Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 23
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 23: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 23. Zaune yake a wata rumfar shan iska dake bakin ruwa shi da Hamad…
3,368 words
Zaune yake a wata rumfar shan iska dake bakin ruwa shi da Hamad suna tattaunawa akan aikin da suka gabatar yau ya yin da Hamad ke rungume da system yana shigar da bayanan wanda Maheer zai haɗa ya tura a can main kamfanin na su dake Oman. Sun ɗauki lokaci mai tsawo suna aikin sannan daga ƙarshe Hamad ya ce.
"Na san cewa baka da kirki a wasu lokutan, but ziyartar Dinaratu da ka yi yasa na ji farin ciki sosai a raina. Hatta su Hajiya sai da ta sanar musu akan yanda abin ya yi mata daɗi..."
Lokaci ɗaya Maheer ɗin ya ji ƙirjinsa ya buga, fatan sa ɗaya Allah yasa kada ace Dina ta faɗa masa cewa ya haɗu da Anaam.
"Miye ka wani ƙura min ido? Wato da ka rasa yarinyar shi ne ka lalubo Dina ka ziyarce ta. Ni na san fa baka haɗu da ita ba, da kun haɗu da yanzu zancen ya canja..."
Share sa Maheer ɗin ya yi tamkar bai ji abin da yace ba sai ma wani zancen da ya ɗauko ya banzarar da wancan ya ce.
"Hayam called me..."
Cike da mamaki Hamad ya ce.
"Miye ta faɗa maka?"
"Ta rasa ina kasa gaba Hamad, idan ta yi maka maganar turawa sai ka ce akwai abin da kake jira. Why?"
"Ni fa ƙa'idojin Babanta ne sam tsarin bai mini ba, ya cika sharɗoɗin ƙaniya, ko waya wannan baya barin ta tana riƙewa..."
"Mun yi magana da su Alhajinku jiya, yau sun je gidan na su har an nema maka aurenta an biya sadaki,In the next 3month coming za'a yi bikin. Ni bazan bari in zama mutumin banza ba idan har kai mutumin banza ne. Ka gama ɓatawa yarinya lokaci ta mutu a kanka tsawon 3years yanzu ka zo kana kula wata ni ba zan yarda da wannan ba..."
Wata irin zabura ya yi ya miƙe tsaye yana mai yi wa Maheer ɗin wani kallon Ƙarya ma kake ya ce.
"Da izinin uban wa aka nema min auren na ta har aka biya sadakin?"
Ba tare da ya kalle sa ba ya ce.
"Da izinin iyayen ka da kuma ni aka nema maka..."
Wayar shi dake kan table ya ɗauka ya kira ƙanin sa Aliyu ya tambayesa, sai ga shi ya tabbatar masa da an yi hakan, still ya ƙara kiran Hajiyar sa itama ta tabbatar masa. Yanke kiran ya yi cikin ɓacin rai ya wani cakumi rigar Maheer ɗin ya ce.
" Kai waye da har za ka mini gatsali a cikin rayuwa ta? Waye kai da har ka isa kasa a nema min auren da ban yi niyya ba? Kai ɗin nan da ka kasa cika umarnin mahaifiyarka ka ruguza rayuwar mace saboda son zuciya har ka isa ka ce za ka shiga gaban al'amari na?"
"A a Hamad! Ka fa yi niyyan aurenta domin soyyayar 3years ba wasa ba ce. Na sani...ba wai ka yi baya bane don kawai matsalan Babanta, ka yi baya ne don an ce maka an yi mata miji, shi ne abin ya baka haushi. Yarinyar nan ta yi iya yinta don kawai taga cewa kak ne wanda ka same ta, saboda tana son ka , haka ta bijirewa umarnin su saboda tana son ka, ta jure sosai ta tsaya har sai da taga maganar aurenta da waccan ta ruguje ƙarshe ta nemeka kai kuma sai kace wai ka haƙura da ita. Hakan ba daidai bane Hamad. Kada ka guje mata a lokacin da ta yarda cewa kai ne mijin da ya dace da ita. Na san cewa ni mai laifi ne, amma babu ta inda laifina ya shafi nema maka auren Hayam da muka yi. Idan Kaga za ka iya sai ku ci gaba, idan kaga kuma cewar you can't continue with her, za ka iya faɗawa su Alhaji sai su koma gidan iyayenta su ce ka fasa a bai wa wani."
Yana gama faɗar haka ya saka hannayensa ya ƙwace rigar sa sannan ya kwashe kayansa ya wuce wurin kwanan sa.
Ya jima a inda ya bar sa bai iya motsa ko ɗan yatsan ƙafansa akan yan da abun ya yi masa ba daɗi domin sam furucin da ya yi bai kamata ba. Maheer ne fa. Sam bai kyautu ace ya biye zuciyar sa ba da har ya faɗa masa wannan maganar domin jarabawa ce wacce ba ta ƙarfin shima a jarabce shi ba.
Daƙyar ya samu ya iya kai kansa gidansa ya faɗa kan cushion ya yi shiru yana nazarin maganganun Maheer ɗin. Ya jima a zaune domin bai samu ya runtsa ba ko kaɗan har misalin ƙarfe biyu na dare wanda hatta kakin da ke jikin sa bai samu ya cire ba.
Ji ya yi ba zai ma iya bari gari ya waye ba, hakan yasa ya miƙe ya fito ya ja motar sa sai gidan Maheer ɗin daman ba nisa ne da su ba.
Koda ya shiga gidan ga mamakinsa ko'ina ya duba baya nan. Dawowa ya yi ya tambayi mai gadi ya ce masa Ina Maheer. Kai tsaye yace masa ai ya ɗauka yasan da tafiyar tasa zuwa Oman hakan yasa bai sanar masa ba da ya buɗe masa gate a tunanin sa akwai abin da yake so ya yi duk da cewa Maheer ɗin baya nan.
Ransa a jagule ya koma cikin gidan ya kwanta akan gadon sa. Tabbas ya gama ɓata masa rai da har zai ɗauki hanya cikin daren zuwa Oman ba tare da ya sanar masa ba.
******
Koda gari ya gama haske Mukarram ya jima a gidan. A dining room suka tarar da shi zaune yana breakfast.
Gabaɗayansu babu wanda bai yi mamakin ganin sa ba musamman Alhaji Mas'ood wanda ya tuna yanda suka ƙare a daren jiya.
"Ya naga duk kun tsaya kuna mamakin gani na? Ba abin mamaki ba ne idan har mutum ya cika mai biyayya kuma yana so ya gama da iyayensa lafiya....."
Agogon wayarsa ya duba sai kuma ya kalli Mahaifin nasa ya ce.
"Alaji naga ƙarfe bakwai da minti biyar, Alhaji Gimba ya isa farkawa kuwa?"
"Eh to, kafin ka kambala abin da kake ka isa gidan ya isa farkawa...Allah ya yi maka albarka. Na gode sosai da ka ji magana ta...."
"Kai...Haba Alaji! Wannan wace magana ce kake haka? Dan Allah ka daina. In Sha Allahu yanzu zan tashi na tafi."
"Aa! Tare zamu tafi, kamar yanda yace, a gaban kowa yake so ka bashi haƙuri..."
"An gama."
Yana gama faɗar haka ya miƙe ya nufi ciki ya yi wanka ya shirya ya fito.
Suna shirin fita sai kiran Muhammad cewa Amina ta haihu ta samu ɗiya Mace. Saboda haka su ɗan ƙara mi shi awa biyu yana zuwa, sannan dan Allah kuma su Ammie su yi su zo.
Koda ya sanar da su wannan maganar har Anaam ta kai makaranta kuma gashi ba waya a hannun ta ballantana a sanar mata. Sai dai kuma tuna cewa suna school ɗaya da Rabi'a yasa ta kira ta tace ta sanar mata cewa Amina ta haihu idan sun fito daga can kawai su wuto gidan Aminar.
Sai da su Mukarram ɗin suka jira sa har misalin 12pm sannan sai ga shi yace musu su haɗu can ɗin.
Koda suka shiga gidan Alhaji Gimban yana zaune ya hakimce akan kujera sai wani huhhura hanci yake yana ji har cikin ransa cewa shi ke da nasara.
Su ne suka fara bashi hannu suka gaggaisa sannan mukarram wanda zuciyar shi ke fal farin ciki musamman ƙaruwar da Yayansa ya samu yasa kai tsaye ya faɗi akan ƙafar Alhaji Gimba wanda sai da ya ba wa kowa mamaki ya shiga magiya sosai kamar da gaske yana faɗin.
"Don Allah Daddy ka yi min afuwa ka yafe min! Tabbas duk abubuwan da na yi maka na yi ne bisa kuskure da ƙurciya kuma in sha Allahu na yi alƙawari ba zan sake ba, ina neman afuwa dan Allah. Kai ɗin nan tamkar uba kake a wurina wanda har abada ba zan canza hakan ba..."
Murmushi Alhaji Gimba ya fara domin hakan ba ƙaramin faranta ransa ya yi ba musamman irin magiyar da ya hau yi wanda komai iya kushenka ba za ka ce na Ƙarya ne yake ba.
Ajiyar zuciya ya sauke daga ƙarshe sannan ya ce.
"Shi ke nan. Jiya na ga alert da dare, Yanzu komai ya ƙare, ina fata zamu girmama ra'ayin juna."
"In sha Allahu. Muna godiya."
Har a mota Su Alhaji Ridwan ba su daina mamakin mukarram da kuma Alhaji Gimba ba, sun ɗauka cewa sai an yi ba daɗi amma kuma sai ga shi sun ba kowa mamaki wanda hakan ita ce rabuwa mafi daɗi da suka yi ba tare da wata matsala ba.
******
Tana shiga gidan Nene suka ci karo da Nene a parlour ta ce mata.
"Anaam! Baki wuce gidan yayan naki ba ashe?"
Tuni hankalin Anaam ya tashi ta wani gwalo ido ta ce.
"Miye ya faru Nene?"
Kallon Rabi'a ta yi ta ce.
"Ba kece na ji Hajiya ta kira ɗa zu ba tace ki sanarwa Anaam Amina ta haihu idan kun gama lectures ku wuce ta can?"
Hannu ta saka kamar da gaske ta dafe goshin ta sannan ta kalle su ta ce.
"Ki yi haƙuri, wallahy na manta ne..."
A xuciye Anaam ɗin ta kalle ta tace.
"Ba wani mantawa da kika yi kawai tsabar wulaƙanci ne."
Daga haka ta ja mugun tsaki ta shiga shaf-shaf ta ajiye kayanta ta shirya ta fito ita da drivern suka wuce, Rabi'a da ta tsaya yin wanka koda ta fito ga mamakin ta sai ba ta tarar da ita ba har ta wuce. Hakan yasa ta ciro wayar ta ta kira Abbah tana faɗamai cewa wai sun shirya za su tafi gidan Aunty Anaam ta wuce ta bar ta. Haƙuri kawai ya bata yace ta jira idan ya dawo sai je ya ajiye ta itama. Cike da takai ci ta koma cikin gidan domin ba abinda ta so kenan ba. Tana shige wa ta kira Umma ta sanar mata, shi ne tace itama ta bari sai za su school da safe tace driver ya wuce su barta wanda ta sani hakan ba ƙaramin ciwo zai yi mata ba.
Tana nan ta ƙume a ɗaki da baƙin ciki ya yin da Anaam ke can ranta fes musamman da ta rungume babyn a jikinta tana ta wani murmushi ta ce.
"Yaa Amina wannan ɗin tawa ce, ni ce zan zaɓa mata suna...kin ji dan Allah Yaa Amina ta..."
Gabaɗaya mutanen da ke ɗakin waɗanda suka haɗa harda wasu en uwan Yaa Aminar suka fashe da dariya sannan Aminar ta ce.
"Waye zai hana miki zaɓa mata suna Anaam? Ai ko Yaa Muhammad bai isa ba ballantana ni."
Washe baki ta yi ta ce.
"Da gaske yaa Amina?"
"Da gaske nake miki Anaam.."
"To sunan ta Maryam Diyana."
Jinjina kai Aunty Amina ta yi ta ce.
"Masha Allah Alhamdulillah! Allah ya raya ta da imani ya albarkaci rayuwar Maryam Diyana."
Da Amin duk suka amsa sannan daga ƙarshe ta miƙe tare da Babyn ta ce.
"Yaa Amina bari in je gun Ammie in faɗa mata sunanta."
"Tau Anaam, sai kun dawo."
Fitowa ta yi tana tafiya a hankali tana jijjiga babyn wanda tana yi tana kallon fuskar ta tana ta murmushi tana yi mata addu'a.
Koda ta shiga ta tarar da Ammie da wata mata da su Fatima sai su Faryat dake ta uban rashin ji ana musu magana.
Zaunawa ta yi ta gaishe su sannan ta ce.
"Ammie wai kin san marar mutuncin Yarinyar nan ba ta faɗamin Cewa Yaa Amina ta haihu ba sai da muka shiga gida Nene ke faɗamin..."
"To ki yi haƙuri, yanzu ba gashi kin sani ba har kin zo..."
"Hmm! Ai wallahy yau-yau ɗin nan zance Yaa Muhammad ya siyo min waya ba sai gobe ba."
Farouk da ya leƙo ɗakin yanzu ya ce.
"To ai Daddynma yana parlourn sa yana kiran ki, yace na kira ki Aunty Anamee."
"Da gaske?"
"Zo muje ki gani..."
A tare suka shiga parlourn still tana rungume da Little Maryam a ƙirjinta tace.
"Yaa Muhammad ina wuni...congratulations."
"Thank you Anaam. Ya kike lectures?"
"Lafiya lau Yaa Muhammad...sunana ne na sanya mata Maryam Diyana."
"Masha Allah. Allah raya mana ita amin..."
"Daddy to Diyana zamu kira ta ko ya ya?"
Cewar Farouk jin cewa wai sunanta Maryam
"kana ji Farouk? Ka tafi ka ɗan bamu wuri zamu yi magana da Auntynka."
"Okay Daddy..."
Yana fita ya kalleta ya ce.
"Maryam..."
Kallon sa ta yi ta ce.
"Na'am Yaa Muhammad."
"Akwai Sauban da ya zo domin ya ganki..ina fata ba wata damuwa? Ina fata za ki bashi kaɗan daga cikin lokacin ki?"
Tuni annurin da ke kan fuskarta ya ɓace zuwa damuwa wacce cikin sakanni ta yi ƙoƙarin daidaita kan ta.
"Anaam....ko akwai wata damuwa?"
Saurin girgiza kanta ta yi ta ce.
"Ba komai Yaa Muhammad..."
"yana waje, zai shigo yanzu, ki ɗan bashi 15-30 minute haka."
"Okay..."
Tun da ya fita ta kasa motsawa daga inda take zaune, gabaɗaya zuciyarta ta tsinke. Ta ma kasa rarrabe shin a wanne tsakani take. Da gaske wani ne Yaa Muhammad ya taho da shi domin ya ganta? To wane irin gani kenan yake nufi?
Tana tsaka da tunani ta ji sallamar sa mai cike da amo mai nutsuwa. Sai da ya nutsu sosai sannan ya jiyo muryarta can ƙasa tana amsa sallamar.
Har ya samu wuri ya zauna bata iya ɗago kanta ta kalle shi ba.
"A haka zamu yi maganar Maryam? Ai ya kamata ki ɗago kan ki ki kalleni domin kin san waye ya zo gare ki."
"Kunne ne yake ji ba ido ba Malam..."
Jinjina kansa ya yi still ba tare da murmushi ya ɓace daga fuskar sa ba ya ce.
"Haka ne kuma, amma dai duk da haka ina neman alfarma da ki ɗago ki kalle ni koda sau ɗaya ne..." ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*PAGE 30*
Hamad
Hankalinsa bai kwanta ba sai da ya ga ya sauka gidan su Maheer ɗin wanda Maami ba ƙaramin mamakin ganin sa ba ta yi ba a wannan lokacin, domin Maheer ya faɗa mata cewa Hamad ɗin ne ya baro a matsayin wakilin sa kafin ya ganta ya koma amma kuma abin mamaki sai ga shi kwana ɗaya ya biyo sawun sa.
Sun ji ma a parlour suna fira amma kuma duk tsayin zaman sa har yanzu bai ga Maheer ba. And baya so ya tambaya domin kada ma ta yi zargin wani abun, ga shi tun jiya ya kasa samun wayar sa wanda ya rasa dalilin hakan.
"Maheer fa yana gidan su Naana tun safe, may be bai sanar maka ba ko?"
Murmushi ya yi tare da jinjina kansa ya ce.
"Eh..ya sanar min Maami, cewa na yi bari na fara gaishe da ke kafin na isa can ɗin."
Cike da jin daɗin maganar sa ta ce.
"Allah sarki! Na gode Hamad, Allah ya yi muku albarka yasa ku gama da duniya lafiya."
"Amin Mami..."
Daga haka ya miƙe yana faɗin.
"Bari na je Mami, daman ba jimawa zan yi ba in sha Allah zan Koma..."
"To ba damuwa, Allah ya tsare ya kai ka lafiya. Muna godiya."
Har ya iso gidan su Naana bai daina tunanin abin da ya wakana a tsakanin su ba daren jiya.
Ɗakin sa da ke gidan ya shige direct bayan ya gama gaisawa da su Abiyh wanda suka cika da murnar ganin sa. Duk wanda ya san Maheer a yanzu yasan waye Hamad a wurin sa, hakan yasa yake samun kyakkyawar tarba a duk lokacin da ya zo gare su.
A hankali ya taka har zuwa gefen gadon da yake kwance. Babban hoton da ke rungume a ƙirjinsa wanda ya yi bacci da shi ya saka hannun sa a hankali ya zare. Hoton mahaifinsa ne wato Dr. Tahameer wanda baya taɓa rabo da shi a koda yaushe.
Yana tsaka da kallon hoton da yau ya zamto masa tamkar wani sabon abu yaga Maheer ɗin ya miƙe a hankali ya taka ya shige toilet, wanka ya yo ya fito ya shirya cikin simple wears sannan ya zauna a sofar da murmushi a fuskar sa tamkar wani abu bai faru a tsakanin su ba ya ce.
"Tabbas na san za ka zo abokina..."
Cike da jin ba daɗi a ransa Hamad ɗin ya ce.
"I'm sorry Maheer! Ban san cewa kalamaina za su yi tsauri sosai har su ɓata maka ba..."
Ƙafarsa ya ɗaga ya ɗora ta akan ɗaya sannan ya ƙara yin baya sosai ya yi resting bayansa yana kallon Hamad ɗin ya ce.
"Ko ka ɗan baka yi kuskure a maganganunka ba Hamad, sai dai wuri ɗaya nake so na yi maka gyara shi ne cewa da kayi na aikata son zuciya. Daukar fansa ta ba son zuciya ba ne Hamad, da gaske nake kuma akan gaskiya ta nake,...."
hannu ya miƙa ya ɗauko hoton mahaifinsa ya ɗaga da hannu ɗaya sannan ya yi using ɗayan hannun sa yana nuna hoton ya ce
"shin kasan waye wannan a wurina kuwa Hamad? Wannan shi ne komai nawa, ban san kowa ba idan ba shi ba, na rayu da shi tsawon rayuwa a matsayin uwa da uba kasancewar rasa kulawar mahaifiya na tsawon shekaru dalilin matsalar ƙwaƙwalwar da ya same ta, ya kula dani ya bani tarbiyya, ya so ni fiye da rayuwar sa ma,shi ɗin kawai likita ne mai ceton rayuka, mutumin kirki ne, amma haka suka ɓata masa suna sannan suka kashe shi daga ƙarshe, son ɗaukar fansa ta ba son zuciya ba ne Hamad, ni ka ɗai nasan raɗaɗin da nake ji akan rasa mahaifina da na yi, ina kewar sa sosai wanda har abada ba zan daina ba, ba za ka taɓa sanin irin raɗaɗin da ke zuciyata ba domin har yanzu kana tare da mahaifinka,hakan yasa ba zan taɓa jin na huce ba har sai na ga mutuwar Mas'ood Galadima. Sannan maganar da ka yi na cewa na ruguza rayuwar mace, tabbas har abada ba zan daina danasanin wannan ba domin na cutar da ita,duk da cewa mahaifinta ne wanda ya kashe min mahaifina, sam banda niyyar cutar da ita ko kaɗan, abun da ya faru a wannan daren har yau danasani nake Hamad, kuma In Sha Allahu zan bata haƙuri na nemi yafiyarta, Allah ma muna yi masa laifi kuma ya yafe mana, ballantana mu 'yan adam. Sai dai kuma ko gobe na samu wata damar tabbas zan kashe sa, shi ne maƙiyina. Ya rage naka ka ɗauke ni mai son zuciya ko akasin hakan."
Miƙewa Hamad ya yi yana jinjina kansa tare da matse hawayen idanunsa sannan ya sake dawowa ya zauna suna facing juna kamar ɗazu ya ce.
"Maheer...tabbas ban san zafin rasa mahaifi ba, amma a iya zamanmu da kai na fahimci irin ƙunci da raɗaɗin da ka ke ji. Ka yi haƙuri Maheer,a yanzu da za ka ɗauki maganar Mahaifiyarka ka bar komai ya wuce da sai ya fiye maka duk wannan. Ina sane da sabbin gang ɗinda ka biya a Abuja domin su shirya kama maka Alhaji Mas'ood don kawai ka kashe shi da hannunka. Ina roƙon ka Maheer dan Allah ka janye daga wannan ƙudirin. Ka bar wa Allah shi ne wanda zai saka muku da zaluncin kashe sa da ya yi. Idan ina kallon ka ta wannan fuskar ni kaina kana bani tsoro, kai ɗin ba Maheer ɗinda na sani ba ne, ka canja sosai, idan har mahaifin ka shi ne komai naka ita ma mahaifiyar ka a yanzu bata da wani wanda ya fiye mata kai bayan iyayenta...."
"Wutar da ke ci a cikin ƙirjina ba za ta taɓa yin san yi ba Hamad har sai ranar da na kashe sa da hannu na."
Shiru Hamad ɗin ya yi na tsawon lokaci tare da ƙura masa ido yana kallon sa tamkar zai karanto abin da yake ɗauke a allon fuskar sa sannan daga ƙarshe ya ce.
" Ni zan koma, ya rage naka ka auna ka ga abin da yafi cancanta."
********
Tsawon kwanaki uku kenan ana ta hidimar haihuwar Amina wanda har 'yan uwanta sun zo daga Gusau.