Kenza eBookz

Duba min baya fakon biri - Chapter 33

Duba min baya fakon biri - Chapter 33

Duba min baya fakon biri Chapter 33: Duba min baya fakon biri Chapter 33. Tare muka shiga ciki da ita bata zauna ba sai bin ko ina da kallo dayi nagidan ga…

2,571 words

Tare muka shiga ciki da ita bata zauna ba sai bin ko ina da kallo dayi nagidan ga falon sai warin taba sigari da wani tsami da nake zaton na giyane . Daki na juya zan shiga don ban iya jure jimirin wanan takaicin a idona da hancina naji muryanta tana fadin hakkuri zakiyi zeey ki fito ki gyara wajen nan don dan iskan baisan inda kansa ke masa ciwo ba har yanzu shi. Dole ke zaki zage ki gyara gidanki kada wani bakon kunya yakai ga shigo maki gida na hankan ga kinga akwai nauyi da kunya sosai don wanda bai sani bama sai ya sani yanzu ga halin da mijinki yake ciki ai. Cikin kuka na juyo ina fadin anty bazan iya wanan abin ba gaskiya kuyi masa magana idan zaisha ya tsaya waje don Allah yasha abarsa warin abin nan yana sa kaina juyawa sosai wallahi. Nasani zeey ko baki fada ba nasan hakan tare da ita muka tsaya muka gyaro ko ina tana fada min muddin yana gari kada in sake inyi wasa da saka kamshi ako ina a gidan. Bata bar gidan ba saida nayi muna girki mukaci tare ga mahaifiyarsu nata kiranta a lokacin don kira yakai ukku tana fadin tana gidan har yanzu muna gab da kammala cin abincin ya shigo. Ban dago kai nako kalleshi ba yana fadin wai ke har yanzu dama kina gidan nan tace to ina zani hafiz kana son kajawa mutane wani tashin hankali kuma inya kama in kwana a nan yau har kwana zanyi gidan nan ai. Dariya ya kwashe dashi yana fadin zakiko hadu da daddy yau ajiku don yanzu nasan ya dawo gida by this hours bai kai dare a wajeshi ashe kasan da hakan kai ina kafito yanzu ? Cikin gari mana ya fada yana zama kusa da ita yace naga mum da boy ai gidan hjy Binta na fito wurin salis acan nagasu zasu shiga islamiya,Ooh abokin tabaran ka ko ta fada tana hararansa. Kajiki da shirme salis din ne abokin tabarana kawai sako naje in karbo a wajensa wai meyasa kuke zargin salis ne haka sosai lokacin na mike ina fadin. Anty zanshiga ciki idan zaki tafi kiyi min magana na fada ina tattara kayan da mukaci abinci da ita a wajen ta dago ta dubeni tana fadin me kuma zakiyi a daki mu muna nan falo zaune ? Akwai assignment din da nake son dubawa na mrs buhari data bamu gobe take son assignment din nata kuma shi zan duba na fada tace dani to sai nashigo kinsan mrs buhari kuwa kuna kuka da ita department din nan don yar kaifice ita. Nasa kai na nufi cikin dakin ba tare dako juyowa ba zan shiga ke nan naji muryanshi yana fadin ba zaki ban abunci ba ke nan saina rokeki ko ? Kunga irin abinda nakewa ke nan mutum ya shigo gida mace tayi maka kimkam kamar icce wai kuce dole sai na zauna da wanan gaskiya nidai ancuceni wallahi. Ta bangarena tsaye nayi na kasa motsawa a wajen na kasa motsawa saboda banyi tsamanin zai bukaci girkina ba kodon yaji zanyi karatune yasa yake son making dina busy oho ? Muryan antyne ke fadin jeki zubo masa ina dama kin aje masa ai dauko masa ki kawo masa na shige kitchen din na tsaya na hada kamar yadda muke hadawa daddy nasa abincin. Da ace zaman lafiya mukeyi da ba wanda yaikaishi samun gata a waje don nidin training din mum ce banda matsala a wajen aiki don na iya komai na aikin gida tun ina gidan mu kuwa. Na dauko abincin zuwa falo a gabansa na dire kayan abincin na juya na dauko ruwa na aje ina jira inji cin mutunci da diban albarkan da zaiyi min a lokacin har na gama na kwanta banji hargowansa ba ma,ana baiyi wani cin mutunci ba. Anty tayi masa kur da ido tana kallonsa ko zaici abincin dayasa nakawo masa din ga mamakinta bayan tafiyana sai taga ya bude kulan abin ya kurawa tuwon semo din ido na dan lokaci. Ko harda abincin nata ba zaka iya ci bane naga ka kurawa abincin idanu kamar mai tunane ya dago yana sauke ajiyan zuciya yace to ya na iya naga kun hada min kai akan yarinyar nan har daddy na batun yi min baki akanta. Da murmushi ta sake tare da jin tausayin kanin nata ya kamata a lokacin hakan kuma ya kara tabbatar mata cewa ya fara saukowa daga abinda yakeji akansa kan auren. Yunkurawa tayi daga inda take zaune zuwa kusa dashi da kyau ta zauna tana fuskantarshi tace hafiz ina son muyi magana dakai na fahinta kadai san banda kowa duniyan nan bayan ku don haka kamar yadda ba zaka yarda a cuceni ba nima hakan ba zan yarda a cutama ba kasani. Hannu ya tsoma cikin ruwan dana aje mai don ya daureye hannun nasa ya soma daureyesu yace ina jinki ai ta kallesa lokacin da ya yanko abincin yana kaiwa bakinsa ta dan murmusa taci gaba da fadin. Ka fada min meye BC damuwanka akan yarinyar nan ko kuma auren ne baka so ga baki daya ka kasa tsayawa kayiwa mutane bayanin komai har yanzu. Don girman Allah ka fada min koma meye kada kace zaka boye min damuwan ka a yanzu don Allah kaga sai mu san meye mafita ga auren nan ? Abincinsa yake ci hankali kwance ya mata bayanin daba zai iya tsayawa yaiwa kowa shiba bayan ita da Addil yanzu ko ko yasha giyar wake ba zai samu Addil da zancen nan ba ai. Anty ta kura masa ido tana kallon yadda yake cin abincin kuma yana fadin zancen cikin kwanciyan hankali da iya gaskiyansa ke nan har kasan ransa baidai kaunar yarinyar nan zeey a rayuwansane. Cikin tashin hankali da sauri ta dafe kirjinta tana fadin Hafiz kasan me kake fada hakane kuwa yarinyar nan fa yar uwarmuce ta jini ko banza muna alakan da zaisa kasota a ranka. Yace kwarai kuwa na sani ai sanin da nayi din yasa ban taba jin ina son taba da kowa nata kuma bani fatan wanan ranan ma yazo da zance wai ni hafiz ina son ta Kai ta sunkuyar kasa tana sauraronsa don tasan akwai wuya yasoni koya nuna kulawa a gareni nan kusa ta dago tana fadin hafiz wai baka hango babban kuskuren da kake kokarin tabkawa rayuwanka nan gaba. Nifa haba Nafisat ya kira sunanta kai tsaye yana girgiza kai tare da fadin don Allah ki bari inma har kina tsamanin nan gaba yarinyar nan zata zamo wani abu har insota ki sani fa shi so a nan yake ya daki kirjinshi yace ba a goshi ba. Na fadawa daddy wanan maganan dazun don mun zauna dashi munyi magana sosai yau kuma ya fahinceni don iyakar gaskiyana nafada kema kuma shi nake fada maki yanzu. Amma ko ka tafka babban kuskure daka fadawa daddy wanan zancen haka kai tsaye don kafi kowa sanin laluranshi ta fada tana mikewa don barin gidan alokacin. Har anty ta tafima ban sani ba don ni ina daki bansan wainar da suke toyawa ba a lokacin saboda nasa daya fitar suka gani doni nafishi jin duk abinda yake ji a kaina. Don a rayuwana gaba daya yanzu na tsani in bude ido in ganshi ko inji an ambaci sunansa a gaba don shine mutumin dana fi tsana fiye da kowa a yanzu din. Jin karan tashin motocinsu ya tabbatar min da sun bar gidan a lokacin kuma hakan na nufin ba mutum daya ya fice da mota ba a lokacin na dan jima kafin na mike na fito falon . Tsaye nayi ina bin ko ina na falon da kallo kafin nayi ajiyan zuciya na taka na tattara kayam da sukai amfani daahi din saida na gyara tsab na saka kamshi na jawo kofan gidan na rufo da kyau na koma dakina na saka key. Zan iya cewa na samu sasauci daga hattaranshi a yanzu don kowa harkan gabanshi yakeyi a gidan tsakanina dashi ballema idan na hada mai breakfast tun safe na fita bansan ya yake karasawa ba. Haka zan dawo in samu gidan kaca,kaca in gyara da yamma ma zanyi abincin in aje masa in shige dakina amma haka zai dawo ya zauna ba kunya yaci ya koshi yabar min kayana a nan saina fito da safe in kwashe in wankesu. Duk da haka rashin haduwan mu yana min dadi sosai don hakane damuwa da fargabana ya rage min don ko da zaran na fita su hauwa da karatuna zasu dauke min hankali sai idan na dawo kuma gidan zan shiga fargaban kada ya dawo ya sameni a waje. Wanan yasa nake godewa Anty Nafisa don ina ganin cewa itace ta taimaka min har yake min hakan a yanzu don kafan da ya daga min. Gashi kamar hadin baki yan uwa bamai zuwa wajena balle kira har baba idan na kirasa a gyrguje zamu gaisa dashi yace yana aikine banda dogon hira dashi balle inyi masa korafi. Inda na gane bai gari wajen abincin daren dana kawo masane yadda na aje haka na samu abincin nawa na kwashe na gyarawa maigadi nayu masa dumamensa . Da zan fitane na kula da motarshi baya gurin da yake ajeta maigadi na tambaya shike fada min yana ganin kamar yayi tafiya don ya gansa da yar jakka ya saka a mota. Hakan yayi min dadi sosai saidana dawo school na bata lokacina na tsaya nayiwa gidan kwal na goge kujerun da ties din kasan har kitchen ga irin watauna don ina ganin kamar ina cikin kayan giyane a zaune. Rana sati kuma har lokacin bai dawo ba na kara bin gidan nayi mai gyaran gaske saidai da kuskure ban yadda na taba bangaresa ba don gudun sheri irin nasa. Hankalina kwance nake gudanar da komai don ji nake kamar ancire mun kaya ajikina ga rashin zamansa gidan kira,a na kunna ina zaune falon ga tashan African tv three na aiki a lokacin naji sallaman mum kamar a mafarki. Da murna na tashi na tareta sai bayan nagama rugumantane kuma na saketa ina fadin mum wallahi nayi fushi mum kamar kin manta kina ya a nan ? Dariya tayi tana fadin ja,ira kin taba ganin uwar data manta da yarta inba shirmenki ba ko yanzu ai son in ganki yasa yau na roki Alh daya barni inzo in ganki don nasan yau kina gida. Mum dama daddy ke hana kowa yazo gurina ke nan tace to inya hana ai daidaine tunda mijin ki yana gari yanzu ko da bainan ai kinga nazo da kaina ban aiko kowa ba. Mum wani miji kuma don Allah ? Ni ban masan baya nan ba wallahi nidai na daina ganinsa kawai hakan yasa nayi tunanen ya kara gaba ke nan kuma. Wani irin zance kike fadi mama kina matarsa har yayi tafiya tsawon kwanaki kice baki san baya garin ba wanan wani irin rayuwa kukeyi a gidan naku ? Shiru nayi don ganin ta kura min ido tana son taji wani abu a gareni hakan yasa na dukar da kaina kasa na daina kallonta. Tace yanzu shi da zai tafi bai fada maki zaiyi tafiya bane kome toni mum ina ruwana dashi mutumin daya fada gabana ya fada a bayana bai kaunan ya bude ido ya ganni balle a kirani wai da matarsa . Mama kina son Allah ya konaki ne akan hakkin aure kome ta fada tana lafeni da idanu cikin canza yanayin fuskanta lokaci guda na dan turo baki gaba ina dukar da kaina. Tace komeya fada ai ruwansa ke dai ki tsare hakkinki duk abinda kikasan mace nayiwa miji kada ki fasa ki masa sai ya saura gareshi amma ba ku taru ku halaka kanku haka ga banza ba . Mum ina fa girki dashi kuma yana ci ai nayi kokari ban fita gidan nan sai nayi masa girki na aje mai kuma koda zan dawo zan samu yaci haka kuma ina gyara gidan nan sosai ko yaushe,,, Ke arr rufe min bakinki wurin nan kada inzo in mamareki an fada maki yin girki kiba miji shine kawai abinda mace zatayi ta burge mijinta ? A gabanki nake shiryawa na wuce dakin Alh kin sani ba baki sani ba zaki min wani zancen girki can da da baki auresa ba an fada maki baya cin anincine kome ?. Gaskiya kin ban kunya dama nasan harda laifinki cikin wanan abin don da acebkin nuna masa ke mace ce kinsan kanki dole ya sauke wanan iskancin nasa. Kafin nayi magana saida na daga na kalli kofan dakin nasa kamar zaifito yaji mezan fada a lokacin nace mum cikin shagawaba anty Nafisa bata fada maki furcinnsa a kaina bane wai sai hawaye . Furucinsa waina banza mama sau nawa akayi irin wanan muna gani kuma ana tare an hayayafa a tsakani idan zaki natsu ki nasu mama ki maida kanki mace tunda ba haka zaki tabbata ba har abada kuna wasan boya a tsakanin ku. Watanku nawa da aure yanzu na takwasa kuke nemafa ke nan a yadda naji Asiya tsohon cikine da ita niki niki hakama mairo ance cikine itama da ita. Sai kece zaki zauna haka don baki san ciwon kanki ba kowafa hakkuri yake da auren nan da yaran da manya kuwa duk auren aiba wani dadi garesa ba kowa yasani amma haka ake daurewa da wullakancin dana miji don kowa raminsa yakewa dama. Sai kawai naga ta mike tsaye a cikin fushi tana fadin inzaki gyara ruwanki mama ni kinga tafiyana tasa kai ficewa daga gidan da sauri na mike ina bin bayanta tare da bata hakkuri kada ta tafi. Saida muka kai kofan fitane ta juyo tace min saurara kiji muddin kina son mu shirya dake to kibi maganata ko hafiz na dukanki kiyi masa biyayyan aure yadda Allah ya hallata muna yi mu mata kinga tafiyana. Ta fice ta barni tsaye sororo ina binta da kallo har saida naji tashin motanta na sauke ajiyan zuciya ina tambayan kaina anya mum tana min son gaskiya kuwa ? Idan ba hakaba tayaya zata umurceni da zuwa wurin wanan kaskantacen da baisan darajan ya mace ba baisan na iyayyenshi ba balle na wani kila dai so take a kwasoni a karye ranan. Haka kawai naji gaba daya na koma wata kalla nayi tunane iri iri a zuciyana ta ina zan farane da zancen mum kai ni dai gaskiya sai ince banyi dacen zuwa duniya ba a gaskiya. Kuka sosai nayi ranan don tun ina na zuci har na koma yi na fili ina maganganu ni kadai kamar tababa a cikin gida ko abinci ban iya tashi na girkawa kaina ba. Monday na shiga school tun haduwan mu da hauwa take korafinnko nayi ciwone during weekend don na fada sosai lokaci guda murmushi kawai na iyayi bancewa kowa kome ba na barwa cikina zancen yana cina.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3️⃣2️⃣

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull