Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 2

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 2

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 2: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 2. Taku ɗaya zuwa biyu tayi cikin azama da nufin fitowa sai gashi sun…

3,366 words

Taku ɗaya zuwa biyu tayi cikin azama da nufin fitowa sai gashi sun rigata buɗe ƙofar. Within minute idanuwanta suka yi tozali da wasu irin mutane, mutanen da za ta iya cewa tunda uwarta ta haife ta ba ta taɓa haɗuwa da mutane irin su ba, domin a iya shigar jikin su kaɗai ya isa ya gigita duk wani mahaluƙin da ya yi tozali da su.

wannan Mask ɗin da wannan shigar...,Shi ya tabbatar mata da cewa wannan Daren ya risketa a Mummunan yana yi, kai ba ita ba, hatta iyayenta da 'ƴan uwanta tasan cewa suna cikin hatsari. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!

Abu na farko da ƙwaƙwalwarta ta fara tunano mata da hasko mata ba kowa ba ne illa Abbanta.

Duk da irin mugun yanayin da take ciki, hakan bai hana mata Ƙwala kiran sunan Abbahn na ta ba, a gigice tace.

"ABBAH!!!"

Wani irin gigitaccen Mari ne Ashu ya kifa mata har sai da ta wuntsila wanda ya yi sanadiyyar ɗaukewar jinta da ganinta na wucin gadi. Daman ga shi wata yaloluwar sleeping dress ce a jikinta marar nauyi wacce Aunty Na'Imatu ta zo mata da ita a matsayin tsarabarta, hannun vex ce da ita sannan a iya cinyar ta ta tsaya mata, daman mai wando ce amma tsautsayi yasa ba ta saka wandon ba.

Kallon Jak Oga Jud ya yi cikin rashin imani ya ce.

"R×pe her..."

Kallon Oga Jud ya yi sai kuma ya kalli su James sannan ya sake mayar da ƙwayar idonsa akan Anaam ɗin yana mai kallon jikinta tun daga sama har ƙasa. Jin ya yi wani irin abu yana fisgarsa a hankali tare da jin yanda kowace irin gaɓa ta jikinsa ke amsawa.

Hannu Ashu ya saka ya fisge mata sleeping dress ɗin da ƙarfin tsiya nan take sai gata ta dawo daga ita sai pant wanda ko shi wani tattausan net ne mai matuƙar taushi.

Wani irin azababben kuka ta saki mai ban tausayi tare da saka dukkan hannayenta tana kare ƙirjinta ya yin da jikinta ya ninka ɓarin da yake fiye da ɗazu.

Haƙiƙa wannan abun yafi marin da yayi mata ciwo da ƙunci a zuciya. Da zai tambayeta zaɓi tabbas da tace ya yi ta maimaita mata marin har sai ta mutu da dai irin mummunan tozarcin da ya yi mata a yau.

Jak kuwa, ganin ta a haka sai ya ƙara gigita masa tunanin sa, hakan yasa kai tsaye ya abka mata ta ƙarfin tsiya ya shiga yaga mata rigar mutuncinta.

Ganin yanayin da yake ciki,hakan ya sa su Oga Jud ɗin juyawa suka yi waje, Ashu na faɗin.

"Ka more lokacin ka da kyau Jak."

Anaam baiwar Allah! Wacce ba ta san taci kasuwa ba amma rumfa ta zo da ƙarfin tsiya ta faɗamata. A yau ta yi kuka mai ɗauke da raɗaɗi, ta yi cizo, tayi duka da dukkan iya ƙarfinta, amma kuma duk a banza, domin a yanda ya ji sa a sama yasan cewa ko yankan naman jikinsa za ta yi ba zata iya dakatar da shi ba har sai ya tabbatar da cewa ya kambala aikinsa.

Wata irin razananniyar ƙara ta saki jin wani irin azabben ciwon da ya ratsa ta tundaga ƙwaƙwalwarta har zuwa cikin zuciyarta,wanda ba shi da yake ɗakin ba, Hatta iyayenta sai da suka kiɗime jin irin ihun da ta zuba wanda ya shiga har can ƙasan ran su.

Kuma daga wannan ƙarar shi kenan numfashi ya yanke a jikinta ba ta ƙara motsi ba.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 2*

Oga Jud na isowa ya kalli Hajiya Nasmah wacce ke kwance malale a ƙasa tamkar ruwa, hankalinsa a kwance tamkar baisan abun da yake faruwa ba ya ce.

"Miye ku ka yiwa Hajiya Nasmah? Kunfa sani daga cikin sharaɗin aikinmu na yau babu duka babu zagi..."

Rado ne ya kalle shi ya ce.

"Ba bu wanda ya taɓa ta Oga Jud, ina ga jin ihun 'ƴar ta ne yasa ta faɗi ta suma."

Girgiza kai ya yi alamar tausayawa kamar da gaske ya ce.

"Gaskiya mai aikin nan ba shi da imani ko kaɗan da ya sanyo wannan yarinyar a cikin jawadalin aikinsa...."

Zaunawa ya yi yana fuskantar Alhaji Mas' ood ɗin ya jinjina kansa ya ce.

"Yallaɓai kana ji na? Mu ɗin kawai 'ƴan aike ne,saboda haka ina fata ba za ka riƙemu a ranka ba. Ban san laifin da 'ƴar ka ta yi masa ba da har ya janyo ta cikin wannan al'amarin. Shawara ɗaya Yallaɓai....idan kuna hulɗoɗin ku na rayuwa to lallai ya kamata kusan da wanda kuke yinta. Duniyar nan ta canza gabaɗaya..."

A hankali suka ga Jak ya iso parlourn tamkar wanda aka yi wa mugun duka duba da yanayin tafiyarsa.

Miƙewa Oga Jud ya yi sannan ya kalli Jak ɗin ya ce.

" Jak...mun gama namu saura naka, now over to you."

Jak na jin haka ya saita bindigarsa direct akan Alhaji Mas'ood. Jira suke su ji ya ɗaukesa kamar yanda yasha alwashi but tsawon mintuna yana nan a tsaye kawai ba tare da ya yi wani yunƙuri ba.

Cike da zallar mamaki Oga Jud ya kalle shi ya ce.

" Jak! what are you waiting for? just killed him..."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Ita ce kalmar da su Mubarak ɗin suka furta a lokaci ɗaya tare da jin yanda zuciyarsu ta tsinke na cewa wai a kashe Abba.

Mubarak ba ƙaramin gigicewa ya yi ba wanda tuni ya manta cewa wai a gaban su yake, domin wani irin ihu ne ya ɓarke da shi yana ta wasu irin sabbatu na fita hayyaci itama Na'imatu haka.

Tsit! Suka yi suna jiran su ji saukar harbi kamar yanda suka ji ya ambata, but har yanzu yana nan a position ɗinda yake ba tare da ya motsa ba.

Agogon hannun James ne ya yi ƙara alamar alarm ɗinda ya saka domin ya ankarar da su ya ɗauki saiti.

Da sauri ya kai idanunsa ya duba sannan a firgice ya zaro ido ya ce.

"Oh shit! 17minute remain..."

Jin hakan yasa cikin wani irin ɓacin rai Oga Jud ya kalli Jak ya ce.

"Damar mintuna kaɗan ne kake da ita Jak...kuma daga zaran sun wuce ka rasa damar ka kenan ta har abada..."

Jinjina kai Ashu yayi ya ce.

"Yes Jak...ka ɗauki fansar ka tun lokaci bai ƙure maka ba...just shoot him! Shoot him Jak.."

Gudu suka fara ganin da gaske neman yake yasa kwaɓarsu ta yi ruwa, da sauri Oga Jud ɗin ya saita bindigar ya danna Kunamar, but cikin wani irin zafin nama Jak ya saka hannayensa ya turesa da ƙarfi sai da ya yi baya wanda saura ƙiris yakai ƙasa, hakan sai yasa bullet ɗin ya kauce daga saitin kan Alhaji Mas'ood ɗin ya sauka a damtsen hannunsa.

Wani irin kallo ne dukkan su suka bi Jak ɗin da shi na mamaki da al'ajabi.

Muryar James da ta sake karaɗe musu dodon kunnuwansu da cewa.

"11 minute left."

Jin hakan yasa suka kwashi kayansu James ɗin ya shige gaba suka fice daga gidan.

******

3:30am Dot. Ƙarfe uku da rabi na dare....Wannan shi ne cikakken lokacin da Na'urorin gidan suka shiga ƙugi tare da dawowa kan aikin su daidai. Cikin seconds Control room ɗin ya rikice tare da sakin Informations kai tsaye akan cewa an samu short na time na tsawon 2hours yayin da sauran Na'urorin suka dakata da aiki gabaɗaya.

Kafin ka ce mi, unguwa ta ɗauka cewa ɓarayi sun shigo suna ciki, domin hatta mutanen unguwa Na'urorin tsaron gidan Alhaji Mas'ood suna matuƙar taimaka musu. Hakan yasa kullum suke bacci cikin lumana da kwanciyar hankali domin babu wani ɓarawon da ya isa ya shigo cikin wannan yankin nasu ba tare da an kama shi ba.

Mubarak...duk girmansa, duk jarumtar sa ya kasa daurewa, bayan ya tabbatar cewa sun fita ne ya janyo su Feruz a jikinsa ya dinga rusa kuka tamkar wani ƙaramin yaron goye.

Na'Imatu ita ce wacce ta yi ƙarfin halin miƙewa jiki ba ƙwari taje ta kawo ruwa sannan ta kunna fitilun ɗakin wanda nan take sai ga cikakken haske ya gauraye ko'ina.

Can suka hango Abbah wanda jini ya gama wanke masa jikinsa yana kwance shame-shame a gefen Ammie shima ba numfashi a tare da shi.

Da gudu suka isa gun su ita da Ya Mubarak ɗin. Karɓar cup ɗin ya yi ya yayyafa mata a hankali sai ga shi ta buɗe idonta waɗanda suka canja launi tsabar yanda tayi kuka na tashin hankali, bata ƙara ruɗewa ba sai da taga Alhajinta, Mijinta kwance a gefenta wanda babu abin da zuciyarta ta raya mata kai tsaye face cewa ya riga da ya mutu.

"Ya Allah! Ya ubangiji ka tausayemu kasa wannan ya zama cewa mafarki ne nake da gaske..."

Tamkar wata 'ƴar maye haka ta ɗago ido a dusashe tana kallon su ɗaya bayan ɗaya, domin ta tabbatar waye da waye suka kashe bayan Alhaji da Anaam ɗinsu.

Can ta hango Su Faryat sun haɗe kai wuri ɗaya suna ta kuka, ko kaɗan sun kasa matsawa inda Alhaji yake kwance a ƙasa sakamakon jinin da suka gani. Kallo ɗaya za ka yi musu ka tabbatar cewa a firgice suke, a matuƙar-matuƙar firgice suke.

Janyo Alhajin Mubarak ya yi zuwa jikinsa yana mai tattaɓa ko'ina na jikinsa tare da sake fashewa da kuka yana faɗin.

"A'a.. Alhaji! Dan Allah ka tashi, ka tashi dan Allah, In Sha Allahu babu abin da zai sameka. Anaam tana nan itama lafiya, babu abin da ya same ta ka yarda dani.."

Ruwan da Na'Imatu ta kawo ne ya janyo da sauri yana shafa masa a fuska, cikin ikon Allah sai gashi shima ya shiga sauke numfashi duk da cewa yana cikin tsananin azabar ciwo.

Buɗe idonsa na farko babu abin da ya fara ambata sai Anaam.

" Anaam! Mubarak ina Anaam? Kashe ta suka yi ko?"

Da ƙarfi ya girgiza kansa yana faɗin.

"Anaam tana lafiya Abbah..."

Lokaci ɗaya wayoyinsu dake ɗakunan su suka hau ɓurari, wasu shigowar saƙuna ne wasu kuma kira ne ta ko'ina.

Ɗankwalin Na'Imatu Mubarak ya fisge da sauri ya shiga ɗaurewa Alhajin Hannunsa inda suka harbe shi. Bayan ya kambala ya miƙe ya kalli Na'Imatu wacce ta rungume su Mufida gefe ɗaya suna ci gaba da kuka sannan ya miƙa ya wuce ɗakin Anaam hankalinsa a tashe. Ganin hakan yasa Hajiya itama ta rufa masa baya a hankali tana mai jin wani irin sabon tashin hankali na daɗa dugunzuma rayuwarta.

Da sauri Mubarak ya shiga furta.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Wayyo Allah! Miye suka miki ANAAM??"

Ganin irin halin da take ciki. Cikin azama ya ja bedsheet ɗinta wanda sai a lokacin ne Idanuwan Ammien suka sauka akan Anaam ɗinda ke kwance kamar mataciyya ba kaya jikinta.

A wannan karon, zuciyarta ce ta buga kai tsaye ta faɗi ganin irin mugun yanayin da Anaam ɗinta autar ta take ciki. Sam ko kaɗan ba su ɗauka cewa wai sun aikata mata wani abu makamancin hakan ba, domin sun ji wanda suke kira Oga Jud yace babu abin da suke buƙata sai wannan kayan. And da suka ji ya yi magana akan ANAAM ɗin ma sun ɗauka cewa kasheta ne suka yi. Ashe ta'adin da suka yi mata kenan.

Mubarak ɗin ma, gefen Anaam ɗin ya samu tare da janyo ta jikinsa ya fasge da wani irin kuka.

Kallo ɗaya idan kayi mata ba ka marmarin sake kallon inda take domin hatta fuskarta ta kumbura da bakinta, ga zanen ƙumba nan ta ko'ina tamkar wacce ta yi faɗa da mahaukaciyar Mage.

Wayar ta da yaji tana ringing ne ya sa ya mayarda ita akan gadon ya miƙe ya je ya ɗauka akan Table reading ɗin ta.

"Yaa Muhammad"

Shi ne sunan da ya gani. Hakan yasa a gigice ya yi picking muryarsa har tana sarƙewa ya ce.

"Yay..yay...yaa Muhammad Anaam ɗinmu..Anaam da Abbah Ya Muhammad!!!"

*******

Gefen su Oga Jud kuwa, tunda suka fara tafiya a motar yake ta surfawa Jak ɗin ruwan bala'i akan abin da ya aikata na ƙin kashe Alhaji Mas'ood da kuma hana sa shi ya kashe sa da ya yi.

Tun da suka fara tafiyar, ya yi masa tambaya tafi cikin kwando amma kuma tunda ya jingina bayan sa jikin kujerar tare da runtse idanuwansa har yanzu bai ɗago ko sau ɗaya ya kalle shi ba, haka kuma bai ce masa ko ci kanka ba.

Haka suka yi ta keta Duhun Daren suna zabga gudu wanda ba su tsaya a ko'ina ba sai a maɓoyarsu mai tsananin hatsari wanda su kaɗai ne a cikinta. Tamkar wani ɗan maye haka Jak ya tangala ya samu ya faɗa ɗaki tare da faɗawa kan katifa sai bacci.

******

2:42pm. Ƙarfe biyu da mintuna arba'in da biyu na rana. Gidan Alhaji Mas'ood. Damɓa Area, Gusau. Zamfara State, Nigeria.

Sosai gidan ya ruɗe da hayaniyar mutane a wajen gidan da kuma harabar gidan, wanda wasu daga cikinsu maƙota ne, wasu 'ƴan uwa, wasu kuma ma'aikatan gidan ne sai Jami'ai na musamman da suka iso gidan kusan Kaki yakai kala uku domin bincike.

Control ɗin room ɗin manyan jami'an suka shiga tare da ma'aikatan naurorin tsaro suka fara bincike. Haka ma ma'aikatansu kaf an tsare su domin bincike.

Mubarak yana tsaye a saman farfajiyar harabar ɗakin Abbah, ɗan wuri ne haka aka killace domin shaƙatawa idan buƙatar hakan ta taso. Ƙayataccen wuri ne wanda aka ƙawata da kayayyakin zamani sannan ga wani glass da aka saka a kewaye shi gwanin sha'awa.

Tsaye yake yana facing waje, babu abun da yake sai kallon mutanen da ke ƙasa suna jimami da alhinin wannan abun da ya faru, kowa ya ji cewa ɓarayi tabbas sun shiga gidan na su har sun harbi Alhaji Mas'ood, amma babu wanda yasan da zancen cewa wai an yi wa Anaam fyaɗe.

Yana nan tsaye tamkar wani mutum mutumi ya hango shigowar motar Babban Yayansu wanda shi ne na farko a gidan Yaya Muhammad amma wasu daga cikin iyayen su da Madu suke kiransa, shi a Abuja yake zaune tare da matarsa Amina da kuma yaransu huɗu, Farouk wanda shi ne babba mai shekara goma sha biyu,sannan Fatima mai shekara tara sai kuma en biyun su masu shekara bakwai wanda su yanzu haka suna nan a gidan kakan nasu Alhaji Mas'ood wanda shi ne ya taho da su bayan ya biyo inda suke a Abujar bayan ya dawo China tare da shi da Mubarak.

Yana gama hango fitowarsu motar tare da Yaa Amina ya sauko a hankali suka haɗu a Main parlour na ƙasa.

Wani raunataccen kallo ne Ya Muhammad ɗin ya bi Mubarak dashi ba tare da ya yi magana ba.

Jinjina kai Mubarak ya yi tare da share guntun hawayensa murya a ƙasa sosai ya ce.

"An yi nasarar cire masa harsashin, Hajiya ma ta samu heart attack ne bayan arba da mummunan lahanin da suka yi wa Anaam, but da taimakon Allah yasa likitocin samun nasarar ceto ta rayuwarta, amma kuma she's still she's unconscious....but Anaam!"

Kawai sai ya fashe da kuka mai ciwo sosai yana mai jinjina kansa cike da jin wani irin raɗaɗi a ƙirjinsa ya kalle shi sai kuma ya kalli Yaya Aminar ya ce.

"Ya Muhammad! Ya Muhammad Sun ce Anaam tana raye amma har yanzu babu numfashi a tare da ita. Babu wata gaɓa ta jikinta dake motsi ko kuma nuna alamun rayuwa a tare da ita...Ya Muhammad ina jin tsoron kada ace wani mummunan abu ya faru da ita...."

Cike da karaya Ya Muhammad ɗin ya taka tamkar mai tsoron gamo da wani mummunan abun ya haura ta matattakala zuwa cikin gidan inda babu wanda aka bari har yanzu ya haura ciki.

Ɗakin Alhajin na su ya fara leƙawa ya hango shi a kwance ga hannun an gyara shi an mishi dressing sannan ga drip ɗaure a ɗayan hannun da kuma jini, a yanda yaga yanayin sa ya fahimci cewar bacci ne ya samu bayan baƙar wahalar da yasha.

Janyewa ya yi a hankali cikin sanɗa domin baya so ya tashe sa. Hakan yasa ya nufi ɗakin Hajiyar inda a nan ne ya tarar da Na'Imatu wacce ta kasance ɗiyar wan mahaifinsu Alhaji SALISU amma a nan aka raineta a nan ta girma take karatu tare da Anaam.

Tana ganin shi taje da gudu ta rungumeshi tana mai fashewa da wani sabon kukan.

Hannu ya kai a hankali yana bubbuga bayanta yana faɗin.

"Is OK...komai ya same mu daga Allah ne. Alhamdulillah a kowane irin yanayi Na'Imatu, bawa bai isa ya kauce wa ƙaddarar sa ba."

"Yay..ya Muhammad Annaamm..."

"Ya isa kinji! In Sha Allahu tana cikin aminci...ki je ga Auntynku can waje. Ina su Faryat?"

"Suna wurin Nene."

Cewa da wata mai aikinsu wacce ita ce tafi kusanci da Ammie da ma sauran mutanen gidan baki ɗaya.

Kusan a tare suka fito waje ganin Hajiyar itama da Oxygen mask sanye a Baki da kuma hancin ta. Lumshe idanun shi kawai ya yi tare da girgiza kai yana jin yanda wani abu ke masa yawo a ƙirji ba daɗi. Wai yanzu Iyayen shi ne a haka? Tambayar kan shi ya fara cewa wai ma su waye waɗan nan mutanen? Miye suka yi musu haka da zafi da har suka cancanci wannan hukuncin?

Ya jima a bakin ƙofar ɗakin Anaam domin bai da ƙwarin gwiwar isa inda take ganin likitoci har uku a kanta.

Ko bayan shigowar shi yafi ƙarfin 2 hours a ɗakin but har yanzu suna kanta suna ta ƙoƙari, baya ma iya hango ta da kyau sakamakon ƙyallen da suka saka suka kewaye ta da shi.

Kallon Doctor Anil ya yi a nutse ya ce.

"Doctor Anil ina so ka faɗamin gaskiyar abin da ya samu Anaam."

Jinjina kai Doctor Anil ya yi yana mai kallon Fuskar ya Muhammad ɗin ya ce.

"To be sincere Mr. Galadima,Anaam an mata fyaɗe ne mai muni wanda har ya yi damaging wasu organs daga cikin reproductive tract ɗinta. And again...bayan wannan ɗin ma, har yanzu fighting take akan numfashi..."

Cikin tashin hankali ya zaro ido yana mai jin yanda zuciyar shi ke wani irin pumping a rikice ya ce.

" Doctor mi ka ke nufi da cewar fighting take akan numfashi??"

Jinjina kai Doctor Anil ɗin yayi ya ce.

" Eh to, what I mean is that, tana raye amma kuma tana battling tsakanin rayuwa da mutuwa magana ta gaskiya Mr. Galadima...."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Wannan ita ce kalmar da ya shiga furta wa tare da faɗawa rijib jikin gini yana mai jin wasu irin zafafan hawaye wanda bai shirya musu ba suka shiga kwaranya daga kwarmin idonsa.

"Mun yi iya abun da zamu iya Mr. Galadima, amma har yanxu mun kasa gano taƙamaimen inda wannan matsalar take,Allah shi ya barwa kansa sani...and due to this trauma da ta samu,honestly speaking komai zai iya faruwa da ita a kowane irin lokaci."

Wayar shi dake hannun shi ce ta ɗauki ruri, a hankali ya kai kallon shi domin ganin wanda yake kiransa.

"Mukarram."

Shi ne sunan da ya gani ya yi appearing a gaban screen ɗin wayar tasa.

Sosai ya ji zuciyarsa ta ƙara karyewa a karo na barkatai, domin bai san ta inda ma zai fara yiwa ɗan uwan nasa bayanin wannan mummunan abun ba.

Mukarram ƙaninsa ne wanda yake binsa, daman daga shi ɗin sai Mukarram ɗin, sannan Mubarak sannan Anaam.

Girgiza kai ya sake yi tare da mayar da wayar a aljihun gaban rigar sa ya zauna daɓas a ƙasa tare da saka hannayensa duka biyu ya dafe kansa.

Yarinya ƙarama! Miye ta yi musu? Ita ɗin fa ƙaramar yarinya ce, she's just 19 Idan zai iya tunawa. Miyasa suka biyo Duhun Dare suka ke ta mata rigar mutuncinta haka? Wallahi ko su waye waɗan nan mutunen sun kunno wutar da ba za su iya maganinta nan kusa ba.

Jiyo Ihun matarsa Amina da kuma Mubarak a gigice suna furta sunan ANAAM ɗin a tare lokaci ɗaya....kai har ma da Na'Imatu idan kunnuwansa sun jiye masa daidai.

Ihu ne mai cike da nuna zallar karaya da jin cewa lallai an rasa wani abu mai muhimmanci.

Wannan shi ne zai sanya shi miƙewa cikin tashin hankali ya nufi ɗakin da suke.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull