Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 11

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 11

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 11: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 11. Murmushi kawai ta yi tana kallonta ta ce.

3,369 words

Murmushi kawai ta yi tana kallonta ta ce.

"To yanzu kin sani. Sai ki shirya..."

"Ai wannan karon bani da zaɓi Yaa Amina..ko namiji ko mace duk wanda aka haifa nawa ne.."

Dariya suka fashe da ita sannan Na'imah ta ce.

"Wannan karon kin saduda ne?"

Tana murmushi ta ce.

"Ai tun haihuwar Mufid ɗin Aunty Aysha na haƙura da zaɓe."

Daga haka suka juya zuwa wata firar wanda sai a lokacin ne Yaya Muhammad ɗin ya samu sukunin shigowa domin yana can yana ji da kambala tsare-tsaren gidan na su.

A nan suka ƙarasa wunin su sai dare suka yi musu sallama suka koma gida.

Bayan sun yi sai da safe kowa ya kama ɗakinsa Anaam ta shige toilet ta yo wanka sannan ta fito, ta jima akan sallayah bayan ta gama shiryawa ta yi nafila ta zauna zaman addu'a kamar yanda ta sabarwa kanta musamman a 'yan kwanakin nan.

Bayan ta ɗauki lokaci mai tsawo tana addu'a tana kuka wanda ya zame mata tamkar kumallo sannan daga ƙarshe ta miƙe tana duba agogon da ke manne jikin ɗakin. Ƙarfe ɗaya da rabi saura na dare shi ne abin da agogon ya nuna mata.

Jikin window ta koma a hankali ta ɗaga kai tana kallon sararin samaniya wacce lullume da Duhun Dare sosai amma akwai hasken taurari da suka ƙawata ta. Unguwar ba laifi, tsarinta da yanayin shirun ta ya burge ta.

Tabbas maganganun Yaa Muhammad gaskiya ne, idan kana biye maganar mutane tabbas har abada ba za ka taɓa yin gaba ba, domin kullum za ka ci gaba da zamo wa cikin baƙin ciki ne da damuwa. Abu ɗaya ta riƙe a ranta, shi ne: kowane ne ya yi sanadiyyar kasancewarta cikin wannan halin, kowane ne ya yi sanadiyyar ruguza mata rayuwa, har abada ba za ta taɓa yafe masa ba.

Karatun ta, mu'amalar ta da kuma abubuwan rayuwarta duk sun tsaya cak, lafiyar ta ma gashi nema take ta gagareta. Ita ba samari ba ballantana tace wani ta ɓatawa rai ya nemi ya ɗauki fansa a kanta. So take ta canja, so take ta dawo rayuwarta kamar can da, amma ƙunci da baƙin cikin da ke cikin zuciyarta sun hana hakan samuwa. So take ta yi walwala ko don faranta ran iyayenta da kuma 'yan uwanta waɗanda suka tsaya mata, ita kan ta so take ta canja ta manta komai, but ciwonda ke zuciyarta da hoton abin da ya faru da ita da ya yi Register a ƙwaƙwalwarta sun kasa barin haka ta faru.

Hannayenta ta saka guda biyu ta toshe bakinta ya yin da ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, ta jima a tsaye tana kukan wanda sai da ta gaji don kanta sannan ta janye ta koma a yanda take da hijab ɗinta ta faɗa kan gadon ta sai da ƙyar ta samu bacci ya sace ta.

Washegari tana kwance da littafi a Hannunta as usual Yaa Mukarram ya shigo ɗakin na ta ya samu wuri ya zauna a gefen gado yana murmushi yace.

"Maryama kina hutawa ne?"

Miƙewa ta yi ta zauna tana mai rufe littafin hannunta ta kalle shi ta ce.

"Yaa Mukarram ina kwana?"

"Lafiya lau, amma why are you alone? Ba ance ki daina zama ke ɗaya ba?"

Hannun shi ta kamo tare da shafa zoben da ke maƙale a middle finger ɗin Shi ta ce.

"Yaa Mukarram har yanzu dai baka cire zoben nan da Aunty Aysha ba."

"Idan na cire na waye zan saka? Ko kin samo min wata ne na kira ta na faɗa mata?"

Zaro ido ta yi tare da girgiza kai ta ce.

"A'a fa Yaa mukarram! Ni tambaya kawai na yi. Ka kada ka haɗani da Aunty Aysha."

"Baki amsa min tambaya ta ba. Miyasa kike zaune ke ɗaya?"

"Yaa Mukarram yanzu Aunty Na'ima ta fita tace mini za ta yi wanka..."

"But ai yanzu daga wajen Alhaji nake, daga shi har Ammie sun fito suna parlour...please ki daina zama ke ɗaya. A irin wannan zaman bad thought da bad ideas suke zuwa..."

Jinjina kai ta yi da murmushi ta ce.

"Ka yi haƙuri,in sha Allahu na daina."

"Za ki bini Indiya?"

Girgiza kai ta yi tana mai kallon littafin da ke hannunta tace.

"A'a..."

"To kina so mu fita gari yanzu?"

Agogo ta kalla taga ƙarfe goma saura ne na safe ta ce.

"Eh, ina so, but naga it's too early..."

Miƙewa ya yi yana jinjina kai ya ce.

"Sai mu fara biyawa gidan Yaa Amina daga can sai mu wuce..."

Saukowa ta yi itama tana faɗin.

"To bari na shirya sai na faɗawa Aunty Na'ima itama ta shirya ko?"

"eh to, yi sauri zan jira ku a waje..."

Daga haka ya wuce ta shirya ita da Na'imar sannan around 11am suka fito a tare.

A hankali ta nutsu tana ƙarewa gidan kallo lokaci ɗaya kuma tana gaisawa da sababbin masu aikinsu. Ganin babu fuskar ko mutum ɗaya da ta sani yasa ta kalli Mubarak da ya rakosu bakin mota ta ce.

"Yaa Mubarak ina su Adam?"

Kallon mutanen ya yi sai kuma ya waiga ya kalle ta ya ce.

"Suna can muka baro..."

Cike da mamaki ta ce.

"Yaa Mubarak mi yasa?"

"Because wasu lokutan idan har muka nemi canja muhallinmu domin wani dalili, to haka zalika wasu daga cikin mutanen da muke tare da su yana da kyau mu canja su Anaam."

Jinjina kai ta yi alamar gamsuwa sannan ta ce.

"Haka ne kuma....amma dai ina da buƙatar Anasi Yaa mubarak, please a dawo min da shi dan Allah..."

Shiru duk sukayi suna kallonta sannan daga ƙarshe ya jinjina kai ya ce.

"Olright...za a dawo miki da shi in sha Allahu...Yanzu ya kamata ki shiga mota Yaa Mukarram yana jira..."

Ya ƙarashe maganar yana buɗe mata ƙofa.

Shiga ta yi ta zauna kusa da Na'imatu ta ɗaga mishi hannu tana murmushi ta ce.

"Mi zan siyo maka?"

Ware hannu ya yi alamar duk abin da kika siyo sannan ya ce.

"Kin san ni ba baƙon tsanani ba ne...ko pure water aka siyo min karɓa zan yi na yi godiya..."

Dariya suka yi sannan Na'imatu ta ce.

"Uhmm! Yaa mubarak Kai ɗin ne za a siyowa ruwa as tsaraba?"

Murfin motar ya rufe yana faɗin Allah ya tsare, daga nan Mukarram dake waya ya tayar da motar suka fice.

******

Gidan Alhaji Gimba.

Sun shafe tsawon sati ba tare da ya sake sanya Faris ɗin a idonsa ba.

Shi duk a tunanin shi ya daina shigowa gidan domin baya cin karo da shi.

Yau kuma sun jima a waje basu dawo gidan ba da shi da Maimunar sai kusan karfe goma saura na dare.

Da gangan ta yada zango a Main parlour domin ta sani sarai Faris bai daina shigowa gidan ba.

Yana riƙe da ledoji a hannun sa ya ce.

"Ya kamata mu shiga ciki Maimuna, kinga dare ya yi ni ina jin bacci..."

Ɗan yatsina fuska ta yi tana wani ƙallewa kamar za ta kare ta ce.

"Ka ɗan jira na ɗan huta domin na gaji sosai..."

Zaunawa ya yi tare da ajiye ledojin ya ce.

"Ni dai da kin daure mun ƙaras..."

Bai iyarda rufe bakin sa ba suka ga Faris ya shigo kai tsaye ko sallama ba su samu arzikin ya yi musu ba.

Kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai tare da ƙara haɗe fuska ya nufi hanyar ɗakin sa.

Cikin zafin nama Alhaji Gimba ya miƙe da gudu yasha gabansa yana faɗin.

"Faris....Faris daman ashe ba ka daina shigo min gidana ba?"

Taɓe baki Maimuna ta yi ta ce.

"Ah to! Ko ɗa zu da na fito da safe tamkar zai bangajeni ya wuce haka ya yi, ba don na bashi hanya ba da tuni ya buge ni ya wuc.."

Cikin wani irin jin takaicinta ya ɗaga gorar ruwan da ya fito daga mota da su ya jefeta da su da ƙarfi wanda ba shiri ta saka hannu ta dafe laɓɓanta tare da ƙwallara wani uban ihu tsabar azaba.

Ai kuwa da gudu Alhaji Gimba ya yi kanta ya riƙo ta a ruɗe ya hau rarrashi tare da saka hannu yana laluben gefen inda ya ji mata ciwon. Cikin zafin rai ya waigo ga Faris ɗin but shi har ya wuce ya haura sama.

Da gudu Hajiya Salamatu ta iso parlourn tare da sauran masu aikin jin ihun da Maimuna take ta zubawa.

"Subhanallah! Lafiya? Miye ya same t..."

Tas! Haka Alhaji Gimba ya kwashe fuskar Hajiya Salamatu da mari ba tare da ya jira ta ƙarasa sauke zancen da ta ɗauko ba.

Cike da mamaki ta dafe kunce ta kalle shi, ta sake ta kalle shi cikin tsantsar al'ajabi ta ce.

" Alhaji ni ka mara?"

" An mare ki ɗin Salamatu! Ni za ku kawo wa iskanci da rainin hankali? Yanzu Faris har ya yi girman da zan kawo mata ya ɗaga hannu ya dake ta? To wallahy tallahy sai ya bar gidan nan kin ji na rantse da Allah sai ya bar gidan nan.."

" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah na roƙeka ka yi mini maganin wannan masifar da ta tunkaro ni ni Salamatu! Yanzu Alhaji Faris ɗin ne kake iƙirarin sai ya bar gidan nan? Da wane laifin kenan? Ni kai na mi nai maka ka mare ni?"

" Saboda shi ƙaton banza ne kuma ya sa hannu ya dakar min mata, daga kawai ta faɗi gaskiya cewa ya kusa rungumeta a hanya... "

Wani kallon Hajiya Salamatu ta yi wa Maimuna sai kuma ta girgiza kai ta ce.

" Ki ji tsoron Allah Maimuna...ki yi zaman auren da ya kawo ki kada ki nemi raba ɗa da mahaifins..."

Sake fashewa Maimunar tayi da wani sabon kukan tana ta wani bori tana faɗin.

"Na rantse da Allah ba zan yarda ba. Ai nan kwata-kwata kin nuna son kai Salamatu...idan ba shi ba taya ɗanki zai mini rashin kunya sannan kuma ki ɗora min laifi? Yanzu idan na haifi yara na a gidan nan suka miki rashin ɗa'a za ki ji daɗi?"

Cikin jin wani sabon shock ɗin da ya ziyarce ta ta kalli Maimunar ta ce.

" Maimuna yanzu ni kike kira Salamatu kai tsaye? A haife na haifeki kusan sau biyu ko sau uku..."

Wata uwar harar ta maka mata sannan ta ce.

" Wallahy ni baki haife ni ba! Kin dai haifi mai irin shekaru na wata ƙila, amma as far as muna auren miji ɗaya banga abin da kika fini da shi ba."

Kallon Alhajin tayi a raunane ta ce.

" Alhaji kana jin abin da Maimuna take faɗa min?"

Wani ƙanƙance ido ya yi yana wani hura hanci ya ce.

" Na ji! Ai daman idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, to jakin ba zai ji kunyar hamɓarar da shi ba. Kuma wallahy ki faɗawa ɗanki cewa na bashi nan da gobe...nan da gobe da safe na bashi Salamatu, ya tattara ya bar mini gidana, idan ba haka ba, duk matakin da na ɗauka ku kuka ja.."

"Ba ka san inda ƙofar ɗakin na shi yake ba? Ai kasan inda yake...ka je ka cim masa ka faɗa masa da kanka mana..."

Duƙawa ya yi ya ɗauki ledojin da ya ajiye yana faɗin.

"Kin dai ji na faɗa miki, wallahy idan na dawo gobe na tarar da shi sai na muku rashin mutunci...idan kuma so kike ki koma gidan tsofaffi sai ki shirya gobe kema ki bi shi..."

Tana ganin sun shige ta faɗa kan kujera ta fashe da kukan baƙin ciki. Wannan masifa ta wannan jarababben auren da ya yi ya ishe ta yasha mata kai. Gabaɗaya ta rasa nutsuwarta ta rasa kwanciyar hankali,Alhaji Gimba Sam bai kyauta mata ba da wannan auren da ya jajibo ba. Ga Faris shima baka isa ka faɗa masa ya ji ba.

Dole tana buƙatar mafita, tasan cewa ko me za ta yi 'yan uwanta ba za su sake shiga sabgar gidanta ba, domin a satin auren nasa ma daga cewa ya kamata ace idan da hali ya raba musu gida shikenan ya hau cin mutunci ya wanke su tas kuma ciki har da yayyun ta guda biyu,da wannan dalilin ne suka ce ba za su sake shiga sabgar su ba, daman tun can ya saba ci musu mutunci ba yau ya saba ba. Saboda haka dole tana neman mafita, ba za ta yarda ya korar mata ɗa guda da suke da shi ba a duniyar. Yanzu da ace suna tare da Alhaji Galadima da yanxu tasan ko ba daɗi ya faɗa masa dole ya ɗauka amma yanzu sam babu mai faɗa masa ya ji, Alhaji Ridwan ma haka, dama-dama ma Yayarsa Hajiya Hadiza wacce ke Bunguɗu, saboda haka dole ta kira ta gobe ta zo ayi ta ta ƙare.

*****

Maheer.

Tsaye yake cikin office ɗinsa da kakin sa na aiki wanda shigowarsa kenan bayan ya kambala aikinsa na yau. ruwa ya ɗauko a fridge ɗinda ke gefe ya buɗe yasha a hankali sannan ya waigo ya kalli abokinsa, amininsa da suka haɗu tun suna jami'a suke abota. Sun yi abota ta amana, sun kasance tamkar en uwan juna. Duk yanda za su yi faɗa sai sun dawo daga baya sun shirya.

Ko yanzu daga yanayin yanda yake kallon Maheer ɗin kai kasan dole akwai magana mai muhimmanci da take bakin sa domin fuskarsa ta nuna cewa ransa a matuƙar ɓace yake.

Extra bottle ya ajiye masa a gaban sa yana faɗin.

"I have already made mai decision Hamad..."

Cikin nuna damuwar da ta bayyana ƙarara akan fuskarsa ya ce.

"Akwai matsala fa Maheer...you have already mess everything and the more kace ka yi wani yunƙuri za ka ƙara ɓata al'amura..."

"And you can't stop me from doing what I think is right..."

A zafafe Hamad ɗin ya wani buga table ɗin da ke gaban sa yana ɗaga murya ya ce.

"You are not right Maheer! You are wrong...."

Hannayensa ya soke a cikin aljihun wandonsa yana mai ƙura masa idanun nan da suka canja launi sosai ya jinjina kai ya ce.

"Okay...na ji. Daman a lokacin da na aikata ban nemi shawarar ka ba, and yanzu ma I can handle it my self..."

Wani irin girgiza kai Hamad ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye tamkar wani zautacce yana jin yanda zuciyar sa ke yi masa ba daɗi ya ce.

"Maheer you made a mistake....tun ranar da ka faɗa min wannan maganar na kasa bacci...na rasa ma wane kalar tunanin zan yi. Sai nike jin a raina kamar ba kai ba, and still har yanxu wani sashen na zuciyata yana faɗa mini cewa ba kai ba ne Maheer...dole akwai wani abin da ba daidai ba..."

"Kada ka tsaya gurɓata tunanin ka Hamad...kawai ka yarda da ni a wannan karon..."

"Maheer ba zan bari ka sake making wani mistake ba. Abin da kake ƙoƙarin yi akwai haɗari a ciki..."

Girgiza kai ya yi yana kallon idon Hamad ɗin ya ce.

"I have no choice Hamad...dole ina da buƙatar hakan."

Daga haka ya juya kai tsaye ya fice daga office.

Zagaya Office ɗin Hamad ya fara yana neman mafita wa abokin sa, Maheer baya jin magana. Sam idan yaso aikata abu baya ji baya gani tamkar ɗa yaso nonon uwar sa. Da yana jin shawara da bai aikata abin da ya aikata ba. And still yana nuna shi sam abun kamar bai dame sa ba. Yanzu idan ban da neman tayar da zaune tsaye mi zai sa ya fara tunanin wannan again....He's Mad at all, Idan ya burge baya ji tamkar tsohuwar motar fire service haka yake dawowa.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 16*

https://chat.whatsapp.com/KgJnAzr5KBoJ9YAa2LxG8w

*Albishirinku jama'a shin ko kuna da labarin katafaren group ɗin mu, da mu ke tura KAYAN KITCHEN da KAYAN ƊAKI, har ma da KAYAN YARA MAZA DA MATA, ba mu tsaya a nan ba duk wasu abubuwan da UWAR GIDA DA AMARYA HAR DA 'YAN MATA masu CAPACITY ke bukata muna turawa, kayan mu na kasashen ketare ne kama daga Kayan kitchen, Kujeru da gadaje har da atamfofi, laces da Abaya, fashion net da bedsheets, hijabs gowns, caps, ribbons duk muna da su akan farashi mai RAHUSA, ga masu sayen ɗaya ko sari muna turawa ko'ina a cikin aminci, mutanen mu na kasashen waje kamar Chadi, Nijar, Kamaru, Ghana duk ba'a bar ku baya ba muna tura muku kaya har kasashen ku. Farashin kayan mu tamkar sari ne zaku saye har ku ɗaura ta ku riba kuma muna discount.

Ga masu bukatar kayan mu sai ku hanzarta shiga wannan link.💃💃💃

Tun misalin sha ɗaya na safe Hajiya Hadiza take cikin gidan Alhaji Gimban amma bai fito ba sai misalin ƙarfe ɗaya na rana.

Wani kallon ta yi masa sannan ta ce.

"Amma dai na kira ka a waya na sanar maka cewa ina cikin gidan nan ina jiranka tun ɗazu..."

Wuri ya samu ya zauna yana wani mimmiƙe hannu wai shi alamar daga bacci ya taso yana faɗin.

"Allah dai yasa lafiya?"

"Eh, daman Hajiya Salamatu ce ta kirani daren jiya take shaidamin abubuwan da suke faruwa a cikin gidan nan...magana ta gaskiya idan har da gaske ne abubuwan da ta faɗamin to baka da gaskiya Gimba.."

Wani irin ɓata rai ya yi yana kallonta ya ce.

"Miye ɗin ta faɗa miki yana faruwa a gidan?"

"Cewa ta yi kace wai Faris sai ya bar gidan. To idan ya bar gidan ina kake so ya je? And kuma bai kamata ace ka bar yarinyar nan tana yi mata rashin kunya ba..."

Tun ɗazu a laɓe Maimuna take jikin ƙofa tana jiran lokacin da ya kamata ace ta shigo pakourn, tana ji kuwa an sako zancen ta ta yi sallama ta shigo cike da nutsuwa ta dire trayn kayan drinks a gaban Hajiya Hadiza cikin girmamawa ta ce.

" Aunty Hadiza barka da zuwa, ina wuni? Da fatan an zo lafiya..."

Sai kuma ta waiga wurin Hajiya Salamatu tana wani kwantar da kai ta ce.

"Ina wuni Hajiya? Barka da fitowa..."

Ai kusan dasƙarewa Hajiya Salamatu ta yi akan kujerar da take zaune saboda tsabar mamakin makircin yarinya ƙarama irin wannan. Idan za ta iya tunawa tun farkon kawo Maimuna gidan nan har zuwa ba ta taɓa ma yi mata kallon arziki ba ballantana ma ta samu mutuncin gaisuwa.

Kallon Hadizar ya yi ya ce.

"To kin gani ko Hadiza? Yanzu don Allah ina so ki faɗamin ina alamar tana mata rashin kunya a nan? Shi ke nan dai idan an ga yaro ƙarami ne sai a ɗauka ba shi da wayo ayi ta neman yanda za'a yi aci masa zarafi ana yi masa ƙazafi. Salamatu sam bata son a zauna lafiya Hadiza. Kuma maganar Faris tabbas ni na ce ya bar mini gidana, domin na ba shi ilmi, na bashi ingatacciyar rayuwa sannan na bani sana'ar yi, saboda haka ko a musulunci don na haramta mishi shigowa gidana ban yi laifi ba, domin a yanxu ina da iyalin da bana son ya riƙa shigo min gidana..."

A hankali suka ji tana sheshsheka sautin kukan ta yana ɗagawa sai ciccika take tana ƙara sunkuyar da kai, ganin hakan yasa jiki sanyaye Hajiya Hadiza ta ce.

" Gaskiya Hajiya Salamatu idan har haka ne to kece ba ki so a zauna lafiya. Kuma ya kamata a matsayinki na babba ki riƙa kama girman ki...idan kika ce komai za ki riƙa magana a kai to fa watarana sai kin zubar mutuncin ki."

"Ah to! Faɗa mata dai ke ko Allah zai sa ta ɗauka. Yarinyar nan ba ruwanta tun da ta shigo gidan nan biyayya take mata sau da ƙafa, amma Salamatu ta ɗauki karan tsana ta ɗora mata. Ubangiji bai hana ni ƙara aure ba, saboda haka ke baki isa ki hana ni abin da raina yake so ba...gwanda tun wuri ki shafawa kan ki ruwa, idan kuma ba haka ba wallahy ni tas zan watsar dake in manta da babinki...Allah ya bani matar rufin asiri shi ne kike ta baƙin ciki dake da ɗan ki, duk abin da nike so yarinyar nan shi take so,amma ke duk tsawon shekarun da muka yi a tare kullum sai dai ki goyi bayan maƙiyana saboda kina munafuka...."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull