Duba min baya fakon biri - Chapter 32
Duba min baya fakon biri Chapter 32: Duba min baya fakon biri Chapter 32. Da kyat na samu kallaman sannu da zuwa ya sake fito min daga bakina don kaina…
2,795 words
Da kyat na samu kallaman sannu da zuwa ya sake fito min daga bakina don kaina daya fara juyawa a lokacin ina jin kamar zan amaye yan hanjin cikina lokaci guda. Hasaran rayuwa ko kana da rai baiyi ba wallahi don ga mutum har mutum tsayayye a zahiri amma ga idanuna bai cika mutum ba a wajena don raunin shi dana rifa na sani na boye. Don hakane bani iya kallonsa da kima ko daraja a wajena yadda na taso da tsanar mashayin giya tun ina fuciciyata sanin da mukayiwa yan giya shine irin fulanin daji din nan dakan fara tambadewa suke shan giya a cikin garin. Zasu biyo hanya suna tambele suna faduwa suna fitsari a wando da amai yara nabinsu da jifa suna masu waka sunyi marisa sunsha kwaya . Sam ban taba dauka akwai yan birni dake wanan rayuwan hasaran ba ashe abin badaga nan yake ba kowa da tasa kalan kaddara a rayuwa abin masiface in Allah ya nufa kana ciki zaka tsunci kanka a cikinsu din din gani nima yau abin ya shafi rayuwata. Shine zama da dan giya dan giyan kuma miji a gareni kuma dan uwana kaiconi da wanan rayuwan dana tsunta a kaina na fada cikin abinda baifi second ba na gama wanan tunanen lokaci guda. Key na murda hannuna rawa na mude gidan ban ko tsaya juyawa ba na shige ciki kai tsaye Allah ya taimaka akwai wutan Nepa a lokacin da sauri nayi dabaran zuwa wurin fanka na kunna don ya kore abinda nake ji kafin na juya zuwa dakina. Jakka na aje ina kaiwa zaune bakin gado dan tunane nayi dashi din akwai hakkin aure atsakanin fa kada Allah ya kamani da laifin hakan akaina wanan tsakaninsane da ubangijinsa. Da sauri na daga daga wajen na fito na nufi kitchen din mu ruwan roba na dauko mai sanyi tare da cup na dora saman wani dan ture na nufi falon dashi. Haba warin taba sigarine daya kunna still ya tareni a lokacin hakana daure har kafana na hardewa a waje daya don rudewa na nufi ida yake zaune ya mike kafa yana waya yana zukan taban a cikin harshen turanci. Dago kai yayi ya jefeni da wani kallo mai kama da muguwar harara wanda hakan ya janyo min faduwan gaba, gaba daya sai naji na rude a wajen lokaci guda. Wani irin tsorone da fargananshi suka ziyarci zuciyana jikina har rawavya dan somayi na aje cikin karfin hali ina fadim ga ruwanan cikin wani kyarman murya da ban taba sanin ina dashi ba a rayuwana. Na juya da sauri don in bar falon ai bankai ga dagawan ba naji tsukin shi yana fadin uban wa zai sha maki wanan abin da kika aje ko nayi maki kama da kazaimai ne wai ? Maza ki kwashe kayan tsiyarki a nan jaka kazama kidahumar banza kawai wai ku wasu irin dabbobine da baku da zuciya hakane ? Shin wai auren nan dolene kome da zaku nacein kamar ni kadaine a cikin dangi inba kwadayi ba da naci irin naku nagado ke baki zuciya ki koma gidan ubankine wai ? Ko ina kwadayin mace sai a rasa wace za a hadani da ita saike kucaka haka mutum da zubi kamar kara koda yake ba laifinki bane naci gadansa kikayi ai don haka ba abin mamaki bane idan kinyi. To ki sani akai kasuwa idan nine badai hafiz ba mata masu ajima ban kalla ba balle ke din nan da banga abin gani a wajenki ba har aba ko kun zata wanan farin naki zai iya rudanane wai ? To fararen suna can suna mutuwa akaina saina zaba make hole rayuwana dasu ba banza irin ki ba ya karasa da sakar min wani uban tsuki. Kada ki dauka donki nazo garin nan nazo don uwata da munafukin ubanki ke son kashewa aurene don in kwatar mata incinta ga kowa ba zuwan mutunci nayi ba da kika ganni nan a yau don haka na fara dake din kafin,,,,, Ina tsaye na bashi baya kamar an dasani a wajen a fusace na juyo kafin yakai karshe nasan zagin mahaifina da suka dafawa laifin hakan akansa zai komayi kafin nace. Ina sakin wani murmushin takaici a fuskana mai nuna takaici ga kalaminsa nace aikin banza dama hausawa sunce gwano bayajin warin kansa ai. Ni da ka ganni na tsagwaron biyayya ga iyayye ya zaunar dani gidan nan don in nuna masu sun haifi diyar da suka isa iko da ita a duniya kuma ako ina. Har ina abin kwadayi ga mai mumunan rayuwa irin naka a nan kadubeka ka dubeni in ba fin karfin iyayye ba nayi maka kama da zama da dan giya ? Wani zabura naga yayi dayasani ja da baya kadan don ganin bai taso ba naci gaba da fadin babu hayar jirgi data mota wanan dai uban nawa daka raina kuka mayar dashi asuwakin bankiku saboda daukan alhaki ya gama maka komai a duniya ai tunda har ya haifeni nakuma zamo matarka a yau kowa ya sheda hakan . Ba mamaki kila lokacin kana a cikin mayenka koda hakan ya faru amma wani gyatumin ya daura hakan don da son ran mune ba hadin kifi da kaska ko a hanya kuwa. Wani zabura yayi yana nufo ni tare da fadin ke kina nufin ubana shine wani gyatumin nace ashe ka gane ina kaiwa dakin na rufo kofa da karfi na saka key ina hakki. Tare da godewa Allah daya ban ikon fadin hakan koba komai yadai ji zafin zancen ai tunda ya taso hakan a kaina bada dan giya daga zuwanka sai masifan tsiya haka ? Wanan abin dame yai kama dama ashe haka matan yan giya suke famane da tarun hakkuri da takaicin rashin zaman lafiya indai hakane gaskiya daddy ya cutawa rayuwana da aura min dansa Hafiz da yayi. Baby kina ina ne mummy gani nan hanyar gidan hafiz daga nan zan wuce office ta fada bata tanka mata ba ta kashe wayan nata tana jan tsuki a daidai lokacin da mai gadi ya bude mata get din gidan ta tura hancin motanta ciki ke nan. Don hankalinta bai kwanta ba ga wayan da taji mahaifiyarsu nayi da dan uwannata daya kira uwar yana masifa sai ya halaka yarinyar nan ko ya bar mata shedan da ba zata taba mantawa dsshi ba har abada. Tun a waya ta fara surfa masa zagi ya kashe wayan haka ta kwana da zancen a ranta ta tashi dashi hakan yasata sammakon fitowa daga gida ta nufo gidan hafiz din tun misalin karfe shidda da wani abu na safe shinr uwar ta kirata ganin tayi sammakon fita haka. Tayi mamaki data samu kofan gidan a bude hakan ya nuna a budema gidan ya kwana ke nan ba,a rufe ba har gari ya waye haka kofan yana bude kai tasa ta shiga ko ina shiru a gidan . Hakan ya bata daman fara kiran sunan kanin nata daga inda take tsaye din ga kayan ruwan daya watsar wanda na kawo masa da tiren da cup har goran ruwan duk a watse cikin falon. Sai guntayen taban daya zuka ya warwatsar a kasa da kwalban yar mitsitsiyar giya duk a falon watse jin bai amsa ba yasa ta nufi kofana tana nocking tare da kiran sunana a lokacin. Can nake jin muryanta sama sama a inda nake zaune wajen dana idar da sallah ina addua tare da tunanen makoma a yau tunda yace sai ya halakani idan ya kamani kuma dan giyane ba hankali garesa ba zai iya hakan dayace yasa na kasa fitowa daga dakin. A hankali na bude dakin tana tsaye a kofan ta bini da kallo tare da fadim bai maki komai ba dai ko na girgiza kai a cikin takaici ina bata hanya don ta karaso dakin tace ki biyoni falo. Iya abinda ta fada ke nan ta juya zuwa falo din nabi bayanta din muna isa yana isowa wajen yake fadin zanyi maganin kine yar iska mara mutunci. Hafiz har a gabana kake gwada rashin mutuncin naka kome ka zauna kema samu waje ki zauna ta fada in a serious voice ga kowan mu kusa da ita na zauna a darare don kada ya taso yai min dukan dayace a banza. Dan shiru tayi kafin ta dago tace dani yau baki zuwa school ne da har yanzu kina daki da sauri na dan kalli inda yake zaune din ba tare da nayi magana ba sai cewa yayi wata tsiya takeyi a schoolbdin koda taje tace ban tambayeka ba malam kafin kace min komai ka kwashe wanan kayan kazantan naka daga nan kafin mummy ko daddy su iso gidan nan. Tunda kai baka da hankali ka rasa inda zakayi shaye shayen ka sai tsakiyar falon matarka don hauka hafiz kako san alhakin hakan ba zai barka ba hafiz wanan wani irin cin fuskane haka wai ? Anya hafiz kana tunanen gaba kuwa kashe mummy kakeson yi da bakin cikin ka kome an maka auren nan na gida don ka natsu ka dawo hankalinka amma ba a huta ba duniyace fa hafiz tsawo da fadi gareta hafiz. Komai shakiyancin mutum ba zai iya ganin iyakarta ba saidai taga nasa hafiz sai yaushe ne zaka natsu kaiwa kanka fada akan irin halaiyan nan mm akane hafiz ? Yanzu ka duba don Allah wani mai mutuncine zai shigo gidan nan haka ya kalleka da daraja ko ita din tayi daraja a idon mutane an samu gidan ku a haka ? Saidai ita matarka da yanzu ya zamo mata dole dole kuma tayi hakkuri dakai tunda kaddaran aure ya hada duk shaye shayen baban boy bai taba yinsa gabana ba asalima bansan yanayi ba sai bayan rabuwan mu nake jin hakan amma waya sani kaga koni matarsa bansan da yanayi ba sai a bakin abokin iskancin nasa yanzu nake ji. Ki bar hadani da wanan kucakar yarinyar da sunan matana a gidan nan wanan fitsarariyar kucakan zaki kira da matana ? Au matar waye a yanzu in ba naka ba kana da sauran ja ke nan ashe har yanzu baka fahinci manufar daddy na hadaka aure da yar uwarka ba to bari in warware maka idan zaka fahinta. Jiya daka dawo a mayenka ka fada min idan wata kake aure ba ita ba idan iyayyenta basu ji wanan haukan dakai mata ba jiyan nan amma ita gata ta shige daki tana hadiyan bakin cikinka. Yadda kake ganin an manna maka ita itama din hakan take gani tsaban biyayya ga iyayyene kawai kaganta a nan din zaune dakai wani kallo ya watsa min daga inda yake zaune din. Tace kwarai kuwa don a rufawa juna asiri daddy ya baka wace yake ganin zata iya hakkuri dakai a cikin dangin ko dangin aiba kowane zai iya yin hakan ba. Enough don Allah kina fadin haka saita dauka ita din wata tsiyace ai nifa ban kaunar yarinyar nan a rayuwata don ku sani. Anji a yanzu baka kaunarta itama bata kaunar ka ai amma yadda tayi hakkuri ta zauna kaima ka danne duk abinda kakeji game da ita a zuciyar ka yanzu ku zauna lafiya kada kuba iyayyen mu kunya. Keda kike ta zncen iyayye su zo su zauna da ita mana kosu ba wani a cikin dangi tunda bani kadai bane namiji ai ko it mum bata da diyan da zata hadata dasu sai ni ? Hafiz ta fada da karfi tare da mikewa tsaye tana fadin ka iya bakinka kada kazo ka fadi abinda zai zamo maka dana sani a gaba. Bani dana sanin komai ko agaban akan wanan mai zubin wawayen zan dawo ina dana sani kome nazone ayita ta kare a daina damuna da zancen wanan yarinyar ana katse min aiyukana dake gabana. Au haka kace ba zaka saduda ba ke nan ta kalloni tace ki tashi kije ki shirya ki wuce school kada ki makara wanan bai san ida ke masa ciwo ba tukun shima ya mike yana fadin idan taje ta tsaya can kada ta dawo gidan nan . Ni dai nashige ina fadin dayafi nono fari a zauciyana a gurguje na shirya na fito na samesu yabini da mugun harara yana jan tsuki ta mike tana fadin mu zamu tafi kaiwa kanka tunane akan hakan. Ban tunanen komai wallahi indai akan wanan yarinyar ne ta gama zama a gidan nan tace muje kyale mahaukaci idanta dawo ka koreta ina shike nan dai ? Motan ta bude muka shiga muka barta ciki har lokacin fada take kwasa dashi tana fadin banda haukan giya a aura maka mace kamar wanan ka tsaya kana bura uba da hauka wai kaiga dan iska ? Baki dai tsaya ya dakeki ba ko ta juyo tana tambayana hakan da kyat na sauke numshi na girgiza kai tare da furta a,a gareta ina hawaye . Kiyi hakkuri don Allah haka yake tun farko da bakin zuciyan nan nasa na banza balle ya fada harkan drugs yanzu shine iskancin nasa ya karu haka. Zancen yakeyi a yanzu baisan babban kuskuren da zai tabka ba a nan idan ya sake aka raba aurensa dake ba baki nayi masa ba wallahi sai yayi kuka da hawayensa ba yana muzantaki a yanzu ba nan gaba zai raina kansane a kan hakan. Ina dai baki fadawa kowa wanan zancen ba zeey don fadan zancen nan zaizo ya shafi kowankune don mutuwan aure baida dadi wallahi ko wani irin aurene kuwa saiya tabawa mutum zuciyansa. Kiyi hakkuri duk wanan haukan shirme yakeyi duk ranan da kuka zama daya dole ya sauko daga duk tsiyar da yakeji avyanzu balle komr hafiz yayi baya sa laifin hakan saboda yana da daurin gindi. Both mummy da daddy suna da hannu cikin lalacewan hafiz Don sun gwada masa gata fiye da tsamani yanzune daddy yake son nuna masa matsayinsa na uba agaresa an riga da an makara ga hakan ko . Nidai ban ma jin wasu zancen nata saboda hawayen dake zuba min duk da na dan makara ranan bata yarda na wuce class ba saida taga dan natsuwa yazo min ta rakoni har bakin ajin don ta daukar min excuse ga malamin dake ciki lokacin kada ya hanani shiga. Ranan haka na wuni a cikon bacin rai sai faman sake sake nakeyu a zuciyana kan yadda zamu kwashe dashi idan na koma din tunda ya furta kada in dawo masa gida a lokacin. Kamar yadda mukazo tare itace tazo ta daukeni don komawa gidan sai naji dan sanyin hakan datayi min sai dai koda muka isa gidan arufe muka samu gidan da katin kwado ya saka ta baya. A gabana ta kira mum tana fada mata abindake faruwa mummy din tace wai hafiz yana da hankali kuwa ko sai na bata mai rai akan zancen nan ne wai ? Kafin tace yanzu ina mama din tace gamu tare da ita gaban gidan tsaye sai mummy din tace ku dan jira yanzun zan kirasa ya bude maku. Amma anty dakin bari na koma gida kawai zaifi don karki tafi yazo yai min wani wullakancin daya wananbdin kuma tunda yace ba bar mai gidansa. Ki koma ina zeey baki yarda da zancena ba ke nan komawan ki gida ai shine babban illa kuma kikoma kice masu me tunda ba sakinki yayi ba balle kije da tushe. Gun baba zan tafi ba gidan daddy zan koma ba na bata amsa da hakan sai naga ta dago ta kalleni kafin ta girgiza kai tace shi baba garba din shine baisan tashin hankali ba ko ? Ai kina zuwa gida zance ya baci harma in ba ai hankali ba sai zumuncin su ya baci da daddy kan hakan don wanan ba karamin zance ba. Jan bakina nayi ban kara magana ba saboda tunane sa bakin ciki dake cina lokaci guda nine yau namiji kewa koran kare haka kuma ina lake saboda iyayye. Baifi rabin awa daya ba sai gashi da mota fuuu ya shigo saida maigadi ya kauce mai da sauri kadaya take shi muna kallonsa ya fito yana busan iska cikin tafiyan kasaita. Yazo dakey din baiyi maganan komai ba ya bude gidan zai juya ya tafine naji tace dashi abinda kayi ka kyauta ke nan hafiz kai me kake son ka zamane wai ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA [3/7, 10:17] Aishatu Aliyu Musa😀🥰: DUBA MIN BAYA FOKON,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
3️⃣1️⃣
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.