Kenza eBookz

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 5

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 5

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 5: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 5. ....... Ya kwashe da dariya yana fad'in "Ashe haka Alti ta…

4,735 words

....... Ya kwashe da dariya yana fad'in "Ashe haka Alti ta iya turanci ban sani ba?" Ta koma kicin ta kawo musu abinci falo sannan ta shige d'akinta don ta yi wanka da sallah. Cikin nutsuwa Bilki ta zuba masa ta saka cokali ta ba shi sannan ta zubawa kanta. Farha tuni ta yi barci don Indomi aka fara dafa mata tana ci kuwa bata jima ba ta yi barci. Ya kammala cin abincin da ya yi masa kyau a ido, ya cika hancinsa da k'amshi, ya yi masa dad'i a baki. Ya nisa ya ce zan saka kudin spice's din nan a asusunki sai ki yi muku order tare da Jamila." A nutse ta ce "To". Ko godiya ta kasa yi masa don haka siddan ta ji wani irin abu ya turnike ta mussaman da yake ta ambaton sunan matarsa da son sai dandanon girkinta ya yi irin nata. Daga haka ya mike ya yi mata sallama zai tafi masaukinsa ya huta shima. "Idan Alti ta fito ki ce mata na tafi sai gobe zan zo da rana dan haka kada ta yi abin karyawa da ni". "Allah ya kaimu ka huta gajiya". Bilki ta fad'a a takaice tana jin haushin Jamila da na Yaya Asad na kutsowa tunda ga k'asan zuciyarta. Don tabbas sune mutane biyu da suka yi mata shamaki da samunsa. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:55] Ya fita bai sake ce wa komai ba don ya lura so take ta hargitse tunda suka iso komai yake neman k'wace mata. Tana jin sautin takunsa a kafar bene ta ja dogon tsaki tare da fad'in "Yan ta'adda kawai masu son kansu" Daidai lokacin k'iran gogan nata ya faɗo wayarta. Tana kallo har ta katse bata d'aga ba don sosai ta ji haushinsa ya dirar mata. Sai dai cigaba da kiran ya yi, akan dole ta dauka ta yi sallama murya a mak'oshinta. Yayin da hakan ya jefa Asad cikin wani irin yanayi. Ya yi k'asa da muryarsa ya ce"Ba ki da lafiya ne?" ke nan?". "Lafiyata k'alau". Ya nisa ya ce Saboda Allah Maigado za ki yi tafiya sai dai na ji a bakin Farouku. Da safe ma mun yi waya na ji alamun a mota kike, na tambaye ki, inda za ki je kika ce wajen aiki, ashe Katsina za ki tafi shine ban isa ki fad'a min ba ko? Amma ni da zan taho Lago din nan sai da na fad'a miki tun ana gobe zan tafi, ina cikin jirgi kafin na tashi ma sai da na sanar da ke ". Haka kawai ya fad'a ta ji ta harzuk'a tunda dama haushinsa da na Jamila ke ciciiyarta a daidai lokacin. Dan haka ba tare da ta tauna kalamanta ba ta ce "Amma ai ban rok'e ka, ka fad'a mini ba, sannan akan me duk abin da zan yi sai na fad'a maka?". Jikinsa ya yi sanyi k'alau tare da tunanin ko ya yi mata wani abu ne? A sanyaye ya ce "Me yake faruwa ne Maigado?". "Kamar na me fa?" A hankali ya ce "Sai da safe". Ba tare da ta amsa ba ta yi maza ta riga shi katse wayar. Yana kwance shi kad'ai kan makeken gado na alfarma cikin tsadadden hotel a birinin na Ikko. Ya yi sororo da waya a hannunsa a fili ya ce "Tooh! Zuciyarsa na bugawa tare da kitsa masa ta je Katsina ta ga mijinta da ya'yanta shine zata birkice ta nemi juyawa maganarsu baya? Ban da haka bai ga dalilin fishi da fisgar da ya ji a tare da ita ba. A fili ya ce "Allah ka k'addara mini auren yarinyar nan, Allah ka sa rabona ce". Don gabadaya hankalinsa ya yi mugun tashi. Tunda yasan ba sonsa take yi ba komai na iya faruwa.

Tun Daren suka yi waya da su Amrah ta fad'a musu ta zo garin. Sassafe Babansu ya dawo daga masallaci Amrah ta tsaya a falo. Ta gaishe ta ce "Dady dan Allah anjima ka kaimu wajen Mahma ta zo kuma ta ce ba zata dade ba, zata juya". Daidai lokacin Faruk ya shigo falon. Da sakakkiyar fuska ya ce "To ku shirya tunda hutu kuke yi anjima zan kai ku ranr da zata tafi sai ku dawo". Dad'i ya kamasu suke ce "Mun gode". Ya haye sama don yanzu kan dole idan ya dawo masallaci yake hawa saman tunda Hawwah ta kafe kwana Kawai zata yi a k'asa amma ba zata yarda ta dinga biyo shi da abinci ko wani abu daban k'asa ba tunda bata d'aki a gun. Dan haka ya amince dan ra'ayinta tunda ya kafe k'asa na y'ayansa ne ba mai takurasu kuma ba zasu dinga kwana su kad'ai ba. Dan haka itama ya lallaba yake bin ta saman da zarar ya dawo daga masallaci da asuba don su samu daidaita a tsakaninsu. K'arfe takwas sun gama shirya ko barcin safe basu koma ba. Gabaɗayansu zumundin ganin uwarsu ya dabaibaye zuciyarsu. Farouk ya kalli Amrah ya ce ",Yaya ai dai bana yi miki rashin kunya ko?" Dariya kad'an Amrah ta yi ta ce "Yaushe rabon da ka ce mini Yaya Farouk?" Ya yi dariya kad'an ya ce ",Saura ki je Ki faɗawa uwata zancen da zai dame ta". Amrah ta kalle shi ta ce "Me zan fad'a kuwa da zai dame ta ?" Ya make kafada tare da fad'in "Idan kika ce bana magana da anty ta yi mini fad'a Allah muka dawo ke ma daina kula ki zan yi". Ta jijjiga kai tare da fad'in"Tun yanzu daina kula ni kawai". Ya yi dariya ya ce "Don dai bana son ki yi kuka ne". Itama dole ta dara don ya bata dariya sosai. Ta shiga dakinta ta fito da yar jaka Karama mai kyau d'auke da kayanta set biyu ta ce "Za ka dauko kayan naaka na saka maka ko kuwa?" Ya make kafaɗarsa ya ce "Ki je d'akin nawa ki dauko mini idan ba haka ba, da iya na jikina zan je sai na ga wa za'a yiwa fad'a a tsakaninmu." Ta kalle shi ta ce "Allah ya shirya ka Farouk ". Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:58] Sannan ta wuce zuwa d'akin nasa don idan bata d'auko masa ba haka zai tafi, kuma ita Mahma zata yiwa fadan ba ita ce babba ba. Yayin da shi kuma yake tsaye rungume da hannuwansa yana yiwa kansa waka wai shi Yayan Mamah mai kafaciti dole a bi shi". Amrah ta fito ta ce"Ka daina cika bakin dole na bika. Kawai tausayinka nake ji". Ya k'yalkyale da dariya yana ce wa "Yayan Mamah ba abin tausayi ba ne Haj Amrah". Dolenta ta k'yale shi don masu gidan ma hakuri suke yi da shi, don su ba ya kula su, tsakaninsa da su gaisuwar safe, sai ko idan zai faɗawa Babansu zai sayi abun makaranta. Amrah dai yake mu'amala da ita kawai. Basu da wata babbar matsala a gida don su kad'ai suke rayuwa a wajensu, da daddare kuma iyayen su sauko su kwana. Sun sake samun saukin matsala ne da mijin Alawiyya ya dawo da ita cikin Katsina. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Kuma basu da nisa da unguwarsu. Dan haka duk sati suke zuwa gidanta Su yini, mamarsu ta turo musu ita da Amrah su yi samosa da springrols da numa meatpie sai Su tafi da shi su saka a fridge. Duk sadda suke so sai su soya abinsu. Sosai Alawiyya take kulawa da su dan har gidan take zuwa jifa jifa tana yiwa wajensu kyakkwan gyara. Dan haka basu wani tagayyara da yawa ba, mussaman da Hawwah ta kasa samun tasirin da zata dakile hankalin ubansu a kansu. Tun Bilki bata dad'e da barin gidan ba ta fara cin karo da matsaloli da ashe zaman Bilkin a gidan ne ya hana ta lura da su. Lafiya take zaune da mijinta amma kuma babu wannan rawar jiki da tarairayar da ya dinga yi mata a watannin farkon na zamansu. A da kafin ta bukaci wani abu sai dai ta ga ya kawo, yanzu kuwa sai ta yi ta fad'a kafin ya samu sukunin siyowa. Sannan su yaya Turai sun koma suna jan kunnen mijinta akan lallai ya saka ido akan ya'yansa kada ya bari su yi kukan rashin wani abu tunda uwarsu da take nan ba abin da bata yi dan ta rufa masa asiri ba. Tuni sun fahimci Bilki ce ta sanya gidan Sahal ya zama gidan masu wadata ta yadda zaka ci abinci laifayye ka k'oshi. Amma tunda ta bar gidan ba dama ka je a baka abinci sai dai ruwan pure water. Idan kuwa yini zaka yi to abincine dai ga shi nan amma ba wani sha'awar da zai baka. Sun sa ni kuma iya k'arfinsa ke nan tunda Hawwah bata da shi dole iya yadda ya bata haka zata yi. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: *Kun tuna Umm Nihla mai yadinkan Yan gayu da Yabin Bulkacuwa ta yi ta kece raini da su?* *Tana nan tana kawo muku su zuka zuka, na alfarma, amintattu, akan farashi mai rahusa* *Malaysianfabricsng* 07020695644.

Haba ba sai sai kuma suka koma suna son ya'yan Bilki ba. Hawwa kullum cikin kuka take tunda yanzu ita aka saka a gaba ana fadin itace farar k'afa ba Bilki ba. Sannan iyashegen da Faruku ya tisa ta a gaba da shi cikin lumana kad'ai na matuƙar damunta. Tsiyataku iriiri yake yi sannan ba dama ya ga Amrah ta hau samanta zai k'ira ta ya dinga yi mata sababin ta tafi neman suna ta bar shi, shi kad'ai. Ba yadda ta iya da shi tunda ubansa ma rarrashinsa yake yi da son ganin dariyarsa.

Da kanta ta fahimci babu riba ko kad'an idan har kishiya ta tafi ta bar maka ya'yanta gara ku zauna kowa ta rik'e ya'yan har Allah yasa su girma. Yanzu ba abin da take so irin ace Bilki ta dawo d'akinta ko dan mijinta ya samu nutsuwa sannan ta tabbatar idan tana nan wulakancin Faruk ba zai yi tasiri ba. Sannan hankalin Sahal ba zai zama kacokan akan su Amrha ba. Yana son d'iyarta tabbas tunda ba abin da ba ya yi mata amma sai take ganin ba kamar manyan ba. Idan zata kwnaa tana Kiran Faruku ba zai amsa ba, ko da kuwa ta bar samanta ta sauko. Idan da safe ya gaishe ta bata amsa ba, Babansa ya yi fadan yaro yana girmamata tana yada girman. Idan ta ce ai baya mata magana sannan ko mai zata ce masa ba zai nuna ya ji ba bare ya tanka. Ya kuwa ce mata ai yaro ne, sannan tunda yana gaishe ta ai ya kyauta kada ta sake ta biye masa watarana ba zai yi ba, bata ga Amrah ma hak'uri take yi da halinsa ba. Bak'inciki kan bak'in amma ba yadda ta iya haka take hakuri tare da amannar yaran sune jarabawar gidan aurenta. Da zai kaisu ya yi kwalliya irin wadda Hawwah ta dade bata ga ya yi irinta ba. Ta kasa hak'uri ta ce "To ko dai kome zaku yi ne Baban Amra?". Ya yi murmushi ya ce "Idan zaman bai k'are ba sai a yi". Duk da zuciyarta ta buga amma da murnarta ta ce "Allah ya nufa gara ta dawo d'akinta ko Faruk ya janye kiyayyar da ya d'ora mini haka siddan." Bai ce komai ba. Don kuwa ya riga yasan Bilki ta yi masa nisa har sai idan aure ta yi ta fito. Da kansa kuwa ya tabbatar matuk'ar ta had'u da namijin da zai biyar da ita ta samu gamsuwa ba zata yi marmarin sake zama da shi ba. Ya dauki d'auki d'iyarta data ke zaune akan gado ya daga sama tana yi masa dariya sannan ya ajiye ta ya ce "Zan tafi daga can Zan wuce d'aurin aure kinsan yau asabar su kuma zan barsu a can sai ta tafi zasu dawo". A sanyaye ta ce "A dawo lafiya". Ta fito ya same su a falon sun Tisa jakar kayansu a gaba. Suna ganinsa suka mike. Ya ce ",Oya ku je ku yiwa Antinku sallama". Ba musu suka hau k'afar benen yayin da shi kuma ya dauki jakar kayan ya fita zuwa wajen motarsa. Amrah ce kawia ta hau ta yi sallamar. Amma Faruk nokewa ya yi daga k'afar benen. Suka sauko a tare Amrah na yi masa fadan ya dinga jin maganar Dady Menene dan ya yi sallama? Uffan bai ce mata ba. Ya shiga gaban mota Amrah ta shiga baya. Har k'ofar gidan ya kaisu sannan ya ce su ce yana gaishe ta, haka nan su gaida Alti da Farha. Ya ja motarsa ya tafi yana jin wani irin nauyi da nadama suna sake mamayarsa tabbas har ya mutu ba zai daina jin ciwon asarar da ya tafka ba. Da gudu Faruk ya hau saman yayin da Amrah ta hau a hankali tana rike da jakar kayansu. Alti ya tarar a kicin dan haka ya shiga ya rungume ta yana fad'in "Altina! Itama ta rungume yaron tana jin dad'in yanayin da ta ganshi tabbacin basa cikin takura. Daga haka ya sake ta da hanzari ya doshi d'akin da zai ga Mahma.

Mkbees Perfumery* *Mopping liquid, Air freshener, Body* *mist ,Khumrah,Kulaccam,Hair* *Mist Carpet Spray,Linen Spray * *Oil perfumes Kano* *Sirrin gayun mace k'amshin* 07032456061

A bakin gado ya tarar da ita tana gyarawa Farha zaman hularta. Ai tana ganinsa ta ruga suka rungume juna. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:02] Sakwanni goma suna haka kafin ya sake ta yana fad'in "Farha ya Abuja?" Ta ce "Lafiya lau ina Yaya?" Daidai lokacin Amrah ta shigo d'auke da jakar kayansu. Itama ta rungume ta. Yayin da suka zauna gefen uwarsu suka sanya ta a tsakiya. A nutse Amrha ta gaishe ta shi kuwa Faruk jingina ya yi a jikinta. Bilki ta yi matuk'ar sanya jarumta ta karbi gaisuwarsu da sakakkiyar fuska. Amma k'asan zuciyarta tausayinsu fal yake yagalgala ta. Da sanyin murya Amrha ta ce "Dady na gaishe ki, ke ma Farha ya ce yana gaishe ki ". Farha da take zaune kusa da Faruku tana tambayarsa k'awayenta na makaranta. Bilki ta ce "Ina amsawa ina kanwarku? Ya ma sunanta?" Faruku ya yi fit ya ce"Lubaba". Bilki ta ce "Sunan Hajiyar ne haka gatsal a bakinka?". Amrah ta ce"Yana ji fa ina ce mata Ifrah amma dan iskanci indai ya ganta a hannuna ko wajen Dady sai ya wani ce mata Lubaba kullum ya fad'a haka sai Dady ya ce masa baka jin nauyin baro mini Faruk? Amma ba ya dainawa. Gaskiya Mamah ki yiwa yayanki fad'a baya jin magana kullum da abin da zai yi na rashin ji". Bilki ta rungume shi sosai ta ce "Yayana da dai nasan ba ka neman fitina amma me yasa yanzu ka canja?" Ya yi murmushi ya ce "Ba na neman fitina har yanzu amma bana son a takura ni ne, Yaya Amrah da Dady sai su dinga takura ni sai na shiga hanyar matar gidan ni kuwa ba zan shiga ba, ta yi harkarta na yi tawa". Amrah ta ce "To me yasa kake mini sababi idan na je sama ko Idan na dauko Ifrah?" Ya galla mata harara ya ce "Tunda Mamah bata tare da mu dole ki dinga kula da ni sosai. Akan me za ki tafi ki bar ni? Ki dinga neman shisshigi ai dama zan fad'awa mama ba ki rik'e amanata da kyau ba". Dariya ta subucewa Bilki don ta lura da gaske yake maganarsa ba wai wasa ba. Sosai suka hi hirarsu cikin nutsuwa duk da yawan hirar k'orafi Faruk yake ta gabatarwa akan Amrah tana takura shi wanda duk na shagwaba da iyashege ne kawai don uwar tasu da kanta ta gane Amrah ce take hakuri da shi tare da lallaba shi. Da azahar ta yi Alawiyya ta iso. Gidan ya sake kaurewa da murna suna tuna rayuwar da suka shafe tsawon lokaci tare tamkar ba za'a rabu ba, yanzu kuwa had'uwa gabad'aya irin haka zai dinga yi musu wahalar gaske. Wannan kad'ai ya isa a gane ba abin da ba zai wuce ba sai ikon Allah. Da taimakon Bilki da Amrah Alti da Alawiyya suka shirya dukkan kayan da Bilki ta ke so wajen d'aya . Duk abin da su Amrah suke so ku suke da bukartarsa ta bar musu. Babban gadonta Amrah ta ce ta bar mata tunda yanzu itace a d'akinta Kuma Dakin babbane gadonta da wadirof sun yi kankanta da yawa. Faruk ya yi tsalle ya ce ",Ba za'a bata ba, na d'akin baki ya ishe ta tunda suma set ne." Ta harare shi ta ce "Kai ka d'auki na d'akin bak'in tunda nasan ce wa zaka yi kai ta baka." Ya girgiza kai ya ce "A a ni nawa sun ishe ni. Alawiyya zata barwa ita kuma ta siyar da nata ta fara business da kudin, ba ki ga yadda take yi mana kirki ba har yanzu? Duk sati sai mun je gidanta mun yi abin da muke so, haka nan ita take zuwa ta yiwa wajenmu general sanitation duk karshen wata. Har firizar can ma ita za'a bawa ". Amra ta yi maza ta ce "Hakane a bata to". Bilki ta yi shiru tana nazarin hukuncin da Faruk ya yanke kaitsaye ba tare da neman shawara ba. Amma ta sani gaskiya ya fad'a. A ranta ta ji yafi dacewa da ya amsa sunan Sulaiman don kuwa halayyarsa rabi irin tasa ce. Dan haka duk ta barwa Alawiyya kayanta har kujerun falon, yayin da Alawiyya ta dinga kuka tana hodiya tare da mamakin yadda ta mallaki kayan alfarma tashi guda. Tuni kuma ta amince zata siyar da nata kayan wasu kuma ta aikawa kanwar Babanta da ta rik'e ta tunda marainiyace ita. Alti ta dinga taya ta godiya a wajen Bilki. Da yamma Basma ta je mata suka yi hira ta yi murnar ganin Bilki ta samu nutsuwa zuciya sannan ta ji dad'in auren da zata yi. Ta jaddada mata zata kula da su Amrah iyakacin iyawarta. Itama Bilki ta bata warmers sabbbi sannan ta ce ta duba duk abin take so na amfani ta dauka. Gaf da magariba ta yi sallama suka ta tafi. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:11] Sai dare mijin Alawiyya ya zo daukarta a mashin d'insa wanda dan kasuwane yana siyar da kayan vegies da yake sarowa daga Raudatul Jannah foods Jos.. A zuwan da Alawiyya take yi siyo kayan snacks da na amafanin gida suka hadu. Har saman ya hawo ya gaisa da Mahmah tunda dama a gidan ya san Alawiyya sai da suka amince da junansu sannan Bilkin ta tura shi K'afur garinsu Alawiyya ya gana da wakilanta. Ya dinga yin godiya alherin da aka yi musu tunda Alawiyya waya ta yi masa ta fad'a masa kyautar bajinta da aka yi mata duk kuwa da kayan d'akinta na yanzu Bilkin ce ta yi mata su sabbi Sai dai ai Basu kama k'afar wanda aka bata ba yanzu. Kafin ta tafi Bilki ta ja ta d'aki ta fad'a mata zata yi aure a cikin sati mai kamawa ta taya ta da addu'a. Farinciki har cikin ran Alawiyya don kuwa bata yiwa uwardakinta sha'awar yin kome. Ta dinga yi mata addu'o'i masu sanyaya zuciyata tare da sake yi mata alkawarin matuk'ar tana cikin garin Katsina to Faruk da Amrah suna da Yaya tamkar uwarsu d'aya ubansu daya zata kula da su irin yadda ta kula da ita. Hankalin Bilki ya sake nutsuwa don kuwa ta gasgata Alawiyya. Ga su Faruk sun sake bada shaidar ba abin da bata yi musu. Suka yi sallama suka rabu cikin sanyin jiki da fatan alheri. *Na ce kina yiwa masu aikinki adalci da sassauci kuwa?* *Ba ki san ta yadda zasu taimake ki a gaba ba. Kowanne dan adam akwai ranarsa, da ace Bilki bata yi mata adalci ba, da bata kular mata da yaranta a lokacin da babu idonta a kusa ba*. Sai da daddare bayan sun kammala cin abincin dare tuni kuma Farha ta yi barci. Ita da Alti suka faɗawa yaran batun auren da zata yi. Dukkansu yaran jikinsu ya mutu ba karsashi suka ce "Allah ya sanya alheri". Amma k'asan zuciyarsu sun ji wani iri shike nan ta bar gidansu da dadynsu for ever? Murya ba amo Amrah ta ce "Mahmah waye shi sannan a ina za ki zauna?" Ba walwala ta ce "Uncle Asad ne sannan a Abuja zan zauna". Amrah ta yi shiru ta rasa me take ji a ranta. Amma dai zuciyarta sai ayyana mata take yi mai kudine fiye da dadynsu amma kuwa Babansu ya fi kyau yafi kirki tunda shi ba ya dariya. Kafin ta ce wani abu Faruk ya ce "Mahmah uncle police wai?" Kai kawia ta daga masa tabbacin eh. Ya rik'o hannunta ya ce "Amma takwarana ya fi shi kirki da kyau Mahmah". Murya ba amo ta ce "Ba kyau na duba ba, sannan haka k'addara ta zaba mini kawai ku dinga yi mini addu'a". A sanyaye suka ce to don hatta Faruk da yake ganin gara ta tafi inda ba zata dinga kuka ba, batun auren nata ya yi awon gaba da kuzarinsa. Wato kishi bala'i ne, ba ga yara ba, ba ga manya ba.😄Ba ga mazan ba, bare kuma mata masu duniya. Allah kasa mu wanye lafiya. Washegari suka bar Katsina wanda su Bilkine suka kai yaran gidan Alawiyya akan da yamma su wuce gidansu tunda da sassafe suka tafi a dalilin zasu tsaya a Kano wajen Yaya Hamida. Suna nisa da Katsina kewar ya'yanta na sake kama ta. Akan dole ta yi hak'uri mussaman da yara basu tayar da hankalinsu sosia ba, amma dukkansu sun yi kuka. Haka Farha har suka kusa isa Kano kuka take yi akan a barta a wajensu ba zata koma Abuja ba. Sai da barci ya sure ta sannan ta yi shiru. Taran safiya a gidan Yaya Hamida ta yi musu, suka karya sannan suka shiga daki Bilki ta sanar mata batun aurenta da Yaya Asad. Take Hamida ta fara kuka tana fad'in tabbas na huce dan ke na ji wa'azi akan illar gaba mussaman ace jini guda ke yin ta. Amma ki sa ni sai da kwakkwarn dalili za ki ga k'afata a gidanki. Me za ki yi da wannan mugun marar mutunci dattijo da shi zai dage sai ya aure ki. Allah ne ya rufa miki asiri bai lalata ki tun kina yarinya ba, masu kakin nan fa kad'an ne na kirki amma wominzers ne na k'arshe. Ai ni tunda bai zo ta'aziyar uwarmu ba, sannan ya daurewa yar iskar Abidan nan gindi akan Yaya Sulaiman Wallahil Azim ba ni ba shi. Dan haka soyayyar da zan nunawa ya'yanki sai na nunawa su Amrah da Farha amma nasa kam kadaran kadaran hakan ma saboda ta jikinki suka fito." Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:13] Sai dare mijin Alawiyya ya zo daukarta a mashin d'insa wanda dan kasuwane yana siyar da kayan vegies da yake sarowa daga Raudatul Jannah foods Jos.. A zuwan da Alawiyya take yi siyo kayan snacks da na amafanin gida suka hadu. Har saman ya hawo ya gaisa da Mahmah tunda dama a gidan ya san Alawiyya sai da suka amince da junansu sannan Bilkin ta tura shi K'afur garinsu Alawiyya ya gana da wakilanta. Ya dinga yin godiya alherin da aka yi musu tunda Alawiyya waya ta yi masa ta fad'a masa kyautar bajinta da aka yi mata duk kuwa da kayan d'akinta na yanzu Bilkin ce ta yi mata su sabbi Sai dai ai Basu kama k'afar wanda aka bata ba yanzu. Kafin ta tafi Bilki ta ja ta d'aki ta fad'a mata zata yi aure a cikin sati mai kamawa ta taya ta da addu'a. Farinciki har cikin ran Alawiyya don kuwa bata yiwa uwardakinta sha'awar yin kome. Ta dinga yi mata addu'o'i masu sanyaya zuciyata tare da sake yi mata alkawarin matuk'ar tana cikin garin Katsina to Faruk da Amrah suna da Yaya tamkar uwarsu d'aya ubansu daya zata kula da su irin yadda ta kula da ita. Hankalin Bilki ya sake nutsuwa don kuwa ta gasgata Alawiyya. Ga su Faruk sun sake bada shaidar ba abin da bata yi musu. Suka yi sallama suka rabu cikin sanyin jiki da fatan alheri. *Na ce kina yiwa masu aikinki adalci da sassauci kuwa?* *Ba ki san ta yadda zasu taimake ki a gaba ba. Kowanne dan adam akwai ranarsa, da ace Bilki bata yi mata adalci ba, da bata kular mata da yaranta a lokacin da babu idonta a kusa ba*. Sai da daddare bayan sun kammala cin abincin dare tuni kuma Farha ta yi barci. Ita da Alti suka faɗawa yaran batun auren da zata yi. Dukkansu yaran jikinsu ya mutu ba karsashi suka ce "Allah ya sanya alheri". Amma k'asan zuciyarsu sun ji wani iri shike nan ta bar gidansu da dadynsu for ever? Murya ba amo Amrah ta ce "Mahmah waye shi sannan a ina za ki zauna?" Ba walwala ta ce "Uncle Asad ne sannan a Abuja zan zauna". Amrah ta yi shiru ta rasa me take ji a ranta. Amma dai zuciyarta sai ayyana mata take yi mai kudine fiye da dadynsu amma kuwa Babansu ya fi kyau yafi kirki tunda shi ba ya dariya. Kafin ta ce wani abu Faruk ya ce "Mahmah uncle police wai?" Kai kawia ta daga masa tabbacin eh. Ya rik'o hannunta ya ce "Amma takwarana ya fi shi kirki da kyau Mahmah". Murya ba amo ta ce "Ba kyau na duba ba, sannan haka k'addara ta zaba mini kawai ku dinga yi mini addu'a". A sanyaye suka ce to don hatta Faruk da yake ganin gara ta tafi inda ba zata dinga kuka ba, batun auren nata ya yi awon gaba da kuzarinsa. Wato kishi bala'i ne, ba ga yara ba, ba ga manya ba.😄Ba ga mazan ba, bare kuma mata masu duniya. Allah kasa mu wanye lafiya. Washegari suka bar Katsina wanda su Bilkine suka kai yaran gidan Alawiyya akan da yamma su wuce gidansu tunda da sassafe suka tafi a dalilin zasu tsaya a Kano wajen Yaya Hamida. Suna nisa da Katsina kewar ya'yanta na sake kama ta. Akan dole ta yi hak'uri mussaman da yara basu tayar da hankalinsu sosia ba, amma dukkansu sun yi kuka. Haka Farha har suka kusa isa Kano kuka take yi akan a barta a wajensu ba zata koma Abuja ba. Sai da barci ya sure ta sannan ta yi shiru. Taran safiya a gidan Yaya Hamida ta yi musu, suka karya sannan suka shiga daki Bilki ta sanar mata batun aurenta da Yaya Asad. Take Hamida ta fara kuka tana fad'in tabbas na huce dan ke na ji wa'azi akan illar gaba mussaman ace jini guda ke yin ta. Amma ki sa ni sai da kwakkwarn dalili za ki ga k'afata a gidanki. Me za ki yi da wannan mugun marar mutunci dattijo da shi zai dage sai ya aure ki. Allah ne ya rufa miki asiri bai lalata ki tun kina yarinya ba, masu kakin nan fa kad'an ne na kirki amma wominzers ne na k'arshe. Ai ni tunda bai zo ta'aziyar uwarmu ba, sannan ya daurewa yar iskar Abidan nan gindi akan Yaya Sulaiman Wallahil Azim ba ni ba shi. Dan haka soyayyar da zan nunawa ya'yanki sai na nunawa su Amrah da Farha amma nasa kam kadaran kadaran hakan ma saboda ta jikinki suka fito." Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 22:17] Hawaye a fuskar Bilki ta ce"Ni ma ba sonsa na ke yi ba, Yaya Faruku ne ya matsa mini amma ko Baba ma ce masa na yi bana sonsa". Yaya Hamida ta ce "Ni dai tunda kun shirya ke da su ba zan ce komai ba, amma ki sa ni Wallahi mu ba ruwanmu da su mussaman ma Asad mugun mutum mai bak'ar fuska da zuciya.". Kan dole suka goge idonsu suka yi hirar sannan aka yanka cake din d'iyar Hamida ta biyu wanda ranar take yin birthday da sai yamma za'a yanka amma Saboda ayi hotuna da su Bilki da Farha aka yanka a lokacin. Duk da Bilki harkar snacks ta k'ware Sai da ta tambayi wacce ta yi cake din tare da su samosa da springrols saboda dad'insu sannan da aka fad'a Mata Farashin sai da ta jinjina tare da karɓar lambar dan ta had'a ta da kawayenta na Kano da suke ta fad'in har yanzu basu samu wacce ta iya snacks irinta ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull