Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 26
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 26: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 26. "Da Kai da Hamad ni duk ɗaya kuke a wurina. Duk abin da nasan zan…
3,347 words
"Da Kai da Hamad ni duk ɗaya kuke a wurina. Duk abin da nasan zan so wa Hamad kai ma zan so maka shi, haka zalika duk abinda zan ƙi masa kai ma zan ƙi maka shi. Maryam mutuniyar kirki ce wacce za ta dace da rayuwarka. Ka daina tunanin matsayi ko kuma dukiya ko kuma kyau. Tabbas ta gefen ka za ka nuna mata dukiya ka kuma nuna mata kyau, amma kuma ita ɗin yarinya ce mai addini da tsantsan tarbiyya da kamun kai. Abu mafi muhimmanci shi ne muyi so don Allah kuma mu bari don Allah."
Jinjina kansa ya yi tamkar wanda aka yi wa dole ya ce.
"I will think about it."
Daga haka ya miƙe kai tsaye ya nufi ƙofa da nufin tafiya,sai dai jin ta sake kiran sunansa ya ja ya tsaya tare da waigowa kurum ya kalle ta.
Miƙewa tayi itama tana kallon sa ta ce.
"Ba alfarma nake nema mata ba ko kuma don ta rasa masoya, cancantar hakan na gani daga actions ɗinka. So....ka yi tunani sai ka yanke hukuncin da ya dace."
Jinjina kansa ya yi tare da ɗan sakin guntun murmushin da iyakacinsa kan leɓensa ya ce.
"I understand. Thank you for your concern."
Cikin nuna jindaɗin furucinsa ta ce.
"Allah ya zaɓa muku mafi alheri a tsakanin ku. Na gode da bani lokacin ka da ka yi."
Yana fita ta faɗa rijib akan kujera da tarin abubuwa masu yawa a cikin ranta. Ya kamata ace ta nemi shawarar Abban Arif kafin ta tattauna wannan maganar da Maheer, but the way Yanda ya ɗauko zancen Alami ta sani sarai yana da wahala ya iya fahimtar ta. Maheer son Anaam yake yi wanda damuwar ta a dare ɗaya ta juya ta koma tasa ba tare da ya san hakan ba. Ko kuma idan ma ya sani yana ɓoye hakan ne wataƙila da tunanin cewa is too early ya fito ya nuna manufarsa akan ta. Alami yana da mata da yara wanda komai daren daɗewa tabbas watarana ko matarsa ko yaransa sai an samu wanda zai goran ta mata akan wannan mummunar ƙaddarar da ta same ta. But Maheer saurayine, idan sun yi aure tare za su fara samun 'ya' ya, 'ya' yan da tasan har abada ba za su taɓa gorantawa mahaifiyar su ba domin sun san zafin ta sannan sun fahimce ta.
Ya kamata ace ta fito fili ta faɗa mishi ƙaddarar ta gudun abun da zai je ya dawo watarana, but a ranta sai take jin kamar hakan bai cancanta ba a yanzu. Dole ita ce ya kamata tayi mai bayani kafin ita Anaam ɗin taje mishi da zancen ta fuskar da za ta iya rikita tunanin sa. But ta ya ya? Ta wace fuska za ta fara yi masa bayani bayan tace ba alfarma take nema mata ba.
Wayar ta Arifa ta miƙo mata wanda hakan shi ne ya yi sanadiyyar katse mata dogon tunanin da ta tafi tare da faɗin.
"Mummy Uncle Hamad ne ke ta kira tun ɗazu."
Karɓa tayi tare da jinjina mata kai ta ce.
"Arif ya dawo?"
"Yana ɗakin sa tun ɗazu, sai faɗa yake wai Ashnan ta lallata masa chargern shi."
"Za ta aikata in dai ita ce. Ki ce mishi ya zo ya karɓo saƙon babanku kafin ya dawo."
"Ok mummy."
*******
Washegari tare Anaam ta shiga ɗakin da Aysha take ita da Na'ima hannayensu ɗauke da kayan kari da suka karɓo daga wurin Nene.
Rabonta da abincin tun jiyan nan da yamma wanda ko shi sai da Ammie ta matsa mata sosai sannan ta karɓa ta ɗan tsakura kaɗan ta ajiye.
Daman tun da suka iso Muhammad ya wuce da su Mufida gidansa wurin su Faryat domin su samu abokan wasa.
Har yau sai fuskar nan ta ta fayau take kamar ko yaushe.
Trayn da ke hannun Anaam ta ajiye akan glass table ɗinda ke gefe Sannan ta taka ta isa gabanta a hankali ta ce.
"Aunty Aysha Mama Hanne ta iso gidannan tun ɗazu tace a kira mata ke. Ko breakfast baki yi ba har yanzu nasan hakan. Aunty Aysha dan Allah dan girman Allah ki yi hak'uri ki sassauta..."
Wasu sabbin hawaye ne ta ji sun silalo mata jin kalaman Anaam ɗin. A hankali ta karyarda kanta ta sake kallon windown da tunɗazu take tsaye a kusa da ita sannan ta jinjina kanta tare da mayar da kallonta akansu ta ce.
"It hurt so much Anaam! Tsawon six weeks ake magana amma kuma na kasa sabawa. Yayanki shi ne duniya ta Anaam. Ban san ta yanda zan iya samun nutsuwa ba bayan rasa shi da na yi..."
Itama Na'ima idon ta fal hawaye ta girgiza kanta tace.
"Baki rasa Yaa Mukarram ba Aunty Aysha. In sha Allahu zai dawo gare ki, zaku ci gaba da rayuwar ku kaman yanda kuke. Duk da cewa ni ƙarama ce, tabbas ban yi daɗewar da kika yi a cikin rayuwar aure ba, amma a hakan nakan ji girman mijina da jin cewa ba zan iya rayuwa idan ba bu shi ba..."
"Ni kuma ban san waye miji ba, amma dai nasan raɗaɗi da zafin rasa Yaya wanda yake zamo wa tamkar uba a wani lokaci. Aunty Aysha kece kike faɗamin cewa dukkan rayuwa tana tafiya ne tare da jarrabawa. Ki yi hak'uri, in sha Allahu watarana zai dawo gare ki. Rashin cin abinci da rashin shiga cikin mutane da kike matsala ne Aunty Aysha, ko Yaa Mukarram ɗin ya dawo ya ganki a irin wannan yanayin ransa zai ƙara ƙuna fiye da wanda yake ciki. Mu kanmu Aunty Aysha yana mana zafi sosai ganin irin rayuwar da kike ciki, amma babu yanda muka iya. Please ki yi haƙuri."
Ganin suka yi ta taka a hankali ta ɗauko tray ɗin ta zauna a ƙasa. Mug ɗin Tea ta ɗauka ta kai bakinta ta hau sipping a hankali har sai da tayi rabi sannan ta ajiye ta ɗauki plate ɗinda ke ɗauke da Irish da egg sauce shima ta ɗan taɓa kaɗan ta ajiye ta tashi ta shige toilet ta yi wanka ta fito.
Fira suka ɗan shiga taɓawa a hankali tsakanin Anaam da kuma Na'ima domin Aysha dai tana nan shiru har ta gama shiryawa suka fito.
Kallon Rabi'a suka yi wacce ta fito da shirin ta na zuwa school taba ta wani tauna cingum kaman bata san su ba. Sai da ta shiga ta gaida Abbah ta fito ta fice sannan sai gata ta dawo inda suke ta kalli Anaam ta ce.
"Malama driver na an aike shi, shi kuma Anasi na ce ya kai ni yace min ke yake jira."
Wani kallon banzan Anaam ɗin ta watsa mata sannan ta ce.
"And so? Kina da wani business da hakan ne?"
"I need to be in class by 10am, ke kuma naga ko alamar shiri ba ki fara ba."
Cike da izza Anaam ɗin ta ce.
"Sai 2pm nake da class and Anasi ba zai fita ba sai na tashi fita..."
Cike da jin haushin kalaman ta tace.
"Wallhy kin ci ƙarya kin kwana da yunwa..."
"Wai miye haka ne? Anaam da hankalin ki za ki tsaya biyeta?"
Cewar Ammie cikin ɗaga murya ganin suna nema su yi faɗa.
Turo baki Rabi'a ta yi tana faɗin.
"Tun da ni har yau ba'a ɗauke ni er gidan ba ai dole ayi ta yi min duk abinda aka ga dama. Idan ba shi ba taya ni za'a ce an aiki nawa drivern da yake kaini ita nata yana nan..."
"Babu wanda ya aikesa, Madu ne ya kira shi gidan shi tun 6am shi ne har yanzu bai dawo ba, kuma ma Anasin ya fara nema shi kuma a lokacin bai kintsa ba shi ne ya neme shi da cewa shi ya tafi..."
Cikin wani irin ɓacin rai Mama Hanne ta ƙundumawa Rabi'ar wani irin mahaukacin zagin da sai da ta ji hantar cikin ta ta kaɗa tsabar yanda taji wani tsoronta ya tsargar mata a zuciya.
Kallon Ammie ta yi ranta a tsakanin ɓace ta ce.
" Wallahy Nasmah kin ji haushi wallahy! Ta ya ya za ki tsaya gaban wata 'ƴar iskar yarinya marar kunya kina yi mata bayani? Ubanta ya sayi motar ko uwarta? Kinga....kinga Nasmah ki kori wannan makirar yarinyar nan a gidan nan tun bata ɗauko miki abinda yafi ƙarfin ki ba..."
Ƙara matsawa ta yi kusa da Rabi'ar kamar za ta kai mata duka ta ce.
" Uban waye kike yi wa haka da baki? Wallhy ni yanzu sai in haɗa miki jini da Majina, shegiya matsiyaci wacce tayo gadon mugun abu. Ke ina dalilin bakai ka haifi ɗa ba yazo ya zamar maka ƙayar kifi a maƙogoro?..."
Saurin saukar da kanta ta yi ƙasa cike da tsoro ta ce.
" Dan Allah ki yi haƙuri Mama Hanne ni ba dake nake ba...."
Ganin yanda ta ci gaba da bala'in yasa Ammie ta saukar da murya ƙasa sosai ta ce.
" Ki yi hak'uri Yaya Hanne, mun san indai Rabi'a ce ai kinsan halinta ki daina ma ɓata bakinki..."
"Wallahy wallahy ni sai na saita mata zama daga ita har uwarta a cikin gidan nan. Shegu munafukai en hassada en baƙin ciki."
Daga haka ta ja hannun Aunty Aysha suka shige parlourn Ammie domin ji tayi ba za ta ma iya tsayawa a nan main parlourn da suke ba.
Ammie na ganin shigewarta ta kalli Rabi'a ta ce.
" Rabi'a rayuwar nan gabaɗayanta darasi ce idan muka dube ta ta wata fuskar. Ki bi ta a sannu tun kina da damar ki."
Kallon Anaam ɗin tayi sai kuma ta sake kallon Rabi'ar ta ce.
"Ki tafi wurin Anasi ki ce masa nace ni nace ya kai ki school ɗin domin Maryam ɗin sai 2pm take da lecture."
A ta ƙasan Ido ta wani harari Anaam ɗin a kaikaice sannan ta wuce buzum-buzum ta fice.
Komai Anaam ɗin bata sake cewa ba kawai ta juya ta koma ɗakin ta, sai da ta tabbatar cewa Lallai sun isa yin rabin school ɗin ta ɗauki wayan ta ta kira Anasi, yana ɗagawa calmly ta ce.
"Ka samu gefen hanya ka yi parking ka faɗa mata cewa fuel ya ƙare, Sannan ta fito ta tsaya a waje ta jira ka ka nemo fuel ɗin ko kuma ka kulleta a ciki. Daga nan ka yi tafiyar ka sai 1:30pm ka koma."
"OK."
Yana tsinke kiran bai yi tafiyar 5minute ba ya ja a slow ya tsaya.
Wani kallon ta watso mishi daga ta can backseat ɗin tace.
"Lafiya?"
Kai tsaye yace.
"Ai hajiya an yi rashin sa'a Mai ya ƙare a motan..."
A sheƙe ta wani kalle sa duk da cewa baya iya ganin ta ta ce.
"Bangane zancen ka ba. Kamar ya Mai ya ƙare?"
Ƙofa ya buɗe yana faɗin.
"Kaman dai yanda kika ji na faɗa miki. Ki fito ki jirani naje na samo ko kuma na kulle ki a ciki har na dawo..."
Cike da baƙin ciki ta yi mai wani kallon ƙasƙanci ta ce.
"Wannan ai bura'uba ce da iskanci! Idan ba shi ba taya ya za ka bar mota ba mai..."
Ba shiri ya ɗago ido ya kalle ta domin zaginda ya ji ta yi ba ƙaramin mamaki ya bashi ba. Tun da yake bai taɓa jin zagi a bakin Na'imatu da Anaam ba. Ballantana ace shi ba ta dubi girman shi ba saboda rashin kunya ta zage shi.
Ƙala bai ce mata ba har sai da ta dasa Ayaa sannan ya ce.
"A motar zan bar ki ko kuma za ki fito ne..."
"Malam ka kunna min AC ka je ka yi sauri ka dawo."
"Babu mai ta ya za'a iya kunna AC...."
Fitowa tayi da sauri tana mai ƙara jin wani sabon ƙololon baƙin ciki ta rabka ƙofar motar tana faɗin.
"Wallahy wannan maganar yau sai ta kai ga kunnen Abbah, wallahy sai ya ji dalilin da yasa ka bar mota babu Fuel, aikin banza kawai, mutum bai iya komai ba sai ƙauyanci....dan Allah ka wuce ka tafi ka samo Fuel ka wani zo ka tsaya ɗan renin hankali kawai."
Hankalinsa a kwance ya kama hanya da ƙafa ya fara tafiya. Daga can bayan sa ya jiyo ihunta tana faɗin wai ya tari lift mana domin yaje ya yi saurin dawo wa.
Tana nan a tsaye tun tana iya hango shi har ya ɓacewa ganin ta. Wasa-wasa sai gashi 12pm na nema ta buga mata a nan wanda ta kira Abbah ta kira Ammie ta kira Yaa Muhammad amma har yanzu babu Anasi babu labarin sa tamkar an aiki bawa garinsu.
Ƙarshe haka ta ɗaga waya ta kira Faris tana mai fashewa da kuka ta faɗa mishi abin da Drivern ya yi mata kuma bata zargin kowa sai Anaam.
*******
A gidan kuwa, suna nan har Ammie ta fara damuwa akan rashin zuwan Muhammad yau sannan gabaɗaya kuma ba su ji daga gare shi ba. Sai gashi ya shigo yace su fito akwai inda za su yanzu-yanzu.
Tambayar sa suka shiga yi akan ina ne yake shirin kai su, yace kawai su daure su bari sai sun isa tukun koma miye za su gani.
Da haka suka shirya Sharp-Sharp, Ammie, Anaam, Na'imatu, Aysha da kuma Mama Hanne suka fito suka shiga wata babbar luxurious Bus dake parke a parking lot ɗin gidan suka tafi.
Har suka isa inda za su babu wanda ya sake yiwa ɗan uwansa magana sai da Ammie taga sun shige cikin wani babban gate ɗin Asibiti sun tsaya a haraba sannan ta kalle shi a ruɗe ta ce.
"Madu na ganmu a asibiti....mi kuma muke a nan? Waye ba shi da lafiya? Ko Alhaji ne Madu??"
Da sauri ya girgiza kansa, cikin tausasa kalamai ya ce.
"Hajiya alheri ne ki kwantar da hankalinki..."
Daga irin kallon maraicin da yaga Aysha na masa yasan dole itama ta ƙagu taji miye abinda ya kawo su nan ɗin.
Hakan yasa ya jinjina kansa ya ce.
"Duk abinda zai samu bawa a rayuwa muƙaddari ne daga wurin ubangiji,haka zalika rayuwa da mutuwa dukkansu a hannun Allah su ke...Alhamdulillah a kowane irin yanayi. Cikin amincewar Ubangiji mun samu kira daga Inspector Amit a daren jiya cewa sun samu gawar a mukarram a yashe...."
Lokaci ɗaya suka ɗauki kalma musamman Aysha da ta fashe da wani irin azababben kuka wanda hatta mutanen da ke sintiri a harabar asibitin sai da suka tsaya suna kallon su.
Cikin ƙarfafa gwiwa ya yi saurin katse su da faɗin.
" Ban fa ce muku ya mutu ba, ya kamata ku bari na kai ƙarshen maganata. Koda waɗan nan bayin Allahn suka tsince shi sun ɗauka cewa bashi da rai. Sai da su Inspector Amit suka isa akai shi asibiti aka tabbatar yana da rai sannan ya kira ni, gabaɗaya ban sanar muku ba sai da ya ɗan dawo hayyanci shi sannan, amma Alhaji yana nan tun da safen nan tare da shi da Mubarak Baba Salisu. "
Daga haka ya shiga gaba suka bi bayan sa sai gasu cikin ɗakin da mukarram ɗin yake kwance.
Duk da cewa gashi sun tabbatar yana raye, ganin mummunan halin da yake ciki ba ƙaramin ɗaga musu hankali ya yi ba. Ya yi baƙi ya rame, ga bange ko'ina da alama har da raunuka a tare da shi. Sai kuka suke suna ta yi wa wanda yayi sanadiyyar shigar sa cikin wannan halin baƙar addu'a da fatan ɗaiɗaicewa har ƙarshen rayuwar sa. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*BOOK ONE* *PAGE 34*
Kallon su Mubarak ya yi tamkar zai fashe da kuka tsabar tausayin halin da ɗan uwan na sa yake ciki ya ce.
"Nan ya samu sauƙi sosai fiye da yanda aka tsince shi a daren jiya...."
Ido Mama Hanne ta waro tsabar mamaki ta ce.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Mubarak a haka ɗin?"
Hannu Anaam ta ɗora akan kafaɗar Aysha alamar rarrashi duk da cewa ba ta da wasu kalmomi za ta iya amfani da su yanzu, ita kanta tana da buƙatar wanda zai ƙwarara ta domin ji take tamkar zuciyanta za ta fashe tsabar damuwa da takaicin halin da ɗan uwan nata yake ciki.
Suna nan a tsaitsaye jiki a sanyaye wanda baka jin komai sai sautin koke-koken su Alhaji Ridwan ya tura ƙofar ya shigo hannayensa riƙe da takardu.
Cike da tausayawa ya kakkallesu yace.
"Haba ku kuwa! Ina amfanin wannan koke-koken da kuka tsaya kuna yi masa a kai. Ai sai dai ce Alhamdulillah tun da har an same shi yana raye. Dan Allah ku yi haƙuri, Mukarram yanzu addu'ar ku yake buƙata. Ku ci gaba da yi masa addu'a in sha Allahu zai samu lafiya."
Daga haka ya ƙara matsawa dab da Alhaji Mas'ood yana miƙa masa papers ɗinda ke hannunsa ya ce.
" An gama shirya komai, and the flight too is ready. Sai ayi a hanzarta tafiya. Allah ubangiji ya bashi lafiya mai amfani yasa kaffara ne."
Jinjina kai Abbahn ya yi ya ce.
"Amin amin yah Allah, na gode sosai Allah ya saka da alheri ya bar zumunci Alhaji Ridwan. Na gode."
"Ina Doctor ɗin yake? Su zo su shirya mana shi yanda za'a ɗauke shi su kawo mana gado."
Cewar Yaa Muhammad yana mai matsawa kusa da Mukarram ɗin da nufin tattara kayan da ke wurin.
Kallon Aysha ya yi wacce tun ɗazu ta dasƙare a wuri ɗaya tamkar mutum mutumi ya ce.
"Zamu ɗauke shi zuwa India domin ci gaba da yi masa magani, za ku taho daga baya zuwa jibi..."
Girgiza kanta ta yi tana mai jin wasu sabbin hawaye ta ce.
"Yaya Muhammad ba zan iya jira ba. Idan kuka tafi dashi kuka bar ni a nan zuciyata za ta iya bugawa. Dan Allah ku tafi dani in kula da shi dan Allah..."
Shiru ya yi na ɗan lokaci sannan daga karshe ya jinjina kansa yace.
"Shi ke nan. Allah ubangiji ya bashi lafiya mai amfani."
"Amin."
Addu'ar samun lafiya duk suka yi masa sannan suka fice ɗakin ya rage daga Abbah sai Ammie da kuma Aysha. Itama Aysha ganin hakan yasa ta fice ta tsaya a bakin ɗakin tayi shiru tana ta yi masa addu'a a cikin ranta.
Ammie kuwa, sai yanzu wasu sabbin hawaye masu zafi sosai suka sake wanke mata fuskarta. Kamar yanda ta kafe idanuwanta tana kallon gadon da Mukarram ɗin ke kwance haka shima Abbah ya yi.
Cike da jin ƙuna a ranta ta mayar da kallonta gun Alhaji Mas'ood, Mijinta, uban 'ya' yanta ta ce.
"Alhaji waye wanda ya aikata mana haka? Miye yasa ya yi mana haka? Kowaye ya yi mana haka ya yi ne kawai domin wata manufa ta ƙashin kansa, dubi ka gani irin muna nan raunukan da suke jikin sa...Alhaji Gimba ya cutar damu."
"Hajiya Nasmah...ki daina kukan nan ya isa haka, ki yi haƙuri ki yi ta addu'ar Allah ubangiji ya tashi kafaɗunsa. Ba na ce ga wanda yake bayan wannan abin ba, amma koma waye mu mun yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinta. Mun bar shi da girman haƙƙin sa da ya ɗauka yaje Allah ya saka masa. Ki koma gida da yaran nan, zuwa jibi sai ku taho kafin nan ya ƙara warwarewa. Ke uwa ce, Haƙiƙa nasan kina jin raɗaɗi da ƙunci fiye da yanda nake ji..."
Sautin kukanta ne ya ƙaru tana mai girgiza kai a hankali ta ce.
" Kowaye ya yi sanadin raba shi da lafiyar sa. Ya saka shi a ƙunci da baƙin ciki, ya raba shi da iyalinshi tsawon lokaci sannan kuma ya yi masa sanadiyyar rasa aikinsa. Alhaji wannan wace irin mugunta ce?"
Kanta ya ɗora a kafaɗar shi a hankali ya ce.
"Ya isa Hajiya. Allah yana tare da shi, babu abin da zai same shi. Aiki in sha Allahu Allah zai maye masa da mafi alheri."
********
Tun da ya koma Lagos ya rasa ma wanne kalar tunani ya kamata ya yi. Gabaɗaya notikan kansa sun kwance. Bacci wannan duk daren Allah sai dai idan ɓarawo ne zai zo ya sace sa, amma yanda yake ganin rana haka yake ganin dare.