Kenza eBookz

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 36

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 36

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 36: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 36. 🖤 BA NI DA IKO... *Littafin Farida Abdallah* *Ku zo mu yi…

3,689 words

*Abuja* Farinciki da walwala tare da fahimtar juna sun samu muhalli a gidan oga Asad. Don tunda ya gano abubuwan da yake yi suke tunzura masa sarauniyar sheba shikenan ya kiyaye yinsu a gabanta mussaman yin kwatance da maimurabus ta bakinta da fada. Ya barta a zuciyarsa yana bin ta da adduar rahama don kuwa ba zai yiwu ace ya manta da ita ba. Yayin da Bilki take kaffa kaffa tare da kiyaye yin abin da zai saka ya murd'e mata tunda ta fahimci so baya hana shi ya nukurkusa mace da bak'in ciki mai saka kuka da rama a tsaye, idan ta nemi raina shi ko bijire masa. Dan haka suke zaune K'alau cikin mutunci da girmama juna. Amrah da Faruk junior sun isa gidan sun samu karɓa daga dukkan ahalin gidan. Don Amrah ma a d'akin Bilkisu take, tare suke kwana akan gadonta. Haka Su Hafcy da Aysha basu bada matsalar koami ba. Ga khadija ta zo hutu wanda watanni kad'ai suka yi saura akan ta kammala gabad'aya. Don haka gidan a cikin hada hada yake mai dad'in gaske.

Baba ya faɗawa ya'yansa Sulaiman zai mayar da shi Funtua. Gabad'ayansu babu wanda ya yi raddi. Oga Asad ne ya ce "To Baba ai sai an shirya don gyaran da za'a yiwa gidan nan ai ba kad'an ba ne". Baba ya ce "A a tuni Sulaiman ya kammala. Kai naka ido ne an hutar da kai an gode maka oga Asad". Yau ma dariya ya yi don kuwa idan baba ya ce masa oga tunda ga zuciyarsa dariyar take fitowa.

Ammar din Faruku da yake shiga shekarar k'arshe a jami'a. Tunda ya k'yalla ido ya ga Amra ya ji a ransa ya yi mata. Rashin hayaniyarta da nutsuwarta sun yi matuƙar burge shi. Mutumin Bilki ne na sosai. Sannan yadda Faruk yake da haba haba da fatan faran haka shima yake. Da yammaci ya isa gidan. Kaitsaye ya haye saman Bilki yana fad'in "Mahmah Mahmah". Bilki na zaune akan kujera ita kad'ai. Alti ta bi yaran sun fita. Ta kalle shi ta ce "Ammar ka yi ta faman doka mini k'ira tamkar makaho". Ya yi dariya ya zube a gabanta akan kafet. Ta girgiza kai ta ce "Fadi yau kuma da me ka zo?" Ya ce "Mahmah kin ce ke ce mai saka mini lallen aure ko?" Bilki cikin alfahari ta ce "K'warai da gaske don kuwa Yaya Salaha da Yaya Hamida dolensu su hak'ura don sun san ni ce mafi kusa da Abbanka". Ya ce "To Alhamdulillahi Mahma. Yanzu kuma idan Amrah ce amaryar fa?" Zuciyarta ta harba da saurin gaske. Dole dai soyayyar nan ita da Yaya Faruku sai Allah ya kullata akan yaransu. Idanuwanta suka ciko da k'walla. Ta shanye kukan ta ce "Ko ita ce don kuwa kaine d'ana ba ita ba, ita ma k'anwar uba ko yayar ubanta ce mai saka mata lallen. Amma fa Ammar bata kammala sakandire ba yanzu ne take ajin k'arshe ". Ya jijjiga kai ya ce "Na sa ni Mahmah. Nima ai sai bana zan kammala digirin farko, kawai ina son ta san da zamanka Manya ma Su sani don ABBA ya ce mini nauyin baki na sakawa a rasa abin da ake so mai k'ololuwar daraja." Ta yi shiru amma so take ta rushe da kuka. Ta tabbatar Yaya Faruku ne ya ce ya faɗawa Amrah idan har yana sonta da gaske. Kafin ta yi magana ya ce "Ki faɗawa Dady don Allah. ABBA ya ce "Shine babana shii zan faɗawa, ni kuma ba zan iya faɗa masa ba". Cikin jarumta ta ce "Zan fad'a masa kuwa don tasan ba zai iya din ba da gaske saboda idan Baban Bilkisu na guri nutsuwar da yake yi ta daban ce. Ya nisa ya ce "Zan fad'a mata don nima a tsorace nake kada wani ya yi mini shigar sauri". Bilki bata ce komai ba don kuwa yana da gaskiya itama k'addara da rabon haihuwarta da Faruku ne ya sanya Sahal yiwa zuciyarta da take son fari mai kyau kutse alhalin bai fi ya zo a dan aikent ba. Sai dai dama ta kud'ire a ranta ba zata bari Amrah ta yi irin kasassbar da ta yi yayin zancen mijin aure ba. Shiya6duo sadda suka zauna take yi mata bitar kyaun namijine abu na k'arshe da zata duba. Addininsa da halayyarsa tare da nasabarsa sune a farko. A yanzu da Bilki take cikin shekarun hankali ta gane abin da take ji akan oga Asad shine so wanda bata ji ko da kwatar hakan a zuciyarta akan sahal ba. Haka nan yadda take girmama tare da mutuntunta duk abin da ya shafi Yaya Faruku ta gane kauna ce wanda babu abin da zai shafe ta a zuciya. A fili ta furta "Allah ya tabbatar da wannan batun, na yi murna. Allah ya saka albarka ". Ammar ya mike ya ce "Ameen Mahmah na samu k'warin guiwa dan haka na samu nutsuwa". Bata ce komai ba . Ya ce "Ina yanmatan na ki, yau gidan babu dad'i shirunsa ya yi yawa". Ta ce "Aysha te debe su sun fice". "Har da twins?" Ya tambaya a takaice. "Hmm har da su kasan Alti da son ta yi yawo ta ga Abuja. Har yanzu bata gaji da ganin titunan Abuja ba". Ya yi dariya tare da fad'in "Da fa zuwa na yi na d'auki takwaran abba mu yawata gari, shi kad'ai a cikin mata". Ta ce "Ai kuwa shiyasa ma baya wani d'okin zuwa sai dai ka dawo gobe idan Allah ya kaimu". Ya ce "Zan dawo".

Ya tafi Bilki ta bishi da kallo tare da sake girmama ikon Ubangiji. Ta fad'awa oga Asad sakonsa shima ya yi murna ba kad'an ba. Amma ya ce "Karatu zata yi tunda tana da k'ok'ari dan haka ba yanzu za'a yi magana ba. Kawai dai ya dinga nuna mata cikin hikima yana sharewa kansa hanya. Can ya kalli Bilki ya ce Amma kuma idan itama ba mai fahimtar share hanya da raragefe ba ce ba fa?" Ta yi dariya ta ce "Baban Bilkisu ba fa zan gaji da baka amsa da fad'in cutata ka yi da ka k'i bayyana da k'arfinka ba. Wacce mace ce zata tankwabar da tsadadden namiji irinka a cikin hankalinta?" Dad'i ya kama shi amma cikin alhini ya ce "Amma Maigado a karo na biyu ma da na bayyana da karfin nawa ai kin tankwabar da ni. Sai da na shiga rigar Faruku fa sannan kika amince da ni". Ta dan murmusa tare da cewa"Yanzu fa? Baka gama mamaye zuciyata da kalolin soyayyarka da yakanarka ba?" Ya murmusa ba tare da ya gamsu ba. Ta sake shige jikinsa ta ce "Ban fa so wani a duniya irin ka ba Baban Bilki, don ban tab'a jin ina kishin wani namiji a duniya irin ka ba." Wani irin dad'i ya kama shi amma sai Ya ce "Maigadona ki fad'i gaskiya. Anya kuwa, kin fa so yaron nan, sannan Faruku fa?" Ta ce "Na fi sonka fa akan komai da kowa. Shi Yaya Farouku ina rasa wa na fi so tsakaninsa da Yaya Sulaiman. Amma babu tantama nafi jinsa fiye da Ansari ". Oga Asad ya saki ajiyar zuciya tabbas yanzu ya gamsu tana sonsa ba shine kawai yake dakon soyayyarta ba. Ya jata jikinsa ya kankame yana sake jin tana mamaye kowanne loko da sako na zuciyarsa. A wannan ranar suburbubudar da ta sha a hannunsa mai matuƙar tsayawa a rai ne, haka nan mai sakawa ta yi ta sonsa ne. Tana samun nutsuwa da gamsuwa a duk sadda ta shiga hannun oga Asad. Basa yiwa juna k'wange a wannan fagen.

***"" Sulaiman na zuwa Kano ya kwana biyu ya dawo Funtua. Yana ganin masu lalurar ido a matsayin babban likita a asibiti Makka eye Hospital. Abida Na zaune tana cin hadasden Ciccibin bojuwa herbs Kano da ta yi order dinsa jiya. Da yake da kankararsa ya iso Mata Sai ta jefa Shi a freezer shine Sai yau ta yi warming take ci. Sulaiman yana kallonta ta ce Na iya mata ne. Ya jijjiga kai ya ce "Ke da Bilki munubarku da yawa Wallahi. Ku dinga yi mana a hankali. Ku ta kid'ima mu haba dan Allah. Oga da kansa da na gansn a gaban Bilki Sai da na rike baki". Ta k'yalkyale da dariyar nishadi tare da fadin Baban junior ina ce dai kana jin Zamzam?" Ya Sosa kansa ya ce "Idan gaskiya zan fad'a cicif nake jin ki Abidan Baba ". Dad'i ya kamata ta kuma tabbatar kayan Bojuwa babu algush kodayake duk kayan da Bilki take tallata mata babu na banza. Bojuwa herbs 08032773332 For your order. Ta ce "To kwalliya ya biya kudin sabulu tunda ka yaba".

Kamar yadda aka yi alk'awari jiya tara ga wata Sulaiman ya dira a Abuja tare da junior. Ba yadda bai yi da Abida ba akan su tafi tare ba ta k'i. Ta kafe akan zata zauna ta yi musu girkin tarabarsu. Don tun jiya laraba aka bude wajen ta kamawa Razina suka gyara gidan ya yi fes. Ita dai Abida mamakin yadda Yaya Sulaiman ya kashe makudan kudade take yi wajen gyan gidan. Bangarensu baba ma komai sabo ya zuba musu. Ta tsinci kanta da addu'ar Allah yasa kada Dady ya ce Baba ba zai dawo ba. Ta tabbatar Dr Sule ba zai yarda ya dawo shi kad'ai cikin kwanciyar hankali bw mussaman yadda ya tafi da k'arfi da guiwa da farinciki. Haka gyara b'angaren Baba da ya yi ta tabbatar bai d'auki al'amarin dawowarsa da sauk'i ba. Ranar goma ga watan goma jirgin da ya dauko su daga Abuja ya sauke su a Kano. Suka shiga motar Sulaiman da ya barta a airport suka d'auki hanyar Funtu. Daga baba sai momi sai junior. Yaya Faruku zai dawo amma sai ya kammala da komai sai ya dawo tare da iyalinsa. Ammar dai zai zauna a gidan oga Asad ne ya cigaba da karatunsa da kuka da harkokin Babansa. Yan aikin Momi tare da mai gadin gidan wanda shima asalima dan Funtua ne James zai tuko su a motar Baba.

*Lame.Ng Skin Beauty and wellness* *Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.* *07036662633*

Cikin nutsuwa Sulaiman yake tuki don baba baya son gudu. Lafiya lau suka isa Funtua. Baba ya dinga mamakin yadda gidan ya zama sabo. Ya tsaya a farfajiyar gidan yana kallon tafkeken gidan nasu. Wanda tazarar da ta tsakanin shashi zuwa wani shashin ba kad'an bane. Amma gabad'aya Sulaiman ya gyare gidan ko ina sai d'aukar ido yake na ban mamaki. Wani irin abu ya mamayi zuciyarsa shikenan zai yi rayuwa a gidan babu Baba k'arami. Hawaye ya k'wace masa da ya hango jikin bishiyar da yafi Zama a k'arkashinta matuƙar bai tafi Ladi farm ba. A fili ya ce "Allah ka jiƙan Isah ka gafartawa mahaifanmu". Sulaiman ya yi maza ya ce "Ameen Baba. Allah ya kara maka lafiya da hak'uri tare da nisan kwana mai albarka." Momi ta ce "Ameen Ameen". Daidai lokacin Abida ta fito tana yi musu barka da zuwa. Suka dunguma suka shiga b'angaren Baba. Mamakinsa ya fad'ada ya ce "Sulaiman irin wannan hidima bata yi yawa ba kuwa? Ka yi ta'adin kudade masu nauyi fa". Cikin nutsuwa Sulaiman ya ce "Da ina da ikon yi muku fiye da hakan da na yi Baba ". Dad'i ya kama Baba ya ce "Kai madallah da Dr Sule angon Abida k'anwar Bilkisu ". Dad'i ya ratsa Abida ta ce "Ameen Baba ". Yayin da Sulaiman ya yi maza ya ce "A a malama daina yin murmushi don an ce angonki, ke uwargida ce." Ta yi dariya tare da fadin yaya Sule kenan". Saia suka yi salla suka huta. Sannan Abida ya gabatar musu da abinci. Tare suka ci gabad'ayansu a falon. Kuzarin Baba ya k'aru. Zuciyarsa ta cika da annuri. Yana jin zuciyarsa na warkewa daga takurar da take ciki. Addu'a ya yiwa Sulaiman tafi cikin kwando. Yana yi yana nasihar ayi ibada, a yi hak'uri da juna, a yi zumunci a kuma kuma kula da marayu don Annabi ya ce kafaɗa da kafaɗa zasu shiga aljanna da mai kulawa da maraya". Abida ta ce Razina ta zauna a shashin Momi ta dinga yi mata aiki kafin nata yan aikin su iso gobe. Sai yamma sannan ta yi musu sallama ta tafi wajenta. Sulaiman kuma ya fita cikin gari da junior. Oga Asad da Bilki sun fi kowa kewar Baba don sun kad'ai za'a bari a Abuja. Sai dai dukkansu sun gamsu tare da amannar komawarsa Funtua shine mafita mafi kyau. Don shi da kansa yafi son zamansa a Funtua. A hankali Faruku ya kammala parking din komawa Funtua. A wannan karon kuma a cikin gidansu zai zauna kamar yadda Sulaiman ya yi fata. Gidansa kuma an gyara an bawa local government hayarsa tana saukar baki a cikinsa.

Sulaiman da Faruku sun fara shiga Ladi farms suna ganin durk'ushewar da ta yi ba kadan ba ne. Akwia dabbobi sai dai ko kusa ba irin na da ba ne. Madarar da ake yi a da yanzu ba a iya yinta. Ba gyara irin na da. Don haka su uku. Oga Asad, Farukun, Sulaiman suka zuba makudan kuɗaden wahen ganin Ga gargadi. Aka gyara duk inda yake da gyara. Aka yi orders din shanun da suke bada madara masu yawa. Sannan aka siyo k'ananun dabbobin da babu irinsu a yanzu a gidan gonar. Anyi haka bisa sharadin idan gona ta fara bada riba za'a biya kowa kuɗinsa da ya zuba da ribarsa. Sai a dinga biyan ma'aikatan tunda ga kan Faruku har zuwa masu shara. Sauaran kudin kuma yana asususn baital man da za'a dinga yin hidimar wakafi da su.

Komai ya gama daidaita Ladi farm ta fara aiki k'arkashin Jagorancin Faruku Musa Funtua.

Ba jimawa Sulaiman ya fara shirin tafiya saudiyya tunda watanni biyu aka bashi. Zai je ya ajiye aikin ne daga nan ya tattaro komai nasa ya dawo gida gabad'aya.

Abida tunda ta ga haka ta tsiri kukan da yake daga masa hankali. Kuma bata yi sai yana gida. Juyin duniya ta ba shi passport d'insa kuma ta ce bata dauka ba. Wani dare tana zaune har shabiyun dare tana masa kuka tamkar Mai wake. Hankalinsa ya kai koluluwar tashii. Ya ce "Za ki dawo da halayyarki ko Abida? Bana son kuka amma kullum sai ki tisa ni a gaba kina tayar mini da hankali ko? Na ce miki ba dadewa zan yi ba, zan dawo. Amma kin ki yarda da ni. Yanzu fad'a mini menene damuwarki akan tafiyar da zan yi?" Cikin kuka ta ce "Zamu raka ka ni da junior." "Abida junior ba shi da passport kafin ayi ya samu visa long process ne, kuma bana son mu tafi gabad'ayanmu mu bar shi, shi kadai kuka zai yi". Ta mike ta fita zuwa d'akinta ba jimawa ta dawo da passport din junior da nata. Ta mik'a masa ta ce yana da passport ga shi nan". Ya ce "To d'auko mini nawa." Ta yi shiru. Ya ce "Kin ji". "Ni fa dadyn junior ban gan shi ba, amma ka gama mana namu shirin zan duba maka a hankali cikikn kayanka ko za'a dace a gan shi ai baka da matsala don ticket kawai zaka siya." Ya ce "Allah ka shiryi Abida ". Haka ya shirya musu tafiya tare da ita da junior sannan hankalinta ya kwanta. Sai da ta ga Komai ya tabbata kowa yasan tare zasu tafi. Ta lallaba ta ajiye masa cikin kayansa a inda zai ga ni. Ranar da ya ga ni kuma ta hakikance dama tasan a gunsa zai fito don ita bata dauka ba. Haka ya yi shiru yana kallonta.

Sun sauka a Jiddah lafiya lau. Kwanansu uku a Jeddah sannan suka wuce Makka suka sauke umra. A hotel suka kwana Sai da ya je ya bude gidansa aka share aka gyara sannan ya je ya dauko su ya kai Su can. Shi kuma ya dinga zirga zirga a asibitin Saudi Germany har ya kammala da su. Basu yarda sun sallame Shi gabad'aya ba. Kasar jamus ta ce nan da shekara d'aya ya dawo ya cigaba da aiki da su don sosai suke jin dad'i aiki da Shi. Sannan rife shi da ta yi ba bisa k'aida ba sai suke ta girmama shi tare da rarrashi don sun san an shiga hak'kinsa. Yayin da k'asar Saudiya kuma suka d'auke shi aiki amma a asibitinsu Na Makka da yake Kano. Dan haka Idan shekara ta cika Yana son dawowa ya dawo ya cigaba da aikinsa. Idan kuma zai cigaba da yi a Nigeria shikenan. Kullum safiya zata tashi ta gyara gidan ta yi musu abinci, sannan tayiwa junior wanka. Komai da wuri take yi ta kammala. Rannan Sulaiman ya ce "Abida yanzu ba ni da duty ne a gidan tunda babu yar aiki?" Ta rike baki ta ce "Dadyn junior aljanna nake nema tuburan. Na yafe maka da din ma da na dinga raba mana duty ba a hayyacina nake ba duk sharrin jinnul Ashiq ne". Ya yi dariya sosai don ya tabbatar Abida ta ajiye duk wani zafin kanta da tunanin aure ba dole ba ne. Satinsu uku sannan sukka dawo Nigeria ya fara aiki a babban asibitin Funtua. Da kuma Makka eye Hospital. Zancen budurwa ya bi ruwa. Litinin da talata yake shiga asibitin Funtua. Sai ya tafi Kano laraba da safe. Ya ga marasa lafiya laraba da yamma da alhamis da safe Har zuwa yammaci. Sai ya dawo Funtua juma'a. Asabar da lahadi kuma yana tare da Yaya Faruku a Ladi farm. Abida ta cigaba da aikinta a general Hospital Funtua. Amma Sulaiman ya tabbatar mata zasu koma Saudiya da zama next year sai ta zurfafa iliminta a can ba zasu dawo ba Sai sun tumbatsa da ilimin likitanci. Ta ji dad'i sosia. An saka junior a makaranta mafi kyau a Funtua. Tare da yaran Yaya Faruku suke tafiya.

Hutun December Na k'arshe shekara gabad'aya yayan gidan da ya'yansu sukanhadi a Funtua dan yiwa Baba barka da dawowa. Har munira ta zo k'asar. Oga Asad da iyalinsa kaf, Usman da nasa iyalin, haka Hamida da Ansari kowa kwansa da kwarkwata, Saddiqa da Anisa da Yaya Salaha. Gida ya cika damkam. Oga Asad ya tura mota aka d'auko Faruku da Amra. Tunda Anisa ya koma Yola. Su da kansu sun tabbatar Idan zasu yi biki ko basu gayyaci kowa ba to kuwa kowa yana isu isu zasu cika taron. Bare a hada da sauaran dangi. Su Bilki suka hadu gabad'ayansu suka ke gidansu su MAMI da gidajena y'anuwanta suka gaishe tare da yi musu alheri. Sati guda suna tare kafin a hankali kowa ya koma inda ya fito da iyalinsa. Zuciyar kowa cike da farincikin dawowar gidansu tamkar shekarun baya. Baba K'arami da MAMI suna shan addu'o'i don su kad'ai ne babu su.

*Watanni biyar a gaba.* Oga Asad da iyalinsa cikin wani shararren shagon gwalagwalai a birinin abudhabi na k'asar Dubai. Shirye shiryen bikin ya'yansu suke yi gida uku. Aysha khadija da Hafcy. Dan haka ya shirya musu tafiya don su yi siyayya. Dukkansu ya ce kowacce ta d'auki sarka da bangles yaran kuma Bilki ta taya su zabe. Dan haka suka dinga d'aukar design da ya kawata da su. Yayin da Bilki take taya Amal, Noor da Farha zabe. Suka kammala ya ce "ke ba ki d'auka ba". Ta murmusa ta ce "Na ga ka siya mini sarka da bangles sannan ina da wasu ma. Sun isa. Ya yi shiru yana mamakin yadda sam bata da zalamar abin duniya haka take tin filazal. Ya hasaso kura Abida da ita ce da tuni ta d'auki makekiyar sarkar da zai yi wahalar gaske ta skaa ta a wuyanta. Da wata ce ta ga ya siyawa ya'yansa mata shida abubuwan da suke cinye kudi mai yawa da sai ta ɗiba itama. Ya numfasa idonsa ya sauka kan wani dunkulallen zobe da zai yi nauyi a ma'auni ya ce "Wannan zai yi kyau a yatsanki sarauniyar shaiba. D'auki ki mayar da gurbin wanda kika bawa Autar Momi da bata gajiya da tara dukiya." Ta ce "Na gode." Washegari ya fita shi da ita. Yayin da yaran ma suka yi tafiyarsu daban tare d Alti da tagwaye. Kaitsaye shagon jiya suka koma. Ta dinga mamakin hakan. Na zato ya ce "Ki d'aukarwa Amrah sarka da bangles irin Wanda bilkis6ta d'auka". Dad'i ya ratsa ta don kuwa ta kud'ire zata dawo ita kad'ai ta siya mata irin wacce zata iya siya. Sai ga shi ya shayar da ita mamaki. Sosia ta ji dad'i. Bata gama mamakin hakan ba ya d'auko mata wata iron sarka mai balls tamkar dai carbi. Kallo daya zaka yi masa ka gane ya kerewa gold daraja. Kudinsa ya zarta kudin duka sarkokin da suka siya. Ya ce ina son murjani tunda ga wannan sai ki dinga mini kwalliya da shi sarauniyar shaiba. A gun ta rungume shi tana fadin "Na gode Baban Bilkisu, Allah ya saka da alheri ya shirya zuri'a."

*Duk wacce ta siyi littafin nan bamu yi saving contact din juna ba.* *To ta yi mini magana na yi saving contact ɗinta.* *Don samun discount yayin siyan kayan garari na Bojuwa herb's*. *Na gdoe Allah ya saka muku da alheri* 08032773332. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:31] *DINGISHIN KWAD'O* *SURAYYA GWARAM* 08032773332.

*Fatan alheri ga Dr Fadila Kabir* *Na gode da kokarinki da shwarwarinki*.

*Allah ya albarkaci su Maheer*. *Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*. *Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*. *Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Just DM for your order @08033773332*.

Chapter notes and social links

🖤 BA NI DA IKO... *Littafin Farida Abdallah* *Ku zo mu yi tafiyar da babu nadama a cikinta*. *1k ne a manhajar telegram* *7039080978, Opay, Farida Abdullahi. Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 07039080978*.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull