Kenza eBookz

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 37

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 37

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 37: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 37. Khadija da ba za'a yi mata jere ba tunda a London zata…

4,280 words

Khadija da ba za'a yi mata jere ba tunda a London zata zauna ya sanya Bilki ta saka aka kara mata sarka da manyan warwaraye tunda y'anuwanta siyayya ake yi musu ta alfarma. Sun kammala siyayyar suturu da kayan kicin a Dubai. Suka zarce Turkey don oga yafi son asalin katakon k'asar turkey masu k'ololuwar daraja fiye da na Dubai. A can aka yaye twins da suka shekaru d'aya da haihuwa. Hafcy da khadija masu son hidimar suka shirya musu birthday celebration a wani kayataccen waje a birinin Istanbul. Sati biyu da dawowarsu Abuja Wanda ya yi daidai da bikin Laura wanda dama tazarar sati uku ne tsakanin bikinta da na su Aysha. Tuni kuma Bilki ta yiwa Amare order din sanyin flusher tare da bridal package daga Bojuwa herbs Kano. Kazar sababi ce kawai sai sati biki za'a turo musu wataƙila ma sai sun isa Funtua. Yara suna ta shirin tafiya Kaduna. Oga Asad ma a cikin hidimar take don da gaske shine uba.m ba abin da bai yi mata ba. Saura hud'u a fara biki ya Bilki ta shirya jibi zasu tafi Kaduna tare da yara zasu yi kwanaki hud'u su dawo. Shi sai ranar d'aurin aure zai zo. Ta kasa boye yadda bata son ta je. Ta ce "Baban Bilkisu gaskiya yara su tafi ni kuma mu je tare ranar d'aurin aure mu dawo". Ya zuba mata ido sosai har ta tsargu. Ya nisa ya ce "Ku je tare Maigado. Yarinyar a hannuna ta girma k'anwar Rukayya ce da tana da rai ai anan za'a yi komai, da bata raye kuma sai iyalina suje gabad'aya ba a tura yara kawai ba." Ta yi shiru tabbacin ita ba hakan take so ba. Tasan Surayya na can haduwa zasu yi da Laura da sauran y'anuwansu su tisa ta a gaba da kallo da zunde iri iri cikin isgili. Amma shi ba zai gane hakan ba. Menene aibu dan ta je rana daya ta dawo? Ya kalleta ya ce "Kin yi shiru sarauniyar shaiba. Ta sake yin shiru. Ya mike ya ce "Bilki jibi zaku tafi Kaduna tare da yara". Ya saka kai ya fice. Takaici ya shak'e mata wuya. Idanuwanta ya cika da k'walla. Akan me za'a ce sai ta je ta yi kwanaki a gidan da ba dolenta ba? Ita bata son cusa kai da shisshigi. Yara ne dole su je ba ita ba. Ko da ya dawo fuska a daure haka suka kwana kowa zuciyarsa na tunzure. Ya riga kuma ya kud'ire sai ta je Kaduna a gobe ko kuma ranta ya yi mummunan b'aci. Yadda ya fitittike ya dauki fishi ya sake hassala ta. Wato duk abin da ya shafi Rukayya bai d'auke shi da sauk'i ba. Da a ce ba sabgar da ta shafe ta ba ce ta tabbatar ba zai yi mata tilas irin haka bare har ya shareta ba. Bak'inciki kamar ta rusa ihu. Da yamma kan dole ta yarda Alti ta shirya mata kayanta a akwati. Tana hadawa tana fadin "Ni ban ga abin b'acin rai irin haka ba Mahmah. Ai da gaskiyarsa a hannunsa ta girma dole ki je a yi komai da ke. Bilki ta yi shiru don ba zasu fahimci manufarta ba. Kan dole da yamma da ya dawo ta shirya ta hau samansa don tasan idan ya cigaba da fishin goben ma ficewa zai yi ba tare da ya tsaya sun yi sallama ba. Idan kuma ta bar yara suka tafi su kad'ai ba sharewa k'alau zata yi ba, tunda ya kafe sai ta je, to sai ta je din kuwa. Ta shiga falonsa baya nan. Ta doshi cikin d'akin. Ta tarar da shi a kwance shame shame tabbacin a gajiye take matuƙa da gaske. Ta mak'ale a gefe bata isa gare shi ba, ba kuma ta juya ba. Ya kalli yadda ta yi. Dariya ta kama shi. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:33] Tunda ta zo ai yasan ta sauko ne. Dan haka ya had'iye fishinsa ya ce "Zo kusa da ni sarauniyar shaiba". Ta cuna baki ta d'auke fuskarta zuwa gefe daya. Haka ya yunk'ura ya tashi ya isa kusa da ita. Ya rik'o hannunta ya zauna sannan ya zaunar da ita kan cinyoyinsa ya ce "Na huce da Maigadon zinare. Ya ake ciki ne, menene?" Cikin shagwaba ta ce "Kai zan tambaya tunda kake yi mini fishi haka siddan". Ya ce " A a ba haka siddan ba dai sarauniyar sheba. Kin kasa gane ni me gabad'aya. Ni fa Na tsani gardama mussaman ace matar da nake aure ne zata dinga yin fito ma fito akan umarnin da zan bata. Na ce ki shirya ki raka yara biki menene abun damuwa ko bacin rai a ciki?" Ta yi shiru don idan ta ja al'amarin rikicewa zai yi. Daga nan ya zarce da rattabo mata alfarmomin Rukayya. Ta nisa a dole ta ce "To zan je". Ya rungume ta yana fadin yauwa Bilkisu yayar Abida". Ta murmusa ta ce "Amma dai Alti da twins su zauna a gida bana jin dad'i kuma su rikicinsu yawa ne da su". Ya ce "Anya Maigado kasalar nan ta ki da saurin hassala ba gamo kika yi ba?" Ta yi masa shiru don kuwa tabbas cikin ne da ita. Ya ce "Ku tafi tare da su. Alti ta dinga tafiya da su gidan saddiqa suna kwana. Amma ke da Farha da tare yaran nan kuna wajen Hajiya". Ta yi shiru a zuciyarta kuma fadi take yi shi a dole a ce kaf iyalinsa sun halarci bikin k'anwar maimurabus. A fili kuma ta ce "To". Washegari suka shiga jirgin kasa da yamma zuwa Kaduna. Suka tarar da motar y'ansanda suna jiransu. Hajiya ta karɓe su ba laifi. Amma da ta shiga dakinta sai da ta yi kukan ganin ahalin Rukayya babu ita sai wata. Surayya ma bata nuna mata komai ba sai dai kuma ba wata fuska. Anyi hidima lafiya an kammala lafiya. Oga Asad kuma ya yi musu mugun k'ok'ari ko Rukayya na da rai iyakacin abin da zai yi kenan. Hatta ruwan roba da lemo da aka dinga wadaka da du duka daga gare shine. Kayan d'akinta kuma masu kyau ya yi mata. Hakan ya rage musu zafin Bilki da tagwayen ya'yanta don sun gane bata gama da shi ba, kamar yadda suke hasashe. Bilki kam a matuƙar takure ta yi wannan zaman don yini ake ana shiga ganinta a d'akin da aka sauke ta tamkar hoto. Tana ganin Laura da sanyi flusher da sauran kayan gyaran Amare ta gane Aysha ce ta yi mata Oder din kayan don da lambar a jikin dukkan kayansu. Shine ta dauki lambar a jikin nata kayan ta yi mata order itama. Ya zo d'aurin aure ya ce su gobe zasu dawo tunda yau za'a kai amarya. Ta roke shia akan idan akan kai amarya ta wuce gidan saddika ta kwana mana gobe sai ta zo ta d'auki yaran su yi sallama da Hajiya. Bai k'i ba ya amince don ya tabbatar ta yi iya kokarinta kuma zuwa gidan saddika ya kamata. Washegari kuwa sai shida jirginsu(train) ya tashi zuwa Abuja. Ya dinga yi mata sannu da tare da godiya har kunya ta kamata. Kwanaki kad'an suka fara shirin tafiya Funtua don a can za'a yi biki da d'aurin auren su Aysha. Kowa a zuri'arsu kokari yake ya yiwa oga Asad alheri don ya gane sun gode da hidimar da yake da su da dukiyarsa da bata tsole masa ido ba. Mazansu da matansu kuwa. Ba yadda za'a yi a dumfare shi da sunan bsbu waji abu ko ana buk'atar abu kaza kowa yi yake yi kawia da dukkan k'ok'arinsa. Hakan ya dada sanyaya zuciyar Baba tare da gasgata Allah ya karbi rokonsa na a jefa soyayya da tausayin juna a tsakaninsu gabad'aya. Bilki da Abida tare da amare Kano suka tafi takanas don yin lalle. Don yin Bilki a Kano ta tabbatar bata sake samun wacce ta iya kunshi irin Maman Farhan ba. Tiryantiryan har Farawa. Yini guda su aka yiwa kunshin da ya amsa sunasa. Oga Asad kuwa mita yake ace sai an tafi Kano yin kunshi don tsabar fitina da wuyar zama iron na Maigado. Sulaiman na gefe na taya shi da fadin ai Abida da Bilki fitina da munubarsu ta kai k'urewa. A hanasu zuwa su tisa mutum da matse matsen k'walla mai sake rauni a kirji". Ya bawa oga Asad dariya k'warai da gaske. Ya ce "Haka kuwa suke yi Dr Sulaiman to ya za'a sai hak'uri yara ne ai ". Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:35] Duk wata nasiha da ta dace ba wacce ba'a yiwa Amare ba. Haka ma Baba da Momi da dukkan iyayen Amare kowa ya yi musu fad'a tare da jaddada musu hak'uri ne kan gaba a cikin aure. Dangin Rukayya sun zo da yawansu aka dinga ina ka skaa da su tare don kuwa komai da su ake yi ba'a barsu sun koka rashin wani abu ba. Sai dai duk inda Bilki ta gilma idonsu na kanta. Basu gaji da nunata ga waɗanda basu gama ganeta a bikin Laura ba. Lallen Bilki da Abida da na Amare ba k'aramin kyau ya yi ba. Kowa sai ya tambayi wacce ta yi. Yaya Hamida ta karɓi lambar ta ce tana komawa Kano zata je itama a ta yarfa mata. For kanawa contact her for your special lalle......09076460821 farawa layin Alkairi suya.

A lokacin bikin ne da manyan y'ansanda suka je d'aurin auren suka tisa da D.p.o da fad'an ace gida irin na su Oga Asad a garin Funtua babu d'ansanda ko daya da yake tsaron lafiyar iyayensa da danginsa? Ya dinga bada hak'uri tare da girke y'ansanda har shida a gidan. Wasu a bakin gate wasu a farfajiyar gidan. Wasu kuwa a bayan gidan. Sai da oga Asad ya ce sun yi yawa a bar guda biyu sun isa. Anyi taro lafiya ana gama lafiya an kai amare gadajensu a Abuja Aysha da Hafcy. Khadija kuma satin sama zasu wuce da mijinta London a can zata zauna. Dangin Rukayya sun koma da shatara na kayan arziki iri iri. Tunda kan kayan gara har zuwa kayan sabeniyos kala kala masu d'auke da sunan amare. Mussaman irin plates din ralzaplace08109544470. Da aka ci abinci da su a bikin sannan kuma har da su aka raba. Wato anyi harkar arziki, bikin girma aka yi. Da kansu sun gamsu Rukayya ta yi aure a cikin ahalin da suka san alheri suke kuma kamanta shi. Don kuwa oga Asad da dukkan iyawarsa yake girmamasu fiye da sadda take raye. Hidimar da ya yi a auran Laura da yadda aka karrama su a wnanan bikin ya rage jin zafinsa da Hajiyarsu Rukayya take yi. A hankali kowa aka fara tafiya. Munira ta fara wucewa. Sannan Usman da Salaha da Ansari. Kowa cikin farinciki yake. Oga Asad kuwa sai da ya yi kukan murna na yadda kafatalin kannensa suka hana shi jigata a bikin. Ya dinga godewa Allah da aka yi hidimar bikin bayan an yi sulhu dan ya tabbatar su Hamida ba zasu zo ba da ba'a yi sulhun ba. A ranar da zai tafi ya durkusa gaban Baba ya ce "Baba Allah ya saka maka da alheri, Ubangiji ya karbi hidimar da kake yiwa zumunci. Na gode da auren Bilkisu na gode da komai Allah yasa ka gama lafiya". Baba ya ce "Allah ya tsare ya dafa maka ya taimakeka akan girman da ya hau kanka. Ka zama mai hak'uri ka ninka juriya akan komai. Tawa ta k'are ko yau ma mutu na bar dukkan yaran nan a hannun Allah da hannunka. Ka yi hak'uri da kowa dan Allah". Dukkansu hawaye suke yi cikin alhini. Haka ya tisa iyalinsa suka tafi cikin kewa. Bai kuma bar garin ba sai da aka dasa harsashin fara gina masa tamftsetsan gida da zai dinga sauka shi da iyalinsa a Funtua. Shi kam ba zai dawo Funtua gabad'aya ba. Amma idan ya yi retire zai yawaita zaman garin. Idan ya gaji ya koma Abuja a haka har rayuwar ta kare. Watanniin su Aysha shida da aure Bilki ta haifo lafiyayen danta a birnin Newyork din Amurka. Tare da oga Asad da kuma Alti. Alti dai ana ta keta hazo. Don bata jima da dawowa daga aikin Hajj ba. Bilki ta roka mata oga ya biya Mata. Shi Kuma ganin yadda take masa hidima da yara gabad'aya babu banbancin ya sanya ya biya babu gardama. Da yake cikin hutu ne sai aka kai yaran Funtua tare da y'an aiki don su kula da tagwaye da suke tafiyarsu ko ina. Sun tafi da Alti me dan ta kula da jariri da Kuma Bilki. Ba yadda za'a yi ka kalli Alti ka ce yar aiki ce. Don suturar mai kyau take snayawa, haka nan Bilki bata mata iyaka da cin abin da take so a gidanta ba. Sai aka yi sa'a ita kuma tasan ya kamata tana yin komai cikin nutusawa bata tsallake iyakarta. Idan Bilki ta ce mata jira take yi danta Faruku ya girma ta danka masa ita Sai ta ji hawaye tana godewa Allah. Don da kansa ya kawo mata d'auki da ya hada ta da Bilki ta zame mata komai ta hana ta zubar da hawayen rashin y'aya' da dangi. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:39] Abida ta dinga mamakin haihuwar Bilki don boye mata cikin ta yi tunda ba gari daya suke ba. A bikin su Aysha kuma bai wani fito ba. Kunya take ji domin ta tuna sadda suke gulmar Rukayya ita da Abidan na ta saki jiki tana ta haihuwa rututu babu hutu har suna fadin namiji take so ta haifa ko su ce so take ta tara magada. Ashe ashe ra'ayin mijinta take bi. Gata itama ta shiga ciki tsundum. Sati biyar da haihuwar suka sauka a Kano daga nan suka isa Funtua dan kaiwa su momi yaron da ya ci sunan oga Asad ya kuma biyo kammaninsa tamkar dai tagwaye. Daga nan kuma su kwashe yaransu su wuce Abuja. Kafin ta bar Funtua ta yi order din maijego package a wajen Bojuwa herbs Kano don matuƙa da gaske ta yarda da kyaun kayan da ingancimsu ga sauk'in farashi. Tunda Abida mai kyankyanmi ta yaba kyaunsu. Ta gamsu da packaging dinsu da sabbin containers ne ai ba wanda zai kushe kayan ko ya ce ba masu kyau ba ne. Contact Bojuwa herbs 08032773332 For your order Nation wide delivery.

Shekaru uku a gaba. Zuwa Yanzu Amal Noor da Farha me a gaban Bilki. An an aurar da Bilkisu shekarar da ta gabata tana zaune a kasar Italy da mijinta. Amal ta kammala sakandire tana ajiy daya a jami'a a Riyad tare da Amrah suana hannun Abida da Sulaiman da suka Koma k'asar Saudiya shekaru biyu da suka wuce. Yayin da Noor take ajin biyar a sakandire Farha na aji uku. Bilki ta ta sake haihuwa bayan Mai sunan Asad da suke kiransa da Sadik. Yanzu mace take shayrwa Har ta yi wayo Mai sunan Momi. Tuni Faruku ya kammala sakandire yana karatunsa a jami'ar alkalam d take Katsina. Ba yadda oga bai yi ba ha zo Abuja ya yi ko ya tafi waje ya bada hak'urin said zai yi masters zai zo. Ammar ya kammala masters d'insa a Birmingham Na k'asar biryani ya dawo ya rungumi kasuwanci babansa Na canji a Abuja. Maganarsa da Amrah ta nuna da zarar ta kammala karatunta za'a yi biki.

Shirye shiryen cikar Baba Babba shekaru tamanin da biyar a duniya suke yi. Wata irin liyafa aka shirya mass. Dukkansu yayan gidan sai da suka baro k'asashe da garutuwansu suka dira a Funtua. Kowa d'auke da kyautukan girma daban daban. Abida da y'arta ta zo mai sunan MAMI tana yawonta ko ina. Taro ya kai taro. Ya'ya sun girma sun zama manyan k'asa. Farincikin Baba baya misaltuwa. Ba abinda ya saka shi hawaye irin yadda shi kad'ai yake ganin yadda y'ay'ansu suka zama zarata masu rik'e da mukamai daban daban. Baba K'arami bai ga hakan ba. Aysha da Hafcy sun zo kowacce da goyonta. Bayan an gama ciye ciye tare da yanka kawataccen cake din deenasnakck and more Kano. Da Hamida ta zo da shi tare da snacks dinsu masu dadin gaske. Cikin nutsuwa aka dinga yin hotuna.

*Na ce kin karanta littafin Malamin bogi na Maman Afra kuwa?* *To Ruwa cikin cokali fa?* *Gaskiya ku bibiyi books din nan zaku nishadantu*. *Ku tuntubeta kai tsaye* 9030283375.

Sai da ya jasu sallah. Kowa ya nutsu gaban Ubangiji. Sannan Baba ya juya garesu gabad'aya yana mamakin yawansu su da y'ay'ansu. Ya yi gyaran muraya tare da yi musu sallama. Suka amsa dukkansu a sanyaye don kuwa lallai Baba nasiha zai yi musu mai shiga jiki. Ya ce "Na yi farincikin ganinku gabadaya. Na samu nutsuwar ba zaku kaskanta ba don kuwa kun hada kai kowa kuma yana neman na kansa. Ina yi muku nasiha ku ji tsoron Allah, ku yi ibada, ku tsare ya'yanku daga fitowa a social media suna bayyana tsaraicinsu da sunan wayewa. Ku guji barci mai yawa don kuwa mabudin lalaci ne, lalaci kuwa yana haifar da dauwammen talauci. Ku guji shirka don cinye imani take yi tamkar yadda wuta ke cinye karmami. Shirka kala kala ce. To ku kula don da yawa mutanen yau suna cikin halakar sun kafirta basu ankara ba. Da yawa idan tsautsayi ko azal ya samu mutum ko jarabawa sai a jinginawa wani tare da gasgata sa hannuna ko wanene ya yi mini shihiri ko sammu. Duk abin da kuka ga same ku mai kyau, to ku jinginawa Allah. Ku yi masa godiya mai yawa. Idan marar dad'ine ku jinginawa jarraba da k'addara da ta same ku kai tsaye da aka rubuta cikin littafin k'addararku. K'addara kuwa bata sauyawa amma tasirin addu'a yana dakushe kaifinta. Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:50] Kada ku ci kudin ruwa don Annabi ya la'anci mai cinsa. Ku guji sauya halitta Annabi ya ce tsinannunu masu feke hakori don su yi wishirya da masu aske gira. Manyan malaman addini sun ce masu sauya halitta daga bak'i zuwa launin fari da masu k'ara girman mazaunai ko kirji duk sun shiga cikin tsinuwar. Kunsan kuwa ko LIMAMIN unguwarku ne matuƙar mumini ne ya tsine muku ai kun yi hannun riga da yin albarka bare ma'aikin Allah. Ku yi iyakacin k'ok'arinku akan tarbiyar yaranku, ku kula da wa suke mu'amala. Ku guji hassada don kuwa durk'ushe mai yi take yi. Ku guji yanke hukunci cikin tsanani don yana janyo nadama. Ku guji b'arin zance don tuntuben harshe yafi tuntuben k'afa zafi. Ku kame daga yawan surutu marar amfani, ku yawaita istigifari. Ku dinga nazarin yadda aka yi mana kunnuwa biyu, idanuwa biyu amma baki daya. Ba dan komai ba ne illah jinmu da ganinmu su fi furucinmu yawa. Ku guji zina, ku nisance ta don kuwa tana kan gaba wajen gadar da talauci bayan haka kuma naso take yi cikin zuri'a tare da cinye imani. Annabi ya ce zina bashi ce. Ku tsare kanku, ku tsare bayanku daga fad'awa tarkonta. Ku guji yada bacin rai. Ku dinga boye laifin wanda suka saba muku don yada shi yana haifar da gaba. Ku yawaita yiwa magabatanku addu'ar rahma. Ku yiwa kanku tanadin lahira tamkar yanzu zaku tafi. Haka nan ku nemi duniya tamkar ba zaku mutu ba. Kowa ya nemi na kansa kada ku dogara da mutum guda. Duk zuri'ar da ta zubawa mutum d'aya ido take jiran tallafinsa da wuri zasu dirkake don kuwa Allah ne kad'ai zai iya da bukatunku babu gajiyawa. Ku nunawa ya'y'anku muhimmanci dogaro da kai. Kowa ya nemi na kansa sai zumunci ya yi dad'i. Duk zuri'ar da kowa yake neman na kansa suke karatu zasu yi karfi su d'aukaka zasu daina zubawa mutum d'aya da ya yi shura a cikinsu idon ya yi musu hidimar dole da bata dole ba, idan bai yi ba kuma, sai a tisa shi a gaba da kushe da gaba. Mafi yawa irin wadannan sun yi iyakacin kokarinsu yau da gobe ce ta sanya suka gaza ko suka daina yi. Amma idan kowa na da sana'a komin ƙanƙantarta za'a samu sauk'in zarmewar da ake yi na jiran wane ya bayar. Masu kud'in ma a yanzu da rayuwa ta tsananta nemansa suke yi kasuwanci suke yi iri iri, ya'yanasu ma sana'a suke yi don su samu kudin, to akan me za'a yi ta zuba musu ido a kullum su bayar?" Daidai nan ya yi shiru yana nazarin yadda jikinsu ya mutu tub'us wasu ma k'walla suke gogewa. Ya nisa ya cigaba da fadin ku rarraba ya'yanku su karanci fanni daban daban ta yadda duk wata kafa kuna da k'afa. Ku yi kasuwanci, ku yi Nima Annabi ya ce arzikin Duniya na kasuwa da gona. Ku yawaita istigifari don mabudin alheri ne. Duk abin da ya yi muku tsanani ku yawaita zubar masa istigifari Allah zai warware muku cikin hikimarsa. Kada ku tsangwami wanda kowacce ta samu jinkirin aure don wannan ikon Allah ne. Duk saurin mai sauri sai ya jira ikon Allah. Aure, haihuwa da mutuwa lokaci ne ba'a yinsu sai lokacinsu ya yi. Annabawa uku a jere da Allah ya ambacesu cikin suratul Maryam. Ilyas Yahya da Isa (A.S.). Basu taba aure ba. Amma rashin aurensu bai hana a basu annabta ba kenan idan mutum a kame yake rashin yin aure ba tawaya ba ce, tunda ko a shari'a ma ba farilla ba ce, sunna ce mai karfi. Nana Aisha bata taɓa haihuwa ba, ita ko bari bata taba yi ba, amma sunanta ba zai shafe ba a doron kasa ba, don kuwa sai aka azurta ta da ilimin da ta yada shi ciki al'umma. Rashin haihuwarta bai hana miji ya sonta fiye da kowa cikin matansa ba. Allah kuma da kansa ya ce yana jin nauyin wanda bai bawa haihuwa ba Ashe kuwa duk wanda ya tsangwamesu Allah yake yiwa isgili, ya jira kuma hukunci ta inda bai yi zato ba. Ku dinga rabon gado da wuri tare da iyakance dukiyar kowa ya hanyar rubutu. Wataƙila yaune had'uwarmuta k'arshe da wasu daga cikinku. Ina rokonku ku girmama manyanku, manyan kuma ku tausayawa kannenku, ku mu'amalancesu da kyautatawa. Allah ya taimakemu gabad'aya. Allah ya yi muku albarka ya rufa muku asiri duniya da lahira ". suka amsa da fadin ",Ameen Baba Allah ya kara maka lafiya da imani". Save Restricted Content Bot, [Dec 15, 2025 at 15:54] *DINGISHIN KWAD'O* *SURAYYA GWARAM* 08032773332.

*Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*. *Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*. *Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Just DM for your order @08033773332*.

*Epilogue* Bayan shekara biyu. Ana ta Shirin auren Ammar da Amrah ta kammala karatun likitanci tana housemanship a specialist Hospital Abuja. Farha tana jikin Bilki ta ce "Mahmah kinsan me ya ya Faruku ya ce min?" Bilki ta jijjiga kai tare da fadin a a ". "Wai na tambaye shi budurwarsa ta alkalam ya ce abokiyar karatunsa ce. Farha ce matarsa. Na ce a ina take wai a Abuja gidan Mahmah". Mahma to dama Yaya da kanwa suna yin aure ne?" Bilki ta ce "Basa yi ". Daga haka ta shige wanka ta barta zaune a bakin gado. Ta koma d'akinta. Ta kira shi a waya. Yaya Faruku ka rikita ni fa. Kuma Mahma ta ce "no". Ya ce "saboda me to?" Saboda Yaya da kanwa basa yin aure mana". Ya ce "Ki ce mata da gaske nake yi dan haka mu za'a fara a kanmu.' Kwanaki biyu a tsakani ta sake tambayar Bilki. Mahma dan Allah ki fad'a mini wacece babar Yaya Faruku dan Allah? Don har cikin zuciyarta ga ni take yi sai dai idan ba shi Mahmah ta haifa ba amma ba ita ba kam. Bilki ta ce "Alti ce'. Farha ta rike kirjinta tare da fadin Ashe "Da gaske yake da ya ce ba ke kika haife shi ba. Allah sarki". Bilki ta wuce ta tana jin yanzu ya yi wuri da yawa. Tunda Bana zai kammala digirin dole ya wuce wata k'asar ko baya so don ba zata yarda ya damawa Farha lissafi ba. Zuwa yanzu Farha ta wasiwasi take yi akan su waye suka haife su ita da Faruku? Dole akwia wanda ba Mahmah ce ta haifa ba a cikikinsu. Haka kawia take fatan Allah yasa ita ta haife ta. Amma tana jin soyayyar ammi da su junior a ranta fiye da kowa a cikin daginsu. Sannan yadda take ganin soyayyarta a idanuwan Mahmah haka take gani a idanuwan ammi. Ana yin hutu Noor da Farha suka cewa Dady suna son tafiya Saudi gidansu junior daga nan su yi umrah. Bai k'i ya amince aka fara nema musu visa. Da zasu tafi sai da Abida ta matsa a tafi mata da ciccibi da kazar sababi tunda freezing dinsu ake yi ba zasu narke ba tunda ba doguwar tafiya ba ce. Sanyi flusher ne aka tafi mata da saiwowin tunda bojuwa herbs suna bayarwa sia ka dafa da kanka tunda ba'a shiga da abu mai ruwa cikin jirgi.

*08032773332 contact Bojuwa herbs Kano for your special kayan mata ingattau amintattu.*.

Haka aka Abida ta matsa sai da aka yiwa maminta d'inkunan native wears don ta gamsu da k'warewar teler da Bilki take bawa dinkin Farha da take k'arama. 08080266674 ku wannan layin masu buk'atar su a dinga yiwa y'ay'ansu mata dinkuna irin na yan gayu y'anuwan masu kud'i.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull