Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 25

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 25

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 25: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 25. "Ai ba komai Oga Muhammad. Dole akwai damuwa gaskiya, Allah ya…

3,357 words

"Ai ba komai Oga Muhammad. Dole akwai damuwa gaskiya, Allah ya bayyanar da shi cikin aminci."

"Amin amin ya Allah na gode sosai."

"Ahm..daman dangane da maganar mu ne da Anaam...to haƙiƙanin gaskiya na so ta da gaske kuma na so na aure ta, amma kuma mahaifiyata ta fito ta kafe tace ita lallai ba ta amince da na aure ta ba, musamman da ta ji cewar ba ta haihuwa..."

Cike da jin wani irin shock ya kalli Sauban ɗin ya ce.

" And who told you that She's infertile?"

" Ita ce da bakinta ta sanar min cewa an yi mata fyaɗe sannan likitoci sun tabbatar ba za ta iya haihuwa ba..."

Miƙewa ya yi tsaye ransa a ƙone ya ce.

"And aka ce kuma dole lallai sai ka zo yanzu ka sanar min magana ta renin hankali! Wai dan Allah miye yake damun mutane ne? Baka san halin da nake ciki ba da har da za ka zo min da maganar banza maganar wofi? Tabbas laifin mukarram kawai muke gani, amma mutanen duniya idan har baka fito musu a mutum ba to fa ba za su taɓa bari a zauna lafiya ba...."

"Please don't be angry! Kawai na ce bari na sanar maka ne kada ka ji ni shiru..."

"Da can a farko ni ne na nemoka? Ni ne na janyo ka nace ka zo ka so ta ko kuma kai ne wanda ya riƙa bina yana mini magiya?"

"Oga Muham.."

"Please get out from here!"

Muhammad ɗin ya faɗa yana mai nuna masa hanya.

Ganin yanda ransa ya ɓaci da gasken gaske yasa Sauban ɗin Miƙewa ya bar masa office ɗinsa zuciyar sa cike da takaicin abin da ya yi, da yasan cewa abin zai ɓata masa rai da tabbas bai zo ba tun farko. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 32*

Daga office ɗin Muhammad ya wuce direct ya nufi gidan iyayensa ransa a matuƙar ƙone dangane da cin fuska da tozarcin da Sauban ya zo masa da shi dangane da Anaam ɗinsa.

Tun daga harabar gidan duk wanda ya kalle sa sai yasha jinin jikin sa ganin yanda fuskar nan take a matuƙar turbane da ɓacin rai.

Cikin sa'a kuwa, ya tarar da su zaune a parlourn Hajiyar tasu wanda har da Amina matar sa a ciki da kuma Dinaratu matar cousin ɗinsa Nameer.

"Madu lafiya kuwa? Ya na ganka cikin irin wannan yanayin?"

Abinda Hajiya Nasmah ta furta kenan a lokacin da tayi ido biyu da shi kamar yanda sauran mutanen da ke parlourn suka yi tsit suna kallon sa.

Babu abin da zuciyarsu ke raya musu musamman hajiya Nasmah face wata ƙila ya zo musu da labarin mutuwar Mukarram ne ganin yanda fuskar nan tayi masa babu daɗi.

A razane Anaam ta miƙe tana mai dire plate ɗin abincin da ke hannunta wanda Nene ta ajiye mata tun ɗazu. Daga yanayin yanda spoon ɗin ke cikin abincin ta can ƙasan plate ɗin shi ne zai tabbatar maka da cewa ko taɓa abincin bata samu nasarar yi ba.

Matsawa ta yi dab da shi idon ta fal ruwan hawaye tace.

"Dan Allah Yaa Muhammad ka yi mana bayani mana. Ko ka ji labarin Yaa Mukarram ne?"

Ƙwayar idonsa ya saka a nata tare da girgiza kansa ya ce.

"Ba labarin Mukarram na ji ba Anaam, rashin mutuncin da Sauban yazo har office ya yi min ne akan ki ya ƙona min rai...."

Shiru ya yi tare da miƙa hannayensa ya kamo duka hannayenta still idonsu a sarƙafe ya ce.

"Anaam...ki manta da Sauban domin daga shi har mahaifiyarsa da yake iƙirarin ta hana shi basu san ƙaddara ba. Kuma don yace ya fasa auren ki it's not the end of the world. Ki ɗauka haka ɗin shi ne mafi alheri...."

Jinjina kanta ta fara a hankali tana mai jin wasu sabbin hawaye waɗanda bata san ko na miye ba. Shin farin ciki take akan fasa auren ta da Sauban ɗin yace ya yi ko kuma baƙin ciki take akan cewa ya fasa auren ne saboda kawai mummunar ƙaddarar da ta faɗa mata? Saboda kawai igiyoyin ƙaddara sun juya da ita sai a yanke mata irin wannan hukuncin? Ba fa a son ranta ne wannan abin ya faru da ita ba, taya ya zai nemi ya guje mata sai kace ba musulmi ba...

"Maryam..."

Yaa Muhammadu ɗin ya ambata a hankali ganin yanda fuskarta ta sauya sosai tana mai nuna alamun tsantsar baƙin ciki da wannan labarin.

Hannunta Hajiya Nasmah ta janyo sai gashi ta biyo ta a hankali ta ɗora fuskarta akan kafaɗar mahaifiyar ta ta tana mai fashewa da kuka tace.

"Ammie dan Allah ku yi haƙuri da zancen nan a yanzu. Ɗan uwana da ya ɓata ya fiye min muhimmanci fiye da wannan maganar a yanzu. Muyi focusing akan yanda za'a yi a gano min dan uwana a daina yi min wannan maganar. Ɗan uwana shi ne nake buri da son ganin ya dawo cikinmu. Ya Allah ya bayyana ka Yaa Mukarram."

Daga haka ta zame a hankali ta taka ta wuce ta shige ɗakinta tare da murzawa ƙofar key.

Girgiza kai Ammie tayi tana kallon Muhammad ɗin ta ce.

" Kai ma bansan miyasa kazo da wannan maganar ba bayan ga wacce ake kai a halin yanzu..."

"Hajiya na kasa riƙe abin a raina ne shiyasa har nayi wannan maganar. Mutane sam basu da lissafin rayuwa, kina Mace har kin isa ki ƙyamaci 'ƴar uwar ki Mace wai don wata ƙaddara ta faɗa mata musamman a matsayin ki na uwa..."

"To Allah yasa hakan ya zama shi ne mafi alheri a gareta,..Alhaji yana can tare da Alhaji Ridwan tun ɗazu ya zo. Shi ma har yanzu dai babu wani bayani daga ɓangaren sa. Inspector Amit ɗin ma haka."

Juyawa ya yi ya fice ya nufi parlourn Alhajin na su ba tare da ya sake yin wata magana ba.

Sai yanzu Yaa Amina ta kalli Ammie cikin rashin daɗin rai ta ce.

" Ai wallahy tun ranar da yazo min da zancen Sauban rai na ya bani cewar Hajiyarsa ba za ta taɓa amincewa ba, domin Mace ce ita mai tsatstsauran ra'ayi da nu na iko akan 'ya' yanta."

"To ai ba komai Amina, Allah ya haɗa kowa da rabonsa. Ta shi kije tun ɗazu fa aka ce miki Diyana ta tashi tana kuka."

Miƙewa tayi tare da ɗaukar baby bag ɗinta tana faɗin to Ammie ta shige ciki.

Ganin Aminar ta tashi yasa itama Dinaratu ta miƙe da ɗan murmushi a fuskarta ta ce.

" Ammie ni zan koma. Allah ubangiji ya bayyana mana Mukarram cikin aminci. Allah ya kawo mana ƙarshen waɗan nan matsalolin yasa komai ya zama tarihi watarana."

Cikin nuna jin daɗin addu'arta Ammie ta ce.

"Amin amin ya Allah Dinaratu, mun gode sosai Allah ya saka da alheri ya bar zumunci."

"Amin Ammie, ni zan wuce, sai an jima..."

"Yauwa...ki gaishe da su Arif."

Tana ficewa Ammien ta mayar da kallonta akan Rabi'a cike da mamakinta ta ce.

"Wai Rabi'a anya kina da tunani kuwa? Yanzu ace duk badaƙalar nan da ake ta yi tun ɗazu sai latse-latsen wayar ki kawai kike kina ta dariya kamar ba ki ji abinda yake faruwa ba..."

Ajiye wayar tayi a gefe sannan ta ɗago kanta tace.

"To Ammie ni ya kike so na yi? Idan nace zan faɗi wata magana kuma cewa za'a yi wa yace na tsomala bakina a ciki. Ko kuma idan nayi maganar a juya ta zuwa wata manufa tun da dai ba so na ake a cikin gidan nan ba...."

"But ko baki ce komai ba ai dai kina nuna kin damu..."

Tana gama faɗar haka ta wuce ciki abinta yayin da mamakin rayuwa irin ta Rabi'atou ke daɗa bata mamaki.

Ita kuma Rabin tana ganin shigewar Ammien ta taɓe baki sannan ta ɗauki wayar ta ta itama ta wuce ranta fes da jin wannan labarin na cewa wai Sauban ya fasa auren Anaam. Hakan ba ƙaramin faranta mata rai ya yi ba, kuma in sha Allahu tana nan ta rasa mai so za ta ga an yi auren su ita da Faris nan ba da jimawa ba.

******

Aunty Dina kuwa, tana isa gida ko hutawa bata tsaya ta yi ba ta ɗauki waya ta kira Maheer wanda daga can ɓangarensa yake ta haɗa kayansa da nufin barin office ɗin zuwa gida.

Ganin kiran Aunty Dina ba ƙaramin ɗaga mishi hankali ya yi ba domin babu abun da yazo a ransa sai tunanin cewa Hamad ya sanar mata dukkan sirrinsa dake tsakanin sa da Anaam and ya gama yarda cewa ya bata labarin cewa shi ne wanda ya saka aka sace Mukarram.

Shiru ya yi ya nutsu sosai tare da zuba fitilun ganin sa akan screen ɗin wayar wacce ke riƙe a hannun sa.

Duk wata lakka dake jikin sa sai da yaji ta saki domin ya riga ya sadaƙar cewa ya shiga tarkon da har abada ba zai iya fita ba. Tabbas Hamad yaci amanar sa, kuma yaci amanar yarda. A tunaninsa ko da ace ta tabbata cewa shi ne wanda ya saka aka sace Mukarram ba zai taɓa yarda idan aka faɗa masa cewa wai Hamad shi ne wanda ya tona asirinsa ba. Hakan a yau shi ne ya tabbatar masa cewa babu aminta a yau.

Haka dai ya tsaya tsawon lokaci yana kallon kiranta wanda ke shigowa yana tsinkewa har kusan sau bakwai sannan daga ƙarshe ya sanyata a flymood ya tarkata sauran kayansa ya wuce.

Tun da ya shige gidan bai fito ba wanda tun da ma yayi sallar isha yana zaune a sallaya bai samu kuzarin ɗagawa daga nan ba.

Maamin shi da ta zamar mishi dole sai ya kira ne ya ɗauko ƙaramar wayarsa ya kunna ta ya kira ta. Suna cikin magana ya ji shigowar text message, bayan sun gama magana ya buɗe yaga message ne daga Hamad.

"Dinaratu tana son Magana da kai urgent, idan kana da ra'ayi you can call her back, Idan Kuma itama laifina ya shafe ta ne sai in ji."

Lumshe idanun sa ya yi na ɗan lokaci yana nazari sannan daga Ƙarshe ya miƙe ya ɗauko wayarsa babba ya cire ta a flymood ya kamo numbernta ya kira ba tare da yasan akan me take neman sa ba.

Ringing ɗaya zuwa na biyu sai gashi ta ɗaga cikin faram-faram ɗin nan nata ta yi masa sallama suka gaisa.

A yanayin yanda ya ji voice ɗinta sai ya ji hankalinsa ya kwanta.

"Maheer..."

Ya ji ta ambata sannan ta ce.

"Daman dalilin kiran shi ne, please idan ba za ka damu ba dan Allah kayi creating time daga yau zuwa gobe ka zo muyi magana."

"OK..."

"Maheer magana ce mai matuƙar muhimmanci please ka yi kokari ka zo."

"In sha Allah, I will."

Ajiyar zuciya ta sauke daga can ɓangaren ta bayan ta yanke wayar tare da yin addu'a a ranta cewa, Allah ubangiji yasa komai ya tafi daidai kaman yanda ta tsara. She wish and pray that Allah yasa abin da yake ranta shi ne yake ransa, and daga zaran ta tuna yanda ya damu da ita sosai sai taji cewa hankalinta ya kwanta akan wannan maganar. Kuma in sha Allah tana ji a ranta cewa ba za'a samu wata matsala ba.

*******

Anaam Ta jima a ɗakinta tsawon lokaci ba tare da ta sake leƙowa ko parlourn gidan ba.

Kuka ne ta sha shi kaman ba gobe. Tana tsaye jikin mirror tana aikin kallon kanta da ta saba tana jin damuwa a ranta taji ana knocking door ɗin ɗakin na ta.

Shiru tayi na tsayin lokaci domin bata ma sha'awar wata kalma mai suna rarrashi daga gare su. She promise cewa za ta manta bayan ta kamar yanda tasan ta yi musu alƙawari but da ire-iren su Sauban ba za ta taɓa daina tunawa ba kuma ba za ta taɓa daina saka abin a ranta ba.

Ƙarshe dai jin cewa ko waye ba zai daina knocking ɗin ba yasa tashige toilet ta wanko fuskarta ta fito taje a hankali jiki a sanyaye ta buɗe ƙofar.

Wani irin mamaki ne ta ji ya daɗa kama mata zuciya ganin sabuwar ƙawarta Na'ima Hassan Muhammad tsaye a gabanta tana yi mata murmushi.

Ganin Anaam ɗin ba ta da niyyan magana yasa ta jinjina kanta ta ce.

"Hey! you are not dreaming, you can hug me if you want, don ki tabbatar ni ɗin ce...."

Wani guntun murmushi tayi tana mai jin farin cikin ganinta a can cikin ranta sai ta girgiza kai tace.

"No need to. I'm sure kece ɗin da gaske and you are Welcome..."

Ta ƙarasa maganar tana mai juyawa ta koma ciki itama ta rufa mata baya suka shiga.

Suna zaunawa ta ce.

"I'm with mah pah. Ya zo ya jajantawa su Abbah abun da yake faruwa na ɓatan Yaa Mukarram. Kinsan na faɗa miki tun last week su Mum basa nan daga ni sai shi ne a gidan."

Ƙara Faɗaɗa murmushin ta tayi wanda ya bayyana kyawawan haƙoranta tace.

"Gaskiya I'm so glad Friendy, thank you so much, Allah ya saka da alheri ya bar zumunci."

Itama Na'imar cikin jindaɗin ganin irin tarbar da ta samu daga wurin Anaam ɗin tace.

"Amin amin yah Allah. Allah ubangiji ya bayyana mana shi cikin aminci."

"Amin. Tashi mu je na kai ki wurin Ammie daga can sai a kai Pah wurin Abbah..."

Dariya ta yi ta ce.

"Ai mun jima da Ammie har da Rabi'atou muna fira sannan aka kawo ni nan, Pah shi ma yana can tare da Abbah tun ɗazu."

"Ok, to bari na saka dai a kawo miki abin sha, bari na kira Nene..."

Kallon fuskarta tayi da kyau sannan cikin nuna kulawa ta ce.

"Maryam are you okay? Naga fuskanki tayi wani iri..."

Jinjina kanta tayi da ɗan murmushi tace.

"I'm fine Na'ima. Is just that, yanayin ne baya min daɗi at all. Yaa Mukarram bamu san a wanne yanayi yake ba Na'ima. I'm scared kada ace wani abu ya faru da shi....."

Hannunta ta ɗora akan na Anaam ɗin tace.

"In sha Allahu duk inda yake yana cikin aminci. Kawai muci gaba da addu'a, in sha Allahu za'a gan shi."

Sai da aka kawo mata ruwa da lemu ta ɗan taɓa sannan suka tashi suka je har parlourn Abbahn, Anaam ɗin ta gaishe da Mahaifin Na'ima sannan itama Na'imar ta gaishe da Abbah sannan suka fito.

Suna shiga parlourn Ammien ko zaunawa basu kai ga yi ba sai ga Yaa Na'iman ta ta shigo ɗauke da sallama a bakinta. Suna haɗa ido ta ɓata fuska alamar ta yi fushi domin daga tafiyan kwana biyu da cewa za su je gaishe da en uwan Haisam su dawo shike nan bata dawo ba sai yau. Ganin yanda Anaam ɗin ta ɓata fuska da gaske yasa ta sakar mata murmushi tare da ware hannayenta tace.

"Surprised...."

Cikin farin ciki ta rungumeta kawai sai ga hawaye shaaa....kamar an kunna famfo, hakan yasa itama Na'imar bata san lokacin da hawayen suka fara zuba daga idon ta ba tace.

"In sha Allah Yaa Mukarram zai dawo gida Anaam cikin ƙoshin lafiya..."

Sosai take zubo da hawaye tana Girgixa kai ta ce.

"Har yaushe to? Yaa Na'ima rayuwa ta sauya mana sosai, ƙunci da damuwa sun mamaye gidan nan namu Yaa Na'ima..."

Girgixa kai Ammie ta yi tace.

"Ya kamata ku bari zuwa anjima ku tattauna wannan domin ku samu daman shigowa da Haisam sannan ku ji da wannan Na'imar itama."

*******

Tun da ya shigo gidan Ashnan ke ta masa surutu amma ko kaɗan hankalinsa baya tare da Ita. Baccin kirki wannan tun a daren jiya bai samu ya yi ba. Tunaninsa gabaɗaya ya tafi akan neman nan da Aunty Dina tace tana yi masa. And ko kaɗan ba zai taɓa iya kiran Hamad ba akan wannan, a yanda yake ji a ransa ma ya datse duk wata igiyar alaƙa da yasan ta taɓa haɗa su har abada domin shi ɗin ba aboki ba ne.

"Maheer..."

Ya ji Aunty Dina ta ambata wanda hakan ne ya saka shi saurin ɗagowa ya kalle ta ba tare da yace komai ba.

Wuri ta samu ta zauna tare da yi masa barka da zuwa cikin sakin fuska kaman yanda ya ji muryanta jiya a waya.

Mai aikin ta ta kira tace ta shige da Ashnan sannan ta sake kai kallonta akan drinks ɗinda aka ajiye masa bayan sun wuce ta ce.

"Maheer ya naga baka taɓa komai ba?"

Kallon tray ɗin ya yi sai kuma ya kalle ta tare da ɗan murmusawa ya ce.

"I'm okay, thank you."

"Maheer...magana ce nike so mu yi da kai mai matuƙar muhimmanci. Ina fatan Allah yasa ka fahimce ni. Allah kuma yasa abinda yake raina shi ne yake ranka kai ma."

Ƙara gyara zamansa ya yi da kyau yana mai ci gaba da kallon ta har yanzu ba tare da yace komai ba.

Ita kuma ganin yanda ya nuna interest sosai yasa taji wani sabon ƙwarin gwiwa ya shige ta sai ta ci gaba da magana da cewa.

" wato dani da Abbansu Arif mun zauna mun yi wani nazari. A irin yanda muka ga ka shiga rayuwar Maryam tabbas wata ƙila akwai wani abun da yake ranka dangane da ita, to gidansu ne aka bijiro mata da wani mutum, and ni kuma ta ɓangarena na fahimci cewa kamar kana son ta ne..."

Wani irin abu ne wanda ba zai iya cewa ga ko miye ba ya ji ya harba mishi har can ƙasan zuciyar shi jin wannan maganar da tayi kama da mafarki.

Ganin irin kallon da yake yi mata yasa ta saurin girgiza kanta tace.

" Noo...Maheer ba fa ina maka maganar yanzu-yanzu ba ne, a'a. Ita kanta Anaam ɗin da familyn ta suna cikin jimamin ɓatan Yayanta da ya faru. Amma dai babu wanda ya cancanci Maryam sama da kai Maheer. Ni nan naga soyayyar ta a cikin idanuwan ka tun a ranar farko da kuka fara haɗuwa...saboda haka idan Allah yasa matsalar Mukarram takai Ƙarshe sai mu je da ƙarfinmu domin nasan in sha Allahu kai ne wanda zai same ta.

Wani kallon ya yi mata yana mai jin yanda duniyar ke juyawa da shi. Faɗi yake yana ƙara maimaita kalmar wai taga soyayyarta a cikin idanun sa tun haɗuwarsu da ta farko. Anya ta san wace irin haɗuwa ce kuwa? An ya ta tsaya ta kalli idanun nan nasa da kyau kuwa? Da ta kalle su da idon basira tabbas za ta gane tsantsar nadama ce da karaya a cikin su ba komai ba. Mummunan rana ce mai ɗauke da mummunan yanayi wanda idan za'a saka ruwan duniya har abada ba za su iya wanke wannan tabon ba. Shi kansa idan ya tuna haɗuwar farkon su ji yake ya karaya ballantana Anaam ɗinda ya barwa mummunan tabon da ba zai taɓa warkewa ba har abada. Shi da yake neman hanyar da zai nemi gafarar ta taya za'a ce kuma wai zancen aure ya shigo?

Tabbas shi ya san cewa ko mazan duniya sun ƙare har abadan abada Anaam ba za ta iya auren shi ba. Da za'a ajiye shi a ajiye mata bindiga tabbas yasan ba za ta tsaya tunani na biyu ba wurin ɗaukar bindigar ta hallaka shi har lahira. Wannan wace irin kalar ƙaddara ce?

Ta ina zai fara tuntuɓar Maaminsa da wannan magana? To ina ma zai fara and miye zai faɗa mata? Yasan ko shekara dubu zai yi yana yi mata bayani indai akan 'ƴar gidan Mas'ood Galadima ce wallhy har abada ko zai mutu bai yi aure ba ba za ta amince ya aure ta ba.

"Maheer..."

Yaa Dinaratun ta ambata ganin yanda ya yi shiru tsawon lokaci ba tare da yace mata komai ba.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 33*

Dawo da kallonsa ya yi kanta har yanzu ba tare da ya furta mata ko kalma ɗaya ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull