Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 34

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 34

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 34: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 34. Bayan sun gama duddubawa a hankali suka shiga watsewa suna…

3,367 words

Bayan sun gama duddubawa a hankali suka shiga watsewa suna lallaɓa ta musamman Aunty Dinaratu da take ta ƙwarara ta tana kwantar mata da hankali wanda daga karshe bayan sun wuce gidan ya rage daga Friendy ɗinta Na'ima Hassan sai kuma Yayarta kuma ƙawarta Na'ima.

Tana ganin ficewarsu ta ɗora kanta saman kafaɗar Yaa Na'ima ta shiga rera kuka a hankali yayin da can ƙasan ranta ke cike da tsoro da kuma fargaba. Tana so ta bayyanawa Yaa Na'ima abinda take ji amma kuma ganin Friendy ɗinta yasa dole ta haɗiye maganganunta ta kora da ruwa domin ba za ta taɓa iya fallasa mata matsalar da ke tsakanin ta da mutumin da yanzu ya zamto Mijinta, wanda za ta fara rayuwa da shi a matsayin Mijinta abokin rayuwar ta ba.

"Anaam..."

Yaa Na'ima ta ambata tana mai ƙoƙarin ɗago kanta domin ta kalli idanunta.

"Haba dan Allah? Tsakani da Allah wannan kukan ya yi yawa. Please ki bawa kanki salama!"

Ɗagowa ta yi tana wata irin ciccika tana girgiza kai ta ce.

"Yaayy.... Ya Na'ima tsoro nake ji..."

"Tsoron me? Babu abinda zai same ki sai alheri, duk matar da kika gani a gidan aurenta da wannan ranar ta fara..."

Hannunta Friendy ta kamo ita ma tana mai jin yanda idonta ya cika da ruwan hawaye ta ce.

"Friendy please you have to be calm,Idan ma kina jin tsoron first night ne I believe he will be gentle and ba Lallai ma ace yau ya nemi wani abu daga gare ki ba ko Yaa Na'ima?"

Jinjina kai Yaa Na'imar ta yi duk da cewa tasan inda tunanin Anaam ɗin ya dosa ta ce.

"Not possible Gaskiya, and idan ma ya nema ɗin ba za ki mutu ba domin ba a kan ki aka fara ba...."

Wata irin cafka ta yi wa Hannun Yaa Na'imar jin yanda wani sabon tsoron ya ninku a zuciyarta tuna abinda ya faru da Ita a daren da aka yi mata fyaɗe...she don't need that thing anymore...ta san azaba da bala'in da yake ciki. Ta suma doguwar sumar da ta ɗauki tsawon kwanaki ba tare da ta san a ina take ba, ta mutu ba adadi sannan daga baya ta yi nasarar dawo wa doron duniyar, ta haɗu da ciwo wanda ya kusa zautar mata da ƙwaƙwalwarta, ba ta so bata burin kasancewa da ɗa namiji domin wannan abun masifa ne.

"Anaamm..."

Da sauri ta girgiza kanta tare da lumshe idanunta da suka rine sosai suka kumbura tsabar kuka ta buɗe baki da niyyar magana Yaa Na'imar ta yi saurin saka hannu ta rufe mata bakin tare da girgiza mata kai alamar ta yi shiru. Daga haka ta sake ɗora kanta a shoulder ɗinta tana faɗin.

"Ki yi ta maimaita hasbunallahu wa niimal wakil kin ji ko? In sha Allahu za ki samu nutsuwa."

Shiru suka yi na ɗan lokaci wanda daga ƙarshe kiran Haisam ne ya yanke musu shirun da ya ratsa su. Tana ɗagawa sai ta ji zancen da ba ta tsamma ta ba cewa.

"Ina Anaam?"

Ɗan kallonta ta yi sannan ta ce.

"Ga ta nan a kusa da ni."

"OK to, An ce su Yaya Amina sun koma gida,please stay with her har mu shigo da angon sai mu wuce."

"OK."

Ta ambata tare da kashe kiran ta kalli Anaam ɗin ta yi murmushi ta ce.

"Kin ji abinda Baby yace ko?"

Dariya Friendy ta yi ta ce.

"Kai Yaa Na'ima, yanzu a gabanmu kike cewa baby ko kunyar mu bakya ji?"

"Kunya? Hmmm! Ai wallahy ku ɗin nan ba'a san me zaku yi ba nan gaba. Allah dai yasa albarka ya bada zaman lafiya."

Suna nan suna ɗan taɓa fira a hankali tsakanin su biyun har suka ji shigowar su. Da sauri friendy ta ƙara gyara mata zaman veil ɗinta murya a ƙasa sosai ta ce.

" Please behave..."

Shi ne na ƙarshe ga shigowa ɗakin sai kuma ya samu jikin ƙofa ya tsaya zuciyarsa cike da fargaba, duk maganganun da Hamad ya fara ba zai iya cewa ga guda ɗaya da ya saurareta da kyau ba domin irin tsananin tunani da ruɗun da yake ciki yama wuce misali.

Sai da suka kambala duk surutunsu sannan Ahmad ya kalle shi tare da miƙo masa hannu yana murmushi ya ce.

"Ango....Mun barka cikin amincin ubangiji."

Tamkar wanda aka sanyawa remote control haka ya ɗaga ƙafarsa a hankali ya janye suka fice wanda yana jin yanda Yaa Na'ima ke ta yi masa raha tana ce masa ya kula mata da 'ƴar ƙanwarta ya lallaɓa ta.

Kanta a ƙasa yake amma har yanzu kuka take mai tsuma zuciya. tana jin ƙarar rufe ƙofar zuciyarta ta ƙara tsananta bugawa wanda dukkan ilahirin jikinta a yanzu kuma kakkarwa yake. Daga Ita fa sai shi ne a ɗakin nan yanzu..miye abinda zai faru kuma?

Duk da cewa baya iya ganin fuskarta, yana jin yanda sheshshekar kukan ta ke tashi a hankali yana ratsa dodon kunnensa wanda ya ƙara haddasa masa mutuwar jiki.

Ya kai mintunan da suka kai sha biyar a tsaye ba tare da ya san abin yi ba wanda sai daga ƙarshe ya yi nasarar furta.

"I....I'm sorry!"

Daga haka ya matsa tare da zaunawa bakin gadon da niyyar yi mata magana wanda bai sani ba ko hakan zai yi making sense ne Ko Kuma a'a.

Ita kuma ganin ya zauna a gefen ta babu abinda ya zo mata a rai sai maganar su Friendy ta ɗazu, hakan yasa a gigice ta ƙara matsawa baya sosai tana faɗin.

"Dan Allah ka yi haƙuri..."

Ganin yanda duk ta ƙara gigicewa tana ƙara matsawa yasa da sauri ya janyota ya matse ta sosai cikin jikin shi sannan a hankali ya furta.

"Relaxed please..!"

Jin yanda ya riƙe ta sosai yasa dolenta ta kwantar da kanta amma ba don ta daina jin tsoron da take ji ba.

Shi ma jin ta nutsu ɗin yasa ya ƙara ɗora ɗayan hannunshi ya zagaye ta a ransa kuma yana mamakin abinda yake saka ta jin tsoro haka.

"I'm sorry...."

Still dai ya sake furta mata kamar shi ne wanda ya ƙirƙiro kalmar tun asali.

Ɗagowa ta yi zuciyarta na wani irin bugawa cikin sa'a kuwa idanuwansu suka sarƙe da na juna.

Ji ya yi tamkar an jona shi a shocking tsabar yanda kaifin idanuwanta ya ji sun shige shi ba kaɗan ba.

Maganar da ke ranta tsawon lokaci ta furxo mai kai tsaye ba tare da wani tunani ba ta ce.

"Rayuwarka da kalar ƙaddara ta sun yi hannun riga....ni da kai ba ɗaya ba ne, ni ɗin ba cikakkiyar mace ba ce kamar kowace budurwar da ake kaiwa ɗakin mijinta cikin alfahari ba. Na riga na samu giɓin da ba zai samu cikewa ba har abada. Ban sani ba ko labarin ƙaddara ta ya gama bazuwa a cikin shafukan rayuwarka. Amma ina so in sanar maka cewa na rasa kai na na kuma rasa ƙimar kai wa gidan mijina, na rasa lafiyata domin likita ya tabbatar min ba zan Iya haihuwa ba har abada.... "

Cikin jin wata sabuwar nadama ya yi saurin katse da faɗin.

"Is Okay....please ki daina kukan nan bana so,kowane bawa da irin ƙaddararsa, daga lokacin da kace za ka gujewa ɗan uwanka musulmi akan dalilin wata ƙaddararsa da kai ma baka fi ƙarfin ta ba, to kai ma baka san a ina rayuwa za ta kai ka ba....."

Daga haka ya ƙara janyota jikin shi ya ƙanƙameta yana mai jin yanda wani sabon tausayinta ke daɗa huda shi.

Ƙara matsawa ya yi ya tokare bayansa da bangon gadon sannan ya ƙara gyara mata kwanciyarta a jikin shi ta yanda ba za ta ji ta gaji ba. Ganin kamar veil ɗinta da ke lullube a Jikinta zai takura ta yasa ya saka hannunsa ya janye shi gabaɗaya ya ajiye a gefe.

Kwance take a jikin shi amma kuma tsoron da take ji har yanzu yana nan bai barta ba, sai dai ta ji ta ɗan samu releive kaɗan ganin cewa bai nuna mata komai ba alamar maganar ta ta sosa masa rai. Wata ƙila kuma Zancen ya shige shi nuna mata ne kawai bai yi ba, Allah ne kaɗai ya sani, but a hakan ma ya Kyauta mata domin ya girmama uzurinta wanda tana ganin hakan kamar alfarma ce a gare ta ko don kasancewar shi daren farko a gare ta.

Suna nan a haka wanda ko dogon motsi bai ƙara yi ba sai da ya ji saukar numfashinta ya sauya alamar ta yi bacci sannan ya zame ta a hankali ya mayar da Ita kan gadon sannan ya sauka. Tsaye ya yi a kanta yana kallon fuskarta cike da tausayi tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ya sake zame mata ɗankwalin kanta domin ta ƙara samun sukuni wanda gashin nan a gyare yake tsab domin ya sha gyara, saidai ba wani mai tsayi bane domin can ya hango er wutsiyarsa da aka yi mata parking can ƙasa.

Yana tsaye kawai ya ji ringing ɗin wayarsa Wanda ba kowa ba ce face Maaminsa. Cikin jin wani irin faɗuwar gaba ya ciro wayar. Sai da ya kalli Anaam ɗin sannan ya ɗauki wayar tare da matsawa jikin window ya yi Mata sallama,bayan ya gaishe ta ne daga can ɓangaren ta ce.

"Gabaɗaya yau ban ji ka ba. Where have you been?"

Har yanzu idanunsa akan Anaam ɗin ya ce.

"I have been busy all the day, but Alhamdulillah..."

"Tunda kafi so ka yi ta aiki tamkar agogo ai sai ka ci gaba."

Murmushi ya yi marar sauti sannan ya ce.

"I miss you so much..."

Daga haka ya tsinke kiran tare da harɗe hannayensa a ƙirjinsa tsawon lokaci yana kallonta sannan daga ƙarshe ya kashe mata fitilar ɗakin tare da rage mata gudun ACn ya ja mata ƙofa ya fice zuwa ɗakin sa.

Ita dai Mace ya lura rayuwarta sauƙi ke gare ta wani lokacin. ji yanda ta yi baccinta tamkar ba ta jin wata damuwa. Koda yake an ɗauki kwanaki ana ta zirga-zirga dole akwai gajiya.

Wanka ya shiga wanda bayan ya fito ne ya tsaya ya duba lokaci, ƙarfe ɗaya saura na dare ne, hakan yasa ya tsaya ya yi nafila ya yi addu'o'i sannan ya kwanta akan gado ya yi shiru yana tunani.

Gabaɗaya Kalamanta sun gama Ruguza shi. Sam bai yi mata adalci ba. Su Oga Jud ba ƙaramin cutar da shi suka yi ba.

A haka dai ya yi ta tunani yana juye-juye tsawon lokaci wanda sai daga karshe ya tuna cewar bai ci abinci ba and itama ɗin ba lallai ace ta ci ba. Al'adar kawo wa amarya kaza har ya manta da ita domin ba wannan ne a tunanin sa ba.

Duk yanda bacci yakai a iya sata to bai samu galaba a kansa ba a wannan lokacin, domin a kunnen shi alarm ɗin sallar asuba ya buga tsabar yanda ya zurfafa a tunani da kuma neman mafita.

Bayan ya yi alwala sai da ya biya ta ɗakinta wanda har a lokacin bacci take sannan ya ja ƙofar ya fi ce.

Ita kam sai misalin ƙarfe shida na safe ta farka a hankali,a farko sam ta manta a Ina take ma na ɗan lokaci, sai da ta ɗago ta kalli ɗakin sannan komai ya dawo mata.

Kallon Jikinta ta yi inda ta ga kayanta suna nan a jikinta waɗanda aka kawo ta da su tun Jiya wanda shi ne ya tabbatar mata cewa babu abinda ya yi mata.

Da sauri ta sauko daga gadon ta shiga banɗakin da suka yi alwalar isha daren jiya Ita da su Yaa Na'ima sannan ta yo alwala ta zo ta yi sallar asuba. wayar ta ta shiga dubawa amma bata ganta a ko'ina ba wanda har cikin Jakarta da Na'ima ta ajiye Mata sai da ta duba. Hakan shi ya tabbatar da cewa sun manta da wayar wanda kamar ma tana hannun Mama Hanne.

Komawa ta yi ta zauna akan sallayar abubuwan da suka faru a tsakanin su daren Jiya suka shiga dawo mata ɗaya bayan ɗaya, tabbas duk maganar da ta faɗa masa ba mafarki ba ne da gaske ne kuma tabbas ya amsa mata ba tare da nuna wata damuwa ba, amma kuma yanzu da ta farka ba ta ganshi a ɗakin ba, and har yanzu bai shigo ba, kada ace yana can ya riƙe abin a ransa yana neman yanda zai yi da ita.

Ji ta yi gabaɗaya zuciyarta ta tsinke lokaci ɗaya wanda a daidai lokacin ne ta ji an yi knocking a hankali.

Gabanta na faɗuwa cikin dusasshiyar muryarta ta ce.

"Come in…"

A hankali aka buɗe ƙofar, sai ga shi ya shigo.

Shadda ce a jikin shi wacce babu abin da ke tashi sai wani ƙamshi mai sanyi da daɗaɗa rai. Tabbas shi ɗin mai kyau ne, kuma ya yi mata kyaun da idan ta ce bai burgeta ba ta yi Ƙarya. Suna haɗa ido ta yi saurin sunkuyar da Kanta tare da lumshe idanunta murya can ƙasa ta ce.

"Good morning…"

"Good morning…"

Ya amsa mata shi ma still idonsa a kanta sannan ya samu bakin gadon ta ya zauna ya sake cewa.

"Ya kike Maryam?"

Itama dai kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta ce.

"Alhamdulillah..."

"Miyasa ba ki shirya ba? Kin san cewa Kina da Exams yau ko ba haka ba?"

Da sauri ta ɗago ta kalle shi da mamaki fal a zuciyarta na cewa ta ya ya yasan cewa tana da Exams? Ita dai tasan cewa an kai ƙarshe akan ta bar exams ɗin har zuwa gaba, but how comes yau kwana ɗaya da auren su ya yi mata zancen exams? Wai shi wannan wane irin mutum ne? Wai shi ya ya ɗauki aure ne?

"kina ji Maryam...bai kama ta ki yi missing ɗin exams ɗin ki saboda mun yi aure ba. Tun jiya komai ya kambala and today you have to be there, Barinta zuwa gaba zai iya kawo miki cikas wanda ba zan so hakan ba. Saboda haka ki tashi ki shirya ina jiran ki a mota."

Yana gama faɗar haka ya miƙe ya nufi ƙofa, kallonsa take tana mai jin yanda hawaye suka ciko idonta wanda bata san dalili ba. Ta jima tana nazari sannan daga ƙarshe ta miƙe ta shige toilet ɗin.

Ko a toilet ɗin tana wankan tana kuka har ta gama, mutum sai ka je wanda aka yi masa dole akan auren ta. BHu rarrashi babu komai,. ko yunwar da take ji kaɗai ta ishe ta domin koda ta farka ta ji hanjinta na kuka. A yanzu ta gama yarda cewa duk abinda su Yaa Na'ima suka faɗamata ƙaryane baya existing.

A daren jiya bai damu da cewa ta ci abinci ko bata ci ba, and again yau ma bai ga zancen da zai fara mata da shi ba tsabar wulakanci sai na zuwa wurin exams.

Haka dai ta gama ta fito ta shirya cikin wani Lace wanda yana daga cikin kayanta da su Yaa Amina suka haɗa mata na cewa wai su ne kayanta gabaɗaya na tsawon wata ɗaya da za ta riƙa yin gayu da su tana kashe masa kala.

Kallon sleeping dress ɗinda ke ciki ta yi da sauran kayayyaki sai kawai ta taɓe baki sannan shirya ta saka gyalenta ta fito.

Suna haɗa ido ga mamakinta sai taga ya sakar mata wani kyakkyawan murmushi wanda daga gani ka san har zuciyarsa ya fito.

Kawar da kai ta yi kamar ba ta gani ba sau kuma ta ja tunga ta tsaya. Sai a lokacin ya buɗe mata motar ta shiga sannan shi ma ya shiga. Yana leƙa baya idonsa ya sauka akan fararen ledoji guda biyu manya-manya wanda yasan tabbas babu mai ajiye su idan ba Hamad ba. Tabbas shi da ya san da su da ya ɗauko ya rage yunwar da take damunsa duk da dai ba shi da tabbacin cewa zai iya ci ko a'a.

Ɗagowa ta yi ta kalle shi da mamakin abinda ya hana shi tayar da motar jin tsawon lokaci bai kunna motar ba.

Waya yake pressing na tsawon Mintuna sannan daga ƙarshe ya miƙo mata yana faɗin.

"kin manta da wayanki a gida, and na san kina da buƙatar magana da wani..."

Ya ƙarashe maganar yana mai kai wayar saitin kunnenta.

Jin muryar Yaa Na'ima yasa ta saki wata ajiyar zuciya mai sanyi ta ce.

"Yaa Na'ima...."

Cike da neman tsokana ta ce.

"Amarya ta ango...Allah dai yasa ba'a gogu ƙwarai ba?"

Ji tayi tamkar ta nutse tsabar kunya. Yaa Na'ima fa wallahy wani lokacin ba ta da kai sai na ɗaukan kaya, idan ba shi ba miye na yi mata wannan maganar kuma da wayarsa.

"Hlo Anaam..."

Banza ta yi mata tare da canja akalar maganar ta ce.

"Yaa Na'ima ina Ammie da Abbah? Ashe jiya na manta da wayata, kamar tana hannun Mama Hanne."

"Ke dai bari, sai da muka dawo wai sannan ta ganta a bag ɗinta. But an jima idan zamu zo Insha Allahu zamu kawo miki....ga Ammie.."

Cikin farin ciki ta karɓa suka gaisa sannan aka bawa Yaa Amina. Da haka da haka sai da ta gaisa da su kaf har Yaa Mubarak sannan daga karshe suka yi sallama.

Tunda ta fara wayar har ta kambala bai ɗauke idonsa a kan ta ba, farin cikin da ya ganta a ciki ba ƙaramin daɗi ya bashi ba domin ya lura lokaci ɗaya yanayinta ya sauya.

Tana gamawa ta miƙa mishi wayar a hankali ta ce.

"Thank you..."

Karɓa ya yi bai ce komai ba ya kunna motar a hankali suka fice wanda bai tsaya a ko'ina ba sai cikin makarantar.

Koda suka shiga har sun shiga but amma ba su fara ba. A motar suka tsaya tsawon lokaci wanda shi bai ce ta buɗe ta fita ba haka itama ba ta yi tunanin buɗewar ba. Bayan mintuna kaɗan ya karya shirun da cewa.

"Na sani u didn't sleep well...and I know it that you are nervous about so many things...Ki nutsu sosai ki rubuta abunda ya kamata..."

Ganin kallon da take yi masa yasa ya jinjina mata kansa a hankali ya ce.

"You will do great...i believe in you. Allah ya bada sa'a..."

Har cikin ranta taji daɗin kalamansa wanda sai da yasa ta ɗan murmusa kaɗan tare da jinjina masa kanta ta ce.

"Thank you."

Sai da ya rakata har bakin exam hall ɗin ta shiga sannan ya juya. Suna haɗo ido da Na'ima Hassan ta waro ido alamun mamaki gashi babu daman yin magana.

"Why are you late?"

Ta ji ɗaya daga cikin invigilators ɗin na faɗi.

Waigowa ta yi ta kalle shi sai kuma ta kawar da kai ba tare da tace komai ba, wanda ba invigilatorz din ba, hatta sauran abokanan karatun ta kowa ya tsuro mata ido yana kallonta tare da yin Gulmarta a zuciyar su. Jiya Na'ima Hassan Muhammad ta ce an ɗaura aurenta, but how comes za'a ce tana nan yau kuma?

Ji ta yi gabaɗaya ga gama tsarguwa, su ce suna mamakin zuwanta exams mace nawa na za ta haihu and the next day Kuma ta fita exams, nawa aka yi? But ba za ta yi blaming Kowa ba sai shi da ya ja mata wannan wulakancin. Hakan sai ya sa ta ji ranta ya ƙara Ƙuntata wanda sai da ta ji tamkar ta zubo da ruwan hawaye.

Ganin ba ta da niyyan magana yasa ya yi mata wuri ta zauna wanda ba jimawa bayan an gama shirye-shiryen komai suka fara.

Iyaka 1hour Kawai suka ga mutum ya shigo direct hannunsa ɗauke da basket na kayan abinci yana neman ta. Ɗaya daga cikin invigilatorz ɗin na tambayarsa kai tsaye ya ce matar sa Maryam Mas'ood Galadima ya kawo wa abinci.

Sai a lokacin ta ɗago wanda tun da ya shigo ba ta lura da shi ba sai yanzu. Ai ko student da gulma tuni suka manta cewa wai a exams hall suke suka fara gulmar ganin wai wannan shi ne mijin maryam Mas'ood.

Mamaki ne muraran ya kama ta domin she never expect him. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 44*

Tsayawa ta yi cak tamkar wacce aka dasƙarar idanunta kar akan shi tana mamakinsa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull