Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 18
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 18: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 18. Ta jima a gadon idan ta juya nan ta juya nan abin duniya duk ya…
3,365 words
Ta jima a gadon idan ta juya nan ta juya nan abin duniya duk ya ishe ta. Ta ɗauka cewa dawowa nan ɗin da suka yi zai sa ta manta da bayan ta sannan ta gina sabuwar rayuwa, but ta ya ya za'a ce su Ammie su ne suke gayyota mata sabuwar matsalar har cikin gida? Komai sai su ce haƙuri haƙuri, but a rayuwar nan akwai gaɓar da idan kace za ka yi haƙuri to tabbas shi ne zai yi ajalinka.
Maheer kuwa, ya jima a rumfar shan iskan gidan yana ta nazari da al'ajabin wannan al'amari. Ko a mafarki aka ce mi shi zai ganta gidan mutanen da ya sani tabbas zai Ƙaryata. But sai gashi unfortunately ba zato ba tsammani ya tsince ta tsaye a gaban shi, sai dai a yanayin da ya same ta ya yi matuƙar baƙanta masa zuciya.
Why is she in pain always? Last ganin da ya yi mata bata cikin yanayi mai daɗi and again yau ma ga shi cikin yanayin damuwa da ƙunci ya risketa. Idan har zai so mutuwar sa to zai ƙaunaci ganin kukanta. Har cikin ƙahon zuciyar sa yake jin kukanta idan tana yin sa wanda hakan ya samo asali ne tun a daren da suka shiga gidan su. Idan tana kuka yana jin sa har cikin kansa. A irin wannan yanayin da take ciki taya ya zai iya confronting ɗin ta da wani zancen neman yafiya? Hakan ba zai faru ba a yanxu, but tun da har Allah yasa a nan take,he will wait for the right time ɗinda ya kamata ya yi magana da ita. But a yanzu kam tana buƙatar space.
********
Hajiya Nasmah ce tsaye a jikin wardrobe ɗin Alhaji Galadima tana jera masa kayan wankin sa da aka kambala wankewa da gogewa.
Sai da ta kambala gyara su tsab sannan ta rufe ta waigo ta kalli inda yake zaune a gefen gadonsa yana duba waya da 'ƴar damuwa ta ce.
"Alhaji kana ganin zaman Faris a gidan nan ba zai ƙara janyo wata wutar matsalar ba tsakanin ka da Alhaji Gimba? Ka fa san halin sa sarai ƙaramin abu sai ya mayar da shi babba. Gabaɗaya hankali na ya kasa kwanciya..."
Ajiye wayar ya yi a gefe ya kalle ta na ɗan lokaci sannan ya jinjina kai ya ce.
" To ai naga Faris ba yaro ba ne. Don ya zo gidan nan ya zauna bai zama wani laifi ba..."
"Duk da haka Alhaji...sau nawa kana yi wa iyalinsa abun arziki amma daga baya ya dawo ya na ganin laifin ka?"
"Na kira Ridwan duk da cewa baya ƙasar mun tattauna, shi ma yace na bar sa ya zauna a nan ɗin tunda ya nema, kada kuma ya wuce inda za'a dawo daga baya ana dana sani..."
Cikin rashin ga suwa da bayanin sa ta girgiza kai ta ce.
"Ni dai duk da haka ina gudun abin da zai je ya dawo..."
A hankali wayar ta ta shiga ɓurarin neman agaji sanadiyyar kiranta da akayi.
Hannu ta miƙa ta ɗauko wayar daga kan ƙaramin glass table dake gefe ta amsa kiran tare da ɗora ta a gefen kunnen ta ta ce.
" Nene lafiya kuwa?"
Hankalin Nenen a tashe daga can ɓangaren ta ce.
"Hajiya ba lafiya! Maryam ba ta dawo gidan nan ba. Na ɗauka tana gidan Amina,amma na kira tace ta dawo, kuma na binciki Anas ya ce ya dawo da ita gidan nan shi bai san inda ta je ba..."
A ruɗe Ammie ta ce.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Miye kike cewa Nene? Anaam ɗin ce ba'a san a ina take ba?"
Kashe wayar ta yi ta ci gaba da kallon Alhajin wanda shi ma lokaci ɗaya ya zabura ya miƙe yana faɗin.
"Tun ɗazu fa nace miki ina neman ta kika ce ta je raka matar Madu..."
"Wallahy Alhaji ni dai na san su Amina taje rakawa gida..."
Bai tanka ta ba har suka fito harabar gidan inda suka tarar da su Nene har da Rabi'a sun tsatstsaya cirko-cirko suna jimami.
Wani kallon Alhaji Mas'ood ya jefawa Anasi ya ce.
"Anas Ina Maryam?"
Hankalinsa a kwance ya ce.
"Alhaji ni ne wanda na kai su gidan Yallaɓai Madu, bayan mun ajiye su kuma muka dawo sai naga sun bar kayansu a motar shi ne naje na kai musu amma ni ban san inda take ba."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Mun shiga ukunmu shi ke nan an sace Anaam tana can tana ganin wahala..."
Cewar Rabi'a tana mai ɗora hannu a kai ta rusa ihu kamar da gaske. Wata uwar tsawar tsawar ce Abbah ya doka mata domin kalaman ta ba ƙaramin ƙara ɓata masa rai suka yi ba ya ce.
"Ke wace irin shashasha ce? Waye ya faɗa miki cewa sace ta akayi?"
"Mahaukaciya ce ai! Wawiya kawai! Fatan sharrin da fatan a sace ta kike ko? To sharrin da kike kira mata a kan ki zai ƙare..."
Da sauri Ammie ta riƙo hannun Mukarram ɗin ganin yanda ya wani yi kan Rabi'ar yana shirin kai mata duka ta ce.
"Mukarram please ka saurara mana dan Allah!"
Wayar shi ya ciro ya koma gefe yana ta kiran waya wanda gabaɗayansu ba su san ko da waye yake yin waya ba.
Su ma dai a nan suka ci gaba da kiran wayar su Amina da sauran dangin su dake nan Abujar amma ko'ina suka kira sai ace ba ta je ba har gidan Nameer wanda ƙiri-ƙiri ya ce bata gidan amma ba don ransa ya so ba.
Ganin yanda Hajiya Nasmah ke ta rusa uban kuka yasa Alhaji Mas'ood ya tako ya matso inda take tsaye a sanyaye ya ce.
"In Sha Allahu a duk inda take tana cikin amincin Ubangiji..."
"Amma Alhaji ina Anaam za ta tafi cikin daren nan? Kana ganin lafiya ƙalau za'a neme ta a rasa haka kawai?"
Ganin suka yi Mukarram ya je da kanshi ya buɗe gate sai ga jami'an tsaro sun shigo cikin gidan mota guda.
Gefen da Faris ke tsaye ana jajen dashi tun ɗazu ya nuna musu kai tsaye ya ce.
"Arrest him! Kuma kar ku saurara masa har sai ya faɗa muku inda ya kai ta..."
"Mukarram...miye haka? Miye haka na ce?....officer please wait..."
Cewar Alhaji Mas'ood yana mai nufar inda Faris ɗin yake, ganin da gaske neman suke su kama shi kamar yanda Mukarram ya umurce su.
Shi ma Mukarram ɗin matsawa ya yi yana faɗin.
"Alaji ka bar su su tafi da shi domin ko tantama babu shi ne wanda ya ɗauke ta. Tun da Anaam take ba taɓa tunanin barin gida ba, amma yana shigowa gidan nan gashi an neme ta an rasa..."
Girgiza kai Alhaji Mas'ood ya yi ya ce.
"Wannan ba hujja ba ce kace shi ne ya ɗauke ta..."
"Kada ka ce za ka yarda da wannan mai fuska biyun Alaji! Dole za'a kama shi kuma dole sai ya fito da ita."
Cike da zallar mamaki Faris ya kalli Mukarram wanda ke ta ɗaga jijiyoyin wuya yana bala'i ya ce.
"Kai ka tabbatar cewa ni ne na sace ta?"
Mukarram ɗin na yi masa wani kallo ya ce.
"I'm 100% sure! Kai ne ka sace ta saboda an hanaka ita a karo na biyu."
Wani murmushin gefen baki Faris ɗin ya yi sannan ya girgiza kansa yace.
"Daman kai kullum a ruɗe kake. Baka taɓa bari ayi abu cikin nutsuwa sai kasan yanda ka yi ka kawo rikicin..."
"Abin da za ka ce kenan? Na ce abin da za ka ce kenan? To bari na nuna maka ƙarshen ruɗewa..."
Mukarram ɗin ya faɗa yana mai kama kwalar rigar sa.
Rikici sosai ya ɓarke a tsakanin su inda jami'an tsaron da ya kira suka tattara suka wuce ofishin su da su.
Har gari ya waye babu mutum ɗaya da ya samu bacci a gidan, gabaɗaya hankalin kowa a tashe yake har su Muhammad dake can wurin hulɗar kasuwancin su, musamman wannan rikicin da Mukarram ya sake jangalo musu na ɗora laifin ɓatan Anaam akan Faris, tabbas idan Alhaji Gimba ya ji to ba lafiya kuma.
Gari na fara yin haske Alhaji Mas'ood ya shirya ya tafi wurin su Faris ɗin domin ya samu ya shawo kan matsalar kafin ta girmama. Sannan kuma ya saka binciken neman Anaam kamar yanda suka tsara da Hajiya Nasmah.
******
Gefen Anaam kuwa ta jima tana baccin wanda ta koma bayan ta kambala sallar Asuba, sai da kusan ƙarfe goma da rabi ta fito Sanye da kayan baccin da ta kwana da su daren jiya. Tana leƙowa suka yi ido biyu da Maheer wanda ke zaune a dinning area da abinci kari a gaban sa, sai Aunty Dina dake gefensa.
Saurin ɗauke kanta tayi kamar yanda shi ma ya yi bayan sun haɗa idon a ba za ta.
Murmushi Dina ta yi tana kallonta ta ce.
"Anaam...kin fito?"
Ƙarasowa ta yi ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun ta ce.
"Uhm! Ina kwana Aunty Dina?"
"Lafiya lau Anaam...fuskar dai kam, yanayin ta ya nuna rashin bacci mai daɗi. Please ki kwantar da hankalin ki kinji ko, in sha Allahu komai zai yi daidai."
Tun da ta zauna bai sake ɗago ido ya kalle ta ba, but yana ganin ta haɗa Tea ta zuba ruwan da yake flask ta ɗaga cup ɗin zuwa bakinta ya yi saurin tura mata wanda yake gaban sa yace.
" Wannan yana da zafi sosai...zai iya ƙona miki bakin ki, but za ki iya shan wannan."
Lokaci ɗaya suka kalle shi ita da Aunty Dina. Ganin hakan yasa ya miƙe yana faɗin.
"Ni zan tafi. Na gode sosai."
Miƙewa Aunty Dina ɗin ta yi ta biyo shi tana faɗin.
"Driver yana jiran ka sai ya sauke ka a Airport ɗin."
"Na gode sosai, amma sai naje hotel ɗin da na sauka na ɗauki kayana daga nan sai na wuce."
Jinjina kai ta yi tana murmushi ta ce.
"Ba damuwa Maheer,mun gode sosai da ziyara, Allah ya bar zumunci."
Har ya buɗe motar zai shiga sai kuma ya juyo ya kalleta ya ce.
"Aunty Dina...dan Allah ina neman wata alfarma."
"Faɗi kanka tsaye."
Ta faɗa tana mai jinjina masa kanta.
"Dan Allah kada ki ce wa yarinyar komai dangane da ni...ahm! Ina nufin kada ki bata labari na..."
Cikin rashin fahimta ta ce.
"Miyasa haka? Amma ai na faɗa mata cewa kai ɗin ƙanina ne."
"Eh, mu bar shi a haka."
"Mi yasa?"
"Ina jiran lokacin da ya dace ne."
Kafaɗa ta ɗaga alamar ba damuwa ta ce.
"Okay! Allah ya nuna mana da alheri."
"Amin. And again...dan Allah idan ba ta so ta koma gidansu kada ku takura ta..."
"Maheer ni ɗin fa kawai matar ɗan uwanta ce. Ban isa na shiga tsakanin hukuncin da suka yanke ba..."
Tamkar wanda zai fashe da kuka ya ƙara saukar da muryarsa ya ce.
"Za ki iya mana...ciwon mace fa akace na mace ne. Dan Allah ki yi min alƙawarin wannan Aunty Dina. Ba laifi ba ne idan kuka sanar da iyayenta cewa tana nan domin hankalin su ya kwanta, amma idan bata so ta koma don Allah ku barta ta yi zaman ta a nan ɗin...ki duba halin da ta shiga tun daren jiya, ko baccin kirki bata samu ta yi ba. Ya kamata ace an kula da ita yanda ya kamata..."
Shiru ta yi na ɗan lokaci tana digesting maganganun nasa tare da ƙura masa ido na tsawon lokaci, sannan daga ƙarshe ta jinjina masa kanta tana murmushi ta ce.
"Shi ke nan Maheer...in sha Allahu I will try my best."
"Na gode da fahimta. Sai an jima."
"Allah ya tsare yasa a sauka lafiya." ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*PAGE 24*
Koda Maimuna ta gama shiryawa ta fito har Alhaji Gimba ya bar gidan ba tare da ta sani ba.
Har sashen Hajiya Salamatu ta tarar da ita cike da izgili da renin wayau ta wani kalleta tana wani tauna cingum riƙe da mayafinta a hannun ta tace.
"Salamatu Ina Alhaji na?"
Tsaye Hajiya Salamatu ta miƙe daga zaunen da take ta kalleta tana girgiza kai ta ce.
"Wai ke Maimuna miyasa baki da kunya ne? Wallahy a haife na haife ki ke kin sani har wacce ta fiki ma. Bai kyautu ace kina biye son zuciyar ki kina mini rashin kunya ba..."
Wani wuwwurga ido ta yi tana taɓe baki tace.
"Dallah malama ni ki shiga ki kirani min mijina ina son Magana da shi."
Girgiza kai Hajiya Salamatun ta yi tana faɗin.
"Alhaji baya nan. Allah ubangiji ya shirye ki...."
Wani Uban tsaki ta buga sannan ta wani kalleta sama da ƙasa ta yi ƙwafa ta wuce.
Tun a gidan take kiran wayar shi amma tana ringing baya ɗagawa, mamaki ne da al'ajabi suka kamata ganin wai yau Alhaji Gimba ya saka ƙafa ya fita ba tare da sanin ta ba, kuma tana kiran wayarsa amma baya ɗagawa.
Koda ta shiga gidan Halirar da guntun hawaye a idon ta. Halira dake zaune bakin madafar abinci tana rabawa yara abin kari ta kalleta da damuwa a fuskar ta ta ce.
"Ki daina ma wani ɓata ranki Maimuna, in dai Alhaji Gimba ne an gama da matsalar shi in sha Allahu..."
Murya a karye ta ce.
"Aunty Halira wai yau koda na tashi baya gidan, and ina ta kiran shi tun ɗazu yaƙi ya yi picking..."
"Zai shigo hannu bada jimawa ba. Share hawayen ki kawai ki jira ni."
Parlourn ta ta shiga ta zauna akan kujerun da naggama ragargajewa wanda ba komai sai ƙashin katako da yagaggen ƙyallen kujerun ta samu ɗaya ta zauna ba dan zaman ya yi mata daɗi ba.
Mita ta fara tana faɗin.
" Wai ashe har yanzu ba ki canja kujerun nan ba aunty Halira...idan mutum ya zauna duk sai ya ji shi a takure ba daɗi."
Washe haƙora ta yi ta shigo da kwano riƙe a hannun ta ta zauna a ƙasan simintin da ya farfashe tsakiyar parlourn ta ce.
"Da fa kika bani kuɗin nan na ce miki na tafi siyen kujerun aka ce sai na ci ko dubu ashirin da huɗu, na yi ta jira baki bani ba ni ko kin san ga mai iyali, siyo wancan karɓo wannan wallahy a haka suka tafi yanzu ba su fi dubu talatin ba..."
Cike da baƙin ciki ta dafe ƙirji tana mai jin mamakinta ta ce.
" Yanzu Aunty kina nufin dubu ɗari da ashirin da na baki kin nakasa su a banza kenan?"
" To tsakani da Allah Maimuna dubu ɗari da ashirin ƙwara nawa ce a wurin mai iyali?"
Cike da masifa ta ce.
"Amma dai Aunty wallhy tallahy baki kyauta ba! Saboda ki canja kujerun nan na baki kuɗin nan, sannan bayan su sau nawa ina turo miki da kuɗaɗe?"
Cike da borin kunya ta rufe ta da masifa tana faɗin.
"To Maimuna tun da kin auri mai kuɗi kin yi kuɗi ai sai ki yi ta yi mini gori! Auren naki dududu yaushe ki ka yi? Nawa ma kika bani daga auren naki zuwa yau ballantana har ki tsaya yi mini gori bayan kin san dani aka yi ta faɗi tashi wurin ganin kin samu alhajin...."
Hannu ta ɗaga mata alamar ta dakata ta ce.
" Ni fa Aunty ba gori nake miki ba wannan maganar gaskiya ce! Kuma ma ai mai bani kuɗin ya daina bani sai ki je ki ci kuma."
Daga haka ta koma cikin kujerar da ta gama yin rame ta zauna tare da naɗiɗiye ƙafafunta ta ciro wayar ta taci gaba da danne-dannenta babu wanda ya sake yi wa wani magana har Auntyn ta kambala cin abincin ta tashi tayi gurmuɗe ta shirya ta fito tana faɗin.
"Ta shi muje..."
Kallon ta Maimunar ta yi ta ce.
"Ina zamu?"
"Wurin samo miki maganin matsalar ki mana."
Cikin rashin fahimtar zancen na ta ta ce.
"Ban gane ba. Ina kenan?"
Ƙugu Aunty Halira ta kama ta riƙe ta wani kalli Maimunar a sheƙe ta ce.
"Au! Daman kin ɗauka a banza a wofi kika samu Alaji Gimban? To wallahy idan ma mafarki kike ki farka domin dani da Ƙawata Dijen Lawai muka shiga muka fita har yasa ki ka ga kina abin da ki ka ga dama a gidan Alhaji Gimban sai abinda kika ce. Kuma yanzu ma idan har kina so ya dawo yanda yake ada to sai kin zuba kuɗi mun tafi wurin boka sann..."
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Maimunar ta ambata tana mai miƙewa tsaye cike da tashin hankali da ya bayyana ƙarara akan fuskar ta.
"Miye wani abin Innalillahi? A banza aka ce miki za ki same shi ne?"
"Uh uhm fa Aunty Halira! Wanda fa yaje wurin boka sallar sa ta kwana arba'in Allah ba zai karɓa ba..."
"To a kan ki aka fara ne? Kuma ma ai daga baya sai ki tuba..."
Cikin jin dai bata gane ba a ranta ta ce.
"kai! A'a ni dai gaskiya Aunty Halira..."
"Ai kuwa na rantse da Allah ba jimawa za ki dawo gida ki ci gaba da zaman baƙin ciki da gabzar tuwon masara miyar kuka don ubanki..."
Jakarta ta warta tana girgiza kai tayi waje tana faɗin.
"Gaskiya ni dai a'a Aunty Halira..."
Wajen ta biyo ta da gudu tana faɗin.
"To na rantse da Allah kada ki yarda ki ce za ki je ki faɗawa su Inna wagga maganar."
Ganin ta kusa fita bata tsaya ta amsa ba yasa ta ƙara ɗaga murya.
"Maimuna!! Maimuna!!..."
Waigowa ta yi ta kalleta ta ce.
"ke ma kin san ba zan faɗa musu ba Aunty Halira, amma sai kuma kin san ba abu ne mai kyau ba."
Jinjina kai ta yi tare da yin ƙwafa ta ce.
"Za ki ci ubanki Maimuna...wallahy sai kin gane shayi ruwa ne."
********
Wuni sukutum suka kwashe a central police station dake Garki Area ana ta abu ɗaya.
Duk inda ya kamata a nemo Anaam a wannan yinin an bincika amma babu labari, hatta Anasi da yake shi ne drivern ta kuma shi ne ya ajiye ta na ƙarshe sai da Mukarram ya saka aka kamo shi a rufe.
Koda Muhammad ya iso still bai goyi bayan Mukarram ba domin shi a ganin shi ya yi gaggawa wurin tuhumar Faris ɗin, idan har yana da ƙudurin ya sace ta ba zai zo gidansu ya zauna ba kuma har ya kwantar da kai yana roƙon a ba shi aurenta.
Duk ƙoƙarin Alhaji Mas'ood wurin ganin an samu an sasanta an saki Faris baki alaikum hakan bai samu ba, domin kuwa suna nan kwatsam sai ga Alhaji Gimba ya shigo afufujan wanda hatta hular kansa riƙe take a hannunsa tamkar wanda aka koro.
Yana shigowa kai tsaye ya isa wurin Alhaji Mas'ood ya cakumi wuyan babbar rigar sa yana faɗin.
"Wallahy tallahy ba zan yarda ba! Ba zan taɓa bari a raina ni ba, ni mutum ko ya yi arzikin ɗan ƙaruna Ƙarya yake yace zai ja dani kuma ba zuba ido ina kallon sa....ni za'a kama wa yaro a zo a rufe shi kamar ɓarawo? Saboda yarinya ta ɓace sai ace shi ne wanda ya sace ta? Yarinyar da ma bata da wata sauran daraja za'a kama min yaro saboda ita?... "
Da sauri suka yo kansu har da police ɗin wanda da ƙyar suka yi nasarar ɓanɓare hannunsa daga wuyan Alhaji Mas'ood ɗin.
Wani kallon Mukarram ya yi masa mai alamar gargaɗi ya ce.
" Wallahi tallahy ka ci arzikin a gaban hukuma muke...na rantse da Allah da kayi dana sanin waɗannan maganganun da ka yi domin tsab zan baje ka a ƙasa..."
"Allah marar mutunci!!!"
Cewar Alhaji Gimba yana mai matsawa inda Mukarram ɗin yake yaci gaba da faɗin.
"Ko yanzu ma ai zaka iya! Go ahead....gani baje ni don girman Allah..."
"Hey! Ya kamata fa kusan a inda kuke! Idan ba haka ba wallahy duk zamu yi maganin ku tunda har naga alamar hali na ƙananun mutane a tare daku..."
D.O.P ɗin ya faɗa yana mai shiga tsakiyar su ganin kamar da gaske nema suke su buɗa.
"Ya kamata ace kun tsaya anbi abun nan yanda ya kamata har a samu a warware wannan matsalar..."