Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 1

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 1

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 1: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 1. *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

3,326 words

*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Note:* Wannan Labarin ƙagaggen labari ne, ban yi shi don cin zarafin wani ko wata ba, na yi ne domin faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa, idan ya yi daidai da labarin wani ko wata ko kuma rayuwar wani ko wata, to akasi ne.

*SHIMFIƊA* A wasu lokutan na Rayuwa, akwai wasu dararen da ba sa zuwarma ɗan Adam da Bacci a cikinsu, sanadiyyar wasu dalilai....wanda wasu sukan rasa Bacci ta dalilin damuwa, Wasu dalilin tsayuwa domin ganawa da Ubangiji mai Rahma, wasu dalilin karatu ne, wasu dalilin tunani mai amfani ko akasin haka, wasu dalilin farin ciki wasu kuma dalilin bakin ciki. Wasu kuma, dalilin wata rashin lafiyar da za ta hana musu yin baccin cikin salama. A yayin da wasu kuma...sukan ke ta DUHUN DARE da mugun nufi wanda ya kan zamo silar cin amana, Sata, cin zarafi da raunata zukatan bayin Allah,kai a wasu lokutan ma, Rayuwar 'ya' ya Mata ta kan zamo Hadaya a laifukan da basu san da wanzuwar su ba a doron duniyar face a dulmiyasu a matsayin fansa wani lokacin. Tafiyar DUHUN DARE mai karatu, za ta sanya ka tambayar zuciyar ka cewa shin wannan wane irin zamani ne muka riski kanmu a ciki....Tabbas ba kowane irin laifi ne tarihinsa yake ƙarewa a dare ɗaya ba, Wasu laifukan sukan rayu a cikin zukata da tunanin dan Adam na har abada tare da barin tabo mafi ciwo a rayuwa.

*PAGE 1*

Misalin ƙarfe ɗaya da mintuna ashirin da uku na dare....(1:23am)

Unguwar ɗif take ta yanda ba ka iya hango komai a wasu lungunan sai tsananin duhu da ya mamaye sararin samaniya da ma duniyar baki ɗaya, ya yin da wasu lungunan ke ɗauke da hasken fitilun Sola da suke haska iya inda ake buƙatar hasken ya isa yanda ake buƙata.

Kasancewar DUHUN DARE ne, ba ka iya jiyo sautin komai sai haushin karnuka da ma wasu halittun da dare ne kaɗai mamorarsu. Amma kuma, hushin karnukan yafi yawa kasancewarsu matsayin ababen bada kariya ma'ana masu gadi a wasu gidajen,ya yin da wasu kuma ke shawagi a cikin unguwa don raɗin kansu.

Wata babbar Mota ce Highlander sabuwa baƙa wulik ke fake daga can nesa daga gidajen da ke yankin, inda babu alamar fitila ko wani haske sai tsananin duhun da baka iya ganin abin da yake wakana ta kowane ɓangare.

Mutum bakwai ne a cikin motar waɗanda suke zaune shiru tsawon lokaci ba tare da sun yi magana ba, sakamakon jiran cikakken lokacin da suka tsara suke jira ya cika domin fita su ke ta DUHUN DAREN domin aiwatar da ƙudurin su. Da wannan, kowa da irin tunanin da yake ransa musamman JAK wanda ya yi shiru tare da resting bayansa sosai a jikin kujera yana mai lumshe idanunsa tamkar mai bacci. Babu abun da yake tafasa a jininsa face muradin ramuwa.

Motar shiru take tsawon lokaci har zuwa yanzu, haƙiƙa sun saba fita operation kala-kala masu matuƙar hatsari da tashin hankali, but...wannan ɗin is different. Domin ba ƙaramin gida ba ne, sannan mai gidan ba ƙaramin mutum ba ne. Sun shafe tsawon watanni Shida suna tsara wannan aikin da aka basu domin su samu komai ya tafi Normal, amma kuma a yau ji suke tamkar shirin su zai iya lalacewa a kowane irin lokaci sanadiyyar irin matakan tsaro da kuma ma'aikatan da ke gidan.

Babban su wanda suke kira da Oga Jud, shi ne ya kalli gefen da mutumin da suka yo hayarsa ta musamman tun daga wata ƙasa domin gudanar da wannan aikin mai suna James suka biya masa kuɗi masu yawan gaske. Shi ɗin ya kasance masani na musamman, kuma ƙwararre dangane da harkokin na'urorin tsaro da kuma iya sarrafasu cikin ɓoyayyiyar hanyar da doka ta yi hani a kai.

A hankali Oga Jud ɗin ya sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya sannan ya cewa James ɗin.

"James...ka tabbatar cewa komai ya kambala ya ɗau saiti kuwa? Rai na yana bani wani abu James..."

Wani irin malalacin murmushi James ɗin ya saki duk da cewa basa iya hango shi da kyau sakamakon Duhun daren da suke ciki, yana jinjina kai domin basu tabbaci ya ce.

"Komai a yanzu yana ƙarƙashin iko na, na karkata tsarin manyan Cameras ɗin gidan gabaɗaya an canja musu tsarin aiki domin su ba za a iya dakatar da su ba, sauran kuma za su dakata da aiki na wucin gadi.."

Jinjina kai Oga Jud ya yi sannan ya kallesu ɗaya bayan ɗaya yana mai kiran sunan su, sai kuma ya duba agogon wayarsa sannan ya ce.

", Jak,James,Rado,Tiger, Ashu, Bamo...agogo ya nuna mana 1:30am dot. Yanzu aiki zai fara, kowa ya ɗau saiti ya mayar da hankali akan aikinsa, duk wanda kuma ya yarda ya kuskure...to ya tabbatarwa kansa cewa lallai rayuwarmu tana cikin hatsari gabaɗaya."

Daga haka za su buɗe motar su fito, wanda shi Oga Jud ta tawagarsa sun fito ne sunan kasuwancin neman kuɗinsu kamar yanda suka saba idan wani ya basu aiki. Amma kuma ban da JAK...wanda shi shi ne kaɗai ya fito wannan aikin ba don neman kuɗi ba, sai don ɗaukar fansar mahaifin sa wanda aka zurma ba tare da laifin komai ba sannan daga ƙarshe aka kashe shi kisa na wulaƙanci har lahira. Kuma wannan ɗin ita ce damar da ya samu, damar da duk wuya ba zai taɓa bari ta suɓuce masa ba komai rintsi,domin hukumomi sun kasa yi musu adalcin da ya dace, saboda haka, koda ace ma yau ɗin tazo da ɓacin rana, to yana fata da burin ya cika muradinsa idan yaso duk abin da zai faru ya faru.

Already sanye suke cikin baƙaƙen kaya daga sama har ƙasa kamar yanda suka saba, hatta takalmin ƙafafunsu baƙaƙe ne,fuskokinsu ma lulluɓe suke cikin Mask wacce kowa da kalar tasa.

A hankali suka fara tafiya yayin da kowannensu ke ɗauke da ƙaramar jaka wacce su kaɗai suka san abin da suka ɗauko a ciki. Wani Babban gida suka yi wa tsinke ginin Upstairs wanda ya amsa sunan sa Gida. Domin Hatta Ginin da a kayi a matsayin shamaki da ganin wanda yake wajen gidan, gina ce mai tsawon gaske wacce keda tsananin ƙarfi da matakan tsaro a jikinta na musamman, ƙofofin gidan gabaɗayansu bisa tsarin tsaron Na'urori suke tun daga main gate ɗin gidan har cikin ɗakuna gabaɗaya. Na'urori ne na motion sensors wanda duk yanda abu zai motsa matuƙar na cutar wa ne nan take za su iya gano shi tare da ɗaukar matakin kai tsaye. Aiki suke ba dare ba rana.

Ta gate ɗin bayan gidan suka durfafa kai tsaye wanda ba su yi tsayuwar minti biyar ba aka zo a buɗe ba tare da robotic sound ba Kamar yanda suka shirya.

Sanye yake cikin kakin security wanda da alama shima ma'aikacin gidan ne.

Thumb-up ya yi musu alamar everything is set and ready sannan ya juya suka bi bayan sa. A nan ya tsaya da su domin aikinsa ya ƙare kamar yanda suka haɗa baki da shi suka biya shi.

A hankali suka shiga ƙarewa gidan kallo, musamman Jak wanda ya ƙura ido yana kallon kowace kusurwa ta gidan da ɗakunan da suke a matsayin na mutanen gidan dake can sama. Babu inda haske yake, kowace window babu abin da kake iya hangowa sai duhu sakamakon kashe fitilar da akayi domin ba wa dare haƙƙkinsa daman bahaushe yace dare mahutar bawa, sai dai kuma,...akwai wani ɗaki ɗaya da suka hango haske da alama mammallakin ɗakin kodai yana farke yana wata sabga ko kuma ma'abocin son yin bacci da haske ne.

Ido James ya ɗaga ya kalli saitin inda Jak ɗin ya ƙurawa ido yana kallo sannan ya waigo ya kalle shi ya ce.

"Ɗaki na musamman ne a gidan, domin mutum na musamman."

Lumshe ido kawai ya yi sannan ya buɗe a hankali ba tare da ya yi magana ba.

Kallon James Ashu ya yi da ɗan mamaki a fuskar sa yace.

"Waye na musamman ɗin??"

Ware hannu James ya yi alamar ban sani ba sannan ya ce.

"I don't know Ashu, Bincike na ne ya nuna mini hakan."

Girgiza kai Oga Jud ya yi yace.

"if we exercise patients...zamu ga ko waye a ciki. let's focus please."

A bakin Main Entrance Door ɗin gidan James ya ja tunga ya tsaya yana mai kallon fuskokin su da kyau tare da jinjina kai ya fara musu bayani cikin nutsuwa.

"A binciken da na yi, akwai Control Room wanda ta nan ne gabaɗaya tsaron gidan nan yake tafiya. Bangon ɗakin cike yake da manyan alluna (screens) waɗanda ke nuna kowane lungu da saƙo dake gidan nan. Cameras ɗin Infrared da ke ciki, suna iya ganin motsi komai duhun da wuri ya ɗauka. Sannan akwai Na'urorin da ke gano mutum (Thermal sensors) Wanda ko da a tsaye mutum yake baya motsi tamkar saƙago to tabbas za su iya gano shi. Wannan tsarin tsaron ana kiran shi da ORION-9 wanda sai gidan wane da wane. tsari ne da ake iya gano fuskar mutum kowane iri ne nan take, tantance murya, duba tafiyar mutum, kai har da ma fahimtar halayyar baƙon da ya shigo gidan ba tare da ya sani ba. Wanda daga zaran ta hango wani abin da ba daidai ba, nan take za ta iya rufe ƙofofin gidan gabaɗaya, ko kuma ta rufe iya inda suspect ɗinta yake har sai jami'ai waɗanda ta tabbatar Jami'ai ne sun iso, ko ta aika da saƙon gaggawa zuwa ga mai gidan kai tsaye wanda idan ya bada order ɗin cewa a gama da kai seconds sun yi yawa ta hallaka ka nan take...."

Duk da irin hatsarin da suke da shi da kuma irin ƙaurin sunan da Gang ɗin na su yake da shi, jin irin bayanan James sai da yasa kowannensu ya haɗiye yawun wahala ciki kuwa harda Oga Jud. Sai dai kuma JAK... Jak shi ka ɗai ne wanda ko kaɗan bai ji ya tsorata ba, babu wani alamar ɗar-ɗar ko kuma jin cewa a ransa wai ba za su yi nasara ba duk da cewa wannan ɗin shi ne karon sa na farko.

"Hey... Jak! Are you with me?"

Cewar James yana mai kallon ƙwayar idonsa ganin kamar baya tare da su.

Jinjina kansa kawai ya yi tare da gyara tsayuwarsa da kyau domin ya tabbatar masa da cewa ya shirya.

Hannu James ya sake ɗaga musu gabaɗaya sannan ya jinjina kai ya ce.

" Wannan Na'urar ba daina aiki tayi ba, na yi amfani da fake information but na 2hours only...Yes I repeat is only for 2hours,saboda haka kowa ya zama focus sannan ya ankare da lokaci."

Daga haka James ya fito da wata ƙaramar na'ura ya manna ta a jikin ƙofar sannan ya daddana wasu numbers a jikin ta yana jinjina kansa ya ce.

"In 90 seconds...the System will enter sleep mode.."

A hankali kuwa, sai gashi ta fara reading, nan take fitilun tsaron gidan suka shiga sauya kala alamar cewa gidan ya dawo ƙarƙashin ikon James ɗin kamar yanda ya tsara na wucin gadi. Gabaɗaya Na'urorin suna kan aikinsu but duk abinda suke hange da aikawa da shi zuwa Control room ɗin ba Gaskiya bane duk na bogi ne kamar yanda James ya tsara.

Shi ne wanda ya fara shiga bayan ƙofar ta buɗe musu, nan take sai gasu a tsakiyar babban Entrance ɗin gidan. A ƙofar hawa benen da zai sadaka da ainahin cikin gidan za su tsaya wanda har yanzu James ɗin shi ne a gaba. Ƙofar ba mukulli ake sakawa a buɗe ta ko wani abu ba,ƙofa ce da take amfani da fingerprint da kuma Retina scan.

Jakar da ke rataye a kafaɗarsu za su saukar, kowa zai fito da safar hannu sannan James zai fito da wata ƙaramar Laser ya ɗora a wurin da ake saka yatsa ɗin domin tantancewa.

Wani shegen murmushi zai sa ke yi sannan ya jinjina kai ya ce.

"Wannan gidan...yana da matakan tsaro mafi hatsari ga ire-irenmu, amma kuma...duk abin da mutum ya ƙera tabbas mutum ne zai iya lalata shi da basirarsa."

A hankali ƙofar ta buɗe, nan take suka taka suka shiga. But ko a nan ɗin ma akwai robotic patrol wanda su tsarin aikinsu sai ƙafa ta ɗauke suke farawa daga nan zuwa ƙarfe biyar na asuba.

Wata ƙaramar ƙwallo ce ya fito da ita ya saki tsakiyar wurin,nan take sai gashi ta fashe wani hayaƙi ya fara wanzuwa yana mamaye ilahirin wurin a hankali, lokaci ɗaya Robots ɗin suka tsaya cak a inda suke ba tare da sake motsi ba.

Bayan sun tabbatar cewa sun isa wurin da suke so. Yanzu sai Oga Jud ya zamo shi ne jagora domin aikin James ya ƙare.

"James and Tiger, ku shiga ku fito mana da Alhaji Mas'ood ɗin, Rado da Ashu ku fito da Hajiya da sauran ƙananun ƙwarin, kai kuma Bamo ka fito da Mubarak, ni da Jak zamu fito da wanda yake cikin ɗaki na musamman da James ya faɗa."

A tare suka amsa da faɗin.

"Ok Oga Jud."

Nan take cikin mintuna ƙalilan sai ga su sun fito da su a tsakiyar parlour wanda ya gauraye da duhu, kowa da tsananin tashin hankali kwance akan fuskarsa. Babu abin da suke ambata a gigice idan ba Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ba.

Babu ma kamar Alhaji Mas'ood da ya kasa yin ƙwaƙwƙwaran motsi sakamakon mamaki, tsoro da al'ajabin da ya kama shi. Ganin irin waɗan nan mutanen a cikin gidansa ba ƙaramin abu ba ne, musamman da yasan irin matakan tsaron da yake da shi a gidan amma suka iya tsallakewa suka shigo, lallai su ɗin mutane ne masu matuƙar haɗari.

Dattijuwar da ta ɗora hannu a kai tana kuka a hankali ne Oga Jud ya doka mata wata irin tsawa da faɗin.

"Ke Hajiya NASMATU!!!"

A gigice ta ɗago kai ta kalle shi wanda ba ita ba, hatta Mubarak, Na'imatu da kuma sauran ƙananun yaran da ke wurin su uku sai da suka gigice jin muryarsa mai kama da ta fasashshen Kalangu.

Duk da suna a firgice, sun yi mamakin yanda ya iya ambatar sunan ta ba tare da kuskure ba.

"Ki rufe mana bakin ki."

Abin da taji ya sake furta wa kenan yana mai kallon inda take cikin hasken torch light ɗin da ya haska.

Da sauri ta saka hannuwanta ta toshe bakinta still hawaye na zuba daga cikin idanuwanta.

Daga haka ya mayar da kallonsa gun Mubarak wanda idan ba gumi ba babu abin da yake, hankalinsa a matuƙar tashe yake.

"Mubarak...na san cewa an ɗebo gajiya, ina maka barka da zuwa."

Sosai Mubarak ya ƙara saukar da kallonsa zuwa ƙasa, jin yanda zuciyarsa ke wani irin bugu tamkar za ta fasa ƙirjinsa ta fito tsabar tsoro da tashin hankali.

Daga haka Oga Jud ɗin zai mayar da kallon sa gun mai gidan gabaɗaya Alhaji Mas'ood Galadima yana faɗin.

"Ina maka barka da arzikin sauka Lafiya ranka ya daɗe...ni dai a nawa ɓangaren da ni da yarana, ba wani babban abu ne ya kawo mu ba. Tashi za ka yi kawai ka ɗauko mana Jakar da ka dawo da ita ɗazu, da kuma wannan Lambar yabo ta girmamawar da aka baka daga ƙasar China (Award) dama sauran guda huɗun nan na can baya. Sannan kuma ka ɗauko mana kuɗi, KUƊI! Kuɗi nake nufi abinda ake kira kuɗi, wannan shi ne kaɗai abin da muke buƙata..."

Jiki na masa wani irin mazari ya miƙe yana faɗin.

" Wallahi zan baku...komai kuke so zan baku, amma dan Allah ku ƙyale mini iyalina."

Jinjina kai Oga Jud ya yi yana murmushi ya ce.

" Ka burge ni Alhaji...da baka nuna taurin kai ba. Yi maza ka ɗauko. Kai Bado yi masa rakiya..."

Ya ƙarashe maganar yana kallon direction ɗinda Bado ɗin yake tsaye.

Bamo kuwa, kallon fuskokinsu ya shiga yi ɗaya bayan ɗaya sannan daga ƙarshe ya fito da wani hoto ya duba sai kuma ya kalli Na'Imatu wacce ke cikin tashin hankali ya ce.

" Ke Na'Imatu!!"

Lokaci ɗaya su ka ɗago suka kalle shi daga Na'Imatun da ya kira har Hajiya Nasmah cikin kiɗima da gigita.

"Miye zaku wani tsuromin ido a tare sai kace nace zan yi miki wani abun? Ki kwantar da hankalinki domin bakya daga cikin aikinmu..."

Daga haka ya kalli Ogan su ya ce.

"Oga Jud ba mutum ɗaya a nan fa..."

Jinjina kansa ya yi sannan ya ce.

"I know! What I think kowaye yana cikin wancan special room ɗin da James ya faɗa mana."

Wani irin tsalle zuciyar Hajiya Nasmatu ta yi jin sun ambaci cewa wai akwai mutum ɗaya da ya yi missing a wurin. A ruɗe ta harɗe hannayenta alamar roƙo ta fara magiya.

" Dan Allah! Dan Allah na roƙe ku... "

" Shihhh!"

Oga Jud ya ambata yana mai ɗora yatsarsa akan leɓensa alamar ta yi shiru sannan ya sake cewa.

"Kwantar da hankali Hajiya Nasmah Uwar marayu. Iya aikin da aka bamu, a iya shi zamu tsaya, bama taɓa tsallaka iyakar da ba tamu ba."

Muƙut! Haka za ta haɗiye kukan tana mai girgiza kanta da wani irin azabar tsoron abin da za su iya aikatawa.

Kallon ƙananun yaran ya yi waɗanda suka cure wuri ɗaya jikin Uncle Mubarak, ya yin da jikin su ke wani irin ɓarin tsoro ya ce.

" Faryat and Feroz...twins ɗin Muhammad ko? da kuma Mufida yarinyar wurin Dr. Mukarram?"

Jinjina kai Mubarak ya yi alamar eh, ganin cewar direct question ɗinsa shi yake tambaya domin shi yake kallo.

"Masha Allah! Allah ya ƙarawa rayuwa albarka."

Suna nan iyaka 20mnt sai ga Alhaji Mas'ood ya fito riƙe da kayanda Oga Jud ya lissafa ya yin da Bado ke tafe a bayan da bindiga a saitin ƙeyar kansa.

Buɗe kayan ya yi ya duba yaga komai ya cika cif yanda yace sannan ya buɗe wata jakar wacce a nan sai ga kuɗi tsibe na gida dana wajen Nigeria.

Dariya ya yi sannan ya miƙe ya kalli Jak, Ashu da kuma James yace.

"Mu je."

A tare suka nufi ɗakin yayin da Tiger, Rado, da kuma Bamo suka ƙara ɗaukar saiti tare da dasa bindiga akan Alhaji da iyalansa.

Kuka Hajiya Nasmatu ke ta yi ƙasa-ƙasa tana mai girgiza kanta tare da yin duk irin addu'ar da ta zo mata a rai. Sosai a yanzu ta ji ƙirjinta ya yi mata wani irin nauyi tare da jin yanda kanta ke tsananin sara mata.

Ganin sun durfafi ɗakin da gasken gaske za su shiga yasa Alhaji Mas'ood yin wata iriyar ƙara tare da faɗin.

"ANAAM!!!"

Harɗe hannayen sa ya yi alamar roƙo da shi da Hajiya Nasmatu da Mubarak cike da wata irin magiya da cewa.

"Dan Allah ku yi haƙuri...dan Allah ku ƙyale ta."

Wani irin zazzafan Naushi Tiger ya sauke wa Alhaji Mas'ood a baki wanda ya saka shi dafe bakin ba shiri sanadiyyar wani irin azababben zafin da ya ratsa shi.

"Kana ji ko yallaɓai...! Dan Allah Kada ku nemi tunzura mu...ka bari muyi komai mu gama cikin mutunci kamar yanda muka fara, mu ɗin nan ba baƙin tsanani ba ne."

Jin hakan yasa gabaɗaya su ƙara shan jinin jikinsu suna masu yin addu'ar neman tsari daga sharrinsu a cikin zukatansu.

A can ɗakin da su Jak ɗin suka nufa kuwa, Ƙwala kiran ANAAM ɗin da Alhaji Mas'ood ya yi, shi ne yasa budurwar dake zaune akan table reading ɗinta a cikin ɗakin da suka yi wa tsinka ta miƙe a gigice jin sautin muryar Abbanta a wani irin bahagon yanayi.

Ita dai a iya sanin ta lafiya ƙalau suka yi dinner, lafiya ƙalau suka gama fira har misalin 10pm sannan ya rakota har ɗakin na ta ta kwanta suka yi sai da safe cikin farin ciki da annushuwa. Ammienta, yah Mubarak, Aunty Na'Imatu da su Feruz duk lafiya ƙalau suka rabu a iya sanin ta. Masu aikinsu ma tasan cewa kowa kafiya ƙalau yake. To amma miye abun da yake faruwa da har Abba zai yi mata wannan kiran a cikin wannan Duhun Daren?

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull