Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 8
Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 8: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 8. Da farinciki sosia Baba Babba ya gaisa da su yana jin auren…
3,747 words
Da farinciki sosia Baba Babba ya gaisa da su yana jin auren Asad da Bilki ne tsanin yin sulhu a zuri'arsu don kuwa ya lura ya'yan Baba k'arami gabad'aya basa iya yin mu'amala mai yawa da shi da ya'yansa dama Bilkin ce tafi sassauci. Yanzu kuwa saboda ita zasu yi mu'amala da gidan Asad daga haka kuma har komai ya warware albarkacin addu'ar da yake yi a kullum na kada zumuncinsu ya waste gabad'aya. Ya dinga sanya musu albarka tare da nasiha mai ratsa jiki. Yayin da tausayinsa ya kama Bilki ya tsufa sosai gabad'aya rauni ya baibaiye wanda ba na rashin gata ba ne illa na rashin cikakkiyar lafiya da kuma rauni irin na gajiya da duniyar da tashin hankalin da yake cikinta. Suka ajiye masa tasa tsarabar wnada jallabiyoyine fararen sai turaren alfarma. Haka momi ta dinga yi musu addu'a cikin bayyananen farinciki. Ta yunk'ura a hankali ta yi ciki wajen yaran tare da adduar Allah yasa Abida na gida. Dakin Abidan ta fara shiga ta tarar da ita kishigide a gadonta junior na kwance jikinta yayin da Farha ke can gefe a zaune tana cin cookie's. Amal da Noor kuma na kan kafet suna game a tablet. Farha na ganinta ta zabura ta mik'e ta nufe ta a guje. Yayin da Bilki ta yi yunkurin d'agata amma ga mamakinta sai ta kasa. Mamaki ya rufe ta don ba wani girma Farha ta k'ara ba haka nan ba nauyinta ne ya k'aru ba. Kan dole ta hak'ura ta rungume ta tare da jan hannunta suka zauna bakin gado. Ta kalli yarinyar ta ga idanuwanta sun cika da k'walla ta ce "Menene?" Muryarta na rawa ta ce "Mahma na dauka nima guduwa mini kika yi kamar yadda muka gudo muka bar su Yaya a Katsina". Jikin Bilki ya yi sanyi. A tausashe ta ce "Amma ai na sha fad'a miki ce wa "Duk inda zan je da ke zan tafi mutuwa ce kawai zata rabamu". Ta goge hawayen idonta tare da rik'o hannun Bilki ta ce "Dan Allah Mahma to zan biki yanzu ni dai na gaji". Ta fashe da kuka sosai. Bilki ta jata jikinta ta ce"Zan zo na d'auke ku tare da su Noor next week inji dadynsu ke ma yanzu shine dadynki". Ta yi shiru can ta ce "To dadynmu na Katsina fa?" A hankali ta ce mata "Dadynki ne mana. Amma tunda zamu koma gidansu Noor to ba uncle za ki ce dinga ce masa ba sai Dady". A hankali ta ce "To! Amma dai Mamah yau zan biki gaskiya. Junior ya yi ta tsokanata amminsa ta hana ni dukansa, su Noor ma su dake ni Ammi sai ta ce ",Ni na tsokanesu na rufe bakina na dame ta da kukan shagwaba. Alti ce kawai take kula ni". Na jijjiga kai na ce ki yi hak'uri idan kuka dawo gida ba zan bari su dinga dukanki ba, amma ke ma ban da rashin kunya tunda basu Yaya Amrah bane da basa iya dukan ki". Abida ta jijjiga kai ta ce "Duk yadda ake kaffa kaffa da ita ki ji sharrin da take hadawa?". Bilki ta yi murmushi kad'an ta ce "Ke dai Abida ki yi shiru amma Farha bata karya kawai kina bawa d'anki kariya idan ya tsokane ta. Abida ta jijjiga kai tabbacin mamakin yarinyar ya yi matuk'ar kamata. Daidai lokacin su Amal suka iso kusa da ita suna fad'in "Mahma sannu da zuwa, ina yini tare da Dady kuka zo?" Ta mik'a musu hannunta suka rik'e ta amsa da fad'in "kuna lafiya? Dady na falo". Suka fice da azama ta bude hadaddiyar jakar hannunta da ta siya wajen umm asalan Egyptian items..... Ta fito da tissue ta gogewa Farha hawayen idonta cikin rarrashi ta ce "Oya je ki gaida Dady ki yi masa welcome kada ya hana ki tsarabar da muka siyo miki ". Ta sauka da sauri ta fice. Sai lokacin ta mayar da hankalinta ga Abida da ta lura ta kafe ta da kallon k'urillah. Murya ba amo ta ce "A a Abida wanne irin kallo ne haka ne?" Da dariya ta ce "Ga ni na yi tamkar cikine da ke Maigado". Zuciyarta ta tsinke don kuwa ita da kanta tana k'alubalantar sauyawarta tashi guda. Sannan kasala ta dabaibaye ta. Kasa d'aga Farha d'azu ya sake jefa mata shakku a zuciyarta. Duk da bata da tabbas din cikin ne. Ta nisa ta ce "Daga dan zamanmu ne har za ki fara yi mini batun cikin Abida? Inace ban gama rufa watanni biyu da auren ba?". Abida ta watsa mata wani irin kallo ta ce "ko jiya kuka tare sai ciki ba zai shiga ba? Wannan gagarumar sauyawar da kika yi fa, ko duk vitamin A-z din da yake zuba miki a baki ne?" Save Restricted Contents Bot, [Sep 15, 2025 at 22:07] Wata irin kunya mai yawa ta dirar mata. Ta yi maza ta yi k'asa da kanta tare da fad'in "Allah ya shirye ki kawai". Abida ta kyalkyale da dariya tana fad'in ".Yaya Asad ya hada wata da aiki nan da watanni zamu ga sakamakon da zata ba shi. Kafin Bilki ta ce komai, Alti ta turo kofar da hanzari bakinta d'auke da sallama. Bilki na ganinta ta yi karfin halin mikewa da sauri suka rungume juna. Abida ta kallesu tana jin babu yadda za'a yi ta yarda ta had'a jikinta da na y'ar aikinta duk da dai Bilkisu ta yi matuk'ar yiwa Alti wanka babu wani abin aibu ko na k'yama a tare da Altin. Sakwanni biyar suka saki junansu dukkansu fuskokinsu d'auke da bayyananen farinciki. Alti ta zauna a gefen kafet yayin da Bilki ta zauna a inda take zaune. Suka gaisa cike da karrama juna. Jimawa kad'an Alti ta fice. Jummai wacce yar kabilar Nufe ce ta shigo d'auke da tiren ruwa da lemo ta dire a gaban Bilki sannan ta durkusa cikin gurbatacciyar hausarta ta ce "Anty barka da yanzu, sannu da zuwa". Bilki ta amsa da fad'in "Ba hausa mun same ku lafiya?" Ta murmusa ta ce "Lafiya kalau Alhamdulillahi Anty. Sannan ta fita. Jummai zata yi shekaru ashirin da biyar ta taba aure har da yaranta biyu suna can garinsu a Bidda a wajen Babansu, tunda suka rabu. Tun kafin a yi mata aure take hannun marigayiya Rukayya sosai ta iya gyara babu gajiya, haka nan ta iya girkin gargajiya daban daban dan idan tana yin sakwara sai ka zaci ba da hannu ake yi ba. Sannan ta iya rainon yara da juriyar fitinarsu. Amal da Noor sun yi matuk'ar shak'uwa da ita. Shiyasa har yanzu take nan tana kula da su. A zuciyatar Bilki ta kudire Alti da jummai kawai sun ishe ta amma charity sai ta bar gidan ba zata zauna ahalil kitabu na yi mata girkin abinda zata ci ba. A matuƙar sanyaye Abida ta ce "Yanzu Maigado ba za ki tausaya mini ki fad'a mini gaskiya akan Yaya Sulaiman ba. Ke ko tausayina ba kya ji. Dubu yadda vitamins din da ake zuba miki na watanni biyu kacal ya mayar da ke amma ni kullum k'ara baki nake yi ina yamushewa, sai na bude baki na fad'a miki ina da buk'atar a zuba mini ne?" Dariya ta subucewa Bilki ta sosai. Ta numfasa ta ce "Allah Abida kalamanki na kashe ni da kunya. Amma fa watannin baya na yi miki rantsuwar ban san inda yake ba. Wallahi tunda ya tafi ban sake ji daga gare shi ba." Hawayen nadama suka k'wacewa Abida babu zato. Cikin rishin kuka ta ce "Na gaji Bilki, Wallahi na gaji, ni kam na shiga ukuna". Tausayinta ya kama Bilki sosai ta matsa kusa da ita ta rik'e ta. Murya a dakushe ta ce "Sannu Abida ki k'ara hak'uri mu cigaba da addu'a da ikon Ubangiji idan yana raye zai bayyana.".
Cigaba Ta d'ago idanuwanta hawaye na tsere duk wata izza da jin kai sun k'wace mata ta ce "Wallahi yana nan da ransa, Wallahi bai mutu kawai tsabagen wulakanci da zalunci ne". Bilkisu ta kasa ce wa komai. Can ta numfasa ta ce "Abida tunda dai kad'an ya rage ki cika shekaru hud'u a dakon dawowarsa kawai ki yi gaiba idan kin samu miji ki yi aurenki tunda har kika furta mini kin gaji na tabbatar kin kai k'ololuwar gajiya ne tabbas". Takaicinta ya shake Abida a zafafe ta ce "Ce miki na yi ina marmarin wani rijalun ne bare ya biya mini nasa littafin ra'asin? Yaya Sulaiman din nake kewa kuma gangar jikina take mararinsa ba waninsa ba. Kawai idan za ki taimake ni, ki taimake ni, idan kuma ba wani taimakon da za ki iya yi mini to yaune rana ta k'arshe da za ki ce na yi gaiba don kuwa daga nan har mahdi ya bayyana zan jira shi ". Ta fad'a cikin kuka na sosai. Maigado ta kasa ce wa komai don sosai Abida ta bata tausayi Duk yadda take danne al'amura a ranta tare da jin kai matakin Yaya Sulaiman ya yi matuk'ar bugunta ta yadda ta fara sauke al'amura masu yawa. Ta tabbatar saukowar da ta yi take mu'amala da ita da kyau har da soyayyarsa da son sanin inda zata gan shi ko ta samu wani bayani gamshasshe. Da ƙyar ta shawo kanta ta yi shiru.
Tsawon lokaci suna zaune jugum jugum don sosai suka shiga alhini. A sanyaye Abida ta shiga bayi ta wanko fuskarta ta fito ta shafa hoda sannan ta fita dan gaida Yaya Asad. Suna gidan aka yi sallar magariba da isha. Basu bar gidan ba sai da Bilki ta damkawa duka yaran tsarabarsu kowa da ledarsa tunda ga kan Amal har zuwa kan Noor. Yan aikin gidan mata ma duk ta bisu da turare. Abida kuwa gwangwajeta ta yi da haddun materials din Malaysianfabrics....07020695644 Wanda take ta yi mata nacin tana so saboda kyaunsu da rashin nauyinsu. Suka tafi baba da Momi suna ta saka musu albarka. A hanya ya kalli yadda ta takure ta kasa sukuni. Ya tausasa harshe ya ce "Sarauniyar shaiba ya dai?" Ta yi shiru bata ce komai ba. Ya yi shiru don ya riga da ta gane ta idan ta shiga yanayi irin haka tafi son shiru. Maimakon ya sake yi mata magana da baki sai kawai ya kunna musu karatun alkur'ani suratul Maryam ta fara tashi da muryar sheik Afif. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: https://t.me/+us5UdbOzEc5iNWVk Kada a manta yau ma a daure a Danna mini likes din nan.
Sosai karatun ya daidaita mata rud'un da ta shiga na ina Yaya Sulaiman ya shiga tunda Abida ta kore mata tunanin ko ya hadu da ajaline. Suka isa gidansu da y'ansanda suka yi masa k'awanya. Ya kammala daidaita parking. Ta ga bai motsa ba. Sai kuma can ta ga ya sauke gilashin danƙareriyar motar, y'ansanda sun fi goma gabad'aya sun k'ame tare da sara masa. Hannu kawai ya daga musu suka sake sake sarawar sannan suka bar jikin motar kowa ya koma inda yake tsarewa a kusurwaowin gidan. Ta saka hannu da nufin ta bude murfin k'ofar sai ta ji ta a rufe. Ta kalle shi amma ta kasa ce wa komai. Sai ta ga ya bude ya fita. Ya kewaya ya bude mata k'ofar da kansa sannan ya yi mata irin gaisuwar da ta ga yaransa sun yi masa yanzun nan. Har cikin ranta tana matuƙar jin dad'in sarawar da yake yi mata. A duk sadda ya yi mata hakan har zuciyarta take jin lallai ita din sarauniyar zuciyarsa ce. Ta murmusa ta ce "Na gode Baban Bilkisu! Daga haka ta dan yi gaba ta bar shi yana rufe motar tare da magana da wani d'ansanda da bata ji me suke ce wa ba. Kaitsaye d'akinta ta nufa ta fara rage kayan jikinta. Daga nan ta fad'a bayi don ta yi maza ta yi wanka kafin ya shigo don sai ya ce shima wankan zai yi su yi tare. Duk saurinta ya shigo d'akin kafin ta kammala wankan. Abin da take zaton shine ya afku don kuwa bayin ya shiga babu jin nauyi. Ya tube kan dole sai da suka yi tare. Daga suka fito kuma abin da ya biyo baya masu nauyi ne.
Da safe Bilki zaune gaban madubi daga ita sai tawul iya cinya tana k'arewa kanta kallo don gabad'aya bata yarda da kanta ba. Maganganun Abida na cewar tana da ciki sun yi matuk'ar tsaya mata a zuciyarta. Zuciyarta ta harba ganin yadda breasts dinta suka cika suka tsaya sannan ya k'ara gari tamkar mai shafa mai. Haka nan ta ciko. Ta gasgata cikine da ita don kuwa rabonta da period tun wanda ta yi satin da za'a daura Mata aure. Ga shi wata na biyu ke nan. Ta furta 'Tirk'ashi ' a bayyane don gabadaya al'amarin wani iri take ganinsa. Wai itace d'auke da cikin Yaya Asad? Duk yadda ta gama fad'in bata sonsa shike nan sai a ji ta haihu wata tara da aure don kuwa tabbas kwanakinta a gidansa kwanakin cikin jikinta. "Wanne irin rabo ne na gaggawa haka?" Ta fad'a a fili . Yara basu dawo ba sai da ya cinye sati biyunsa da ya fad'a. Soyayya da riritawa ba wacce bata ga ni ba. Ita da kanta idan yana yi mata wasu abubuwan sai ta ga kamar ya wuce ya yi su. Bata fad'a masa batun cikinta ba shima kuma ya kife ta a baibai bai nuna mata ya gano ba. Alti Jummai da yaranta uku Amal Noor da kuma Farha sun dawo gidanta wanda Abida ce ta kawo mata su. Da farko Bilki tana zaune lafiya da Amal da Noor. Komai tare suke yi da Farha sannan bata banbanta su akan komai. Tana jinsu tamkar ya'yan cikinta. Yaran sun saba da ita tun a gidan Momi. Mahma sama Mahma k'asa kamar yadda Farha ta ke k'iranta. Sosia take jin dad'in zamantakewarsu. Tuni ta koma aikinta, kullum Kuma suna waya da su Amrah mutanen Katsina. Hankalinta ya kwnaata tabbas yanzu ne ta yi aure a da kam ba wani abu da zata idar na jin dad'i ko na nutsuwar zuciyarta. Har dinga ganin ba zata samu wata a gidan Yaya Asad ba don kuwa ta yi amannar yana matuƙar sonta k'warai da gaske.
*Bayan wata d'aya* Yana kishingide gefen gadonta ta shigo d'akin hannunta rike da bowl fari kal mai dan zurfi ta zauna gefe daga k'asa kan kafet. Tana cin abinta cikin nutsuwa. Ya zura mata ido yana nazarin yadda ta zama mai ciye ciye sannan ta ninka farinta, haka nan ta zama mai kwadayi.
"Madam ko dai na yi ajiya ne ba a faɗa mini ba?". Ya fad'a da wata irin murya mai kashe jiki. Ta matse ta ce "Ajiya a ina ke nan?" Ya yi murmushi mai sauti ya ce a cikinki mana ". Yadda ta kalle shi tana tura masa ɗan bakin nan nata ne yasa ya san cewa tabbas ya yi ajiyar bakin shi ya ƙi rufuwa saboda murna nan da nan ya ta so daga inda yake kwance ya rumgume ta yana sumbatar ta, cikin tsananin farinciki da murna. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Yayin da ita kuma take jin wani iri takura da zullimin yadda cikin ya yi mata shigar sauri. Amma kuma soyayyar da yake gwada mata tare da yin bare bare akan sha'aninta yana matuƙar k'warara ta.
Kwanci tashi har aka yi hutu. Hafcy da take hostel a Skyline University ta kammala aji d'aya zata shiga biyu. Bilkisu kuma ta kammala sakandire. Aysha ta kammala da Enugu ta dawo gida Sai Dai kwanakin sati ta yi ta wuce Lagos yin wani kwas na watanni uku zuwa yanzu ta cinye wata guda. Tun a kwanakin da ta yi Bilki ta gane Aysha tsagera ce, Sai dai bata nuna mata ma ta gane tana mata kallon riani ba. Yaran Basu Dade da dawowa gidan ba yaran ta fahimci halin kowacce daga cikin su. Bilkisu ta fi sauƙi sauki, kullum tana gaishe ta da safe, amma ba ta sake mata kamar da, duk da tana kokarin jawo yaran a jikinta. Hafcy kuma ba ta da kunya idan ta ganta sai kallon sama da k'asa tana tabe baki ko ta yi mata dariya, abin ya fara damunta amma ba ta nuna ba, kuma ba ta taba yi mata magana ba. Amal dai da Noor sune nata komai itace ke yi musu tare da Farha. Abu daya ne yake bata mata rai da Hafcy ko ba ta ci darajan matan ubanta ta gaisheta ba, to ta ci darajar ita kanwar uban su ce su girmamata amma yarinyar nan sam ba ta ganin girmanta da mutumcinta kamar za ta yi mata magana sai kuma ta fasa, ta zura mata ido kawai ta ga iya gudun ruwanta amma idan ta zauna shiru ko a wajen aiki ne sai ta yi ta tunanin kar dai ta baro gidan Sahal a dalilin rashin adalcin miji yanzu kuma ta faɗo l gidan da ya'yan miji za su tayar mata da hankali domin ga Hafcy nan ta dau hanya. Hafcy dai tata da suke son Juna. Duk shekarar Duniya Sai ta yi mata dinkin sallah, haka nan lokacin uwarsu na da rai akai akai take k'iranta ya gaishet Konda aka yi rikicin Ladi farm bata fasa k'iranta ba hakan ya tabbatar lwa Bilki ba'a hana yarinyar mu'amala da ita ba. Amma tunda ta dawo ta tarar da zama matar Babansu Shike nan take yi mata abubuwan Raini iri iri. Ko abinci aka dafa a gidan ba ta ci sai abin da taga dama zata bawa umarni Jummai ta yi mata ko Charity. Kullum za'a yi girkin gida amma Hafcy zata bada umarnin ayi musu nasu daban. Koada yaushe abinci kibikibi Kuma ba'a iya cinyewa haka aka barinsa ya lalace.
"Mahma anya ba za ki yiwa yaran yaran nan togaciyar girkin da suke Sawa ana yi musu wanda ya wuce bukartarsu ba? Abin da suke yi bai kyautu ba, idan megidan ya ga ni ba zai ji dadi ba." Alti take wannan batun da taa ga almobazarancin ya yi yawa .
Balki ta yi shuru kawai tana jin Alti na kora mata jawabi, yau ma hadaddiyar fried rice da coslow Ga Kuma pepper chicken aka dafa, amma Hafcy ta sanya aka dafa musu brown superghetti da pepper fish wai k'awayenta zasu zo. Har dare ba Wanda ya zo Kuma abincin gal warmers ko ta kansu bat sake bi ba.
"Mahma bai kyautu ba gaskiya. A matsayinki ta uwa a gare su ya kamata ki tsawatar musu."
Bilki ta jinjina kai, tasan gaskiya Alti ta fada, uwa take a wajensu kuma hakkinta ne ta gyara musu idan taga an yi ba daidai ba. Duk da ba ta so ta yi magana ba, amma ya zama dole tun kafin Megidan ya ga ni ransa ya baci kuma daga karshe laifi ya dawo kanta.
"Haka ne Alti je ki abin ki zan yi musu mgana in sha Allah" Ta tashi ta tafi ta bar Balki na nazarin yadda za ta tari yaran da magana, da ƙyar dai ta yi kundubslan tashi ta nufi dakin yaran har Farha duk suna cikin dakin tare da su, da yake suna da tibi a dakina suna ta kallon cartoon su kuma manyan na saman gado kowacce na latsa wayarta. Shigowar Balki ya ba su mamaki, domin ba ta taba shigowa dakin su ba. Tana shiga ta kalli su Amal ta ce "Ku je falo ku ce Alti ta kunna muku cartoon din a can Farha." Ta fada tana kallon ta da sauri ta yi gaba tana fadin" To Mahma Noor mu ku zo je."
Sai da suka fice sannan Balki ta mayar da hankalinta wajen manyan tana kallonsu.
"Sannu da gida Anty."[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: In ji mai sunanta Bilkisu. "Ya hutu?" Ta fada tana kallonta. Sai ta amsa da lafiya lau, da ma ita suna gaisawa marar kunyar ta k'arshe Hafcy ce. Yanzu ma ko kallon Bilki ba ta yi ba, hankalinta na kan wayar hannunta Stool din madubi Bilki ta jawo ta zauna lokaci daya tana fadin" Sannu Hafsat." Da gayya ta yi mata sannu domin ta ji kunya, idan ita ba za ta gaisheta ba, ita bari ta watsa mata kunyar gabadaya.
Amma yarinyar nan ba ta ji kunya ba sai ma ɗagowa da ta yi, ta sakar ma matw wani kallo kafin ta amsa da lafiya kawai ta cigaba da latsa wayarta. Ta ji wani iri amma sai ta danne ta numfasa ta ce "Bilkisu da Hafsat me ya sa ba kwa cin abincin da na saka ake dafa mana gabadaya?" Ta tambaye su tana kallonsu. "Muna ci mana." Bilkisu ta amsa amma ban da Hafsat.. "Ba kwa ci, sai dai ku saka Jummai ta yi muku naku daban. Kunsan kuma ba yadda za'a yi a dora tukunyar abinci a gidan nan a hanaku. Sai mu yi d'aku ku k'i ci, ku saka a dafa muku fiye da cikinku, abincin yana yin yawa da safe sai an zubar me ya sa haka?" Bilkisu ta yi shuru domin ita ko tana son ci sai Hafsy ta hana ta. Hafcy kuma ko nuna ma tana jin su ba ta yi ba.
"Ba zan takura muku sai kun ci abincin da na saka aka dafa ba. Amma ina so ku sani in har ba za ku ci ba, ku fada min, sai na fad'a mata ta daina sanwa daku idan jummai ko charity kuke son su dinga dafa muku ya wadatar ba sai an yi barna da yawa ba." Suka yi shuru ba wacce ta yi magana. "Ina fatan kun fahimta? "E Anty" Bilkisu ta fada kafin ta cigaba da fadin" Ki yi hakuri Anty." Bilki ta mike tana fadin" ba komai ni dama saboda b'arnan abincin ne ya sa na yi magana." Har ta kama hanyar fita ta ji Hafcy na magana cikin gunguni "Ai ko mun yi b'arnar Daddynmu ke kawowa ba wani ba " Ta fada tana hararan ta gefen ido. Bilki ta juyo tana kallonta da kamar za ta ce mata wani abu sai kuma ta kasa hadiyewa ta ce" Haka ne shi yake kawo wa." Daga haka ta fice daga dakin nasu, ta koma nata ta dade a gefen gado tana fama da zafin zuciya, yarinya karama take yi mata rashin kunya amma ta kasa daukan mataki. Ta dade zaune tana tunanin kafin kiran sallar mangariba ya tashe ta, ta shiga tiolet ta dauro alwala amma a ranta ta kud'iri niyyar ko mai za su yi ba zata sake yi musu magana ba, kamar yadda suka fada gidan ubansu ne, su yi yadda suka ga dama.