Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 22
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 22: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 22. "Sosai kuwa Abbah...tana da ƙoƙari sosai, because duk lectures…
3,331 words
"Sosai kuwa Abbah...tana da ƙoƙari sosai, because duk lectures ɗinda aka yi bana nan ita ce wacce ta yi mini bayani...gaskiya she's good Abbah and tana da tarbiyya domin ni tun da na fara haɗuwa da ita har yau ban taɓa gani tana hulɗar maza ba."
"Uhm...haka ya yi kyau. Allah ya bada sa'a. Ki ce ina gaishe da ita gobe."
"Za ta ji kuwa in sha Allah Abbah..."
Tamkar en kallo haka mutanen da ke parlourn suka dawo domin dai daga shi sai ita ne suke ta shan firar su wanda sai yanzu Hajiya Nasmah ta buɗe bakinta ta yi mishi magana ganin yanda ya shantake kamar ba shi ne ke faɗin cewa sauri yake ba ta ce.
"Amma dai Alhaji kasan cewa jiran ka ake ko?"
Jinjina kai ya yi ya ce.
"Haka ne, bari mu je...sai mun dawo. Daman na yi tunanin idan mubarak bai dawo ba ince masa ya cim mana can ɗin amma tun da ya dawo sai mu tafi, shi Madu da Alhaji Salisu tun ɗazu ya sanar min da cewa suna can..."
"To Allah ya tsare."
Yana ficewa Ammie ta kalli Anaam ɗin ta wani Harare ta tana yin murmushi ta ce.
"Ohh! Da kin san da Abbahn kika yi masa ya ji?"
Girgiza kai ta yi tana dariya ta zo ta yi hugging na ta ta ce.
"Wallahy na yi missing ɗin ku sosai...Ammie ina Nene?"
"Tana nan ciki, ina ga tana kitchen suna girkin yamma. Ya kika baro Su Dinaratun?"
"Lafiya ƙalau suke, ta ce a gaishe ki."
Tun da ta shigo gidan har yanzu bata ga Rabi'a ba, kuma ba ta damu da tambaya ina take ba. Kai tsaye ta haura ɗakin ta tabar Aunty Amina ita da Ammie ta yi shigewar ta.
Koda ta shiga mamaki ne ya daɗa kamata ganin yanda aka sake sauya mata sabbin kaya zuwa wani design da kuma colour, sosai ɗakin ya daɗa kama zuciyar ta domin ba ƙaramin tsaruwa ya yi ba.
Lokaci guda kuma ta ji hawaye sun tarar mata a ido ganin yadda su Abbahn ke komai domin farin cikin ta, gabaɗaya yaushe ma suka dawo gidan ballantana ace har an sauya mata kayan ɗakin ta? Kawai so suke ko ta wace su faranta mata. Ta san fa cewa ta yi ba daidai ba. Ta tayar musu da hankali ta ɓoye kanta amma kuma duk da haka babu wanda ya yi mata faɗa daga cikinsu, ƙarshe ma tarbon ta suka yi suna ta farin ciki.
Kan gado ta faɗa ta lumshe idanun ta tana mai jin yanda take ƙara ƙaunar su a ranta and kuma ta yi alƙawari In Sha Allahu a kan komai na rayuwa ko ya yi mata daɗi ko bai yi mata daɗi ba za ta ƙara tsallake maganar su ba.
******
Maimuna
Wani kallon banza Maimuna ta yi wa Hajiya Salamatu tana wani cin cungom tana ƙas da shi ta ce.
"An dai ji kunya wallahy! Raƙumi da shanye ruwan ɗan tsako...In ban da ma zalunci da cin amana da son ɗaukar wa kai alhaki shi ne za ki ɗauke mini miji ki tsero da shi tsabar cin amana..."
"Ke...ke Maimuna!"
Alhaji Gimba ya ambata yana mai kallon fuskarta har ya iso dab da ita ya ce.
"Ashe baki da kunya? Salamatun ce kike yi wa waɗan nan maganganu na banza da wofi?? Ita sa'arki ce? Na ce miki ita sa'ar ki ce!!!"
Jikinta na wani irin ɓari ta girgiza kanta da sauri alamar a'a tana mai matsawa baya domin ba ƙaramin tsoro ya bata ba. Cikin ƙanƙanin lokaci tunanin ta ya sauya ta shiga kallon Alhaji Gimba a matsayin wanda ya zare domin ta gama yarda a ranta cewa tabbas ba shi ka ɗai yake ba, dole akwai wasu almatsutsai a kansa.
Ita da take gaggayawa Hajiya Salamatu magana bai taɓa ƙorafi ba shi ne yau zai yarfa ta yana neman ci mata mutunci.
"Ba zan ɗauka ba, ba zan lamunta ba kin ji na faɗa miki. Da ki saɓawa Hajiya Salamatu gwanda kin koma gidan iyayenki..."
Daga haka ya juya ya yi shigewar sa ya barta nan cikin tsananin mamakin da ya kusa ya kashe ta tsabar kaɗuwa.
Ganin ta tsaya ta kasa yin ko ƙwaƙwƙwaran motsi yasa Hajiya Salamatun ta kalle ta tare da nuna mata hanya ta ce.
" Ki bi nan, zaki ga ƙofa ta farko hannun daman ki shi ne za ki shiga."
Cikin rashin kuzari ta taka a hankali ta fara tafiya har ta isa ɗakin ta buɗe ta shige. Parlour ɗaya ne da bedroom a ciki Wanda suke ɗauke da furnitures masu kyau kala ɗaya.
Faɗawa ta yi kan kujerar parlourn da ƙarfi ta fashe da kuka. Tabbas a yau ta gama yarda cewa maganar da Aunty Halira take faɗamata cewa Hajiya Salamatu ba'a banza take zaune ba ta yarda da ita. Tabbas asiri ne wannan domin Alhaji ba zai taɓa yi mata haka ba. Kai! Biri ma yay kama da mutum. Ta ya ya ma za'a ce tana amarya amma ya tsallake ya baro ta ya ɗauko wannan jagwal ɗin ya taho da ita sannan idan ta kira shi ya dinga bala'i, idan ba asiri ba ne wannan da me za ta kira shi? Dole ta tashi tsaye ta ƙwaci 'yancin ta tun wuri kafin ta ji an ce ta yi waje.
******
Har gida suka zo suka samu Alhaji Ridwan wanda tun da suka iso yake ta rarrashi yana faman ba su baki akan su yi haƙuri a samu a sasanta tsakanin su da Alhaji Gimba.
Muhammad yau shi ne wanda ya dawo tamkar Mukarram domin har yau ya kasa daina mamakin cewa Alhaji Gimba wai shi ne ya shigar da Alhajinsu ƙara bayan duk irin abubuwan da ya yi masa a rayuwa.
Daƙyar suka samu ya haƙura akan za su shirya su je gidan Alhaji Gimban ko Allah zai sa a daidaita kafin gobe ta yi, domin ita ce ranar shiga kotu.
Muhammad ɗin ne ya ce.
"Amma dai wani wurin ya kamata ace mun haɗu domin zuwa gidan sa zai iya juyawa zuwa wani abu na daban..."
Alhaji Salisu ya ce.
"Haba Madu! Wai miye rayuwar duniyar nan ne gabaɗaya? Sulhu fa alheri ne, and taka ƙafar da za ku yi domin neman sulhun Allah zai ba ku lada, zuwa gidansa ba zai ƙara ka da komai ba kuma ba zai rage ka ba sai dai ma ka samu lada, shari'a saɓanin hankali ce, idan kasan farkon ta baka san ƙarshen ta ba. Saboda haka gidan shi zamu je yanzu."
Shiru Yaa Muhammad ɗin ya yi ba tare da ya ce komai ba suka ranƙaya suka nufi gidan Alhaji Gimban.
Sun jima sosai a parlourn baƙin sa suna jiran sa, kamar ba zai fito ba sai kuma gashi ya fito.
Tsaye ya yi ya shiga bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya yana mamakin tsaurin ido na su da har suka iya shigowa gidan sa suka zauna.
"Gimba..."
Saurin ɗagawa Alhajin Salisun hannun ya yi fuska a turbune ya ce.
"Dakata Yaya Salisu! Wallahy kai ma sai ne tsefe ka babu abin da ya dameni..."
Cike da mamaki Alhaji Mas'ood ya ce.
"Yanzu Gimba Alhaji Salisun ne kake cewa za ka tsere?"
Waigawa ya yi gun Alhaji Ridwan ya ce.
"Ai kai ne babban munafiki ma, wato shi ne za ka ce min abokan cinikayya ne za ka zo da su shi ne ka ɗebo maƙiyana ka shigo min da su har cikin gidana..."
Cike da takaici Alhaji Ridwan ɗin ya girgiza kan sa ya ce.
"Alhaji Gimba wai sai yaushe ne za ka canja? Yaushe za ka girma ka gane cewa kuskure kake aikatawa? Tsawon shekarun da muka shafe a tare tun lokacin ƙurciya har zuwa yau ya dace ace ka ko yi sanin miye zaman tare irin wannan yake nufi. Mun yi kuka tare munyi dariya tare, a makaranta ajinmu ɗaya, garinmu ɗaya, duk wata wahala tare muka sha, bayan mun dawo Mas'ood ya janyo mu cikin kasuwancin da har yau sanadiyyar sa ne muke cikin wannan rigar..."
" Kake ciki dai kai! Domin kai ne wanda zuciyarsa ta mutu da baka iya tunanin komai sai abin da Mas'ood ɗin ya tsara maka. Ni kuma a yanzu na wuce wannan lokacin... "
" Duk da haka dai! Idan mutum yasan halacci ya kamata a riƙa tuna baya...."
Jinjina kai Alhaji Salisu ya yi ya ce.
"Ai duk abin da mutum ya zamo a rayuwar nan to babu wanda ya yi masa sai Allah, Allah ne kaɗai mai azurta bawansa idan ya so ya kuma hana shi a lokacin da yaso. Allah ne ya gina ka ba mutum ba, babu wanda kuma ya isa ya yi maka abin da Allah bai yi maka ba. Ba wai mun zo nan domin neman wata rigima ko tayar da husuma ba, mun zo ne domin mu baka haƙuri akan abin da ya faru. Tabbas in don kuskure sun aikata kuskure na shigar da Faris ƙara domin ni kaina na san har abada Faris ba zai taɓa iya cutar da Maryam ba...."
"Shin yanzu duk wannan kewaye-kewayen da kuke mi kuke so ayi?"
Kallon kallo suka fara jin wata irin tambayar da ya jefa musu wacce da alama akwai wani abin da yake ransa.
Runtse ido Yaa Muhammad ya yi sannan ya buɗe ya kalle shi ya ce.
"Alhaji! Mukarram ya yi kuskure na shigar da Faris ƙara, wanda kafi kowa sanin halin sa game da zafin rai..."
Cikin ɓacin rai ya wani ɗaga murya yana yi musu wank kallon ya ce.
"Zafin ran ya ci ƙaniyar sa! Na ce yaci ƙaniyar sa! Idan ana maganar fusata da nuna ƙarfin iko shi ɗin har waye shi? Miye ya isa ya yi? Waye shi da zai saka yarona ya kwana a police station? Ba zan taɓa yafewa ba..."
"Alhaji kada ka manta cewa har yanzu Mukarram shi ɗin yaro ne. Hankalin ka da nasa har abada ba zai taɓa zuwa ɗaya ba. Don Allah ina roƙon ku ina neman afuwa da gafara, don Allah ka yi haƙuri ka janye ƙarar nan da ka shigar..."
Wata irin dariya ce ta ƙwace masa jin yanda Muhammad ɗin ya saukar da kai yana roƙon sa. Shiru suka yi suna ta kallon sa wanda daga Muhammad ɗin har Mubarak ji suka yi tamkar za su fashe saboda baƙin ciki. Sosai Mubarak yake ta godewa Allah a ransa na cewa gwanda da Mukarram ba ya wurin domin yasan ba zai taɓa iya sarrafa fushinsa ba akan wannan abun.
Sai da ya gama dariyarsa son ransa sannan ya ce.
"Wai kun tsorata ne har haka? Tsoron shari'ar kuke ko kuma tsoro kuke cewa ba za ku iya dani ba?"
Sai Yanzu Alhaji Mas'ood ɗin ya jinjina kansa sannan ya buɗe bakin sa ya ce.
"Eh haka ne! Mun tsoro ta kuma ba zamu iya ja da kai ba. Matuƙar dai hakan zai baka farin ciki a ranka to ni ɗin nan da ahlina muna baka haƙuri domin mun tsorata domin mun san ba zamu iya dakai ba. Ka yi haƙuri ko don albarkacin tarenmu na baya. Don Allah don girman Allah ka yi haƙuri..tsawon shekarun da muka kwashe a tare idan yau Duniya ta ji ta ga kuma muna shari'a ai sam abun bai kawo kallo ba."
"Ka yi haƙuri Gimba, ka yarda cewa wannan duk shaiɗan ne yake so ya ga ya farraqa tsakaninmu..."
Cewar Alhaji Ridwan yana mai ƙara saukar da murya alamar ban haƙuri, da haka dai suka har suka yi nasarar shawo kansa munsan da ya ji Alhaji Mas'ood ɗin ya buɗe baki da kansa yana bashi haƙuri alamar ya karaya, ko ba komai yau za ta kasance ranar alfahari ranar da ba zai taɓa mantawa da ita ba cewa Mas'ood ya roƙeshi alfarma da magiya da komai, wannan kaɗai ya nuna cewa ya faɗi kuma shi ne ke da nasara akan sa.
Bayan ya gama jin kokensa cike da alfahari ya shiga zaga parlourn yana faɗin.
"Na ji, na kuma yarda zan janye ƙara,amma kuma ku sani ina da sharaɗi..."
Ido suka zuba a tare suna kallon sa tare da baza kunne domin jin wane irin sharaɗi ne.
"babu ni babu ku har abada, babu ruwanku da rayuwar iyalina nima haka, idan kuka sake shiga harkar gidana wallahy ba zan ƙyale ba, ku je kuyi harkar gabanku in yi tawa. Sannan magana ta gaba kuma, ina so sai kun kawo min wannan rasa kunyar ya faɗi a gabana ya bani haƙuri sannan zan yarda in janye ƙarar nan, idan ba haka ba zan haƙura ba. Sannan dole za'a biya ni duk kuɗaɗen da na kashe wurin shigar da ƙara da kuma kuɗin lauyoyi da na biya..."
Abubuwa ya lissafo wanda duk wanda ya ji yasan cewa fitina ce kawai yake nema da rashin son zaman lafiya.
Bayan sun gama jinsa Abbah ya jinjina kansa daga ƙarshe ya ce.
"Duk mun ji, mun kuma amince in sha Allahu, Mukarram zai zo ya durƙusa a gabanka ya baka haƙuri, ko ba komai ai kai tamkar uba kake a gare sa...."
"Aa kam! Da ne akayi wannan Alhaji Mas'ood, yanzu kam daga ni har ku mun san cewa wannan kalmar Ƙarya ce domin abubuwa sun faru da dama."
Da wannan suka kai ƙarshe cewa Mukarram zai dawo ya ba shi haƙuri duk da cewa zukatansu na cike da shakku da rashin hankali na neman hanyar da za su bi su lallaɓo Mukarram ya dawo ya ba shi haƙuri, ba bayar da haƙurin ne tashin hankalinsu ba, a'a cewar da ya yi sai ya durƙusa a gaban sa.
Gida suka koma direct wanda sai da suka yi har sallar isha sannan suka shiga gidan, Yaa Muhammad bai wani jima ba ya ɗauki Aunty Amina suka tafi gida.
Alhaji Mas'ood kuwa, tare da su Anaam suka zauna zaman cin abincin daren wanda sai yanzu ne Anaam ɗin ta haɗu da Rabi'a, ko kallon inda take ba ta yi ba tun da suka zauna, sai bayan ta ga su Ammien sun iso table ɗin ne ta kalli Anaam ɗin ta ce.
"Sis Anaam ashe kin dawo? Welcome back..."
Kallon su Abbah ta yi a kaikaice sai kuwa gashi ashe ita ɗin suke kallo, hakan yasa ta jinjina kai tare da ƙago wani murmushin dole ta ce.
"Uhm! Tenx.."
Murmushi Mubarak ya yi yana mai juyawa abincin da ke gaban sa da spoon ya ce.
"Hmm! Ai ni Diyana ta bani mamaki..."
Shagwaɓe murya ta yi tare da wani karyar da kai ta ce.
"Abbah ka ce Yaa Mubarak ya fita harkata....tauyayi..."
Kallonta ya yi, sai kuma ya kalli Mubarak ɗin ya ce.
"Ka yi abin da yake gabanka. Sannan ka kwanta da wuri gobe ka wuce Gusau."
"Alhaji yanzu dole sai Mukarram ɗin ya dawo ƙasar nan? Kafa san yanayin aikin sa..."
"Ajiye spoon ɗin hannun sa ya yi ya kalli Ammien ya ce.
" Hajiya Nasmah ya zan yi da jidalin Alhaji Gimba? Dole hakan ce za ta faru, an jima idan na kambala abin da nake na nutsu In Sha Allahu zan kira sa da kaina. Hakan da zamu yi ko kuma ince da muka yi ba wai yana nufin mun faɗi bane. Zaman lafiya yafi zama ɗan sarki, and ni Alhaji Gimba har gobe har abada komai zai faru shi ɗin abokina ne. Sai dai iyakar da ya yi mana a tsakaninmu ina so don Allah a kiyaye, ya kamata a girmama muradinsa tun da yace baya so..."
"Alhaji Salamatu ita ce wacce take kirana, ba zan iya ganin ta kirani na yi avoiding call ɗin ta ba..."
"To ya za'a yi Hajiya Nasmah? Mafita ake nema domin a samu a zauna lafiya."
"Allah yasa mu dace."
"Ameen..."
********
Washegari koda Anaam ɗin ta shirya ta fito da nufin fita lectures ta nemi Anasi ta rasa, sai dai wani new da ta tarar yana jiranta wai shi ne sabon drivern ta.
Ciki ta koma tana faɗin.
"Ammie ina Anasi? Ya naga wani daban?"
"Ai tun ranar Alhaji yasa aka sallame sa..."
"But Ammie Anasi fa bashi da laifi! Ni ce nan na ba shi umurni nace kada ya sanarwa kowa inda nake. Miye laifin da da za'a kore sa? Ni wallahy shi nake so Ammie, kawai a dawo min da shi..."
Ciki Ammien ta koma ba tare da ta ƙara tanka mata ba. Bayan ta tabi ta ɗauki wayar Ammien ta kira mubarak idon ta cike da hawaye ta ce.
" Yaa Mubarak don Allah a dawo da Anasi bakin aikinsa, ba laifin sa ba ne, ni ce mai laifin..."
"To ki sanarwa Alhaji mana. Ni miye nawa a ciki tun da baki ne na kore sa ba?"
Girgixa kanta ta yi ta ce.
"Yaya Mubarak na ɗaukarwa kai na alƙawarin cewa ba zan ƙara musu da umarnin Abbah ba,amma dai dan Allah a dawo da Anasi bakin aikinsa, yana da iyali, yara da mata biyu, please Yaa Mubarak..."
"Okay..."
"Na gode Yaa Mubarak, Allah ya tsare yasa a sauka lafiya."
"Amin, bye."
Koda ta koma ta shiga motar sai ta tarar da Rabi'a zaune a ciki itama da alama lectures ɗin za ta tafi tun da har ta ganta a ciki kuma ga kayan karatu rungume a jikinta.
"Ni dan Allah ki yi sauri ki shigo idan za ki je mu tafi, kin wani tsaida mutane har an kai ga shiga lokaci na..."
Cike da zallar mamaki Anaam ɗin ke kallon bakin Rabi'a yanda take maganar cike da renin wayau da isgilanci sai kace motar gidan ubanta.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*PAGE 29*
Babu abin da zuciyarta ke saƙa mata da ya wuce kawai ta wanke mata fuska da mari,amma kuma tuna alƙawarin da ta ɗaukar wa kanta yasa kawai ta shiga motar kurum ba tare da ta tanka mata ba.
Har suka school ɗin babu wanda ya yi magana a cikin su. Anaam na sauka suka haɗe da Na'ima Hassan hakan yasa duk ɓacin ran da ta ɗebo ta ji gabaɗaya ta nemi shi ta rasa, Allah ya sani tana ƙaunar Na'ima domin bata da hayaniya sannan ba ta da kwashe-kwashen ƙawaye ko kuma samari.
"Mutuniyar dai kam yau an saurin zuwa."
Murmushi Anaam ta yi tana jinjina kanta tace.
"Yes! Saboda na koma gida and yanzu kinga no need na tsaya jiran yara kafin na iso nan..."
"Allah sarki! To ya su Mama?"
"Lafiyan su ƙalau, Abbah ya ce yana gaishe da ke."
Dariya Na'imar ta yi ta ce.
"Haba dai! Ai sai dai ni na gaishe da shi..."
Rabi'a tsaye ta yi daga can nesa da su tana kallon yanda suke ta fira cikin nutsuwa suna dariya, tuni sai taji abin ya baƙanta mata rai, ko ya ya ne atleast ya kamata ta nuna muhimmancin ta gare ta na kasancewar ta 'ƴar uwar ta. Amma shi ne ta yi kamar ba ta ganta ba ta yi wucewar ta.
******
Sai da a ka kwana biyu sannan Alhaji Mas'ood ya samu courage ɗin Kiran Mukarram ya sanar mai abin da yake so ya yi.
Cikin wani irin baƙin ciki mukarram ɗin ya ce.
"Alaji Ka faɗa masa cewa na ce hauka yake...Hauka ya fara duk a gamata..."
"Mukarram!"
"Na'am Alaji..."
"Tun farko ba sai da na faɗa maka cewa ka bani hankalinka da nutsuwarka ba? Durƙusawa wada ba gajiyawa ba ne Mukarram, just kasan yanda za ka yi ka yi arranging zuwanka ka zo ka bashi haƙurin kawai a wuce wurin. Wannan umarni nake baka ba shawara ba..."
Girgiza kai kawai ya yi tare da haɗiye sauran maganar sa ya ajiye wayar gefe. Mukarram sam bai ɗauko hali da rayuwar sa ba, da ya biyo hali irinsa da bai shiga yin irin wannan fushin ba marar amfani da saka dana sani.
Ya ji ma zaune a rumfar shan iskar dake cikin gidan nasa sannan daga ƙarshe ya tattara ya koma ciki wanda a lokacin kusan sha ɗaya saura na dare ake magana.
*******
Maheer