Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 29

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 29

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 29: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 29. "Na san mafarki kuma nasan burin ka tun asali Mukarram. Tun a…

3,364 words

"Na san mafarki kuma nasan burin ka tun asali Mukarram. Tun a lokacin farko da na so kaci gaba da aiki a company ka manta da asibiti ka ƙi ka na cewa Aikin yasa na ji na gamsu da abinda kake muradi. Tun da ka kama aiki a India daidai da rana ɗaya ba'a taɓa yin complain a kan ka ba sai dai ma godiya da lambobin yabo da karramawa da ka ke samu daga gare su. Wallhy mukarram har yau na kasa yarda ace wai su ne suka baka takardar cewa wai sun sallame ka, na yi matuƙar mamaki bayan sun ji cewa you were kidnapped Wanda sun san cewa is not your fault amma kuma suka kore ka. Wannan abun ya Dakar mini zuciya and as far as ka tsayu tsayin shekaru kana taimakawa al'umma kuma suna jindaɗi suna gode maka, I will never let that dream of yours to be shattered. That's why tun daga wannan ranar na bai wa Yayanka kwangilar gina maka wannan domin nan ne yafi dacewa da kai ba company ba."

Kowannen su sai da ya yi hawayen farin ciki musamman Hajiya Nasmah wacce ta ƙara jin girma da kimar Mijinta a idanun ta. Tabbas shi ɗin cikakken mahaifi ne wanda ya cancanta wanda ya san girma da Muhimmancin iyalansa.

" Hajiya!"

Mukarram ɗin ya ambata yana mai kallonta idanunsa cike da ruwan hawaye.

"Hajiya kinga abun alkairi daga Alhaji?"

Murmushi da kuka take duka a lokaci ɗaya wanda tana yi tana kallon su ɗaya bayan ɗaya tana jinjina kanta ta ce.

"Alhamdulillah! Allah shi ne abin godiyarmu Mukarram. Alhaji muna godiya, ubangiji mai Rahma ya ci gaba da tsareka cikin amincinsa ya ƙara maka lafiya da yalwar arziki. Yanda ka ke ta fafutuka wurin inganta rayuwar yaran nan kai ma Allah ya biya ya baka aljanna maɗaukakiya, Allah basu ikon ci gaba da yi maka biyayya yasa su kasance masu yi maka addu'a ko bayan ranka yasa kuma su amfaneka har lahira. "

Cikin jin farin ciki a ransa ya ce.

" Amin Hajiya, na gode da wannan kyakkyawar addu'ar, ina roƙon ubangiji ya ɗaure mu a haka har cikin aljanna."

"Ameeenn"

Duk suka amsa sannan Alhaji Ridwan ya yi musu jagora aka buɗe gate ɗin suka shiga da ƙafar su. Asibiti ce aka gina masa ta musamman wacce ta ji gyara tamkar a ƙasar waje, komai an yi masa bisa tsari da burgewa. Ba Mukarram ɗin ba, hatta Aysha cike take da farin ciki musamman da taga sunan asibitin ya Kasance AL-MUFIDAH SPECIALIST HOSPITAL. Gabaɗayansu sun cika da murna da farin ciki. Suna nan suka ga wasu motoci sun shigo sai ga wasu mutane sun fito ɗauke da kayayyaki har da abinci, nan take aka shirya ƙwarya-ƙwaryar Walima wasu wasu ɗin su inda kowa ya tashi ya tofa albarkacin bakinsa sannan aka ci aka sha, baƙi daga ciki suka watse wasu kuma suka koma gefe suna taɓa fira. Gefe ɗaya Mubarak ya koma tare da Anaam inda suka kira Na'ima vedio call suna tsokanar ta wanda daga ƙarshe har da guntun hawayenta na jin haushin an yi ba da ita ba.

Rabi'a itama tana gefe ita da su Aunty Amina da Ammie suna ta ƙara yaba kyawun asibitin suna farin ciki.

Mukarram, Muhammad da kuma Nameer a tare suka shiga kewayawa suna kallon ɗakunan wanda Muhammad shi ne ke gaba yana musu bayanin komai. Bayan sun shigo office ɗinsa ne murmushin sa ya ƙara Faɗaɗa ya kalli Yayan nasa ya ce.

"Wallahy Kateh ni na ma rasa bakin magana. Allah ya saka muku da alheri..."

Jinjina kai Nameer ya yi ya ce.

"And that's how life is. Sai ka rasa wani abun sannan kake samun wani abun, musamman idan ka yi haƙuri da jarabawarka ka godewa Allah Wallahy sai ka ga Allah ya yi maka fatahin da yafi wanda kake da shi a baya."

"Na yarda da wannan maganar Nameer, ga shi komai ya wuce farin ciki ya samu fiye da na baya, because now I'm with my parent and na samu abin da yafi wanda nake da shi a baya."

Murmushi Muhammad ya yi ya ce.

"I pray that one day one time Itama Anaam rayuwarta ta canja sosai ta manta da duk wani ƙuncin da ta taɓa shiga a baya..."

Jinjina kai Nameer ya yi ya ce.

"Akwai wanda ya fito yana son auren ta and In sha Allah bana tunanin matsala har abada."

Ido suka zubo dukkan su suna kallon shi da alamar neman ƙarin bayani daga cikin zancen da yake musu.

"Shi ɗin ɗan Uwan Dinaratu ne, tun ranar da tayi fushin nan ta zo gidana tun a ranar ya ganta, and he keep asking about her all the time,sai gashi kuma jiya ya zo min da zancen yana son aurenta and idan an amince masa zai turo da wakilansa."

Jinjina kai Mukarram ya yi yana kallon sa ya ce.

" Miye aikinsa? A ina yake da iyayen sa?"

With confidence ya ce.

" Kamfanin motoci yake da a Lagos, amma dai iyayensa da shi ɗin asalin en Zaria ne... "

" Ya yanayin sa yake? I mean....yanayin tarbiyarsa da kuma mu'amalarsa da mutane?"

Cewar Muhammad yana mai samun kujera daga cikin haɗaɗɗun kujerun office ɗin ya zauna.

Har yanzu da ƙwarin gwiwa a kalamansa ya ci gaba da cewa.

" He's nice. Mutumin kirki ne kuma ya taso gidan tarbiyya wanda har yanzu ban san shi da wasu ɗabi'u na ashsha ba."

"Nameer...you know who Anaam is, and you also know how she suffers..."

"Mukarram, har abada ba zamu katange Maryam daga yin rayuwar aure ba. Haƙiƙa ta haɗu da jarrabawa, amma kuma in sha Allahu rayuwar auren da za ta yi itama wannan zai zamto tarihi na har abada a cikin duniyarta. Maheer zai riƙe ta amana domin bani haufi a kansa. Na sani har abada ba zai barta tayi kuka ba. And ko yanzu a shirye yake idan har ku kun shirya, yana da gidanda zai ajiye ta a nan domin ta samu damar zuwa lectures ɗinta ba tare da wata matsala ba."

Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na tsawon lokaci wanda sai da Nameer ya sake buɗe bakinsa ya ce.

"Don sauban ya fasa Aurenta bisa dalilin mahaifiyarsa ba shi zai sa ace kowace Uwar haka take ba. Wasu lokutan mukan ji rashin gamsuwa a duk lokacin da wani sabon al'amarin zai shigo a cikin rayuwarmu, amma kuma idan muka karɓe shi hannu biyu with clean heart muka saka Allah a ciki, sai kuga komai ya tafi normal."

A hankali Muhammad ya sauke ajiyan zuciya yana mai jinjina kansa ya ce.

" Shike nan Nameer. And Alhamdulillah tun da kace ma ɗan uwan Dinaratu ne. In sha Allah ba wata damuwa, idan muka yi magana da Alhaji, idan har kuma ya amince sai ya turo da iyayen nasa..."

Girgiza kai Mukarram ya yi ya ce.

"Ko Alhajin da Hajiya sun amince, sai idan itama ta amince sannan za'a yi."

"Mukarram daman ai babu wanda zai yi mata dole. Idan ta amince ta ji tana da ra'ayi da shi za'a yi, idan kuma tace ba ta yi babu dole."

"To Allah dai ya zaɓa mata mafi alheri amin."

Ƙara tattaunawa suka ci gaba da yi sannan daga ƙarshe suka fito inda Alhaji Ridwan ya damƙawa Mukarram takardu da komai da akayi domin asibitin da sunan sa sannan kusan magrib suka tattara kowa ya kama gaban sa.

Sai da aka mayar da sati biyu cif sannan Muhammad ya nemi Nameer da maganar cewa sun amince. Daman da suka je wa Alhaji Mas'ood da zancen shi kuma sai ya dangana su da Alhaji Salisu wanda shima ya dangana su da Alhaji Ridwan wanda yanzu amintar su da amanar da ke tsakaninsu shi da Alhaji Mas'ood ɗin ta dawo tamkar en uwantaka. Alhaji Gimba ne daman a tsakaninsu wanda yanzu da babu shi komai yafi tafiya daidai domin daman can shi ne mai matsala kuma a kullum sai ya nemi duk yanda zai yi ya ƙirƙiro matsala don kawai rashin son zaman lafiya da neman ganin laifin juna.

Bincike sosai ya ce musu ya yi dangane da ahlin Maheer ɗin kuma ya same su mutanen kirki a can Zaria wanda kowa ke yaba kyawun mu'amalarsu. Hakan shi ne yasa suka amince musamman da akace suna da alaƙa da Dinaratu.

Farin cikin da Dina ta shiga a lokacin da labarin ya risketa ba ya ma misaltuwa. Hakan yasa ko bacci bata samu daman yi ba sai da ta kira shi ta na mishi albishir.

Shi kuwa gama wayarshi da Maaminsa kenan ta kira shi tana mishi bayani cikin farin ciki da nuna jin dadinta.

Bayan ya katse kiran ne ya koma kan kujera ya yi resting bayan sa sosai tamkar wani marar lafiya. The more yake jin wannan maganar the more yake ƙara fuskantar barazana da rashin sukuni can a ƙasan zuciyar sa. Girman haƙƙin yarinyar nan shi ne abin da yake ɗawainiya da shi, nauyin abin yake ji a Ƙirjinsa domin ya sani shi ne silar baƙin cikin ta. Akwai kunya sosai domin ya gwada yafi sau dubu ko zai iya magantuwa wurin ganin ya roƙi gafarar ta amma kuma har abada yasan ko wuƙa za'a daɓa masa ba zai iya ba. But idan ta kasance matarsa wannan yana da tabbas ɗin cewa he can do it. Allah baya taɓa yafe laifin wani akan wani, matuƙar ba ta yafe masa bai san inda rayuwa za ta kai shi ba.

Zina bala'i ce, Zina masifa ce wacce ta kasance babbar alfasha. Manzon Allah (S.A.W) yace babu wanda zai kusanci zina, face an cire an tunɓuke masa rigar imanin sa. Allah da kansa ya ce kada ku kusanci Zina domin ta kasance alfasha.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! A duk lokacin da ya tuna da wannan hankalin sa ba ƙaramin tashi yake ba. Bai yi niyya ba, bai san ma ya aikata ba, sai bayan lokaci mai tsawo sannan abun ya dawo a cikin tunanin sa. Ba ita ba, hatta shi kan shi ya cutu domin he ruined his life ta Yanda ba zai iya goge hakan ba domin ba zai iya dawo da hannun agogo baya ba. Ƙarin tashin hankalinsa shi ne bijire ma umarnin mahaifiyarsa da ya yi. Gashi yanzu wurin neman gyaran gira ya rasa idonsa gabaɗaya. idan ta ji abin da ya aikata bai san a wanne hali za ta kasance ba. And yanzu ma wannan auren da yake da niyyan yi har yanzu ya kasa aminta cewa zai iya yin aure a bayan idon ta. Auren ma da 'ƴar maƙiyinta wanda ya zamo silar rugujewar ahlinsu.

Sai dai kuma, idan ya auna girman baƙin cikin da ya ƙunsawa yarinyar da jinyar da ta shafe tsawon lokaci tana yi, samar mata farin ciki da gina mata sabon tubali shi ne gaba akan komai.

Haka yasa ko ya ji kamar zai janye sai kuma ya ƙara jin ƙwarin gwiwa, domin shi ne wanda ya ɓata komai saboda haka shi ne zai gyara.

Ya jima a nan inda yake yana ta saƙa abubuwa a ransa, sannan daga ƙarshe ya tashi ya canja zuwa wasu black t-shirt da 3quater jeans ya fita ya je wurin Hamad.

Kitchen ya shiga direct domin da shigowarsa ya ji wani daddaɗan ƙamshi yana yi masa maraba.

Plate ya ɗauka ya zuba white rice ɗinda ya gani da stew wacce ta ji nama ya fito parlour ya ɗauki ruwa a wata ƙaramar freezer dake gefe sannan ya zauna ya fara ci tamkar wanda baya da wata damuwa.

Hamad yana jin motsin sa ya fito domin ya tabbatar shi ne kaɗai wanda zai iya shigo masa a wannan lokacin.

"Maheer ina jin tsoro,and har gobe mamaki nake akan abubuwan da ka aikata dama waɗanda kake shirin aikatawa."

Spoon ɗin hannunsa ya dire yana kallon sa ya ce.

"Ni da na yi kidnapping mutum har kana tantama da mamakin auren da nace zan yi."

Zaunawa ya yi yana facing ɗin shi da kyau ya girgiza kai ya ce.

"I know it cewa ba kai ne wanda ya sace Mukarram ba, amma don Allah aminina ka haƙura da maganar nan, the more yanda kake ƙara kusantar yarinyar nan the more yanda kake ƙara gayyato matsala da kuɗinka. No need ace duk sai ka yi wannan, ubangiji da zuciya yake aiki. it's not your fault, ƙaddara ce wacce idan ta zo babu wanda ya isa ya kauce mata, kaje ka yi ta roƙon gafarar Mahaliccinka ka koma wurin mahaifiyarka Maheer. Kai ne abokina kuma Aminina, duk abin da ya shafeka ni ma ya shafe ni...."

Lumshe idanunsa ya yi a hankali sannan ya buɗe su yana mai jin kalaman abokin nasa har cikin zuciyar sa. Bayan ya kammala ne ya kalle shi calmly ya ce.

" I wish I can do it Hamad. But wallahy tallahy girman abin da na aikata mata ya hana ni sukuni ya hanani zaman lafiya. Hamad idan ban roƙi gafarar ta Rayuwata za ta ɗaiɗaice. Ka yarda auren wannan shi ne maslaha a gare ni and itama...."

"Maheer Maami mai fahimta ce, ko baka bayyana mata wancan ba yanzu ka faɗa mata gaskiya."

Saurin girgiza kansa ya yi ya ce.

"Noo Hamad, i can't. Because ban san ta yanda zan fara mata explaining ba. And again even Abiyh too, ba zai ma saurare ni ba. But in sha Allahu I promise you cewa zan kula and ba zan taɓa bari wani abu marar daɗi ya faru ba."

Shiru Hamad ya yi tare da zuba ido tsawon lokaci yana kallon sa wanda in ban da tunani babu abin da yake.

Ajiyan zuciya Maheer ɗin ya sauke sannan ya ce.

" I know you always think about me negatively, please ko sau ɗaya ne a wannan karon ina so ka yarda dani. I promise you cewa kafin wa'adin da na ɗiba ya cika zan yi ƙoƙari na gyara komai In sha Allah....."

"But Maheer ni fa iyayen Ƙaryar da kace ka ɗauka ne abin ya ƙara rikita ƙwaƙwalwata. How comes za ka ɗauki wasu mutane waɗanda baka sani ba a matsayin waɗanda za su shige maka gaba akan maganar aure? Maheer ka kuwa san girma, darajar da kuma martabar da aure yake da Ita? I don't want any..."

"Hamad I promise you to take care of that kada ka damu. In sha Allah har ayi komai a kambala har ya komai ya ƙare a tsakaninmu babu wani abin da zai faru."

Ya jima ko yanzu tsawon lokaci bai ce komai ba, sai daga baya ya ɗan nisa kaɗan sannan ya miƙe tsaya yana jinjina kansa ya ce.

" Shi ke nan. Allah ubangiji ya yi mana jagora amin. Gobe idan Allah ya kai mu sai ka shirya ka tafi. Dinaratu tace ya kamata kaje ka nemi yardar yarinyar kafin ka tura magabatan naka, and also kuma daga nan iyayenta su ma suna so su ganka, Kaga ya kamata ka...."

"We are going together...yeah! Kai ne wanda zai rakani. Saboda haka ka shirya, but mu bar shi har next tomorrow, because I have something that I need to take care of. And one more thing Shi ne, ka nemi inda za ka sauka ko dai ka zauna a gidan Yayarka ko kuma ka zauna a hotel..."

Cike da zallar mamaki ya ce.

"Shi sabon gidan na ka fa?"

"Wannan ɗin na masu aure ne. Idan kuma auren ne da kai sai ka faɗamin?"

"To kai da kake sauka a ciki auren ne da kai?"

"Amma kuma kaɗan ya rage na zamo. So what about you?"

Miƙewa Hamad ɗin ya yi ya nufi hanyar bedroom yana faɗin.

"Ai kai ma indai ba wani munafurci ka shirya ba a bayan idona to kamar ɗaya muke domin ba zaman auren za ka yi ba sai idan ka je ka yi a gaban Maami tukun."

Murmushi kawai ya yi sannan ya miƙe da bottle water a hannunsa ya wuce ya koma gida.

********

Gidan Alhaji Mas'ood kuwa, tun da suka wayi gari su Nene suka hau haramar shirye-shirye akan tarbon wanda suka sa ran cewa shi ne mijin Anaam ɗin su.

Duk budurin da ake Rabi'a ba ta da labari a kai sai da ta fito taga ana ta shirye-shirye sannan ta hau tambaya aka sanar mata cewa wanda zai auri Anaam ne zai zo gidan. A tsaye take cikin kitchen amma akan tsabar mamaki sai sa ta faɗi zaune.

Waigowa Nene ta yi ta kalle ta tace.

"Subhanallah! Rabi'a lafiyanki kuwa?"

Miƙewa ta yi tana mai jan numfashi sosai tare da ƙoƙarin daidaita kan ta ta wani ƙirƙiro murmushin dole ta ce.

"Ba komai Nene, er zamewa ce na yi. Allah ya kawo shi lafiya."

Anaam da ke ɗaki tun ɗazu tana vedio call da Yayar ta Na'ima ne ta wani girgiza kanta ta ce.

"Yaa Na'ima tun ɗazu muke ta abu ɗaya dake. Wallahy ban san yanda zan misalta miki irin tashin hankalin da nake ciki ba. Yaa Na'ima so kawai ake Namiji ya sake guduna a karo na biyu, wallhy tallahy har cikin raina nake faɗa miki maganar nan ni da za'a bar ni to har abada ba zan yi aure ba. "

" Gudun maganganun mutane kike? Ko kuma kina gudun danginsa su ƙi ki kaman yanda na Sauban su ka yi?"

Wani murmushin gefen baki ta yi tare da girgiza kanta ta ce.

" Ko ɗaya ya Na'ima. Ni wannan a yanzu sam ya daina damuna. Domin ba mutane ke da Rayuwata ba, saboda haka ba su da Ikon saka ni kuka. Is just that na fi so na yi zamana haka... "

" Abin da ba zai faru kenan ba Anaam, because ba wanda zai bar ki a haka domin shirme kike yi. And beside wannan ɗin nan Aunty Dina ta faɗamana cewa shi ɗin yana tsananin son ki and shi ɗin ɗan uwanta ne kuma kin gan shi. So miyasa kike jin tsoron haɗuwa da shi bayan ba wannan ne karo na farko ba?"

Girgiza kanta ta yi da sauri a wannan karon tana mai jin ruwan hawaye ta ce.

" A yau haɗuwar ta bambanta Yaa Na'ima...ƙirjina wata irin dokawa yake, ni ka ɗai na san yanda nake ji..."

"Kin ji hakan a lokacin da aka ce ki je ku gana da Sauban?"

"A'a Yaa Na'ima..."

Dariya ta yi mata sannan ta kashe wayarta tabar nan nan a cikin tsoro da fargaba.

Bata ƙara jin zuciyarta ta tsinke ba sai da ta ji an ce sun shigo suna parlourn baƙin Abbah suna jiran ta. Gabaɗaya sai ta ji ta ruɗe ta gigice domin a yanda taga take-taken ahlin na ta wannan ya tabbatar mata da cewa kowa ya gama goya masa baya musamman da suka san cewa ɗan uwan Aunty Dinaratu ne. A haka Ammie ta samu ita da Aunty Aysha da ta iso gidan yanzu suka lallaɓa ta ta shirya.

Rabi'a kuwa, tun da taji wannan labarin ta kasa zama ta kasa tsaye. Lallai yau wannan ranar ta kasance ranar farin cikin ta domin dole ta rama wulakancin da ta yi mata kuma wannan shi ne time ɗinda ya dace. Tabbas sai ta shayar da Ita baƙin da har abada ba za manta da ita ba.

Hakan yasa ta shirya tana jin ance sun shigo suna parlourn Abba ta lallaɓa ta sace jiki ta shige tsulum sai gata a gaban su.

Tunda ta shigo Maheer ya ɗaga ido ya ga cewar ba Anaam ɗin ba ce bai sake kallon ko inda inuwar ta take ba. Shi ma dai Hamad ɗin har ta dasa Ɗuwawunta ta zauna akan kujera mamakinta yake.

Murmushi ta yi tana mai kallon Hamad da shi ne wanda taga yana kallon ta ce.

"Sannun ku da zuwa..."

"Yauwa Sannu."

Ya amsa ta kai tsaye yana mai ci gaba da kallon ta.

Ɗan ƙara muskutowa ta yi zuwa gaba tana mai ƙara Faɗaɗa murmushinta ta ce.

"Ahm...uhmm! Daman ni sistern Maryam ce. Ni ma a nan gidan nake kuma a nan nake zaune, a nan kuma nake karatu. Ahmm daman cewa na yi bara na zo na mu gaisa da saurayin namu ko kuma ince angon namu..."

Jinjina kai Hamad ya yi ya ce.

"Thank you. And wannan ɗin shi ne.."

Ya ƙarashe maganar yana mai nuna mata inda Maheer yake zaune.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull