Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 27

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 27

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 27: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 27. Bai shirya aurenta ba, Sam bai kawo ta a cikin lissafin rayuwar…

3,354 words

Bai shirya aurenta ba, Sam bai kawo ta a cikin lissafin rayuwar sa ba. Dama ace tun farko bai biyewa son zuciyarsa ba har yaje tsautsayi yasa ya faɗa a turke mai taɓo ba har ya aikata wannan mummunan aikin da yanzu bai ma san ta ba. Fansar da ke tsakaninsa da mahaifinta da yanzu a tsakanin su ɗin ne kawai, but ta ya ya zai fara ma zancen auren ɗiyar maƙiyinsa wanda ya kashe masa mahaifinsa? Ta ya ya zai iya fuskantar mahaifiyarsa da wannan magana?

She deserve to be happy because kukanta yana ƙuntata masa zuciya. Damuwarta da ganin zubar hawayenta suna hana masa sukuni. He's always feeling guilt because Shi ne silar zubar hawayenta. But har cikin zuciyarsa he meant to seek her forgiveness, amma Kuma babu plan ɗin aurenta a cikin tsarin sa. Ko sama da ƙasa za su haɗe ya sani har abada mahaifiyarsa ba za ta amince da ya aure ta ba.

"Tabbas Maryam ita ce tafi cancanta da ka aura Maheer. You are the one that ruined her life. Kai ne silar baƙin cikinta da damuwar ta, ka lalata mata gobenta ka rusa mata mafarkinta. Kai ne kaɗai wanda yasan sirrin baƙin cikin da ke kwance a akwatin sirrinta."

A hankali ya buɗe idanunsa waɗanda suka gama ƙanƙancewa tsabar damuwa ya kalle sa sai kuma ta kawar da kansa.

Shi kuwa Hamad ɗin, ƙarasowa ya yi cikin parlourn ya zauna still idanunsa a kansa ya ci gaba da cewa.

"Maheer rayuwa za ta yi mata wahala ko Ince tana kan yi mata wahala duk akan baƙin Fentin da ka goga mata. Ba kowane irin namiji ne zai iya fahimtar ta ba. Amma kuma duk wannan na san ba zai taɓa samuwa ba domin nasan har abadan abada Maami would never allow you to Marry her Ko da kuwa ita kaɗai ce mace a duniya. Maheer masu iya magana kan ce idan mutum yasan farkon fitina bai san ƙarshen ta ba. Duk wannan masifar kai ne wanda ya janyowa kansa. Alhaji Mas'ood zai iya zuwa a matsayin maƙiyin Mahaifiyarka na farko domin shi ne wanda ya kashe mata mijinta. Ban san ta wace fuska za ka fara kallonta ba idan kaje mata da zancen auren 'yarda... "

"And idan kuma na aure ta ba tare da ta sani ba fa?"

Cikin jin wani irin maɗaukakin mamaki Hamad ya waro ido ba shiri ya kalli Maheer ɗin tsabar shock ya ce.

"Maheer an ya kai mutum ne kuwa? Wannan wace irin magana ce? Taya ya kake tunanin aure ba tare da sanin mahaifiyarka ba?"

"Ka faɗi gaskiyar da ya kamata ace na duba domin cire ta a cikin ƙangin da na saka ta kamar yanda Dina itama taga cancantan hakan..."

Da sauri Hamad ya girgiza kansa ya ce.

"Ba zai taɓa faruwa ba Maheer. Mahaifiyar ka fa...mahaifiyarka wacce baka da tamkar ta a duniya and kai ma kai ne wanda bata da tamkar ka a duniya. Wannan alama ce ta cin amana da ha'inci. Kada ka ci gaba da zamowa mutum mai son kansa Maheer. Kada ka yi ƙoƙarin sake ɗora wani sabon laifin akan wanda ka binne a baya. Haƙƙin uwa ba ƙarami ba ne kada ka manta...infact! Mu rufe wannan babin domin shi ne abin da ya fiye mana alheri gabaɗaya."

Miƙewa ya yi ya shige Sharp-Sharp ya canja kaya ya fito kai tsaye ya fice ya bar Hamad a zaune ba tare da ya sake kallon inda yake zaune ba.

Girgiza kai Hamad ya yi yana mai sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya ran sa fal da mamakin rayuwa irin ta Maheer. Idan ya yi wani abun sai ka rantse da Allah cewa wani irin jahili ne wanda bai san abin da yake yi ba. Idan ba shi ba ta ya zai furta cewa ya yi aure ba tare da sanin mahaifiyar sa ba? Auren ma da ɗiyar maƙiyanta. Hmm! Hauka yake ma.

******

Sai da su Ammie suka shafe tsawon sati ɗaya suna zaman ji da mutane masu zuwa yi musu jaje da barka da arzikin dawowar Mukarram sannan daga ƙarshe suka shirya tafiya ita da Anaam, mubarak, Rabi'a da kuma su Mufida yaran su Mukarram ɗin. Ya yin da ita kuma Na'ima akace ta shirya tabi Mijinta su koma Adamawa daman kuma ga shi yaron cikine da ita. Haka ta koma amma ba don ranta ya so ba.

Duk wanda ka kalla daga cikinsu baya cikin ɗaɗin rai idan ka cire Rabi'a. Wannan ta kasance daga cikin tafiya marar daɗi da suka taɓa yi saboda irin halin da Mukarram ɗin yake ciki, duk da cewa an sanar da su ya samu sauƙi sosai. Amma kuma a wurin Rabi'a ita kam wannan tafiyar ta kasance mata ta musamman da ta bar mata tarihi a rayuwar ta domin ita ce tafiyarta ta farko zuwa ƙasar waje.

Hakan yasa take cikin tsananin farin ciki sai nishaɗi take tana ƙara godewa irin jajircewar da Umma ta yi wurin ganin cewa zamanta ya ɗore a gidan wanda ga shi abubuwan ci gaba sai zuwar mata suke wanda suke daɗa ƙara mata girma da jin kanta a wani irin babban matsayi.

Hakan yasa ta yi wa Umma alƙawarin cewa za ta yo musu siyayya mai yawa idan ta tashi dawowa.

Har Airport Na'ima Hassan ta cim mata ita da mahaifiyarta suka yi musu barka da arziki sannan suka yi musu fatan sauka lafiya da addu'ar Allah ya bai wa mukarram ɗin lafiya.

Tun da suka tsaya suna magana Anaam ta lura da irin kallon banzar da Rabi'a ke jifan Na'ima da shi tamkar idanunta za su zazzago. Murmushi kawai tayi tare da kawar da kanta tayi tamkar bata ganta ba amma kuma a ranta ta shirya mata martani na musamman idan suka sauka. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 35*

Gidan Mukarram ɗin suka fara sauka. Sun tsaya ne da sunan su huta su ci abinci amma kuma damar hakan bata samu ba, domin Anaam bata saurara musu ba sai da suka shirya haka nan suka isa asibitin da yake kwance.

Alhamdulillah! A wannan karon sun same shi cikin yanayi mai dama-dama ba kaman last week da suka iske shi tamkar ba zai rayu ba.

Kyakkyawan murmushi ya sakarwa Anaam wacce tun shigarta ɗakin ta ja tunga ta tsaya a bakin ƙofa tana mai zubo da ruwan hawayen tausayin Yayan na ta. Ganin kowa ya gaishe da shi ya yi mishi ya jiki amma ita ta tsaya a gefe yasa Mubarak ya ce.

"Duk murnar ce haka? Abeg ki fara gaishe da mutum tukun sannan sai ki ci gaba da tsayuwa tun da aikin Soja kika fara."

Ware hannayensa ya yi alamar ta taho, ganin hakan yasa ta taka a hankali taje ta bashi side hug tana mai zubo da ruwan hawaye ta ce.

"Yaa Mukarram ya jiki? Allah ya baka lafiya mai amfani."

"Amin Maryam, na gode. Ya kike ya school?"

Hannayenshi ta kamo tana mai bin ko'ina na jikin shi da kallo ganin irin raunukan da ya ji da kuma shatin bulolin da ta gani ɓaro-ɓaro sun fito yasa ta ƙara sautin kukanta tana faɗin.

"Dukan ka suka yi ta yi ko Yaa Mukarram? Suka yi ta azabtar da kai? Miye ka aika ta musu da zafi haka?"

Hannu ya kai a hankali yana share mata hawaye tare da ƙara Faɗaɗa murmushinsa wanda duk wanda ya kalle sa yasan yana yin sa ne ba don daɗin rai ba ya ce.

"Haba ke kuwa! Miye na kuka? Ba gani raye a gabanki ba. Wahala ruwa ce, komai daren daɗewa watarana za'a shanye..."

Murya cike da kuka Ammie ta ce.

"Ko ni tambayar da nake ta yi wa kai na kenan tsawon lokaci. Laifin me suka ce ka aikata musu da ka cancanci wannan zaluncin?"

Wani murmushi ya saki wanda yafi kuka ciwo ya wani girgiza kai ya ce.

"Tun da na haɗu da tsohon ma'aikacin Alhaji Gimba ban ƙara sanin a ina nake ba. Na rasa yanda akayi hakan ta faru, sai dai na farko na gani a cikin wani ɗaki mai tsananin duhu. Dukan safe daban na rana daban na dare daban. Na tambaye su mi suke so sai suka ce babu abin da suke so, su kawai umurni aka ba su akan su yi min wulaƙanci su yi ta duka na har na ƙwamma cewa mutuwa da rayuwa....."

Lokaci ɗaya suka ɗauki kalma akan tsananin mamakin irin wannan abun da al'ajabi. Ammie na wani irin kuka tana girgiza kai ta ce.

"Gimba ina roƙon Allah ubangiji ya wulaƙanta ka, yanda Alhaji ya janyo ka inuwa ya sanya maka rigar arziki har ka cusa mana waɗan nan kalolin baƙin cikin Allah ya haɗa ka da masifa da bala'i, Allah ya...."

"Ya isa Hajiya Nasmah?!!"

Abbah ya faɗa a ɗan tsawace yana mai ɗaga mata hannu. Ido suka zuba suna kallon shi kallo na mamaki da al'ajabi. Itama Ammie da wani irin mamaki ta kalle shi tare da jinjina kanta ta ce.

"Alhaji!! Alhaji mi kake nufi? An zalunce ni an zalunci ɗana kuma ka hanani Magana? Alhaji..."

"Ba haka ba ne Hajiya Nasmah. Wannan abun duk bashi da amfani, kuma daga yau bana so in ji wata magana makamanciyar wannan..."

Ganin suka yi Muhammad ya fice daga ɗakin kai tsaye wanda hakan baya rasa nasaba da jin furucin mahaifinsu. Mutum kullum kamar shi ne yafi kowa haƙuri, ga dama ga hujjoji amma yaƙi bari su goge renin da yake tsakanin su da Alhaji Gimba. Wannan wace irin rayuwa ce? Tambayar Muhammad ɗin ke ta yi wa kansa kenan tamkar zai suƙe tsabar ta kai ci.

Mubarak na ganin ya fice shima ya sulale ya yi tafiyar sa, A haka duk suka fice wanda ya rage daga Abban sai Anaam da kuma Aysha, daman Rabi'a ita a bar maganar ta domin tana can tana abun da ya dame ta wato chatting da farin cikin ta.

******

Maheer na cikin shirin sa na tafiya Oman wanda har ya riga ya haɗa Bag ɗinsa kawai ya ji ƙarar wayarsa. Yana dubawa ya ga numbern Hamad.

Ignoring Kiran ya yi tare da ɗaukan jakan ya fice wanda yana batun shiga mota sai ga Hamad ɗin ya shigo.

Kallon Hamad ɗin ya yi sai kuma ya kawar da kai tamkar bai taɓa sanin sa ba.

Cike da mamaki Hamad ya ce.

"Dina told me that you agree to marry the girl. And you even bought an apartment in Abuja..."

"Yeah..."

"Maheer kuskure kake neman aikatawa a kan wani kuskure. Kada ka auri yarinyar nan. Ka manta da ita ka fita harkarta Maheer...."

Wani kallon ya yi masa yana mai ƙara tamke fuska ya ce.

"Don't be scared, na riga na sayi iyaye and za su tsayamin daga farko har ƙarshe..."

Kusan dasƙarewa Hamad ya yi jin wata irin bahaguwar magana. He hired a parent? Maheer na da hankali kuwa? Anya yasa abin da yake? Ta ya ya zai sa yi iyayen Ƙarya?

Cikin jin rashin gamsuwa da maganan yasa ya yi saurin girgiza kai ya ce.

"No no! You must be joking...infact ma waɗan ne irin mutane ne za su yarda ka yi hayar su domin su yi maka jagorancin auren rashin gaskiya?"

Wani smirking ya yi tare da jinjina kansa ya ce.

"Kuɗi na basu, I paid them ta Yanda ba za su iya cewa a'a ba because i can't present my parent to them and Haka kuma ba zan iya ma Maami presenting iyayenta ba and the worst of it Shi ne ma yarinyar..."

Cikin takaici Hamad ya girgiza kansa ya ce.

"I would never allowed that to happen. And Even Dina too, ka yaudare ta. Da ta san waye kai har abada ba za ta taɓa bari ka ko raɓi inda inuwar Anaam take ba. Kai ɗin sai yau na tabbata kura ne lulluɓe da fatar akuya. Wallahy ka ji tsoron Allah."

Daga haka ya juya ya yi tafiyar sa. Lokuta da dama na rayuwar sa ya kan ji nadama da takaicin sanin wannan mutumin da ya ɗauka a matsayin amini a rayuwarsa. Daga lokacin da ya tsallake umarnin mahaifiyarsa ya je ya saɓawa Ubangiji tun a lokacin yake jin wani iri a ransa dangane da shi. Ya cutar da yarinya mutane ya jefa ta a tashin hankali da baƙin ciki kuma still bai ishe sa ba nema yake ya sake ƙuntata mata a karo na biyu.

Shi kuwa Maheer, ɗage shoulder ɗinsa ya yi yana mai taɓe baki alamar ko a jikinsa sannan daga Ƙarshe ya shige mota wanda ɗaya daga cikin ma'aikatan companyn na su ne wanda yake as driver ya ja suka tafi.

*******

Sai da muka shafe kwana uku muna zarya wanda daga gida sai asibiti domin bamu samu damar zuwa ko'ina ba. Daman tun a ranar kowa ya shiga yin sabgar gabansa musamman Yaa Muhammad da ya ɗauki zafi sosai akan hukuncin Abbah da ya yanke akan Alhaji Gimba wanda su Sam bai yi musu daɗi ba.

Yau ma shigowarsu kenan bayan sun dawo daga asibiti suka tarar da Abbah, Yaa Muhammad da kuma Yaa Mubarak suna zaune da takardu a gabansu wanda da alama akwai aikin da suke.

Zaunawa suka yi suka gaishe da su sannan Abbah ya kalli Anaam yana murmushi ya ce.

"Maryam kuna ta ɗawainiya ko? Sannun ku da ƙoƙari Allah ya saka muku da alheri ya bar zumunci."

Cikin nuna jin daɗin addu'arsa ta washe baki ta ce.

"Amin amin Abbah. Kai ma Allah ya saka maka da alheri, Allah ya ƙara maka tsawon rai mai albarka amin."

"Amin, na gode. Ya ya labarin karatun ku? Na'ima tana keeping ɗin ki updated ko?"

Jinjina kanta ta yi ta ce.

"Eh Abbah, ko ɗazu ba jimawa mun yi waya da ita, lectures komai lafiya ƙalau Abbah.."

Cike da neman tsokana Mubarak ya ce.

"Amma dai wannan Na'imar Yare ce ko? Ko yaren dai wata ƙil ba sananne ba..."

Ɓata fuska ta yi tana mai kallon Muhammad ta ce.

"Yaa Muhammad ka ce ya fita harkata wallahy."

Tattara papers ɗin gaban shi yana faɗin.

"Tun da shiga sabgar da babu ruwansa ne aikinsa ai sai ya yi ta yi."

Sai yanzu Alhaji Mas'ood ya waiga gun Rabi'a da ke ta ɓata rai still da murmushi ya ce.

"Rabi'a! Na ji kin yi shiru, ya labarin karatun na ki? Ke har yanxu baki da wata Ƙawa be?"

Girgiza kanta ta yi ta ce.

"Ni ban yi kowace Ƙawa ba Abbah, ni daman tara ƙawaye ba ɗabi'a ta bace, domin ta nan ne ake haɗuwa da ɓata gari."

Cikin nuna jin daɗin maganar ta Abbah ya jinjina kansa ya ce.

"that's very good to hear, Allah ya taimaka ya baku mazaje na gari."

Kallon ta yake har yanzu, wanda ya fahimci kamar har yanxu akwai sauran magana a bakinta, hakan yasa ya ce mata.

"Rabi'a ko akwai wani abu?"

Jinjina kai ta yi tana mai ƙara kwantar da kai ta ce.

"Abbah wannan ɗin shi ne zuwa na na farko, dan Allah a ɗan zaga gari damu mana."

Jinjina kai ya yi ya ce.

"Okay. Wannan ai ba abin damuwa ba ne sai ku tafi tare da Mubarak..."

Turo baki Anaam ta yi sannan ta ce.

"Ni dai Abbah a ganina tunda tafiyar nan ba ta daɗi ba ce bai kamata ace mun tafi yawo ba. Yaa mukarram mutum ne wanda yake ɗaukar damuwar en uwansa da matuƙar muhimmanci a kowane irin yanayi, bai kyautu ace a irin abin da ya same shi ba wai ace har mu shirya mu shiga gari gaskya hakan bai yi ba,ko shi ya ji he won't be Happy Kuma zai ga kaman ba'a ɗauke shi da Muhimmanci ba. Saboda haka ni a ganina ma ya kamata mu bi Yaa Mubarak mu koma gida da yammar nan saboda yanayin karatu and especially ita da ba ta da wanda yake sanar da ita abin da yake faruwa a class ɗin na su."

Jinjina kai Abbah ya yi cikin jin gamsuwa da bayanin ta ya ce.

" Gaskiya wannan tunani ne mai kyau, kuma hakan shi ne daidai. Saboda haka ke Rabi'a ki yi haƙuri ki bari har ku sake dawowa sai ku je. "

Jinjina kai ta yi ba don ran ta ya yi mata daɗi ba sannan ta miƙe tsam ta yi shigewarta. Tabbas ran ta ba ƙarami sosuwa ya yi ba domin ta fahimci da gangan Anaam ɗin ta yi domin kawai ta ƙunsa mata baƙin ciki.

Hakan yasa tana shigewa ta faɗa kan gado ta fashe da kuka tana mai janyo wayarta ta kira Saurayinta tana koka masa irin kalar wulaƙancin da Anaam ke yi mata. Da ƙyar ya samu ya rarrashe ta tare da yi mata alƙawarin cewa ta kwantar da hankalinta, suna yin aure ba jimawa zai kai ta duk ƙasar da ranta ke so.

Har su Anaam suka je suka yowa su Ammie sallama a asibitin Rabi'a na ciki sai da akace ta fito su tafi sannan ta fito. A ranta sai tsine su musu take tana faɗin ina amfanin wannan tafiyar da baka tafi ko'ina daga gida sai asibiti. Sannan da Abbah ya ce za su dake dawowa su dawo a ina tunda Mukarram ɗin an riga an kore sa a aiki. Baƙin ciki dai ne sun yi mata shi kuma ba zata yafe musu ba.

Tana nan a ƙuntace har suka isa Airport inda a nan ne ta matsa dab da Anaam ta kalle ta sannan ta jinjina kanta ta ce.

"Wannan shi ne karo na biyu, ki sani ba zan mata ba, kuma ba zan yafe ba."

Wani irin malalacin murmushi Anaam ɗin ta saki sannan ta Girgiza kai ta ce.

"Shi dai yaro yaro ne. To mu zuba mu gani ni da ke."

Har suka isa gida babu wanda ya sake yiwa wani magana. Kowa sabgogin gabansa ya ci gaba da yi wanda daga karshe ma Anaam ɗin ta tattara kayanta ta koma gidan Amina bata dawo ma gidan ba sai da ta share tsawon sati uku wanda a lokacin ne su Ammie suka dawo har da Mukarram ɗin wanda ya warke sumul kamar ba shi ba.

******

Hajiya Salamatu na tsaye a kitchen tana ta kokarin haɗa girkin rana Alhaji Gimba ya shigo yana ta wata annushuwa yana farin ciki.

Murmushi ta yi tare da girgiza kai ta ce.

"Alhaji wata ce kuma ta samu?"

Jinjina kai ya yi ya ce.

"Sosai kuwa Salamatu. Case close in ji bature. Saboda haka gobe sai gida. Ki faɗawa ɗan ki cewa ya shirya ya koma ya ci gaba da tsaremin sana'a ta."

"in sha Allahu Rabbi. Alhamdulillah! Allah ya ƙara tsarewa ya karemu daga sharrin maƙiya."

"Amin. Ki faɗawa idan ta farka domin ni fita zan yi. Na ga kwanakin nan ba ta da wani aiki sai na Kwanciya ta yi ta baccin asara ko gajiya ba ta yi."

"Uh uhm! To Allah ya kyauta, In sha Allahu zan faɗa mata."

Yana ficewa iyaka 30mnt sai ga Maimuna ta shigo kitchen ɗin tana ta buga uwar Hamma alamun jin yunwa. Kallon ta Hajiya Salamatu ta yi ta ce.

"Maimuna an taso? To daman Alhaji yace na sanar dake ki shirya gobe zamu koma gida...."

Wani irin kicin-kicin ta yi da fuska alamar rashin jindadi ta ce.

"Wallahy idan ma wani asiri kika yi kika shiga tsakanina da Mijina to ina tabbatar miki da cewa nan ba da jimawa ba alleshinki ya kusa karyewa. Muguwa azzaluma mai ƙwacen miji."

Daga haka ta juya kai tsaye ta koma ba tare da ta haɗa Tea ɗinda ta yi niyya ba.

Ita kuma Hajiya Salamatu girgiza kai kawai tayi tana mai faɗin Allah ya shirye ki a ranta sannan ta ci gaba da aikin da yake gabanta.

******

A gidan Dinaratu kuwa, yau da wuri ta shirya kalaman da za ta tsarawa Nameer Mijinta wanda ya kasance cousin brother ɗin Anaam. So take ta yi komai cikin tsari domin bata so su samu matsala akan maganar Alami. Maheer shi ne wanda yafi dacewa da Anaam saboda haka tana nan ta tsaya sai inda ƙarfin ta ya ƙare.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull