Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 33
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 33: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 33. Wani irin faɗuwar gaba take ji tun safe har zuwa yanzu and yanzu…
3,354 words
Wani irin faɗuwar gaba take ji tun safe har zuwa yanzu and yanzu da take tsaye tana kallon sararin samaniya sai take daɗa jin yanda bugun zuciyarta ke daɗa tsananta yana ƙara dasa mata sabon tsoro da fargaba. Sai da ta yi nafila sannan ta roƙi Allah ya zaɓa mata mafi alheri kaman yanda Yaa Na'ima ta tunatar da ita.
Daman sun ji ma yau ita da Su Yaa Amina har da cousin ɗinta Sa'adah da ta iso ɗazu. Tun misalin ƙarfe tara suke zaune suna ta firarraki suna tattaunawa tare da ƙara bata shawarwari har sai da 12am ta yi clocking Sannan suka watse.
Duk abinda suka jima suna faɗa mata ya gama yin register a brain ɗinta kuma ta yi alƙawarin za ta yi iyayinta wurin ganin ba ta basu kunya ba, musammam Yaa Dinaratu da ta tsaya kai da fata wurin ganin cewa komai ya tafi daidai. Tana so ta zauna da zuciya ɗaya ko don ta faranta mata itama, uwa uba Yaa Muhammad sa kuma Yaa Mukarram da suka tsaya suka zamto bangon jingina kuma waɗanda babu abinda suke so da gani sai farin cikin ta.
Tasan shiga wata rayuwar zai yi mata wahala musamman da mutumin da har yau ba ta san ina ya dosa ba. A Rayuwar saurayi da budurwa kaɗai ana gina soyayya da shaƙuwa har ta yi tasiri ballantana wanda har maganar aure ta shigo an yi komai na al'ada da addini amma kuma har yanzu ana gobe ɗaurin aure bai san farin cikin ta ba haka zalika bai san baƙin cikin ta ba.
Hoton rayuwar Na'ima da Haisam ne ya zo mata a tunaninta da kuma rayuwar da yayyunta suke yi da matansu mai cike da tsantsar soyayya da kulawa. To ita a yanzu ina ta kama kenan? Idan ransu ya kai gobe aka ɗaura aure da me za ta fara ko kuma shi da me zai fara idan suka kasance a cikin rufi ɗaya? Anya zai amince da ita ya yarda da ita bayan ya ji labarin cewa ita ɗin ba cikakkiyar mace ba ce. Anya ba zai sake ta ba tun a cikin daren idan ta faɗa masa irin ƙaddarar ta? To wai miyasa tun farko ta bari har aka kawo nan ba tare da ta faɗa mishi ba? A lokacin da Sauban ya zo gare ta da yake bata tsaya nauyin baki ba sai ga shi cikin lokaci ƙanƙani kowa ya kama gabansa ba tare da ciwon rai ba. But ta ya ya a yanzu ta yi sake har hakan ya faru? Idan ya ce ya saketa gobe a wanne hali iyayenta za su kasance?
Rufe idanunta ta yi gam tare da girgiza kanta ta ce.
"Ya Allah...idan akwai alheri a cikin wannan aure ka sa ya tabbata Ya Allah...idan kuma babu alheri a cikin sa ka raba ni da shi cikin sauƙi kamar yanda ka rabani da Sauban..."
Tana gama faɗin haka ta buɗe idanun tare da matso ƙwallar da ta ji ta tarar mata ta juyo da nufin zuwa ɗakin mahaifiyarta.
Tana tura ɗakin Ammien sai ga shi sun yi kiciɓis.
" Aff!...Maryam Daman fitar da zan yi yanxu ɗakin ki zan tafi.. "
Faɗawa ta yi jikin mahaifiyar ta ta, ta fashe wani irin kuka mai tsuma zuciya tana faɗin.
"Ammie tsoro nake ji. Gabana faɗuwa yake gabaɗaya nema nake na rasa nutsuwa ta..."
Ƙara kwantar da kanta yi a shoulder ɗinta ta shiga bubbuga bayanta a hankali tana faɗin.
"Is okay my dear...."
Sai da ta sha kukanta ta ƙoshi ba tare da ta hana ta ba sannan ta janye tare da kamo hannunta suka zauna akan sofar calmly ta ce.
"Rayuwar 'ya Mace abin da ta ƙunsa kenan Maryam. Daga gidan iyayenta da suka tarbiyyantar da ita sai kuma gidan da ita ce za ta bada tarbiyyar. Matuƙar ta rayuwa rayuwa mai inganci a gidan iyayenta sannan ta samu gidan nagartaccen namiji to ta gama yin sa'a, domin In sha Allahu kamar yanda ta ginu da kyau a gidan iyayenta a haka za ta gina gidanta wanda ake fata da burin ta gina shi ne har gidan Aljanna. Ban isa in hana ki damuwa ba Maryam, amma ina miki rarrashi da ban haƙuri, ki yi haƙuri, a hankali you will blend with it. Ahlin Dina mutanen kirki ne, bana tunanin wata matsala daga wurin mijinki. Ki yi hak'uri ki zauna lafiya, kowa haƙuri yake yi. Ki manta da abinda ya faru dake a baya, wannan ya riga da ya zama tarihi in sha Allahu har abada...."
Cikin kukan ta ce.
" To Ammie idan matsalar rashin haihuwata ya dame sa fa? ko kuma danginsa?"
"Maryam....likitan ya kan duba matsala tare da amsa ta bisa ga yanda ilminsa da kuma abinda ya gani dangane da matsalar ya bada, amma kuma komai yana hannun Allah ne, babu abin da ya gagaresa, ko da wannan matsalan ko babu ita, za ki iya ki haihu za ki iya kuma ba za ki haihu ba wanda wannan duk yana daga cikin Ikonsa. Ki kwantar da hankalinki, idan ma ba ki haihu ba matuƙar yana son ki to hakan ba damuwa bane."
Daga haka ta sake kama hannunta ta ce.
"Mu je Alhaji yana neman ki."
Miƙewa ta yi ta bi bayanta har ɗakin mahaifin na ta inda a nan suka tarar da shi shi kaɗai yana zaune akan sallaya yana addu'a da alama sallah ya gama.
Murmushi ya sakar mata yana faɗin.
"Maryam Amarya.."
Sunkuyarda kanta ta yi tana mai ƙurawa ƙasan carpet ɗin ido ba tare da ta ce komai ba.
Ta sowa ya yi ya zo ya zauna a kusa da ita ya kira sunanta a hankali ta ɗago ta kalle shi ya ce.
"Gobe za ki shiga wata rayuwa ta daban. Ina miki fatan alheri, Allah ubangiji ya zaunar dake a ɗakin ki lafiya, Allah ya yi miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya, Allah ubangiji ya baki ikon yi wa mijinki biyayya ya haɗa hankulanku wuri ɗaya ya kuma baku zuri'a ɗayyaba."
Gefen veil ɗinda ke lulluɓe a saman kanta ta kamo ta share hawayenta a hankali can ƙasan maƙoshinta take ta furta amin sannan daga ƙarshe ta ce.
" Abba ka yafe min dan Allah!.."
Janyota ya yi ya rungumeta a gefen damansa tamkar zai yi kukan shi ma ya ce.
"ke ɗin nan mutuminiyar kirki ce, ba don wai kina 'yata ko kuma don ni ina mahaifinki ba ne yasa na faɗi haka ba a'a...ke mutum ce ta daban. A lokacin da kika taɓa barin gida saboda Rabi'a ne na ji ɓacin rai mai tsanani amma tunda kika dawo komai ya wuce na yafe miki, ba ki taɓa mini wani laifi na azo a gani ba bayan nan tun daga tashin ki har zuwa yau. Allah ya ƙarawa rayuwarki albarka tare da 'yan uwanki gabaɗaya. "
" Amin Abbahna na gode sosai Allah ya saka da alheri ya ƙara maka nisan kwana da lafiya mai amfani. "
" Amin. Ta shi ki je ki kwanta ki ɗan rage ko kaɗan ne, ga shi daman daren ya tafi sosai na nisa za'a yi asuba."
"To Abbah...Allah ubangiji ya tashemu lafiya."
*******
Washegari da ta kama Friday, tunda wuri kowa ya tashi aka shiga hidimar wunin buki da kuma shirin ɗaurin aure wanda za'a gudanar misalin ƙarfe goma sha biyu na rana.
Hayaniya ce ke tashi a ko'ina,gidan gabaɗaya ya ruɗe da hayaniyar farin cikin en uwa da abokan arziki.
Tun misalin ƙarfe takwas na safe mai make-up ta gama shirya Anaam cikin ƙayatacciyar kwalliya da ta yi daidai da zubin mashahurin Lace ɗinda yake jikinta wanda ya fito da ita.
Hannunta cikin na Yaa Na'ima suka fito cikin gidan tana tayata gaishe da mutane. Mama Hanne na ganinta ta kece da wata irin guɗa ta shiga yi mata kirari wanda komai hasssadar ka sai ka ji abin ya burgeka.
Camera man ɗinda ya shigo shima tun a nan ya fara yi mata hotuna da vedios wanda duk inda ta matsa ba ta wuce ma motsinsa.
Wani irin mugun tsaki Rabi'a ta buga a can ƙasan zuciyarta sannan ta yi wa Umma wani kallo mai cike da nuna zallar damuwa ta ce.
"Umma gabana fa faɗuwa yake wallahy..."
Ɗan guntun tsaki Umman ta ja tana faɗin.
"Mts! Sai fa kin kwantar da hankalinki Rabi'a, bana son garaje."
"Umma wasa-wasa sha ɗaya ake magana har yanzu ko unguwar nan bai shigo ba, ko abokin nasa har yanzu shiru."
"Zai zo mana, miye kike yi wa gaggawa?...kinga..wuce mu je ciki ki ƙara goga maganin kada wanda kika saka ace ya fara bin iska."
Har suka shige babu wanda ya kula da tsiyarsu inda kowa ke ta farin ciki suna ta arerewa.
Tana tsaye ita da Aunty Aysha Mubarak ya shigo tare da Yaa Naseer da kuma Yaa mukarram ɗauke da wasu ledoji a hannun Yaa Mubarak ɗin.
Kallon fuskarta ya yi cike da tsokana ya ce.
"Amarya bakya laifi..."
Banza ta yi masa tare da juya masa baya tana magana da Sa'adah tamkar ba ta ji abinda yace ba har suka haura suka shige sashen Abbah.
******
Tare da shi da Hamad suka iso Abujar, daga nan suka wuce suka haɗu da Ahmad wanda yake abokin Maheer ɗin daga nan kuma suka wuce Hotel suka shirya su uku wanda sukaɗai ne suka san gaskiyar abin da yake faruwa.
Ahmad yasan cewa tabbas iyayen Maheer na Ƙarya ne kuma na bogi domin ya faɗa masa dalilin sa cewa idan har Anaam ɗin ta ji cewa daga wata ƙasar yake yana da wahala ta amince masa, hakan yasa ya yi hayar iyayen Ƙarya wanda daga baya ya yi alƙawarin zai sanar mata gaskiya. Wannan shi ne iya abinda Ahmad ya sani amma bai san ainahin dalili da tushen wannan auren ba.
Ya san Maheer a school ne kawai amma bai taɓa ziyartar ƙasar da yake ba, daga school sai school sai yanzu da shi Maheer ɗin ya nemo shi daga baya.
Yana gama shiryawa Hamad ya kalle shi yana murmushi ya ce.
"Ita dai ranar aure daban ce kuma ta musamman ce. Ka fito yau a wani mutum na daban..."
Ajiyar zuciya ya sauke a fili sannan ya kalli Hamad ɗin ya ce.
"Zan fita wani wuri zan dawo ba jimawa..."
Saurin duba agogo Hamad ya yi ya ce.
"10:52am ne fa yanzu, we need to be there on time, atleast 11:30 ta yi mana a can..."
"I will be right back."
Daga haka ya fito ya shiga motarsa ya wuce.
Wasa-wasa tun Hamad na lissafin time ɗinda ya ɗauka har ya kai ga miƙe tsaye ya kira Ahmad wanda ya je haɗa kan waɗanda za su tafi ɗaurin auren a cikin familyn ƙaryar Maheer ɗin wanda ciki har da mata su biyar en ɗaukan amarya wanda suka tsayu kamar da gaske ya ce Ahmad mu haɗu gidan Alhaji Mas'ood ɗin har yanzu Maheer ɗin bai dawo ba idan ya dawo sai ya cim mana can.
Yana hanya Oga Nameer na ta aikin kiran sa domin yaga an gama cika lokaci kaɗan ya rage amma babu Maheer babu labarin sa sai nemansa ake.
Koda Hamad ya isa, ƙofar gidan da harabar gidan ya cika tinƙis da manyan mutane da mawaƙa da maroƙa ana ta hidimomi.
Wuri ɗaya ya tarar da Nameer da Mukarram suna tsaye. Kallon shi Nameer ɗin ya yi ya ce.
"Hamad ina Angon? Mintuna kaɗan ne fa suka rage...."
"Ya ɗan tafi ya dawo, in sha Allahu before time ɗin ya cika za ka ganshi ya dawo.."
Abu wasa-wasa har aka kai ga shaida ɗaura auren su amma bai iso ba. Ran Hamad ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, tun yana kiran wayarsa tana shiga har ta kai ƙarshe idan ya kira sai ace masa switch off.
Kowa sai tambayarsa yake ina Muhammad wanda har sai da ya ji shi kansa ya tsargu da lamarin. Amma kuma ganin iyayen Hayar da ya ɗauka suna nan a na ta komai da su sai ba su koma kan rashin zuwan na sa sosai ba.
Cikin gida kuwa, su Hajiya Nafisa na jin an gama ɗaura aure suka hau yin hamdala suna ta zubawa Anaam ɗin addu'o'i wacce jikinta gabaɗaya ya yi san yi.
Kuka take ta rusawa suna aikin rarrashinta cike da nuna soyayya da tausayinta.
Saɓanin Rabi'a da ta shiga cikin tashin hankali da tsananin baƙin ciki a lokacin da kunnuwanta suka jiye mata shaidar ɗaurin auren Maheer ɗin da Anaam. Lokaci ɗaya ta zube ta fara bori wai aljannun ta sun taso,wasa-wasa sai ga shi sun tara jama'a tare da janyo hankalin wasu da yawa daga cikin gidan.
Ganin daga ƙarshe kowa ya banzarar da su yasa Umma ta kwasheta ita da Shema'u suka shige ɗaki da ita.
Suna shiga Umman ta ce.
"Dan Allah ki tashi ki daina wannan abun Rabi'a...."
Cikin wani irin kuka ta tashi zaune tana kallon Umma ta ce.
"To ni Umma yanzu don Allah ya kike so nayi? Wallahy idan ban same shi ba zan iya mutuwa wallahy..."
"Ai dai haɗuwa ne baku yi kuka haɗa ido ba, to ki jira tukun ki gani idan kuka haɗa ido ina tabbatar miki a nan wurin zai sake ta a gaban iyayenta da en bukin da su ka tara. Ni hakan ma yafi bani farin ciki domin mayar da ita Ƙaramar bazawara sai yafi musu komai zafi da baƙin ciki...."
Da haka dai har ta samu ta rarrashe ta sannan ta tashi ta sake yin wanka ta shirya ta shafa maganin a ido sannan suka sake fitowa a tare.
*******
Bayan mutane da yawa sun watse misalin ƙarfe biyar na yamma sai ga shi a hankali ya shigo gidan bayan mai gadi ya buɗe masa gate.
Hamad yana nan a haraba tare da Dinaratu da Nameer suna tattaunawa suka ga ya buɗe mota a hankali ya fito.
Har yanzu yana nan da babbar rigarsa babu abunda ya canja, ya sha kyaun da duk wanda ya gani sai ya yaba domin ba ƙaramin wankuwa ya yi ba.
Da sauri Hamad ɗin ya iso ya tare shi ransa a matuƙar ɓace ya ce.
"Wai miye duk wannan? Miyasa za ka yi haka?"
Sauke muryarsa ya yi ƙasa ya ce.
"I'm sorry Hamad. Amma ba zan iya nuna fuskata a cikin wannan taron jama'ar ba. Ina tsoro kada wani ya gane ni matsala ta faru..."
"Matsala tun yaushe da ta faru Maheer? Wallahy duk wannan abun da kake ba baki nake maka ba, but ka bi a hankali. Ka sanya ni sai Ƙarya nake ta yi musu tsabar ka raina wayau na..."
"I'm sorry...."
A tare suka ƙarasa wurin su Aunty Dina wacce ya sakarwa murmushi ita da Oga Nameer ɗin ya ce.
"Na san bani da bakin magana, amma dai ina bada haƙuri..."
"Haba ba komai ai Hamad ya yi mana bayani, Allah yasa albarka ya baku zaman lafiya."
"Amin amin Aunty Dina, na gode."
Hannu ya miƙawa Nameer suka yi masabaha sannan Nameer ɗin ya kalli Hamad ya ce.
"Su Alhaji suna ciki sai ku shiga ku gaishe da su, na ji ance Baba Salisu da Alhaji Ridwan yau za su koma gida, idan baka gaisa da su yau ba bana tunanin ku iya haɗuwa gobe."
A tare suka taka suka shiga babban parlourn da ke ƙasa inda suka tarar har da Alhaji Yakubu mahaifin Nameer wanda yake Yaya ga su Hajiya Nasmah.
Ido suka zuba mishi har ya samu wuri ya zauna cike da nutsuwa ya gaishe da su.
Kallonsa Alhaji Mas'ood ya yi ya ce.
"Allah bai yi zamu haɗu da kai ba sai yau bayan ɗaura aurenku. Allahu ta'ala ya baku zaman lafiya ya baka ikon riƙe min ita bisa gaskiya da amana."
Jinjina kai ya yi idon nan nasa a ƙasa ya ce.
"In sha Allah."
A ransa kuma mamaki yake wai yau shi ne ya auri 'ƴar wanda ya kashe masa baban sa har da cewa wai ya riƙe masa 'yarsa bisa amana da gaskiya.
Nasiha Alhaji Ridwan ya hau yi masa tsawon lokaci sannan daga ƙarshe suka fito tare da mukarram da kuma Mubarak, Hamad, Maheer ɗin suka nufi cikin gidan.
Rabi'a ita ce farkon wacce ta fara tare shi wanda daman can tana nan tana dakon zuwansa tun farko, ido suka haɗa tana ta mishi murmushi tana iyayi har ta ƙara so dab da shi ta ce.
"Welcome..."
Wani kallon ya yi mata sai kuma ya kalli su Hamad, cikin sa'a ya samu suna can suna magana da wasu mata ya ɗan ƙara matso ta yana mai haɗe fuska ya ce.
"Idan kika ƙara kula koda inuwata ce sai na sa an ɓatar da ke. Wannan mummunar marar kyau, wacce ƙarti goma sha biyar suka yiwa fyaɗe ita nake so ba ke ba. Ko mai gadin gidana yafi ƙarfin ki ballantana ni Maheer Tahmeer Alee. Ƙazamar banza baƙauyiya."
Daga haka ya zaga ta gefen ta ya wuce wanda kowa ya ɗauka cewa wata maganar arziki ce ta haɗa su ba su san cewa wuta ce mai tsananin zafi da ƙuna ya ɗauke ta ya jefa ta a ciki ba.
Sai da suka gama gaishe da kowa sannan suka fito.
Kallon Hajiya Hanne Mummy Nafi ta yi ta ce.
"Sai na ga kamar fuskar sani a wurin yaron nan Yaya Hanne..."
"Allah ko! To wata ƙila kin san shi ne can a wani wurin ko kuma mai kama da shi..."
Daga haka ta miƙe tana faɗin.
"Ku zo fa mu yi harama yamma ko Ince dare na ƙara yi. Ina Hajiya Balaraba..."
"To masu bikon na ta sun iso ne waɗanda na ji ance suna tafe?"
"Tun yaushe da suka iso suna ɗakin Hajiya Nasmah. Itama kuma tun ɗazu na ji ance an gama shirya mata."
Koda aka fito da ita wani irin kuka ne take yi tamkar za ta haɗiye zuciya, sosai ta rirriƙe Ammie tana ta wani sabbatu mai ban tausayi. Da ƙyar yaa Muhammad ya yi nasarar janyo ta zuwa jikin shi ya kai ta har cikin motar shi wanda daman shi ne wanda ya ce zai kai ta har cikin ɗakin ta kamar yanda ya yi alkawari.
Mummy Nafi, Mummy Jamila, Na'ima Hassan sai kuma wata Hajiya Uwani da fito daga gefen Maheer ne suka shiga motar Muhammad ɗin, yayin da su Yaa Amina da su Yaa Na'ima suka shiga sauran motoci waɗanda Ahmad shi ne wanda ya zo da wasu friends ɗin shi sai kuma su mukarram da suka tafi da sauran en uwa.
Babu kowa a gidan sai Ammie da wasu en tsirarrun mutane sai kuma Rabi'a ita da Umma wacce tace tana da zama da Alhaji Mas'ood idan an yi sallar isha domin tana da wata magana da shi.
*******
BOUNMU CRESCENT, BABANGIDA BOULEVARD, MAITAMA, ABUJA,NIGERIA.
Lafe take a jikin Mummy Nafi har suka isa gidan na ta abinda ake kira gida.
Tana jin an buɗe ƙofa an ce a fito da ita ta sake fashewa da wani sabon kukan....
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*BOOK ONE* *PAGE 43*
Mummy Nafi ce wadda ta riƙo hannayenta tana yi tana rarrashinta cikin zallar tausayi suka nufi cikin gidan.
Gidan tsit yake babu ƙarar komai babu hayaniya, saɓanin gidan Abban ta da ta baro hayaniyar mutanen buki da sauransu. Wata 'ƴar ƙaramar duniya ce zan kira gidan domin ya haɗu iya haɗuwa, komai a tsare yake gwanin sha'awa tamkar a Turai, kalolin fitilu ne gasu nan iri daban-daban da suka ƙawata harabar gidan yasa ya ƙara kyau sosai.
A hankali suka taka suka tsaya a bakin ƙayataccen parlourn inda Mummy Nafin ta umarce ta akan ta yi addu'a kafin ta shiga.
Tana zaunar da ita bisa cushion da addu'a a bakinta Hajiya Balaraba ta ce.
"Ai ina ga mu kai ta ɗakinta zai fi..."
A nan Yaa Muhammad ɗin ya yi mata sallama ya koma yayin da Aunty Aysha suka ɗunguma da ita suka nufi sama inda aka buɗe wani bedroom suka shige da ita.
Santin ɗakin suka shiga yi musamman Yaa Amina da Sa'adah da suka yi ta yaba gidan tun a haraba har zuwa nan ɗin.