Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 15

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 15

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 15: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 15. *Albishirinku jama'a shin ko kuna da labarin katafaren group ɗin…

3,372 words

*Albishirinku jama'a shin ko kuna da labarin katafaren group ɗin mu, da mu ke tura KAYAN KITCHEN da KAYAN ƊAKI, har ma da KAYAN YARA MAZA DA MATA, ba mu tsaya a nan ba duk wasu abubuwan da UWAR GIDA DA AMARYA HAR DA 'YAN MATA masu CAPACITY ke bukata muna turawa, kayan mu na kasashen ketare ne kama daga Kayan kitchen, Kujeru da gadaje har da atamfofi, laces da Abaya, fashion net da bedsheets, hijabs gowns, caps, ribbons duk muna da su akan farashi mai RAHUSA, ga masu sayen ɗaya ko sari muna turawa ko'ina a cikin aminci, mutanen mu na kasashen waje kamar Chadi, Nijar, Kamaru, Ghana duk ba'a bar ku baya ba muna tura muku kaya har kasashen ku. Farashin kayan mu tamkar sari ne zaku saye har ku ɗaura ta ku riba kuma muna discount.

Ga masu bukatar kayan mu sai ku hanzarta shiga wannan link.💃💃💃

Washegari har akayi walima aka watse Anaam tana tare da Na'ima, sai da suka dawo gida sai ga Rabi'atou ta shigo ɗakin da suke ita da Na'ima wanda suna zaune ne Anaam na ragewa Na'ima make-up ɗinda fuskarta ta shigo.

Suna yin ido biyu da Anaam ɗin ta sauke hannunta daga fuskar Na'imar kawai ta kama hanya ta fice.

Za ta iya cewa bayan mutumin da ya yi mata fyaɗe da kuma Alhaji Gimba Rabi'atou za ta iya zuwa ta uku a cikin jerin mutanen da ta tsana a duniya.

A lokacin da ta fara samun sukuni da kuma fighting akan yanda za ta manta da bayan ta, Rabi'atou ita ce wacce ta nuna mata abin da har ta mutu ba zai goge a ƙwaƙwalwarta and har Umman ta take ganin cewa wai kuma ba ta aikata laifin komai ba.

Hakan yasa ta ji gabaɗaya daga ita har Umma ta tsane su a yanzu. Idan za ta gan su sau dubu a wuri tabbas za ta tashi ta canja wurin zama domin ta samu hankalinta ya kwanta.

Ɗakin da Aunty Amina take ita da Aunty Aysha can ta nufa.

Ita kuma Rabi'atou tana ganin fitar Anaam ɗin ta taɓe baki sannan ta ce.

"Koma dai miye baki da yan da za ki yi dani domin ni ɗin jinin ki ce da uban ki da ubana uwa ɗaya uba ɗaya...."

Wata uwar tsawa Na'ima ta daka mata wacce ta yi sanadiyyar saka ta haɗiye sauran maganarta ba tare da ta shirya ba.

Cike da takaicin ta ta kalle ta tana jinjina kai ta ce.

" Wai ke Rabi'a ba za ki taɓa yin hankali ba ko? Wato abin da ya faru a baya har yanzu bai sa kin yi laushi ba kenan?"

Zumɓuro baki ta yi zuwa gaba tana faɗin.

"To ba ki ga ita yanda tayi min ba kamar wani taga kashi..."

"Ai dole ta yi acting haka because kin ɓata mata rai ne..."

"Oho mata Aunty Na'ima. Ni dai wallahy dole a raba kayan da Yaya Haisam ɗin ya kawo a bani rabona tun da ba ita kaɗai ce ƙanwar ki ba..."

Cike da zallar mamaki da ya kusa kashe Na'ima ta kalle ta ta ce.

"Wane kaya ke nan za'a raba Rabi?"

"Kayan da aka kawo da sunan ta mana..kuma alhali..."

Jinjina kai ta yi cike da takaici ta ce.

"Saboda ubanki Salisu ne ya siyo ko Mas'ood ko kuma ƙanin uwar ki Basiru? Na ce wanne ne daga ciki ya siyo kayan da har kike wani ɗaga shoulder kina faɗin kina da haƙƙi a ciki?"

Miƙewa Rabin ta yi tsaye tana kallon idon Na'imar domin ba ƙaramin mamaki ta bata ba jin irin waɗannan kausasan kalamai da ta yi amfani da su wanda hakan ya tabbatar mata da cewa idan ta matsa mata za ta iya jin duka a kowane irin lokaci.

Ganin yanda still ta kafeta da ido cike da ɓacin rai yasa ta yi hanyar waje tana gunguni ta ce.

"Ai dai idan ba ki san darajar iyayen ki ba ni na sani, saboda haka ba zan zagesu ba. Daman yanzu don kin samu wannan mai kuɗin ne yasa kike ta wani ɗaga kai kina wulakanci..."

A zafafe Na'ima ta taso sai gashi ba shiri ta zuba da gudu ta yi inda Umma.

Kiciɓis suka yi da Anaam wacce ta fito daga wurin su Aunty Amina za ta je ɗakin Abbah da yake kiranta.

Shan gabanta Anaam ɗin ta yi tare da kallon ta sama ƙasa sannan ta ce.

"Na ɗauka abin da ki ka min kin yi sa a bisa kuskure da rashin sani, hakan yasa na ke ta ƙoƙarin inga cewa na yafe miki a raina domin bana so ina jin haushin ɗan uwana. Ashe duk abin da kike da gangan ne, wato har mutanen da basu san abin da ya faru dani ba kike bi kina faɗa masu ko? And still kina zagi ne kina cewa kina jin haushi na. Da na yi miki me Rabi'a? Ko kayan da aka kawo na ji labarin tun jiya kuke yamaɗiɗi da maganar cewa wai sai an raba an baki naki, to bari ki ji! Kin dai san cewa nafi ƙarfin wannan kayan gaba da baya domin ba ni da Ƙishirwar sutura, amma wallahy tallahy ɗan kunne wannan ba za'a baki a ciki ba, na fi son in ajiye su harabar gidan nan in kunna musu wuta da a baki wani abu daga ciki. Ki fita har kata Rabi'a, ki daina yawo da magana ta, idan ba haka ba wallahy tallahy sai na miki rashin mutunci na ƙarshe."

Daga haka ta raɓa ta ta wuce tabar ta nan tana kallon ta har ta ɓace wa ganin ta.

Tamkar za ta fashe haka ta shiga cika tana batsewa har ta isa inda Umma.

Tana zuwa ta fashe da kuka ta shiga faɗa mata Ƙarya da gaskiya akan Anaam da Na'imatu.

Bayan ta dasa Aya Ummar ta jinjina kai ta ce.

"Bar ni da su! Bana so ne in tayar da wata magana su yi min gurguwar fahimta a tada hitina ace nice bana son zaman lafiya, musamman da ya kasance Hajiya Hanne na nan. Saboda haka ki bari a kambala hidimar nan mutane su watse tukun. Za ki ga irin matakin da zan ɗauka."

Ta san irin rashin mutuncin da Baba Salisu ya yi mata lokacin da akayi auren Naseer da ta tayar da rigima lokacin bukin wanda ya kusa sanadiyyar igiyar auren ta. Shi ne yanzu take taka-tsan-tsan.

*******

Bayan Anaam ta shige sashen Abbah a hankali suka shiga taruwa suna ta fira har misalin ƙarfe ɗaya na dare.

Muhammad, Mukarram, mubarak, Na'imatu da kuma Ammie duk suna ɗakin tare da Abbah da Anaam suna ta tattaunawa dangane da batun ɗaurin auren da za'a yi gobe da kuma firarrrun rayuwa da tsakanin family. Bayan sun bar nan Mubarak ya sake jansu zuwa parlourn Ammie da shi da Na'imatu da Anaam wai su ƙara firar ban kwana.

Suna zaunawa sai ga kiran Haisam ya shigo wayar Na'ima, answering call ɗin ta yi tare da ɗosana wayar a kunnenta.

Kallon kallo suka fara tsakanin Anaam da Mubarak suna yi suna kallonta suna dariya, ganin hakan yasa ta miƙe ta bar musu parlourn na kusan tsawon 30mnt sannan ta dawo ɗauke da tray a hannunta mai ɗauke da Gasashen tsirai da kuma lemu da glass cups.

Ajiyewa ta yi gaban su sannan ta samu wuri ta zauna da yanayin jin tsarguwa a ranta ganin irin kallon da suke ta mata suna dariya ƙasa-ƙasa.

Miƙewa ta yi tana mai hawaye ta nufi hanya za ta fice sai ga Hajiya Nasmah ta shigo. Riƙo ta ta yi cike da mamaki ta kalle ta sai kuma ta kalli su Anaam ɗin ta ce.

"Lafiya? Ya naga hawaye a idon ki Na'ima?"

Zubo da hawayen ta yi sannan ta kalle su ta ce.

"Haka kawai wai Ammie sun kama suna yi min dariya tun ɗazu. Kuma sun san bana son hakan, amma sai wani kallo suke min suna dariya a ƙasa-ƙasa..."

Dariyar suka fito fili suna yi Mubarak ya ce.

"Ammie dariyar yanda take waya da Haisam ne muke yi bayan ta gama rantse-rantsen cewa ba za ta aure shi ba..."

"kai dai an yi babban banza wallahy!..."

"Amm.."

"Dan Allah ni tashi ka bani wuri."

Miƙewar ya yi salin alin ya fice zuwa ɗakin sa. Muryar Anaam suka ji tana faɗin.

"Ki yi haƙuri yaa Na'ima."

Hannun Na'imar Ammien ta ja tana faɗin.

"Kada ki yi hak'uri ƙyale ta kawai. Ta zauna tana biye Mubarak alhali tasan cewa jibi warhaka kina gidan ki kin barta da kewa."

Haka dai Ammie ta samu ta lallaɓa ta har ta hak'ura wanda sai da Anaam ta gama cin tsirenta sannan ta tashi ta bi bayan Na'imar ta lallashe ta har ta samu ta haƙura. Sai ga shi sun yi rabin kwana a zaune suna fira sai can bayan sallar asuba suka kwanta.

Da garin ya gama wayewa misalin sha biyu na rana aka ɗaura auren Na'imatu Salis Galadima da kuma Doctor Haisam Usaid.

Tun da aka kambala suke kuka a tare kamar a tare aka ɗaura musu auren ita da Anaam ɗin. Gabaɗaya a wuri ɗaya suka wuni suka kwana har gari ya waye suka hau jirgi zuwa Jihar Adamawa inda a can ne Haisam ya koma da aiki yanzu.

*******

Maheer.

Tsaye yake a jikin windown ɗakin hotel ɗinda ya kama tsawon kwanaki yana waya da Hamad wanda yake jin yana matuƙar-matuƙar ƙona masa rai a yanzu. Sai yake ganin Hamad ɗin tamkar ba amininsa da yake ji da shi ba. Gabaɗaya ya sauya kamar ba shi ba. Kuma ya gama fahimtar cewa tun da ya sanar da shi abin da ya aikata shike nan ya sauya. Yanzu ma taƙaddama kawai suke akan cewa ya dawo Lagos wurin aikinsa tun da har ya kasa samun ta wanda tunda suka fara magana bai yi maganar da ta kai uku ba, shiru ya yi tsawon lokaci yana sauraren Hamad ɗin sannan daga ƙarshe ya ce.

"Na kasa gane inda ka dosa Hamad...gabaɗaya sai nake ganin kamar farin ciki kake da ƙaddarar da ta faru dani..."

Daga can ɓangaren Hamad ɗin ya ce.

"Ba farin ciki nake ba Maheer. Daga lokacin da ka ƙetare iyakar ubangiji daga lokacin za ka daina ganin daidai a rayuwarka. Ka baro Zamfarar nan ka dawo bakin aikinka kada ka yi saki na dafe...."

Cikin ɗaga murya ya ce.

"Ba za'a dawon ba! Ba za'a dawon ba na ce..."

"Then....za ka ji saƙon sallama daga Maritime nan ba da jimawa ba...kaga sai ka yi wa Maami bayanin dalilin da ya saka har aka kore ka..."

"Ba Za ka taɓa ganin hakan ba Hamad.."

"Zan gani mana! Tabbas zan gani matuƙar ba ka daina wannan shashancin ka dawo wurin aikinka ba..."

Cike da mamaki ya ce.

"Yau ni ka ke kira shashasha Hamad?"

"Dame zan kira ka idan ba shashashan ba? Ka wai malam kaje ka aikata abin da ko wani ƙaramin yaro ba zai aikata ba. Idan ba shi ba ina kai ina hulɗa da 'yan daba? wai har ka yarda ka haɗa hannu da su tsawon lokaci ka biye su saboda kawai kai babu wanda ya isa ya faɗa maka ka ji...ka ɓata sunan ka, ka aikata abin da har abada ba za ka daina danasani ba..."

Ƙitt! Haka Hamad ya ji Maheer ɗin ya tsinke kiran.

A zafafe ya shiga haɗa kayansa nan da nan ya je ya kama hanya zuwa Airport ransa a gashe tamkar zai mutu akan takaici da baƙin ciki.

Yana nan a reception kawai yaga shigowar saƙon Hamad. Kamar ba zai buɗe ba, sai kuma wata zuciyar tace ya buɗe yaga miye abin da kuma yake nema.

Har wani ƙara buɗe idanunsa ya yi ya shiga karanta bayanan Anaam ɗin da yaga Hamad ɗin ya turo masa.

Bayanan inda suka koma ne da address da komai ya tura masa. Duk wani bayananta sai da rubuce masa su hadda bayanin sabuwar University ɗinda aka nema mata da kuma lokacin da za ta fara karatu da komai.

Ya mutu da mamakin ganin wannan saƙon na Hamad, daman ashe tun tuni yasan tana a Abuja amma ya bar shi tsawon lokaci yana ta wahala yana raina masa da wayo.

"Hamad banza ne, banza kawai bad boy!"

Abin da ya furta kenan tare da mayar da wayar cikin aljihu ya shiga sabon tunani.

Daga nan bai tsaya sanya ba ya kama hanyar sa ya koma Lagos.

*****

Gidan Alhaji Mas'ood kuwa, tun a bakin Main parlour Mukarram yake Ji yo hayaniya wacce ta yi matuƙar ba shi mamaki.

Yana shigowa ya yi ido biyu da Umma tana ta zuba masifa akan cewa wai dole Rabi'a a nan za ta zauna itama ayi mata miji wanda daga ƙarshe ta ɓige da fashewa da kuka.

Bayan ta sauke Alhaji Mas'ood ɗin ya jinjina kansa yana kallon ta ya ce.

"Abun da kike so kenan Hajiya Umma?..."

Da Mubarak da kuma Mukarram lokaci ɗaya suka yo caa! Musamman Mukarram da ya ji tamkar ta kikkifa mata mari ya ce.

"Haba Alhaji! Akan me za ka biye ta? Don Na'ima ta zauna a gidan nan sai akace dole itama sai ta zauna?"

Tana wani kukan munafurci ta wani girgiza kai ta ce.

"Ka ji ko Alhaji? Irin waɗan nan kalaman su ne ke sa kowa ya riƙa ji a ransa kamar ba ɗaya ake ba...idan ba shi ba ai da Na'ima da Rabi duka ɗaya ne..."

Cikin jin haushin ta mukarram ɗin ya ce.

"To ai Hajiya Umma ke ce kike nuna kamar ba ɗaya suke ba! Don an aurar da Na'ima sai kice dole Rabin itama sai ta zo ta zauna nan an aurar da ita? And miyasa ma ba ki tayar da zancen ba sai da kika ga Baba Salisun ya wuce..."

"Mukarram!"

Abbah ya daka masa tsawa ganin yanda yake ta wani ɗaga murya yana gaggasa mata magana.

Shiru ya yi tare da zubawa Abban ido yana jira ya ji mi zai ce.

"Gida dai nawa ne. Zaman Rabi'atou a gidan nan babu abin da zai ƙara mana ko kuma ya rage mana. Saboda haka ku barta ta zauna a nan ɗin, ai da nan da gidan Salisun duk ɗaya ne. Sai su ci gaba da karatu ita da Maryam Kaga har yanzu dai tana da abokiyar shawara...."

Kallon Hajiya Nasmah mukarram ya yi ya ce.

" Ammie wai ba za ki ce komai ba? Yarinya fitsararra kamar Rabi miye za'a yi da zaman ta a nan?"

Hannun sa Mubarak ya ja da ƙyar suka bar ɗakin wanda har suka fice bai dai na mita ba.

Sai faɗin yake.

" Ni wallahy sanyin Alaji ya yi yawa! Shike nan shi komai dai sai yace ayi ta haƙuri da 'yan uwa? Idan ba samun wuri ba wacece Hajiya Umma da har za ta zo gaban sa tana ɗaga masa murya yana zaune yana kallonta."

Can parlourn kuwa, kallon Umma Hajiya Nasmah ta yi tana jinjina kai ta ce.

"Duk inda bawa yake rabonsa baya taɓa wuce sa Hajiya Umma. Kullum ki riƙa saƙa alheri a cikin zuciyar ki."

Daga haka ta wuce ta bar musu parlourn ta yi shigewarta.

******

Maheer kuwa, kwana biyu ya yi a Lagos bayan ya kammala aikin da yake gaban sa na kwana biyu sannan ya sake tsallakewa ya wuce Abuja kai tsaye da nufin ganawa da Anaam.

Har ya sauka Abujar bai dai na kallon address ɗinda Hamad ɗin ya tura masa ba. Tabbas yana so ya ganta. Kusan shi ne babban abu mafi muhimmanci da ya kawo sa ƙasar saboda haka ba zai yarda ya yi wasa da damar sa ba. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 21*

Faris ne zaune a parlourn Alhaji Mas'ood wanda yafi 2hours da zuwa. Koda ya zo gidan bai yi tunanin cewa za'a bar shi ya shiga ba, because shi yasan abin da Daddynsa ya yi musu Sam bai kamata ba. But unfortunately yana zuwa security tun daga gate ɗin farko na unguwar suka sanar da zuwan sa sai ga shi cikin ƙanƙanin lokaci Alhaji Mas'ood ɗin ya yi musu izini akan su bar shi ya wuce.

Ya kasa ɓoye baƙin ciki da damuwar da ke ransa, hakan yasa ya yi masa bayanin halin da suke ciki dangane da Alhaji Gimban daga shi har mahaifiyar shi.

Bayan ya sauke duk wani zancen da ke ƙunshe a cikin akwatin sirrinsa Alhaji Mas'ood ya kalle shi ya ce.

"Na ji duk bayanin ka Faris. And a yanzu what do you want me to do?"

Ɗan muskutowa ya yi zuwa gaba kaɗan daga kan kujerar da yake zaune yana mai kallon fuskar Abbahn ya ce.

"Abbah kamar dai ko yaushe. Ka sani duk duniyar nan ba bu wanda yake faɗawa Daddy magana ya ɗauka fiye da kai. Sai da na fara sanar da Daddy Ridwan but bai saurare shi ba,ƙarshe ma dai haka suka ƙare ba daɗi...."

Jinjina kai Alhaji Mas'ood ya yi ya ce.

"To nima dai kamar haka ne Faris...Alhaji Gimba ya canja sosai, ni ko Alhaji Ridwan wani daga cikinmu zai iya faɗa masa magana ya ɗauka kamar yanda ka ce, amma a baya. Yanzu sam ba bu wannan. Shawara ɗaya ce a nan shi ne, tun da har abin ya zo a haka, to ka samu mata ka yi aure, in sha Allahu matuƙar ka yi auren to abubuwa za su daidaita a tsakanin ku. And a yanzu kuma tun da yace baya so kana shiga gidan to ka daina na ɗan wani lokaci..."

A hankali ya zame ya sauko ƙasa tare da matsowa dab da ƙafafuwan Abbahn in a pleading tone ya ce.

" Abbah! Har yanzu ni ina son Maryam. Abin da ya faru da ita wannan jarabawa ce kuma babu wanda yafi ƙarfin jarabawa a rayuwar nan, saboda haka still dai ni ina son ta a haka, idan ka amince ka shirya nima a shirye nake...."

Girgiza kai Alhaji Mas'ood ɗin ya yi yana wani murmushi ya ce.

" Ban katsi hanzarinka ba Faris, but dan Allah wannan maganar ina so ka bar ta. Ka barta har abada domin kai da Maryam aure ba zai taɓa faruwa ba tsakanin ku...."

"Haba Abbah! Ta ya za ka ce haka dan Allah! Wallahy tallahy ina son ta, so na domin Allah, kada ka yi tunanin akwai watarana da za ta zo wacce za ta saka wai na wulaƙanta ta ko na bari wani nawa ya yi Wulaƙanta ta..ina son Maryam Abbah, dan Allah ka yarda dani ka aura mi...."

"Ba za'a aura maka ita ɗin ba Faris kutumar Ubanka..."

Cewar Mukarram wanda shigowar sa parlourn kenan. Ganin kawai suka yi ya yo kan Faris ɗin ya wani cakume shi cike da rashin arziki ya ɗaga hannu yana shirin kwaɗa masa mari cikin zafin nama amma ya miƙe da sauri ya riƙe hannun sa ransa a ɓace yace.

" Sake shi Mukarram! Ka sake shi na ce!"

Ransa na wani irin tafarfasa ya wani yarfar da shi yana wani sauke nurfafashi tamkar wanda ke shirin gwabza yaƙi.

Shi ma Alhaji Mas'ood ransa a ɓace cike da zallar mamaki ya ce.

"Mukarram yanzu a gabana ka ke irin wannan zagin? Iyeh! Wai ke mike damunka ne?"

"Amma Alhaji ba ka ji irin maganar banzar da yake faɗa ba? Saboda kunya ta yi masa ƙaranci har yana da guts ɗinda zai iya sake takowa cikin gidan nan har yace a aura masa Anaam? In fact waye ma ya bashi izinin shigowa gidan nan?"

"Ni ne? Ni na ba shi izini saboda gidana ne. Ko za ka hana ne?"

Tamkar zai yi kuka ya ɗaga yatsa ya nuna Faris ɗin ya ce.

"Alaji Faris ne fa! Faris ɗan gidan Alhaji Gimba. Ko ka manta abin da suka yi mana?"

"Shi ɗin aminina ne wannan kuma ɗan sa ne,hakan yasa ni ma ya zamto ɗana kamar yanda ka sani a baya. Ko da ace abubuwa sun ɓaci a tsakaninmu da mahaifinsa, tun da har ya ci gaba da riƙe ni a matsayin uba to shi ɗin ɗana ne. Saboda haka he has every right da zai iya shigowa gidan nan a duk lokacin da ya so."

Cikin jin wani iri a ransa ya girgiza kai ya ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull