Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 30
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 30: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 30. Wani irin abu ne wanda ba za ta iya cewa ga ko miye ba taji ya…
3,375 words
Wani irin abu ne wanda ba za ta iya cewa ga ko miye ba taji ya wuce mata har can ƙasan zuciyarta ganin. Bakin ta har yana rawa wurin furta.
"Wan...wannan ɗin?"
Sai yanzu ya ɗago ya kalle ta jin irin reaction ɗin ta.
Ita kuma yi tayi tamkar ta gigice ganin wanda aka ce shi ne zai auri Anaam, wannan ɗin ai ba ma bahaushe ba ne. Kyaunsa da haibarsa ba ƙaramin hautsina mata kwanya ya yi ba.
Ta ya ya ma za'a ce wannan shi ne zai aure ta? Ta ina suka bi suka da ce? Ta ya za'a Haɗa wannan kyakkyawan da waccan mummunar ma?
Cike da jin haushin yanda ta yi reacting tamkar wata mahaukaciya yasa Hamad ya buga tsaki ya ce.
"Mts! Malama lafiya? What's all this nonsense?"
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*BOOK ONE* *PAGE 38*
Da sauri ta girgiza kanta tana mai ƙoƙarin dawo da nutsuwarta, sai dai hakan ya gagara. Zuciyarta sai dokawa take tamkar ana mata luguɗe. Da ƙyar ta samu wani irin wahalallen yawu ya wuce mata a throat ɗinta murya na cracking ta ce.
"Ah..ahm...babu komai."
Ko kalma ɗaya har yanzu ba ta ji ta fito daga bakin Maheer ɗin ba. Kallon ta kawai yake yi da idanuwan nan nasa masu sanyi amma cike da da wani irin iko da izza da su ka sa Rabi'a jin tamkar ƙafafuwanta da sauran gaɓɓan jikin ta ba ba za su iya ci gaba da ɗaukar ta ba kuma tsabar yanda ta ji sun yi mata sanyi.
A can cikin zuciyarta kuwa, wani irin kishi ne mai zafi ya taso mata, sam ba ta taɓa tsammanin cewa mutum irin wannan zai iya son Maryam ba a rayuwa. An ya kuwa yasan abin da ya taɓa faruwa da ita a baya? Ita ɗin nan fa ba cikakkiyar budurwa ba ce kamar ita. Ita ɗin sauran maza ce wacce darajarta da girman ta su ka zube.
Kawar da idon sa ya yi gefe a karo na biyu zuciyarsa fal mamakin ita kuma wannan wace ce.
Cike da jin ganin ta ma da suke ya ginshe su yasa Hamad ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce.
"Where is Maryam?"
Wani murmushin yaƙe ta yi tare da jinjina kanta ta ce.
"She's coming...yeah...she's coming now..."
"And da ace kuma Ita ce a nan a madadinki....tabbas da sai ya fi amfani."
Jin saukar kalaman na sa ta yi tamkar an caka mata wuƙa a dodon kunnenta tare da jin wata irin kunya da ta yi mata dabaibayi.
Alamar motsin Anaam ɗin ta jiyo wanda shi ne abinda ya sake haddasa mata wata irin mummunan faɗuwan gaba wanda ita kan ta bata san dalili ba.
Cike da nutsuwa ta yi sallama ta shigo parlourn wanda da za ka tsaya ka yi mata kallon ƙwaf za ka fahimce cewa tamkar a rikice take. Ji take tamkar ƙafafunta za su harɗe ta ta faɗi ƙasa tsabar yanda take ji.
Tun da Maheer ya ɗago ido ya Kalle ta sai ya ji zuciyarsa ta tsaya cak! Ƙyar idanunsa suka tsaya a kan ta yana mai yi mata kallo wanda shi kansa bai san dalili ba.
Idanunta na sarƙewa da na Maheer ɗin ta ji wani sabun abu ya ratsa ta, hakan yasa ba shiri ta kawar da Idonta wanda a nan ne kuma ta ga Rabi'a zaune dan gal-gal tamkar wacce ke da ticket ɗin gayyata.
Take ta ji wani irin tsoro ya kama mata zuciya, zaman da tayi niyyar yi sai ta ji ya gagareta. Tambayar farko da ta fara yiwa kanta ita ce miye Rabi'a take yi a nan ɗin? Shin ta zo ne domin ta fallasa musu sirrinta ko kuma wata ƙil ma har ta gama fallasawa ɗin. An ya Rabi'a tana da kunya da mutunci a rayuwar nan? To ai da ta kwantar da Hankalinta domin ita da kanta ta yi niyyar faɗa nasa naƙatsunta ba sai ta wahalar da kanta ba. Tabbas dole ta sanar da duk wanda ya zo neman aurenta wannan sirrin domin a zancen aure babu yaudara babu munafurci a ciki. Idan ya ji da shi da iyayen sa za su zauna da ita a haka fine, idan ma sun ji ba za su iya ba babu dole a ciki. Duk jan kunnen da Yaa Muhammad ya yi mata akan kada ta sanar da shi wannan magana sam ba za ta iya ba, domin Ita har ta bari ya ji a bakin duniya to tabbas zai ɗauke ta a mayaudariya kuma ba za ta so hakan ta faru ba....
"Maryam.."
Hamad ya ambaci sunanta yana mai katse shirun da ya ratsa tsakanin su.
Kallonsa ta yi a natse wanda duk iya ƙoƙari ta yi but kalmomin da ta yi niyyar furta su domin ta amsa kiran sunanta da ya yi ta kasa.
Ganin kamar ba ta ma hayyacinta yasa Maheer ya taso kai tsaye ya ɗan tsaya a gefen ta cikin muryar nan tasa yacce ya kasa ɓacewa a tunanin ta tun wayar da suka taɓa yi a gidan Aunty Dinaratu ya ce.
"Hey! Are you okay?"
Rabi'a kam lokaci ɗaya ta ji zuciyarta ta karye ta gama nutsewa a kogin asara daga irin yanayin kallon da taga Maheer na yi wa Anaam ɗin Wanda babu komai a cikin sa sai zallar kulawa da nuna soyayya. Ita kanta ta san cewa Tabbas Anaam ba kyakkyawa ba ce, ba mai dogon gashi ba ce sannan Ita ɗin ba fara ba ce,sai dai tana da wani abu da Ita Kanta ta san cewa ba ta irin shi, wato nutsuwa da kamala uwa uba tarbiyya da rashin son hayaniya. Kuɗi ko kuma gata musamman da ta kasance 'ƴar Auta hakan bai sa ta ɗauki wasu gurɓatattun ɗabi'u ba. And da hakan a wasu lokutan sai ta riƙa jin cewa kaman ba za ta taɓa iya kamo ta ba har abada.
"Maryam..."
Ji ta yi ta kasa motsi, gabaɗaya sai ta ji wani abu na circulating tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin ƙafanta.
Ƙara matsawa ya yi saitin kunnen ta wanda daga shi sai ita ne kaɗai ke iya jin maganar sa ya ce.
"Mu yi magana a tsayen ya yi miki?"
Runtse idanun ta ta yi gam tana mai girgiza kai a hankali alamar a'a sannan ta matsa inda yafi mata kusa da cushion ta samu wuri ta zauna a ɗosane tamkar ace ƙyat ta zuba da gudu.
Wata cushion ɗinda ke dab da ita ya samu ya zauna ba tare da ya koma inda ya fara zama ba a farko.
"Ko zamu iya yin aure? I mean za ki Aure ni?"
Hannu bibbiyu Rabi'a ta saka ta dafe bakinta tsabar ruɗewa wanda saura kiris ta saki ihu tsabar mamaki.
Anaam itama da sauri ta ɗago ta kalle shi jin wata magana mai kama da karan tsaye.
Cike da jin haushi Hamad ya yi saurin girgiza kansa yana mai kallon Anaam ɗin ya ce.
"Kina ji Maryam....kin san ita rayuwa kowa da abinda yake ra'ayi kuma yake jin ya masa har zai ji cewa yana son wannan abun kuma yana da muradin kasancewa tare da shi. To hakan ne tsakanin ki da abokina, ya ganki a gidan Dinaratu, kuma tun daga lokacin ya ji babu wata wacce yake so da ƙauna sama da ke..."
Girgiza kan ta tayi murya a ƙasa sosai ta ce.
" Ban can can ta ba. Ni ban dace da shi ba...Rayuwa ta da tashi sun yi hannun riga. Ni ɗin ba Mace ba ce kamar kowa.. "
" Subhanallah! Maryam wannan wace irin magana ce? Miyasa za ki ce haka?"
Girgiza kanta ta yi tana mai jin hawaye ta ce.
"Bamu da ce ba. Miyasa dole sai ni? Ga en mata a ko'ina..."
"Shi bai gansu ba, ke ya gani kuma yake son ya aura. Mu ko a yau kika ce kin amince a shirye muke Maryam."
"Amma..."
"Shihhh!"
Maheer ɗin ya ambata yana mai jin wani irin ƙuna da zafi a can ƙasan ransa. Ba muryarsa ba, hatta launin idanunsa sai da suka sauya tsabar yanda ya ji wani irin nauyi da kunya ya kama sa. He's at fault of every single pain da take going through. Duk ƙuncinta da damuwarta shi ne sila.
Ɗagowa ta yi ta kalle shi da Idanuwan nan da suka gama jiƙewa da ruwan hawaye jin yanda ya dakatar da Ita daga ƙarasa sauran Magananta.
Gyaɗa mata kansa ya yi tare da lumshe mata idanunsa waɗanda suka gama aika mata da saƙonnin marar adadi.
Laƙwas! Haka ta ji duk wata lakka dake jikinta ta saki domin ba ƙaramin kashe mata jiki ya yi ba.
"I promise to stand and be with you har sai lokacin da ki ka ji cewar duniyar ta yi miki daidai. Idan har na bari wannan hawayen damuwa ya ci gaba da kwaranya daga fararen idanun nan naki to ni ɗin nan ba Maheer ba ne. Ki yarda dani, na yi miki alƙawarin tsayuwa tare dake a kowane irin yanayi.... "
Tamkar a mafarki ta ji ya kamo hannunta na dama yana Ƙoƙarin saƙalawa a nashi.
A gigice ta ƙwace hannun sannan ta matsa ɗan baya kaɗan tana mai kallon Rabi'a wacce daman tun ɗazu idanun ta ke kansu ƙyar ko ƙyaftawa babu.
Shi kuwa, girgiza kansa ya yi da sauri ya ce.
"Please I'm sorry..."
Miƙewa suka ga Hamad ya yi kai tsaye ya nufi hanyar fita waje yana faɗin.
"I will wait outside..."
Ganin hakan yasa itama Rabi'a ta miƙe jiki a saɓule ta kama hanya tamkar za ta kifa tsabar baƙin ciki ta fice. Wato shi bai ma damu da duk su ɗin da suke wurin ba. Soyayyar sa yake bugawa hankali kwance ko kunya. Daman irin mutanen nan ba kunya ce da su ba. Tsab ma zai rungume ta tunda ba Allah ne a zuciyar su ba. Yanzun ma da aka baro su wayasan abin da zai iya yi mata. Ita kuma er daɗi soyayya sai wani narke masa take tana wani kukan gulma wai Ita taga mijin aure. Kuma duk a gama ta wannan ɗin ba zai aure ta ba, ko ta ina basu haɗa hanya ba, wata ƙil ma jikinta kawai yake so kuma daga zaran ya samu zai ƙara gaba.
Da wannan tunanin ta shige sashen Hajiya Nasmah inda ta tarar da ita ta kambala sallahr Zuhr tana batun fitowa.
"Ammie..."
"Na'am Rabi'a...."
Kallon ta ta yi da kyau cikin rashin fahimta ta ce.
"Lafiya naga kamar kin ruɗe?"
Girgiza kai ta yi ta ce.
"Ammie ba dole in ruɗe ba. Shegen mutumin can yana zuwa kawai ya kama hannun Anaam ya riƙe har yana neman ya rungumeta, don Allah yasa ma ina zaune a wurin da ba'a son iya abinda zai...."
Hannu Ammie ta saka hankali tashe ta dafe ƙirjinta a gigice ta ce.
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku ni Nasmah! Mi kika ce Rabi'a? Shi baƙon daman ɗan iska ne... "
"Wallahy Ammie ba ki ji irin kalaman da ya shiga furta mata ba, kuma daga ji kin san na yaudara ne domin ban taɓa jin irin su ba, kuma duk saurayin kirki Ammie wallahy ba zai furta su ga...."
Muƙut! Haka ta yi saurin haɗiye wani yawu tare da fara zare ido ganin Mubarak da Aunty Amina sun yi sallama sun shigo.
Kallon su Ammie ta yi cikin tashin hankali ta ce.
" Yauwa Mubarak! Gwanda da Allah yasa ka zo da wuri. Ashe yaron nan da ya zo ɗan uwan Dinaratu ɗan iska ne bamu sani ba...."
"Uhmm..Ammie ina nufin kamar yana so ya yi mata wata maganar rashin ɗa'a ne amma bai kai ga yi ba tukun."
Daga Mubarak har Yaa Amina tsayawa suka suna kallonta wanda tsab sun gama fahimtar ta.
Kafaɗun Mahaifiyar tasa ya kama yace.
"Ammie please listen to me...Aunty Dinaratu da Yaa Nameer har abada ba za su taɓa kawo wa Anaam mutumin banza ba. Ki fara sanin gaskiyar zance kafin ki ce za ki yanke hukunci."
"Mubarak Amma ka ji...."
"Ammie Yaa Muhammad ya ce Aunty Amina ta zo domin a shirya tarbon baƙin gobe. Just Ki bar min wannan maganar a hannuna, zan bincika yanzun nan in ji, idan har wannan maganar ta zamto gaskiya tabbas za'a ɗauki mummunan mataki, idan kuma ta kasance Ƙarya da ƙazafi tabbas ita munafukar nan sai ta ci gidansu...."
A hankali ta lallaɓa ta tsere daga ɗakin domin ba ta sa ran abin ya tsaya a haka ba. Ta so Ammie ta sa a ci masa mutunci a kore sa kowa ma ya rasa. Amma wallahy tallahy ba za ta haƙura ba. Dole sai ta rama wulakancin da ta yi mata a baya.
Shi kuwa Mubarak bayan ta fice ya kalli Ammien ya ce.
"Ammie miyasa za ki riƙa biye zancen makira Rabi'a? Kin manta ko waye ita?"
Girgixa kai tayi tana kai sauke ajiyar Zuciya ta ce.
"Wallahy Mubarak har hankalina ya ɗaga sosai. Kwata-kwata na manta."
Yaa Amina dake shimfiɗe Little maryam ne ta ɗago kai ta ce.
"Ammie cikin sati biyu zuwa uku fa suke son auren nan ya faru."
Waro ido Ammie ta yi ta ce.
"Da gaske Amina?"
"ni ma dai haka na ji a wurin Dinaratu ɗazu da ta kirani muna magana a Waya."
*******
Daga wannan maganar babu wanda ya sake magana a cikin su tsawon lokaci wanda kowa a cikin su ya yi nisa sosai ya nutsa a duniyar tunani.
Shi dai kamar koyaushe, maganarsa ba ta cika yawa ba. Yanzu iya abunda ya zo ya faɗa mata kenan? Idan har shi ba shi da magana to Ita tana da ita.
There is more da take so ta faɗa masa dangane da rayuwarta. Ba ta so ya ji wannan maganar a shanun talla. Ita ce wacce take so ta sanar masa. Ko kuma ta ce Aunty Dinaratu ta faɗa masa....
"I will take my leave. Thank you so much for your time."
Yana gama faɗar haka ya miƙe ya fara tafiya. Abinci ta shiga bai wa Idonta domin wannan ne karon farko da ta samu damar ƙare masa kallo yanda Ran ta ya so.
Dogon gaske ne,Mai haiba da cikar kamala, maganar sa sam babu hatsaniya.
Har yanxu kalamansa basu daina dukan ƙwaƙwalwarta ba. So take ta dawo da su baya ɗaya bayan ɗaya ta yi musu fashin baƙi. Domin ta tantance ta kuma fahimci ma'anar kalamansa. Duk wannan da zai ji labarin mummunar ƙaddarar ta tabbas da ya janye kalamansa domin zai ji cewa su ɗin basu da ce ba.
Ta jima Ita ɗaya, sannan daga ƙarshe ta miƙe ta kalli gefen inda aka ajiye musu abinci da kayan ci da sha, but a yanda ta ga komai a tsare hakan shi ya tabbatar mata da cewa ba su Taɓa komai ba.
Shigewa ta yi zuwa cikin gida inda ta tarar da su Mukarram a zaune suna magana a parlourn Ammie.
Kallon ta mubarak ya yi yana dariya ya ce.
"Amarya..."
Ɓata fuska ta yi tare da wucewa kawai ba ta ce komai ba ta fice ta wuce ɗakin ta.
Har ɗakin su Yaa Amina suka bi ta Ita da Aunty Aysha suna ta ƙara Lallaɓata tare da kwantar mata da hankali akan cewa in sha Allahu ta dace da miji.
Duk saurin Alhaji Mas'ood koda ya iso gidan har Maheer ya yi tafiyarsa wanda ya so su gaisa da shi amma kuma wai har ya tafi da sunan ana jiran shi bayan ya amsa kira daga wurin aikinsa.
Wasa-wasa Abubuwa sai ga shi sun kan kama, wanda tuni Maheer har ya turo iyayen ƙaryar da ya shirya da sunan su ne dangin mahaifinsa dake nan wanda duk wannan gadar zare ce kawai ya shirya domin babu wasu dangin mahaifinsa da suka san da zaman sa a nigeria ɗin, kuma baya Fata ace sun san ya zo nan ɗin. Musamman Alhaji Armaya'u da ke da tsananin fushi da zafin zuciya, wanda idan har ya ji cewa Maheer ɗin yana ƙasar Nigeria kuma yana amfani da sunan su wurin neman aure tabbas zai Iya ɗaukar bindiga kai tsaye ya harbe sa ba tare da ya Tsaya wani tunani ba. Shiyasa duk abinda yake kullum a cikin taka tsan-tsan yake domin yana tsoro kada Allura ta tono garma. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*BOOK ONE* *PAGE 39*
Sai dai duk wannan taka-tsantsan ɗin da yake zuciyarsa ba ta daina bugawa fiye da ƙima ba. Domin ya san cewa duk abinda yake ginawa a yanzu tamkar yana tafiya ne akan bakin rijiya da baya-baya, ƙaramin kuskure ɗaya kan iya rusa komai da ya jima yana ginawa.
Hakan yasa akoda yaushe yana nan gangar mahaifiyarsa gudun kada ta zarge shi da wani abu,duk rungutsumin nan da ake daga ita har familyn ta ba su san abin da yake shiryawa ba.
******
A ɓangaren Anaam kuwa, Tun daga ranar da suka haɗu rayuwarta ta sauya gabaɗaya. Duk wani motsin ta ya canza, ko magana take da wani za ka fahimci cewa hankalin ta sau tari baya tare da kai yana can nesa a wata duniyar.
Shirye-shiryen ake ta yi amma ita ganin take komai kamar a mafarki. Zuwa biyu ko uku ma za ta ce amma har yau wata doguwar magana ba ta haɗa su ba.
Tana so ta tambaye shi dalilin da yasa har yau ya kasa samun lokacin gaisawa da mahaifinta, abin da yafi tsaya mata a rai shi ne zuwan da ya yi last Abbah yana cikin gidan amma ya kawo uzuri a gaggauce ya yi tafiyarsa yace sai idan ya dawo.
Shi kuwa Abbah har yau bai nuna wata damuwa ba domin Sam bai kawo komai akan kauce masa da Maheer ɗin yake ba.
Dangin ta da abokan arziki kowa ya yi amanna da shi kuma kowa sai yabon kirkinsa yake, hakan yasa a wasu lokutan take jin hankalinta ya kwanta. But idan ta tuna cewa har yau basu magantu akan giɓin da rayuwar ta ta samu ba sai ta ji zuciyarta ta karye. Ko kaɗan ba ta so ta kasance abin zargi ko kuma ta zamo marar daraja a lokacin da take tunanin cewa ita ɗin ta dace.
Yau ma zaune take a tsakiyar gadonta ta naɗiɗiye ƙafafunta tana shan Ice-cream mai san yi sosai. Agogon wayarta ta duba wanda ya nuna mata ƙarfe goma sha ɗaya da minti ashirin na dare cif. Call Log ta shiga ta tsurawa numbern sa ido wanda ita ce wacce ta saka Hamad ya turo mata ita ɗazu da nufin kiransa ta faɗa masa gaskiyar rayuwarta domin ba za ta iya bari akai ga zarga mata igiyar sa guda uku a kanta ba alhali tana da wani sirrin da ya kamata ace ta sanar mai.
Ta jima tana kallon numbern tana mai jin abubuwa da yawa a cikin ranta.
"Should I call him?"
Girgixa kanta ta yi da sauri kamar wacce take magana da wani ta ce.
"A'a..gaskiya Anaam bai da ce ba, allow him to call you first..."
Kallon numbern ta ƙara yi tare da marairaice fuska ta ce.
"But akwai abubuwa da yawa da nake so na gaya maka.."
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tare da lumshe idanunta sannan ta mayar da wayar gefe ta ajiye sai kuma ta ɗauki robar Ice-cream ɗinta ta ci gaba da sha. Sai dai kuma ba ta san cewa shi ma a daidai wannan lokacin ba yana nan a zaune da wayar a hannun sa yana aikin dakon jiran kiranta.
Tunda Hamad ya faɗa masa cewa Anaam ta karbi numbern sa akan tana so ta faɗa masa magana mai muhimmanci tun a lokacin ya zauna yana zaman jiran kiranta. So yake ya ji wace iriyar magana ce, so yake ji miye wannan ɗin mai muhimmancin da take so ta faɗa mai?
Shigowa Station ɗin da Maheer ɗin yake zaune Hamad ya yi yana mai ajiye wata Na'ura a gefe wacce aka sanyata a ƙasan ruwa ya ce.
"wai har yanzu zaman jiran kiran na ta ka ke?"
Ɗagowa ya yi ya kalle sa tare da jinjina masa kansa ya ce.