Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 19
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 19: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 19. "Wace matsalar kenan za'a warware D.P.O? An riƙe min ɗa ba bisa…
3,355 words
"Wace matsalar kenan za'a warware D.P.O? An riƙe min ɗa ba bisa ƙa'ida ba sannan ka ce za'a warware matsala? Wallahy tallahy na rantse da Allah kotu ce za ta raba ni da su."
Sai yanzu Alhaji Mas'ood ya kalle shi ya ce.
"Alhaji Gimba! Kai ma kasan har abada ba zan iya cutar da Faris ba, ko kuma na bari ina gani a cutar da shi. Bincike ne kawai ake kuma daga zaran an kambala bincike an same shi ba shi da laifin komai dole a sake shi...."
"Hmm! Wallahy tallahy sai mun yi shari'a dani da kai Alhaji Mas'ood kuma sai an bi wa ɗana haƙƙkinsa..."
A zafafe Mukarram ya ƙara yowar gaba yana faɗin.
"Ɗan ka? Wane ɗan? Ɗan da ka bari a faifan duniya yana walagigi ka kore shi daga gidan ka har kana da bakin cewa wai za'a bi masa haƙƙi? Ka roƙi Allah cewa ba shi da hannu a ɓatan Maryam Alhaji Gimba..."
"Wai Mukarram miyasa baka jin magana ne ni kam? Dan Allah dan girman Allah ka barmu muji da abin da yake damun mu! Idan kuma ba za ka saurara ba you can silently walk out please I abeg you..."
Shigowar Nameer ita ce ta ja hankalin su suka zuba ido suna kallon sa. A yanxu duk wani ɗan uwa da za su gani ko su ji ya bugo waya ba su da wani buri da fatan da ya wuce ace yau ga labarin Anaam an ji a ina take.
Mubarak ne ya yi ƙarfin halin cewa.
"Yaa Nameer ko ka jiyo labarin Anaam ɗin ne ka ji a ina take?"
Jinjina kai ya yi jiki a sanyaye yana mai kallon fusokin su ya ce.
"Anaam tana gidana tun a daren jiya..."
"What??"
Duk suka amsa da ƙarfi suna masu ƙura masa ido tamkar za su haɗiye shi tsabar son jin sauran bayani.
A hankali Alhaji Mas'ood ya ce.
"Da gaske kake Nameer Maryam tana gidanka?"
"Ƙwarai kuwa Alhaji! Ina mai neman afuwar ku baki ɗaya. Nima ina zaune misalin sha ɗaya na dare saura ta shigo gidan...."
"Amma Nameer kasan da hakan ka bar mu muke ta shan wahalar nemanta saboda rashin adalci..."
"Ba haka bane Yaya Muhammad. Da na ce mata dole na sanar muku sai tace idan na kuskura na faɗa muku cewa tana gidana to za ta gudu kuma ba za'a san inda take ba..."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! To miye ya yi zafi haka?"
Cewar Mukarram yana girgiza kansa tsabar mamaki.
Nameer ya ce.
"Saboda mutanen da kuka ajiye a gidan ne hakan bai yi mata daɗi ba. Please ya kamata ku duba..."
Tuni aka fito da Faris da kuma Anasi waɗanda ke kulle a cell tun daren jiya.
Ran Alhaji Gimba ba ƙaramin ɓaci ya yi ba ganin yanda aka fito da Faris kamar wani ɓarawo alhali ba shi da hannu a ciki.
Suna gama cika takarda ya karɓi kayan Faris ɗin da hannunsa sannan ya kalli inda su Alhaji Mas'ood ɗin ke tsaye ya wani jinjina kansa cike da baƙin ciki ya ce.
"Wallhy tallahy ba zan manta ba, kuma ba zan yafe ba Mas'ood Galadima ka saurari martani..."
Daga haka suka kama hanya suka wuce a tare. Har suka shiga mota Faris bai iya ɗaga ido ya kalli mahaifin nasa ba. Har yanxu a ransa bai ga laifin Alhaji Mas'ood ba sai dai laifin Mukarram amma kuma yanzu ko ya faɗa masa ba zai yarda ba, saboda haka gwanda kawai ya zuba masa ido ga duk abin da ya yi niyyar aiwatar wa.
Muhammad kuwa, kallon Mukarram ya yi cike da takaici ya ce.
"Shin yanzu hakan ya yi maka daɗi a rai? Ya yi maka daɗi na ce Mukarram? Ko da yaushe baka taɓa yin tunani mai kyau, and idan aka yi maka gyara sai ka ga kamar kafi kowa sanin ya kamata...a duk lokacin da ka yi wata haukar to ka sani mutunci mahaifinka da na en uwanka ka ke zubarwa!"
******
Maheer
A daren da ya isa ne Hamad ya zo gidan da aka tanadar masa daga kamfanin su ya same shi zaune yana cin abinci.
Lokaci mai tsawo ya share yana kallon Hamad ɗin ba tare da ya furta ko kalma ɗaya ba.
Ganin hakan yasa Hamad ɗin miƙa hannu ya ɗauki cup ya tsiyaya lemu yana faɗin.
"Idan ma maita ka ɗauko a wannan karon kurwata kur!"
Wani murmushin gefen baki ya yi sannan ya lumshe idanun sa ya buɗe yana mai ƙara jin Hamad ɗin har cikin ransa ya ce.
"Thank you! Thank you so much."
"sai wata godiya kake min...did you met with the girl?"
"yeah..."
Wani murmushin kama rainawa kan ka hankali Hamad ɗin ya yi yana mai ci gaba da kallon fuskar sa yace.
"You are joking!"
"Da gaske nake maka."
Ƙara gyara zaman sa ya yi da kyau yana mai fuskantar sa yanda ya kamata ya ce.
"To ka roƙe ta ɗin?"
"No...not yet. I'm waiting for the right time."
"Alright....wish you all the best."
Kiran Maamin sa da ya yi picking shi ya katse musu firar ya kara wayar a kunnensa ya ce.
"Halo Maami..."
"Maheer ya kake?"
"Lafiya lau Maami, ya aiki? ya asibitin"
"All is well Maheer. Ya naka aikin?"
"Lafiya ƙalau Maami....i miss you."
"I miss you too Dear..Allah ya taimaka ya bada sa'a."
"Amin Maami..."
"Ina Hamad? Ko baku samu haɗuwa ba yau?"
Kallon inda Hamad ɗin yake zaune ya yi ya ce.
"Ai a wuri ɗaya muke Maami ko kin manta ne? Ga shi nan ya zo yana cinye min abinci...tuzurun banza haka kawai ya ƙi ya yi aure."
Murmushi kawai ta yi ta ce.
"Allah ya baku na gari masu albarka. Yaushe za ka zo?"
"In sha Allah zuwa ƙarshen month ɗin nan zan zo na ganki."
"To Allah ya yarda. Sai da safe, ka kula da kanka."
"In sha Allah Maami. Allah ya bamu alheri. I love you Maami."
Miƙewa Hamad ya yi yana faɗin.
"Na so jin yanda ka yi ka haɗu da Maryam, but...tun da har baka yi niyyar sanar min ba, idan lokaci ya yi zan sani."
"Ɗan baƙin ciki ai nasan ba haka kaso ba. So ka yi a kama ni ko ba haka ba?"
Cewar Maheer ɗin yana wani rausayar da kai gefe guda.
"To dama ai duk wanda bai ji bari ba, ai dole zai ji hoho watarana. Ni Maami kawai nake tausayi a duk lokacin da na hango katoɓarar da kake shirin aikatawa...."
"Hamad! get out..."
"Noo....please don't be angry...ni gaskiya kawai nake faɗa maka..."
"Please get out." Ware hannayensa ya yi tare da ɗaga kafaɗa ya ce. "Okayy ooo! Have a nice dream Maheer. Sai mun haɗu a station gobe idan Allah ya yarda." Da harara ya bishi har ya ɓacewa ganin sa sannan daga ƙarshe ya miƙe ya bar abincin nan ya yi shigewarsa. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EuUnKg7IhONLRHaPjgFgsb
*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*PAGE 25*
Sai da ya kambala sauraren shawarwarin kowa sannan ya buɗe baki a hankali cikin rashin hayaniya kamar ko yaushe ya nisa ya ce.
"Duk na ji maganganun ku...musamman kai Madu da kace farin cikin ta yana gaba da komai. Yes! Farin cikin Maryam a gareni yana gaba da komai, and ku shaida ne ina yin duk abin da ya kamata domin naga ta samu farin cikin da take buƙata. Har baro garina na yi...garin da shi ne tushena shi ne asali na, amma haka na haƙura na baro don kawai ta samu farin ciki. Saboda haka a wannan gaɓar...ba zan kori Rabi'atu daga gidan nan ba wai don kawai ita bata son zamanta..."
"Amma Alaji..."
Saurin ɗaga masa hannu ya yi alamar ya dakata ya ce.
"Ya isa Mukarram! Kun gama naku, Saboda haka ya kamata ku saurare ni. Idan har nuna son kai shi ne ɗabi'arku da rashin ɗaukar zumunci da muhimmanci ni bana daga cikin ku. Alhaji Salisu da ni uwa ɗaya uba ɗaya muke idan kun manta in tuna muku, yaran sa da ku ni duk ɗaya kuke a wurina babu bambanci. Faris zai iya barin gidannan ko shi idan yaso amma ba don wai ni na kore sa ba, haka ma Rabi'atu matuƙar ba ita ta so tafiya ba har abada ba zan ce ta tafi ba. Da suke zaune a gidan ai ba a kanta suke ba. Yanda muke ƙoƙari muna gudun ɓacin ran ta ya kamata ace itama tana dubawa. Idan abubuwan da suke faruwa a rayuwarmu basa wucewa ai da an shiga uku. Saboda haka Rabi'atu ba za ta bar gidan nan ba saboda ita, idan ta gama ta dawo gidan, idan ta gama taci gaba da zamanta a gidan Nameer babu wanda zai hana ta..."
"Alhaji ya kamata fa a duba wannan lamarin..."
Cewar Hajiya Nasmah, domin sam ba ta yi tunanin irin wannan hukunci daga gare shi ba. Ko a lokacin da su Muhammad ɗin suka so ta dawo wurin su Alhajin ƙin amincewa ya yi, amma yau kai tsaye yake faɗa da bakin sa cewa a bar ta ta yi ta zama a gidan Nameer.
Ƙara kwantar da murya Mubarak ya yi ya ce.
"Alaji ni ma dai ban ga abin nan ya yi making sense ba. Don Allah..."
Hanya fitar parlourn ya nuna musu yana faɗin.
"Please za ku iya bani wuri, ina da buƙatar na huta please."
A hankali suka miƙe suka sulale ɗaya bayan ɗaya suka bar shi daga shi sai Hajiya. Itama tana buɗe bakinta ya ce ta bashi wuri baya son maganar kowa a halin yanzu.
******
Alhaji Gimba.
Gidan su dake Life Camp ya wuce da shi direct. Tun a harabar gidan da suka fito mota ya fara balbale shi da masifa tamkar zai kifa masa mari yana faɗin.
"Ni za ka kawo wa iskancin banza iskancin wofi! Gabaɗaya Ka gama zubar mini da mutunci na a gaban maƙiyana. Wace irin lalacewa ce ace ka rasa inda za ka je ka zauna sai gidan Mas'ood? Mas'ood da baya so na baya ƙauna ta..."
"Alaji ya kamata fa..."
"Wallahy tallahy idan baka rufa min baki ba sai in zabga maka tafi ka ji na faɗa maka ba! Uwar taka ma sai ta zo nan kafin na yanke hukuncin da naga ya cancanta. Shi ke nan ka baromin kasuwancina ka dawo gidan maƙiyi na ka zauna saboda kawai baka san ciwon kan ka ba ko? To wallahy tallahy ba zan yarda ba, kuma sai na ɗauki mataki ka ji na gaya maka..."
Hannu ya saka a aljihu ya ciro wayarsa da ake ta kira tun ɗazu wanda bai san ma daga ina kiran yake ba.
Har ya kai wayar kunnen sa bai san waye mai kiran nasa ba. Jin muryar Mace yasa ya bar gun Alhajin ya matsa can nesa da shi ya ce.
" Wa ke magana?"
Sautin murmushin ta ya jiyo daga can ɓangaren ta ce.
"Uhm! Rabi'atu ce ta gidan Abbah."
Cikin rashin fahimta ya ce.
"Wane Abbahn kenan?"
"Ta gidan Alhaji Mas'ood wacce na kawo maka breakfast ranar da safe. Daman na ce bari na kira na ji halin da kake ciki an ce an wanke ka baka da laifi a ɓatan Anaam. Allah yasa kana lafiya?"
Jinjina kansa ya yi tamkar yana a gaban ta ya ce.
"I'm fine....Thank you."
Daga haka ya katse kiran ya waiga ya kalli mahaifin nasa wanda shi ma ɗin shi yake kallo tun ɗazu.
"Waye ya kira ka?"
Wani kallon mamaki Faris ya yi masa ba tare da ya ce komai ba.
"Waye ya kira ka na ce?"
"A friend."
Abin da ya furta kenan sannan ya kama hanya ya shige gidan direct ya shige ɗakinsa.
Har ya shige ciki Alhaji Gimba bai daina kallon sa ba sannan daga ƙarshe ya yi ƙwafa ya fito da wayarsa ya kira Hajiya Salamatu baiwar Allah wacce hankalin ta ke can a tashe,tana ɗagawa ko gaisuwarta bai tsaya amsawa ba ya ce.
"Ki zo Abuja Salamatu domin ba lafiya...asirin ki ya tonu daga ke har ɗan na ki..."
Hankalinta a tashe ta ce.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Alhaji wannan wace iriyar magana ce haka?"
"Ba kin tura shi gidan maƙiyina ba don kawai kuga na tozarta? To wallahy ta Allah ba taku ba. Shi ne har da kukan munafurci kina faɗin baki san a ina yake ba, to wallahy sai na ɗauki mataki kin ji na faɗa miki."
Maimuna dake laɓe tun ɗazu bayan ta ji sun yanke wayar ne ta ciro wayar ta ta kira shi tamkar za ta fashe tsabar yanda take ciki tana batsewa. Yana ɗagawa ta ce.
" Alhaji yau ni ce na dawo banza a wurin ka?"
Cikin hargagi ya ce.
" Eh ɗin! Eh Maimuna tun da haka kika ce!....kinga...Dan Allah ni ki barni na ji da abin da ya dame ni dan Allah. Kin cika naci kin cika matsala. Da ki ka ga ban ɗauki kiran ki ba ai sai ki saurara ki ji. Mts!"
Tamkar wacce ta samu matsalar ƙwaƙwalwa haka ta zare wayar daga kunnenta jin cewa kamar ya katse kiran da gaske. Tana dubawa kuwa ta ga da gaske ya tsinke kiran, hakan yasa ta faɗa kan kujera ta fashe da wani irin mugun kuka tana faɗin.
" Na shiga ukuna ni Maimuna? Tun yanzu? Kwana ɗaya gabaɗaya? Yaushe ma aka yi daren balle dare ya waye? Wallahy ba zan yarda ba. Na rantse da Allah ba zan yarda ba.."
Daga haka ta miƙe ta zari mayafinta ta bar gidan.
******
Jiki a sanyaye Mubarak ya shigo ɗakin Hajiyar ta su yana mai samun wuri ya zauna akan kujera ya ce.
"Ammie Anaam taƙi ta saurare ni....infact taƙi ta saurari kowa har Yaa Muhammad. Wai ashe duk laifin kowa take gani Ammie? Fushi take da kowa. Kuma ya zamuyi tunda mai gida ya yanke hukunci mu miye namu a ciki?"
Cikin nuna rashin jin dadinta ta ce.
"Yaushe ta ce za ta dawo gidan Mubarak?"
Girgiza kai ya yi ya ce.
"Ta ce fa matuƙar Rabi za ta ci gaba da zama a gidan nan to ita ba za ta dawo ba."
"Oh ni Nasmah! Wannan wace irin rayuwa ce? Ga Alhaji Shi ma ya tsaurara, hatta gidan Nameer ɗin ya ƙi amincewa na je."
Miƙewa ya yi yana faɗin.
"To ai ko can ɗin da take zaune ba damuwa ba ne. A ƙyale ta taci gaba da zamanta har Allah ya kawo mana ƙarshen abin."
"Dole kam haka za'a yi Mubarak. Allan yasa mu dace amin."
Yana fita ta ciro wayar ta ta kira Dinaratu, bayan sun gaisa Hajiya Nasmah ta ce.
"Dinaratu Anaam ɗin fa?"
Kallon gefen da Anaam ke zaune ta yi wacce ke rungume da Ashnan tana bata abinci ta ce.
"She's here Ammie...Anaam. Ga Ammie..."
Ta ƙarashe maganar tana miƙawa Anaam ɗin wayar. Anaam kuwa, tana jin cewa wai Ammie ce sai ta sauke Ashnan ta miƙe kawai ta bar parlourn kai tsaye ta shige ɗaki.
A sanyaye Dinaratu ta ce.
"Ammie ki yi hak'uri...ta tashi ta bar wurin, haka ta yi wa Mubarak ɗazu da ya zo,but In sha Allahu a hankali za ta sauko kuma ai kun sani."
Cikin nuna rashin jin daɗi ta ce.
"Hmm! To shi ke nan Dina, na gode sosai. Ki gaishe da su Arif."
"Tau za su ji in sha Allahu. Sai da safe."
******
Tun da Hajiya Salamatu ta iso Alhaji Gimba bai sarara ba, cin mutunci sai abin da ya manta, tamkar wani mahaukaci haka ya dawo wanda hatta Faris a wannan karon sai da ya jikin sa ya yi sanyi.
Da kukanta da hawayenta ta hau rantse-rantse akan ita bata san cewa Faris na gidan alhaji Mas'ood ba amma firr yaƙi yarda ya ce Ƙarya take ta san komai.
Bayan kusan kwana biyu da shafe bai ƙara shiga sabgar su ba, sai da ya ji ransa ya ɗan ƙara sanyaya sannan ya kira su a parlour cike da rashin arziki ya kalle ta ya ce.
"Salamatu!"
"Na'am"
Ta amsa tana mai kallon inda yake tsaye.
"Salamatu idan har na isa dake a duniyar nan. Babu ke babu ƙara hulɗa da iyalin Mas'ood, ko ta Waya wannan ban amince ba. Yanzu dan Allah daɗin ki ne ace wai an laƙaba masa satar Maryam harda tozar ta shi su sa a rufe shi police station tsabar wulaƙanci?"
Girgixa kai ta yi ta ce.
" Wallhy Alhaji ni ma kam sun yi matuƙar bani mamaki da har suka iya sa a rufe Faris akan ɓatan Anaam..."
"To ai ke ake faɗawa Salamatu? Idan za ki yi hankali sai ki yi. Maƙiyinka har abada komai za ka yi masa Maƙiyinka ne domin har abada ba zai so ka ba....saboda haka dole zan ɗaukar masa mataki."
"To Alhaji. Allah ubangiji ya kyauta yasa kuma mu dace..."
Duk faɗan da suke Faris na gefe yana chart da Rabi'atu wacce ta nace da kiransa ba dare ba rana tare da turo masa messages wanda tun bai kawo komai a ransa ba har ya ɗan fara jin interest a kanta.
******
Tun da ya koma duk bayan kwana biyu haka sai ya kira Aunty Dina domin kawai su gaisa. Ko sau ɗaya bai taɓa attempting tambayar ta Anaam ɗin ba, tun da ya tafi duk kiran da yake mata maganar Anaam ɗin ba sake shiga tsakanin su ba sai yau da dawo gida misalin sha biyu saura na dare ya kira ta.
Cike da mamaki ta ɗauka ta ce.
"Allah yasa lafiya Maheer?"
Jinjina kai ya yi yana mai ƙara lowering voice ɗin Tvn da yake kallo ya ce.
"Lafiya ƙalau Aunty Dina...."
Daga haka sai kuma ya yi shiru,ya yin da ta nutsu sosai ita kuma tana jira ta ji mi zai ce.
"Ko zan iya magana da ita please?"
Cikin rashin fahimta ta ce.
"Wa ke nan?"
"Baƙuwar gidan ki. Ina so in ji ya ya take..."
"Ohh! Wai Maryam ka ke nufi?"
"Yeah!"
"Okay. Lemmi check on her Idan ba ta riga ta yi bacci ba."
Daman tana ɗakin Arifa da Ashnan ne ya kira ta. A hankali ta fito ɗakin ta zo bakin ɗakin Anaam ɗin ta tsaya, ta jima tsaye a bakin ƙofar tana tunanin yanda za ta yi convincing Anaam ɗin akan ta karɓi wayar domin tasan ƙaramin aikinta ne taƙi karɓar wayar. And shi kuma he's still on the phone bai yanke ba.
Bayan ta gama addu'ar Allah yasa bacci take ta tura ɗakin ta shiga, zaune ta cim mata da System ɗin Aunty Dinar a gaban tana kallon Film ta ce.
"You still awake?"
Murmushi ta yi tare da tsayar da film ɗin tana jinjina kan ta ta ce.
"Ina ɗan rage daren ne Aunty Dina..."
"Uhm"
Ta faɗa tana mai zaunawa a kusa da ita tana facing ɗin ta kai tsaye ta ce.
"Maheer yana so ya miki magana Anaam...hope ba a takura jindaɗin ki ba?"
Agogon system ɗinda ke gaban ta ta kalla taga dare ya yi ta ce.
"Aunty Dina yanzu?"
"Uhm! Yanzu ya kira, kin san yanayin aikinsa ba koda yaushe yake da time ba. Ga shi ma bai kashe ba..."
Ta ƙarashe maganar tana mai ɗora wayar a gefen kunnenta.
Lumshe ido ta yi sannan ta buɗe a hankali ta ce.
"Halo..."
Jin bai amsa ba, yasa ta ɗan janye wayar kaɗan ta duba don ta tabbatar shin yana kan Layin ko kuma ya yanke kiran, but ga mamakin ta call ɗin nan har yanzu.
Sake mayarwa ta yi ta ce.
"Halo...."
Muryarsa ta ji a hankali yana faɗin. "How are you?" ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*PAGE 26*
Lokaci mai tsawo suka ɗauka akan wayar wanda da za a tambayeta ita kan bata san dalilin riƙe wayar a kunnen ta ba, domin dai tun cewa da ya yi ya take bai sake cewa komai ba, and itama kuma ko amsar farko ba ta bashi ba ballantana ya yi tunanin wata kalar maganar daga gare ta.