Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 36

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 36

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 36: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 36. Sake kallon shi ta yi wanda cike da ƙwarewa yake murza starrying…

3,365 words

Sake kallon shi ta yi wanda cike da ƙwarewa yake murza starrying motar tare da wani bajewa tamkar wani basarake. Jin ba ta amsa wannan ɗin ba yasa ya ɗan wai go kaɗan ya kalle ta. Suna haɗa ido ta yi murmushi wanda ya bayyanar da kyawawan fararen haƙoranta ta ce.

"Yes..thank you."

"I'm sorry about yesterday... I should have asked if you ate."

"Is okay..."

ta furta a hankali tana mai jin yanda wani abu da ba za ta ce ko minene ba yana mintsilar zuciyarta a hankali. Daga fitowarsu gida zuwa yanzu taji wani sauyin da ba ta taɓa tunani ba ko kuma yin mafarkinsa.

Kalmar Aunty Aysha ta tuna wanda ta ce mata wasu mazan ba za ki iya yin karan tsaye lokaci ɗaya ki ce za ki fassara su ba, time suke so da kuma iya zama da su. Haƙuri da bin dokokin su shi ne matakin farko na cin nasarar wata zamantakewa duk da dai wasu mazan ba ka iya musu ba. Koda yake a kwana ɗaya mi ma za ta ce ta ƙarar ballantana ta yi saurin yanke hukunci?

"Ahm....kina da wani exam ɗin gobe ne?"

Girgixa kai ta yi alamar a'a sannan ta ce.

"Till Monday..."

"Alright. Allah ya nuna mana."

"Amin..."

"Dole za ki riƙa karatu fa. I asked Mubarak to bring your reading materials so that you won't be left out."

Shiru ta yi zuciyarta na bugawa a hankali abubuwa masu yawa na ta zuwa cikin tunaninta, wasu ta yarda da su wasu kuma ta watsar a haka har suka isa gida babu wanda ya ƙara yin wata magana.

Suna shiga ta wuce ɗakinta ta cire kayan jikinta ta shige ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wata simple Atamfa wacce aka yi wa doguwar riga plane ta saka hijab ta yi sallan Zuhr.

Tun tana kan sallaya take jiyo muryoyi kamar na mutanen gidansu, tana kambalawa ta fito ta taradda su Yaa Na'ima da su Sa'adah, Yaa Amina da kuma Aunty Dinaratu, sai yaran su da suka zo da su gabaɗaya.

Farouk, da Arif, Arifa, Fatima, da kuma mufida su ne 'yan matasa a cikin su bisa ga su Feruz.

Cikin wani irin farin ciki ta daka tsalle ta rungume Yaa Amina tana ta dariya tana musu sannu da zuwa.

Ɗaukar little maryam ta yi a ta rungumeta tana faɗin.

"Ya akayi kuka san ina nan? Ban ji ma da shigowa ba fa."

Na'ima ta ce.

"Mijinki ya faɗa mana cewa ya kai ki wurin exams, idan kika dawo zai sanar mana."

"Aunty Anaamee Amarya..."

Kallon Farouk ɗin ta yi tare da ɗan hararensa ta ce.

"Da zuwanka za mu fara ko?"

Dariya ya yi ya ce.

"No. I'm sorry,zamu je China next week tare da Grandpa...it will take you long to see me again.."

"Da gaske kake Abbah zai tafi da kai?"

"Allah kuwa, tambayi Mummy ki ji..."

Kallon Yaa Aminar ta yi ta ce.

"Yaa Amina kinsan fa Farouk ya gama rainani saboda yanzu ya ga ya kusa kamo tsayina saura kaɗan."

"Da shi zai tafi, daga nan zai fara school..."

"But na san cewa bai yi waec ba?"

"To kin san shi da shegen naci kamar ubansa Mubarak, da har Baban ya so ya yi faɗa Abbah ya ce ya ƙyale shi ai alƙawari ne a tsakanin su."

"To, ka ji fa al'amarin kaka da jika. Allah ya taimaka ya bada sa'a.."

Kallon su Arif ta yi tana yi musu magana ɗaya bayan ɗaya suna ba ta amsa sannan ta kalli Na'ima ta ce.

"Wai Yaa Na'ima shikenan Rabi'a ba za ta iya canja halinta ba? Yanzu da gaske ba za ta zo inda nake ba?"

Wata dariyar mugunta ce Na'ima ta sheƙe da ita sannan ta ce.

"Ai wallahy da ace yau kina gidan nan na tabbatar sai kin zuba ruwa ƙasa kin sha..."

"Miye ya faru?"

Ta faɗa tana mai zaro ido sosai domin a tunaninta wani abu ne ya faru.

"Baba na jin labarin Umma ta zo tana zuba rashin arziki ya shigo ya ci musu mutunci ya yi mata tas! Sannan kinsan tun wani saki da ya taɓa yi mata ta daɗe wanda sai da Abbah ya je ya dawo da ita tun lokacin take shakkarsa idan ta ji yayi batun saki."

Yaa Amina ta ce.

" Ai wallahy yau Baba ba ƙaramin burgeni ya yi ba, wallahy ya yi daidai. Shaiɗanun mutane kawai, a gabana fa ranar take faɗawa Ammie cewa wai Maheer yana yi wa Anaam rashin ɗa'a and kin san halin Ammie da saurin ɗaukan abu. Sai da Mubarak ya yi saurin kwatseta sannan ko kunya ta Kama hanya ta fita."

Aunty Aysha ta ce.

" Ai kam dai umma ta ɓatawa Rabi'a rayuwa,Allah ya kyauta yasa su gane gaskiya. Yau haukan da suka fito da shi ai ba ya ma magantuwa, Allah ya sawaƙa... "

Hannun Anaam Aunty Dinaratu ta ja suka shige cikin wani katafaren kitchen wanda yake shi ne. Ya haɗu ta ko'ina, ga kayan zamanin nan komai gwanin burgewa.

Murmushi ta yi tana mai ƙarewa kowane lungu da saƙo kallo. She liked it and she also love it. Yanda aka tsara shi ya burgeta.

Ta fi minti goma tana kalle-kalle kamar wata baƙuwa sannan daga ƙarshe Dina ta dawo wanda daman Waya ce aka kira ta.

"Anaam ya dai? Hope babu wata matsala?"

Murmushi ta yi mata sannan ta jinjina kanta ta ce.

"Babu matsala Aunty Dina, and ni tun a jiyan na faɗa masa komai..."

Zaro ido ta yi ta ce.

"What??"

Turo baki tayi tana magana can ƙasa ta ce.

"Nikam Yaa Dina na faɗa masa gaskiya wallahy..."

"Oh God!! To miye yace miki? Ya nuna miki wani abu? Ya nuna rashin jin dadi koda a fuska ne?"

"A'a! Cewa ya yi ba komai, kuma duk wanda yace ya guji ɗan uwansa musulmi akan wata ƙaddara to shi miye yasan zai same shi a gaba, saboda haka kada na damu...daga nan ya jani a jikinsa har na yi bacci...."

Wata sassanyar ajiyar zuciya ta saki wanda ya haifar mata da wata irin nutsuwa tana mai furta Alhamdulillah a can ƙasan Zuciyarta. Jiya gabaɗaya ko baccin kirki wallahy ba ta samu ta yi ba. Idan ta juya sau goma su biyun nan sai sun zo mata a rai. Da tsananin tsoro ta kwana yayin da cikinta ke ɗure da ruwa gudun kada ya laluba ya ji wata matsala ya birki ce. But to her biggest surprise sai ga shi ya kira ta wai tasa a haɗa musu breakfast zai zo ya karɓa. Da hakan sai ta ji hankalinta ya kwanta and yanzu jin hakan sai ta ji ta ƙara samun nutsuwa.

"Yaa Dina ya naga duk kin yi wani iri?"

Numfashi ta ja ta sauke a hankali sannan ta riƙe hannun ta ta ce.

"Anaam ni ce jagorar komai da ni da mijina domin ta ɓangarena ya fito, bana fata ko kuma burin wata ɓaraka da za ta sa ayi kuka da ni ko kuma ɗan uwanki Nameer. Don Allah ki yi Haƙuri ki riƙe sirrin ki, mijin ki shi ne kaɗai fargabar ki, bayan shi babu wani wanda zai dame ki, saboda haka ki kwantar da hankalinki ku zauna lafiya."

Jinjina kanta ta yi ta ce.

" In sha Allahu Yaa Dina. Na gode sosai."

"Ba komai, Allah ya baku zaman Lafiya amin. Muje ki ci abinci gashi nan na kawo muku."

Daga haka suka fito suka ci gaba da fira wanda ba su koma gida ba sai bayan magariba.

Tana cikin gabatar da sallahr Isha ta ji ya shigo, tun da ya kawo ta ba ta ƙara sanya shi a idon ta ba sai yanzu.

Yanzun ma koda ta kambala har ya ajiye mata basket ya wuce wanda bata ƙara ganin shi ba sai da gari ya waye.

Tun tana saka rai da tsammanin ganin shi, bai dawo ba, don ma sun jima suna waya da Friendy har bacci ya sace ta bai shigo ba.

Da wani black 3quater ya shigo ɗakin da white shirt misalin ƙarfe tara na safe.

Kallon shi ta yi sai kuma ta kawar da kai gefe ta ce.

"Good morning..."

Shiru ya yi yana observing ɗinta na en daƙiƙu sannan daga baya ya ce.

"How was your night?"

Wani kallon ta yi mishi a kaikaice a ranta ta ce ɗan rainin wayau ban sani ba, ni zaka bari ina jin tsoro, atleast ko ya ya ne ka nuna min alamar kana cikin gidan domin in ji sanyi. Kamar ko yasan abin da yake ranta ganin yanayin fuskar ta ya ce.

" I'm sorry...jiya ban dawo da wuri ba ne..."

Shi dai wannan kalmar ta ban haƙuri wato ba ta mishi wuya ko kaɗan...

"Please ki zo, I want show you something..."

Daga haka ya juya ya fita wanda ya kusa 15mnt sannan ta fito ta same a bakin Door Wanda hakan ya bata mamaki. She thought ya ji ma a ƙasa wurin wata sabgar, ashe yana nan bakin ƙofar yana jiranta. And still kuma da murmushi har yanzu fuskarsa ba ta sauya ko ya nuna alamun fushi ba.

Wata ƙofa ya buɗe a kusa da ɗakinta suka shiga. Ya Allah! Wato wani ɗaki ne na musamman mai ɗauke da gado, set na kujeru da kuma study area Wanda aka ƙawata cikin best colour ɗinta.

Kan table ɗin wasu kalolin fitilu ne da kuma Laptop da kayan rubutu, sai kuma bookshelves dake gefe wacce aka cika da textbooks da kayan amfani gasu nan, har wata single closest ta gani ta tura a hankali sai ga kayan lauyoyi a ciki komai da komai.

Wani irin kallo ta bishi da shi na al'ajabi da ban mamaki.

Jinjina kai ya yi sannan ya ce.

"Aikin da muka yi kenan daga daren jiya zuwa yau. We need to fulfil that dream of yours together. I will be the luckiest person in the world the day you become what you want to become. Ko bamu rayu tsawon wannan lokacin a tare ba, I will be happy a duk inda nake...ki daure ki yi karatu, ɗan lokaci ne ƙalilan wanda matuƙar akwai rai da lafiya, kamar gobe ne."

Hawayen da ta ji kamar za su zubo ta yi saurin dannewa, cikin farin cikin da ba ta san ma yanda za ta misalta shi ba ta ce.

"Thank you so much. Allah ubangiji ya saka maka da mafificin alheri..."

Harɗe hannayensa ya yi a ƙirjinsa ya jingina bayansa a bangon ɗakin yana kallonta yanda duk ta wani susuce.

Ita kuma sai wani kallon shi take tana jin komai sabo a ranta. A cikin wannan aikin da yace ya kwana yana yi mata da kuma kalamansa na yanzu ta rasa wanne ma yafi mata daɗi a rai. Wato muhimmancinta har ya kai haka kenan. Gabaɗaya ta nemi fushin da ta ɗauka da shi ta rasa.

Suna tsaye babu wanda ya yi wa wani magana ya ji wayarsa ta hau vibrating a hankali. Yana cirowa yaga sunan Maami.

Ƙara kallon Anaam ɗin ya yi wacce har yanzu shi take kallo sai ya ji gabaɗaya ma ya ruɗe.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 45*

Alhamdulillah! Ina miƙa saƙon godiyata ta musamman ga Gidauniyar Arewa Talent wacce ta kasance ginshiƙi wurin ganin cigaban marubuta,tabbas wannan ƙungiya ta kasance wani haske kuma jigo ga matasa masu baiwa, da haɓaka tasirinsu a wurin al'umma,Ina matuƙar godiya da wannan karammawa tare da fatan Allah Ya saka muku da alkhairi, Ya ƙara ɗaukaka gidauniyar, Ya sa ku zama sanadiyyar cigaban al'ummar Arewa da ma Najeriya baki ɗaya. Allah Ya albarkaci wannan aiki, Ya sa ya zama mai anfani ga al'umma, Jagora Shugaba Muhammad mun gode Allah ya ƙara girma.

****Wayar ya ɗaga a hankali trying to avoid her gaze ya ce.

"Maami..."

Muryartar a ɗan ƙagauce daga can ɓangaren ta ce.

"Maheer wai lafiyanka? I have been calling since amma kuma ba response ɗin ka.."

Hanyar waje ya nufata a gaggauce jin sautin na ta kamar da alamun faɗa yace.

"Na shiga wani abu ne Maami...but I'm sorry. Na ji kaman ranki ya ɓaci."

"No...not all, ai nasan duk abinda kake mai muhimmanci ne. Abeeh ne ya kira ni asking me wai yaushe za ka zo?"

"Wani abu ya faru ne Maami?"

"No ba abinda ya faru, I told you cewa ya kwanta asibiti for 5days and kai ma ka ƙi ka nutsu kwanan nan ballantana in ji yaushe za ka zo ka gansa, shi ne ya kira ni domin bai ganka ka zo ba and kuma ba ka kira sa ba."

"please Maami tell him that I'm sorry, I'm a bit occupied now...but Idan na samu time zuwa an jima zan kira shi in sha Allah. Allah ya bashi lafiya "

"Amin...kada ka manta please..."

"Okay Maami..."

Daga haka ya katse wayar sannan ya mayar da ita cikin aljihunsa.

Sake dawowa ɗakin ya yi wanda ya tarar da ita tana duba wani textbook ya yi mata murmushi ya ce.

"You like it?"

Jinjina kai ta yi a hankali tana mai yin murmushi ta ce.

"Thank you so much..."

Wani irin natsattsen murmushi ya yi wanda ya ƙara sanyata jin wani irin abu mai sanyi na daɗa ratsa zuciyarta wanda ba za ta iya fassara ma abinda take ji ba.

Kasa cewa komai ta yi, zuciyarta na bugawa da ƙarfi tamkar wacce aka ritsa a ragar so tana mai ƙara nutsa kallonta cikin textbook ɗin domin kaucewa kallonsa.

"please let's go and eat, kada ki zauna da yunwa kaman jiya."

Komai ba ta ce ba har suka sauko ƙasa inda taga abinci an girke wanda duk a tunanin ta shi ne wata ƙila ya dafa da kansa. But sai dai kuma daga yanayin zubin abincin da yanda aka tsara shi sai ya yi mata kama da na eatry.

Yana ganin ta ɗauki spoon ya yi excusing kansa ya koma ciki, ba jimawa ya fito cikin shigar jeans and t-shirt da Kuma P-cap wacce ta ƙara fito da shi sannan uwa uba ga sun glasses ɗinda ke ƙara masa kyau wanda ya yi sanadiyyar saka zuciyarta bugawa.

"I will be out for some hours....but zan dawo ba jimawa."

Jinjina kai ta yi tare da haɗiye sauran Tea ɗinda ta ji ya maƙale mata a maƙoshi tun bayan fitowarsa. Ji tayi gabaɗaya kalmomin bakinta sun tsaya akan yanda zuciyarta ta shiga racing tana neman ta zauce.

Yana juyawa ya yi taku ɗaya biyu sai kuma ya tsaya cak sannan ya juyo ya kira sunanta a hankali wanda hakan ya sake hadda sa mata sabon bugun zuciya ya ce.

"Maryam..."

"Na'am..."

Ta amsa tana kallon cikin idanun sa waɗanda ba za ta iya hangowa ba a halin yanzu, sai dai kuma tana iya jiyo kaifinsu ga dukkan ilahirin jikinta.

"Take care...If you need anything...just call me..."

Murmushi ta yi a hankali tana mai ƙara jin farin ciki ta jinjina masa kanta ta ce.

"Okay..."

Daga haka ya fita ya bar ta tana kallon ƙofar har sai da ya ɓacewa ganinta.

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta miƙe da gudu ta koma kan kujera ta kwanta tana ta wani blushing tana ƙara jin yanda zuciyarta ke wani irin fisga. Lumshe idanunta ta yi a karo na barkatai tana tambayar kanta cewa.

"is this how it feels? Da gaske a kwana ɗaya na fara jin wani abu? Shin hakan ne ga dukkan matan duniya ko kuma ni ka ɗai ce?"

Ringing ɗin Wayanta da ta ji shi ne abinda ya farkar da ita daga duniyar tunanin da ta Nutsa mai cike da ban al'ajabi da kuma ban mamaki.

Tasowa ta yi ta ɗaga kiran Friendy wacce tace mata suna bakin gate ita da su Hafsa en class ɗin su.

A tare suka wuni da su Friendy ɗin sannan da su Yaa Na'ima wacce suka zo ita da su Mummy Nafi da su farouk wanda kamar wasa sai gashi har suka bar gidan bai dawo ba sai misalin eight na dare.

Yanzu kam tsintar kanta ta yi da rashin jin haushinsa wanda bata sani ba ko don ta wuni da su Yaa Na'ima ne oho!.

Tana ganin shi a parlour ta kalle shi ta ce.

"Welcome..."

Jinjina kai ya yi ya ce.

"Thank you. Na ga kina da baƙi ne, hakan yasa ban dawo ba."

Daga haka ya wuce riƙe da wata bag wacce ba za ta iya fassara abinda yake cikinta ba.

Cikin ta koma itama ta yi sallah sannan ta janyo wayar ta tana dubawa inda ta shashace wurin charting da Friendy ɗinta.

Har ta gama duk abinda za ta yi ta kwanta bai ƙara tako ɗakin ba. Mamaki take domin dai kenan inda ba ta ci abinci tare da su Yaa Na'ima ba da shikenan da yunwa za ta kwana.

Washegari da wuri ta shirya ta fito inda ta tarar da abin karinta ta zauna taci sannan sai ga shi ya fito ya ce ta tashi su tafi.

Har bakin Exam hall ya ajiye ta sannan ya kalle ta ya ce.

"Allah ya bada sa'a."

A hankali ta furta.

"Amin. Thank you."

Da kanshi ya fito ya buɗe mata ta fito wanda sai da ya tabbatar ta shiga Hall ɗin sannan ya juya ya koma.

Bayan sun kambala sun fito ta nufi motar amma kuma ga mamakinta sai ta tarar da Anasi yana zaune yana jiranta.

"Anasi ina mijina?"

Ta furta mai cike da mamakin ganinsa.

Ɗan rusunawa ya yi kaɗan alamar girmamawa ya ce.

"Sannu da fitowa Hajiya...daman ɗazu ne ya kirani ya ce na zo na mayar dake gida zai ɗan tafi wani uzuri."

Jinjina kanta ta yi sannan daga haka ya buɗe motar ta shiga ta zauna a backseat sannan ya ja suka tafi.

Ta ji daɗin ganin Anasi domin drivernta ne na amana.

******

Rabi'a dai tunda suka koma Gusau ba ta da wani aikin da ya wuce mata kuka da danasanin abinda ta aikata. A yanzu ta gane cewar duk wanda bai godewa Allah ba tabbas zai gani a ƙwaryar shan sa.

Gabaɗaya lokaci guda rayuwarta da ta fara cikin jindaɗi tare da kafe manyan buruku ta ruguje tamkar a mafarki.

Umma ta yi mata baƙin ciki ta janyo ta ƙasa gashi ta ƙare babu Faris ɗin babu Maheer.

Lumshe idanunta tayi tana mai matso wasu sabbin hawaye da suka zame mata abin ci da shan ta ta miƙe zaune daga kwancen da take tare da janyo wayar ta ta sake dailing numbern Faris a karo na barkatai but still har ta tsinke bai yi responding ba.

Muryar Umma ta ji a kanta wacce ke ɗauke da zallar rarrashi ta ce.

"Ki yi haƙuri Rabi'a..."

Tana mai rushewa da wani sabon kukan tace.

"Wani irin in yi haƙuri don Allah Umma! Kin riga kin gama dani..."

"Haba Rabi'a! haka fa Allah ya tsaro. Yanzu ki yi ta ƙoƙarin ƙara kiran Faris ɗin. Ko shi ai bashi da wata makusa ƙaddara dai ce ta faru..."

"Umma ya ƙi ya ɗaga.."

Jinjina kai ta yi ta ce.

"To ki bar min shi a hannuna In sha Allahu gobe zan tafi wurin malam..."

Da sauri ta girgiza kanta ta ce.

"A'a nidai Umma! Ƙila wancan shegen maganin da kika kawo min shi ne silar ruguxa komai wanda har asara ya janyo min bayan rasa Maheer da na yi. Daman can bake kika haɗani da Faris ɗin ba saboda haka da kaina zan yi ta trying har na samu ya dawo gare ni."

"Uhm? To ai nima na goyi da bayan hakan, domin Faris dai su ma gidansu masu kuɗi ne wanda wallahy muddin kika aure sa za ki huta har nima na samu. Sannan kuma ga shi ma shi ka ɗai ne a wurin ubansa ba shi da ƙanne wanda suke ciki ɗaya ballantana 'yan uba. Dukiya idan yau ubansa ya faɗi ya mutu ta zama tasa halak malak... "

"To amma Umma ai yanzu Baban na sa ya yi aure, kuma budurwa ce ya auro kinga kuwa dole za ta haihu, ko Ince haife-haife tunda ba za ta yarda ta zauna haka kawai ba, daman kuma ko ba'a faɗa ba don dukiyar ne ta aure shi..."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull