Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 13

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 13

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 13: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 13. Jinjina kansa ya yi yana kallon idanun ta ya ce.

3,366 words

Jinjina kansa ya yi yana kallon idanun ta ya ce.

"Ƙwarai kuwa Na'imatu. Zaman na miye haka? Kin ƙi karatun da ya zamo shamaki ga yi miki auren to mi za'a jira? Ganin ki a gida zaune yasa Iyayen Haisam suka zo tuntuɓar auren naku har sau biyu, an riga an yi muku baiko kuma sun ganki zaune a gida ai dole su biyo sawu Na'imatu. Kin riga kin san waye Haisam, lokacin auren ne aka matso da shi kusa ba wani abu..."

Cikin jin wasu sababbin hawayen ta ce.

" Abbah ni bana so yanzu dan Allah..."

"Haisam ne fa Na'imatu, kada ki manta ke ce wadda ki ka kawo shi, sai da kika amince sannan aka yi muku bai ko, mun ba su uxurin cewa za ki yi karatu kuma suka amince, yanzu kuma sun ganki a gida ba ki karatun sun zo har sau biyu sun bincika...ba zamu zama kamar wasu ƙananun mutane ba Na'imatu. Tun da har kika ƙi ki ci gaba da karatu, to auren ku ya tabbata in sha Allah in next 6weeks coming..."

Ɗan ƙara muskutowa ya yi daga kan kujerar zuwa gaban kaɗan idonsa akan ta ya kira sunanta ta yanayin da ya tabbatar mata cewa da gaske yake.

" Na'imatu... "

Tana hawaye sosai ta ɗago a rauna ne ta kalle shi ta ce.

" Na'am Abbah..."

"Kin san ni, kin san waye ni, kin fi kowa sanin cewa bana magana biyu. Haisam ya tabbatar min da cewa za ki ci gaba da karatun ki kuma a shirye yake da ya baki duk wani goyon bayan da ki ke buƙata."

Kusan a tare suka miƙe ita da Anaam suka fice daga parlourn.

Tun a hanya Anaam ta kama hannunta hankalin ta a tashe ta shiga ba ta baki har suka isa ɗakin Na'imatu.

Na'imatu kukan saka auren ne take ba tare da ta shirya ba, sannan kuma ba tare da an sanar mata ba. But itakam Anaam wani sabon tsoro ne ya cika mata zuciya. Ba ta jin ita kam za ta iya yin aure a duniya, maza...sam ta tsani Maza, daman can ita ba ma'abociya yin samari ba ce, ba ta ma taɓa yin saurayi ba, sai Faris kaɗai da yace yana son ta, ba tare da ya samu wata fuska daga gunta ba kuma aka dakatar da shi. A yanzu da yayyunta kaɗai ta yarda,duk wani namiji matuƙar ba ɗan uwanta ba ne tsoron sa take. Ta sani su kaɗai ne ba za su iya cutar da ita ba.

A parlourn Abbah kuwa, jiki sanyaye Ammie ta kalle shi ta ce.

"Alhaji kana ganin ba'a shiga rayuwar yarinyar nan ba? Ina nufin kada taga cewa an yi rayuwarta karan tsaye..."

Kallon ta ya yi ya ce.

"Haba Hajiya Nasmah! Ke ma dai wani lokacin sai ki riƙa tunani kamar irin na su. Idan ba shi ba miye abun karan tsaye a nan? Haisam ne wanda ita ce ta kawo shi da kanta. Babu wata damuwa in sha Allahu, ku je ku ci gaba da shiri kawai."

"To shi ke nan. Allah ya tabbatar mana da alheri."

"Amin. Kana ji Madu? Ka je ka fara process ɗin nema musu Admission ɗin please."

Miƙewa Muhammad ya yi yana faɗin.

"Okay! In sha Allah. Bari na koma, sai da safe.."

"Allah ya bamu alheri, ka gaida su Amina."

"Za su ji Hajiya. Na gode."

*******

Mahdi Hussain Residence, Old Duqm Area, Al Wusta Governorate, Oman.

Maami ce zaune a parlourn mahaifinta tana sauraren faɗan da Abiyh ɗin yake yi mata.

Daman bayan sun gama tattaunawa da Maheer ne ya zauna neman mafita na tsawon lokaci. Bayan ya tabbatar cewa zai iya rasa damar sa yasa ya wuto gidan kakannin nasa kai tsaye ya kawo ƙararta, domin ya sani nan ne kaɗai za su faɗa mata ta ji.

Bayan ya gama yi musu bayani ne Naana ta ɗaga waya ta kira ta nan take sai ga ta ta iso gidan babu ɓata lokaci.

Sosai suka shiga yi mata faɗa suna mai tunasar da ita muhimmancin aikinsa idan ita ta manta, wanda ba su san cewa gadar zare ce ya shirya musu ba domin kawai ya samu damar cika muradinsa.

Bayan ta ji sun yi shiru musamman Abiyh da ya fi ɗaukar abin da za fi yasa ta kalle shi cike da girmamawa ta ce.

"Ka yi haƙuri Abiyh..sam bani da burin hana sa hidimtawa aikinsa, sai dai yanayin sauyin da na samu tattare da shi ne yake ɗaga hankalina, wanda ba ni ba, hatta ku karan kan ku kun fahimci abin da nake magana a kai dangane da shi....and sam bana so wani abu ya taso wanda har zai iya alaƙantasa da su Alhaji Arma..."

Jinjina kai Abiyh ya yi yana kallon ta yace.

"Laylah! Aikinsa shi ne gaba da komai, abin da nake so da ke shi ne, a matsayin ki na Uwa, to ki dage da yi masa addu'a da fatan samun nasara a rayuwa, da kuma addu'ar kariya da shiriyar ubangiji a duk inda yake. Shekara kamar kwana ce Laylah, in sha Allah za ki ga kamar gobe ne ya je ya dawo and na san cewa idan ya samu sarari zai riƙa ziyarta ki na sani..."

Jinjina kai mahaifiyar ta ta yi itama ta ce.

" And na sha faɗa miki cewa, idan har ya kawo abu ki daina saurin kushewa Laylah, Maheer bashi da wani makusanci na sosai da sosai da ya wuce ki, tun da ya rasa mahaifinsa kinfi kowa sanin irin tsananin wahalar da aka sha kafin aka samu ya dawo hayyacinsa....ki daina ƙoƙarin hana shi abu matuƙar dai ba hanyar Allah ya kauce wa ba. Ya kamata mu riƙa girmama muradan 'ya' yanmu a duk lokacin da muka duba muka ga cewa babu shirme a ciki. Duk faɗin kamfanin Maritime amma suka ɗauka daga namu wannan ai abin farin ciki ne. Saboda haka dan Allah ki bar shi ya je..."

Gyaɗa kanta ta yi a hankali ta ce.

" In sha Allahu Naana ba zan hanasa tafiyar ba. Allah ya tsare yasa a dawo lafiya. "

" Amin amin."

Koda suka tabbatar mai cewa sun shawo kanta har gari ya waye bai samu ya runtsa ba. Kwana ya yi yana lissafe-lissafen abubuwan da ya kamata ya yi idan ya sauka a Nigeria.

Koda ta shigo ɗakinsa bayan sallar Asuba har ya gama shiryawa.

Murmushi ya yi tare jinjina mata kansa ya ce.

"I'm sorry Maami na...ba wai na yi hakan domin ɓata miki ba..."

Hannun shi ta riƙa tana mai katse shi ta ce.

"Is Okay Son...Allah ya kai ka Lafiya ya ba da sa'ar abin da aka je nema. Ka kula da kanka...and please ka tsaya a inda kake...ka kula da ibada Maheer..."

"In Sha Allahu Maami. Na gode sosai, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka."

"Amin. Mu tafi...yau zan raka ka har Airport da kaina."

******

Koda ya sauka a Nigeria babu abinda yake ji yake mafarki kamar ya gan shi a ƙofar gidan su Anaam. Hakan yasa da saukar sa Lagos bai ma tsaya wani tunani ba ya nufi hanyar Gusau.

Sosai ya shiga cikin tsananin tashin hankali musamman da ya fara tunawa abin da ya faru sai ya ke jin tamkar yanxu ne komai yake faruwa.

Ji ya yi tamkar ƙafafunsa ba za su iya ɗaukar sa ba akan yanda yake ganin gidan na su na yi musa wani iri ✍️ OUM-AMEER ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 18*

https://chat.whatsapp.com/KgJnAzr5KBoJ9YAa2LxG8w

*Albishirinku jama'a shin ko kuna da labarin katafaren group ɗin mu, da mu ke tura KAYAN KITCHEN da KAYAN ƊAKI, har ma da KAYAN YARA MAZA DA MATA, ba mu tsaya a nan ba duk wasu abubuwan da UWAR GIDA DA AMARYA HAR DA 'YAN MATA masu CAPACITY ke bukata muna turawa, kayan mu na kasashen ketare ne kama daga Kayan kitchen, Kujeru da gadaje har da atamfofi, laces da Abaya, fashion net da bedsheets, hijabs gowns, caps, ribbons duk muna da su akan farashi mai RAHUSA, ga masu sayen ɗaya ko sari muna turawa ko'ina a cikin aminci, mutanen mu na kasashen waje kamar Chadi, Nijar, Kamaru, Ghana duk ba'a bar ku baya ba muna tura muku kaya har kasashen ku. Farashin kayan mu tamkar sari ne zaku saye har ku ɗaura ta ku riba kuma muna discount.

Ga masu bukatar kayan mu sai ku hanzarta shiga wannan link.💃💃💃

Sai da ya sauka daidai ƙofar gidan sannan ya tabbatar da cewa ya tabka babban kuskure. Haƙiƙa idonsa ya rufe, babu abin da ya ke so ya ji ya gani fiye da ganin Anaam ido da ido, it take him long to see her, tun ganin da ya yi mata a India. Ya kasa baccin kirki ya rasa nutsuwar sa. Haƙiƙa sai yanzu ya ƙara fuskantar miye ma asalin rayuwar bayan wacce ya fito a baya, ɗan Adam girma ne da shi daraja ce da shi, idan ka zalunce shi sai haƙƙinsa ya ɗaiɗaita maka rayuwa ya hana maka zama lafiya. Da ace ya ɗauki maganar mahaifiyarsa tabbas da duk wannan ba ta faru ba.

Idan sau dubu ya tuna abin da ya faru tsakanin shi da Anaam sai ya ji har cikin zuciyar shi tamkar zai mutu, dare da safiya a yanzu duk ɗaya ne a wurin shi, tunanin halin da take ciki ya hana mishi sukuni. To amma yanzu da ya zo gidan su as matsayin waye ya zo? Wa yake nema? Idan ya ce Anaam miye alaƙar da shi ita? Idan yace wurin ahlin gidan ya zo mi zai ce ya kawo shi? Ya ce shi ne wanda rapping na ta? Oh no! Babu abin da ya yi making sense daga ciki...

"Malam Ya dai?"

Ya ji muryar Adam ta karaɗe masa kunnuwa a lokacin da bai tsammata ba.

Shi kuwa Adam ɗin ƙara kusanto inda yake ya yi yana mai ci gaba da yi masa kallon tuhuma ya ce.

"Tambayarka nake waye kai? And wa kake nema a nan?"

Shiru ya yi tare da tsura masa ido na wasu en daƙiƙu sannan daga ƙarshe ya jinjina kai ya ce.

"Gidan wani friend ɗina nake nema yace a nan Layin suke..."

"But you are just standing here since, Kuma sai wani kallon gidan nan kake, ai idan baka san abu ba tambayawa za ka yi..."

"Eh to, haka ne, I'm sorry."

Jinjina kai Adams ya yi ya ce.

"Ya ya sunan friend ɗin naka?"

Ka ji kuma wata sabuwa! Waye zai ce yana nema a wannan Layin? A yanda gidajen nan suke a jere bisa tsari da burgewa baya tunanin akwai gidan da zai ambaci sunan wani ba'a san shi ba. And idan kuma ya ce bai san wani ba dole zai zarge shi kuma....

"Tambayar ka nake malam miye sunan shi?"

"While..abokin karatu na ne a London, to ya taɓa bani labarin garin su da gidansu sau ɗaya, shi ne na ce bari na yi masa ba za ta tun da har Allah yasa yau na shigo ƙasar su kuma garin su, shi ne nake bin labarin da ya bani ina neman gidan. Sunan sa Ahmad Usman..."

Ɗan Jim Adam ya yi na ɗan lokaci alamar yana nazarin sunan sannan daga ƙarshe ya kalle shi ya ce.

" Daman da na ganka ban ma yi tsammanin cewa kana jin Hausa ba, amma kai kuwa ka yi kasada da kace zaka gano gidan su ta wannan hanyar. And magana ta gaskiya kuma babu wani gidan su Ahmad Usman dai a wannan Layin, sai dai ko za ka bincika wancan second line ɗin ko kuma ka kira shi a waya."

Ɗan murmusawa ya yi tare da jinjina kansa yana kallon Adam ɗin ya ce.

" Thank you so much. Bari na je na gaba na bincika, I just want to surprise him ne."

"Okay...Allah yasa a dace."

Juyawa ya yi kai tsaye ya je gari ya kama Hotel ya shige ya kwanta akan gado tamkar wani marar lafiya. Wai yau Maheer shi ne wanda ya ƙware da yin Ƙarya? Hirar su da Adam ba ƙaramin wahala yasha ba, domin ya kasa fitowa ya faɗa masa cewa ga wanda yake nema. Ko kaɗan ba zai yi kuskuren ambatar sunan Mas'ood Galadima ba, domin a duniya ba shi da wani maƙiyin da ya wuce shi. 'yarsa ce wacce babu ruwanta a ciki ya yi wa laifi, saboda haka ita kawai zai nema ya faɗa mata gaskiya sannan kuma ya roƙi gafararta ko Allah zai sa ya samu sukunin rayuwa.

To amma ta ya ya zai ganta? Tamkar wani magani daga bayanan ya rasa kowace hanya zai bi wurin ganinta. But wata ƙil idan ya ci gaba da zuwa ƙofar gidan yau da gobe zai iya ganinta a waje ko kuma a mota. To kuma yaushe hakan zai samu? Ga shi ya katange Maamin sa daga samun damar magana da shi domin kada ta gano inda yake a yanzu, but har tsawon yaushe kenan zai ci gaba da hana ta magana da shi? Dole yana buƙatar mafita da gaggawa.

*******

Gidan Alhaji Gimba.

Tun ranar da Hajiya Hadiza ta zo gidan Hajiya Salamatu ba ta sake sanya Faris a idonta ba. Kiran duniya ta yi mishi amma ta kasa samun wayar shi, ta yi kuka har ta gaji, ta bincika ko'ina dangi da mutanen kasuwancin su amma ta rasa ina ne ya shiga.

Shi kuma gogan ko a jikinsa, damuwar sa ɗaya ce Maimunarsa. Idan yana tare da ita baya ji baya gani, duk tsawon lokacin nan da suke shafe yana ɗakin Maimuna zaman shi hankalinsa kwance, wata ƙila ma tana tunanin ya manta da cewa raba kwana ake tana da haƙƙin kwananta a kansa. Sai dai rashin jituwar da ke tsakanin su yasa ko kaɗan ba ta sa wannan a ranta ba. Damuwar ta ɗaya ce ɗan ta tilo da take da shi. Maimuna Sam babu alheri a tare da ita. Idan tasan girma da muhimmancin iyali Sam bai kyautu ace ta nemi shiga tsakaninsu ba da zuwanta na jiya-jiya.

Ta Yi kuka har ta gaji, wanda daga ƙarshe ta kawo na gani ta zuba musu, iyaka idan ya fito su gaisa kuma ko shi tana ji tana gani watarana ko gaisuwar ta ta baya amsawa,abinci kuma har yau ita ce take girka shi idan kuma ba ta yi ba ya hauta da zagi da cin mutunci.

Yau ma tana zaune misalin ƙarfe goma na dare sai ga kiran Faris tamkar a mafarki. Hannu na rawa ta ɗaga da sauri ta ce.

"Faris....! Haba Faris miye ya yi zafi haka?"

Cike da jin kewarta a ransa ya ce.

"Ya ce na bar masa gidansa...mi zan zauna na yi kenan? Barin gidan shi ne maslaha a garemu gabaɗaya."

Kuka ta fashe da shi tare da girgiza kanta tamkar suna gaban juna ta ce.

"Idan yace ka bar masa gida ni ba gani ba! Idan shi baya da buƙatarka ni ina da, domin bani da wani ɗa a duniya sai kai,miye amfanin zama na a nan yanzu?"

"Mum..."

Ya ambata a rauna ne.

"Ki zauna a gidan ki kasa ki damu dani, ina nan lafiya lau, ki kwantar da hankalinki."

"Faris..Ina jin tsoro, zuciyata ta karye da waɗan nan ɗabi'un mahaifin naka..."

"Ki yi ta haƙuri, watarana sai labari, ki daina saka matsalolin sa a rai domin ba yau ya saba ba, kin fi kowa sanin waye shi, saboda haka ki ƙara haƙuri kin ji Mum."

"Dan Allah ni dai ka dawo gida, kada ka biye zancen sa dan Allah ka dawo..."

"I will...kada ki damu."

Daga haka ya tsinke wayar ya bar ta da sharar hawaye.

******

Na'imatu.

Tun da Abbah ya sanar da ita zancen aurenta ta hanawa kan ta sukuni. Tun ranar ta yanke waya da Haisam tamkar wanda ya aikata mata wani mummunan laifi.

Yanzu ma wanka ta fito bayan an gama mata gyaran jikin da take jin idan ana yinsa tamkar ana ƙonata ne, domin sam bata ra'ayi bata kuma muradi. Da Ammie ta ji roƙon ta da yanzu ba ta ɓannata kuɗin ta wurin wannan aikin ba domin babu wani amfanin da zai yi mata.

Wayar ta dake gefen ta ne ta ci gaba da ringing ba tare da samun wani sarari ba, a ran ta mamaki take halin naci irin na Haisam, da ace yana da zuciya da yanzu ya haƙura ya daina kiranta. Ga mata a duniya mi zai dole sai ita bayan ta ce ta fasa.

A zuciye ta ɗaga cikin rashin mutunci ta ce.

"Wai Haisam ana dole ne?"

Daga can ɓangaren Haisam ɗin ya girgiza kan sa cikinn sanyin sa ya ce.

"A'a! Ba'a dole Na'imatu, amma ya kamata zuwa yanzu ace kin haƙura, na san na aikata miki kuskure na rashin sanar dake amma ki yarda dani, wallahy ko a ranar da muka yi waya da daren nan ban san cewa an saka ranar ba har an bugo IV..."

"Wannan kuma kai ta shafa..."

Jin tayi an warce wayar daga hannun ta an wanda ba shiri ta ɗago ta kalle ta, tana ganin Anaam ce ta ɗauke kai tare da zura hannu ta ci gaba da aikin shafe-shafen da take.

Kashe wayar Anaam tayi gabaɗaya tare da jinginawa jikin dressing mirror ta ɗan ɗosana ɗuwawunta kaɗan ta zuba mata ido tana kallonta na tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta jinjina kanta ta ce.

"Aunty Na'imatu hakan sam ba daidai bane. Kuma na san ba halin ki ba ne, Haisam bai da laifi a wannan maganar, ni banga wani abin tada jijiyar wuya ba da har kika zaƙe kina ta wannan fushin alhali kuma kin san ba bu fashi auren nan dole za'a yi..."

Ranta a ɓace ta ce.

" But why yake min ƙarya cewa wai ban san da zancen ba? Akwai wanda zai shige gaba ya yi masa zancen auren sa idan bai nuna yana da ra'ayi ba?"

Murmushi Anaam tayi tare da girgiza kai tana kallon Na'imatun ta ce.

" Yaa Na'ima ki yarda kawai cewa ba ki da gaskiya,amma ni banga laifi a nan ba. Kuma wallahy mun yi magana da shi ya rantse mini da Allah cewa shi ma bai san da zancen ba sai da yayansa ya kira sa ya sanar masa cewa an gama saka rana..."

Faɗowa ta yi ta zauna a gefenta ganin yanda take ta wani ƙara ɓata rai tana ciccika kamar an kwaɓa fulawa ta ce.

" Yaa Na'ima ni fa ina jiye miki wannan abin kunyar da kike neman janyowa kan ki, domin watarana idan kika zo kina mana ƙafafa da Haisam wallahy har ya Mubarak ba zai ƙyale ki ba, sai ya dinga miki tsokanar da sai kin yi kuka. Ki yi haƙuri ki lallaɓa zuciyar ki ki kori shaiɗan...."

Wata harara ta maka mata a ƙasan ido sannan ta yi ƙwafa ta miƙe taje ta ɗauko kayan ta a closet ta saka.

" Wallahy Yaa Na'ima kin fito amaryar Haisam sak! Kamar yau ne bikin ma..."

" Wai Anaam dan Allah ba za ki iya fita harkata ba ne?"

Miƙewa ta yi tana ci gaba da dariya ta ce.

"Allah ya huci zuciyar amaryar Doctor Haisam Usaid..."

Towel ɗinda ta cire ne ta raruma ta jefe ta da shi da ƙarfi sai ga Anaam ɗin ta zuba da gudu ta yi waje tana dariya.

Tana fita ta shige ɗakin Ammienta ta ɗauko wayar Ammien ta kira Haisam ta ce.

"Kana ji Likita? Kada ka damu da abin da take dan Allah kar ka ji haushi...komai zai wuce."

Cikin jin daɗin irin karar da Anaam ɗin ke masa ya ce.

"Ba damuwa, ni ko kaɗan ban ji haushi ba daman, na san ɓacin rai ne watarana zai wuce in sha Allah. Na gode sosai Ƙanwata, Allah ya bar zumunci."

"Amin. Ango Yaa Na'imata,sai an jima."

*******

Maheer.

Washe gari tun misalin ƙarfe sha ɗaya na safe ya sauka a farkon Layin gidansu.

Bakin gate ɗin wani gidan ya samu ya tsaya tare da ciro wayarsa ya kira Hamad ya ce.

"Hamad na kasa yanda zan yi na ganta...and I need to see her."

Cike da gatse Hamad ɗin ya ce.

"Miye ya hana ka shiga gidan kai tsaye?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull