Kenza eBookz

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 7

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete - Chapter 7

Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 7: Dingishin kwado Book 3 & 4 complete Chapter 7. Kan Bilki a k'asa bata yarda ta dago ba ta ce "Shine nake son…

3,433 words

Kan Bilki a k'asa bata yarda ta dago ba ta ce "Shine nake son na ji ya ya matsayin yin harkar ta baki?" Abida ta dinga kyalkyala dariya mai k'arfi mussaman da ta ga Bilkin da dukkan zuciyarta take neman fatawa akan lamarin, kunya kuma ta hana ta d'ago su kalli juna. Har Abida ta yi dariyarta mai isar ta bata katse ta ba, kuma bata ce komai ba. Da kanta ta numfasa ta ce "Maigado fatawar addini zan yi miki matashiya ko kuwa ta likitanci.?" Murya ba amo ta ce "Duka Abida ni gabad'aya na shiga rudun ne. Kin san kanki yafi nawa ja, tuna mini ma na islamiya din". Abida ta zama serious tunda ta gasgata da gaske take yi a rude take. Amma k'asan zuciyarta sai mamaki take yi duk shekarun da Bilkisu ta shafe a gidan aurenta bata taɓa sanin oral sex ba sai yanzu? Ta numfasa ta ce "Bari na fara yi miki bayanin a mahangar musulunci a takaice" Bilkisu ta gyada kai tabbacin tana sauararen ta.

Abida ta fara da ce wa "Malaman da suke ganin halaccin saka al'aura a baki sun yin haka ne saboda babu wani dalili bayyananne a cikin Hadisi da Alqur'ani da ya haramta irin wannan aiki. Malaman musulunci irin su Yusuf al-Qaradawi suna da wannan ra'ayi! Haka nan kuma ba a ambaci wannan aiki a matsayin wani bangare na farfaganda ba a Hadisi, duk da cewa Musulunci ya jaddada muhimmancin aika d'an sako kafin fara mu'amala tsakanin ma'aurata kamar su sumbatar juna da tabawa da makamantansu da suka zo a Hadisi k'arara. Mazhabobin tunani (Mazahib) irin su Shafi'i da Hanbali sun dauki hakan a matsayin halattacce, sannan a matsayin wani bangare na yin wasannin da zai ƙara armasa mu'amala. Yayin da wasu mazhabobi ke daukar al'aura a matsayin najasa, suka haramta yi ta baki."

Da k'yar Maigado ta d'ago ta ce"Na fahimta to menene hangen likitoci kuma?"

Abidan ta nisa ta ce "A likitance ana iya yin mu'amalar ta bakine muddin babu wata cuta a al'aurar ma'aurata wadda baki zai iya kamuwa da wani ciwo sanadin hakan, sannan kuma babu rauni ko kuraje a wajen! Likitoci na ba da shawarar amfani da kwaroron roba ko dam ɗin hakori kafin yin kowane nau'i na jima'i na baka. Amma gaskiya mutane basu karbi amfani da wannan abubuwan ba ko kad'an. ". Bilki ta ce "To shike nan na gamsu na kuma fahimta".

Abida ta ce "Amma ba'a son idan har za'a yi mace ta bari a dinga tura mata har makwogaronta don kuwa tana iya kamuwa da infection din baki mai tsananin gaske wacce take rikidewa ta koma( Oropharyngeal) Sai dai maza sun fi mata had'arin kamuwa da cutar Oropharyngeal (tana kasancewa tsakanin wasu kofofi biyu ta makogwaro) . Idan har miji zai saka bakinsa a wannan wajen a tabbatar an tsabatce wajen sosai mussaman yadda halittar mace take da lungu da loko! Zaku iya yin abinku amma ki tabbatar kina tsabtace wajen da kyau, ke kuma kada a dinga kai miki har makoshi sannan kada a tsananta yinsa babu kakkautawa. Anfi son yin mu'amalar baki once in a while kin ga ne?" Bilki ta ce "Na gane sai dai ai shi din ne kuma, ko zai yarda? ". Abida ta ce "Ban ce kada a yi gabad'aya ba, amma kada ya wuce harshe da lebenki da zagayen bakinki. Kada a dinga yi har can cikin. Sannan ke ma ki tsananta kula da wajenki. Sai kuma a takaita yinsa ya zama a marmarce ta yadda ba zai zama kullum ba."

Gyada kai kawai ta yi tabbacin ta ji. Ta ce "Farha ta daina kukan nema na?" Abida ta ce "Jiya ma ta yi, yau dai ban tashi ba suka tafi makaranta. Amal da Noor suna d'an lallashinta. Abida ta bude maltina ta sha ta kalle ta ta ce Wato shanye abin da yake zuba miki kike yi shiyasa kika ce mini vitamin A-z?" Bilki ta mik'e tana fad'in "Kin baci Abida maganganunki sun fi k'arfin kunnuwana." Maimakon ta yi shiru sai ta ce "Yanzun saboda Allah shi Sahalun ashe kansa a duhu yake ko kuwa tsabar mugunta ya sanya bai taɓa jiyar da ke dad'i mai ratsa kwanya ba?". Bilki ta zuba mata ido ta rasa abin fad'a. Abida ya zarce da fadin ko da yake "Gwara hakan kin ga yanzu ai kin banbance mazan ma daban daban ne, na tabbatar kuma cikin k'ankanin lokaci yayana zai sa ki fara jin haushin soyayyar da kika yiwa wanccan yaron. Ba za'a d'auki lokaci mai yawa ba, za ki fara jin kunyar kiyayya muraran da kika dinga nuna masa tunda yana caje mini ke da kyau da kyau". Kan dole Bilki sai da dariya sosai ta k'wace mata tana fadin"Ba dai zan ce miki komai ba". Sai gaf da magariba ya sauko daga samansa wanda shine a k'ololuwar k'arshe.

Har dakin da yake jiyo muryoyinsu ya shiga da sallama. Abida ta amasa sallama tana kuma gaishe shi. Ya amsa yana ce wa "Autar momi sai yau kika zo mata?" Ta ce "Yau din ma ina laifi?" Ya kalli Bilki ya ce "To na fita masallaci sai na dawo. "A tausashe ta ce "A dawo lafiya". Daga haka ya fice. Abida ta dinga fad'in kin ga mutum ya washe ya k'ara k'uruciya wa ma zai ce ba sa'an aurenmu ba ne ? Oh oh Yaya Asad duniya ne, ya ga y'ar yarinya ta ji kayan aiki, shine ya rik'e wuta sai da aka kawo masa ita yake yin yadda ya ga dama da ita. To ki fad'a masa na ce ya batun motar tawa, na ji shiru fa. Tunda ya same ki sai ya cika alk'awarin da ya yi mini." Bilki ta zabura ta ce"Gaskiya ciccibin nan yana da kyau fa Abida gabad'aya fa na hade na ciko". Abida ta ce "Gaskiya kayan Bojuwa herbs ba algush, gangariya ne na shaida hakan Contact 08032773332 for all your kayan mata.

Bata tafi ba sai da ta yi sallar magariba sannan ta tafi a gaggauce. A harabar gate ta iske shi. "Yaya ya batun motar tawa ne?" Ta tambaye shi kaitsaye. "Tana daf da isowa Abida ai kinsan bana alk'awarin bogi" Ta ce "Hakane". Ya kasa sakewa da ita kamar da, domin sai yake ganin sun gama yin gulmarsa da Bilki tunda mata suna son hirar oza room. Cikin kwanaki biyar da suka yi suna cin amarci Bilki ta san ta auri jarumin maza kuma sadauki ji da ita yake yi kamar tsoka daya a miya ba ya fita ko'ina sai masallaci har wayoyinsa ya kashe abinci kuma safe da rana da yamma Abida ke aiko musu da shi daga gidan Momi. Bilki ta samu nutsuwar jiki da ta zuciya cikin sati daya a gidan Asad. Sannan ta gane zaman da ta yi a wanccan auren kusan zaman lalata kuruciya ne kawai. [10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: [Sep 15, 2025 at 21:55] A haka suka tafi k'asar America. Soyayyar da ya nuna mata da gata ya sanya ta fara jinsa a ranta ta dinga tuno lokacin da suka je hutu gidansa daidai haihuwar Bilkisu. Yadda yake shiga kicin ya yiwa kansa abinci a dalilin matarsa na da tsohon ciki. Tabbas yana cikin maza kadan da suke yiwa mata hidima da zuciyarsu da aljihunsu. Don a yanzu ma da ya girma bai fasa komai ba. Tana zaune sai ya hado musu coffee ko ya shiga kicin ya hado musu abin motsa baki dangin fruits ya kawo gabanta. Yawan motsa jikin da ya rayu akansa ya taimaka masa don kuwa bai tara teba ba, sannan kuma a tsaye yake kan k'afafuwansa ga kuzari da hanzari tunda ya rayu yana motsa jiki. Idan ya fita Allah Allah take yi ya dawo ya dinga damuk'arta, yana yamutsa ta tana jin dad'i har cikin kanta, abin da bata samu a inda ta zaci zata samu ba, take samunsa a inda ta yi zaton ba zata samu ba. Amarci gangariya suke zubawa wanda Bilki bata taɓa zaton ana samun irin haka ba. Shi kansa a zuciyarsa yake tambayar kansa wai mata dama ko wacce da irin taste dinta ne ko kuwa dan ita Bilki tafi matarsa k'uruciya ne? Gabadaya ji yake tamkar yanzu ne yake samun gamsuwa da nutsuwar da yake so. Har cikin bargonsa yake jin son Bilki irin yadda bai taba ji akan kowacce mace ba. Na ce ba? Kina nan kina ta yin tashin hankali akan namijin da idan kin mutu wata zai aura ya sota kamar yadda ya so ki koma fiye da ke har ya manta da soyayyarki? Dan Allah mata mu yi ibada, mu yiwa mazanmu biyyaya iyakar iyawarmu don kuwa aljannar mace zata fi gamsu ne idan mijinta ya amince da ita. Mu rungumi sana'a ko aikinmu da kyau a sassauta soyayyar da zata saka matsanancin kishin da zai hanamu sukuni ya halakamu. A guji canja halitta da nufin burge rijalu! Wallahi ba abin da zai sauya su daga zama polygamist. 😅 Kwanaki ashirin ya kammala aikin da yaje yi k'asar. Suka k'ara kwanaki biyar suna yawon bude ido a cikin birnin California.

Daga nan kuma suka wuce London ta k'asar Birtaniya. Kwanansu biyu a garin suka kaiwa Khadija ziyara makarantarsu. Itace kuma Bilki ta d'ade bata ganta ba a cikin ya'yansa, tun tana karama sosai. Kallo d'aya tak ta gane yarinyar ta juye Babanta sak ba abin da ya rabata da shi na kammani har hanzarinsa ta kwashe. Aysha da Amal ne suke kama da uwarsu. Sauran yaran kuma gasu nan ruwa biyune. Amma Noor ma kam kamarsu d'aya da Khadijan. Da walwala ta karbesu da girmamawa. Bilki ta ji dad'in girmamata da ta yi. Ta kudire a ranta zata iya kokarinta ta basu fuskar da zata zame musu uwa, su kuma shigo gidan ubansu ba tare da zullimin babu uwarsu ba. Ya ce tunda a hutu take ta zo su tafi masaukinsu. Cikin mintina kad'an ta fito janye da k'aramin akwatinta. Basu koma masaukinsu na sai da Khaditta jagorance su zuwa gidan abincin da suke da halastaccen abinci (Halal food). Daga nan suka koma hotel din ya kamawa Khadija d'akinta wanda tazarar gaske da nasu d'akin. Sosai suka huta suka sha hotuna wanda Khadija take yi musu wani sun sani wani ma kawia daukarsu take yi basu ankara ba. Zamansu na London ta fahimci Baban Bilkisu mai tsananin son ya'ya ne. Don kuwa asuba yake k'iran Khadiha ya ji ko ta tashi sallah. Idan zasu koma barci bayan sun idar sai ya sake k'iranta yana fad'in "Idan kin ji yunwa ki yi order duk abin da kike son ci kada ki ce sai kin jiramu". Idan sun tashi, sun yi wanka sun shirya sai sauka k'asa ta fito su hadu sannan a wuce wajen karya su karya tare. Sannan kuma ta fahimci shi mutum ne mai yin abu babu nuku nuku ko cutar da kai don idan Khadija zata yi musu hoto ita ce take nuna masa yadda zai tsaya ko zai rik'e Bilki. Ya yi kuma yadda ta ce din babu jin nauyi ko kunya. Haka itama yake rungume ta Bilki ta yi musu.

Ana jibi zasu bar London Khadijah ta ce "Dady zamu je gidan Anty Ayusha fa na fad'a maka tana mini kirki, Ina zuwa na yi weekend a gidanta, k'asan idan y'an arewa muka hadu a turai duk zama muke yi dangin juna. Ita da mijinta suna mana kokari suna guiding dinmu sosai."

Ya ce"To zuwa anjima idan mun je yiwa sisters dinki tsaraba sai mu je gidan". Sosai Khadijah da Bilki suka saba suka samu kyakkwar fahimta duk da Khadija tana yawan tuna mominsu tare da jin da yanzu itace a gefen Dady ba Anty Maigado ba. Sannan yadda yake zumudi akan amaryarsa ta gane ko momi na da rai zai iya nad'e k'afar wando ya yi zawarcinta har ya aure ta duk rikicin da za'a yi kuwa. Amma ta danne don kuwa gara ace auren ya yi da ace Babansu na harkar banza da zubar da mutuncinsa da nasu. K'arfe biyar saura na agogon GMT Ummi ta karbi ziyarar manyan baki cikin sa'a suka tarar da Baban Husna a gida dan haka da karramawa ya karbi kwamishina a falonsu. Cikin mintina kad'an aka cika gabansu da cimaka iri iri. Sosai ya yi musu godiyar yadda suke kula da su Khadija suka basu kofar zuwa wajensu. Ya yiwa yaransu kyautar bajinta sannan suka tafi. Bilki tana yaba kirkin Ayusha da mijinta tare da yiwa Husna, Hanan da Aryan addu'ar su zama masu albarka. Fatan alheri ga kanwata marubuciya Ummi Ayusha Muhammad da iyalinta da suke zaune a birnin London. Washegari suka mayar da Khadijah makaranta suka yi bankwana suka rabu cikin sanyin jiki don sun ji dad'in zamansu taree que ne illa tuna mominsu shike nan su da ita sai a darussalam. Ta dinga yi mata addu'o'in neman gafara har ta samu nutsuwar zuciyarta. Ta dauki wayarta ta shiga what'sapp ta shiga ta tura hotunansu cikin group dinsu da Aysha ta bude musu su kad'ai. Su hud'u ne a ciki Aysha Khadija Hafcy sai Bilkisu tunda itama da wayarta Amal da Noor ne babu su. Cikin mintina kad'an Aysha ta yi tagging hoton Bilki da Babansu ta ce amma kuwa Khadija kin ci amanar momi da kika turo mana wannnan abin, na rantse tunda na zo duniya ban tab'a ganin abu mai muni a zuciyata irin wannan pic's din ba. Yanzu Dady abin da ya zama ke nan, ji yadda ya wani mak'ale ta? Ke kuma da yake sarai sunanki shine har da turo mana?" Hafcy ma ta ce "Yaya Khadijah kam ai gabadaya al'amarinta babu kishin kai ". Bilkisu dai stickers din dariya take ta turawa babu adadi don gabad'aya Dady ne ya bata dariya yadda yake sanye da k'ananun kaya ya dawo kamar saurayi yana ta soyewa abinsa. Aysha kuwa ta kufula ta zazzage ta tare da fad'in zata cire ta daga group din tunda take dariya bayan abin kuka ne ya same su. Khadija ta ce "Ya Aysha ki yi hakuri Anty Maigado bata da damuwa. Da ya auro wacce bamu santa ba ta zo ta cutar da shi muma ta cutar da mu fa? Ai gara ita duk tsiya dai y'aruwarmu ce". Nan da nan Aysha ta danna voice na tsawon lokaci tana fad'in "Ta ina ta zama danginmu? Sun kai Baba Babba fa kotu? Sannan an ce za'a ba shi anty Laura don ta cigaba da kula da su Noor tunda sun saba da ita amma fir ya k'i ta. Sai kawai ya kwaso mana wannnan mai tafiya mazaunai na sittin, saba'in, sannan yanzu na gano tuntuni ya so aurenta tunda har mai suna ya yi mata." Ta fara kuka murya na rawa ta ce"Na tausayawa poor momi! Allah sarki ta sha wahalar haihuwa an tashi an sakawa d'iyarta sunan budurwa wohoho me za'a ce da maza ne?" Ta kammala cikin tsananin kuka. Khadija tana kwance tana sauararen Aysha jikinta ya mutu tabbas itama ta ji babu dad'i amma kuma ya zasu yi ne tunda ba zata dawo ba, sannan basu isa hana shi yin aure ba. Kanta ya kulle mussaman ita bata ga aibun Anty Maigado ba. Sannan zuwansu duk abin da zai yi mata baya shawara da matarsa kawai bata yake yi, kuma bata ga ko a fuska Anty Maigado tana jin babu dad'i ba. To shi ke nan duk kokarinsa na ya faranta musu, sai kuma su k'i kwnatar masa da hankali ta hanyar zama lafiya da matarsa. Ta kuma fahimci Aysha tana son jagorantarsu su musgunawa matar Babansu ta yadda zamanta da shi zai gagare ta. A sanyaye ta yi nata voice din da fad'in Momi is gone ba zata dawo ba forever. Mu yi hak'uri mu zauna da matar da Dady ya aura da girmamawa dan yasan mun gode da hidimar da yake yi da mu babu gajiyawa. Idan ya gane muna da damuwa da matarsa zai kasa samun nutsuwar da ta dace da shi. Don haka mu yiwa Momi addu'ar samun rahamar Ubangiji shine abin da tafi bukata. "

Nan da nan Aysha ta ce "Hidimar da yake da mu ashe ba Allah ne ya kallafa masa ba? Tunda ke ba kya kishin uwarki sai ki k'arata ke kad'ai sannan kada ki kuma turo mana wannnan bak'incikin! Hafcy ta yi tagging da fad'in "Wlh kuwa Yaya Aysha duk yadda nake son matar nan yanzu haushinta nake ji, tunda ta yi kuskuren auren Dady ai ba sauran girmanta a idona tamkar mai jiran momi ta mutu ta aure shi". Bilkisu dai bata ce komai ba sai dai ta shiga tunanin maganganun yayarsu na cewa saka mata sunan anty Maigado ma cin amanar mominsu aka yi. Daga haka Khadija ta sauka daga what'sapp din tare da tunanin Aysha zata d'agawa masu gidan hankali dama ita bata da dad'in mu'amala. Yayin da Aysha ta dinga jan kunnensu Hafcy saura su ce zasu shige mata. Tirk'ashi.

Ranar juma'a da daddarre suka sauka a birinin Abuja suka tarar da tawagar y'an sanda na dakonsu. Har gida aka kawo su. Ita dai Bilkisu tana kallon yadda ake ta k'ame musu tare da sarawar girma. Wannan nau'in gaisuwar na matuƙar yi mata dad'i a zuciyarta. A daddafe suka yi wanka da ruwan zafi sannan suka yi salla suka kwanta barci ya yi awon gaba da su don sun gaji lik'is. Da yake asabar ce da suka yi sallar asuba sake rungume ta ya yi suka koma barcinsu. Sai wajen 12 suka farka. Suka yi wanka sannan suka nufi kicin don karyawa don kuwa a cikin katafaren kicin din dainin eriya yake. Tuni an tanadar musu abinci kalakala na alfarma. Da kansa ya zuba mata sannan ya zubawa kansa. Ita dai cikin tsantseni take cin abincin duk kuwa da ba shi da makusa kawai ita yadda duka ba musulmai ba ne suke yi musu abinci ne ya dame ta. A tausashe ta ce "Baban Bilkisu mu je gida anjima mu gaida su Baba daga nan mu dauko yara da Alti".

Ya girgiza kai tare da fad'in "A a Sai na gama hutuna zasu dawo". Ta zuba masa ido ta ce "Baban Bilkisu ka ce mini fa za'a sake baka hutun tafiyar da ka yi na sati biyu. Kuma yanzu sai mu yi ta zama haka?". Ya zuba mata ido cikin wani irin salo ya ce "Ba za su dawo su dinga katse mana amarci ba. Dan haka gobe zamu je mu gaishe su amma ba da yara zamu dawo ba". Ta yi k'asa da kanta don har zuwa lokacin nauyinsa da kunyarsa basu gama barinta ba. Ya cigaba da kallon yadda ta sake yin fari, fatarta ta yi wani irin smooth na ban mamaki. Zuciyarsa ta harba da sauri don kuwa ta sauya sosai wanda bai lura da hakan ba sai a lokacin. Zuciyarsa ta amince masa cikine da ita don gabad'aya ta danyace ta sake zame masa yarinya sosai. Ya tafi lissafin aurensu idan har daidaine suna cikin sati na bakwai don anyi bikin da sati biyu suka tafi America. Sun shafe satika biyar kafin su dawo, ke nan suna daf da shiga watanni biyu. Zuciyarsa ta cika da farinciki a duniya yana son yara yana son ya'ya da yawa. Tun kafin ya tabbatar da zatonsa ya ji son abin da yake cikinta yana ratsa shi ta ko ina. Ya tausasa harshe ya ce "Me yasa kike son su dawo tun yanzu?". Cike da tab'ara ta ce "Gaskiya ban son abincin wannan matar na fi son na Alti". Ya yi shiru tare da tunanin yadda shi da iyalinsa suke son girkin charity mussaman ya rabota da hotel d'in da take aiki ta dawo zama a gidansa gabad'aya. Tana da d'akinta a sashin y'an aiki. Ya numfasa ya ce"To kafin su dawo ki dinga yi mana dan gaskiya ba zan yarda hankalinki ya kasu biyu ba a wannan kwanakin. Kawai ki bari na kammala cikace su". Ta rausayar da kai ba tare da ce masa komai ba domin duk zalamarta akan al'amarin yayan nata ya k'ure ta. Matuk'ar ya mu'amalance ta sai ya gurje ta da kyau. Ta fara jinsa cikin zuciyarta, duk wani kallon da ta dinga yi masa a baya na baibai ya fara gushewa daga idanuwanta. Ta gasgata Abida da take yawan fad'a mata bak'in namiji ba shine muninsa ba, sannan yayansu ba mummuna bane kawai dan ta rufe zuciyarta akansa ne. Yanzu kam ta amince ba mummuna bane sannan tabbas jarimi ne ko cikin jarumai. Washegari sai yamma lis ya dauke ta zuwa gidansu, da ledar tsarabar mutanen gidan. Da kansa yake tuki, yayin da take gefensa a zaune. Gabaɗayansu sun yi kyau na ban mamaki. Sassanyen k'amshi na tashi a jikin kowannensu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull