Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 17

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 17

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 17: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 17. Har suka kambala shiryawa suka fito babu wanda ya sake yin magana…

3,373 words

Har suka kambala shiryawa suka fito babu wanda ya sake yin magana sai da taga za su shiga mota ta sake fashe musu da kuka,hakan yasa Haisam ya koma ciki ya ɗauko mata mayafinta suka tafi Airport ɗin tare da su suka raka su wanda har suka dawo gidan ba ta daina kuka ba, sai da ya yi da ƙyar da rarrashi ya samu ta haƙura.

Suna sauka a Abuja suka ga Anasi ne yazo ɗaukar su zuwa gida. Kallon sa Anaam ta yi itama jiki duk a sanyaye na jin kewar Na'imar ta ce.

"Anasi hala Yaa Mubarak baya ƙasar?"

Cike da girmamawa ya ce.

"Eh ranki ya daɗe...tun jiya suka tafi tare da Mai gida Madu...sannunku da zuwa Hajiya..."

Ya ƙarashe maganar yana mai kallon su Yaa Amina dake bayanta suna magana da juna.

Bayan sun gama gaisawa ne ya saka kayansu a motar sannan ya buɗe suka shiga, sai da suka tsaya jiran Naseer sannan daga ƙarshe ya kira Anasin ya ce su tafi zai zo daga baya.

Suna shiga gidan suka yada zango a main parlour suka hau gaishe-gaishe inda Anaam ta koma gefen Ammie ta rakuɓe jikinta ba tare da ta yi wa kowa magana ba.

Kallon ta Ammie ta yi da murmushi a fuskarta ta ce.

"Anaam..."

Jin sunan ta a bakin Ammie kuwa sai yasa ta fashe mata da kuka.

Hannu Ammien ta saka ta hau bubbuga bayanta tana faɗin.

"Ai daman da ganin fuskar nan a raina na ce tun daga can an sha kuka..."

Dariya suka yi dukkan su sannan Aysha ta ce.

"Ammie shagaɓa dai ce irin ta Auta amma gabaɗaya ba su wani damu ba sai ɗazun nan da zamu fito suka hau kukan gulma...itama Na'imar Haisam na kama hannunta a Airport ɗin ta juya suka koma gida ko Aunty Amina?"

Anaam na jin haka ta miƙe tsam ta nufi ɗakin ta domin ta san tunda su Aunty Aysha suka fara to neman tsokana ne.

Tana shiga ɗakin ta ja wani uban burki da cike da zallar madarar mamaki ta shiga ƙarewa Rabi'atu kalo tun daga sama har ƙasa.

Tabbas Rabi'a ce kwance a gadonta Sanye kuma da tufafinta a jikinta.

"Ke!"

Ta daka mata wata uwar tsawa tana mai ƙara riƙe ƙugunta da uban mamaki ɗauke a allon fuskarta.

Miƙewa Rabin ta yi ta zauna tare da cire Earbud ɗin da ke kunnen ta ta saki wani murmushin mai cike da zallar izgili da renin wayo ta ce.

"Au! Wai Anaam ce? Har kun iso kenan?"

"Uban waye ya baki damar shigo min ɗaki har ki ɗauki kayana ki saka a jikin ki tsabar renin wayo?"

Saukowa ta yi daga gadon tamkar ba ta san abin da ta yi ba, ta hau kallon jikin ta tana dudduba kayan sannan ta sake kallon Anaam ɗin ta ce.

"Wai wannan kayan kike magana? To ai kin san ban zo da shirin zama ba, shi ne kuma Ammie ta ce tun da Aunty Na'ima ta yi aure dan Allah na zauna domin na riƙa deɓe miki kewarta, shi ne aka lallaɓani na tsaya, to kuma ga shi ban zo da kaya ba, shi ne Ammie ta ce na saka kayanki kafin a yi mini sababbi..."

A zuciye ta wani juya ta fice tamkar za ta fashe tsabar baƙin ciki.

Ita kuma Rabi'a faɗawa ta yi kan gadon ta kece da wata irin muguwar dariya. Daman plan ne ta yi wanda tana sane ta aika ta. Tun farko ɗakin Na'ima Ammie ta nuna mata sannan ta ce mata akwai kayan da Na'ima ta bari za ta iya fara amfani da su kafin a yi mata sababbi, shi ne yau tana jin cewa su Anaam sun taso ta sulalo ta zo ɗakin ta saka kayanta sannan ta kwanta a gadonta don kawai ta baƙanta mata rai.

Wayar ta ta ɗauka ta kira Umma tana ta babbaka dariya ta faɗa mata yanda suka kwashe da Anaam ɗin. Bayan sun gama dariyar ne umma ta ce.

"Ai kin min daidai, gwanda da kika yi mata hakanan, ko ba komai dai ran ta ya ɓaci. Sai ka ce ita kaɗai ce 'ya..."

Saurin katse kiran ta yi ta sauko daga kan gadon ta yi waje ta tsaya daga inda take iya hango su ta shiga kallon su.

Anaam kuwa har da hawaye jin wai Abbah ne ya ce za ta ci gaba da zama a gidan, hankalin ta a tashe ta ce.

" Ammie idan haka ne to amma miyasa za'a ce ta shiga ɗakina ta zauna har da saka kayana?"

Cike da neman kare kai Ammie ta ce.

"Ni kuma? A'a ni kam ban ce ta shiga ɗakin ki ba, ɗakin Na'ima nace ta shiga tunda ta tafi sannan akwai sauran kayan ta idan tana so..."

Cikin sauri ta ƙara so parlourn inda ta tarar da su a tsatstsaye kowa fuska ba walwala ganin yanda Anaam ɗin take. Da damuwa ƙarara a fuskarta ta ce.

" Dan Allah Ammie ki yi haƙuri...ina ga ashe ban ji ki da kyau ba ne shiyasa na za ta ɗakin Anaam ɗin kika ce..."

Rai a ɓace Nene ta kalle ta ta ce.

"Kin sani mana! Tun ranar ai a ɗakin Na'ima kike, kuma ɗazu har tambayata kika yi da kika ga ina gyaran ɗakin Anaam ɗin na ce miki ɗakin ta ne..."

Rantse-rantse ta fara har da guntun hawayenta ta hau magiya ganin yanda gabaɗaya su Yaa Amina ke bin ta da wani mugun kallo.

Ganin hakan yasa Ammie ta ce.

" Shi ke nan Nene! Tun da tace bata sani ba a bar shi a haka. Kije ki cire mata kayanta, kuma dan Allah ki tsaya a ɗakin ki kada ki sake shigar mata ɗakinta..."

Kallon Anaam ɗin ta yi kamar da gaske ta ce.

"Ki yi haƙuri ba zan sake ba. Yanzu zan cire miki kayan ki na kawo mik.."

"Don't even try it! Ki je ki yi ta sakawa. I don't need it anymore. Ɗakina kada ki sake shiga bana so!"

Daga haka ta juya ta koma ciki tare da murzawa ƙofar key ta kwanta akan Gado ranta a matuƙar jagule ta shiga tunanin yanda za ta fara rayuwa da Rabi'a. Allah ya sani bata son ta a kusa da ita ko kaɗan bata ma son ganin ta. And again su Ammie sun fi kowa sanin halin da ta shiga ta dalilin ta, amma kuma shi ne za su amince mata akan ta zo gidan ta zauna. Hakan zai yi matuƙar yi mata wahala.

*******

Maimuna.

Tun da Alhaji Gimba ya ji da gaske Faris ya bar masa kamfaninsa gabaɗaya ta rasa gane kansa.

Hakan sai ya yi matuƙar sanya ta a damuwa, and gashi tana gani kullum yanzu yana sashen Hajiya Salamatu wurin bincikarta inda Faris ɗin yake wanda har abincin yanzu wani lokacin a can yake ci.

Sosai ta rasa sukuni da nutsuwar zuciya domin ita sam ba haka take so ba. She want him to be hers alone, and matuƙar suna tare da su damar hakan ba za ta taɓa samuwa ba. And tana so ta mallake komai, tana so ta zamo wata, ko a dangi wani abu ya taso ita ce za'a riƙa yin labarin ta ace tafi kowa.

Abinci ta sa aka kawo mata tun ɗazu, amma har ya yi sanya ta kasa taɓawa. Tsaki take ta ja ranta tun ɗazu. Wayar ta ta ɗauka ta kira Auntyn ta Halira ta fashe da kuka tana faɗin.

"Aunty Alhaji fa ya suɓuce wallahy!"

Daga can ɓangaren Halirar ta ce.

"Kutumar Uba! Mene?"

Ƙara sautin kukan ta ta yi ta ce.

"Wallahy Aunty Halira Alhaji nema yake suɓuce..."

"To ke kina aikin me? Ta ya ki ka bari har haka ta faru?"

"To ni Aunty Ina zan sani? Gabaɗaya indai aka ce miki zance na kuɗi ne to Alhaji Gimba ba ya ji baya gani...sai rashin mutunci yake mini a 'yan kwanakin nan..."

"Kina ji Maimuna? Gobe da sassafe ki yi sakko ki zo...ai wallahy in yasan wata bai san wata ba..to amma fa kada ki bari Inna tasan cewa za ki zo gidana Maimuna (cewa da mahaifiyar su)...."

Cikin farin ciki ta ce.

"In Sha Allahu ba zan faɗa mata ba. Ba zama tasan na fito har na zo gidan ki ba..."

"Tau ya yi. Ki sha kuruminki kin ji ko? Sai mun yi maganin Alhaji na yi miki alƙawarin wannan."

Yanzu kam har da uban murmushinta jin cewa za ta samu maganin matsalarta ta ce.

"Na gode Aunty Halira...da ace bani da ke a duniyar nan ban san ya zan yi ba..."

Dariya Halirar ta yi wanda har tana iya jiyo sautin ta daga can ɓangaren ta ce.

"Ba komai, hakan ai shi ne zumuncin. Idan baka sharewa ɗan uwanka hawaye ba waye zaka share wa? Allah dai ya bamu alheri. Ki gaida gidan."

******

Maheer.

Tun around 5pm yake ta wuraren su Anaam ɗin amma ya rasa yan da zai yi ya shiga unguwar ko yanzu. Ya ɗauka da yazo a mota zai iya shiga idan ya samu wata Idea ɗin, but har kusan 9pm ya kasa taɓuka komai.

Hakan yasa a wannan karon ya ji cewa ya sare. Ya ɗauka abin sauƙi ne da shi amma kuma mai matuƙar wahala ne. Allah ya sani ya so ganin yarinyar nan ya roƙeta gafara amma kuma hakan yaci tura. Ya yi iya ƙoƙarinsa amma kuma ya kasa...ɗazu sai Ƙarya ya yi wa Maamin sa cewa wai wani aikin ne ya biyo ta kan training ɗinda yake yasa suka zo Abuja.

But har yaushe zai zauna yana yi mata ƙarya? How long zai ɗauke shi har ya samu ganin wannan yarinyar? Ko a mota ya ganta ta ya zai fara approaching na ta? Ya riga ya baro kyau tun ranar wanka. Bai san ta yanda zai iya ya ganta ba. Karatun da aka ce za ta fara ma ba tabbas because she supposed to be in class today Kamar yanda Hamad ɗin ya ba shi hint, but ba ta je ba, and ya bincika a Nile ɗin ta hanyar wani mutum wanda ya tabbatar masa da cewa batun karatun ya tsaya domin tace ba ta son Nile ɗin kuma.

Idan zai kwana yana nadama yasan hakan ba zai taɓa canja komai ba, because a wannan Duhun daren ya aikata mummunan kuskuren da baki ba zai iya gyarawa ba, sai dai ya ɗan rage zafi da raɗaɗi idan har ya samu damar magantuwa da shi da ita. Sai dai yau kuma ya sare! Ya sare da zancen cewa wai zai iya haɗuwa da ita.

Ya haƙura da nemanta, zai je ya ci gaba da addu'a, idan har yana da rabon ganin ta watarana zai ganta, idan kuma ba su da rabon haɗuwa tabbas zai bar muhimmin saƙo wanda zai isa zuwa gare ta watarana.

Da wannan ya taka motar a sanyaye ya koma gidan Dinaratu wanda koda ya shiga gidan mijin ya dawo suna zaune a parlour bayan sun kambala cin abinci suna hutawa.

Murmushi ta yi ta ce.

"Abban Arif ka gan shi dai ga shi nan a gabanka don ka tabbatar da gaske nake ba wasa ba..."

Cike da mamaki Abban Arif ɗin ya kalle shi yana murmushi ya ce.

"To ni dai na ce Maheer ɓatan hanya ya yi Dinaratu..."

Dariya suka yi sannan ta jinjina kai ta ce.

"Ni ma dai haka na ce."

Hannu ya bashi suka gaisa sannan ya zauna ya ci abinci. Bayan ya kambala ya miƙe yana ta musu godiya ya ce.

"Ni kam zan koma Mutanen gidan nan..."

Wani kallon Abban Arif ɗin ya yi masa ya ce.

"A daren nan za ka bar gidan nan Maheer?"

"Noo! Kada ka damu, ina zaune a Hotel ne and kuma ma gobe zan koma Lagos..."

Miƙewa ya yi yana kallon Maheer ɗin ya ce.

"Duk da haka dai ya kamata ka kwana a nan, idan yaso goben sai ka wuce..."

"Ba fa wata damuwa wallahy, na gode sosai..."

"Maheer a nan za ka kwana. Shi ke nan shi Hamad da yake zuwa ƙasar ku yana kwana a gidanku bai san ciwon kansa ba ne kenan?"

Zaro ido Maheer ɗin ya yi yana murmushi sannan daga ƙarshe ya girgiza kansa ya ce.

"Nooo...ba haka ba ne kayi haƙuri."

*******

Anaam.

Tunda ta shige ɗaki bata fito ba sai da ta yi sallar Magrib sannan ta fito tare da yin tamkar wani abu bai faru ba.

Kallon ta Ammie ta yi ta ce.

"Tun ɗa zu Yayanki ke son Magana dake amma kin shige kin kulle sai ƙwanƙwasa miki ake kina ji kin yi shiru. Ki yi haƙuri da 'yan uwan ki kin ji? Ya kamata ace kin manta da abin da Rabi'a ta yi miki domin ita ba da wata manufa ta yi hakan ba."

Jinjina kai ta yi a hankali alamar ta ji sannan ta ce.

" Ina Yaa Amina?"

"Ga ta can tana shiri Auwalu zai kai ta gida tun da Mijinta baya nan."

Juyawa ta yi ta koma ciki ta shiryo shaf-shaf sannan ta fito ta iske Aunty Aminar ta ce.

"Yaa Amina na yiwa Anasi magana shi zai kai mu sai na raka ki gidan, idan mun je sai na dawo."

Jakarta ta miƙawa Fatima suka nufi hanya tana faɗin.

"Ok to mu tafi...ai mun gama shiryawa ma tun ɗazu har mun yi sallama da su Aysha..."

"Ina Aunty Ayshar take? Tun da na fito naga ban ganta ba."

"Sun fita tare da Abban Mufid tun ɗazu.."

Ɗan murmusawa Anaam ɗin ta yi sannan ta ce.

"Daman fa Yaa Mukarram kewar Aunty Aysha ce kawai ta dame shi, hakan yasa ya yi ta uzzura mana akan mu dawo haka nan.."

Dariya Amina ta yi ta ce.

"Ba ruwana ni dai."

Koda suka isa parking space ɗin sun tarar da su feruz a motar tare da Farouk suna zaman jiran su. Suna shiga ba ɓata lokaci suka kama hanyar gidan Muhammad ɗin wanda suna yi suna fira har suka isa gidan. Suna shiga harabar gidan suka fito a tare sannan ta yi musu sai da safe suka fito ita da Anasi suka kamo hanyar gida.

Suna shigowa ta hango Mutum tsaye kamar Faris a gaban gidan yana magana a waya.

Gabanta ne ya yanke ya faɗi domin ita duk a zaton ta Gizo ne yake mata ba shi ɗin ba ne.

Sai dai kuma, tana ƙara matsawa tana ƙara hango fuskar sa da kyau, hakan yasa ta ja tunga ta tsaya sannan ta kira Anasi tana kallon direction ɗinda Faris ɗin ke tsaye ta ce.

"Anasi waye wancan?"

Kallon inda take kallo ya yi sannan ya sake kallonta ya ce.

"Faris ne ranki ya daɗe..."

Cikin wani sabon mamakin ta ce.

"Faris! Wane Faris ɗin?"

"Faris dai wanda kika sani na gidan Alhaji Gimba..."

"Miye yake a nan shi kuma?"

"To wallahy ranki ya daɗe shi ne abin da ban sani ba. Amma dai kwana biyu a gidan nan yake zaune..."

Komawa ta yi ta jingina jikin mota ta lumshe idanun ta sosai domin ji ta yi ƙafafuwanta ma sun gaza ɗaukar ta. Yanzu Su Abbah suna sane Faris yake zaune a gidan ko yaya? Su ma su Yaa Muhammad suna sane? Ta ya ya za'a yi Faris ya zo ya zauna a gidan nan?

Hawayenta ta share bayan ta gama duk nazare-nazarenta sannan daga ƙarshe ta kira sunan drivern ta wanda ke tsaye a gefe tun ɗazu ya tsaya zaman jiranta.

Matsowa ya yi kusa da ita jin ta kira sunan shi ya ce.

"Ranki ya daɗe gani..."

"Kasan gidan Yaa Nameer?"

"Ƙwarai kuwa ranki ya daɗe."

Motar ta koma ta zauna kai tsaye tace ya kai ta gidan. Ba ɓata lokaci ya shiga suka kama hanya wanda koda suka isa unguwar dare ya yi sosai.

Bayan ya shiga ya sauke ta ta kalle shi ta ce.

"Koda an tambaye ka kace baka san inda nake ba ka ji ko?"

Da sauri ya jinjina kansa ya ce.

"An gama ranki ya daɗe. Allah ya tashemu lafiya..."

Daga haka ya shiga motar ya juya. Umarnin Anaam shi ne kan gaba da na kowa a gidan, domin ita ce wacce ta sa a ka dawo da shi bakin aiki bayan an sallame shi, saboda haka duk abin da take so ya aikata zai yi kai tsaye ba tare da tsayawa wani tunani ba.

Nameer da matarsa ta tarar a corridor ɗin gidan hankali a tashe jin security sun sanar musu cewa Anaam ce.

Kusan a tare suka kira sunanta ganin cewa da gaske ita ce.

Kukan da take riƙewa ne ya ƙwace mata da gudu ta faɗa jikin Nameer ɗin tana faɗin.

"Yaa Nameer su Abbah sun fi son maƙiyana fiye da ni..."

Cikin tashin hankali matar ta ce.

"Subhanallahy! Anaam wannan wace iriyar magana ce haka?"

Ɗagowa ta yi ta kalle ta ta ce.

"Wallahy Aunty Dina sun fi son su dani..."

Dasƙarewa Maheer ya kusa yi daga inda yake Tsaye akan tsabar shock ɗinda ya ziyarce sa na ganin Anaam a gaban sa tana kiran Dinaratu da Aunty. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 23*

Duk bayanin da take kora musu yana tsaye jikin ƙofar parlourn tun ɗazu yana saurare. Ya rasa dalilin da yasa yake jin a ransa ya cewa ya tsani duk wanda ke neman ya ɓata mata rai. And imagine ace wai iyayenta da kan su amma ba za su iya bata farin cikin da take so ba. Hakan yasa kenan Alhaji Mas'ood ba kawai mutanen waje ba. Hatta iyalansa baya iya basu farin cikin da ya dace da su.

Ganin yanda take ta kuka sai ya ji ransa ya sosu sosai. Hakan yasa ya yi hanyar kitchen ya buɗe fridge ya ɗauko ruwa da glass cup ya zo kai tsaye ya tsaya a gefen kujerar da take zaune ya tsiyaya ya miƙa mata.

Lokaci ɗaya Yaa Nameer ɗin da Aunty Dina suka ɗago kai suka kalle shi kamar yanda Anaam ɗin ta yi.

"I just wanted to help..."

Ya ambata ba tare da ya janye hannun sa daga miƙa mata ruwan ba.

Jinjina kai Aunty Dina ta yi tace.

"Kada ki damu Anaam, he's my brother...."

Anaam na jin hakan sai ta karɓi ruwan ta kurɓa sau biyu sai ta ajiye a ƙasa.

Cikin sigar lallashi Nameer ya ce.

"Ki yi haƙuri Anaam, idan su Gwaggo (cewa da Ammie) suka gano cewa bakya cikin gidan kuma basu san inda kika je ba, za su shiga tashin hankali..."

Girgiza kai ta yi still da ruwan hawaye a idanunta ta ce.

"Ya Nameer ni fa ba zan koma gidan ba, and idan ka ce zaka sanar musu wallhy zan gudu daga nan...."

"Please allow her to stay, and don't tell her parent Kamar Yanda ta roƙeka..."

"But Maheer za su shiga damuwa, and idan suka gano cewa tana gidan nan daga daga miye za su ɗauke ni?"

"Farin cikin ta da kwanciyar hankalinta is the top priority Oga Nameer....and idan har hankalinta ya kwanta ta samu nutsuwa komai mai sauƙi ne. Basa so hankalin su ya tashi suka kawo mutanen da ba ta so a gidan?..."

Agogon hannunsa ya kalla sannan ya sake kallon su yana jinjina kansa ya ce.

" Getting to 12am now...please ku barta ta huta tukun."

Miƙewa Dina tayi ta ja hannun Anaam ɗin ba tare da kowa ya sake cewa komai ba suka haura sama ta buɗe mata wani ɗaki suka shiga. Komai a tsabtace yake gwanin sha'awa, wardrobe dake gefe ta buɗe ta ɗauko bedsheet ta shimfiɗa akan gadon sannan ta fita ta ɗauko mata sababbin sleeping dress ta bata ta ce idan tana so ta shiga ta yi wanka.

Toilet ɗin ta shige ta yo alwala ta fito ta gabatar da sallar Isha sannan ta sauya kayan jikinta ta haura gadon ta kwanta ta yi lamo tana nazarin kalaman Maheer. Ta ya za'a yi ace mutumin da ya ga hawayenta lokaci guda ya iya fahimtar damuwar ta amma ace su Abbah su kasa hakan? Tabbas da ace sun damu da farin cikin ta da basu kawo Faris da Rabi'a ba a cikin gidan nan ba. Ita yaushe tace musu tana da buƙatar wata wacce za ta ɗebe mata kewar Na'ima?

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull