Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 28

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 28

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 28: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 28. Yana gama cin abincin dare ta zo ta zauna tana mai kallon fuskar…

3,360 words

Yana gama cin abincin dare ta zo ta zauna tana mai kallon fuskar sa ta ce. "Abban Arif wannan karon dai Maheer ya fallasa kansa akan son da na ce maka yana yi wa Anaam.... ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 36*

Kallon ta ya yi yana mai kurɓa ruwa daga glass cup ɗinda yake gabansa ya ce.

"Da gaske?"

Cike da ƙwarin gwiwa ta ce.

"Eh, ganin da ka yi masa ɗin nan kwana biyu da suka wuce. Ya zo ne domin ya sanar dani cewa yana sonta da aure. Please ya kamata ka fahimci manufata akan ganin cancantar Maheer da na yi."

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Look sweetheart, Ni fa ba wai ina ƙin Maheer ba ne, is just that bana so ace kece wacce ke son cusa mishi ita wanda hakan ba daidai ba ne, but idan shi ne ya yi ra'ayi ya ji yana sonta don karan kanshi I don't have any problem with that. Domin Maheer mutum ne mai matuƙar kirki, yana da sana'ar sa and yana da nagartattun family. His life style is different daga maza je da yawa. Allah yasa haɗuwar su ta kasance alheri."

Cikin jin tsantsar farin ciki ta saki wani irin murmushi ta ce.

"Amin amin yah Allah Abban Arif. Na gode sosai da fahimta ta da kayi. Anaam will live a peaceful and beautiful life in sha Allah. Ban taɓa ganin mahaifiyarsa ba, but Hamad ya san su farin sani, kuma tsawon shekaru bai ta ganin wani abun Allah wadai daga gare su ba."

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Haka ne. In sha Allahu...zan samu Oga Muhammad sai mu fara tattaunawa da shi tukun Muji..."

"Noo..! Kada ka fara mishi magana tukun, shi Maheer ɗin ya ce sai kun fara yin magana sannan aje gare su, yana da Muhimmin abin da yake so ku fara yin magana akai. Yace zai zo gobe don na faɗa masa ka yi tafiya sai yau idan ka dawo."

"Alright, ba damuwa, Allah ya kai mu goben lafiya."

"Amin. Shi kuwa Hamad ka ga dai yaƙi wannan yarinyar da aka kai masa kuɗin auren ta."

"Subhanallah! To miyasa?"

Hannayenta ta ware tare da ɗaga shoulder ɗinta ta ce.

"I don't know, ni kawai abin da ya faɗamin shi ne wai baya da ra'ayi da ita, and da na binciki Aliyu shi ma dai yace hakan ya faɗa masa. To yanzu dai har Alhajinmu ya je gidansu ya bai wa iyayenta haƙuri."

"Eyyah! To Allah yasa hakan shi ne mafi alheri."

"To amin ya Allah."

*******

Gidan Alhaji Gimba tun da suka wayi gari ya kira wayar Faris akan zancen tafiyarsu amma ga mamakinsa har ya bar gidan tun da sanyin safiya.

Abu wasa-wasa sai ga shi har misalin ƙarfe biyu sannan ya shigo bayan Alhaji Gimban ya gama zazzagawa Hajiya Salamatu ruwan rashin mutunci.

Tamkar wanda bai san abinda yake faruwa ba haka ya shigo gidan bayan yasan mahaifin nasa ya kira shi ya fi sau ashirin.

Ido suka zuba suna kallon sa wanda Alhaji Gimba ya wani taso cike da masifa ya ce.

"No wonder ka ke ta wasu ɗabi'u na daban, ashe neman mata ka fara."

Fuskar sa cike da mamaki ya kalle sa ya ce.

"Neman mata kuma?"

"Eh mana! Ai nasa an bibiyeka ne ko baka sani ba? Ina nan ina jiran ka ka koma ka ci gaba da tsare mini business ɗina, shi ne za ka tsaya shashanci kana biye mace."

Cikin ɗaga murya shi ma ya fara masa magana a harzuƙe ya ce.

"Ni fa ba yaro ba ne Daddy! Koda yaushe ina so ka sani ni ɗin ba yaro ba ne! Ba lallai sai ka saka ni a gaba ba ka tafi na ce zan zo daga baya..."

Hankali a tashe Hajiya Salamatu ta taso a fusace ta wanke masa fuska da mari tana faɗin.

"Har sau nawa zan faɗa maka cewa ka daina yi masa magana a haka? Shi ɗin nan fa mahaifinka ne Faris...Ka duba irin halin da ya shiga da sharrin da aka yi masa kuma duk don saboda kai ne! Mu fa musulmai ne ba kuma muna da dokoki da ubangiji ya sharɗan ta mana akan haƙƙoƙan iyaye da kuma na 'ya' ya... "

Zuciyarsa ce ya ji ta ƙara tafarfasa tamkar zai fashe tsabar zafin rai ya kalle ta sai kuma ya kalli mahaifin nasa yana nuna shi da yatsa ya ce.

"To idan haka ne ya kamata shi ma mijinki ki faɗa masa ya daina ɗauka ta a matsayin wanda bai san abin da yake ba. Kina ji a gaban ki yanzu ya gama faɗamin cewa wai na fara neman mata..."

"To idan ba neman mata ka fara ba miye tsakanin ka da yarinyar da aka ce yanzu kullum sai ka haɗu da ita?"

Yana mai ƙara ɗaga sautinsa ya ce.

"Ita ɗin budurwa ta ce, and I love her I want to marry her."

Cikin jin daɗin maganar da ya yi Alhaji Gimba ya ce.

"To ai ni that's what I want. Rashin auren ka yana damuna. Ka faɗamin gidansu yau ɗin nan ba sai an kwana ba zan je na nema maka aurenta..."

Girgiza kansa ya yi ya ce.

"Ban shirya ba tukun. I'm waiting for the right time."

"Right time ɗin Uwar me ka ke nema? Miye ka rasa a yanzu? Ko karatu take za'a iya yi kuma taci gaba da karatun ta, nobody will stop her..."

"Daddy tabbas zamu yi aure da ita, amma kuma muna jiran lokaci. Kayi tafiyar ka zan biyo ka daga baya. Muddin da wannan abar a tare da kai to har abada ba zan taɓa tafiya da kai ba..."

Ya ƙarashe maganar yana mai muna inda Maimuna take tsaye zaune tun ɗazu ta zuba musu ido tana kallon su.

" Faris matar tawa ce kake faɗin wannan magana akan ta?"

Banza ya yi masa tare da takawa ya shige ɗakinsa ya bar su nan.

Taɓe baki Maimunar ta yi sannan ta harari Hajiya Salamatu sama da ƙasa sannan ta ce.

" Uhm! Ai ni kuturwar uwa ce wacce zama dani ya zama dole, wallahy tallahy ko an ƙi ko an so dole ace da Mijin iya Baba."

Wani kallon Alhaji Gimban ya yi mata sannan ya ce.

"Maimuna bana son kina yi wa Hajiya Salamatu rashin kunya, na sha faɗa miki ba ɗaya ba ba biyu ba. Ita ɗin uwargidana ce, daman don tana goyon bayan maƙiya na ne yasa na auro ki, yanzu kuma da ta gane gaskiya ki bini a sannu, wallahy tallahy a kowane irin lokaci kina ganin takardar sakin ki kuma dole ki cikawa rigar ki iska. "

Jin hakan shi ne abin da ya haifar mata da wani irin mummunan faɗuwar gaba, hakan yasa ba shiri ta saukar da kai ta ce.

" Ka yi haƙuri ni bada ita nake ba."

"To ki bata haƙuri."

Kai tsaye ta ce.

"Ki yi haƙuri Hajiya."

Murmushi ta yi ta ce.

"Ba komai Maimuna. Allah ya ƙara mana hak'uri gabaɗaya."

"Amin."

"To sai mu tashi mu yi harama tun da ya kafe, duk sanda ya gama yaga dama sai ya taho."

*******

A cikin ƙayataccen kitchen ɗin Maaminsa yake tare da ita tana haɗa girkin da za ta kai wa Abiyh wato mahaifinta. Tun da ta wayi gari ya kira ta ya faɗamata abincinta yake so ya ci. Hakan yasa ta yi farin ciki ta tashi ta hau aikace aikace.

Shi ɗin ba gwani ba ne a girki kamar Hamad,domin tun da ya taso hannun mahaifin sa komai shi yake yi masa wanda hatta ruwa idan yace yana so a baki, to tabbas a baki zai sha ba tare ya riƙe kofi a hannunsa ba. Hakan yasa ya kasance ɗan gata na musamman, bayan kuma rasa mahaifinsa sai ya kasance rabin rayuwar sa duk a school ne. Hakan yasa bai iya girki ba domin bai san yanda ake shiga kitchen ba sai idan yana tare da Maamin sa ko kuma idan yana tare da Naana, wato kakar sa kuma iyaka ya tsaya yana tayata fira har a kambala. Shiyasa wani lokacin idan Hamad ya ɗanɗasa musu girki abin har mamaki yake basa tamkar wata Mace.

Yau ma dai kamar ko yaushe zaune yake akan stool riƙe da Tab a hannunsa yana rage aikin da ya baro wanda lectures ne yake yi wa ma'aikatan su da suke a Nigeria yana ba su horo.

Fira take ta masa sosai yayin da shima ya ƙagu ya kambala domin ya bata attention ɗinsa because it's the happiest moment to him a duk lokacin da suke fira da ita musamman firar da ta shafi Mahaifinsa.

Yana nan yana saurarenta sai kuma ya ɗago ya kalle ta wanda a lokacin ne idanunsa suka sauka akan abincin da take juyewa a warmer.

Murmushi ya ce tare da sniffing sosai ya ce.

"I will taste it too, and I'm sure cewa I'm gonna enjoy it well. Hannunki akwai daɗi my Maami, shiyasa tsohon nan yake tsallake girke-girken da ake masa yace dole sai naki, ita kuma Naana yanzu ba ƙarfin shiga kitchen."

Murmushi ta yi sannan ta je ta ɗauko plate da spoon ta zuba mishi tana faɗin.

"That's why a duk lokacin da na yi sallah sai na roƙi ubangiji akan ya haɗaka da mata ta gari, mai tsananin kirki da biyayya wacce ta iya sarrafa kalolin girke-girke kamar ni domin nasan kai ɗin nan muddin ba ka samu macenda ta iya girki ba za ka sha wahala domin baka iya ciyar da kanka. "

Ɗan guntun murmushi ya sakar mata kawai tare da jinjina kansa ba tare da yace mata uffan ba. But a can ƙasan ransa sai da ya ji wani abu ya harɓa masa mai kama da tsoro da kuma jin fargaba da tashin hankalin tuna abin da yake neman aikatawa bayan idon ta.

Ba zai bari ta sani ba, tabbas zai yi komai ya kambala kafin wa'adin aikin sa ya cika, wanda daga nan yasan in sha Allahu bayan sun yi auren zai samu hankali kwance ya faɗa mata gaskiya, idan ya samu ta yafe masa sai ya saketa taje ta yi auren ta shi ma ya dawo gida wurin mahaifiyar sa.

A yanzu ya gama yanke hukuncin aurenta, domin ya gama aunawa ya tabbatar cewa aurenta shi ne masalaha domin sa ma mata salama da sukunin rayuwa, idan har aka tabbatar da auren su koda ace ya sake ta ne daga baya shikenan ta fita daga kuncin da take ciki, daga wannan lokacin bata da wata fargabar auren wani namiji because kowaye yasan cewa ta taɓa yin aure saboda haka, he will never expect her to be Virgin ce.

"Maheerr....."

Maamin tasa ta ambata tana mai kamo ɗayan hannunsa ta ce.

"Why are you quite? In dai akan aure ne your Maami will never force you. Because ni na san cewa aure lokaci ne, idan lokaci ya yi za ka yi. Ba zan taɓa takura ka ba domin kai ɗin ba yaro bane kamar yanda ka saba faɗamin nasan cewa kasan abin da ya kamata. Just take your time Wurin nemo min suruka ta gari wacce ta dace da matsayinka da kuma tsarin rayuwarka. But who ever she is, let her be from our cycle, Idan ta kasance er Oman shike nan hankalina ya gama kwanciya bani da sauran wata fargaba."

Jinjina kansa ya yi tare da saurin miƙewa ya ce.

" Let's go Maami. Ya kamata muje da wuri yana can yana jira."

Cike da mamaki ta ce.

" Are you going with me? Ka fasa tafiyan ne?"

"I will. But ina so na rakaki ne, daga can akwai inda nake so mu biya, idan mun dawo zuwa yamma I will take my leave."

"Okay."

Sai da tayi wanka ta shirya ta fito, daman shi ya yi wankan tuntuni, hakan yasa koda ta fito har ya saka ma'aikatan ta sun kai abincin a mota sannan ya zauna zaman jiranta.

Suna zuwa iyaka 30minute ya ɗaukota a mota daga shi sai ita suka je shopping. Hajiya Lailah ba ƙaramin farin ciki ta yi ba domin sun ji ma basu fita a tare ba.

Sai wani ji da kanta take tana ɗaga shoulder musamman idan ta haɗu da Waɗanda ta sani ta yi ta nuna shi tana alfahari da cewa shi ɗin ɗanta ne ita ce mahaifiyarsa. Wannan ta kasance ɗabi'arta tun asali domin tana matuƙar ƙaunar sa.

Siyayya ya yi mata mai yawa wanda Abayas ne masu tsananin tsada waɗanda suka dace da ita da kuma sauran kayan buƙata duk ya saya mata a matsayinta na mahaifiyarsa wanda ba don ta rasa ba.

Wurin da aka ajiye gold ta tsaya ta zaɓo wata rantsatstsiyar sarƙa mai kyau marar hayaniya ta siya ta biya da kuɗinta koda yazo sai ta fito da ita tana murmushi ta ce.

"Wannan ɗin....it will serve as my first gift a wurin surukata Idan Allah ya nuna mini."

Kallon ta ya yi cike da mamaki a ransa sai kuma ya kalli sarƙa sannan ya jinjina kansa kawai ya yi murmushi tare da kai hannu ya karɓi necklace ɗin ya ce.

"Ni zan ajiye..."

Dariya ta yi ta ce.

"Kaman ya ya? Ni na siya kayata saboda haka ni zan ajiye..."

Langwaɓar da kansa ya yi ya ce.

"Maami dan Allah mana!"

"To akan me za ka ce kai za ka ajiye saboda neman rigima? Kai ka siya ko ni?"

"But Maami idan tana tare da ni, zai fi bani ƙwarin gwiwa da himma wurin ganin cewa na samo miki ita da wuri. And duk time ɗinda na ɗauko ta na kalla zan ji sanyi a raina sannan na san cewa watarana nima zan yi aure na zamo miji mai bayar da umarni ko ba haka ba Maami. "

Dariyar ta ƙara yi sannan ta jinjina kanta ta ce.

"Haka ka dawo kuma? To shi ke nan na bar maka ka riƙe ɗin. Allah ubangiji ya nuna mana wannan lokacin lafiya yasa ina raye.

" Amin amin yah Allah my Maami."

Daga haka ya ja hannunta suka wuce suka sha lemu a wani wurin shakatawa sannan suka koma gida.

Sai da ya yi sallar Asr ya huta sannan ya yi wanka ya fito ya wuce. Plane ɗin Abuja ya hau direct ya sauka a sabon gidansa da ya saya wanda har yanzu bai gama yanke shawarar da ya ji tana zuwa masa a rai ba.

Sai misalin 11pm Sannan ya fito cikin manyan kaya sai baza uban ƙamshi yake ya hau sabuwar motar da ya saya a lokacin da ya sayi gidan yaja ya tafi gidan su Yaa Dinaratu.

A rumfar shan iskan da ke can gefen harabar gidan suka zauna da shi da Nameer ɗin kamar yanda ya buƙata.

Da ya ƙara jin maganar a bakin Maheer ɗin hakan sai ya ƙara bashi tabbaci wanda ya saka shi jin daɗi sosai a ransa. Sai dai kuma bayanin da ya ɗora masa ne daga baya sai ya ji zancen ya yi masa wani iri domin bai fahimce shi ba sannan kuma bai ji cewa ya gamsu ba.

Hakan yasa ya girgiza kansa ya ce.

"To amma miyasa baka so su san daga wata ƙasar kake?"

Kai tsaye ya ce.

"Because bana so ta ji a ranta cewa kamar watarana zan iya raba ta da iyayenta ne ko kuma in raba ta da 'ya' yanta, but a hankali watarana zamu kai karshen wannan."

"But Maheer..."

"Oga Nameer...dangin mahaifi su ne ake ado da su da kuma tinƙaho a wurin neman aure, dangin mahaifina dake nan su ne za su jagoranci komai, and mahaifiyata za ta zo ita da danginta sai dai kuma ni ɗin bana so ko kaɗan su ji cewa wai daga Oman nake ko wani nawa please ka yi min wannan alƙawarin."

Jinjina kai Abban Arif ɗin ya yi sannan ya sauke numfashi s hankali ya ce.

"Shike nan, Allah ubangiji ya yi jagora. In sha Allah zan samu yayyunta guda biyu zamu tattauna daga nan za su kai maganar wurin mahaifinsu, duk abin da suka yanke, in sha Allahu za ka ji daga gare ni."

"Thank you so much sir."

Daga haka suka yi sallama ya fito. Yana fitowa daga gidan ya kira numbern Hamad, yana jin ya yi picking ya ce.

"Har yanzu kana kan bakanka ko kuma zaka sauko ne ka tayata ni fighting?"

Girgiza kai Hamad ya yi tamkar yana a gaban sa ya ce.

"Ba zan taɓa goyon bayan rashin gaskiya ba. Lokaci na ɗibar maka Maheer,daga zaran kuma ya cika indai baka janye ba to ina tabbatar maka sai na faɗawa Maami da su Abiyh abin da kake shiryawa, haka zalika sai na faɗawa Dinaratu."

Wata irin Dariyar kama raina wa kanka hankali ya yi sannan ya ce.

" Ba za ka taɓa iyawa ba Hamad."

" Zamu gani!"

" Ni ma na ce zamu gani." ✍️ *OUM-AMEER* ✍️'

*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 37*

Yau ko da suka wayi gari tun Asubah Alhaji Mas'ood yace su shirya kaf Ahlin gidan akwai inda za su tafi wanda ko Hajiya Nasmah da take matarshi ba ta san miye shirin nasa ba, domin kamar yanda kowa ya tsinta daga sama to itama haka ta tsinta. Hakan yasa itama ta hau shiri kaman yanda kowa ke yi, suna nan sai misalin 11am Sannan suka jeru har da su Mukarram suka tafi.

Mamaki ne ya ƙara kama su ganin yanda ilahirin motocin gidan suka jeru a tsari wanda tabbas wannan baya rasa nasaba da umarnin Alhaji Mas'ood.

Suna cikin tafiya ya basu umarni da su tsaya, bayan sun tsaya yasa aka rufewa Mukarram fuska da ƙyalle sannan yace su ƙarasa a inda za su isa a haka.

Ganin hakan yasa Hajiya Nasmah ta kalli mijin na ta tana murmushi ta ce.

"Alhaji what are you up to? Na yi ƙoƙarin haɗa tunanina but na kasa..."

Jinjina kansa ya yi yana murmushi ya ce.

"Albishir ɗinda baka san da shi ba akace yafi daɗi zama daɗi. Ke dai kawai ki haƙura za ki gani."

" Tau Alhaji, Allah ubangiji yasa mu ga alheri amin."

Daga nan shiru ne ya ratsa tsakaninsu har suka wani katafaren gini wanda ya amsa sunan sa.

Tun a bakin tamfatsetsen gate ɗin ginin ya ce kowa ya tsaya nan sannan ya ce a fito da Mukarram.

Matsowa Muhammad ya yi zuwa gaba da shi da Mubarak suna ta murmushin farin ciki. Kallon su Anaam ta yi da mamaki domin dai ita a iya sanin ta tasan cewa Yaa Muhammad yana China tare da Yaa Naseer sai kuma Yaa Mubarak da yake Gusau, but how comes za'a ce suna nan a lokaci ɗaya? and still ga shi har da Yaa Nameer shi ma ya zo tare da Baba Salisu da Daddy Ridwan kai har da ma wasu mutane tsirarru waɗanda ba ta waye su ba.

Fuskar Mukarram ɗin Abbah ya yi umarni da aka buɗe sannan kuma yace ya yi addu'a kafin ya buɗe idon na sa.

Muhammad shi ne wanda ya buɗe masa fuskar yana mai yi masa wani murmushin farin ciki ya ce.

"Ka buɗe idanunka da zuciyarka Mukarram sannan ka karɓi wannan Alkairin da hannu biyu."

A hankali kuwa ya shiga buɗe idon yana mai kwararo addu'a yana tasbihi zuwa ubangijin da ba shi da abokin tarayya har ya kambala buɗe.

Ƙirjin shi ne ya ji ya buga bayan ya ware idanunsa ya kalli girman Gate ɗin da ginin da ke zagaye da shi yana mai kallon Yayansa da Alhajinsu ya ce.

"Zuciyata tana faɗamin wani abu, amma dan Allah wannan ɗin mine ne?"

Jinjina kai Yaa Muhammad ya yi still da murmushi a fuskar sa sannan ya ce.

"Kyautar Asibiti ce daga mahaifinka Dr. Mukarram...."

Cikin tsananin mamaki ya ce.

"What? Asibiti kuma?"

Jinjina kai Alhaji Mas'ood ya yi yana kallon sa ya ce.

"Asibiti ce Mukarram..."

"But Alhaji I already made my decision cewa zan ci gaba da aiki a company."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull