Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 31

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 31

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 31: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 31. "She didn't call..."

3,375 words

"She didn't call..."

Dariya Hamad ya yi wacce babu komai a cikin ta sai zallar izgili da tsokana ya ce.

"To kai kira ta mana.."

Girgiza kai ya yi da sauri ya ce.

"No...I don't want to pressure her.."

"You cared?"

Sake girgiza kan sa ya yi ya ce.

"I don't. Kawai dai na damu ne akan maganar da take so ta faɗamin..."

"Maheerrr..."

Hamad ya ambata yana mai samun kujera a kusa da shi ya zauna.

Shiru kawai ya yi tare da zuba masa ido bai ce masa komai ba.

"Maheer har yanzu a wani gefen na zuciyata bana goyon bayan wannan abun. Iyayenta, dangin ta da kuma friends ɗin ta duk sun yarda da kai, amma kai kuma babu komai a tare da kai sai neman fansa..."

"Hamad mu bar wannan zancen a yanzu please.."

Yana gama faɗar haka ya tashi ya wuce ya bar Hamad nan.

ANaam kuwa, tana nan zaune sai ga kiran Ƙawarta Na'ima Hassan ya shigo.

Saurin ɗagawa ta yi tare da faɗin.

"Kai...wallahy ni har kin ban tsoro..."

Dariya Na'imar ta yi daga can ɓangarenta ta ce.

"Are you expecting someone?"

"Noo...kawai dai ina enjoying kai na ke kuma kina nema ki takura ni..."

"Gaskiya ne Amarya...Ya ya kike?"

"Fine....and you?"

"Alhamdulillah."

Shiru ta yi tana tunani wanda har sai da Na'imar ta ce.

"Hello Friendy..."

"Na'ima za ki zo gobe?"

"Yeah.. In sha Allah zan zo...da wuri ma zan zo tare da Mum."

"Thank you. Allah ya kai mu."

"Amin. Akwai wata damuwa ne?"

Girgiza kai ta yi ta ce.

"No...not all. Kawai dai ina so ki zo."

"Alright...Mudan ya kawo ɗinkun nan kuwa?"

"A'a, na ji suna waya da Yaa Na'ima ya ce wai sai gobe da yamma zai zo."

Allah ya kai mu gobe lafiya."

"Amin. Bye."

******

A ɓangaren Rabi'a kuwa, Ta kasa samun nutsuwa tun bayan abin da ya faru. Duk lokacin da ta tuna irin kallon da ya yi wa Anaam da yadda ya riƙe hannunta sai ta ji zuciyarta ta ƙara ƙonewa.

Ƙarin baƙin cikin ta shi ne kaf gidan babu wanda ya koma kanta, da ita da babu duk ɗaya wanda hakan ba ƙaramin zafi yake mata ba. Babu abinda suke yi su kirata su ce ta zo ta ji. Amma a lokacin da Yaa Na'ima na gidan komai da ita ake yi tamkar 'ƴar gida, yanzun ma da ba ta gidan komai za su iya musamman Anaam sai ta kira ta ta sanar mata. Haka su ka yi ta uzzurawa sai da Haisam ya kawo ta satin nan amma ita kuma sun mayar da ita saniyar ware tamkar ba er uwar su ba.

Ta kokawa Umma wannan matsalar yafi a ƙirga amma sai dai ta ce mata ta yi hak'uri ta jira ta kafin ta zo, to yanzu ma Baba Salisu a yanda suka ga take-takensa so yake ya hana Umma zuwa kuma wallahy ko yaƙi ko yaso dole sai ta zo don wata ƙil ma Maheer ɗin rabon Rabi'ar ne ba su sani ba.

Saboda haka dole ta zo domin ayi komai a gabansu. Kuma ita ɗin ko sun ƙi ko sun so ita ɗin dai jinin su ce kuma ba za su taɓa iya canja hakan ba.

*******

Washegari koda 12pm ta buga na rana yana tsaye a bakin motar sa a harabar gidansu Anaam ɗin. Idan ya ce ya samu ishashshen bacci a Daren jiya tabbas ya yi Ƙarya. Tunanin maganar da tace tana so ta faɗa masa mai muhimmanci ta hana shi nutsuwa. Ba zai iya Kiranta a waya ba, sannan ba zai Iya haƙura da maganar ba, hakan yasa ya ture schedules ɗinsa na yau ya ƙumo sakko ya iso garin Abuja.

Wannan maganar ce kaɗai abinda ya kawo shi, saboda haka baya tunanin cewa yana da buƙatar shiga cikin wannan gidan na su a yau.

Yana tsaye yana tunanin yanda za'a yi a kira masa Ita tsulum sai ga Rabi'a tamkar an jefo ta.

Sanye yake cikin milk shadda wacce ta zauna daidai da jikinsa sannan ga hula Zanna bukar a kansa wacce ta ƙara masa kyau da haiba, uwa uba Shade ɗinda ke idonsa sai ta ji ya ƙara tafiya da zuciyarta. A duk lokacin da ta ganshi ji take yana ƙara matsayi a cikin zuciyar ta, Faris ma yanzu kwata-kwata ta daina yinsa ta kuma daina jin sa a cikin ran ta.

Kallon ta yake tunda ta zo ta tsaya ba tare da ya ce mata komai ba.

Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce.

"Wallahy tallahy Ina son ka...ina masifar mahaukacin son ka. Ban da ganin namiji mai kyau irin naka ba ni dai a iya tsawon rayuwata."

Tana kai wa nan ta yi shiru tare da ɗan sunkuyarda kanta na tsawon lokaci tana mai jiran reply ɗin sa. Sai dai kuma ta san shi a fuska ne amma ba ta san shi a hali ba,domin komai bai ce mata ba, bai kuma ga zai iya ce mata komai ba domin ya ɗauka ba ta da hankali,shin tun a first day ɗinsa a gidan ya ɗauka cewa she has mental problems.

Ajiyan Zuciya ta sauke tare da lumshe idanunta ta buɗe tana mai yin wani kalar murmushi ta ce.

"Ni kowane irin hali ne ke gareka tabbas ya mini. Komai ka yi burgeni yake, ni da Anaam duk ɗaya ne a gidan nan, amma kuma a fuskar cikar kamala da zamowa cikakkiyar mace mu ɗin ba ɗaya ba ne. Shin ko kana da labarin cewa an taɓa raping ɗin ta?"

A razane ya ɗago idonsa ya kalle ta wanda in banda baƙin glass ɗinda ke idonsa ya yi musu shamaki tabbas da babu abinda zai hana ta ganin tsoratar da ya yi.

Taɓe baki ta yi ta ce.

" Uhm! Wai kai da ka ɗauka ita ɗin wata cikakkiyar mace ce? To Ita ɗin sauran ɓarayi ce, ƙarti goma sha biyar ne suka haɗu suka yi raping ɗin ta wanda sai da ta kwanta doguwar jinya tamkar ba za ta rayu ba. Hatta Ƙwaƙwalwarta sai da ta kusa ta taɓu akan depression ɗinda ya so ka ma ta ko ince ya ka ma ta. Ita da take mummuna mi za ka yi da ita mace babu fasali babu ma'ana? Babu komai a jikinta da ya rage sai fanko haka kuma ita ɗin ba kyau ne da ita ba ballantana ka ce domin shi za ka iya Hakura ka aure ta...."

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 40*

Maganar ce ta tsaya mata cak a maƙoshinta lokacin da ta lura da yanayinsa tamkar wanda aka kafa a ƙasa.

Wani irin yanayi ne ya mamaye fuskarsa, duk da cewa black shade ɗinda ke idonsa ya rufe kaso da yawa na daga cikin idanunsa wanda ba lallai ta iya fahimtar yanayin nasa ba. Daga yanayin tsayuwarda ya yi da kuma yanda yake kallonta shi ya sa ta ɗan fahimci cewar kamar kalaman na ta sun yi matuƙar girgiza shi ƙwarai.

Hannu taga ya sa ya cire glass ɗin a hankali. wani irin abu ne ta ji ya sauko mata a zuciya ganin yanda idanunsa suka canja a sarari.

Tabbas waɗan nan idanuwan sun sauya sosai, ba sanyi ba ne a cikinsu kamar yanda ta saba ganin shi, ƙuna ce a cikinsu mai haɗe da fushi da tsananin takaici.

Kallonta yake kamar yanda take kallon sa murya a ƙasa sosai ya ce.

"Who told you that?"

Duk da cewa a tsorace take, a hakan ta ƙoƙarta ta buɗe bakinta ta ce.

"Ai wannan ba ɓoyayyen abu bane. Ko wayarka ka ɗauka ka yi searching za ka ga hoton ta ya fito da labarin abin da ya faru da ita a baya. Duk gidan nan har Dinaratun da ta kawo ka duk sun san da wannan, but sai su ka ɓoye maka because suna so su yaudare ka."

Wurin wani irin shiru ya ɗauka wanda ba komai sai iskar da ke kaɗawa a hankali wacce a maimakon ya ji san yi, wani irin zafi ne ya ji yana tsatstsafo masa ta ko'ina.

Babu abinda zuciyarsa ke yi face tsananin bugawa ya yin da kalaman Rabi'ar ke daɗa maimatuwa a cikin kansa. "Karti goma sha biyar? Cutar depression?"

Matsowa ta ƙara yi a kusa da shi kaɗan ta ce.

"Da hakan idan ka yi nazari ita ɗin Sam ba ta dace da kai ba....ni ce na cancanta, da ni da ita duk ɗaya ne a wurin Abbah, idan har kace musu ni kake so babu wanda ya isa yace zai hana. Mahaifina bai yi kuɗin mahaifinta ba, amma dai dukiyar mahaifinta tamkar tamu ce, ni ɗin na haɗa dangi da Fulani domin mahaifiyata bafulatana ce, hakan yasa kaganni kyakkyawar gaske wacce kyawuna ya yi daidai da fasalinka, zamu haifi yara kyawawa... "

" Enough please... "

Ya ambata a ɗan rikice yana mai ɗaga mata hannunsa. Kallonsa take a tsorace har ya gama buɗe Mota ya shige ya fice daga gidan ba tare da ya sake kallonta ba.

Wani irin lallausan murmushi ne mai sanyi ya bayyana akan allon fuskarta ganin alamar cewa ta yi nasara.

"Ko ka yarda ko kar ka yarda, na riga na saka shakku da zargi a cikin zuciyarka...saboda haka ɗaurin auren Jibi in sha Allahu dani za'a ɗaura shi."

Ta juya kenan sai suka haɗa ido da Na'ima da kuma Mummy Jamila ƙanwarsu Alhaji Mas'ood da ta iso jiya tare da wasu en uwan su.

Wani kallon Na'ima ta bi ta da shi tare da faɗin.

" Ke da waye kuke tsaye?"

Waigawa ta yi tana mai kallon bayan ta tamkar ba ta san komai ba sai kuma ta waigo ta ce.

"Ni kuma...??"

"Eh, na hango ki da wani.."

"Uhm! Wani class mate ɗina ne ya zo karɓar jotter ɗinsa da na ara ganin kwana biyu ban shiga school ɗin ba..."

Girgiza kai Na'ima ta yi ta ce.

"Ki daina Rabi'a,Abbah baya son wannan ɗabi'ar...."

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Na ji. Ina za ku je?"

Wani kallon Mummy Jamila ta yi mata ta ce.

"Kin aike mu ne?"

Taɓe baki ta yi ta ce.

"A'a Mummy Jamila..."

Gaba suka yi wanda suna batun shiga mota da nufin Anasi ya fita da su sai ga motar Na'ima Hassan ta shigo gidan ita da Mum ɗin ta.

Yaa Na'ima na ganinsu ta ƙara so a hankali da cikinta wanda ya fito sosai ta fara murmushi tana musu sannu da zuwa.

Bayan sun gama gaisawa ne Na'ima Hassan ta kalle ta ta ce.

"Yaa Na'ima ina za ki tafi kika baro min ƙawata ita ɗaya?"

Dariya ta ce.

"Saƙon Ammie za mu karɓo cikin gari,amma yanzu in sha Allahu zan dawo."

Kallon su Rabi'a take ta yi tamkar za ta shaƙo Na'ima Hassan, ta rasa miyasa ta ji ta tsane ta a duniya. Har da ita suke haɗa baki ita da Anaam wurin neman hanyar musguna mata, ga kuɗi ga komai amma kuma dai ita ma dai babu fasali kamar ƙawarta ta. Shiyasa hali da siffa su ka zo ɗaya har suke abota. Munafukai,...

Tana ganin sun buɗe bayan motar sun saukar da wasu kwalaye da aka yi wrapping ta matsa da murmushi kamar da gaske ta ɗauki kwali biyu tana faɗin.

"Bari na taimaka muku da wannan."

Murmushi Suka yi sannan Na'ima ta ce.

"Thank you Rabi'a..."

Suna shiga main entrance ɗin Wanda ita ma Anaam ɗin har ta iso da saurin ta domin tarbar ƙawarta kawai suka ji abu ya faɗo wasu abubuwa sun amsa da alamun fashewa.

Cikin tashin hankali Mum ɗin Na'ima ta kalli Rabi'ar ta ce.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ke ko babba dake za ki tsaya kayan nan su suɓuce miki a hannu?"

"Sorry..hannuna ke ya suɓuce."

Within seconds wani irin sihirtaccen ƙamshi mai sanyaya zuciya ya bice ko'ina na wurin.

Cike da baƙin cikin wannan aika-aikar Na'ima Hassan ta duƙa ta buɗe kwalin wanda gabaɗaya taga kwalaben da ke ciki duk sun farfashe. Da ace faɗowa kawai suka yi da tabbas da wahala su fashe da yawa haka, amma da gangan ta ɗaga sama a bayan idon sa ta sako kwalin tsabar baƙar muguntar da ke ciciyar zuciyarta.

Tun da Mum ta yi tafiya ta saka ta a gaba akan cewa ta siyo ƙawarta turarukan na musamman wanda daman can sana'arsu ce sai da turaruka da kayan ƙamshi na amare, sanin Muhimmancin Anaam a wurin Na'imar yasa Mum ta zage ta haɗo mata kayan ƙamshi masu masifar tsada amma shi ne wannan shegiyar yarinyar ta yi sanadiyyar halakar da su.

Wani kallon Anaam ta shiga yi mata wanda ta tabbatar cewa da gangan ta sako wannan kwalin ba don ya suɓuce mata ba ne.

Na'ima da Mum Ɗinta ba su san halin ta ba ne, da ace sun san Halin ta tabbas ba za su bari ta ɗauko musu kaya ba.

Tattara wa suka yi Anaam na ta aikin ba wa Mum haƙuri suka taka suka shiga gidan.

Suna shigewa Rabi'a ta bushe da dariyar mugunta ta ce.

"En iskan Munafukai. Sai aje ayi iyayi in gani."

*******

Gefen hanya ya samu ya yi parking, ji ya yi gabaɗaya numfashinsa ya rikice. Wani irin faɗuwar gaba ya ke ji wanda ya sanya shi dafe sitiyarin motar da ƙarfin tsiya tamkar zai ɓallashi gida biyu.

Kalaman Rabi'a ne suka shiga maimaituwa a cikin kansa tamkar yanzu ne take furta masa su.

Lumshe idanun sa ya yi tare da ɗora kan sa saman sitiyarin motar yana mai jin wani irin ciwo na sukar zuciyarsa.

Not only wai saboda jin an ci zarafinta an ɓata mata suna ba ne,Noo..saboda duk abinda take going through shi ne sila. Shi ne wanda ya fara komai, shi ne wanda ya jefa ta cikin wannan Duhun wanda har yau babu hasken fitilar da zai iya dusashe shi. Ya tafi da niyyar ɗaukar fansa wanda neman fansar bai amfane shi da komai ba sai lalata mata rayuwa.

"Ya Allah...."

Ya furta a sarari yana mai girgiza kansa.

Bai taɓa tsammanin cewa wannan al'amarin zai juye ya dawo haka ba, shi da ya rayu cikin gata da sarauta a wurin mahaifinsa, sai ga mutuwa ta zo ta ɗauke masa shi ta sandiyyar azzaluman babanta, daga nan ya dawo rayuwa tare da mahaifiyarsa wacce ita ce duniyar sa. Sai ga shi kuma a yanxu ya sake tsintar kansa cikin wata rayuwa ta rashin gaskiya da rashin sukuni, lokaci rayuwar ta juye masa sama ƙasa ba tare da ya yi aune ba.

Jin kalaman Rabi'a ba ƙaramin karye masa zuciya suka yi ba. Hakan sai yasa ya tuna irin kallon da take masa mai cike da tsoro da ruɗani, sai ya tuna da hawayen da ya gani kwance waɗanda basu nuna komai ba sai zallar karaya.

Sake gina girgiza kansa ya yi ya ce.

"I did this to her...I'm the causer of everything da yake faruwa da ita."

A hankali ya sake buɗe idanun sa wanda a wannan karon ji ya yi idanun na sa sun cika da wani abu wanda bai taɓa jin irin sa ba. Tausayi...tsantsar tausayinta yake ji.

Wayarsa ya ciro da sauri ya kira Hamad. Hamad shi ne ɗan uwansa, amininsa kuma abokin shawarar da bashi da kamar sa a yanzu. Ko mutum ya kashe tabbas zai iya samun Hamad ya sanar masa domin ya san har abada ba zai faɗawa kowa ba. Fushi ne da son gaskiyarsa yasa yake tsare wuta wani lokacin har ya yi tamkar zai rabu da shi, kuma shi ya san mutuwa ce kaɗai za ta iya raba su.

"Halo...."

Murya a matuƙar raunane ya ce.

"Hamad..."

"Yes! Wai kana ina ne nikam? na je base har sau biyu baka nan and yanzu kuma na ji muryarka ta canja, ko har Anaam ɗin ta kira ka tace ta fasa auren ne?"

"I hurt her Hamad..."

Shiru Hamad ya yi domin har ya fahimci abin da yake magana a kai.

Jin ya yi shiru yasa Hamad ɗin ya jinjina kansa tamkar yana a gaban sa ya ce.

"I know..."

"I didn't know that it was this bad...she suffered saboda ni. Laifin da na aikata mata yasa sunanta ya je viral cikin cin mutunci da ƙasƙanci..."

Ajiyar zuciya Hamad ya yi sannan a hankali ya furta masa cewar.

"Ka fi ni kusa da ita a yanxu,saboda haka ka yi duk abin da ya kamata."

Yana jin Hamad ya katse kiran ya sauko da hannunsa a hankali sannan ya koma ya kwanta jikin kujerar mota tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ya ja motar ya tafi cikin rashin kuzari da rashin walwala.

******

Gidan Alhaji Gimba Kuwa, a yanxu lafiya lau suke zaune a gidan babu wani hayaniya ko tashin hankali. Faris ya koma bakin aikinsa a kamfanin Mahaifin nasa wanda shi ne gaba da komai. Alhajin yana nan shi ma a tare suke gudanar komai, a yanzu duk wata matsala da ta faruwa a baya ya riga ya zame musu tarihi domin Maimuna dole ta zauna ta ci gaba da biyayya ba don ta so ba. Tabbas da ace tana da kuɗi ko ita ko iyayenta wallahy tallahy da ta tafiyar ta ta huta, ko kuma da ace tana da wani mai kuɗin da zai aure ta idan ta fita da tabbas ta nemi saki ta tafiyar ta. Gabaɗaya alkawarin da ya ɗaukar mata ya kasa cika shi. Komai a yanzu matar sa a gaba. Sai ta yi kamar taje wurin Aunty Halira ta kai ta wurin malamin sai ta ji kuma bari dai ta bari ko zai can ja.

Yanzu ya dawo normal tamkar ba shi ba, sai dai hulɗa da Alhaji Mas'ood Galadima da gaske ya yanke ta har abada. Tun da aka yi musu wannan iyakar tun daga lokacin ko waiwayar inuwar inda suke bai ƙara yi ba.

Yau ma yana tsaye misalin ƙarfe biyar na yamma wanda ya fito kenan da nufin komawa gida sai ga kiran Alhaji Ridwan ya shigo wayar sa. Sai da ya kirashi kusan sau huɗu sannan a na biyar ya ɗauka ya ce.

"Wai Ridwan lafiya?"

Cike da jin ba daɗi daga can ɓangaren Alhaji Ridwan ɗin ya ce.

"Haba Gimba saboda Allah! Duniyar nan fa da kake gani wallahy ba komai ba ce...."

"Lafiya ka kira ni? Kasan kai tauraruwa ne mai wutsiya wanda jin ka ko kuma ganin ka ba alheri ba."

"Hmm! Allah ubangiji ya shiryeka. Daman 'yarka Maryam ce ta gidan Alhaji Mas'ood za ta yi aure jibi, to shi ne naga na tura maka saƙo a what'sapp tsawon 2weeks ba ka buɗe ba, shi ne nace bari na kira ka na sanar maka domin kana da haƙƙi da a sanar maka..."

" Ita kingin mazan ce ta samu miji har za'a yi aure?"

" Haba Alhaji Gimba... "

" Ridwan da ka ta! Shin ba gabanka ba ne aka yi mana iyaka da Mas'ood?"

" Ina amfanin a yi ta abu a rayuwa wanda baya wucewa... "

Cike da tashin hankali ya shiga ci wa Alhaji Ridwan mutunci yana gasa masa magana son ransa yana faɗin shi ɗin ba ɗan maula ba ne, kuma shi bai yasar da zuciyar shi kare ya lashe ba. Haka dai Alhaji Ridwan ya katse kiran rai babu daɗi Wanda duk wayar nan da suke yana zaune tare da Alhaji Mas'ood a gefen sa.

Haƙuri Alhaji Ridwan ɗin ya bashi tare da ƙarfafa sa akan cewa ya yi haƙuri tun da ya ƙi saukowa ya manta da shi kawai ya ci gaba da harkokinsa.

Cikin ƙanƙanin lokacin Familyn Alhaji Mas'ood suka fara shirye-shiryen buki na gani na faɗa. Babu abin da suke idan ba aikin kashe kuɗi ba. Gata kam Anaam ta sha shi ta ko'ina tamkar wacce za'a ce daga ita an gama aurarwa a gidan.

Yau ma, Bayan sun je ƙayataccen sa lalle da ya tara dubban jama'a sun dawo ne Na'ima Hassan ta kalle ta ce.

"Wai nikam Anaam ba ki sanar da Maheer ba ne?"

Ajiyar Zuciya ta sauke ta ce.

"Ko da ban Faɗamasa ba ai na san Hamad ya sani" ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 41*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull