Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 32
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 32: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 32. "Don Hamad ya sani shi ne angon?"
3,351 words
"Don Hamad ya sani shi ne angon?"
Girgiza kai ta yi ta ce.
"No..but shi ne ya kira ni ya na bani excuse akan cewa abokin nasa aikinsa ya riƙe shi wanda bai san ta yanda zai fara mini bayani ba, amma in yi haƙuri gobe zai zo. With this kin ga dole Ince Hamad ya sani.."
Dariya ce ta suɓucewa Friendy ɗin ta tace.
"Malama kawai ki ce ya ba ki haushi ne don ya ƙi attending that's why ki ka ce haka? And I can see it Yanda kike ta cin magani...ki yi haƙuri tunda har ya baki excuse ɗin sa nasan in sha Allah gobe he will be here..."
Ita dai Anaam ba ta sa ke ce mata komai ba har suka isa gida wanda suna shiga Yayan Na'ima ya zo ya ɗauketa zuwa gida ita da Mum ɗin ta, bayan sun wuce ne Anaam ta shige ɗakin da Mummy Nafisa ta ke ciki wato autar su Ammienta domin gaishe da ita.
Tana shiga ta yi mata murmushi tare da ɗan rausayar da kanta alamar shagaɓa ta ce.
"Mummy Nafi yanzu don Allah sai yau za ki zo?"
Janyota ta yi zuwa jikinta tana murmushi ta ce.
"Ayi hak'uri yanayin aikina ne yasa haka. Masha Allah! Ya kike ya hidima?"
"lafiya lau Mummy Nafi. Yaa kamal fa?"
"Kamal bai dawo ba Anaam, but In sha Allahu kafin jibi dole ya sauka Abujar nan domin ɗaurin auren ki..."
Sunkuyar da kan ta ta yi ƙasa ta ce.
"uhm! Ka ji Mummy dai..To shi Yaa Kamal ɗin yaushe ne auren na sa?"
Hijab ɗinda ta yi sallah ta cire ta ninke tana faɗin.
"Ban sanar mishi ba Anaam, tunda yace har yau bai samu wacce yake so ba ai sai ya yi ta zama a haka."
"In sha Allahu shi ma zai yi watarana."
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Haka ne kuma, Allah ya zaɓa mafi alheri amin. Bari na je Aunty Nasmah tun ɗazu suke jirana ita da Yaya Hanne."
Daga haka ta fice ta bar Anaam zaune tana rage powdern fuskanta. Tana nan zaune wayar ta tayi ƙara, tana dubawa ashe Yaa Na'ima ce. Ɗaga kiran ta yi tace ta same ta ɗakin da Mummy Nafi ta sauka.
Iyaka 5minute sai ga ta ta shigo tana tafiya a hankali har ta iso ta zauna gefen tana kallon Anaam ɗin ta ce.
"Su Yaa Amina sai aikin neman ki suke tun ɗazu..."
Taɓe baki ta yi ta ce.
"Ƙyale su Yaa Aminan nan kullum maganar su ɗaya ce."
Dariya ta yi ta ce.
"To ai su so suke komai ya yi daidai Anaam..."
Girgiza kanta ta yi ta ce.
"Yau fa na ƙudurta a raina babu wanda zan tsaya saurare ko su Mama Hanne ne kuwa..."
Cikin alamar tsokana ta ce.
"Har Maheer..."
Taɓe baki ta yi ta ce.
"Ban san ma a ina yake ba, yana duniyarsa ina duniyata. Tun ranar da ya zo ɗin nan kika gaisa da shi har da abokin sa tun ranar bai sake zuwa ba and ko a waya wannan bamu taɓa magana ba Yaa Na'ima...I'm scared..."
A mamakance Na'ima ta ɗan waro ido ta ce.
"Wai kina nufin ba ki kira shi ba har yanzu and shi ma bai taɓa kiran ki ba?"
Shiru ta yi tare da Sunkuyar da kanta ta shiga murza en yatsunta da su ka sha lalle maroon su ka yi kyau sosai kamar ba za ta ce mata komai ba, sai kuma ta lumshe idanunta sannan ta buɗe su a hankali ta ce cike da fargaba ta ce.
" Ban san dalilin da yasa nake jin tsoron kiran sa ba Yaa Na'ima. and ina da maganar da nake so na furta zuwa gare shi tun kafin igiyoyinsa uku su zargu a kaina. Ina jin nauyi da kunya a ƙirjina, ina jin tsoron kada ya fara jin tarihina har ya fuskance ni ba tare da na fara sanar da shi ba. Ina matuƙar son na yi magana da shi, akan wannan ɗin ko ni ce na fara kiran sa ba zan damu ba matuƙar ya fahimce ni. To idan na kira sa ban san mi zai ce ba, I'm not even sure zai ɗauka Ko kuma ya fahimce ni ta Waya... "
Hannayenta Na'ima ta kamo ta jimƙe a na ta a natse ta ce.
" Anaam..."
Ɗago idanun ta tayi waɗanda suka jiƙe da ruwan hawaye ta amsa da sassanyar murya ta ce.
" Na'am..."
"Kina jin soyayya...ina nufin do you have feelings on him?"
Kai tsaye ta girgiza kanta a hankali ta ce.
"Ba na jin soyayya kuma ba na jin ƙiyayya. Ban sani ba ko don iyayena da dangina duk amshe shi hannu biyu ne, ban sani ba ko don Ya fito daga ɓangaren Aunty Dinaratu ne, and ranar da iyayensa suka zo suka kawo kayan lefe da kayan aurena sun nuna tsantsar so a gare ni, hakan yasa na ke jin cewa ba zan iya watsa musu ƙasa a ido ba. Haka iyayena bana so na janyo musu zagi ko kuma su ji a ransu kamar bana jin maganarsu."
"Ko ma miye Anaam mu Familynki mun san cewa ba laifinki ba ne. Shi ɗin wata ƙila ma yana nan yana jiran kiran ki. A wasu lokutan na rayuwa, maza suna son su ga irin muhimmancin da mace za ta fara nuna musu..."
Wani irin faɗuwar gaba ta ji wanda ita kanta ba ta san dalilinsa ba. Tun da aka fara shirye-shiryen auren nan, wani irin abu ke damunta. Wani abu take ji a zuciyarta wanda ba ta iya fassarawa.
Wataƙila saboda yanayin yanda ya nuna mata ne na rashin kulawa, watakila kuma ya ji komai dangane da Ita yasa ya ƙara yin baya-baya da Ita. Yace son ta yake da aure amma kuma har yau bai taɓa yi mata wata maganar da ta danganci soyayya ba.
"Miye kike tunani Anaam??"
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sake kallonta ta ce.
"Abubuwa da dama Yaa Na'ima..."
"Ni sai in ga kaman harda damuwar aure da fargaba. Duk wanda zai yi aure sai ya shiga irin wannan yanayin, kuma kin san na shiga irin yanayin nan ni ma, and I assured you komai zai wuce in sha Allahu..."
Wani murmushi ne ya suɓuce mata na ba za ki gane ba tana mai girgiza kanta a lokaci ɗaya ta ce.
" Uhm! Yaa Na'ima kenan! Ba Za ki gane ba ne...."
Dariya ta yi ta ce.
" Ba wani ba zan gane ba ai haka kuka ta mini lokacin ke da Yaa Mubarak har sai da na yi kuka. Saboda haka ni dai abin da kawai zan faɗa miki shi ne ki yi ta addu'ar neman zaɓi mafi alheri daga wurin ubangiji, abun da ya faru dake ba saya kika yi da kuɗin ki ba ƙaddara ce ta faɗa miki. Ko ya ji babu abin da zai faru. Kuma ma wallahy ni ina ji a jiki kamar en gulma har sun same shi sun sanar da shi wannan maganar. Kuma da ace baya da ra'ayi da yanzu kin ji zance ya canza. Please ki nutsu ki daina damuwa..."
"To Yaa Na'ima na gode sosai...."
"Yaa Mubarak tun ɗazu yake neman ki wai shi bai saka miki na shi lallen ba saboda haka ke yake nema..."
Dariya ta yi ta ce.
"To sai ya yi me idan ya ganni ɗin?"
"Wai kina ɗaukar zancen nan wasa ko? Wallahy da ƙullin lallen sa a hannu ban san a ina ya samo ba."
"Ya wuce Mummy Jamila tun da na ganta da robobin lalle a hannun ta ɗazu."
"Hmm! Gidan nan Alhamdulillah! Ya cika sai nishaɗi ake komai gwanin burgewa kafin kuma en gutsiri tsoma su Umma su iso...."
"Yaa Na'ima nidai ta shi ki samo min lemu mai san yi kada in fita kuma wani ya ganni ya riƙe ni a can."
"Af! Ke yanzu don ba ki da tausayi mai ciki kike sakawa aiki? Ni fa ko mijina wallahy baya sakani aiki, komai shi yake mini har na iso garin nan..."
Dariya ta yi ta ce.
"To yaa Na'ima ya za ki yi tun da aurarwa za ki yi. So kike ki kai ni ɗakina saboda haka dole ki yi min duk abinda nake so wallahy ko in kira Yaa Haisam.."
Miƙewa ta yi ta shige toilet itama Na'ima ta wuce waje.
*****
Yau ta kasance Alhamis wanda Gidan Alhaji Mas'ood ya cika da hayaniya na en uwa da abokan arziki.
Shirye-shiryen auren sun yi nisa sosai Kowa sai kai komo yake yana abinda yake gaban sa.
Rabi'a kuwa na nan tana kallon komai a hankaɗe tana jin daɗin domin Umma ta tabbatar mata cewa auren nan ba zai faru ba. Kullum son Maheer ƙara ninkuwa yake a zuciyar ta, da gaske take son sa kuma shi take son ta rayu da shi ba Faris ba. Idan har komai ya tabbata ta yi nasara tabbas tasan Abbah zai ɗaura aurenta da Maheer wanda duk su Muhammad babu wanda ya isa ya ce zai hana sai dai su haɗiye zuciya su mutu.
Duk abinda take tana nan ta na duba lokaci wanda ba ta ji cewa mafarkinta ya kusa tabbata ba sai da ta jiyo ana yi wa su Umma sannu da zuwa.
Da gudu ta fito ta rungumeta wanda saura ƙiris su rufta zuwa ƙasa tsabar jindaɗi da farin cikin ganinta ta ce.
"Oyoyo Umma na Oyoyo uwata maganin kuka na!"
Kallon ta kowa ya shiga yi yayin da Hajiya Hanne ta buga wani irin uban tsaki ta ja hannun Mummy Nafi suka yi waje wanda daman sun fito da shirin wucewa gidan Anaam ne domin gyare-gyare.
Wata irin shewa Umma ta yi ta ce.
" Wallahy dole a ganni, kuma dole a bar ni, kuma zaman ɗiyata daram a cikin gidan nan domin itama gidan ubanta ne. Kuma ma daga nan zuwa jibi ba'a san abinda Allah zai iya yi ba..."
Cike da takaici Ammie ta girgiza kanta ta ce.
"Wai ke Umma don Allah miyasa ne neman fitina ya yi miki yawa? Miya sa ba ki so a zauna lafiya? Yanzu na tara mutane ya dace ace da isowar ki ki fara mini irin wannan abun?"
Taɓe baki ta yi ta ce.
"Ah to naga kamar ana so a ɗauke ki banza, komai ya tashi a gidan nan sai inga ana maisheni baya alhali nima ina da ruwa ina da tsaki a gidan nan. Da mijina da mai gidan nan uwa ɗaya uba ɗaya suke, mijina ne a gaba sannan na ki, amma komai sai ki riƙa nuna ni ɗin tamkar wata bare ce wanda. Ke kin sani duk abin da Alhaji Mas'ood zai yi sai ya shawarci yayansa sai ya nemi izininsa, amma kuma.... "
Wata daga cikin ƙawayen Ammie da ke zaune tun ɗazu tana kallon Umma ce ta girgiza kanta ta ce.
" Hajiya Nasmah please ki daina kula wannan domin ina tunanin tana da motsin ƙwaƙwalwa. Duk zaman saurarenta da nake na za ta ita ce uwar mai gidan ko kuma yayarsa ko ƙanwarsa, ashe laƙe-laƙe ne ƙarfin halin ɓarawo da sallama..."
Wani malalacin murmushin gefen baki Ummar ta yi sannan ta ce.
" Wallahy kuna nan ba da jimawa ba sai na shayar da ku mamakin da har ku mutu ba za ku manta da ni ba....Kai ku wuce muje ciki. "
Ta ƙarashe maganar tana mai kallon Ƙanwarta Shema'u da ɗayar 'ƴarta ƙanwar Rabi'a mai suna Rashida. Suna shiga cikin ɗakin Rabi'a Shema'u ta ce.
" Aunty Ni fa babu mai bani mamaki irin Na'imatu...."
"Hmm! Ai ita wannan ɗan wake ce kafi ubanka. Kamar kada ta zauna a gidan nan, yanzu fa har uban na ta ta tattara ta watsar saboda neman suna ta riƙe Alhaji Mas'oodu kamar shi ne wanda ya haife ta. Tunda ta yi auren nan ga shi tana batun mayar da shekara amma har yau bata taka taje Gusau ba, to ko dangin uwar ta ta mayar da su banza ta kama Nasmah da dangin ta. "
Cike da jin wani sabon baƙin ciki Rabi'a ta ce.
" Ai Umma sai ma kinga yanda suka mayar da ni banza wofi a gidan nan. Komai da Yaa Na'ima ake sun bar nan kamar bola. Ko niƙi-niƙi kayan da aka kawo wa Anaam tun da na gansu a filin da aka ba za su aka tarbesu har yau ban sake sanin Inda aka yi da su ba.... "
Jinjina kai Umma ta yi ta ce.
" Kwantar da hankalin ki. Kin dai tabbatar kin faɗa masa cewa kina son sa? Kuma kin tabbata da kika ce kina son sa bai ce miki baya son ki ba ko kuma ya yi miki wani rashin mutunci?"
"Wallahy Umma ko ɗaya. Komai bai ce ba kawai shigewa ya yi motar sa ya tafi. Oh my God! Umma Wai kingansa kuwa? Kin ga kyaunsa da irin zubin halittar sa? Kuma na san maganata ta gama yin tasiri domin jiya bai zo wurin event ɗin nan ba, kuma gashi komai da shi aka tsara MC sai neman ango yake amma shiru har aka ƙare. Ita ma Yaa Dina munafuka sai wani azarɓaɓi take cikin raina na ce duk sai na ci ubanku na yi maganin ku...."
"Ki bar su kawai! Kin same shi kin gama Rabi'atuna. Kuma ina tabbatar miki duk kayan lefen nan a gaban su za'a kwaso su a baki...ke da hannunta ita Nasmah ɗin za ta ɗauko su ta bamu. Ga wannan...."
Ta ƙarashe maganar tana mai ciro wani ƙulli a haɓar zanin ta ta miƙa mata ta ce.
"ki ɗiba ki jiƙa a ruwa sai ki yi masa shafin kwalli, ki fara daga yau zuwa gobe, ki yi duk yanda za ki yi ki haɗa ido da shi, ina tabbatar miki gobe aure dake za'a ɗaura ba Anaam ba."
Rungumeta ta yi cike da wani irin farin ciki tace.
"Na gode Umma ta, na gode miki. Allah ya ja da ranki ya ƙara miki nisan kwana. Wallahy Umma ke kanki sai kin riƙa alfahari idan har ya zamo surukinki, sannan za ki dama za ki fantama umma domin wallahy kallon sa kaɗai idan kika yi za ki tabbatar shahararren mai kuɗi ne ba na wasa ba, and ko danginsa sai kin gani umma...Wayyo Allah. "
Wata irin dariya Shema'u tayi ta tsantsar mugunta sannan ta ce.
" Ni ko ina so in ga idon Hajiya Nasmah yanda za ta tozarta ta wulakanta akan mutanen da take tinƙahon ta tara...."
"Hmm Bari! Ai lokacin da na so Alhaji Mas'ood ya auri Binta (cewa da ɗayar Ƙanwarta wacce ta yi zawarci a baya amma yanzu ta yi aure.) da ace ya aure ta da yanzu mune ke faɗa a ji a gidan nan. Amma da yake ko ita Bintar munafuka ce gata can ta sake auren matsiyaci tana ganin wahala...."
Taɓe baki Shema'u ta yi ta ce.
" Hmm! Ai Aunty Binta an yi banza ta ƙarshe wallahy. Wallahy ni da ace nice a wannan lokacin wallhy da duk abinda zai faru ke ko zan yi yawo ba zani a jikina wallahy sai na aure shi..."
"To ai gashi nan taji tsoro ta ja baya tana can tana auren gara lamba ɗaya. Ita kuma Nasmah ta zauna ta miƙe ƙafa tana cin duniyar ta da tsinke ita da yara..."
Haka dai suka yi ta fira har sai aka gama shirya ma amarya zuwa wurin Walima ba su fito ba sai da Rabi'a ta ce su tashi time ya yi su shirya su tafi Hall ɗin.
****** Misalin Ƙarfe biyar na yamma. Ana tsaka da shan romon walima inda su ka samu halarta wani babban malami Dinaratu ta fito wajen Hall ɗin ta kira Maheer a waya.
Wata irin hayaniya ce ta mamaye bakin ruwan,yayin da manyan jiragen ruwa ke ta sauke kaya, cranes ne ke ta ɗaga containers sama suna sauke su a hankali, yayin da ma'aikatan kuma ke ta kai komo cikin sauri domin ganin sun aiwatar da komai cikin nasara.
Maheer ne tsaye gefen babban jirgin ruwa da ya sauko daga ƙasar Singapore wanda ke sanye da farar helmet, safety jacket orange colour da kuma baƙin shade a idanunsa Kamar Ko yaushe. Hannuna na dama riƙe da tablet wanda yake duba bayanan consignments da aka sauke yayin da kuma hannun hagun ke riƙe da na'urar sadarwa da yake magana da abokanan aikin sa.
"Sir...Wannan container ɗin fa ba ita ce cikin manifest ba."
wani daga cikin ma'aikatan ya faɗa yana mai nuna masa wata container.
Ɗan ƙara stepping Maheer ɗin ya ɗan matsa kaɗan sannan ya ɗaga glass ɗin idanunsa ya duba lambar da ke jikin container ɗin ya ce.
"Check the bill of landing again..."
Takardar da ke can ta ƙasan hannunsa ya yo dama da ita ya duba sannan ya ce.
"Sir...wannan lambar ba ta cikin list ɗin da aka aiko mana."
Lumshe idanunsa ya yi kaɗan sannan ya jinjina kansa ya ce.
"Okay... hold the container,Don't release it har sai an gama bincikenta."
"Yes sir."
Daga haka Maheer ɗin ya juya ya nufi wajen wani crane operator wanda ke ƙoƙarin sauke wata babbar container ya ce.
"Careful Mr. Sas!..."
Ringing ɗinda wayar sa ta yi ne ya dakatar da shi yana mai duba screen ɗin wayar.
'Sis Dina'
Office ya koma yana mai jan numfashi a hankali ya kira wayar ta ta. Kamar ta san cewa tunaninsu ne fal a cikin ransa tun ɗazu. Ya so kiran Anaam ɗin kamar me amma kuma ya kasa, yana so ya tambayeta ya take amma kuma ya kasa kiran.
Yana jin ta ɗaga ta mi shi sallama ya ce.
"Barka da warhaka Aunty..."
"Barka Maheer...ya aiki?"
"Lafiya lau Aunty...ina bakin ruwa, ina kan duty."
Jinjina kanta ta yi kamar suna ganin juna ta ce.
"Yanzu Hamad yake sanar min cewa kana bakin aiki... amma miyasa baka zo event ɗin jiya ba? An shirya komai da kai amma kuma baka zo ba, ran Anaam sam bai yi daɗi ba."
Shiru ya ɗan yi tare da ƙura ido yana kallon jirgin ruwan da ake saukewa wasu containers sannan daga ƙarshe ya ce.
"Aunty kin san ina Lagos ne...Ina cikin shirin tahowa nan sai ga emergency shipment ya shigo jiya da safe nan."
"Alright...Allah ya taimaka."
"Amin, in sha Allah gobe da wuri zamu fito."
"ah to, gobe ɗaurin aure ai dole ku iso da wuri kam. Allah ya kawo ku lafiya."
"amin."
"Maheer nikam na ce har yanzu Maami ba su iso Abuja ba? Na ga gobe ɗaurin aure and ko yau wurin walimar nan babu relative ɗinka ko ɗaya.."
Daram! Haka ya ji ƙirjinsa ya buga. Shi fa waɗan nan mutanen bai san su ba, bai san ko su waye su ba, Kuɗi ya biya shi kuma Ahmad ya samo masa su.
And again, tuna sunan Maamin sa da ya yi sai da ya ji wani sabon tsoro ya shige shi, ko ɗazu ba'a fi 2minute ba sai da ta kira shi suka jima suna magana sannan ta kashe. Baiwar Allah ba ta san ma da wani zancen zai yi aure ba, shi har yau mamakin irin ƙarfin halin sa yake domin yanda ya Haƙiƙance yana shirin auren nan abun har mamaki yake bashi.
To amma ƙaddara ta riga fata, zai yi duk yanda zai yi domin ya samu komai ya daidaita sannan ya koma gare ta. Hakan yasa yake ɓoye kansa wanda ko gobe baya tunanin cewa zai iya bayyana kansa filin ɗaurin auren nan domin tunaninsa ya bashi ba'a rasa wani wanda ya san shi a wurin ɗaurin auren nan.
"Maheer..."
Da sauri ya dawo hayyancisa yana mai faɗin.
"Maami tana Zaria kuma yana da wahala ta zo nan, kin san ɗan fari..."
Murmushi ta yi ta ce.
"Allah Sarki! Allah yasa albarka."
"Amin"
*******
Tsaye take jikin windown ta misalin ƙarfe biyu na daren Juma'a wacce ita ce ta kasance rana mai ɗumbin tarihi a cikin ranakun rayuwarta domin ita ce ranar da duniya za ta shaida ɗaurin auren ta...
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*BOOK ONE* *PAGE 42*