Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 16

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 16

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 16: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 16. " Alaji wai miyasa kake mana haka ne? Kai shi ke nan kamar kai ne…

3,369 words

" Alaji wai miyasa kake mana haka ne? Kai shi ke nan kamar kai ne kafi kowa haƙuri, komai aka yi sai shi ke nan sai ka mayar da shi na komai ba."

"Zama mai haƙuri a koda yaushe shi ne cika mutum Mukarram..."

Girgixa kai mukarram ya yi tare da runtse idanunsa da ƙarfi ya naushi iska sannan ya kama hanya kawai ya bar parlourn.

Kafaɗar Faris ɗin Abbah ya dafa yana mai jinjina kansa ya ce.

"Ka yi haƙuri Faris..tun ba yau ba ka riga da kasan waye Mukarram. Saboda haka kada ka damu da shi. Samu wuri ka zauna mu yi magana."

Kan kujerar da ya fara zama a farko ya koma ya zauna a kanta sannan Abbah ya ce.

"Faris ka yi haƙuri, amma ba zan iya aura maka maryam ba. Ka je ka samu wata sai a samu a yi auren. Sannan yanzu da ka baro masa kasuwancin sa sam bai yi ba..."

Kamar zai fashe da kuka ya kalli Alhaji Mas'ood ɗin ya ce.

"Wallhy Abbah ba zan iya ci gaba da kula masa da kasuwancin sa ba. Ya je ya samu dangin matar da ya auro su ci gaba da running business ɗin nasa amma ni ba zan yi ba."

"Faris...idan ka bari kasuwancin mahaifinka ya samu tangarɗa to kai ma ka samu..."

"A'a Abbah! Shi dai ya samu tangarɗa ba ni ba tun da har haka ya zaɓa. Idan har aka samu matsala sai yafi fi ni jin ciwo domin sai da yasha wahala kafin ya samu ya tsaya da ƙafafuwansa."

"Faris..."

"Abbah ka gafarceni. Gaskiya ba zan ci gaba ba, kuma ni ko garinma ba zan koma ba..."

Juyin duniya Abbah ya yi amma Faris ya ƙeƙashe idonsa ya ce shi ba zai koma ma garin ba, ƙarshe ma ya ce.

"Sannan dan Allah Abbah ina neman alfarma da ka bar ni a nan ka bani dama in ci gaba da zama a nan ɗin kafin mu ga ni."

Shiru Alhaji Mas'ood ɗin ya yi na en wasu daƙiƙu yana nazari sannan daga ƙarshe ya jinjina kansa ya ce.

"No problem, You are permitted. Ai nan ɗin gidan ku ne kada ka damu, ka zauna har san da ka ji ya yi maka."

"Na gode sosai Allah ya saka da alheri ya bar zumunci."

"Ba damuwa, ka tashi, zan yi wa Hajiya Nasmah Magana sai ta baka wurin da ya dace ka zauna."

*******

Mukarram kuwa yana fita ya nufi wurin Hajiya Nasmah yana ta jidali tamkar zai tada gidan yana faɗin.

"Hajiya tsakani da Allah abin da Alaji yake a gidan nan sam baya kyautawa! Idan ba shi ba miye na barin Faris dan Allah ya shigo cikin gidan nan har ya zauna yana masa zancen banza na cewa wai a aura masa Anaam..."

"Alhaji har abada ba zai taɓa aura masa Anaam ba kai ma ka sani..."

"Ga shi kuwa ya zauna yana sauraren sa. With all the bad things da suka yi har Alaji wai yana da zuciyar da zai tsaya yana sauraren sa. Ga yarinyar nan fitsararra da ya amince wai ta dawo gidan nan ta ci gaba da zama..and kina nan ke ma kina gani. Sai a yi ta abu a gidan nan amma sai ki yi shiru bakya magana Hajiya fisabilillahi!"

"Wai Mukarram kai miyasa kullum kai ba ka da haƙuri ne? Kada fa manta fa shi ne mai gidan nan gabdaya, duk abin da yake so yaga cancantar sa ni miye nawa a ciki matuƙar ba Allah ya saɓawa ba? Saboda haka kamar yanda na saba gayamaka mukarram dan Allah ka riƙa haƙuri da mutane a rayuwa. Kai ɗin nan fa magidan ci ne, yau baka so ka kawo wata magana a gidan ka wanda kana ganin ka cancanta ka isa kuma ta zo ita matarka ta ce ba haka ba, ba za ka ji daɗi ba. Haƙuri matakin nasara ne a rayuwa."

Wuri ya samu a ƙasan carpet ɗin na ta ya zauna. Cikin son canja firar ta su ya ce.

"Wai Hajiya miyasa ne ni kam wasu matan ba su da lissafi ne wani lokaci? Koda yake har da Naseer ma da ya biye su."

"Mi kuma suka yi?"

"Hajiya Rakiyar Na'ima almost 5days now, ai ya kamata ace sun dawo tun da dai ba wasu dangi gare su a can Adamawar nan ba. Shi Haisam ɗin ma ai za su takura shi tsakani da Allah!"

Kallon Nene ta yi wacce ta ajiye mata tiren abincin a gabanta ta ce.

"Kin gama dafa zogalen ne?"

Cike da girmamawa ta ce.

"Eh, na gama. Na zuba na Alhaji daban kamar yanda kika ce. Sannan ga shi nan na zuba miki a wannan bowl ɗin..."

Jinjina kai ta yi sannan ta kalli inda mukarram yake zaune yana latsa wayarsa ta ce.

"A zuba Zogalen ne za ka ci?"

Ajiye wayar ya yi ya kalle yace.

"Wanne kalar abinci ne?"

"Rice and beans ne with oil..."

"To idan akwai garin ƙuli-ƙuli a haɗa mini da shinkafar kada a saka waken."

"Okk to...Nene ki ɗauka ki haɗa masa, akwai sauran zogalen a kitchen ɗin?"

"Eh akwai, ai da yawa fa aka kawo, na fige sauran na ajiye idan kina buƙata zuwa gobe ko jibi sai a dafa."

"Yauwa, na gode. To kije ki haɗa masa sai ki kawo masa nan ɗin."

Kallon Hajiyar ya yi ya ce.

"Hajiya baki ce komai ba."

Tana kan haɗa abincin da za ta ci ba tare da ta kalle shi ba ta ce.

"Gobe In Sha Allahu za su dawo. Komawar ku ba kace sai next week ba."

"Eh."

"To dan Allah ka bar su su huta. Yanzu kafin ta sake ganin su a Adamawar sai yawancin rai musamman Ayshar da Amina."

"To Allah ya kai mu goben lafiya."

"Amin."

Suna nan a zaune tana cin abin Shi ka yana zaman jira sai ga Alhaji Mas'ood ya kira ta yace ta zo yana neman ta.

*******

Maheer.

Tun da ya sauka a Abujar bai yi wani baccin kirki ba har garin Allah ya waye.

Mota ya ɗauka ɗungum suka nufi anguwar, suna hango gate na farko ya ba mai motar umarni akan ya tsaya daga ne da tukun kafin ya yi magana da wanda zai je gun sa.

Tunanin ta yanda zai tsallaka gates ɗin ya fara har ya kai ga iya isa gidan na su ma. Gate ne fa ta ko'ina and ga jami'an tsaro a bakin kowane gate ɗin. Idan suka fara tambayar shi abin da ya kawo shi da kuma wurin waye ya zo mi zai ce?

Wayar shi ya ciro ya kira Hamad wanda dai duk tsiya duk daɗi ba shi da tamkar shi. Sai da ta yi ringing almost twice Sannan daga ƙarshe ya ɗaga.

Ransa a ɓace ya ce.

"Ai dai kasan zan kira ka. Ban san dalilin da zai sa ka riƙa nisa da waya ba alhali kasan cewa dole zan kira ka."

Daga can ɓangaren Hamad ɗin ya ce.

"Is not possible ace za ka kirani wai idan za ka yi wani abun because ba yau ka saba ba..."

"Malam kada ka ƙara ƙona min raina...just tell me abin da ya kamata na faɗawa securities ɗin nan domin na samu na shiga gidan su yarinyar."

"While...you can tell them Cewa kai ne.."

Shiru Maheer ɗin ya yi yana jira ya ji ƙarashen zancen but sai ya fahimci cewa Hamad ɗin bai da niyyar yin wata maganar, hakan yasa ya wani lumshe ido sannan ya buɗe ya shiga kallon zarazaran yatsun hannun sa na hagu ya yin da ɗayan hannunsa na dama ke maƙale da waya a kunnensa camly ya ce.

"Hamad I don't understand! In faɗa musu cewar ni ne kamar ya?"

"Ah to, mi zan ce maka? Tun da kana so ka shiga gidan su ai sai ka ce kai ne wanda ya yi musu laifi ya cutar musu da 'yar su don Allah su barka ka shiga gidan..."

Cike da takaicin maganar Hamad ɗin ya ce.

"Wai miyasa ka ke min haka ne?"

"Because kai ne kake yin abin da bana so. Ka bar wannan shirmen Maheer! Idan ka bari ka shiga hannu ba za ka sha da daɗi ba..."

"Wai kai a tunanin ka sai da kai zan iya? I can handle this mah self, Saboda haka ba ruwan ka..."

Dariya ce ta so suɓuce wa Hamad ɗin, amma haka ya cije ya ce.

"Kai ne ka kirani ba ni ne na kiraka ba kada ka manta. Ka je Allah ya bada sa'a. Ina gaida Maryam Mas'ood Galadima, kace nima ina taya ka neman gafarar ta..."

Kitt! Haka ya katse kiran tare da naushin front seat ɗinda ke gaban sa kamar zai kama da wuta tsabar takaicin Hamad. Hamad ba shi da mutunci ko kaɗan kuma ba shi da tausayi a 'yan kwanakin nan.

Ganin sun jima a tsaye mai drivern ya ɗan wai go kaɗan ya ce.

"Sir please you need to hurry...."

Cike da masifa ya katse shi da faɗin.

"shut up! Just shut up! Kada ka ƙara min matsala. Zan biya kuɗi ko nawa kake so."

Shiru mai motar ya yi tare da mayar da kansa yana kallon gaban titin kawai ba tare da ya sake cewa komai ba ya yin da Maheer ɗin shi ma ya yi shiru yana ta nazarin abin da zai ce,wanda daga ƙarshe ya kalli driver seat ya ce.

" Take me to Gwarinpa."

"Okay sir."

Abin da drivern ya ce kenan tare da kunna motar ya juya suka kama hanya. Dalilin da yasa bai yi masa musu ba shi ne saboda ya gansa kalar masu kuɗi wanda daga yanayin sa da yanayin dressing ɗinsa kaɗai zai tabbatar maka da cewa shi ɗin yana da kuɗi.

******

Gidan Alhaji Gimba kuwa. Tun tsawon kwanaki uku ake ta yi masa complain daga kamfaninsa cewa ayyuka sun tsaya amma duk ya ɗauka kawai dai Faris wata ƙila yana kan wani uzuri ne na ɗan lokaci, but kiran da Ishaq ya yi masa tun da sassafen nan shi ya tabbatar masa da cewa akwai matsala.

Hankali a matuƙar tashe ya hau kiran wayar Faris amma baya ɗagawa,kusan kira ya fi guda ashirin amma yaƙi ya ɗaga.

Hakan yasa ya baro sashen Maimuna cikin sauri ya fito parlour ya shiga ƙwala kiran Hajiya Salamatu.

Tana fitowa ta kalle shi ta ce.

"Lafiya ka ke ta min wannan kiran haka?"

"Ina Farisu Salamatu?"

Taɓe baki ta yi tace.

"Ni ina na sani! Ba ka kore shi ba..."

Cikin masifa yana wani ɗaga murya ya ce.

"Bana son sharri da munafurci Salamatu! Ni yaushe na kore sa? Cewa na yi ya daina shigo min gida, to saboda rashin hankali sai ya banzarar min da kasuwanci ya yi tafiyarsa? Uban waye yake so ya kula da kamfanin?"

"Ah to? Yanzu dai ni ma ban san a ina yake ba..."

"Wallahy Ƙarya ne? Na rantse da Allah Ƙarya ne wai ki ce ba ki san a ina yake ba. Ɗauko wayarki ki kira shi yanzu a gabana..."

Ciki ta koma ta ɗauko wayar a ranta tana addu'ar Allah yasa daga yau wannan matsalar ta kai ƙarshe ɗan ta ya dawo ko hankalinta zai kwanta.

Tana iso gabansa ta kamo Layin Faris ɗin ta kira nan da nan sai ga shi ya yi picking.

Yana jin sallamar sa ya fisge wayar daga hannun ta ya kara kunnen sa ya ce.

"Yanzu Faris kana ganin ina kiranka baka ɗaga wayata!"

Hankalin Faris ɗin a kwance ya ce.

"miyasa za ka damu da Yaron da ka kora daga gidan ka akan dole sai ya amsa wayarka? Tun yaushe na baro gidan? Baka tashi nema na ba sai yau?"

"Gidan nan na ce ka daina shigowa ni ban kore ka ba. And yanzu da ka bar kamfanin haka uban waye kake so ya ci gaba da gudanar da shi?"

"Ka ɗauko dangin matarka su gaba da gudanar maka da shi."

Daga haka ya katse kiran daga can ɓangarensa. Kallon Hajiya Salamatun ya yi hankalinsa a tashe yace.

"Salamatu Faris ba shi da hankali! Ta ya zai bar mini masana'anta ba kowa? Ki fa faɗa masa cewa ya dawo....kinga..."

Ya faɗa yana mai ƙara kusanto ta sosai ya ci gaba da cewa.

"Sake kiran shi ki ce na ce ya dawo gidan shi ke nan na yarda yaci gaba da zamansa a nan ɗin..."

Maimuna dake tsaye tun ɗazu ta wani zaro ido jin furucinsa ta ce.

"Alhaji wane irin ya dawo cikin gidan nan baligi da shi?"

Wani kallon ya yi mata ya ce.

"Faris fa shi ne komai na kamfanin Maimuna. Idan har ya rushe to ke ma ina tabbatar miki da cewa kin rushe har abada..."

Taɓe baki tayi tana ɗaɗɗaga kafaɗa ta ce.

"Kai dai ne kake ganin kamar dole sai da shi..."

"Na rantse da Allah Maimuna zan zazzabmiki tafi idan baki rufe min baki ba! Ina miki maganar kamfanina kina min shirmen banza."

Muƙut! Haka ta haɗiye wani wahalallen yawu jin furucin da ya fito daga bakinsa wanda ko a mafarki ba ta yi tsammani ba.

Ita ko Hajiya Salamatu wayar ta sake ɗagowa ta kira Faris ɗin ta sanar mai kawai sai ya ce.

"Saka wayar a hands free Mum.."

Hands free ɗin ta danna tana mai kallon fuskar alhajin ya yin da gabanta ya tsananta bugawa domin bata san abin da Faris ɗin zai ce ba.

"Ba zan dawo ba. Ka je ka nemi wanda kake so ya ci gaba da kula maka da kamfanin ka..."

"Faris!"

Ta ambata da sauri, amma kuma kafin ta sake magana har ya tsinke kiran.

******

Sapphire Court Estate, 3rd Avenue, Gwarinpa. Abuja, Nigeria.

Tun da suka isa gate ɗin unguwar hankalin sa a kwance ya sanar musu sunansa da kuma gidan da ya zo, hakan yasa ba ɓata lokaci bayan sun sanar musu aka basu izini ya wuce gidan direct kansa tsaye.

Cike da mamakin ganin sa Matar gidan da ta fito tarbonsa jin shi ne yau ya zo gidan na su ta ce.

"Maheer...Yau kai ne a gidan namu?"

Murmushi ya yi mata tare da mayar da hannun sa ta baya ya sosa bayan kansa yana ɗan murmushi ya ce.

"Wallahy ni ne Aunty Dina..ina wuni? Barka da gida?"

Itama da Murmushin a fuskarta ta juya zuwa ciki tana faɗin. "Lafiya lau Alhamdulillah! barka da zuwa. Shigo ciki..." ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 22*

Cikin mintuna ƙalilan aka jera masa lafiyayyen girki a kan table.

Idan zai iya tunawa rabon sa da girkin gida tun da ya baro ƙasar sa,wanda duk yanda girkin gida yake ko yayane yasan cewa yafi na kasuwa.

And again gidan Dinaratu ba baƙon sa ba ne. Ita ɗin ta kasance Yayar Hamad wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya da ita, amincin da yake tsakanin sa da Hamad da shaƙuwa yasa ahlinsa suka zamto tamkar nasa, musamman lokacin da Maami da Abiyh suka tsaya wurin nema masa aiki a Maritime har ya samu. Hakan yasa suka ji daɗi suke mutunci da su, suka zamto tamkar en uwan na jini. Shi ɗin ne ma bai cika ziyartar dangin Hamad ɗin ba, but shi time to time yakan shiga Oman har gidan su Abiyh idan ya tashi yakan je ya ziyarce su.

Sosai ya ci abincin sannan daga ƙarshe ya fita masallaci ya gabatar da sallar Zuhr ya dawo. Bayan ya dawo ne Yayar ta su ta kalle shi ta ce.

"Ba zan ɓoye maka ba Maheer....na yi mamakin ganin ka."

Murmushi ya yi tare da resting bayansa a jikin kujerar da yake zaune ya ce.

"Ki yar da kewarku na yi. Ina su Arif?..."

Idanunsa ya ɗaura akan rantsatstsen agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa yana faɗin.

"Koda yake na san yanzu suna school..."

Dariya ta yi tana jinjina kan ta tace.

"Su Arif kaɗai ka sani. Ga Ashnan da 4yrs har ta fara zuwa school itama. Rabon ka da gidan nan zai kai 5yrs Maheer..."

Hannayensa ya harɗe wuri ɗaya alamar ban haƙuri yana murmushi ya ce.

"Aunty Dina ayi haƙuri. Daga yau zan gyara in sha Allahu."

"Tau Allah yasa. Miye ya kawo ka Abuja? Aiki ko ziyara? Na dai san baku da wasu 'ƴan uwa a nan..."

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Haka ne, but amma fa akwai dangin mahaifina a nan.."

"Da gaske? But bamu taɓa sani ba."

"Uhm! Ba za ku sani ba gaskiya. Amma akwai yayan mahaifina Alhaji Armaya'u Aliyu. Sannan akwai Last born ɗinsa dake aure a nan Hajiya Sakina."

"Allah sarki! Lallai sanadiyyar su yau gashi mun samu ganin ka. Ziyara ka zo ko wata hidima kuke a familyn na ku?"

Ji ya yi tana neman ta ƙuresa domin ko giya yake sha yasan bai isa ya taka gidan ɗaya daga cikin su ba. Domin Su ɗin ba za su taɓa karɓar sa ba ya sani, and Maami ma ba za ta yafe masa ba idan ya saɓa alƙawarin da ya ɗaukar mata. But har yau har gobe yana jin kewar su a ransa. Duk da cewa rabonsa da su tun yana ƙaramin yaro, har yau yana iya tuna irin kula da soyayyar da suka nuna masa musamman Alhaji Arma da yake ji da shi sosai. 'yan uwansa da yake haɗuwar da su a shafukan sada zumunta yana jin kewar su a ransa wanda shi ma yana fata ace suna tunawa da shi kamar yanda yake tunawa da su.

"Maheer..."

Murmushi ya sake yi mata tare da girgiza kansa ya ce.

"Eh to, kusan haka ɗin zance dai tun da har Allah yasa na zo garin, wato ziyara amma na zo gabatar da wani abin ne kuma daga zaran na kambala in 2days In Sha Allah zan juya na koma Lagos..."

"Eyyah! To Allah ya taimaka ya bada sa'a."

"Amin."

"Amma Hamad kuwa yasan kana nan?"

Jinjina kai ya yi ya ce.

"Yeah...he knows. But amma fa bai san cewa na zo nan. I just want to surprise him..."

Dariya ta yi ta ce.

"Ai kam dai! Ni ma ɗin ai gashi ka bani surprised ɗin."

"Dan Allah idan ba damuwa ina so ki bani mukullin mota zan ɗan fita wani wuri..."

Miƙewa ta yi tana faɗin.

"Ah No...ba wata matsala wallahy bari na kawo maka ka ɗauki wacce ka ke so."

Sama ta haura wanda ya kai kusan 5mint a zaune sannan ta sauko riƙe da Keys a hannun ta suka nufi waje a tare.

A parking lot ta tsaya tare da buɗe tafin hannun ta tana kallon shi ta ce.

"Ka ɗauka daga cikin biyu ɗin nan,...wannan ɗin ta yayanku ce, daman tafiya ya yi but I'm expecting him today..."

Hannu ya miƙa ya ɗauki na wata baƙar mota wacce ke ta wani walwali akan sabon taka yana faɗin.

"kada ki damu zan ɗauki wannan ɗin, na gode sosai."

"Okay...Allah ya tsare."

"Amin."

*******

Dr. Haisam Usaid Residence, Doubeli Extension, Jimeta, Adamawa State, Nigeria.

Tun da suka wayi gari suke ta haɗa kaya domin juyawa zuwa Abuja. Wayewar safiyar yau kiran da Mukarram ya yi wa Wayar Aysha yafi goma, ko kiran wayar Naseer ɗin bai yi ba, domin ganin yake duk laifin sa ne tun da ya ƙyale su su kuma sun kasa yin tunanin cewa ya kamata ace sun dawo haka nan. sai bala'i yake musu akan su tattaro su kayan su hakanan su fito.

Anaam dake zaune gefen trolley ɗinta da ta gama rufewa ne ta kalli Na'ima wacce jikin ta ke sanyaye tun ɗazu ta ce.

"Ni fa Yaa Na'ima na lura sai wani farin ciki kike akan zamu tattara mu barki ke da Dr. Haisam...."

Hawayenda take ƙoƙarin riƙewa ne suka ƙwace mata jin wani zance na Anaam mai ban takaici.

A tare suka haɗa baki wurin faɗin.

"Subhanallah! Na'ima..."

"Ba ku ji abinda Anaam take faɗa ba ne? It make me to feel sad..."

Cike da nadamar ganin yanda Na'imar ke kuka ta ce.

"I'm sorry Yaa Na'ima wasa nake miki...ni kai na nasan zan yi kewar ki sosai."

Ƙarasa zuge zip ɗin handbag ɗinta Aunty Amina ta yi sannan ta miƙe tsaye tana dariya ta ce.

"Uhm! Ai dai kun fi kusa, saboda haka ba ruwanmu a ciki."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull