Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 24
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 24: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 24. Anaam ma sha'anin gabanta kawai take, tun ranar da suka gaisa da…
3,361 words
Anaam ma sha'anin gabanta kawai take, tun ranar da suka gaisa da Sauban bata sake ganin sa ba, haka kuma babu wanda ya yi mata zancen sa har Yaa Muhammad ɗinda ya kawo sa. A ranta ba ta za ta iya cewa ga abin da take ji ba dangane da shi, a irin zantukan da yazo mata da su tabbas sun yi kama da wanda yake neman aure, abin da ta kasa ganewa shi ne, anya Yaa Muhammad ya faɗa masa wacece ita kuwa? Da gaske sun faɗa masa cewa ita ɗin ba cikakkiyar mace ba sannan ba za ta iya haihuwa ba har abada? A yanxu fa ta kasance cikin sahun matan da ake kira da Juya wato wacce ba ta haihuwa. Idan har yasan da wannan mi zai sa ya aureta bayan ga mata nan bila adadin ga duniya waɗanda suka kasance cikakkun mata waɗanda za su iya haihuwa.
Da wannan tunanin take kwana da shi take tashi a ranta, aure sam baya daga cikin Layin ta, amma dai idan iyayenta suka tsaya akan hakan, lallai ba za ta iya bijire musu ba.
Yau ma sai da ta kai har bayan Magrib a gidan Aunty Amina, har ta ce a nan za ta kwana sai kuma daga baya ta canja shawara ta ce gida za ta tafi.
Koda suka iso Abbah yana zaune wanda sai a lokacin yake cikin abincin dare. Zaunawa ta yi a kusa da shi kasancewar yau akan carpet yake zaune ƙasa yana cikin abincin cikin nutsuwa, tana gama gaishe da ta fiddo sabuwar wayarta da Yaa Muhammad ɗin ya siyo mata kamar yanda ta buƙata ta shiga what'sapp ɗinta tana chart da Aunty Na'ima da kuma Yaa Mubarak da yake Gusau.
Tana nan har ya kambala sannan ya kalleta cikin nutsuwa ya kira sunanta ta amsa sannan ya ce.
"Muhammad ya gabatar min da yaron da ya zo da buƙatar cewa yana so zai aure ki, ni ne na bashi izinin cewa yaje ya ganki, idan Allah yasa kun daidaita shikenan."
Shiru ta yi tare da sadda kanta ƙasa tana goga yatsanta akan screen ɗin wayarta tana ƙara jinjina maganar Abbahn na ta a ranta.
Yana nan zaune yana jira ya ji ko za ta ce wani abu kawai ya ji wayarsa ta hau ƙara.
Ɗaga wayar ya yi kai tsaye ganin sunan Madu da ya yi appearing gaban screen ɗin wayar. Daga yanayin yanda ya ji muryar Madun yasan cewa ba lafiya ba.
"Alaji kana ji na?"
"Ina jin ka Madu. Allah yasa lafiya?"
"Akwai matsala Alaji. Matar Mukarram ce ta sanar min cewa har yau bai koma gida ba, ta yi tunanin yana nan ne amma kuma bata samun magana da shi, ni kuma na ɗauka uzuri ne ya yi masa yawa wanda ko ɗazu ka sai da ya turomin text ya ce min yana nan lafiya lau...."
"Ka neme sa a waya ka kuma tambayi wurin aikin sa? Ni ma tun da ya tafi bai kira ni ba and na yi mamakin hakan domin da wahala a tsallake yini ba tare da ya kirani ba."
"Alaji sai da na gama bincike na sannan na kira ka na sanar maka? Mukarram ya ɓata Alaji kuma ko tantama bana yi Alhaji Gimba shi ne wanda ya aikata hakan. Wallahy wannan mutumin bashi da kirki ba shi da mutunci ko kaɗan Alaji. Kuma a wannan karon don Allah ina roƙon ka kada ace za'a bi wata alfarma ko kuma sanayya..." ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*PAGE 31*
Koda ƙarfe biyar na yamma ta yi ilahirin gidan ya cika da Kaki iri daban-daban domin taya iyalan jimami da kuma ɗaukar rahoto akan yadda abin ya faru domin yin bincike.
Gabaɗaya gidan ya gama rikicewa da koke-koke tamkar gidan mutuwa.
Duk surutunda ake ta yi Alhaji Mas'ood bai yi magana ba sai da ya ji wurin ya ɗauki shiru sannan ya kalli babban jami'in da ke zaune akan kujerar da ke gaban sa ya ce.
"Inspector....abin da na sani shi ne an nemi ɗana cikin kwanaki uku an rasa, and bana zargin kowa a wannan ɓatan da ya yi..."
Cike da mamaki Muhammad ya ce.
"Haba Alaji! Ya za ka ce haka? Kafa san ko waye yake bayan wannan abun..."
Hajiya Nasmah na share hawayen ta da gefen hijabinta gwanin tausayi ta ce.
"Ni daman sam a raina ban yarda da cewa Gimba zai yafe abubuwan nan cikin sauƙi ba, yanzu ina amfanin sulhun da akayi?"
Hannu Alaji Mas'ood ya ɗaga musu alamar baya son jin kowace irin magana sannan ya mayar da hankali wurin Inspector wanda fuskar sa ta gama cika da alamar tambaya ya ce.
" Sulhu? Daman akwai wanda kuke zargi?"
Da sauri Alhaji Mas'ood ɗin ya girgiza kan sa ya ce.
"Ba ma zargin kowa Inspector Amit. Abin da nake so kawai ku yi iya ƙoƙarinku wurin nemosa please..."
"Shi ke nan Alhaji. But ina so ku faɗamin abin da ya faru tun daga farkon dalilin zuwan sa har zuwa sallamar da ya yi muku domin komawa."
Sun jima suna rubuce-rubuce sannan daga ƙarshe suka yi musu sallama suka koma.
Ganin yanda Hajiya Nasmah ke ta rusa uban kuka yasa Alhaji jikin sa a sanyaye ya ce.
"Haba Hajiya! Komai fa ya yi tsananin maganin sa Allah. Addu'a ita ce ta kama ce ki ba wannan kukan ba, kin mayar da kanki tamkar su Anaam ke da su babu wanda ke iya ƙwarara wani...."
Girgiza kanta ta shiga yi cikin kukan tana faɗin.
"Ai nan ba batun ƙwarara kai ba ne Alhaji! Kafi kowa sanin inda mukarram yake kuma a hannun wa yake, amma shi ne za ka ce wai baka zargin kowa? To a bar shi a hannunsa har sai ya kashe sa ko me? Duk abubuwan da Gimba ya yi mana a baya Alhaji kana so ka ce har yanzu ba za ka iya bari hukuma su tuhume sa ba kenan?"
"Ki yi hak'uri Hajiya Nasmah...ni ba haka nake nufi ba, shin yanzu idan mun saka an kama sa wace hujja muke da ita kenan? A tare gabaɗaya muka shiga gidan sa kuma a tare muka fito, lafiya lau ya je gidan Madu ya dawo ya kwana ɗaya a gidan nan sannan ya juya da nufin komawa, dan Allah ta ya ya zan ce ina zargin sa?"
Cikin bayyanar da wani irin tsananin fushi ta miƙe a fusace ta ce.
" Wallahy ko ka ƙi Alhaji ko ka so Gimba shi ne wanda ya sace Mukarram! Ya rage naka kasa a tuhume sa ko kuma a bar shi da shi ya kashe sa."
Tana gama faɗa hakan ta bar masa parlourn ta yi shigewarta wanda a hankali su ma su Muhammad ɗin suka shiga zamewa aka bar shi shi kaɗai yana tunani.
*******
Ƙarfe goma na safe motocin 'yan sanda guda biyu suka tsaya a gaban katafaren gidan Alhaji Gimba.
Cikin mintuna ƙalilan ƙofar gate ɗin ta buɗe suka sulale cikin gidan kai tsaye.
Sai da polisawan suka gama fitowa sannan daga ƙarshe Inspector Amit ya fito. Fuskar nan babu alamar wasa ya dumfarin cikin gidan inda ya tarar da su cikin shirin su na tafiya zuwa Gusau.
Cikin tashin hankali Hajiya Salamatu ta sako ido tana kallon su ta ce.
"Lafiya kuwa?"
Alhaji Gimban bai kai ga tashi daga inda yake zaune ba Inspector Amit ya ce.
"Good morning Alhaji Gimba...I'm Inspector Amit Umar Gengeh"
Komawa ya yi ya zauna daɓas yana mai bin su da kallo ya ce.
"Good morning Officer...lafiya? Miye ya kawo ku gidana haka kai tsaye? And babu neman izini babu komai kawai sai ku faɗomin..."
Wuri Inspector Amit ya samu ya zauna ba tare da ya jira an bashi izini ba, cikin ƙwarewa ya jinjina kansa ya ce.
"Pardon me please! Mun zo akan zancen ɓatan Mukarram Mas'ood Galadima..."
Wani murmushin gefen baki Alhaji Gimban ya yi sannan ya wani karyar da wuya ya ce.
"Mukarram kuma? Ce maka suka yi ni ne wanda ya sace sa ko? Daman ai wannan a wurin iyalan Alhaji Mas'ood ba sabon abu ba ne..."
File Inspector Amit ya ciro ya ɗora akan glass center table ɗinda ke gabansa ya ce.
"Mukarram ya ɓata ne one day after meeting you, Wanda dukkan ahlin dama sauran abokanan hulɗar ku sun tabbatar cewa sun zo nan gidan domin yin sulhu da kai daga nan kuma washegari aka neme shi aka rasa."
Wata dariyar ce ya sake fashewa da ita sannan daga ƙarshe ya tsagaita yana kallon Inspector ɗin ya ce.
" Wannan kuma zancen banza ne Officer. Mun zo mun yi sulhu da su sannan muka gindaya sharɗoɗa akan kowa ya girmama muradan juna, ta ya kake tunanin cewa zan koma kuma na sace shi? Wannan ɗin ba matsala ta ba ce..."
Ƙara matso wa Inspector Amit ya yi zuwa gaba ransa a matuƙar ɓace ya jinjina kansa ya ce.
" Wannan case ɗin kuwa shi ne babbar matsalar ka, because your name keeps coming up. Kowa yasan irin takun saƙar da ke tsakaninku da rashin jituwa na tsawon lokaci, saboda haka a wannan karon ba za ka tsere ma wannan ba..."
Tuni Alhaji Gimba ya ji ransa ya fara sosuwa domin ya ga alamar wankin hula na nema ya kai shi dare. Hakan yasa ya tamke fuskar nan ya ce.
" Listen to me Inspector....I'm a respected businessman. You can't just walk into my house and accuse me..."
Ba tare da Inspector Amit ya motsa daga inda yake zaune ba ya jinjina kansa ya ce.
"Na sani Alhaji Gimba. But duk girman respect ai ba zai hana a bincike ka ba haka zalika ƙarfin iko doesn't erase suspicion....Ka nutsu sosai ka bani haɗin kai domin mun yi komai cikin mutuntawa. Yanzu ina so ka faɗamin...a wannan ranar kana ina tun daga wayewar gari har zuwa yammaci?"
Ɗan Jim ya yi na ɗan lokaci alamar nazari sannan daga ƙarshe ya ce.
" I was at home, ina tare da iyalina. Sai misalin ƙarfe biyar na yamma muka fita tare da Amaryata domin ta faɗamin tana so ta fita shan ice cream. Misalin ƙarfe goma na dare muka dawo gidan."
Jinjina kai Inspector Amit ya yi bayan ya gama rubuce-rubucen sa sannan ya ce.
"Any proof? Ina nufin CCTV record, wuraren da kuka kasance a yinin ranar da kuma phone records?"
"Ni fa ban aikata laifin komai ba Inspector! Ka daina ƙoƙarin ɗoramin laifi ko kuma sanya mini magana a baki na..."
Sai yanzu Inspector Amit ya ɗan murmusa ba tare da ya ɗauke idonsa ba akan Alhajin Gimban ya ce.
"Daman ai duk wanda ake tuhuma ko yana da laifi shi dai kawai ƙoƙarin yake yaga ya kare kansa..."
Miƙewa tsaye Alhaji Gimba ya yi tare da nuna Inspector Amit ɗin da yatsa a fusace ya ce.
"Lallai ka iya bakinka Inspector! Don't cross your line! Zan sake maimaitawa ni ban sace kowa ba!!"
A fusace Amit ɗin shima ya miƙe cikin wata irin razananninyar ƙara irin ta zaratan 'yan sandan gaskiya ya ce.
"Sit down Alhaji Gimba! Don't try that with me. This is a serious crime, Idan ka yi wasa za ka ƙare a cell I'm telling you!"
Sulalewa ya yi ya koma ya zauna, karo na farko kenan da ya ji cewa a ransa kamar ya karaya.
"Ka sha yi wa mukarram barazana ko ba haka ba? And last shi ne wanda kuka yi akan ɓatan ƙanwar sa da ya shigar da ɗan ka ƙara. Ba ka ce sai ya biya akan yanda ya wulaƙanta maka ɗa ba?"
Shiru ya yi wanda sai yanzu Faris dake tsaye a gefen da Mum ɗinsa ke tsaye ya ce.
" Inspector Alhaji ba shi da hannu a ɓatan Mukarram ka yarda da ni. Komai an yi shi ya ƙare..."
Jinjina kai Alhaji Gimba ya yi ya ce.
"Tabbas na faɗi wasu maganganun a bisa kuskure da kuma yanayin fushi da na kasance a cikin sa a wannan lokacin, amma ni sam bani ne wanda ya sace sa ba."
Hannu Inspector Amit ya saka ya buɗe file ɗinda ke gabansa ya fiddo wani hoto ya ɗora akan table ɗin gaban Alhaji Gimban ya ce.
"Ka san wannan?"
Sai da ya gama kallen hoton tsab sannan ya girgiza kansa ya ce.
"Gaskiya ni ban waye sa ba..."
Hajiya Salamatu dake iya hango hoton da kyau ta ce.
"Alhaji ba ka gane sa ba? Nura Sitati ne fa tsohon drivernka ko ka manta?"
"Ohhp! Haka fa akayi. Mts! Ka yi haƙuri Inspector kasan mutanen hulɗa da yawa suke, shiyasa ban gane shi ba kasancewar ya shekara uku da barin aiki a ƙarƙashina..."
"Mi miye dalilin da yasa ya daina yi maka aiki?"
"Saboda na gaji da aiki da shi ne, hakan yasa na sallame sa na samo wani..."
Jinjina kai Inspector Amit ya yi ya ce.
"An gan shi a motar da mukarram yake ciki safiyar da ya fito domin zuwa Airport, drivern gidan Alhaji Mas'ood ya tabbatar mana da cewa shi ne wanda ya haɗu da shi na ƙarshe..."
"What!!! Ni ban san komai ba, ban san ma a ina yake ba a yanxu, bani da wani business da shi."
Mayar da photon ya yi sannan ya mayar da takardun ya rufe file ɗin ya mayar ya miƙe tsaye yana kallon Alhaji Gimban ya ce.
"You are the first person of interest. Kada ka bar garin Abuja, kada ka ce za ka yi wani yunƙuri. If you are found innocent...you will be fine..."
"Hhmm! Inspector barazana kake min?"
Murmushi kawai ya yi sannan ya ce.
"Ba barazana ba ce Alhaji Gimba. Idan har aka tabbatar baka da laifi, shike nan komai ya ƙare, idan kuma kana da hannu a wannan aikin, na yi maka alƙawari sai na janyo ka ƙasa..na barka lafiya."
Sai da ya tabbatar sun tafi sannan ya faɗa kan kujera tare da jin wani irin matsiyacin gumi da ya shiga tsatstsafo masa ta ko'ina.
" Oh! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wannan masifa Allah ka yi mana maganinta! Ace a rayuwa daga wannan sai wannan. Yanzu kuma Mukarram ɗin ne ya ɓata ake tuhumar ka? Wai yaushe wannan abun zai ƙare a tsakanin ku?"
A fusace ya miƙe tsaye ya wani kalle ta ya ce.
" Ban sani ba! Ban sani ba na ce! Ke har fata kike takun saƙa da gabar da ke tsakanina da Alhaji Mas'ood ta ƙare? Infact...yaushe ma kika fara tsoma baki a abinda ba'a tambaye ki ba? Rai na yana faɗamin abubuwa da yawa dangane dake, ki bi ni a hankali. Babu ranar da gaba za ta ƙare a tsakaninmu har sai mun mutu mun bar duniyar! Aikin banza kawai aikin wofi! Komai ai sai da hujja, idan suna da hujjar kuma su zo su kama ni in gani."
"Haba Daddy! Miyasa za ka sauke fushinka a kanta?"
"Na sauke! Na ce na sauke ɗin? Uban waye duk ya janyo ni a wannan idan ba ku ba? Da kun saurari magana ta daga kai har uwar taka da yanzu ina nan zaune hankalina a kwance. Wallahy duk sai na yi maganin ku, na rantse da Allah sai na yi maganin ku, ku jira na ƙare zan dawo kan ku."
Daga ya yi fuu ya wuce ciki tamkar zai ta shi sama.
Wani irin farr da ido Maimuna ta yi wacce tun ɗazu take tsaye ta fashe da dariya tana ta wani farin ciki ta ce.
" Kullum ba'a iya komai ba sai sanyawa miji hawan ruwa da janyo mai magana. Ya dai kamata a canja hali, ko ana neman asiri a bari har a fara iya kulawa da miji."
Tana gama faɗar haka ta sake kecewa da dariya sannan ta shige ciki tabar su nan a tsaye.
*******
Hidimar sunan babyn Aunty Amina haka dai aka yi shi ba da daɗin rai ba, musamman gefen dangin Yaa Muhammad ɗin da abin ya zamto musu tamkar mutuwa.
Babu inda ba su bincika ba, har can wurin aikin sa sai da aka je aka bincika wanda daga can Mubarak ɗin ya dawo tare da Aysha wacce ta rame ta bushe saboda tsananin damuwar da take ciki.
Iyayenta ma sun zo daga Gusau suka yi musu jaje suka koma.
Abu kamar wasa sai ga shi sun shafe tsawon sati biyu babu Mukarram babu labarin sa. Ammie ta yi kuka kamar me musamman da aka tabbatar musu cewa har yanzu ba'a samu labarin sa ba.
Anaam ma duk yanda aka yi da ita ta kasa samun nutsuwa ballantana ma har ta iya fita lecturers, kullum tana nan tare da Ammie wanda ta yi matuƙar tsorata, hakan yasa ta dawo kwana a ɗakin Ammien domin ganin take kamar ita ma za'a zo a ɗauke ta bayan fyaɗen da aka taɓa yi mata a baya.
Zuwan Na'ima ne ma yasa ta ɗan sassauta daga irin mummunan yanayin tsoron da take ciki.
Duk iskancin Rabi'atu a wannan karon sai da ta sha jinin jikinta domin yanayin da ahlin gidan suka shiga ba ƙaramin raunata mata zuciya ya yi ba. Amma duk wannan cakwakiyar da ake ciki, tana nan tana wayar ta da Faris wanda a yanzu soyyayar da ke tsakanin su ta girmama sosai ba tare da kowa ya sani ba.
******
Maheer kuwa, yana tsaye a gaban ma'aikatan su da yake ba wa horo a tsakiyar filin ma'aikatar ta su Hamad ya shigo kai tsaye ya ratsa tsakiyar su yaje gaban Maheer a fusa ce ya tsaya kai ya ce.
"Miyasa za ka aikata hakan Maheer? Shi fa ma'aikaci ne kamar kai...."
Takawa ya yi a hankali ya fara tafiya yayin da Hamad ɗin ya bi bayan sa, sai da da suka kai bakin wani gini mai ɗauke da na'urorin jiragen ruwa ya tsaya a nan yana kallon Hamad ɗin ya ce.
" Miye kake magana a kai?"
" Kasan ko akan miye nake magana Maheer, kada ka ce baka sani ba. Mukarram da kasa aka kama hakan bai kamata ba..."
Cike da wani irin mamaki Maheer ɗin ya ƙara zuba masa fararen idanun sa yana kallon sa ko ƙyaftawa babu na tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ya ce.
"Wai kai ka ɗauka cewar ni mutumin banza ne Hamad? Neman fansa da nake ba shi zai sa na kasance ɗan daba ba. I would never do such kind of thing...."
Still cikin rashin yarda da kalamansa Hamad ɗin ya girgiza kansa ya ce.
"Hakan dai ba rayuwa ba ce. Ni yanzu al'amuranka sun fara bani tsoro."
"Uhm! Ni kuwa kai ne wanda yake bani tsoro Hamad,Because na kasa yarda da cewa har yau baka gama sanin waye ni ba. A iya zamana da kai...na san abinda za ka iya aikatawa da wanda ba za ka iya aikatawa ba. Saboda haka idan har da gaske kana son ci gaba da kasancewa da ni, ya zame maka dole ka ƙara neman sanin waye ni, idan ba haka ba kuma zamu raba gari da kai. Da uban su nake da case ba da su ba....saboda haka ka matsamin a hanya ta na wuce..."
******
Muhammad na zaune a office wanda fitowarsa kenan daga meeting, abin da ya zame masa kamar na dole sanadiyyar dole ya yi attending baƙin su kada kasuwancinsu ya samu matsala.
Tun da ya fito ya zaune akan kujera tare da resting bayan sa ya lumshe idanun sa yana mai jin yanda kansa ke wani irin Sara masa tamkar zai tsage ya rabe gida biyu tsabar rashin bacci da damuwar da yake fama da ita na rashin sanin a wanne hali ɗan uwansa yake ciki? Ya mutu ne ko kuwa yana raye? Idan yana raye a ina yake? Ya ci abinci ko baici ba? Yana samun damar yin ibadah ko kuwa?
Sauban da ya shigo office ɗin tun ɗazu ya ɗan ɗauki lokaci yana sallama wanda sai da ya saka hannu ya ɗan bubbuga handle ɗin kujerar sannan ya yi firgigit da mummunan mafarkin da ya zurma ido a buɗe na tsawon lokaci.
Ɗan murmusawa ya yi sama-sama yana faɗin.
"Ohh! Sauban! Na ɗan sha'afa ne wallahy, hakan yasa ban ma ji sjigowan ka ba, sorry..."
Wuri Sauban ɗin ya samu ya zauna yana faɗin.