Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 20
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 20: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 20. Aunty Dina dake gefen ta shiru kawai ta yi tare da zubawa…
3,371 words
Aunty Dina dake gefen ta shiru kawai ta yi tare da zubawa sarautar Allah ido domin dai ba ta ji wata magana daga ɓangaren na su guda biyu ba.
Shi kuma Maheer ɗin, jikin window ya koma ya ci gaba da kallon hasken fitilun da suka gama ƙawata birnin Lagos ɗin, ya yin da ya kafe a wayar yana jin tamkar ya fito mata da maganganun rarrashin da ke suka ji ma dasƙare a cikin akwatin sirrin sa, sai dai kuma, ta ina and ta ya ya zai fara bata haƙuri? Mi zai ce mata? And gashi ma a waya ne saboda haka bai ga ta inda abin zai yi making sense ba. Abu ɗaya zai iya yi shi ne, idan har ya rage aikinsa zuwa next week, in sha Allah he will handover everything to Hamad sai ya je ya gama da matsalar ta sannan idan ya dawo sai ya tafi Oman ya gano Maami sannan ya dawo.
Da wannan shawarar da ya yanke ne ta ji saukar numfashin sa a hankali sannan ya ce.
"I....i just call to check on you. Have a nice dreams..."
Still dai har yanzu bai ji sautin muryarta ba har ta yanke wayar.
Anaam kuwa, janye wayar ta yi tare da miƙa ta ga mammalakiyarta ba tare da ta kalle ta kawai ta ƙara janyo System ɗin zuwa gabanta ta yi playing taci gaba da kallon da take.
Mintuna kaɗan Aunty Dina ta ɗauka tana kallonta kamar ta tambayeta sai kuma dai ta basar daga ƙarshe ta miƙe ta nufi hanya waje tana yi mata saida safe.
Har ta ƙarasa ɗaki ta kasa haɗa tunani mai kyau akan wannan wayar da suka yi a gabanta, miye Maheer ɗin ya gaya mata ne? Ita kuma miyasa ba ta ce komai ba? Ko kuma dai bai ce mata komai ba?
"Hey! Miye kike tunani haka?"
Cewar Nameer yana mai ƙure ta da kallo ganin yanda ta shigo duk jiki a saɓule.
Murmushi ta yi tare da ɗan girgiza kai ta ce.
"Uhm! Ba komai. Al'amarin Anaam ne nake tunani a rai na."
Sai da ya gama sauya kayansa zuwa na bacci sannan ya kalle ta ya ce.
"Maryam ta cika shegen taurin rai da kafiya wani lokaci....baki ga yanda hankalin Alajin su ya tashi ba..."
"Ko ɗazu babu irin rarrashin da Mubarak bai mata ba, kai hatta gwoggo Hanne sai da ta kirani na bata wayar ta yi ta rarrashi har da yi mata alƙawarin cewa sai ta tabbatar Rabi'a ta koma gidansu amma hakan bai sa ta saduda ba."
Wayarsa ya ɗauka daga kan madubi sannan ya samu wuri a bakin gadon ya zauna yana faɗin.
" While...za mu iya bata lokaci mu gani, sometimes matsantawar ba ta da amfani. Allah yasa mu dace."
"Haka ne. To amin..."
Ɗago kansa ya yi ya kalleta ya ce.
"Za ki yi wanka ne?"
Girgiza kanta ta yi ta shiga rage kayan jikinta tana faɗin.
"A'a...na yi da yamma da na dawo daga aiki, yanzu kuma ina jin sanyi sanyi saida da safe idan Allah ya kai mu..."
Ajiye wayar hannunsa ya yi akan bedside drawer ya kwanta yana faɗin.
"To idan kin kambala ki rage hasken ɗakin."
Har ta kambala shirin baccin ta ta yi joining nasa a bed ɗin tunanin su Maheer bai kau a ƙwaƙwalwarta ba.
****** Maimuna.
Bata ƙara shiga tashin hankali ba sai da ta nemi Hajiya Salamatu a gidan ta rasa, tun tana sauraren ta ga ta fito a kaikaice har ta kai ga kai tsaye ta tambayi mai aikinta cewa ina Hajiya, ita kama kai tsaye ta faɗamata cewa ai tayi Abuja kamar yan da ta sanar mata cewa ta tafi Abuja ta kula mata da gida.
Hakan yasa a gigice ta shirya ta wuce gidan iyayenta inda ta samu Babanta a ƙofar gida tare da Yayanta Halliru suna sauke motar itacen da suke kasawa a ƙofar gidan.
"Maimuna! ya naga kamar kina kuka? Subhanallahy...."
Cewar Baban na ta ganin yanda ta fito a motar kamar wacce aka sanarwa da saƙon mutuwa.
Cikin gidan ta shige ba tare da tsaya inda suke ba. Rufa mata baya ya yi ya bar Hallirun yana ci gaba da sauke itacen tare da masu mota wanda koda ya shiga har ta zube ƙasa warwas tana kuka tana faɗin.
"Inna matar Alhaji Gimba sai da ta san yanda ta yi ta raba ni da shi Inna...yanzu ga shi tasa ya yi mini wulaƙanci sun koma Abuja ya barni nan a wulaƙance..."
Tsamen hannun ta Innar ta yi daga surhen da take wankewa ta wani kalle ta tace.
"Wace maganar banza ce wannan? Shi Alhajin shi ya faɗa miki da bakin sa cewa ya koma Abuja da zama?"
"To Inna ai daga yanda ya yi tafiyar sa ya barni ba sanarwa sannan bayan na kira sa ya bini da zagi da cin mutunci ya isa ya isar min da saƙon cewa hakan shi ne manufarsa..."
"Ke dan Allah tafi can! Shi ke nan ba za ki yi masa uzuri ba ki ji miye abin da ya faru kawai za ki wani zo kina laƙabawa matarsa..."
Cikin jin wasu hawayen baƙin ciki ta wani girgiza kai ta ce.
"Inna fa har ita ta tafi Abujar! Wallahy wannan plan ne suka haɗa kawai wallahy..."
Buta Baban ya ɗauka yana faɗin.
"Duk wanda ya shiga motar kwaɗayi to lallai tashar wulaƙanci ce garejin sa...saboda kin raina ni kin raina matsayina kika tafi wani gidan kika gabatar masa da su a matsayin iyayen ki saboda bani da komai. To ki je can ki faɗa musu sai su yi miki maganin matsalar ki...saboda haka ta shi ki fice min daga gida..."
Wani marayan kallon ta yi masa alamar ka tausayeni ta ce.
" Haba Baba! Miyasa ne kake ta son dawo da abin da ya wuce..."
Wani faskaren da ke gefe ya wawuro yana shirin zabga mata yana faɗin.
" Wallahy sai kin bar gidan nan yanzu ba sai an jima ba..."
Ganin hakan yasa ta miƙe da gudu ta ɗauki Jakarta ta fice tana ta kuka. Ta sani sarai in dai Baba ne tsab zai iya ruguza mata shi a kai musamman idan ta tuna dukan da ya yi mata a lokacin da ta haɗa baki da Aunty Halira suka kai Alhaji Gimba gidan da suka ce masa shi ne gidan su kuma Aunty Halirar ita ce jagorar komai wanda hatta yinin buki can akayi, nan gidan su kuma a nan aka ɗaura auren inda suka ce masa gidan kakansu ne.
Baba sai da ya kusa suma tsabar kaɗuwa da baƙin cikin abin da suka masa, da ƙyar aka samu aka rarrashe shi ya haƙura amma har yanzu ba don ya manta ba.
Bayan ta tafi ne Innar ta kalle shi a sanyaye ta ce.
"Haba Malam dan Allah! Ya kamata ka tsaya ka saurare ta, wata ƙila gaskiyar ta faɗa..."
"Dubu bana son zancen banza zancen wofi...taje can ta ƙara ta. Da farko ma na za ta wani abin ne ya same ta, hakan yasa na biyo ta na shigo ashe-ashe shashanci ne,ai kin ga Halliru ya yi tsayawarsa a waje bai shigo ba ballantana ya ji abin takaici."
Shiru ta yi tare da duƙawa ta ci gaba da aikin da take tana faɗin.
" To ina amfanin rayuwa babu yafiya? Ko kai dai da kake ubanta ka yafe mata ballantana shi da zai ce har yanzu yana kan gaba da ita. Ga fili nan kuma sai ya yi ta har yauma tanadi..."
Maimuna kuwa, direct gidan Halira ta nufa ta fashe mata da kuka tana faɗin.
"Ni wallahy ba zan yar da ba! Ki ji walakanci Aunty Halira imagine wai dukkan su suna Abuja sun bar yashe a gida kamar wata mai gadinsu...."
Taɓe baki ta yi ta ce.
"Uhm! Wannan kuma ke kika jiyo, kuma wallahy somin taɓi ne akace hatsin gara a Langa. Wannan ɗin kaɗan kika gani. Nan gaba sai dai ki ji sun ƙara gaba sun wuce Cana inda ya taɓa zama ke kuma kina nan a mai gadi....idan abu ya tashi na dangi sai ya kira ki yace dan Allah ki wakilci Hajiya Salamatu, ko kuma idan ana son wani tallafi sai ya ce aje wurin matar shi tana nan zaune a gida....To wai daman aka ce miki ita Salamatun wawiya ce da za ta barki hakanan ba tare da ta ɗauki matakin raba ku ba bayan tasan kin aure mata miji?"
Cikin jin wani sabon tashin hankalin ta ce.
" Ni wallahy duk bana son hakan ta faru...Dan Allah Aunty Halira ki taimake ni. Yanzu haka daga gida nake Baba ya koro ni,har yanzu yaƙi haƙura da abin da ya faru lokacin auren nan..."
"Ai fa! Yanzu dai ke ka kai su in kaya ne. Daman yaushe za ki tsaya biye Baba da Inna wanda su kullum ba su da wata magana sai ta ayi ta haƙuri? Duk karatun da nake yi wa Baba baya ɗauka Maimuna, yanzu dan Allah da ace Alhaji Gimba yasan daga gidan da kika fito zai aure ki ne? Wallahy ba zai aure ki ba ke ko kallo ba ki ishe sa ba..."
"To ni dai yanzu miye abun yi Aunty Halira ni fa wallahy matakin nake so na ɗauka na gaggawa..."
"Uh uhm Maimuna! Gaggawa aikin shaiɗan ne. Abu ɗaya zamu yi shi ne, yanzu ki tashi kawai ki je ki hau mota, kuma motar kasuwa ki bishi Abujar..."
Wani zaro ido ta yi cike da jin tsoro da kuma mamaki ta ce.
"Aunty Halira in bishi Abuja kuma? Ba ki ji fa irin cin mutuncin da yayi min ba ranar da na kira shi. Wallahy fes ya tsefeni tamkar bai taɓa sani na ba, ni abun har tsoro ya bani ma..."
Wata uwar harara ta gallara mata sannan ta buga tsaki ta ce.
"Banza a banza kawai! Mai tsoron a mutu shi ne gawar fari. Ki daina wannan abun ki zama jaruma. Saboda haka yanzu Abujar kema za ki bi shi ai aure bai fi aure ba kamar yanda na saba faɗa miki, saboda haka babu abin da wannan guzuma ta fiki da shi sai dai ma Ince ke kika fita. Ki shirya ki je ki hau motar kasuwa sai yafi ba shi baƙin ciki don so nake ki ɓata masa kamar yan da shima ya ɓata miki sannan ki ci uban wannan munafukar matar tasa, duk inda suka saka ƙafa kema ki saka,in ya so idan kun dawo sai ki zo idan kin shirya a yi maganin su gabaɗaya."
" To ni Aunty Halira idan naje Abujar sai in yi ya kenan?"
Cike da jin sabon takaicin ta ta ce.
" Wai ke Maimuna ba mace ba ce? Na ce ke ɗin ba Mace ba ce? Daga zaran kin isa ki kira sa ki ce masa ganin ki kema kin iso Abuja, idan kuma ya ƙi ya ɗaga kiran ki tura masa tes ki ce masa ganin Abuja wuri kaza. Ai don ubansa ko ya ƙi ko ya so dole ya kulaki..."
Miƙewa ta yi tana jinjina kan ta tace.
" In Sha Allahu haka za'a yi Aunty Halira. Na gode, bari na hanzarta. Wannan karon ko Ishaq ba zan nemi shawarar shi ba, sai na isa Abujar, duk tsiyar da za'a yi ayi."
"Yauwaaa Ƙanwata! Kuma ki samo kuɗi, ki amso kuɗi da yawa ki tara, ko kuma ki turo min kin ji ko? Daga zaran kin dawo mu tafi inda za'a wanke miki baƙin cikin zuciyar ki."
*******
Gidan Alhaji Galadima.
Gidan yau koda suka wayi gari Mukarram da iyalinsa sun shirya za su koma India. Zai koma wurin aikin sa domin break ɗinda ya ɗauka ya ƙare.
Sai da suka kambala shiga mota Abbah ya kalle shi ya ce.
" Mukarram ina mamakin yanda wurin aikin su suke iya tolerating halayyar ka har suke iya zama da kai sannan kuma da yanda marasa lafiya suke jure rashin haƙurin ka..."
Dariya ya yi yana girgiza kai ya ce.
"Alhaji wallahy ku kai ɗai ne ke yi min irin wannan kallon wanda ina mamaki har yau kun kasa fahimta ta."
"Hmm! Mukarram ke nan! Mu ne fa muka haife ka! Halin ka wane iri ne bamu sani ba?"
Dariya ya ƙara yi sannan ya ce.
"Alaji ina ƙara ba da haƙuri. Sannan dan Allah kada ka ci gaba da fushin nan da Anaam, daga zaran ka tafi gare ta nasan za ta dawo ko kai ko Hajiya..."
Jinjina kai ya yi ya ce.
"Za a yi abin da ya kamata In sha Allahu..."
Daga nan ya kamo hannun Mufid yana yi masa wasa ya ce.
"Kai ba da kai za'a koma ba, muna nan tare da kai..."
Hannu Mufid ɗin ya maƙale alamar a'a sannan suka ƙara sallama da su Ammie suka wuce.
Suna komawa Alhajin ya zauna a dinning table da nufin yin breakfast sai ga shi Mubarak ya shigo yace masa wai wasu mutane sun zo neman sa su biyu kuma sun ce dole sai shi za su gani.
Ɗan Jim ya yi ya kalli Hajiya Nasmah kamar yanda itama take kallon sa sannan daga ƙarshe ya jinjina kansa ya ce.
"Ka ce su shigo."
"Okay..."
Sanye suke cikin suit baƙi, bayan sun ƙara so ciki suka gaisa cikin mutunci sannan ɗaya cikin su ya miƙa masa takarda yana faɗin.
"Saƙo ne daga court..."
Karɓa ya yi tare da yi musu godiya sannan suka juya suka koma.
Tsaye Mubarak ya yi kamar yanda itama Hajiya Nasmah ta yi suna jira ko zai buɗe takardar su ji abin da ta ƙunsa. Bai ba su wata wahala ba, because a nan ya buɗe ta a gaban su ya karanta cewa wai ana neman sa a kotu Alhaji Gimba ya shigar da shi ƙara akan zargin ɓoye masa ɗansa na tsawon lokaci sannan da kuma ɗora masa ƙazafin satar Anaam da suka yi.
Bayan ya kammala karantawa jiki a saɓule Hajiya Nasmah ta ce.
"Oh ni 'ya su! Tun farko ka ga abin da na yi ta gudu Alhaji amma sai kace min ba komai...."
Cikin nuna zallar mamaki Mubarak ya ce.
"Wallahy Hajiya ko a mafarki ban taɓa yarda cewa Alhaji Gimba zai iya shigar da Alaji ƙara ba. Na ɗauka komai ya wuce. Miye rayuwar duniyar nan ne bakiɗaya? Shiyasa fa wani lokacin ni wallahy bana ganin laifin Yaya Mukarram domin mutanen zamanin nan sai ka buɗe musu naka idon sannan ake zaunawa lafiya. Shi duk abin da ya yi mana bamu ce zamu shigar da shi ƙara ba sai shi ne ko kunya wai zai shigar da kai ƙara?... "
Zaunawa Alhajin ya yi akan kujerar dinning table din ya kalle shi ya ce.
"Mubarak ya isa. Ɗauko wayarka ka kira mini Madu kace yazo yanzu-yanzu ina jiran sa...Hajiya kema ki taimake ni da wayata please in kira Ridwan mu ji yanda za'a yi da wannan al'amari...kuna ji na?"
Ya ambata yana mai kallon fuskokin su ya ce.
"Please ku bar maganar nan a nan please ko Mukarram kada a sanar masa."
"Tau ya yi Alaji, in sha Allahu."
******
Gidan Aunty Dina kuwa, a gajiye ta dawo daga Office wanda tun da ta zauna ta ci abinci ko ɗakin ta bata isa ba.
Fira suke da Anaam akan lectures ɗinda ta fara fita yau kusan 3days kenan, wanda drivern su Arif shi ne wanda yake kai yana dawowa da ita.
Da murmushi a fuskar ta take bai wa Aunty Dina ɗin labari tana faɗin.
"Aunty Dina wata ƙawar da na yi tun ranar farkon da na fara shiga lectures ɗin ne wai take mamakin cewa da na yi ni bana riƙe waya a yanzu..."
"To miyasa take mamaki?"
"Oho mata! Wai ita wallahy bata ma yarda ba kawai dai bana son bata numbern waya na ne..."
"Akwai zama a class ɗin na ku?"
Jinjina kanta ta yi ta ce.
"Sosai ma, sun ma fi mu yawa fa..."
"Anaam ni ma fa wannan matakin da kika ɗauka na rashin riƙe waya ni a matsayin shirme na ɗauke sa. A wannan zamanin da muke ciki, waya rayuwa ce, and za ki rage wasu damuwowin da dama idan kina da ita..."
Girgiza kan ta ta yi ta ce.
"Ni kam na san dai sai dai ta ƙara min wata damuwar Aunty Dina...a yanzu dai nafi farin ciki a haka.."
"But bakya tunanin class ɗin ki zai yi ƙasa a nemi a raina ki ganin cewa baki da waya?"
"Ba wannan maganar Aunty Dina...duk wanda zai kalle ni yasan nafi ƙarfin ace wai kuɗin siya min waya ne babu sai dai kawai ra'ayi...."
Sallamar Maheer ce ta katse musu firar kamar daga sama haka suka ji shigowar sa.
Cikin zallar nuna mamaki Aunty Dina ta ce.
" Maheer!"
Wuri ya samu ya zauna da murmushi a fuskar sa ya ce.
" Barka da gida..."
Tun da ya shigo idonta yake kansa har ya zauna ba ta daina kallon sa ba. Sanye yake da jeans and Tshit da suka yi matuƙar amsar jikinsa, ga wata Pcap black da ya rufe yalwataccen gashin kansa da ita sai faɗaɗen glass ɗinda ya ƙara fito da shi a cikakke kuma haɗaɗɗen mutum wanda duk macen da ta kalle sa sau ɗaya sai ta ji zuciyar ta ta buga.
Suna haɗe ido ta wani juyar da kanta gefe kamar wata marar gaskiya. Ƙarshe ma sai ta miƙe kawai ta bar wurin kai tsaye ta haura sama.
Kallon shi Aunrty Dina ta yi ta ce.
"Wannan ba za tan fa?"
"Ka wai na zo duba ku ne..."
Murmushi ta yi ba don ta yarda ba a cikin ran ta. A fili kuma sai ta jinjina kan ta ce.
"Muna godiya sosai..."
"Bari a kawo maka ruwa..."
"Noo! Thanks. Please ki bar shi."
"To ya wurin aikin na ku?"
"Alhamdulillah! Na baro Hamad."
Ta shi ya yi yace mata zai fita ya dawo ba jimawa. Yana fita ta tashi ta haura ɗakin Anaam ɗin ta iske ta tana kwance akan gado ta ce.
"Why did you do that? At least ya kamata ki gaishe da shi kafin ki wuce..."
Miƙewa ta yi ta zauna tare da ɗago kai ta kalle ta ta ce.
"Kawai ni kaina ban san miyasa na yi hakan ba. Ƙwarai ya kamata ace na gaishe da shi ko don zaman sa na ƙanin ki, amma ban san miyasa ba..."
"Kodai ya yi miki wata maganar rashin ɗa'a ne a waya ranar?"
Saurin Girgiza Kanta ta yi ta ce.
"Wallahy ko ɗaya Aunty Dina. Ranar ka cewa ya yi ya kira ya ji yaya nake, bayan haka bai ce komai ba..."
"To hakan ya ɓata miki rai ne?"
Nan ma girgiza kan ta ta yi ta ce.
"A'a. Ina laifin wanda ya damu da kai...kawai dai Aunty Dina ki yi haƙuri amma ni harkar maza bana son ta..."
Zaunawa tayi tare da ɗora hannunta a kafaɗarta ta ce.
"Dole a haka za ki yi haƙuri ki bada fuska matuƙar dai mutumin kirki ya fito miki da niyyar aure saboda Allah. Ban san manufar Maheer ba, but ki yarda dani mutumin kirki ne..."
"Aunty Dina waye zai yarda ya aure ni a yanda nake a yanxu?"
Kai tsaye ta ce.
"Mutumin da ya yarda da ƙaddara mana...and miye ɗin ya faru dake da har za'a ce ana gudun auren ki? Ki ma daina wannan tunanin kin ji ko. In sha Allahu duk wannan sai ya zama tarihi a rayuwar ki watarana..."
Wani yawu ta haɗiye da ƙyar tana girgiza kan ta ta ce.
" Aunty Dina kenan! Ke kike ganin haka, amma ni ina hango abin da bakya hangowa. Aunty Dina likita ya tabbatar ko haihuwa ba zan iya yi ba sanadiyyar abin da ya faru dani....wasu fa ina ji har fanko sai da suka kira ni..."
"Rayuwa ai cike take da ƙalubale, matuƙar ka san kanka to dole ka shirya mata a duk yanda ta zo maka. Allah shi ne kaɗai wanda yasan daidai..."
Da haka dai ta samu ta ɗan lallasar mata zuciyar ta sannan daga karshe ta miƙe ta barta ta wuce domin ta jiyo dirin su Arifa sun dawo daga school wacce idan suka tafi basa dawowa tun safe sai six na yamma.
Shi kuwa Maheer tun da ya fita bai dawo gidan ba sai around 9pm Wanda a lokacin har Nameer ya dawo yana gidan.