Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 14

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 14

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 14: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 14. "No! Kai ma kasan hakan ba zai faru ba, jiya ma common Mai gadin…

3,321 words

"No! Kai ma kasan hakan ba zai faru ba, jiya ma common Mai gadin gidan na su na kasa faɗa masa gaskiyar cewa Ita nake nema....Allah dai ka rabamu da mugun ji da mugun gani Hamad. Imagine wai ni a gaban gate man and ya tambayeta sai ƙarya na shirga masa tsabar rashin gaskiya."

"Shiyasa na yi ta ƙoƙarin dakatar da kai Maheer. Ta ya ya kake tunanin ka tsaya ido da ido ka faɗa mata cewa kai ne and ta yafe maka kawai ka wuce? Hauka kake na gaya maka! Leave that Gurl and go back home, kaje ka yi ta istigfar....."

"Hamad ba za ka fahimci halin da nake ciki ba. A yanda na fahimce ta tana da sanyi da sauƙin hali, ya kamata na sauke girman haƙƙin ta da yake kai na..."

"Duk na ji fa! But ta ya ya?"

"while....ni na san yanda zan yi handling komai da kai na."

"Okay oo! Fatan alheri Maheer Tahameer Alee. But idan aka yi rashin sa'a aka kama ka aka rufe ka, kasan fa kai da iskar duniya mai daɗi har abada."

"Fatan da kake min kenan?"

"No! I'm just telling you the real truth Saboda naga alamun cewa kanka ya kwance..."

Lumshe idonsa ya yi a hankali sannan ya buɗe ƙarshe ya ce.

"Sai an jima."

Kusan wuni ɗaya zungur ya shafe a nan tare da mai gadin da ya zauna tare da shi a bakin gidan da ya tsaya, a masallacin gidan suka yi azahar suka yi la'asar but ga mamakin sa tun zaman sa wuni ɗaya ko mota ɗaya bai ga ta fito ko ta shiga gidan Alhaji Mas'ood Galadima ba. And ko mutum ɗaya bai ga ya shiga ko ya fita daga gidan ba.

Kallon Matashin mai gadin da suke zaune a benci ɗaya ya yi ya ce.

"Wancan gidan kamar ba kowa?"

Kallonsa Matashin ya yi ya ce.

"Miyasa ka ce haka?"

"Kawai dai na ga, wuni ɗaya amma ko tsuntsu ban ga ya shiga gidan ba."

Waigawa Matashin ya yi ta kowane ɓangaren wanda sai da ya tabbatar ba kowa sannan ya yi ƙasa da murya ya ce.

"Ai sun ji ma da yin Hijira bawan Allah."

Cike da zaƙuwa Maheer ɗin ya ce.

"Hijira? Hijira as how?"

"A'a fa! Kada ka laƙa mini jakar tsaba kaji su bini bawan Allah, kada ka zo ka wuce ni ka bar ni cikin jalala alhali ko saninka ban yi ba haɗuwar bakin gate rabuwar kan benci..."

Hannu Maheer ya zura a aljihun wandonsa ya ciro kuɗi masu matuƙar yawa ya ɗora masa a jikinsa. Wani irin dafewa matashin ya yi yana wani zare ido. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 19*

https://chat.whatsapp.com/KgJnAzr5KBoJ9YAa2LxG8w

*Albishirinku jama'a shin ko kuna da labarin katafaren group ɗin mu, da mu ke tura KAYAN KITCHEN da KAYAN ƊAKI, har ma da KAYAN YARA MAZA DA MATA, ba mu tsaya a nan ba duk wasu abubuwan da UWAR GIDA DA AMARYA HAR DA 'YAN MATA masu CAPACITY ke bukata muna turawa, kayan mu na kasashen ketare ne kama daga Kayan kitchen, Kujeru da gadaje har da atamfofi, laces da Abaya, fashion net da bedsheets, hijabs gowns, caps, ribbons duk muna da su akan farashi mai RAHUSA, ga masu sayen ɗaya ko sari muna turawa ko'ina a cikin aminci, mutanen mu na kasashen waje kamar Chadi, Nijar, Kamaru, Ghana duk ba'a bar ku baya ba muna tura muku kaya har kasashen ku. Farashin kayan mu tamkar sari ne zaku saye har ku ɗaura ta ku riba kuma muna discount.

Ga masu bukatar kayan mu sai ku hanzarta shiga wannan link.💃💃💃

Sai da ya gama haɗa kan kuɗin ya ƙirga su tsab ya zuba a aljihunsa, sannan yasa hannu ya dafe aljihun sosai ya ƙara matsawa dab da Maheer ɗin ya kalle sa murya cike da zallar gulma ya ce.

"Yallaɓai kawai sai wayiwar gari mukayi muka ga basa nan, ba wanda yasan miye ya faru ya akayi, sai daina ganin ahlin gidan muka yi...."

Cike da zaƙuwa Maheer ya ce.

"Ina suka koma please?"

"Wallahy shi ne abin da ban sani ba ranka ya daɗe. An ce dai sun tashi amma ban san inda suka koma ba. Garin suka bari? Unguwa suka canja? Allah ne masani...kasan fa ni kawai mai gadi ne. Daga bakin gate ɗin nan sai kan bencin nan, sai kuma idan na gama aikina wanda zai canje ni ya zo sai na shirya na tafi ƙauyenmu nayo kwana biyar na dawo..."

Wani irin takaicin sa ne ya rufe Maheer ɗin wanda bai san ma time ɗinda ya miƙe tsaye ba ya wani kalle sa sannan ya kama hanya kawai ya fara tafiya.

Ya rasa abin da yake damun rayuwar wasu mutanen, ga shi dai kamar mai hankali amma kuma daga ganin sa kasan kan nan nasa ba daɗi, a yanda yaga yaci serious ya ɗauka da gaske yasan labarin su Anaam ɗin daga sama har ƙasa, ashe bai san komai ba wawa kawai malam.

"Yallaɓai...."

Tsayawa Maheer ɗin ya yi fuskar nan a turbune ya waigo kawai ya yi masa wani kallon da sai da ya haɗiye wasu yawu daƙyar sannan jiki a sanyaye ya ce.

"Daman ina so na faɗa maka ne cewa suna na kalla, duk sanda kake neman wani bayani ina nan a na...."

Ci gaba da tafiya ya yi, domin ji ya yi ransa ya ƙara gashewa da takaicinsa fiye da ɗazu ma.

Har ya koma masaukinsa bai daina jin haushin sa ba. Tambayar kansa ya fara cewa ina suka tafi? India? Da can ne tabbas da ya jima da sani. Yayanta ne kawai a can. Sai dai idan sun juya zuwa wata ƙasar daban.

Yana nan dai yana ta tunani ƙarshe ya miƙe ya yi alwala sannan ya sauya kayansa zuwa farar jalabiya ya fice masallacin Magrib.

******

Yau koda suka wayi gari gabaɗaya gidan na su ya kacame da aikace-aikace da kuma shirye-shiryen saka lallen Na'ima da kuma kawo lefenta da dangin Haisam suka kira jiya suka sanar. Akwai babbar yayarsa Barrister Hajara da take nan a Abuja to daga nan za su fito.

Komai na girma aka shirya musu kamar yanda suma daga can ɓangaren suka shiryo kayansu na alfarma domin farantawa Na'ima.

Ƙarfe goma sha biyu na rana suka shigo gidan ɗauke da sha tara na arziki. Tun a harabar gidan Su Anaam dake ɗaki ana yi wa Na'imatu kwalliya suka jiyo ƙugin motocin su. Miƙewa Anaam ta yi cike da zumuɗi ta leƙa windown ta shiga kallon yanda ake ta fito da kaya. Waigowa ta yi ta kalli Na'imar fuskar nan cike da murmushi ta ce.

"Ya Salam! Yaa Na'imatu kin gansu kuwa? Kin ga Barrister Hajara da wannan ƙanwar tasa Anisa? Zo ki ga kaya Yaa Na'ima..."

Ƙwace kanta ta yi daga hannun mai kwalliyar ta wani waiga ta kalle ta cike da mamakin ganin yanda Anaam ɗin ke ta farin ciki. Sosai abin ya ba mamaki domin ta ji ma bata ga Anaam cikin irin wannan yanayin farin cikin ba. Hakan yasa rashin mutuncin da ta shirya yi mata sai ta fasa ta juya kawai aka ci gaba da zana mata make-up ɗin ta. At least ko don Anaam ya kamata ace yanzu ta ɗan sassauta domin tana matuƙar ƙaunar farin cikin ta.

Suna nan kawai suka ga tayi fit ta bar ɗakin da gudu ta sauka ƙasa inda ake ta shigowa da kayan ana ta abin arziki.

Sai da ta kusa kai wa tsakiyar parlourn inda su Ammie suke kawai ta juya tamkar wacce ta tuna da wani abu ta koma ɗakin ta ta tsaya jikin mirror tana ƙarewa kanta kallo.

Tabbas ta yi alƙawarin manta komai, amma kuma taya ya mutane su ma za su manta da abin da ya faru? Idan suna da adalci tabbas ya kamata ace sun manta kamar yanda itama ta ɗaukarwa kanta alƙawari. To amma ina! Duk yan da za ta yi dole wata sai ta nemi yan da za ta yi ta ci mata zarafi.

Yanzu a haka za ta yi bukin nan na Yayarta kuma ƙawarta Na'ima ba tare da walwala ba? Babu yanda za ta yi ace ta yi bukin nan cikin jindaɗi ba tare da wata damuwa ba? Ta ci buri sosai bukin Na'ima...ta ci burin yin abubuwa ma su tarin yawa na farin ciki da nuna cewa ta isa. Auren Yayanta Mukarram da akayi ƙarshe ma ba ta da wani wayau aka yi shi, auren Yaya Naseer ma suna secondary aka yi shi. Sun jima gidan su ba'a yi buki ba sai na Na'imatu da ta ci buri, but sai ga shi kuma a haka bukin ya zo mata saboda mummunan abin da ya same ta.

Girgiza kanta tayi tare da kama gefen veil ɗin rantsatstsar Abayar da ke jikinta ta share hawayen da suka gama wanke mata fuskar ta kawai ta faɗa kan gado ta yi kwanciyarta.

Har aka ci aka suɗe ba ta fita ba, dangin Haisam sai neman ta suke amma babu ita babu labarin ta, Ammie sam ba ta sa ran cewa tana ɗakin ta ba. Kowa ya ɗauka suna can tare da Na'imatu ashe tana ɗaki ita ɗaya.

Tana nan a kwance sai ga Aunty Amina ta shigo wanda sam itama bata san tana ɗakin ba, kawai ta shigo ne da nufin ta yi sallah domin da suka zo da safe a nan ɗakin ta sauka.

Kallon ta tayi fuskar ta ɗauke da mamaki ta ce.

"Anaam..."

Ɗagowa ta yi ta kalle ta tana mai ƙaƙalo wani murmushin ƙarfin hali ta ce.

"Na'am Yaa Amina. Kar dai ki ce min har an kambala?"

Cikin yanayin tuhuma Aminar ta ce.

"Miye kike ɗaki a kwance Anaam?"

Miƙewa ta yi ta zauna tare da zuro ƙafafunta zuwa ƙasa ta ce.

"Shigowa na yi in yi sallah..."

"But tun ɗazu fa ake ta neman ki, har su Anisa sai da suka ce a kiraki ku gaisa amma ba a ganki ba."

"Ina can fa tare da Aunty Na'imatu..."

"Har can Fatima ta dubo ki suka ce kin jima da baro ɗakin Anaam."

Shiru ta yi daga ƙarshe ganin da gaske an gano tana ɗakin tun ɗazu.

A hankali Aminar ta taka ta isa inda take ta zauna a gefen lallusan gadon na ta tana kallon gefen ta cikin nutsuwa ta ce.

"Anaam ki daina haka. Ki daina cewa za ki riƙa haramtawa kan ki shiga jama'a. Kamar yanda kika ɗauki alƙawarin canja wa to ki yi shi da dukkan zuciyarki. Ki manta da mutane da kuma maganganunsu, ki yi abin da yake gaban ki. Hidima ce za'a yi gidan nan kuma Na'ima ba ta da wata shaƙiƙiya wacce take son gani a gefen ta a duk lokacin da ta buɗe idonta fiye da ke."

Cikin jin wasu irin zafafan hawaye ta kalli Aminar ta ce.

" Yaa Amina ina jin kunya..."

Hannunta ta saka ta rufe mata bakinta tare da girgiza mata kai ta ce.

" Allah ya raba ki da abin kunya Anaam, domin ba ki aikata laifin komai ba, kunya na can ga wanda ya cuce ki ya zalunci rayuwar ki, ki daina jin kunyar kowa domin ba a son ran ki hakan ta kasance ba kin ji?"

Jinjina kai ta yi tare da saka bayan Hannunta ta share hawayenta tace.

" Na gode Yaa Amina, na gode sosai. In Sha Allahu na daina."

Cikin jin daɗi ta ce.

" Yauwa Anaam ɗin Yaa Muhammad. Bari na tashi na yi sallah daman abin da ya shigo dani kenan. Ke ms kuma na san ba ki yi ba, saboda haka ki tashi kada lokaci ya shige."

Saukowa ta yi bayan Aunty Aminar ta fito daga ban ɗakin itama ta shiga ta yo alwalar ta zo ta yi sallar sannan Aunty Amina ta kama hannunta sai parlour inda aka baje akwatun nan lefen Na'ima.

Wani ƙayataccen murmushi ne ya suɓuce mata ganin jerin akwatuna guda goma sha biyu masu azababben kyau.

Da gudu taje ta shiga shafa su tana yaba kyaun da suka yi. Kallon ta Mubarak ya yi ya wani girgiza kai ya kalli Amina ya ce.

"Yaa Amina ni ban san ya mata suke da lefe ba. Idan ki ka ga suna rawar ƙafa sai kice tun da suke duniya gidan su ba'a taɓa ɗinka musu sutura ba ko kuma ba'a taɓa siya musu kayan kwalliya ba ko akwati ba..."

Taɓe baki Anaam ta yi ta ce.

"Wannan kuma daban Yaa Mubarak,.."

Dariya Aunty Amina ta yi ta ce.

"To ai nima Mubarak zancen nan dai har da ni a ciki domin an yi mini lefen nan..."

"Ah to Aunty Amina da ke yake wallahy."

Cewar Anaam tana kallon shi tana dariya.

Miƙewa ya yi ya fara tafiya yana faɗin.

"Bari in tashi kafin ki haɗani faɗa da Uwar ɗaki na."

"Ai da ka tsaya ka gani Yaa Mubarak..."

"Anaam..."

Amina ta katse ta da kiran sunanta.

Da katawa ta yi da maganar tare da mayar da kallon ta gun Aminar ta ce.

"Na'am Yaa Amina..."

Wa su saitin akwatuna dake gefe 3pcs ta nuna mata tana murmushi ta ce.

"Ga kayan ƙawa can Haisam ya ce ya kawo miki..."

Kallon direction ɗinda take nuna mata ta yi tare da zuba idanu ta kalli kayan sannan ta kalli Aminar ta ce.

"Wai ma! Da gaske Yaa Amina?"

"Ina wasa dake ne Anaam?"

Girgiza kai ta yi tana dariya ta ce.

"A'a. Amma dai ana yi sama-sama wani lokacin...."

"To da gaske nake miki, wan can kayan ki ne."

Cikin rashin tantance shin wai ma a wane yanayi take ta sake kallon akwatunan sai kuma ta kalli Amina ta ce.

"Yaa Amina daman ana yin Hakan? Daman ana yin kayan ƙawar Amarya?"

"Ban taɓa gani ba ni dai sai yau a wurin Haisam. Ki karɓa ki yi godiya kamar yanda muka yi. Wannan ba komai ba ne, duk yana daga cikin haɗin kai da yaga kuna da shi da kuma zaman lafiya. Allah ya kauda shaiɗan a tsakanin ku ya ƙarawa zumuncin ku albarka."

Jinjina kai ta yi tana murmushi ta ce.

" Gaskiya Yaa Amina na ji daɗin wannan kyautar sosai har cikin rai na. Ba don na rasa wani abu ba, na ji daɗi sosai. Na gode sosai..."

"To muje kin ga lokaci ya ƙure sosai a yi miki make-up ɗin nan ki shirya mu wuce sa lallen nan...."

Hanyar ɗakin Ammienta ta nufa tana faɗin.

"Yaa Amina ba zan yi make-up ba gaskiya, lokaci ya ƙure sosai, bari na ga Ammie daga nan sai na wuce na shirya."

Ta na barin wurin sai ga su Umma matar Alhaji Salisu sun yi sallama sun shigo ita da sauran 'yan uwan su da suka daga Gusau.

Sosai aka shiga hidima da su wurin ba su abinci da kuma yi musu barka da zuwa. Suna yin sallah ba su zauna ba suka wuce ƙayataccen Hall ɗinda suka kama aka yi shagalin sa lalle aka gama suka juyo misalin karfe takwas na dare suka dawo.

Kowa ya yi mamakin ganin yan da Anaam ta saki jikinta ta gwangwaje tamkar ba ita ba. Ba su ma ƙara shan mamaki ba sai da suka ga ta ruɗe da farin ciki da aka ce mata Mukarram da Familyn shi sun sauko ƙasar suna hanyar zuwa gida.

Su kuma su Umma da suke kullum ba su rabuwa da tsegumi, kowa na can yana abin da ya dame sa su kuma suna nan tun da suka ga ɗanƙara-danƙaran akwatun nan Na'imatu da kuma na wai na Anaam suka shiga tashin hankali.

Tun da ake zancen Auren Haisam ɗin nan da Na'imatu ba su ɗauka cewa haka yake ba. Sun ɗauka cewa can wani shashasha ne Alhaji Mas'ood ɗin ya ɗauko zai aurawa Na'ima ashe-ashe shegen mai kuɗi ne.

Cike da baƙin ciki Rabi'atou ta kalli mahaifiyar ta ta ta ce.

"To ni Umma yanzu dan Allah shi ke nan ba za'a bani komi ba a kayan nan ba? Ni da nake ƙanwar ta uba ɗaya bani ya kamata ace an yi wa akwatunan nan ba?"

Taɓe baki wata ƙanwar Umma da suka zo da ita ta yi wacce ake cewa Shema'u ta ce.

"Uhm! To idan ma akace shi Haisam ɗin bai san ki ba ma kada ki yi mamaki. Sannan ko ku ɗin tun da muka zo gidan nan naga suna yi muku wani kallon hadarin ka ji tamkar ba matar Alhaji Salisu ba da 'ya' yan sa. Shi ke nan ɗiyan wacce ta mutu ma sun fi ku daraja a idon su..."

Miƙewa Jamila ta yi wacce itama ƙanwar su Alhaji Mas'ood ɗin ce amma ba uwa ɗaya uba ɗaya ta ce.

" Gaskiya kuna da matsala hajiya Umma! Miye abin gulma da tsegumi a nan? Na'imatu fa a gidan nan ta tashi, sannan ko kun ƙi Allah wallahy kun san cewa Alhaji Masa'udu da Hajiya Nasmah ba su da abin zagi gareku domin sun yi muku riga da wando idan ga halacci...."

A harzuƙe Umma ta wani taso ta hayayyaƙo mata tana faɗin.

" To ai yanzu Jamila ke ce babbar munafuka da baki ganin laifinsu! Ƙaramin misali...ki kalla tun da muka iso garin nan sun sake komawa kanmu tun da muka gaisa ɗin nan?"

" To ai hidima suke, kuma kina ganin yanda suke ta tara jama'a..."

"Amma ai ga Yayarta can da danginta ta ja su kusa da ita, kuma duk abin da za'a yi suna tare..."

Wata dariya Jamilar ta yi sannan ta girgiza kanta ta ce.

"Shi dai wani wallahy sam ba shi da ganewa. To yanzu yan da ta ja en uwanta a jiki haka kike so ta ja ki? Kada fa ki manta ke kawai matar yayan mjinta ce kuma ta san cewa ba son ta kike ba...."

Wannan maganar ba ƙaramin zafi ta yi wa Umma ba, hakan yasa ta wani bangaje Jamilar tana faɗin.

" Dalla ja can baƙar munafuka kawai. Daman ai na jima da sanin cewa kina baƙin ciki dani kin fi son Nasmah fiye da ni..To wallahy kaya dole a raba su a ba Rabi'atou na ta domin ba finta suka yi ba. Kuma dole ta dawo nan da zama domin itama Alhaji Mas'ood ɗin ya samo mata irin mijin da ya samo wa Na'ima ehee!"

Waje Jamila ta fice ta nufi inda sauran dangi suke na mutunci ta bar musu ɗakin domin ta fahimci cewa ba su taɓa ganewa.

Sai yanzu Shema'u ta nisa sannan ta wani ƙara gyara zama tana faɗin.

" Humm! Lallai Aunty Umma kina ruwa. Yanzu har yaushe ki ka zauna ki ka bari har wannan renin ya shiga tsakaninku da irin su Jamila? To wallahy idan ba ki ɗauki mataki ba nan gaba ko dukan ki sai ta ce ta yi. Ya kamata ace yanzu kece uwar Na'ima tunda dai ke ce kishiyar uwar ta kuma uwar nan ta ta ta mutu,komai ya kamata ace an sanya ki gaba. Maimakon kawo lefen nan ace a jira ki ba su yi hakan ba...."

" To ko ƙanwar uwar ta Balaraba kin ga sun jira?"

" Ba su jira ta ba amma dai tana isowa kina gani Hajiya Nasmah ta kira ta suka haye sama, tun lokacin kin ƙara ganin ta ba sai da aka fito za'a tafi sa lallen ba..."

Jinjina kai ta yi tare da yin kwafa sannan ta ce.

" Ki bar ni da su Shema'u. Wallahy duk sai na yi maganin su. Kuma daga yau Rabi'atou tana nan a gidan nan sai ya samo mata mijin itama. Zan ga uban da zai kore ta gidan..."

"Da kam yafi."

Dan Allah ma su son shafukan baya ku duba channel akwai a ciki tun daga farko har inda aka tsaya Please.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️

*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 20*

https://chat.whatsapp.com/KgJnAzr5KBoJ9YAa2LxG8w

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull