Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 12

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 12

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 12: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 12. Ganin suka yi Maimunar ta sauko ƙasa ta durƙusa gaban Hajiya…

3,367 words

Ganin suka yi Maimunar ta sauko ƙasa ta durƙusa gaban Hajiya Salamatu tana share hawaye tana faɗin.

"Ki yi haƙuri Aunty nah! Ke ɗin na san tabbas ba tsara na ba ce, hakan yasa nake ta baya-baya ashe kuma ban sani ba sai da na kai ga ɓata miki rai..please ki yi haƙuri, in sha Allahu zan ƙara kiyayewa."

Uhm! Wai akace idan baka iya kama ɓarawo ba to fa ɓarawon ne zai kama ka. Wato Hajiya Salamatu ta shiga wani irin mamaki ne da al'ajabi wanda suka hana ta ma tayi magana. Lallai wannan yarinyar ƙarshe ce wurin makirci,...

Cike da hargagi Alhaji Gimba ya taso mata tamkar zai kai mata duka yana faɗin.

"Wai Salamatu ba ki ji Maimuna na magana ba ne?"

Ɗago idon ta ta yi ta kalle shi sai kuma ta kalli Hajiya Hadiza wacce itama ita ɗin take kallo sannan ta jinjina kai ta ce.

"Na ji ta Alhaji. Allah ya shige mana gaba ya yi mana jagora."

Tana gama faɗar haka ta miƙe tsaye ta sake kallon Hajiya Hadiza ta ce.

"Hajiya idan kin tashi ki gaida gidan, mun gode Allah ya saka da alheri."

A sheƙe ta wani kalle ta tare da taɓe baki ta ce.

"Ameen. Gida zai ji."

Shigewa ta yi sashenta kai tsaye tabar su nan abin duniya duk ya bi ya ishe ta.

Suna ganin ta shige Hajiya Hadiza ta kalli Maimuna ta ce.

"Kina ji Maimunatu....ki ƙyale ta kawai ki ci gaba da sha'anin gabanki. Ban taɓa tunanin Salamatu za ta iya juyewa ta dawo mai mugun hali ba watarana. Don mijin ki ya auro yarinya shi ke nan kawai da ke da ɗan ki ku shiga gallazawa rayuwar ta? Ba'a auren ke aka auro ki?"

Alhaji Gimba ya ce.

"Ah to! Kin dai ganarwa idon ki yanzu. Saboda haka ni amarya ta bata da wata matsala duk abin da ya faru laifin ta ne..."

"Na gani kam. Allah ya kyauta. Ni zan kom..."

Da sauri Maimuna ta kalle ta tace.

"Haba Aunty gaskiya ba za ki tafi yanzu ba. Ki shigo sashena ki ci abinci ki huta mu ƙara fira sannan ki tafi tun da gashi ma yau yana gida..."

Washe baki ta yi tana girgiza kai ta ce.

"Ah ba komai wallahy bari na tafi."

"Gaskiya ni dai ba inda za ki....baby ka faɗa mata dan Allah ta tsaya mu ƙara gaisawa."

Ta ƙarashe maganar ta na mai kallon gefen da Alhaji Gimba yake zaune.

Jin hakan ya sanya shi jinjina kai ya ce.

"Ko daure ki tsaya please tun da ta nemi alfarma."

"To shi ke nan mu tafi."

A tare suka miƙe suka nufi sashenta suna yi suna magana.

********

Anaam.

A hankali rayuwa ta shiga tafiyar da ita tare da ƙoƙarin manta abin da ya faru da ita duk da cewa har abada ba za ta taɓa canjawa kanta ƙaddara ba.

Batun makaranta ta jingineta gefe, daga ita har Na'imatu babu wanda ya sake zancen karatu daga cikinsu haka zalika daga Abbahn har su Yaa Muhammad babu wanda ya sake yi musu zancen karatun. Malamin su Farouk ne ma kaɗai aka tsayar mata wanda yake zuwa duk yamma yana koyar da su Alƙur'ani da sauran litattafai.

Iyakacinta zama gidan nan kullum tana tare da Ammienta ko Abbah da kuma sauran en uwa, wani lokacin kuma idan ta so sai ta shirya taje gidan Yayanta Muhammad ta kwana biyu sannan ta dawo ko kuma idan abin ya motso ta ta shirya su shiga gari tare da su Fatima su Farouk.

Waya ma wannan ba ta da ita hannun ta a yanzu, tun abin da Rabi'atou ta nuna mata a waya tun a lokacin taji wayar ta fice mata a rai ba ta ma da buƙatar ta.

Ko gefen su Abbah sosai suka ga canji daga wurinta, domin gabaɗaya zaman kaɗaicewa da take ta daina yinsa, yawan damuwa ko kuma Kuka duk ta rage sai can ba'a rasa ba. Gefen lafiyar ta ma sosai suka duƙafa wanda ko bayan dawowar su nan sau biyu suka kai ta Check-up a Egypt wanda an tabbatar musu da cewa komai lafiya lau sai dai due ta abin da ya same ta gwaje-gwajen da aka yi mata da yawa sun nuna yana da wahala ta iya samun haihuwa a rayuwa. Wannan labarin ba ƙaramin kaɗa musu zuciya ya yi ba musamman Ammie, domin ita Anaam ɗin sai suka ga ma kamar maganar ba ta dame ta ba, suka ɗai ne suka ɗauki abin wani babban al'amari wanda ba su sani ba wata ƙil ƙurciya ce ke damunta sai nan gaba za ta fahimci giɓin da rayuwarta ta samu.

Yau ma suna zaune parlourn Ammie after magrib prayer da tulin kayan fruit da kayan ciye-ciye a gaban su Abbah ya shigo tare da Mubarak wanda dawowarsu kenan daga Gusau.

Kusan a tare suka gaishe da Abban ita da Na'imatu sannan mubarak ya kalli Anaam ya ce.

"Wannan tulin duk na miye ne?"

Kallon Na'imatu tayi sai suka fashe da dariya sannan Na'imar ta ce.

"Azumin lada muke Yaa Mubarak."

"Iyyehh! Da gaske? Yaushe aka fara?"

Wani kallon Anaam ta mishi domin ta gano cewa neman magana kawai yake, hakan yasa ta wani murguɗa baki ta ce.

"To ni dai saboda Allah na yi, kuma mutum ba ruwansa da ni wallahy..."

Dariya suka kwashe da ita sannan Abbah ya kalle ta yace.

"Ni ma dai na so na yi tambaya, amma tun da naji wannan kashedin...to na haƙura, Allah ya bada lada."

Kwaɓe fuska ta yi a shagwaɓe ta ce.

"Abbah ka fa san halin Yaa Mubarak da neman tsokana. Ka daina biye shi please..."

Zamowa Abban Ya yi daga kan Kujera ya zauna saman lallausar carpet ɗinda ke malale a tsakiyar parlourn kusa da Anaam ɗin ya ce.

"A zuba min wannan abun....miye shi?"

Dariya suka yi jin wata kalar tambayar tsokana da shima Abban ya ɓullo da ita. Hannu Na'ima ta miƙa ta janyo casserole ɗinda ke ɗauke da kyakkyawan Sinasir ɗinda ya ji gashi mai kyau ya yi saƙa tace.

"Abbah da gaske kai ma neman magana kawai kake, amma ai kasan wannan ɗin Sinasir ne..."

"Au da gaske? Ai na ɗauka wani abin ne na daban.."

Zaunawa shi ma Mubarak ya yi yana faɗin.

"Bari dai nima na zauna a cika sahun nan da ni....miye wannan ɗin Anaam?"

Ya ƙarashe maganar yana mai nuna mata wani bowl plate dake gabanta.

Harara ta maka masa sannan ta ce.

"Wannan ɗin ne baka sani ba Yaa Mubarak?"

"Ko ma dai miye a zuba min shi sannan a zuba min Zoɓo mai masifaffen sanyi wanda Nene ta haɗa...."

Wata irin dariyar ƙeta ce suka fashe da ita sannan Anaam ta kalle shi ta ce.

"Ba Nene ce ta haɗa ba fa, wata new cook ce mai suna Saro, but you can taste it ya yi daɗi ba laifi..."

Hannu ya ɗaga yana faɗin.

"No...thanks. A zuba min drink ɗin 5alive gashi nan na gani, is okay for me."

Haka dai suka zauna tare suka ci abincin cike da nishaɗi sannan daga ƙarshe bayan sun kambala Abbah ya ce zuwa ƙarfe tara da rabi na dare idan sun kambala abin da suke su je yana neman su.

******

Maheer.

Kusan 2weeks suka share a gidan iyayen Maamin sa wurin hidimar auren ƙanin ta Abdallah wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya.

Su kansu sun ga can ji a wurin Maheer, familyn Maamin sun kasance mutune masu matuƙar kirki da son zumunci. Tun da Hajiya Laylah ta dawo Oman ɗin bayan rasuwar Mijinta Doctor Tahameer, har yau Maheer bai taɓa neman wani abu ya rasa ba, wani abu bai taɓa tasowa ya yi kukan rashin dangi ba ko wani abu. Duk da cewa a wasu lokutan yakan ji cewa ko ya ya ne yana so ya sake ganin dangin mahaifinsa ko da sau ɗaya ne. But a nan ɗin ma Alhamdulillah yana farin ciki sosai, a yanzu bayan dangin mahaifiyarsa da yake da su, ba shi da wani wanda ya fiye masa Hamad Lawal. Abdallahn ma bayan kasancewarsa ƙanin mahaifiyar sa, shi ɗin abokinsa ne ta wani ɓangaren,sai dai abotar su tafi ƙarfi tsakanin shi da Hamad domin su ɗin classmate ne wanda ko bacci baya raba su,yanzu ma still wurin aikin su ɗaya ne, sai dai Shi Maheer ɗin yana nan a Oman ya yin da Hamad ke a Nigeria.

Har aka yi bukin nan aka gama bai wani yi participating sosai ba,kiran duniya Naana ta yi masa ita da Abiyh amma kullum cikin kawo musu excuses yake har aka ci aka suɗe wanda ɗaurin auren kawai ya samu ya halarta, domin yana can yana ta wani process na daban wanda haƙarsa ba ta cim ma ruwa ba sai yau ɗin nan ya samu abin da yake so.

Sai da ya fara kiran Maamin tasa domin tabbatarwa cewa shin ta koma gida ko kuma har yanzu tana gidan su Abiyh ɗin,jin tana gidan yasa daga wurin aikinsa ya taho direct gidan ya sameta a parlour ita kaɗai tana duba ayyukan da suka tarar mata bayan hutun da taje na kwana biyu.

Cikin farin cikin ganin ta ita kaɗai ya isa wurin ta tare da samun wuri ya zauna yana murmushi ya ce.

"Na ɗauka kin gaji bakya buƙatar aiki nan kusa..."

Ajiye pen ɗin hannun ta tayi tare da ture papers ɗinda ke gabanta ta ɗan yi baya kaɗan ta jingina bayanta jikin kujera ta kalle shi itama tana murmushin ta ce.

"Ya kamata na ɗan rage wasu kafin na yi resuming back."

"Uhm! Haka ne kuma, Allah ya taimaka."

"Amin."

Shiru ne ya ratsa tsakaninsu wanda ta jima idon ta na kanshi tana ta nazarin shi na ɗan lokaci sannan daga ƙarshe ta ce.

"Kamar kana so ka faɗa min wata magana Maheer...am I right?"

Jinjina kansa ya yi tare da miƙo mata takardar da ke hannun sa kai tsaye yana mai addu'a a cikin ransa cewa, Allah yasa kada ta yi ƙoƙarin katse masa wannan shirin nasa.

Karɓa ta yi idonta a kanshi ta ce.

"miye wannan ɗin?"

Ɗan ƙara gyara zamansa ya yi zuciyar sa na wani irin bugawa ya ce.

"Ki fara dubawa tukun mana Maami."

Jinjina kan ta ta yi tare da ƙara gyara zaman glasses ɗinta ta buɗe takardar ta fara dubawa kamar haka:

Al-Noor Maritime and shipping LLC. Head Office: Al-Noor Dock Control Tower, Port of Duqm SEZAD. Al Wusta Governorate, Oman.

To whom it may concern: This serve as an official letter for special assignment Notification to: Employee: Maheer Tahameer Alee. ID: ANMS-OPS-4471.

Following management review and operational requirements, Mr. Maheer Tahameer Alee has been choosed for a one year training to our Nigerian operations branch,for Port operations coordination Logistics supervision and safety compliance. Training support for local dock teams, Special maritime logistics project implementation.

New Duty Station: Al-Noor Maritime and shipping Nigeria Ltd. Operations and logistics Unit, Apapa Port Complex, Wharf Road, Lagos, Nigeria.

Accommodation, transportation, health Insurance and travel arrangements will be provided in accordance with company policy.

Mr. Maheer Tahameer Alee remains a staff of Al-Noor Maritime and shipping LLC, Oman,and is expected to resume duties in Duqm upon completion of this assignment.

We wish him a success in this responsibility. Signed: Engr. Wassil Khalid. Director Of Operations. Al-Noor Maritime and shipping LLC.

Folding ɗin takardar ta yi sannan ta ajiye ta a gabanta ta zuba mishi ido na tsawon lokaci.

Sosai ya ji gaban shi ya tsananta bugawa domin bai san miye take tunani a cikin ranta ba.

"Maami kin yi shiru..."

Runtse idanun ta tayi sosai tare da girgiza kanta sannan ta buɗe ta kalle shi ta ce.

"And mi yasa dole sai kai?"

Ƙara kwantar da murya ya yi cike da lallami ya ce.

"Ni ma ban sani ba Maami...but tun da kika ga haka sun ji daɗin wan can aikin na wa ne..."

Da sauri ta girgiza kanta ta ce.

"No! I will call Wassil my self domin ya yi cancelling wannan contract ɗin bana so..."

Ganin ta janyo waya yasa shi saurin kama hannun ta yana faɗin.

"Maami please ya kamata ki fahimta, idan ki ka yi requesting na cewa ba zan tafi ba, komai na iya faruwa da aiki na..."

"To ya farun mana Maheer sai me? Ƙarshe dai su ce sun sallame ka and kai ka san cewa hakan ba damuwa ba ne because akwai hanyoyi da dam..."

"Maami dan Allah ki saurare ni...dole ina buƙatar kasancewa a can domin mutanen nan sun ɗora yardar su gareni da kuma fatan cewa zan cika alƙawarin da na ɗauka tun ranar farkon da suka ɗauke ni...Maami a wasu lokutan ba kuɗin aiki ko kuma wani matsayi muke dubawa ba,yardar da aka ɗora a kanmu da kuma dogaro damu ne yasa muke yin wasu ayyukan...Maami dan Allah..."

Hannu ta ɗaga mi shi tana mai ƙara haɗe fuska alamar da gaske take ta ce.

" Duk na ji...ai ba yau ka saba yi musu aikin ba,saboda haka ban amince da wannan tafiyar ba a wannan karon, idan za su canja ka su canja ka, idan kuma ba za su canja ba to sai dai su baka takardar sallama. Tafiyar da kayi last time har yau na kasa gane kanka, idan ka sake komawa a karo na biyu ban san kuma da wane canjin zaka dawo mini ba. Alaƙarka da Nigeria sam bana son ta a yanzu Maheer, ka tsaya inda na ajiye ka."

Tana gama faɗar haka ta miƙe kawai ta nufi ɗakin ta tamkar za ta kifa tsabar damuwa.

Hannayensa ya saka duka biyu ya dafe kansa yana mai jin gabaɗaya duniyar tana juyawa da shi. Anya kuwa Maami ta san irin halin da yake ciki kuwa? He need to be there. Duk abin da zai faru dole yana da buƙatar kasancewa a Nigeria a halin yanzu.

Tunanin sa ɗaya ne a yanzu cewa ta ya ya zai samu ya fahimtar da ita? Da ƙyar ya samu wannan letter ɗin ta fito wanda da ta san hanyoyin da ya bi da ba za ta ma yi tunanin cewa wai ta kira Engineer Wassil ba. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ Ma su tambaya wai free ne ko paid, Book One free ne, Book Two kuma zai zo muku a Paidbook 500 Naira KACAL.... *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 17*

Alhaji Mas'ood.

Sai da lokacin Isha ya yi sannan ya fice masallaci bayan ya dawo ya wuce part ɗinsa inda ya tarar da Muhammad yana jiransa.

Bayan sun gama gaisawa ya ɗauko file ɗinda yake gabansa tare da ɗan ƙara matsawa kusa da Alhajin yace.

"Lissafi ya taru Alaji, shi ne nace ya kamata a ɗan rage..."

Hannu Alhaji Mas'ood ya ɗaga masa ya ce.

"Ɗan da ka ta da maganar lissafin nan Madu. Kun yi lissafi da Naseer ko?"

"Eh mun yi kwana biyu da suka wuce."

"Ok to, yanzu mu bar nan wannan zancen tukun. Tun da Allah yasa ka zo gidan yanzu, ina so na yi magana da su Maryam a gaban ku."

Yana gama faɗar haka ya janyo wayarsa ya kira Hajiya Nasmah ya ce ta zo tare da su.

Iyaka 10mnt sai ga su sun shigo parlourn har da Mubarak.

Wuri suka samu suka zazzauna sannan Abbah ya kalli Anaam a tausashe ya ce.

" Maryam!"

Ɗagowa ta yi ta kalle shi tana mai amsawa ta ce.

"Na'am Abbah."

Jinjina kai ya yi ya ce.

"Alhamdulillah! Mun godewa Allah sa irin canjin da muka gani zuwa gareki, abubuwa sun sauya sosai fiye da yanda ma bamu tsammata ba. Saboda haka ne naga cancantar cewa ya kamata ace kin koma karatu, zama a haka ba shi ne abinda aka fi so ba. Abin da ake so shi ne kullum a rayuwa a riƙa samun ci gaba. Burin duk wasu iyaye a rayuwa shi ne, idan suna da 'ya mace, su tarbiyyantar da su bata ilmi nagartacce, su bata ingantacciyar rayuwa, sannan idan ta kai munzalin aure su aurar da ita da mutumin da ya dace da ita wanda zai ci gaba da kula da ita har ƙarshen rayuwarta. To kamar haka ne Maryam, mu iyayen ki muna da wannan burin na son ganin mun cike wannan mafarkin akan ki da kuma Na'imatu gabaɗaya. Saboda haka ba zan yi ƙasa a gwiwa ba wurin gode miki akan yanda kika bamu haɗin kai wurin ganin wannan matsala ta ki kau, because mun ga canjin sosai Alhamdulillah. Saboda haka ina neman ki alfarma da ki sake ba karatu dama a karo na biyu, in sha Allahu komai zai yi daidai."

Jin yan da sautin kukan ta ke tashi a hankali yasa Muhammad ya ƙara matsowa kusa da ita cikin nuna kulawa ya ce.

" Kin ga Anaam....if you don't have interest nobody will force you...kawai Alhaji ya ga cancantar hakan ne, kuma komai kika ga ana son ɗoraki a kai ana yinsa ne domin ɗora a hanyar gobe mai kyau...but idan ba ki da ra'ayi, za'a iya haƙura..."

Jinjina kai Mubarak ya yi ta ce.

"Tabbas za'a iya haƙura idan har baki da ra'ayi, domin rayuwar ki ba ta wani ba. But ina so ki sani Anaam, nuna karaya ko yarda da faɗuwa ba naki ba ne. Ƙaddarar mutum bai isa ya canja ta ba, but idan wani abu ya samu mutum wanda ya karya masa zuciya, idan ya farfaɗo ƙoƙari zai yi ya fuskanci rayuwar da ƙwarin gwiwa da kuma fatan cika muradinsa da suka nemi rugujewa a baya. Kada ki manta ke ɗin fa 'ƴar gidan Mas'ood Galadima ce wacce ta gaji gwagwarmaya tun daga wurin mahaifinta. Mahaifinki bai yarda da faɗuwa ba a kowane irin yanayi, saboda haka ya kamata ki yi koyi da shi ki jarjice ki gina sabuwar rayuwa."

Ɗago idon ta ta yi ta kalle shi tare da share hawayenta da bayan hannun ta ta jinjina kanta ta ce.

" Daman na daɗe da ɗaura ɗamarar fuskantar sabuwar rayuwa a kowane irin yanayi Yaa Mubarak, na manta baya na, tabbas na manta komai kamar yanda na ɗaukar wa kaina alƙawari, saboda haka na shirya komawa karatu kamar yanda kuka buƙata. Sai dai ina neman wata alfarma guda ɗaya dan Allah..."

Ido suka zuba suna kallonta na ɗan lokaci wanda kowa a ransa nazari yake akan alfarmar da tace tana nema.

Jinjina kai Abbah ya yi cikin jin farin cikin amsar da ta bayar ya ce.

"Kowace irin alfarma ce ki faɗe mata Maryam muna jin ki, kuma in sha Allahu matuƙar dai ba ta kauce wa hanya ba to tabbas a shirye muke domin cika miki muradin ki."

Kai tsaye ta ce.

"Abbah so na ke na canja course ɗina, ina so in canja course zuwa Law Department, ina so in zama Lauya Abbah, dalilai masu yawa sun sa naga cancantar cewa ya kamata in zama Lauya...amma ban sani ba ko Aunty Na'ima tana so ta canja itama?"

Ta ƙarashe maganar tana mai kallon inda Na'imar take zaune.

Kallon fuskar Na'ima Ammie ta yi sannan ta mayar da kallonta gun Anaam ta ce.

" Haƙiƙa wannan tunani ne mai kyau, kuma Son ki zamo Lauya shi ma idea ce mai kyau, and na ji daɗin wannan shawarar sosai her cikin raina, amma dai ina ganin don ki zaɓi canja course bai kamata ace itama Na'ima sai ta canja ba, Ina ga yafi ita taci gaba da yin Nursing ɗin ta kamar zai fi..."

Jinjina kai Abbah ya yi ya ce.

" Maganarki haka take Hajiya Nasmah, and Kamar yanda na sanar da ke a waya tun kafin na dawo cewa mun saka ranar auren Na'imatu, to haka ne ta tabbata, Mubarak ka ɗauko katin ka ba su..."

Ya ƙarashe maganar yana mai kallon inda Mubarak yake zaune. Jin maganar Abban yasa Mubarak ta shi ya ɗauko musu wani ƙaramin kwali da akayi wrapping ya miƙawa Ammie.

Kallon kallo suka fara tsakanin Na'imatu da kuma Anaam jin wata irin magana mai kama da almara. Shi ne da kansa yace babu wacce za'a yi wa aure sai ta kambala karatun ta ta kama aiki.

Cike da damuwa Na'ima ta ɗago idanuwanta da suka gama shabkewa da ruwan hawaye ta kalli Abbah a raunane ta ce.

"Aure kuma Abbah?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull