Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 35

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 35

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 35: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 35. Ƙara kallon shi ta yi daga sama har ƙasa domin ta tabbatar ko dai…

3,375 words

Ƙara kallon shi ta yi daga sama har ƙasa domin ta tabbatar ko dai shi ne yake yi mata gizau, but shi ɗin ne mutumin da suka fito tare daga gida ba wani ba.

Har yanzu hankalinsa kwance tamkar ba a gaban mutane da yawa yake ba. And the worst of it Yanda kowa ke kallonta yana kallon shi shi ne abinda yafi tsaya mata a rai da ƙara dagula lissafinta.

"Sir...this is exam hall,you can't just walk in like that..."

Jinjina kansa ya yi yana mai kallon matar da ta yi maganar ya ce.

"I'm sorry...but she didn't eat since morning, and I don't want her to be writing exams with empty stomach."

Kalmar tasa ta yi matuƙar tsaya mata a rai wanda yasa ta kasa motsi sai aikin kallonsa ba tare da ta marmaɗa ba. Mamaki take a ranta da cewa shin wannan shi ne mutumin da take ganin bai damu da ita ba tsawon lokaci? Shi ne wanda take tunani da jin cewa ita ɗin kamar ba ta cancanta ba?

Invigilator ɗin ta ɗan kalle shi sannan ta ce.

"OK... but make it fast."

"Thank you Madam.."

Ya ambata yana mai matsawa a hankali ya iso kusa da ita. Cikin sauti marar tashi wanda daga ita sai shi sai kuma people around her kaɗai suke jin shi ya ce.

"Why did you seat here? Bakya tunanin cewa za ki iya takura?"

Ita dai girgiza kai kawai ta yi ba tare da ta yi masa magana ba domin mamakin duniya ya ishe ta.

Students ɗin gaba ɗaya sun kasa mayar da hankali kan jarabawar su tsabar gulma, Kowa sai aikin kallon su yake wanda shi ko kaɗan bai nuna alamar ma ya damu da su ba.

Idonta ne ya sauka akan Friendy ɗinta wacce tun ɗazu gulmarsu ke ciciyar ranta. Sai wani blushing take tana yi mata alama da ido wanda ita dai Anaam ba ta fahimci komai ba.

Ajiye basket ɗin ya yi a gefen desk ɗinta sannan cikin murya mai sanyi ya ce.

"You should eat... even if it's little kinji Ko.?"

Kallon shi kawai take har yanzu wanda a hankali ta saka hannu ta riƙo gudun kada ya zame sai ta karɓa ta ajiye a ƙasa.

"Thank you..."

Ita ce kaɗai kalmar da ta iya furta masa a hankali.

Murmushi ya yi mata wanda ya ƙara saka zuciyarta bugawa da ƙarfi har sai da ta kawar da kanta gefe ba tare da ta shirya ba. A kunnen ta taji yana faɗin.

"I will wait outside...Just take your time."

Daga haka ya juya wanda bata ɗauke Idonta a kanshi ba sai da ya ɓacewa ganinta.

Murmushi ta yi tare da saka hannu ta ɗauki pen ɗinta taci gaba da rubutu wanda a yanzu ta ma daina fahimtar abinda take yi ma gabaɗaya. Idan ta runtse idanun ta ta buɗe shi kawai take gani a ciki. Daman gashi bata san da zancen exam ba kawai ta shigo ne tana iya ƙoƙarinta, and yanzu kuma shigowan da ya yi sai ya ƙara dagule komai wanda sai Allah ne kaɗai zai sa ba za ta yi carry over ɗin ta ba domin wallahy gabaɗaya mind Ɗinta Ba'a nan take ba, it fly some where else.

A waje kuwa...zaune yake cikin motarsa da tab a hannun sa yana yiwa ma'aikatansu online morning lectures kamar yanda ya sa ba. Abinda yasa ya zaɓi hakan shi ne, baya so ya bar aiki da yawa ga shi lokaci sai tafiya yake. A lissafin sa yanzu sun ci 7month da fara wannan training ɗin harda wasu kwanaki wanda Maami da kanta kullum cikin lissafi take. She has no choice ne domin su Abiyh sun fi ƙarfin ta, and what she keep telling him is that, duk wannan contract ɗin ya ƙare har abada ba zai ƙara yin wani makamancin sa ba. To yanzu dole before shekara ɗaya nan ta cika ya kambala musu aikin su kamar yanda ya ɗauki alƙawari tun farko. he's the one that insist, hakan yasa ko kaɗan baya so a samu wata ɓaraka daga wurinsa, hakan yasa yake ta aiki tuƙuru ba dare ba rana, and da wannan ɗin sai yake daɗa ɗaukaka a idanun manyansa domin yasan kansa ya kuma san aikinsa.

Yana cikin aikin tamkar wanda aka mintsila ya ji kalamanta na daren jiya na dawo masa ɗaya bayan ɗaya,musamman da ta ce wai rayuwarsa da ƙaddarar ta sun yi hannu riga. Wannan kalmar ta dake shi sau ba adadi and zai yi duk yanda zai yi yaga cewa ta amshi wannan ƙaddarar ta ta hannu biyu ba tare da jin cewa tana da wani naƙasu ba. Ya yi alƙawarin tsaya mata da kuma cika mata duk wani mafarkinta da zai ƙara mata ƙima da ɗaukaka ta a rayuwa.

Yana nan abun duniya ya ishe shi sai ga kiran Hamad, lumshe idanun sa ya yi sai kuma ya buɗe yana mai answering call ɗin ya ce.

"Hamad..."

Daga can ɓangaren Hamad ɗin ya ce.

"Dinaratu ta faɗamin cewa ba ka jima da karɓo abinci daga wurin ta ba and gani na zo gidanku bakwa nan.."

"My wife is writing exams. Idan ta kambala zamu dawo.."

Abinda ya furta kenan a taƙaice yana mai gyara zamansa tamkar ba shi ba.

Cikin rashin yarda da shi Hamad ya yi shiru na ɗan lokaci yana nazarin maganar sannan daga ƙarshe ya ce.

"Maheer ka daina yaudarar yarinyar mutane, So na gaskiya ɗaya ne a rayuwa, idan ka bari ta fara son ka baka yi mata adalci ba...."

Cike da jin haushi ya katse shi da faɗin.

"Za ka fara ko? Kai da yake a kullum ba ka taɓa hasaso Alkairi..."

"No....i already know what you are up to....Just ka faɗawa yarinyar nan gaskiya ka roƙeta ka ƙyale musu 'ƴar su, gwanda kukan da za su yi yanzu da wanda za su yi bayan an ɗauki dogon lokaci..."

"Daga jiya zuwa yau mi kake tunani nace mata? Ai Komai nake ji dole na ɗaga mata ƙafa for now because she's in so much pain. Few months ne suka rage min a Nigeria ɗin and kafin nan in sha Allahu komai zai ƙare, bana so mu rabu tana mai jin haushi na."

Daga haka ya katse kiran yana mai ƙara jin takaicin irin yanda Hamad ya ɗauke shi a rayuwar nan. Ta ya zai fito ya furta mata wata magana daga jiya zuwa yau, it sound very crazy ya fuskance ta da a wannan lokacin,hakan ba zai ma faru ba. He will wait for the right time but yanzu sam bai kyautu ba.

And idan ta yi kuka a yanzu mi yake da shi da zai faɗawa Oga Nameer? Ya faɗa masa sau ba adadi cewa Akwai abokinsa da yake sonta but sai ya fi jin nutsuwa idan shi ne ya aure ta. To taya yake tunanin fuskantarta daga jiya zuwa yau? Wai an ya ma Hamad yana ƙaunar sa kuwa a rayuwar nan?

*******

Tun a daren jiya Abbah ke ta zirga-zirga da kuma ji da baƙin sa wanda bai samu damar zaunawa ba sai yau.

A hanya Ammie ta haɗu da Umma janye da hannun Rabi'a wacce fitowar ta kenan daga sashen Alhajin bayan ta kai mai breakfast domin har yanxu akwai taron mutanen da bai zai iya saukowa yaci abinci a ƙasa ba.

Kallonsu ta yi sannan ta ce.

"Hajiya Umma ina za ki haka?"

Wani kallon ta yi mata sannan ta ce.

"Wurin Alhaji Mas'ood za ni domin ina da magana da shi."

"Kin sa an yi masa magana ne kafin ki shiga? Ina nufin yasan da zuwan ki?"

Taɓe baki ta yi ta ce.

"Tun jiya dai na sa an sanar mai bai dawo ba ne da wuri, shiyasa zan shiga tun mutane basu taru ba..."

Wani kallon mamaki Ammie ta bi ta da shi domin ta lura kamar ma Umma ta haukace ne a wannan karon. Ɗakin mijinta za ta shiga a wannan lokacin? Ba Yayarsa ba ba uwar sa ba ba ƙanwar sa ba...

" Matsa min na wuce..."

"Wai Hajiya Umma ko dai kin fara shaye-shaye ne? Kodai wai kin manta wurin mijinki kike son zuwa kika yi ɓatan hanya za ki shiga wurin mijina? Mas'ood ne fa a nan ba Salisu ba..."

Ta ƙarashe maganar tana mai nuna mata ƙofar shiga sashensa nasa da yatsa wanda tana kan maganar sai ga Jamila ta fito daga ciki.

Kasaƙe ta yi tana kallon Jamilar har ta ƙara so sannan ta sake kallon Hajiya Nasmah ta ce.

"Ita wannan ɗin da ta fito daga ciki fa?"

"Ita ɗin ƙanwar sa ce hajiya Umma, ke kuma matar yayansa ce, ki jira shi a ƙasa koma miye idan ya fito sai ki yi maganar da shi....."

Fuuuu! Haka ta janyo hannun Rabi'a ɗin suka sauko sannan ta ja tunga tsakiyar parlourn ƙasa ɗin ta shiga zage-zage tana habaice-habaice wai auren asiri ne aka yi wa Maheer ɗin da Anaam, kuma ko auren Na'ima da Haisam shi ma auren asiri ne.

Cike da baƙin ciki Mummy Jamila ta kalle ta ta ce.

"Ni dai Umma ina baki shawara ki daina ɗorawa kan ki wahala. Hajiya Nasmah ta wuce ki har gaban abada ba za ki kamo ta ba..."

Tas! Haka ta wanke mata fuska da wani irin zazzafan marin da sai da ta dafe kunce. Duk abunda suke en uwan Ammien na ji su Mama Hanne wanda sai da ta haɗasu da Allah akan kada ma su fito ballantana su tanka mata har ta ji daɗin ci gaba da tujara.

Na'ima da fitowar ta kenan taga abin da yake faruwa ta ɗauki wayarta ta kira Yayanta Naseer ta ce mishi dan Allah idan Babansu bai wuce ba ya taimaka ya zo ya saka Umma gaba su wuce gida.

Alhaji Salisu wanda har ya gama shiri tare da Naseer za su koma sai Naseer ɗin ya shiga bashi bayanin da Na'ima ta yi mai, nan take sai ga shi ya bayyana cikin gidan cike da tsananin fushi ya kalle ta ya ce.

"Hajiya umma lafiya kike tayarwa da mutane hankali?"

"Ina fa lafiya Nasmah da Jamila na neman su yi min rashin kunya..."

"Hajiya Umma koda kika shigo gidana kin iske Hajiya Nasmah na auren ƙanina, ita ɗin ba tsarar ki ba ce, koda kika shigo gidana kin tarar da ita cikin gidan Mas'ood da yaranta guda biyu. A can da ina ɗauke kai na ne saboda wasu dalilai..."

"A haka za ka yi ta ɗauke kanka har abada tunda zuciyar ka ta riga da ta mutu, kullum kana nan daga kai har 'ya' yan ka sai abinda ƙaninka ya ce..."

"Umma!!"

Ya ambata cikin tsananin mamaki.

"Yanzu ni kike faɗawa irin wannan magana?"

"To Alhaji ta ya ba zan faɗa maka ba ina gani an mayar min da 'ya banza marar galihu a cikin gida. Da abinda suka riƙa yi mata ai da cewa ya yi ba za ta zaunar masa a gida ba sai ya fiyemin daɗin rai bisa ga abinda suka yi min. Sai da ta fara soyayya da mutum sannan za'a kewayo tsabar zalunci a ɗauki wata a bashi! Miye Maryam ɗin ta fi ta da shi da har za'a yi mata wannan... "

Ba Ammie ba, hatta Su Yaa Mubarak sai da suka kusa sumewa tsabar mamaki da al'ajabi. Daman ashe duk fitinar da take nema abinda suke ƙullawa kenan? Lallai yau sun ƙarawa tabbatarwa cewa Umma ba ta da hankali.

Daga can gefen da suke tsaye Mubarak ya kalli Mukarram wanda ke riƙe da hannun Mufid ya ce.

"Gaskiya na yarda da zancen Na'ima da ta ce matar nan tana da motsin ƙwaƙwalwa..."

Mukarram ɗin na murmushi ya ce.

"Ni wallahy da an ji shawara ta kaima da na isa da kai da na ce a aura maka Rabi'a ko Allah zai sa matar nan ta rage wannan ƙiyayya da takun saƙar da take da Hajiya.."

Dariya Mubarak ɗin ya fashe da ita wanda gabaɗaya lokaci ɗaya suka ja hankalin mutanen da ke wurin sannan ya girgiza kansa ya ce.

" Ai wallahy tun cikin dare za ta saka mini fuel ko ta sokeni da wuƙa domin bata da mutunci ba ta da kirki ko kaɗan....ranar fa haka muka tarar da Ita Rabi'a tana ƙaƙabawa Mijin Anaam ɗin sharri ƙiri-ƙiri ko kunya.."

"Allah ubangiji yasa Baba Salisu ya kwashe su duka ya wuce da su tunda shi Alhaji bai iya ɗaukar action ɗinda ya da ce... Don Allah ma yasa Baba Salisun ba irin halinta ne da shi ba wallahy da yanzu ta jima da farraƙa mana zumuncinmu."

"Hmm! Shiyasa Mahaifiyarsu Na'ima har abada ba na barin yabonta, mutuniyar kirki.."

"Daman ire-irensu mutanen kirki ba su cika daɗewa a duniyar ba. Allah dai yasa mu dace."

Shi ma dai Baba Salisu cike da kunyar wannan abun da ta yi ya kalle ta ya ce.

"Ki wuce mu tafi gida Umma...."

"Amma dai Alhaji..."

Saurin katse ta ya yi da faɗin.

"Wallahy tallahy yau ɗin nan sai kin bar gidan nan mun tafi, idan kuma ba ki biyo ni to ina tabbatar miki a bakin auren ki..."

Wata irin guɗa Mummy Jamila ta rangaɗa sannan tace.

"Ni Wallahy tallahy dama sakin nan ya tabbata a kanki wallahy da sai na fi kowa farin ciki. Kinga idan aka koma gidan mai dattin hula sai a gane gidan ɗan uwana da ake rainawa yafi can sau dubu. Banda rashin godiyar Allah da baƙin kishi na mugun abu, ke da ita ba miji ɗaya ba amma ki ɗauki wahala ki ɗaurawa kan ki ki hana kanki zaman lafiya. Kullum cikin kitsa mugun nufi ina za ki ji daɗin zaman duniya. Wallahy ke da farin ciki matuƙar ba canja rayuwarki kika yi ba to kun yi hannun riga har abada. Kin iya mugun abu kuma kin koyar da 'ya' ya ina amfanin wannan abu..."

"Ke Jamila?"

Suka ji Alhaji Mas'ood ya daka mata wata uwar tsawa yayin da yake saukowa zuwa ƙasa.

"Ashe haka kika dawo ban sani ba! Matar yayanki kike gaggayawa irin waɗan nan maganganun?..."

"To amma Yay..."

"Don Allah ki saurara min Jamila! I'm very disappointed on you..."

Wani irin kuka ne Hajiya Umma ta fashe da shi tana mai girgiza kai alamar ita ga ta an ci mata mutunci.

Kallon shi Alhaji Salisu ya yi ya ce.

"Akan me za ka shiga kare ta Alhaji Mas'ood? Shin kana da labarin cewa haka kawai ta ɗaga hannu ta wanka mata mari? Umma ba ta son zaman lafiya kafi kowa sanin hakan, duk tsawon shekarun nan ba ta da aiki kullum sai ƙulla sharrance-sharrance da makirce-markice sai ka ce wata ƙaramar yarinya. Abokiyar zaman nan yanzu itama ba ta raye to miye abin baƙin ciki da neman fitina a nan?"

" To Alhaji Ka san sha'anin iyali da tunanin mata... "

" Ba wani tunanin mata Alhaji Mas'ood. Sharrin ta da ƙulle-ƙullenta yawa ne da su. Idan banda neman fitina keda kika zo jiya taya kika san cewa wai yaron nan Rabi'a yake so? A ina kika ji, miye shaidarki? Kawai in banda neman haɗa en uwa faɗa ke babu abinda kika iya? Duk aka yi hidima indai kina nan to ba za'a taɓa kwashewa dake lafiya ba ina amfanin hakan? To Wallahy tallahy wannan ɗin ya zama shi ne na ƙarshe idan ba haka ba kuma zamanki a gidana zai yanke na har abada. "

Shiru ta yi tamkar ruwa sun cinyeta tana mai zubo da ruwan hawaye. Ta ji tsoro sosai domin tunda take bai taɓa yi mata tijara da buɗe ido irin na yau ba. Tabbas zai iya aikatawa tunda har ya iya ci mata mutunci a cikin wannan uban taron da ya tara,ko sakin da ya taɓa yi mata bai ci mata mutunci kamar yau ba.

" Wuce ki ɗauko kayanki, kuma har ke Rabi'a wallahy sai kin bar gidan nan a yau kin ji na rantse..."

Jin furucinsa na ƙarshe yasa Alhaji Mas'ood ɗin ya ce.

"A'a Alhaji..Rabi'a karatu take, Kaga an zuba kuɗi an yi registeration..."

"Idan kuɗin ka ke ji da ka biya mata ka barni in biyaka, amma wallahy tallahy zamanta ya ƙare a gidan nan..karatu ai ba dole sai ta yi shi ba, na cire ta karatu daga yau kuma sai in ga wanda ya isa.."

Cike da jin farin cikin kalamansa Mukarram ya jinjina kansa ya ce.

" Ai kuma Baba tunda ka furta magana ta ƙare. Babu kuma wanda ya isa ya ja da maganarka. Allah ubangiji ya sauke ku lafiya. Ka yi haƙuri don Allah. "

Rabi'a na wani irin kuka ta wuce fuuu ta shige ɗakinta zuciyarta cike da baƙin ciki. Tana haɗa kayan tana kuka sai ga Umma ta shigo ita da Shema'u.

" To ai daɗa! Sai haƙuri... "

Waigowa ta yi tamkar tana jiranta ta ce.

" Sai haƙurin me Umma? Ai duk kece kika kaini ga wannan, tun daren jiya nace miki tunda haka ta faru ni ina da hanya ta amma kika kafe wai ke kinsan mafita. Yanzu ga shi kin ɓata goma biyar bata gyaru ba. Ina zaune hankalina kwance ina jin daɗin rayuwa ta kin zo kin kofsa mini...ni wllhy kawai an cuce ni an mini baƙin ciki,.. "

Daga haka ta sake fashewa da kuka tana tuna irin daular da za ta bari ta koma gida, ba za ta ce babu jindaɗi a gidan Babanta ba amma dai gidan Abbah shi ne maƙura. Nan fa sanadin Anaam har driver take da na kanta, duk inda za ta tafi yana nan sai abinda ta ce, shopping, saloon, ragargazar kuɗi babu irin wanda ba ta yi kuma babu wanda ya damu da ita, amma kuma dare ɗaya rana tsaka za'a katse mata wannan jin daɗin gaskiya ba'a yi mata adalci ba.

Ta jima tsawon lokaci tana shiriritar koke-koke sannan daga karshe ta fito da himilin kaya tana ta ci gaba da rusa kuka. Gabaɗaya gidan ya kama da wutar gulmarsu ita da Umma wanda cike da kunya suka fito suka wuce.

Bayan sun tabbatar sun wuce Hajiya Nafisa ta kalli Ammie ta ce.

"Aunty Nasmah rayuwarki tana burgeni a lokuta da dama. Wallahi wanda Allah yake yi wa faɗa baya faɗa. Ki ji shegiyar mata tijararriya..."

Tsaki Mama Hanne ta ja ta ce.

"Na tsani Umma, na tsane ta ji nake idan na ganta tamkar na shaƙeta tun Case ɗin Binta da aka taɓa yi. Sannan a yanxu Ƙarin babban baƙin cikinta shi ne baro ta da Nasmah ta yi ta dawo nan da zama, da kuma ganin an aurar da Na'ima ga Haisam wanda sun ɗauka matsiyaci ne. Sannan uwa Uba yanzu wannan ɗin da Maryam ta Aura shi ne ya ƙara haukata su.."

Girgixa kai Hajiya Nasmah ta yi ta ce.

" Hmmm! Allah dai ya kyauta kawai. Duniyar ce yanzu ta zama abinda ta zama. Kuje ku duba sauran kayan can na Anaam idan akwai abinda za ku ƙara mata ku ƙara mata, idan babu kuma sai a saka su Habu su mayar da su a rufe.

*******

Ya jima a motar yana jiranta sannan daga ƙarshe ya hango fitowanta ita da Friendy.

Fitowa ya yi yana Kallonsu har suka ƙaraso sannan Na'ima ta ce.

"Ina kwana..."

"Lafiya Lau, ya Exams ɗin?"

"Alhamdulillah!"

"Mun gode da hidima, ga shi ko gajiya ba'a ɗebe ba kuma an dawo exams..."

Tana murmushi ta ce.

"Ah ba komai wallahy, Allah dai ya bada zaman lafiya da zuriya dayyaba amin."

Basket ɗinda ta riƙo musu ya karɓa tare da buɗe motar ya saka sannan ya buɗe mata ya yi mata alama da ta shiga. Ba ita ba hatta Friendy da wasu daga cikin mutanen da hankalinsu ke wurin ya gama burgesu. Duk gulmar da wasu ke ta yi tun da aka kambala exams ɗin tana jin su wanda a kunnenta ta ji wasu da kai tsaye suke kushe ta suna yaba shi suna faɗin Sam babu inda suka da ce da shi da ita. Daman mutanen duniya baka iya musu. Mutane ba su da haɗi da kai amma suna da gadon maganarka.

Tana shiga ta yi wa Friendy hannu tana ta murmushi daga nan ya tayar suka wuce.

"How was the exam?"

Abunda ta ji ya ambata kenan kaman daga sama, hakan yasa ta ɗago ta kalle shi sai taga idon shi yana kan titi hakan yasa ta amsa da.

"Alhamdulillah!"

"Did you eat well?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull