Sulaiman ba Shi da wata alfarma. Kuma Wallahi a bakinsa ta ji wannan kalaman. Yanzu ta ina zan fara cewa ya d'auke Ki, alhalin a lokacin da ya kamata na ce ki kma din ban yi iko da ke kin yarda ba. Duk yadda zan mayar da Sulaiman ya zama dana ai Dai ke ce na haifa. Da ace ba ni na haife ki ba to da na gwada masa kwamjina amma a yanzu da ya tafi a fahimtar mun zuba miki ido kin bijirewa zama da shi alhalin bai yi miki komai ba, bai kuma sake ki ba , kin ga ai ni ba ni da bakin magana. Save Restricted Content Bot, [Oct 28, 2025 at 11:02] Kuma ma menene abin damuwa dan zai k'ara aure? Ina ce ko zaune kuke k'alau zai iya k'ara aure tunda an halasta masa. Kanta na kasa hawaye na tsere bi da bi. Wani irin cunkushewa mak'oshinta ya yi. Ga k'irjinta ya yi nauyi tamkar an d'ora gingimemen dutse. Wato dai da gaske Sulaiman sai ya nukurkusa da bak'in cikinsa. Ta dinga jin ya kamata ta tsayawa kanta. Ta yi laifi, ta karbi laifin, ta bada hak'uri, ta janye amma duk bai kalli nadamarta da bibikonsa da take yi ba. Tunda aure yake nema zata hak'ura don kuwa ko shine dagi wajen fad'a ba zai yi aure ita tana zaune a gidan ubanta bata san matsayinta ba. Tunda bai ga nadamarta ba bari Kawai ta ɗauko rigarta ta mayar. Zata koma Abidan Baba ta da, ba Abidan yanzu da ruwa ya daki babban zakara ba.
Daidai lokacin suka jiyo shi a falon farko yana kwada sallama a sukwane. Momi ta mike tana fad'in "Sulaiman ga mu a nan". Da hanzari ya shigo yana fad'in "Ina Baba?" Ganin Baba ga Abida durk'ushe kanta na k'asa ya sanya tsugunnawa. A diririce ya ce "Baba ka ce mata ta bani kayayyakina da ta kwashe mini. Tun ranar muka dawo ban ga passport dina ba. Dazu da safe ta shiga ina barci ta kwashe mini duka ATM dina. Yanzu kuma ta dauke mini wayata guda daya da ledar takalmana." Baba ya yi shiru k'walla na cika masa ido don kuwa Baba k'arami ne yake masa yawo a zuciyarsa. Shine yake yi musu Sharia tun suna yara. Sai idan Sulaiman bai gamsu da hukuncin Baba k'arami ba sai ya zarto ya kawo masa kara tare da gabatar da hujjar Abida na kwashe masa kayayyakinsa tana boyewa saboda Baba k'arami yana bata kariyar tunda bai ga lokacin da ta dauka ba to kuwa ba ita ba ce, alhalin ita ce ba kowa ba. Shi kuma Baba Babba idan ya lallabata tare da yi mata kyautar talotalo ko dawisu ko tattabara sai ta je ta fito masa da abin da ta boye. Mussaman takalmi haka siddan idan ta ga takalminsa a bakin k'ofa sai ta kwashe ko ta d'auke kafa daya ta bar masa d'aya. Bisa hujjar yana ce mata bak'a mummuna, ko Abida kwaila mai gwalli. Baba ya numfasa tsawon lokaci ya kass magana. A dabarance ya goge k'wallar idonsa wanda Sulaiman ya ga ni. Jikinsa ya yi sanyi, zuciyarsa ta karye da tausayin Baban nasu. Ya kalli Abida ya tabbatar kuka take yi. A ransa tamkar ya rufe ta da dukan da zata yi kukan gaskiya. Har yanzu ba zata bar Baba ya huta ba. Ta zo ta tisa shi a gaba tana kukan munafurci ga shi shima har ya fara. Ya kuma san bincike ta yi masa a wayarsa shine ta ga abin da ya dameta. A ransa ya ce "Ki adana kukanki zuwa gaba yarinya. Baba ya yi k'arfin halin cewa "Je ki d'auko mini kayansa " Murya ba amo ta ce "Ni ban d'auke masa ba fa. Akan me zai dinga k'ala mini sata. Tun ina karama yake mini sharrin na yi mass sata kafatalin gidan nan Abida ce barauniyarsa akan me zai dinga keta mini haddi irin haka?" Ta kece da kukan da dama bata gama yinsa ba tunda kishine ke yagalgalata. Sulaiman ya yi mata k'uri yana kallon ikon Allah.
Har cikin zuciyarsa yake jin kukanta. Ya masa magana don gabad'aya ya zama speechless. Ba wani kuzari ya ce "Wallahi ke kika d'auka ba mai shiga d'akin ya taba mini kayana sai ke, ko danki ba zai je ya zabe abubuwana masu muhimmanci ya bar ni da tarkace ba, babu mai yin wannan TA'ADAr sai ke." Baba ya kaurara murya ya ce "Tashi ki dauko mini kayansa Abida ". Yadda Baba ya yi magana cikin sigar umarni ya sanya ta tashi ta nufi d'akinta. Jimawa kad'an ta dawo da wayarsa da ATM. Ta mik'a masa ya karɓa ya ce "Saura passport". Nan da nan ta ce "Wannan kuma ban dauka ba. Ban san inda yake ba, ka dai duba a cikin kayanka". Da hanzari ya ce "Wallahi kin dauka yana hannunki ko kaffara ba zan yi ba akan haka." Baba ya ce ",Je ki kawo mini." Ta fara kuka tare da cin layar bata d'auka ba iyakacin abin da ta d'auka ta fito masa da kayansa. Juyin duniya ta k'i ta yarda ma ta dauka bare ta bayar. Baba ya ce "To ku je ta duba maka a nutse". Save Restricted Content Bot, [Oct 28, 2025 at 11:05] Abida ta yi maza ta mike tare da fad'in "To Baba" . Yayin da Sulaiman ya ce "Baba baya dakin nan Wallahi. Tunda ta je yi mini shara ta d'auke kuma tun a ranar sai da na faɗa maka." Baba ya ce "yanzu dai tashi ka je ku duba cikin nutsuwa ba da tashin hankali ba." Tuni Abida ta fice. Kan dole Sulaiman ya tashi ya bi bayanta amma ya riga yasan yana hannunta ba ganinsa za'a yi ba tunda ta fice da shi tun tuni. Yana shiga dakin kawai ya ganta a tube ta cire doguwar rigar jikinta ta wurgar kan kujera. Daga ita sai gajeran wando skin tight iya guiwarta sai half best. Ko brexiya bata saka ba tunda kananun nono gareta da suke a makale basu zube ba. Don haka bata cika saka bra ba Sai ta yi nishadi. Ya yi turus zuciyarsa ya buga. Ganin shatin nipples a cikin farar half best dinta da ta kamata. Ya dan diririce. Murya ba amo ya ce "Ke ban son shakiyanci fito mini da abubuwana kin ji." Gabad'aya ta tunkare shi ta ce "Caje ni, laluba ko a jikina na boye tunda baka gasgata ni ba. Kaitsaye ta rik'o hannuwansa akan ya laluba ko zai ga ni a jikinta. Gabad'aya jikinsa ya dauki mazari.
*Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*. *Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*. *Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Just DM for your order @08033773332*.
Ya yi maza ya tsalla gefe. Da haki ya ce "Abida you are trying me fa". Kallonsa kawai ta gane sakonta ya bige shi. Ta daure fuska ta yi juyi tana fad'in "A a to indai ba a cikina na boye ba ina zan ajiye?" Ya zagaye ta ya zauna a bakin gado daga k'arshe ya juya mata baya Yana kallon window. Ta jijjiga kai tasan ba k'aramin jarumta ya yi da bai kai hannunsa kan nipples dinta ba mussaman da suka fito sosai irin yadda yake son ya gansu, alamun tsosto suke so. Ganin ta birkita shi Sai kawai ta d'auki rigarta ta sanya. Ta isa kusa da shi. Ba wani Dogon turanci Kawai ta zube a gabansa. Murya cike da rauni ta ce "Yaya Sule Ga ni na durkusa on my kneel ka karya mini Duk wata fiffika to ka yafe mini haka nan mussaman ma da ya kasance sharrin marab'ai na hadu da su. Amma Duk da haka na yarda na bata maka, ka yi hakuri." Daidai lokacin wayarta ta hau kuwwa. Tana durk'ushen ta d'auka ganin sunan Dady ne. Ta dauka. Tun kafin ya amsa gaisuwar da take yi masa ya ce "Ki kaiwa Sulaiman wayar". "Ga Shi ma". Ta mik'a masa. Ya karɓa yana fad'in wanene ne?" Yana jin muryar oga Asad ya daidaita ya ce "Yaya barka da yammaci ". "Yauwa Dama zan tambaye ka zaka zo me ko kuwa ita ta zo gobe?" "A a zan zo in sha Allah wajen 2 haka". "To shikenan sai ka zo". Ya kalli Bilki da take kallonsa.ya ce "Ya ce zai zo". "Tom shikenan Allah ya kaimu". Sulaiman ya mik'awa Abida wayarta. Ta karba ta had'a da hannunsa ta rik'e. Ta marairaice ta ce "Ka yafe mini Yaya Sulena?" Ya harareta ya ce "Ai na ga alamun da isgi6ma kike bani hak'uri. Yaya Sule, Yaya Sule tamkar kina son na ji baush6ne tunda ai idan kin so yi mini Ta'adi me kike fad'in Sule." Ta yi maza ya ce Dr yaya Sulaiman, mijin Abidan Baba, Baban junior. Allah ya taya ni baka hak'uri. Allah na son mai afuwa ka yafewa k'anwarka masoyiyarka. Ni fa Sai yanzu na gane ashe tun da can ma Yaya Sule kwamushe zuciyar Abida ya yi shiyasa take ganin sauran maza a ragwage ashe dr take Kira. Shiyasa yana tayawa Kara karbe shi babu gardama. Wataƙila fa da ka yi nauyin baki na rigaka furtawa tsabagen ka tafi da ni. ". Bai san sadda gajeriyar dariya ta k'wace masa ba tare da fad'in "Da dai ba Abida ce ba". Itama ta murmusa ta ce "Da gaske fa Baban junior ka ga yadda ka hadu ne? Ga ka dogo wankan tarwada ga hanci ga ka namiji a tsaye. Ga ilimin addini ga na zamani. Ga hak'uri da yafiya, ga girmama iyaye, ga son y'anuwa, ga adalci ga iyalinsa. Idan harkar odafare ne ba sauki sai an k'ure Abida. Ya ya kuwa ba zan mace a kanka ba Dr Baban junior?" Save Restricted Content Bot, [Oct 28, 2025 at 11:10] "Ya mike tare da fad'in "Allah ya shirye ki".
Itama ta mike tare da bude masa dukkan hannuwanta alamun ya zo ta rungume shi. Shi gabad'aya sai ya ga tamkar da jinnun a tare da ita da gaske. Ta ce "Zo mana tunda dai mun shirya ka kuma gane sharrin jinnu ne masu son ganin bayan aurena". Hawaye ya k'wace mata. K'warai da gaske ta kife shi. Yaa rasa mai zai ce don kuwa tsakaninsa da Allah ta kunna shi tunda ta yi masa sanadin ganin k'ananun kirjinta da suke motsa shi. Ya yi jarumtar cewa "Yanzu za ki ba ni passport din, ko ba za ki ba ni ba?" Ta zuba masa ido, yayin da shima ya zuba masa nasa idanuwan. Tsawon dakika goma suna kallon junansu. Sulaiman ya gama gamsuwa Yana son Abida har yanzu. Shi ya fara janyewa daga kallon. Ita kuma cikin rashin kuzari ta ce "Ba zan baka ba, don kuwa ina da hak'kin kulawa da tarbiyarka. Ba zai yiwu na yi sakacin da zaka sake tserewa ba. Ko ina zaka tafi, kafata kafarka matuƙar da aurenka a kaina". Da mamkin kulawa da tarbiyarsa da ta ce. Ya ce "To kuma idan babu auren fa?" Zuciyarta ta harba ta ce "Ai nasan zaka yafe mini, ba zai yiwu na yi zaman jiranka a banza ba". "A takaice ya ce "ai kuwa kin yi ma". Nan da nan ta hauro. Ta ce "Yaya Sulaiman tsakanina da Allah Ina son ka yi hakura ka yafe mini, na fi son ka huce, ina son ka hak'ura Allah me shaidar Hakan. Amma fa gaskiyar magana na fara gajiya, don laifin nan ba da gayya na yi ba. Sharrin jinnul Ashiq ne amma ka cije ka kafe gaskiya kuma na fara kaiwa gejin rarrashinka ya ya haka ne?" Ya hassala ya ce"Abida ki fa bini hankali, ki fa shiga taitayinki." Idonta akan fuskarsa ta ce "Har a sannu na bika, yanzu muka a guje zan n bika don Wallahi na gaji. Ina da bukata mahaifata na buk'atar jin ruwa na gaji ko ka zuba mini, ko ka raba ni da zaman zullimi haba dan Allah shekaru hud'u ai ba watanni ba ne." Ya girgiza kai ya nuna mata k'ofar fita tare da fad'in "out". Ta rausayar da kai ta ce "Yaya Sulaiman tsakanina fa da Allah na gaji. Ko dai ka yi hak'uri ka yafe mini, ko ka gajarce mini zullimin da nake ciki akanka. Fito kawai ka fad'a mini makomata." Ya sake girgiza kai ya damko hannunta ya ce "na damka miki damar aurenki a hannunki, idan kin so ki rike, idan kin ga hagu ki tankwabar da shi. Ta yi maza ta fizge hannunta ta damke hannuwanta da kyau. Murya na rawa ta ce "Na damke shi da kyau." Hawaye ya k'wace mata. Ta ce "A ina zan zauna ina son komawa gidana". Kaitsaye ya ce "Ban da shi a yanzu". Daga haka ta ce "Ya yi kyau na gode sai anjima."
*Umm Aslan&Asalah Egyptian Items* *Egyptian abayas* *Egyptian nighties*. *Bags and jewelries* *Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria* *Tuntube ta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*. # +201121544627 # +2349162662750 *DINGISHIN KWAD'O 4* *BY* *SURAYYA DEE*
*PAY 1K VIA* 2384876855 *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* 08032773332.
Cikin gaggawa ta fice ta bar masa d'akin tare da kudirin ba zata sake nemansa ko ba shi hak'uri ba. Ta yi iya yinta ta jure komai. Ta ba na shi hak'uri irim hak'urin da bata yi zaton zata bawa namiji irinsa ba. Don haka enough is enough ba zata sake bibiyarsa ba zata kame.
Yayin da ya bita da ido, tare da ayyana ta yi fishi don ya ga yanayinta ya fita daga yanayin salamar da ta aro ta tafawa kanta tunda suka yi arba. Gabad'aya sai yake jin wata irin damuwa ta yi masa k'awanya tunda ga k'asan zuciyarsa.
Kaitsaye ɗakinta ta shiga ta dinga kuka tamkar hawayenta zasu kafe. Ita kam ta gaji ba zata sake zuwa yana disgata ba. Idan Allah yasa an daidaita haka take so. Idan kuma ya gama yanke shawarar ba zai sake zama da ita ba, Kawai ya fito ya furta ya sahale masa idan ya so ya biyata basukan da take binsa ta cigaba da aikinta da addu'ar ta samu nutsuwar zuciya. Junior ya yi lakwas Yana kallon tana kuka wiwi. Murya ba amo ya ce "Ammi Ki Daina kuka. Ba kin ce Idan Dadyna ya dawo ba zamu dinga kuka ba, ba zamu dinga zama a d'aki ba?" Ta kasa bashi amsa a dalilin haka ta dinga fad'a masa a lokutan baya kafin bayyanar Sulaiman. Ga shi ya dawo kukanta na na neman ya zarta sadda ba'a gan shi ba. Gabad'aya ya taurare ya murd'e ya k'i barin komai ya wuce a tsakaninsu. Cikin Kuka ta ce "Ya k'i ya dauke mu, mu tafi gidanmu junior " Ya ce "To zan je na tambaye shi"
Ta kasa cewa komai. "Ammi na je?" "Je ka". Ya sauka da gudu ya fice zuwa d'akin babansa.
A bakin k'ofar ya tsaya ya dinga bugun. Dr Sulaiman cikin kasala ya ce " shigo". Junior ya shiga. Ya tsaya ya ce "Ammi na kuka, zamu tafi gidanmu". Sulaiman ya mike ya isa kusa da yaron ya d'auke shi ya daga sama. Ya zauna bakin bada ya rungume Shi a jikinsa. Yaron ya dinga sakin ajiyar zuciya. Haka kawai tausayi mai tsananin gaske ya shake Sulaiman jin yaro na ta sakin ajiyar zuciya jikinsa. Jini ba k'arya ba ne. Ya shafa kansa ya ce "Sulaiman". Junior ya kalle shi ya ce "Ammi fa ta hana su Farha da Noor ce mini Sulaiman ta ce sunan babana ne". Sulaiman ya murmusa ya ce "Ta ce " maka sunan dadynka Sulaiman" Kai junior ya daga masa. Ya ce "ka ce qwa Ammi ta daina kuka idan na dawo daga Kano zan d'auke ku mu tafi gidanmu ". Junior ya fara tafin murna ya ce "Zaka saka ni a school din su Farha" Sulaiman ya girgiza kai ya ce "Dadynsu mai kudi ne kai kuma dadynka mai allura ne. Zan saka ka a wacce zan iya idan muka tafi garinmu". Junior ya yi shiru ya ce "Ina ne garinmu?" Har Sulaiman zai ce Funtua sai ya yi maza ya ce Katsina ". "Ya ce "to yaushe zamu tafi?" Sulaiman ya dinga mamakin surutun dan yaron. Ya numfasa ya ce "Idan na dawo daga Kano". Ya mik'a masa hannu ya ce "promise?" Dariya ta kubucewar Sulaiman ya ce "promise". Suka k'ulla alk'awari. Yaron ya juya a guje don ya faɗawa uwarsa zasu koma gidansu ta daina kuka. Ya je ya fad'a kuwa. Ta daure ta daina kuka amma ta yanke shawarar ba zata kuma bibiyarsa ba. Za ta dinga addu'a tare da buga masa wuridin da zai kasa shareta. Amma ta gaji da yadda yake wulakantata.