Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 21

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 21

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 21: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 21. Ta yin abinci ta yi masa bayan sun gama gaisawa sai ya girgiza…

3,367 words

Ta yin abinci ta yi masa bayan sun gama gaisawa sai ya girgiza kai ya ce.

"Thanks. Ina so zan koma Lagos ne..."

Cike da mamaki suka haɗa baki wurin ce masa.

"Yanzu? Miyasa?"

"Yeah...ana jira na wurin aiki na,daman wani uzuri ne ya kawo ni kuma na kambala...."

"Okay...Allah ya tsare."

"Aunty Dina please ko zan iya ganin ƙanwar kin nan kuwa? 2minute...only 2minute..."

Ya faɗa daga ƙarshe ganin yanda suka tsuro ido daga ita har Nameer ɗin suna kallon sa.

Ɗan kallon Nameer ɗin ta yi a kaikaice sannan ta jinjina kai ta tashi ta shiga ta kira ta tace wai Maheer na so ya ɗan yi mata magana.

A bakin ƙofa ya koma yana jiran ta, bayan ta fito ta tsaya a ɗan nesa da shi ta ce.

"Ina wuni..."

Ido ya zuba kawai yana kallon ta ba tare da ya amsa ba. Abubuwa ne masu yawa a cikin ransa. He wish a yau ɗin nan ya iya buɗe masa ya roƙeta ko zai samu nutsuwa da kwanciyar hankali.

But wani abu ya ji mai kama da tsoro da kuma kunya sun mamaye masa zuciya. Abun fa ba mai sauƙi ba ne! Miyasa tun farko zuciyar sa ta amince masa hulɗa da su Oga Badru? Ga shi bai ɗauki fansar ba amma kwanciyar hankali ya gagare sa, alhali kuma wanda ya kashe masa Abbunsa yana nan yana jindadi a duniyar.

Juyawar da ta yi za ta koma shi ne abin da ya dawo da shi hayyacinsa da sauri ya ce.

"Dan Allah ko za ki iya ɗan ƙara jira na mintuna biyu? Just 2minute please...."

Dakatawa tare da juyowa ta jingina jikin ƙofar ta kalle sa, sai kuma ta kawar kanta gefe.

A zaton ta zai taɓuka yace wani abun kamar yanda ya roƙi alfarmar 2minute ɗin, but sai ga shi sun ƙara shafe mintuna fiye da goma bai ce komai ba.

Yana ji yana gani ta sake juyawa ta buɗe ƙofa ta yi shigerta ciki. Mamakin sa ne ya daɗa kama ta. shi ɗin magana wahala take masa ko miye? Ko kuma dai tsabar renin wayau ne da renin hankali irin na maza?

Ya ji ma a tsaye yana ta faman nazari wanda daga ƙarshe kawai ya juya ya bar gidan ba tare da ma ya yi musu sallama ba, daman akwai abokin sa Ahmad da ya haɗu da shi tun ɗa zu, shi ne wanda ya kawo shi ya tsaya domin ya kai shi Airport ɗin. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 27*

Ido suka zuba mata har ta gama haye stairs ɗin ta shige sannan daga ƙarshe Aunty Dina ta miƙe ta cicciɓi Ashnan da ta yi bacci kan kujera ta kai ta ɗaki. Zaune ta tarar da Arifa da tulin litattafanta a gaban ta saman gadon ta tana ta faman rubutu.

Lallaɓawa ta yi a hankali ta ajiye ta sannan ta kalli Arifar ta ce.

"Har yanzu wai baki ƙarasa ba?"

Idon ta akan rubutun da take ba tare da ta ɗago ba ta amsa.

"Wallahy Mummy aikin ne da aka bamu yau da yawa."

"To ni dai dan Allah ki yi a hankali kada ki tayar da ita yau rigima take ji."

Tana gama faɗar haka ta fito ta sauko parlourn ta zauna a inda ta bar Nameer ɗin tana faɗin.

"Ni fa jikina ya bani kamar Maheer na son Anaam..."

Wayar shi ya ajiye a kan handle ɗin kujerar da yake zaune ya mayar da hankali a kanta ya ce.

"Mi kika gani?"

"Kawai dai naga yanda ya damu da ita, ko ranar sai da ya kira ni a waya yace na bata and yau ma idan har ba shi da interest da ita kai ma kasan Maheer ba zai dawo gidan nan ba."

Ɗan Jim ya yi kaɗan alamar nazari sannan daga ƙarshe ya sauke ajiyar zuciya ya ce.

" Ni kuwa kin ga Hakeem Alami har ya mini maganarta..."

Cike da mamaki ta ce.

" Wane Hakeem ɗin Abban Arif?"

" Alami dai friend ɗina da kika sani....tun ranar da suka zo ɗin nan ya fara mini magana, so ban yi taking issue ɗin serious ba, sai shekaranjiya da muka haɗu yake faɗamin cewa ai har ya faɗawa Hajiyarsa zancen auren nasa tace ba damuwa..."

Cikin rashin gamsuwa da bayanin sa ta ɗan taɓe baki can ƙasan maƙoshi ta ce.

" Uhm! Ni dai gaskiya a'a. Alami fa yana da mata Abban Arif har da yara biyu and kasan sha'anin yarbawan nan wani lokacin ba daɗi ne da shi ba..."

" Dina kin san fa waye Alami da familyn shi, mutane ne masu kirki musamman mahaifiyar shi, kuma tun da ta amince kin ga ai ba wata matsala. Sannan Rofiyat da kike magana akanta ba gida ɗaya zai ajiye su ba kema kin sani..."

Cikin rashin jin bata gamsu ba har yanzu ta ce.

" Ni dai Allah ya gani wallahy na fi so wa Anaam saurayi, musamman da irin ƙaddarar da ta same ta, Maheer ba a nan yake ba, daga zaran ya ɗauke ta daga nan shikenan ta manta da bayanta, amma sha'anin kishiya ta ji da shi ta yaya..."

"Dina Maheer ɗin ya faɗa miki ko kuma ita ya faɗa mata cewa yana son ta zai aure ta ne?"

Girgiza kanta ta yi ta ce.

"A a! Bai ce ba, but the way yanda ya damu da ita from the first day da ya ganta ya isa ya fahimtar da kai cewa akwai wani abu a ransa...."

Ɓata fuska ya yi ya miƙe tsaye ya warce wayarsa yana faɗin.

"Ba zan yi stopping Hakeem ba Dinaratu....daman na ce ya jira har sai ta koma gaban iyayenta, so idan ta amince da auren sa ba ruwanki a ciki..."

Itama da ɗan Kaushi a kalaman ta tace.

"And idan kuma ta amince da auren Maheer ɗin kada ka ji haushi kai ma dan Allah."

Bai ƙara ce mata komai ba ya wuce ya haura ya shige ɗakinsa. Mamakin sa ne ya kamata har da wani tafa hannu a fili ta ce.

"Oh Namiji! Wato duk irin Kulawar da nake ba ta akan wani ya zo daga gefena shi ne yake nema dole sai ya mini baƙin ciki ko? Hmm! Allah ya kyauta."

Daga haka ta miƙe taje ta kambala sauran night routines ɗinta Sannan ta je ta kwanta.

Washegari bayan Nameer ya gama shiryawa ta raka shi ya fita ta dawo inda su Arif ke breakfast ta zauna har sai da suka kambala suka fita zuwa mota sannan ta tare Anaam ɗin wacce ta ɗauko kayan karatun ta cikin sakin fuska ta ce.

"Anaam..."

Kallon ta tayi ta ce.

"Na'am Aunty Dina..."

"Jiya kun tattauna wata magana ne da Maheer kuwa?"

Kai tsaye ta girgiza kai ta ce.

"A'a..."

"Bai ce miki komai ba?"

"Eh Aunty Dina...ka wai tsayawa ya yi bai ce min komai ba daga ƙarshe na juya zan tafi yace wai dan Allah na ƙara jira na mintuna biyu, ƙarshe dai na tafiyata nikam..."

Murmushi ne ya suɓucewa Aunty Dina wanda yasa Anaam ɗin ta yi mata wani kallon mai alamar tambaya.

" Kin ga ina murmushi ko Anaam? Wata soyayyar da haka take farawa..."

Ƙirjin ta ne taji ya yi wani ras har bata san da lokacin da ta dafe shi da hannun ta ba ta ce.

"Soyayya Kuma Aunty Dina?"

Jinjina kai ta yi tana kallon ta ta ce.

"Ƙwarai kuwa...a wasu lokutan saƙon soyayya ba lallai sai da magana ba Anaam...yi maza ki je kada ku yi latti."

Motar ta je ta shiga wanda duk surutun da su Arif ke yi mata yau babu ɗaya daga cikin su da ta amsa. Gabaɗaya tunanin ta ya koma ga maganganun su da Aunty Dina. Soyayya fa ta ce? Yanzu Shi wannan ɗin ne yake son ta? To miye ma ya gani a wurin ta da har zai ji yana son ta? Idan za ta iya lissafawa a ɗan ƙanƙanin lokacin da ya ganta ba su taɓa ido biyu tana cikin daɗin rai ba...

"Hajiya mun iso fa tun ɗa zu..."

Cewar drivern yana mai karkato wuyan sa ya kalli inda take zaune a gidan baya. A zaton sa ma bacci take yi ganin sun kai kusan minti biyar da shigowa harabar school ɗin amma kuma ba ta yi yunƙurin fita ba.

Jin saukar kalaman sa a kunnen ta sai ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ya Lula ta ce.

"Ohh sorry Dan Allah na ɗan sha'afa ne...thank you.."

Sai da ta fito sannan ta kalle shi ta ce.

"Please ko yau 2pm zan tashi kasa ka manta.."

Cike da girmamawa ya ce.

"In sha Allahu Hajiya ba zan manta ba. Allah ya taimaka ya bada sa'a."

Sabuwar ƙawarta ta hango wacce har yanzu bata ma san sunanta ba tana yi mata murmushi har ta ƙarasa inda take tsaye tana jiran ta tace.

"Welcome Hajiya Maryam.."

Murmushin itama ta mayar ta tace.

"Please ki yafe min idan...na san idan na ce ban san sunan ki ba za ki ji ba daɗi a ranki..."

"Nooo! Baki da matsala....yau da gobe kece za ki sanarwa da wani ko wata sunana..."

Cikin jindadin nuna sauƙin kanta Anaam ta ce.

"Haka ne. Na gode da fahimta amma dai still ina son riƙe sunan a yanzu..."

Hanyar lecture hall ɗin suka nufa wanda a hanyar ne ta ce mata.

"Sunana Na'Imatu Hassan Muhammad..."

Cikin wani irin farin ciki Anaam ta wani wai go ta kalle ta tace.

"Da gaske kike sunan ki Na'Imatu dan Allah??"

Na'Imar na dariya ta ce.

"To daman ana Ƙaryar suna ne Maryam? Suna na kenan Na'ima..."

"Sunan Yayata kenan kuma aminiyata, bai jima da tayi aure ba muka kai ta Adamawa. Na ji daɗin haɗuwa dake..."

Still da murmushi a fuskar ta tace.

"Ni ma haka. Allah ya bamu sa'a."

"Amin amin."

Da haka suka ƙarasa lecture hall ɗin suka zauna wanda bai fi 10mnt ba lecturer ɗinda suke jira ya shigo musu suka sha karatu sai 10am suka fito.

Fira suka ci gaba da yi har wani ya ƙara shigowa sannan suka fito cafeteria suka sha abun sha suka je masallaci suka sallah suka dawo suka ƙara yin wata lecture sannan suka fito suka wuce gida.

Tana isa gidan ta iske Aunty Amina zaune ita da Aunty Dina suna fira. Da gudu ta faɗa jikinta cikin jindaɗin ganin tace.

"Oyoyo Yaa Amina..."

Girgiza kai Aunty Aminar ta yi ta ce.

"Hmm! To ai dai ga shi na biyo sawu..."

A mairairaice ta ce.

"Yaa Amina ke ma laifina za ki gani ko?"

"A a Anaam...ta ya zanga laifin ki, duk abin da baka da ra'ayi da shi yana da wuya ka iya zama inuwa ɗaya da shi. Amma kuma ya kamata ka duba irin ƙoƙarin da iyayenka suke yi a kanka. Abbah har baro tushensa ya yi saboda kawai farin cikin ki, amma kuma sai kika bari shaiɗan ya yi galaba a kanka har kika kasa ganin ƙoƙarin iyayenki da alherin su a kanki. Anaam ina ruwan ki da zaman Rabi'a gidan? Kai ba ita ba, duk wani wanda zai zo ya zauna gidan miye ruwan ki da shi? Ai sai ka kula da mutum ka shiga sabgar sa sannan zai nemi ganin wurin baccin ka. Idan kika ce ba za ki yi hulɗa da ita ba nobody will force you. Barin gidan iyayenki saboda Rabi'a Sam hakan bai kawo kallo ba..."

Hawayenda suka silalo mata ne ta share da bayan hannun ta tare da saukar da kanta ƙasa tana ci gaba da sauraren ta.

"shin kina da labarin cewa yanzu haka an aikowa Abbah takardar sammaci daga kotu akan ƙarar da Alhaji Gimba ya shigar akan sa cewa ya ɓoye Faris a gidansa sannan ya laƙa wai laifin cewa shi ne wanda ya sace ki..."

A razane ta ɗago kanta ta kalli Aunty Aminar jin wata maganar da ba ta yi tsammani ba.

Jinjina kai Aunty Aminar ta yi ta ce.

"Eh...da gaske ne abin da kika ji, yanzu haka shirin shiga kotu suke Anaam duk don saboda ke. Abin da kika aikata sam bai kamata ba, atleast ya kamata ace kin yi tunani kafin ki aikata hakan..."

Hannun Anaam ɗin Aunty Dinaratu ta kama a hankali ta saukar da murya ta ce.

" Daman haka rayuwa ta take, shi daman ɗan Adam ya kasance mai yawan kuskure sannan kuma mai karɓar gyara a duk lokacin da ya gano cewa ya aikata kuskure. Ki koma gida Anaam ki ba wa su Ammie haƙuri domin ba akan daidai ki ke ba. Ki kauda kai ga duk abin da Rabi'a za ta yi a gidan ki manta da ita, daga zaran Allah ya daidaita ki da mijin da ya dace dake shikenan sai ki bar mata gidan..."

Murya a karye ta ɗago ta kalli Aunty Dina ɗin da hawaye tab a idon ta ta ce.

" Aunty Dina waye kike tunanin zai aure ni a yanda nake?"

" Nagartaccen namiji wanda Allah ya rubuta cewa shi ne mijin ki Anaam. Ki daina wannan maganar na faɗa miki ki daina wannan maganar. Yanzu ba ga Na'imatu can zaune a gidan Mijinta ba? Nima gani zaune da mijina, itama Amina gata zaune lafiya a gidan yayanki...dan Allah to miye yafi haka farin ciki?"

" Kullum abin da nake faɗamata kenan. Ba kece kike da ikon rubutawa kanki ƙaddara ba, saboda haka abin da ya faru dake ba kece kika tsara ba, ki daina ba kanki wahala dan Allah Anaam. Yanzu ki tashi ki shirya na cewa Mubarak idan kika dawo zan kira sa yazo ya mayar damu gida."

Miƙewa ta yi taje ta tsinto abinda take so daga cikin kayan da Ya Nameer ya saya mata tsawon zaman ta a gidan ta fito parlour ta ajiye sannan ta je ta ɗauko lemu ta zo ta zauna tana sha a hankali su kuma suna ci gaba da fira wanda sai da aka kira La'asar sannan suka je suka yi sallah, sai da 5pm ta buge sannan Mubarak ya zo suka tafi.

Har suka isa gidan daga ita har Mubarak ɗin ba wanda ya yi wa wani magana.

*******

Maimuna kuwa, gida ta koma ta shirya tsab gari na waye taje ta hau motar zuwa Abuja. Sai da drivern yakai ƙarshen inda zai tsaya sannan ta fito aka fito mota da wargajejen akwatinta ta haye kai ta zauna ta ciro wayarta a jaka ta kira Alhaji Gimba.

Sai da ta yi mishi kira biyu a na uku sannan ya ɗaga ya ce.

"Sorry Maimuna dan ki yi min uzuri kwana biyu na shiga busy..."

Taɓe baki tayi tamkar yana a gabanta sannan ta ce.

"Ah to! Yanzu dai ai an gama tunda gani nima na iso Abujar, idan ka ga dama ka zo ka ɗauke ni, idan kuma baka ga dama ba ka barni na kwana a tasha..."

A ta can ɓangaren Alhaji Gimban, zaune yake tare da lauyan sa suna ƙara tattaunawa, jin zancen da ta yi yasa ya miƙe tsaye cike da mamaki ya ce.

" Miye kika ce Maimuna? Da izinin Uban waye kika baro zuwa Abuja? Ni za ki zubarwa da mutunci har da ce min wai kin hawo motar kasuwa Maimuna?"

"Uhm! Allah na tuba! Ai dai naga aure ba fin aure ya yi ba kuma matarka ba wani zane tafi ni ba da har za ka kawo ta Abuja ku tare ni kuma ku baro ni tsaron gida...wallahy tallahy ba zan yarda ba ka ji na rantse maka..."

"Rashin kunya za ki mini Maimuna? Na ce rashin kunya za ki mini? Wallahy tallahy na fi ki tijara kin ji na faɗa miki..."

Wani irin kuka ta fashe masa da shi tare da ƙara narkar da murya a shagwaɓe ta ce.

"Haba Alajina dan Allah! Miyasa kake min wannan wulakanci haka mi nai maka? Idan ka gaji da aure na ne kawai ni ka rubutomin takardar sakina ta wayar nan kawai na juya na koma gida abina...."

Sauke muryar ya yi shima yana mai jin yanda zuciyar sa ke wani irin pumping tsabar yanda ya ji saukar sautin kukan ta ya ce.

"To ai ke ɗin ce Maimuna har yanzu baki gama fahimta ta ba, idan ina cikin matsala ina neman mafita bana son takura da damuwa..."

"To ka yi haƙuri dan Allah. Na daina in sha Allahu ba zan sake ba..."

"To shi ke nan yanzu kina ina?"

"Ina tasha, bari na ba wani wayar ya faɗa maka inda muke."

Yana gama wayar ya sallami lauyan sannan ya koma ciki ya shiryo ya fito ya tarar da Hajiya Salamatu zaune tare da Faris ya ce.

"Hajiya zan je na zo da Maimuna, wai ta zo tana tasha tsabar rigima irin ta ta.."

Cikin jin faɗuwar gaba ta kalle shi kamar yanda shi ma Faris ɗin ke kallon shi ta ce.

"Maimuna kuma Alhaji?"

Miƙewa Faris ya yi ya kama hanyar ɗakin sa yana faɗin.

"Ka ji wata matsala kuma. Yanzu dan Allah muda muke neman mafita miye za ta wani zo salon kawai ta ƙara mana matsala."

"Iyyehhh! To sannun ku isassu! Idan akwai wanda ya aura min ita daga cikin ku sai ya sake ta in gani ko kuma ya hana mata zuwa gidan.

Daga haka ya wani kaɗa babbar rigar sa ya kama hanya. Sai da ya kai ƙofar fita sannan ya waigo ya kalle ta ya ce.

" Ni maimunar bata ma fiye min ku ba! Wallahy ni ta fiye min ku domin bata tsallake magana ta, amma ku idan ba ƙullin munafurci da goyon bayan maƙiyana ba babu abinda kuke. Kuma ku sani, wallahy wannan case ɗin da kuke gani da ace ba Alhaji Mas'ood ba ne, ace wani ne ya aikata maka haka wallahy da babu abin da ya dame ni sai dai in kashe ka za'a yi a kashe ka."

Tana ganin ya fice ta girgiza kanta cikin alhini a fili ta ce.

" Oh ni Salamatu! Yanzu kuma idan ban da neman fitina miye zai kawo ta nan?"

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 28*

A parlour ta taradda Abban na ta, abin da ba ta za ta ba. Ko ka ɗan bata sa a ranta cewa za ta tarar da shi ba kasancewar ranar aiki ce ba weekend ba.

Kallo ɗaya ta yi mishi sai ta ji zuciyar ta ta karye. Tabbas sai yanzu ta ƙara yarda cewa ta aikata rashin hankali, Abbahn da always yake ƙoƙarin ganin farin cikin ta ace shi ne wai ta kasa yarda da hukuncinsa harda yi masa ya ji.

"Anaam..."

Abban ya ambata yana mai jin wani sanyi a ransa na ganin ta yau ta dawo cikin gidan.

A hankali ta ƙarasa inda yake ta rungumeshi tare da ɗora kanta a kirjinshi cikin nuna nadama ta ce.

"Ka yi haƙuri Abbah...na gane na aikata kuskure ku yi haƙuri dan Allah.."

Ɗago ta ya yi ya kalli fuskarta da murmushi ya jinjina kansa ya ce.

"Na ji ba daɗi a raina a lokacin da aka gano cewa kina gidan Nameer...da ace kin furta cewa za ki je can ba wanda zai hanaki...but komai ya wuce. Allah ya yi miki albarka. Allah ya taimake ki ya baki sa'ar wannan karatu da kika fara."

"Amin Abbah..."

"Ni zan fita wurin Alhaji Ridwan yana jirana tun ɗa zu."

"To Abbah Allah ya tsare yasa a dawo lafiya."

"Ameen...Akwai abin da kike so na taho miki da shi?"

Girgixa kai ta yi tana murmushin farin ciki ta ce.

"A'a Abbah, Allah ya dawo da kai lafiya..."

"Amin amin."

Har ya kusa ƙofa sai kuma ya dawo baya ya kira sunanta ta dawo ya ce.

"Na ce ya lectures ɗin? Kina jin daɗin makarantar kuwa?"

"Sosai Abbah...karatun Alhamdulillah akwai daɗi kuma ina fahimta...and guess what Abbah...na samu wata friend mai suna Na'imatu..."

"Wow..that's very good to hear my dear...kin ga dai har yanzu kina tare da Na'ima...but hope tana da mayar da hankali a karatu kamar yayartaki?"

Jinjina kanta ta yi tana ta wani farin ciki ta ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull